Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min hankali kaga yanda zamu kare da kai, wallahi sai kayi nadaman zuwanka duniya." cewar Khairat.

"Ke." mutumin ya fad'a cikin daga murya.

"Wai kinsan dawa kike magana? to mune garin nan dan mune gwamnati."

"Mtsssssss." wani dogon tsaki da Khairat taja.

Gyara tsayuwa tayi ta rik'e k'ugu da hannu d'aya tana nunashi da d'aya hannun tace "kasan ni kuma wacece, duk kasancewarka a cikin gwamnati nasan baka kai mahaifina ba, kasan koni yar wacece? to ni yar Mani Bukar ce, kuma nasan kasanshi."

Jim ya d'anyi kafin ya basar yace "to saime dan kina d'iyar Mani Bukar, cemin za kiyi ragowar sojoji, ke yanzu duk da abinda ya faru dake amma kike wannan bud'a hanci, kamar wata wacce take cike da budurci."

Ranta ne ya b'ace duk da hawayen da suka taho mata, matsowa ta sakeyi daf dashi za tayi magana amma sai Umar Faruk ya d'auka ko zata mareshi kamar yanda shima ta masa, da sauri ya shiga tsakaninta dashi yana kallonta yace "waike me yake damunki ne?"

Kallon sani tama Umar Faruk amma kuma tana ji ba zata iya tunashi ba, wani tsakin ta kuma ja ta bisu da harara ta wuce abinta, Umar Faruk binta yayi da kallo kafin yaga in da ta shiga shima ya juya ya hau mashin d'inshi yana tunanin maganganun da mutumin ya fad'a mata.

Tana shiga ta fara waige waige ta in da za taga mahaifin nata, can ta hangoshi da wata qosashiyar mace da gani kasan ba qarya babbar macece, a hankali ta fara takawa harta tsaya bayansu basu sani ba, cikin taushin murya tace "sannu da jin dad'i."

Juyowa sukayi dukansu in da jikin Papa ya d'auki rawa, matar kam a wulak'ance ta fara kallon Khairat, matsowa tayi kusan matar za tayi magana Papa ya gaggauta jan hannunta yayi gefe da ita ya fara magana cikin rad'a.

"Khairat meya kawoki nan?"

"Kamata yayi tambayi ne yaushe na shigo garin."

"Naji yaushe kika zo?"

"Papa wacece waccen matar, kenan har yanzu baka daina abinda kake ba?"

Hannunta ya rik'e yace "a'a shalele, wallahi na daina duk abinda nake, na riga dana tuba da duk wani aikata zunubi, wannan matar ma ba wani abu bane tsakaninmu a yanzu, kawai tana so ta b'ata min suna ne, shi yasa nake binta a hankali."

Kai ta girgiza tace "Papa, kamar ya kake binta a hankali? me take maka?"

"Khairat, wannan matar tace tana d'auke da cikina, kuma ta kaini asibiti an tabbatar min da hakan, kinga dole na bi a sannu."

Juyawa tayi ta kalli matar sannan ta kalli Papa tace "wannan matar bata da wani ciki, kuma yanzu zan tabbatar maka da haka."

Tana fad'a ta tunkari matar, tsaye tayi gabanta tana murmushi tace "Papana ya fad'a min na kusa samun kani , rashin yarda da banyi ba yasa nace bara duba da kaina na gani."

Tana fad'a ta kamo hannun matar ta fara kallon tafin hannunta wai ita tana so ta gano ciki🀣, sakin hannunta tayi tana mata kallon tuhuma, k'ara matsawa tayi kusanta ta bud'a ijiyarta tana kallo, matar kam duk tsoro ya kamata dan haka ta tsaya ma, sakinta tayi ta kalli Papa tace "babu wani ciki a tare da ita, wahalar da kai kawai take yi, da alama ma kamar ba zata iya d'aukar ciki ba."

"Inji uban wa? wallahi ko banda ciki yanzu ni nasan ina haihuwa."

Kallon Papa tayi tace "ka gani ko, ko makarantar koyan likitanci ban tab'a shiga ba, amma ta bayar da kanta saboda tana tunanin ni ma'aikaciyar lafiya ce."

Soshe soshe matar ta fara na rashin gaskiya a hankali ta aje kwandon hannunta wanda take zuba kayan data d'auka, tafiya ta fara yi su kuma suna kallonta, saida ta d'anyi nisa ta juyo tace ma Khairat "kin kub'utar da ubanki."

Murmushi ta mata tace "sai dai ki kama uban wani amma ba nawa ba."

Tana fita Papa ya shafa kan Khairat yace "Allah miki albarka shalele, gashi kin kub'utar da Papanki."

Tafiya suka fara yace "ina alfahari dake gimbiyata."

Ba tace komai ba har suka shiga mota yana tuki har suka isa gida, zaune suka samu Mamie a falo ko hijab d'in jikinta bata cire ba haka ma kayansu na gabanta, zaune Papa yayi yace "ya kike zaune haka?"

Kallon Khairat Mamie tayi tace "ki shiga ciki za muyi magana."

Wucewa kawai tayi ta shiga d'akinta, wanka ta fara tana tunanin fuskar data gani, bud'e idonta tayi duk da ruwa na sauka a kanta tace "Umar Faruk ko? tabbas shine."

Tab'e baki tayi ta ci gaba da wankanta harta fito ta shirya cikin dogon wando fari da pink d'in riga mai siraren hannuwa, turare kawai ta shafa ta d'auki abin sauraronta ta makala a kunne ta fara tik'ar rawa abinta.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣3⃣


Papa ne ya gyara zama yace "ina jinki, dan da alama akwai magana sosai a bakinki."

"Hakane, kuma mai mahimmanci ce maganar."

"To ina jinki."

Saida ta kalleshi tace "baban Khairat, gaskiya ina so ka mata aure, bana so yarinyar nan ta jawo mana wata magana, idan zai yiwu gaskiya bana so aurenta ya wuce wata d'aya."

"Toh, meya faru ne haka? wani abun tayi?"

"Eh, in har mukayi wasa wallahi Khairat zata iya auren wannan yaron Raj, wanda hakan kuma bai dace ba, ni kuma bana so wani abu ya faru dan yaran yanzu zasu iya yin komai akan abinda suke so, shi yasa nake so ka d'auki maganar da mahimmanci, dan a gaskiya wata d'aya ya wuce banga Khairat a d'akin mijinta ba, tofa zan koma in da na fito dan aurenka ne zai mutu."

Yanda tayi maganar ya bashi dariya, amma saiya had'eta yace "Mamien Khairat kenan, yau da alama da rigima kika shigo garin nan, amma fa karki manta abinda kike so ayi kamar za'a tilastata ne akan abinda bata so."

"Ba wani nan, ya zama dole ka kauda ganinka daga b'acin ranta, in ba haka ba dama babu abinda za kayi."

"To naji, yanzu bara na kirata naji koda wanda take so."

Yana fad'a ya fara kwalla mata kira, amma ina ta toshe kunnuwa da abin sauraro koji ba tayi, saida Papa ya tashi ya bubbuga k'ofar da qarfi sannan ta bud'e tana kallonshi, "kizo." kawai yace ya koma falon.

Bayanshi ta biyo harta zauna kujera mai fuskantar tasu, ganin sun kafeta da ido yasa ta cire abin kunnuwanta tana kallonsu, Papa ne ya kalli Mamie ya kalli Khairat yace,

"Shalele, mahaifiyarki ce ta zo da wata magana mai girma, kuma na goyi da bayanta, shine nace bara naji ko akwai zab'inki?"

Da kai ta masa alama da me kenan, d'orawa yayi da "ina so naji ko akwai wanda kike so a cikin zuciyarki? saimu tattauna dashi."

Wata shek'akk'ar dariya tayi tace "wai kun gaji dani ne da kuke son aurar dani kome?"

Papa ne yace "a'a shalele, aishi aure shine darajar 'ya mace."

Mamie kuma tace "ai kin kai munzalin da za'a gaji dake d'in, shekara ashirin da biyar ai ba shekara sha biyar bace."

Tsaye Khairat ta mik'e tace "kaji ko, to wallahi babu wanda zai min aure ban shirya ba, kuma me yasa baki fad'a masa abinda ya faru a jiya ba, baikona fa kika dakatar."

Wucewa taje tayi Papa ya kalleta yace "to baki fad'a min wanda kike so ba?"

Tsaye tayi ta kalli Papa tace "ni babu wanda nake so, har yanzu ban samu wanda ya dace ba."

Tana fad'a ta juya Mamie ta bita da ido tana fad'in "kaji kuma, jiya fa hannu ta mik'a wani zaisa mata zobe, amma yau tana cewa bata son kowa."

Papa ta kalla dake dariya tayi tsaye tace "shikenan tunda kun mayar dani mahaukaciya."

Da sauri ya tashi ya rik'o jakar data d'auka yana fad'in "haba madam, kiyi hak'uri ki bar min komai a hanuna, insha Allah za kiga auren Khairat da idonki harki saka mata albarka."

Zuciyarta ce ta karye ta kalleshi tana zubar da hawaye tace "dan Allah kayi wani abu dan ganin Khairat tayi aure, wallahi ina jin tsoron faruwar wani abun marar kyau, ka sama mata miji na gari daya dace, wanda zai d'orata akan addininta sannan ta gyara rayuwarta."

Hannunta Papa ya rik'e yana kallonta yace "zan iya baki zab'i?"

"Zab'in me?" ta fad'a tana share hawaye.

"A gaskiya Na'ima a yanzu babu abinda nake so kamar naga Khairat ta fara sabuwar rayuwa mai kyau da tsabta, in hai muna so haka ta faru sai mun had'ata da jigo, kinga kuma a duk cikin masarinta dana sani banga mai wannan nagartar ba, amma bansan ko ke zaki iya samoshi koda a cikin danginki ne?"

Shiru Mamie tayi dan sosai ta gamsu da bayaninshi, amma kuma saita kasa tuna komai dan haka tace "a'a, karfa muje wajen neman na gari kuma mu had'ata da bata gari, kawai ina ganin tunda ga Mujahhid nan d'an uwanta ai sai a had'asu."

"Umm hakane, to ki kwantar da hankalinki insha Allah gobe da safe zanje na samu yaya *Suleiman* sai muyi magana."

"Amma kana ganin Khairat ba zata bada matsala ba? danni yarinyar nan halinta sai ita fa."

"Ki barta, wannan karan dai kam zan nuna mata ni mahaifine, zan shawo kanta da yardar Allah."

Cike da jin dad'i Mamie tace "gaskiya naji dad'in haka, Allah ya k'ara mana shiriya."

"Ameen, ban fad'a miki bane, amma harna fara zuwa islamiyya ta manya, daga sallah magrib zuwa insha, kuma a yanzu babu abinda ke min dad'i kamar kasancewata a majlisi na ganni gaban malam ina d'aukar karatu."

Cikin nuna tsatsan farin ciki Mamie ta fad'a jikinshi tace "hakan yayi kyau, gaskiya ka kyauta, Allah ubangiji ya yafe kurakurenka na baya."

"Ameen." ya fad'a tare da sauke ajiyar zuciya ya sake matseta.

😎 _Daga nan dai na bar gidan nayi nawa gidan nima._


*Tunda safe* koda Papa ya gama kari ya fita bayan Mamie ta bishi da addu'ar fatan nasara, Khairat kuma na d'aki na bacci lokacin tashinta baiyi ba.

Yaya Suleiman yayi matukar mamakin ganinshi a bazata haka, amma kuma farin cikin ganin d'an uwan nashi wanda yake masa wuyar gani yasa bai nuna a fuska ba har saida ya samar masa masaukin daya dace sannan, yana zuba masa lemon a cup yace "gaskiya fa ka shammaceni sosai, irin wannan bazata haka kuma da sassafe."

Cikin dariya yace "gaskiya dama nasan zansha wannan maganar, wallahi kawai cewa nayi zaifi nazo da safe dan wannan lokacin ne zan iya samunka gida."

"Gaskiya kam, dan ina shirin fita ma yanzu."

Zaune yayi suka gaisa sosai kafin shiru ya biyo baya, yaya ne yace "kamar da magana ko Ousman? fad'i ina jinka, meke faruwa?"

"Babu komai yaya, ba wata matsala bace, nazo ne akan maganar 'yarka da kuma d'ana."

"Wai kana nufin Khairat da Mujahhid?"

Kai ya girgiza yace "eh su, naga kamar lokaci yayi daya kamata ace mun had'asu tunda ba yara bane."

Duk da yaya Suleiman ya d'anji wani abu amma dai kuma ba komai bane, cikin farin ciki yace "ranar daka saka kazo ka fad'a min, ko kuma ka zo kawai ka sanar danine dan nasa albarka a ciki?"

Dariya yayi yace "yaya kenan, ai kaine uban 'ya, dan haka kai muke jira kasa mana rana."

Dariya shima yayi da k'arfi yace "haba dai wasa kake, ai duk diyanka ne dan haka kasa ranar data maka kawai."

Papa ne yace "amma kafin musa ranar aida munji ta bakin Mujahhid d'in ko? dan kasan yara fa, watakila bai shirya ba ko kuma yana da wani tsarin a ransa."

"Haba dai Mani, yaranmu ne fa mu muka haifesu basu suka haifemu ba, kawai ka fitar mana da ranar, tunda yana da aikinyi kawai aurene ya gagara sai yawo a gari tare da abokai, idan kuma kai kana jin tsoronsu ba zaka iya ba ni saina saka ranar."

Dad'i Papa yaji dan haka yace "to ba komai hakan ma ai yayi, kawai ka tsayar mana da lokacin, sai muyi fatan Allah ya nuna mana ranar da alkairi."


"To tunda kace haka, yanzu mu barshi nan da wata d'aya, hakan ya maka?"

Wani sabon dad'i ne ya sake kashe Papa dan jin ansa daidai da lokacin da Mamie ta diba , da sauri yace "hakan ai yayi yaya, Allah ya nuna mana ranar, Allah ya tabbatar mana da alkairinsa."

"Ameen ameen, kawai kuje ku fara shirye shirye, muma tanan wajen zamu fara, duk da ma dai abun duk gidane."

"Gaskiya ne yaya, kuma da wannan nake maka albishir d'in dauke muku duk wata dawainiya, hatta gida da zasu zauna a ciki ni zan bayar insha Allah."

"Masha Allah, to hakan ma yayi Allah ya sanya alkairi."

*A haka* suka tsayar da maganar auren Khairat da Mujahhid, tun a hanya Papa ya kira Mamie ya fad'a mata, wai zo kaga farin ciki wajen Mamie marar misaltuwa, sai dai Papa yace karta fad'ama Khairat sai zai fad'a mata yanda zata fahimta, suna gama waya Mamie na zaune kawar Khairat ta shigo da sallama, amsawa Mamie tayi cikin daure fuska saboda tasan k'awacen 'yarta da *Rashida* ba alkairi bane, cikin ladabi ta zauna gefen Mamie tace.

"Mamie ina kwana?"

"Lafiya lau, daga gida a ke?"

Saboda jin tambayar wata iri yasa ta d'ansha jinin jikinta tace "eh Mamie daga gida nake, dama nazo ganin Khairat ne, jiya take cemin ta dawo gari."

"Ina fata dai ba fita za kuyi ba ko?"

"A'a Mamie, ai yanzu mun daina fita in ba da rana ba."

"Kice dai kun shiga hankalinku."

"Gaskiya kam Mami."

Kallonta Mamie tayi tace "Rashida, me zai ku nutsu kusan cewa annabi ya faku, Rashida zaifi muku ku fara neman ilimin addini, ku koma islamiyya tunda ba'a tsufa da neman ilimi, kuma bokon nan kunyishi keda k'awarki iya gwargwado, dan Allah ku koma in da zaku san ubangijinku da yanda zaku bauta masa domin tsiranku duniya da lahira."

A kunyace tace "insha Allah zamu koma Mamie, mun gode sosai."

Tashi tayi tace "bara na shiga ciki, nasan mutuniyar bacci take har yanzu."

"Umm." kawai Mamieta fad'a danta lura Rashida bata wani d'auki zancen da muhimmanci ba, binta tayi da kallo ganin kayan dake jikinta itama dai kamar Khairat d'in sai dai ita ta fita jiki hakan yasa matsatsin kayan ko kyau basa mata.


Kwance take akan makeken gadonta rufe ruf da zanin rufa pink saboda sanyin da d'akin ya d'auka na ac, zaune tayi akan gadon ta daddab'ata tana fad'in "macho, machota tashi gani na zo."

Dogon tsaki taja tana bud'e zanin daga kanta, saida ta tashi zaune sannan ma ta kalleta, jingina tayi da kan gadon ta kalleta cikin muryar bacci tace "infa gaki saime, me zaki min? hada wani zuwa ki tasheni."

Shiru tayi ba amsa dan tasan ta tab'o dala ba ganmo, ganin ba tayi magana ba yasa ta sauka daga kan gadon ta nufi ban d'aki tana tattare gashinta daya bazu wanda tun tana kwance aka since matashi.

Jin qarar ruwa yasa Rashida ta tabbatar wanka ta fara hakan kuma yasa ta gyara zama, dan tasan awa d'aya ce zata fito da ita daga bayin, bugu da qari itama ba zata iya barin gidan ba har saita samu abinda take so, dan in bata jira ba zata ma kanta asarar kud'i kuma tana da tabbacin zata samu.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣4⃣


Fitowa tayi da d'aurin qirji iya cinyoyinta taja kujera ta zauna a kai tana kallon kanta a madubi, mai take so ta shafa amma tana jin k'iwa, Rashida ce ta taso ta tsaya bayanta tasa hannu tana shafar kanta tana murmushi, ta madubi ta kalleta tayi qaramin tsaki, sun jima a haka babu wanda yayi magana, saida ta gaji da miskilancinta sannan tace "me kike so?"

Kallonta tayi ta madubi amma ba tayi magana ba, sake cewa tayi "kiyi magana macho, nasan wani abu kike so shi yasa kika zo."

Kai ta sosa ta fara magana "eh to, wallahi macho, gidane babu kudi gashi babu kayan abinci, mun shiga wani hali saboda ba kya nan, yanzu ma banso na zo wallahi dole ce tasa na zo."

Juyowa tayi ta kalleta tace "d'auko min kayana nasa."

Juyawa tayi ta nufi wajen kayan nata tana hararanta ta qasan ido, da hannu ta nuna mata wanda zata d'auko mata, tana kawo mata tace "ki kira min Biba."

Nan ma a qufule ta juya ta fita, Khairat ma nayin hakanne da gangan dan abotarta da Rashida bata da wata mamora, shi yasa wani lokacin take sata aikin ma da bai kamata tasa ta ba idan ta lura akwai abinda take so a wajenta.

Ta riga Biba shigowa kafin itama ta shigo tace "gani Hajia."

Ciki ciki tace "ki wanke hannuwanki a ban d'aki kizo ki shafa min mai."

Saida ta kalleta sannan ta shiga dan wanke hannuwan, haka ta fito ta fara shafa mata man a jiki har suka ida Rashida na zaune, da taimakon Biba tasa kaya sannan ta zauna gaban madubi ta murza powder kad'ai sannan tasa Rashida ta d'aura mata d'an kwali, masha Allah tsaf ta fito cikin riga da siket d'in atamfa wacce tasha d'inki tsadadden.

Saida ta gama kallon kanta a madubi sannan ta juya ta bud'a wani coffre ta d'auko poshet (post) ta tsaya gaban Rashida, budawa tayi ta d'auko kudi yan jikka goma goma sababbi guda biyar ta mika mata, tana sa hannu ta karba Khairat ta juya zata fita Rashida tayi saurin rumgumota ta baya tana fad'in,

"Oh, mon chouchou, na gode sosai Allah bar min ke ta wajena."

Murmushi kawai tayi ta janye kanta daga jikinta ta fice, binta tayi a baya haka ta sauka daga kan matakala kamar wata sarauniya, kai tsaye wajen cin abinci ta nufa ta zauna saman kujera, Rabi ce tayi saurin zuwa ta fara zuba mata farfesun kayan cikin rago da kuma soyayyar kaza ga kuma doya da aka mirginata cikin k'wai, fresh milk ta d'auko mata ta zuba mata sannan ta fara ci, Rashida kam an samu kud'i ko ta abincin bata bita, sallama tama Mamie sannan ta kalli Khairat tace "macho na tafi, sai mun had'u."


Ba wani sosai taci ba, dan Khairat a rayuwa bata san k'iba, dan d'an kumarin dake gareta ma yanzu jinshi take a wani babbar matsala, dan haka take kula da jikinta sosai amma bata son motsa jiki saboda ragwantaka, tana kammalawa ta komo falo ta zauna kusan Mamie, hankalinta na a wayarta Mamie kuma na kallo tana d'an satar kallonta wani lokacin tana murmushi.

*****************


*Umar Faruk* kuma tun jiya daya ga Khairat ya kwana cikin tunanin halin daya ganta, sam baiyi tunanin haka daga gareta ba, ya d'auka zata canza ko dan abinda ya faru da ita amma sai yaga akasin haka, ta wani b'angaren kuma haushin abinda wannan mutumin ya fad'a yake ji, da haka har safiya tayi ba tare da yayi wani baccin kirki ba, duk lokacin daya farka Khairat ce zata ziyarci tunaninshi da ganinshi.

Haka kawai yaji yana burin ya sameta a wajen aiki, shiri yayi sosai cikin qananan kayanshi bak'ar riga mai dogayen hannu da wando kalar qasa, yana shiga ma'aikatar ya fara duba wajen ajiye motoci ko zaiga motarta amma babu, duk da haka bai sare ba bayan ya shiga ciki ya aje jakarshi cikin dubara da sand'a ya nufi bureaunta, lekawa yayi ta madubi amma babu kowa kamar dai yanda yake, wata ajiyar zuciya ya sauke cikin sanyin jiki ya dawo mazauninshi, yana zaunawa ya fara tambayar kanshi wai me yasa ya damu da son ganinta ne, tsaki yayi kawai ya fara aikin gabanshi.


****************

Khairat ce ta 'kwalla kiran Biba, tana zuwa tace ta d'auko mata jaka a d'aki da gyale, cikin 'yan mintuna ta dawo da jaka da takalma da gyale duk kalar atamfar dake jikinta, tana sakawa tayi hanyar fita Mamie tayi saurin cewa "sai ina kuma Khairat?"

"Mamie zan lek'a bureau ne naga meke faruwa acan, saina dawo."

Harta wuce Mamie tace "zo mana gimbiyar Papanta."

Dawowa tayi ta tsaya gabanta, tashi tayi tsaye ta shafi fuskarta tace "Allah ya miki albarka Khairat, Allah ya baki yaya na gari, Allah ya kiyaye hanya kinji ko."

Cikin jin dad'i ta rumgume Mamie tace "yau dai da wayona naji addu'ar sa albarka ta fito daga bakinki, na gode Mamiena, saina dawo ba zan jima ba."

Sumbatar goshin Mamie tayi ta fita cike da farin ciki yau Mamie ta mata addu'a, ita kanta Mamie sai taji ba dad'i dan in zata iya tunawa gaskiya ta jima rabon data mata addu'a irin haka.

*Kuskure da iyaye mukeyi sakacin yiwa yara addu'a, wasu na ganin laifin Khairat data zama fitsararriya, amma bansa Khairat ta zama haka ba har saida na samu dalili, Mamie ta kasance mai zuciya da yanke hukunci cikin hushi, hakan ya janyo tun Khairat na qarama ta daina daina janta a jiki bare tasata a hanyar data dace, hakan kuma bai dace ba ko kad'an, yaro ko yana qarami kake masa addu'a zan sai kana masa, uwa uba kuma addu'ar na bibiyarsa ta alkairi ko akasin haka, mu kula iyaye Allah ya bamu ikon tarbiyantar da yaranmu.*


Da takonta na qasaita ta shigo wajen, kallon Abba yayi kowa da komai take da kyau, Umar Faruk daya duqufa da aiki, gabanshi ne yaji ya tsinke ya fad'i hakan ya tilasta masa juyowa da k'arfi, kasa dauke idonshi yayi daga kanta, duk da ba murmushi a tare dashi amma kuma fuskarshi a sake take, ganin yanda kowa ke kallonta kamar da wani abu a jikinta yasa ta tsaya waje d'aya, sake kallon kowa tayi dake wajen ta girgiza kai tayi murmushin takaici.

A hankali tace "kowa ni yake kallo saboda yanzu kuna ganin kamar na zama daban a cikin mutane, kowa so yake yaga ina cikin damuwa, ni kuma abinda nayi alk'awarin ba zan shiga ba kenan har abada."

Tana fad'a ta juya a fusace ta nufi in da ta aje motarta, Umar kuma buga tebur d'in dake gabanshi yayi tare da fad'in "kai."

Da gudu ya tashi yabi bayanta mutanen kuma suka bishi da kallo, Ishaq abokinshi ne yayi murmushi ya kalli na kusa dashi yace "dama ace duk soyayyar da aka fara da qiyayya to tafi zafi."

"Soyayya suke dama?" cewar mutumin.

"Kai ai basai an fad'a ba kasan akwai soyayya wannan wajen, watakila basu fahimci hakan ba."

"Lallai ko abokinka ya d'auko dala ba gammo, to ina had'in kifi da kaska? ai wannan qarmanje ne."

"Ban gane ba, ita kasan meye ra'ayinta to da za kace haka?"

Cewar mutumin "ai ko ban sani ba aikinta ya nuna abokinka baya da wani girma da qima a idonta, tunda nidai banga ko kallonshi tayi ba, zaifi ka bashi shawara ma tun wuri ya fitar da abinda ke ranshi, dan wahalar banza zaisha."

"Ai kuwa in dai har gaskene, to wallahi zaka sha mamaki, dan kana nan zaune za'a gayyaceka daurin aure."

"Tare dani dashi da kai za'a gayyata." cewar mutumin yana kama aikin gabanshi.


Tana daf da shiga mota Umar Faruk ya fito da gudu, juyawa tayi ta kalleshi ta tsaya saida ya karaso, tsaye yayi ya kuma rasa me zaiyi sai yanzu yake jin haushin abinda yayi, juyawa yayi zai koma ciki tace "kazo ka tambayeni me nake ji ne?"

Juyowa yayi yace "a'a, akan me?"

Dogon tsaki taja ta bud'e motarta ta shiga taja tayi gaba, shima ciki ya koma yana tsananin jin takaicin abinda ya aikata, shin me yasa yayi haka???

*****************

Tun yamma da Mujaheed ya dawo gida mahaifiyarshi ta fad'a mashi halin da ake ciki tare da zigashi akan karya yarda, bud'ar bakinshi cewa yayi "Mama bama sai kince ba, wato ni zasu rainawa wayo ko? kafin ta zama ragowa ina biyarta amma tana wulak'anta ni, su kuma sun biye mata aka su ba zasu bata wanda bata so ba, yanzu kenan sun saduda ne shine za'a kawo min ita ni d'an iska ko, to wallahi basu isa ba."


Tunda

Please Login or Register in order to submit comment