Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KWATAR KAI 1


NA


FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA




Godiya tatabbata ga Allah dayasake hadamu acikin wani sabon littafin,tsira da amincin Allah sukara tabbata gashugabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidan sa baki daya,

Wannan littafin kagaggen labarine ,bawai yafaru akan wani kowata bane,aa kirkirarsa nayi,

GARGADI!!!!!!!
Banyadda ajuyamin wannan littafin tawata sigarba harsaida izinin marubuciyar.

********************************

Assalamu alaikum,yayi sallama tare da dage labilen dakin yashiga.
Tana zaune bisa kujera ta amsamai,babu yabo babu fallasa,yasamu wuri yazauna gefenta.
Tayimai wani irin kallo,shima yakalleta sannan yasadda kansa kasa,yace
Suwaiba yayada
Tace damefa?
Yace nagane kinayimin wani irin kallo,kamar kinga Mara gaskiya.
Takara maida hankalin ta sosai akansa,tace yo aiganinayi kashigo dakina yanzun,kumani banga amfanin yin hakanba.
Yakalleta cike da mamaki,yace yaufa kwanana TALATIN kenan dayin aurennan,kuma inaga aikamar iyakar kwanakin dakikabani kenan ko?naga suncika shiyasa nadawo gareki yau.
Takalleshi ayatsine,takauda kanta,wani takaici yakara isarta,takuma daure cikin rashin damuwa tace:yo har kwanakin suncika?ninaga sunyi sauri.
Yayi dariya yace suncika mana,yaunake dawowa dakinki,ai iyakar abinda dama kikabani kenan,kuma aikinga baikamata...........
Tadaga mai hannu tare dafadin kaga! Dakata Nasser!batambayarka nayiba!nadai baka abinda kakeso,kuma burinka yacika,kayi Amarya!nayarje maka kaje kayi WATA GUDA adakinta,kuma kayi to magana tame?aiba tambayarka nayiba.
Yace AAh !toaini sainaga rankine kamar bayadda nasaba ganinkiba,kuma yau nadawo dakinki,tsawon lokacin danadauka awurin Amarya,yau kuma nadawo wurinki,aikamata yayi inganki kina fara'a,da dokin ganina,kema kizama tamkar Amaryar.
Tace niasuwa!!aibankai wannan matsayin awurinkaba,Nasser danakai wannan matsayin awurinka!kanajina kamar Amarya,dabaka dauki tsawon kwanaki TALATIN awurinta baka waiwayeniba!kobanza nasan waceceni awurinka!nasan matsayin daka ajiyeni!kabullomin ta hanyar da Amaryarka zata rainani!domin tasanniba komai bace awurin mujina!kuma kasiyoma kanka rashin zaman lafiya agidanka!!
Yace:to dakata suwaiba,nagane inda kikadosa,to amma kuma naga ai kwanakin nan kekika dibarminsu baninadiba dakainaba,kekikaga Dama kikabani,kuma nayi,tomiye kuma abin tashin hankali aciki?
Tace:kuma kayi??saboda bakasan darajar matarkaba !kayi watsi da ita tsawon WATA GUDA,saboda kayi Amarya!
Yace Toni miye laifina aciki?
Tace aibazaka ganiba!abinda idanunka sunrufe!baka ganin kowa sai Amaryarka!!taya za'ayi kaga kayi badaidaiba?aikomai kayi da ita daidaine!
Kawulakantani!!!kabiyomin ta hanyar da Amaryarka zata daukeni babakin komaiba!!tunda har mujina zai iya watsidani NA tsawon wani lokaci,batare kuma daka damuba!kaga kenan dani da banza duk dayane!!!
Yace suwaiba inda nasan Karin kwanakin dakiyimin zaizama haka dabanyiba,danasan ranki zai baci akan cika umarnin dakikabani da banyiba,amma tunda hakan tafaru kiyi hakuri,abarshi komai yawuce,imma kuskurene nayi tona dauka,don Allah kiyi hakuri.
Tace aidama iyakar abinda zaka bani kenan,nikuma kacuceni kacuci banza!!to kakwana da sanin cewa,idan aka kasa samun zaman lafiya agidanka daga irin rashin adalcinkane!!
Yace in Allah ya yadda bama abinda zaifaru,sai zaman lafiya,ai Hauwa'un tanada hakuri
Tace batambayarka nayi halintaba!nidai inta kawomin raini,adalilin abinda kayimin bahakura zanyiba.
Yace abar maganar,Uwar guda sarautar mata!duk yadda kikeso aihakan za'ayi,mulkin gidanfa ahannunki yake,bawadda ta isa takwace maki wannan sarautar,duk yadda kikabi dagidanki ahaka za'abishi,wane umarni zaki bayar kuma yanzun?yafada acikin wasa tare dashafo fuskarta.
Bayan kwana biyu ,suwaiba nazaune tare da kawarta FARIDA,wadda takawo mata ziyara,sunata fira.
Suwaiba tace:kenifa Farida gaba daya shawarar dakikabani banji dadintaba,hakanan abanza kinsa naba mujina damar yayta kwana dakin Amaryarsa harnawani lokaci,amma bawani abinda yasauya,sunason junansu haryanzun,kuma kekikacemin inbasu lokaci sugama dokin juna tukunna,sugundiri juna,ammani banga alamar hakanba,nabasu danata abanza!!!
Farida tace banganeba?kinanufin kice suna dokin junansu haryanzun?to wannan wace irin mayyar kishiyace kikasamu?
Toni bari kiji,hakanayima mujina,acikin sati biyu sunfara gundurar juna,saigashi inakallo sukafara tashin hankali,da fadace-fadace,intakaice maki auremma baije ko inaba,dole angulu takomo gidanta natsamiya,muka dawo mukazauna dagani saishi.
Suwaiba tace Toni dai wannan shawarar taki batayimani amfaniba,kedai tayimaki,ammani batauiba,don haryanzun rawar kai yake da Amaryar nan,tun INA danne kishina harnafara gajiya,wai dama haka Namiji yake idan yakara sabon Aure?kiga dake da babuke acikin gidamma duk daya,gaba daya idonsa yarufe bayaganin kowa sai Amaryarsa,wallahi Farida na yadda idan mace bata danne zuciyartaba,alokacin damujinta yakara sabon Aure,zata iya kashe nata auren,domin kuwa wani rawar kai zakiga yanayi tamkar baitaba aureba sai akanta,wani abimma idan sunayi tamkar basa ganin idon kowa akansu.
Farida tace shiyasa Nina danaga mujina yafara wannan rawar kan saboda yayi Amarya,saina barmashi ita,nace yaje yayta zama daita nawani lokaci yagama dokin sannan yadawo gareni,amma inkika cika shigemasu ranki kullun baci zairikayi,gara inya gama dokin yadawo gareki,kinga saiku zama dai dai.
Humf!!suwaiba tayi ajiyar numfashi tace:kedai kinyi nasara,ammani banga alamaba,kullun suna manne dajuna,Farida nayi hakuri sosai nakauda kaina ,amma duk dahaka suna cikani!!!
Baburina inkoretaba,amma sonake muzama dai dai nida ita awurin Nasser ,wannan kirinkin dayakeyi akanta yaisheni!!waiyaushene zamu zama dai dai nida itane?????
Farida tace kikarayin hakuri,kibada wani lokaci,kigani komai zaiwuce,saikin kara kauda kanki.
Suwaiba tace niwallahi gabadaya Nasser ma mamaki yakebani,kiga mutum kamar bashiba,nabashi KWANA TALATIN,amma kodan irimma jayayyarnan bayyiba,wai misalima yace yaya za'ayi inje inyi wadannan kwanaki adakin wata,aibai kamataba,ingaya maki Farida saiyayi mursisi,yaje yayi,kidamuwa bayyiba,harda wanuyimin godiya ,to idan yarinyar nan tarainani! acikin gidan nan,zaiga tashin hankali !!!domin kuwa shiya jawosa!shiya zubarmin da kimata a idonta.
Farida tace Ah!gaskiya baikyautaba,domin. Koni danacema mujina nabashi kyautar kwanakina yaje yayi shi adakin Amaryarsa gaskiya saida yaja,Nina kafe nace saiyayi,tokinga aikasan ankulaka,amma kawai daga cewa kaje kayi shikenan kamar dama kanajira,bawata jayayya,gaskiya bayyimaki halacciba,amma bakomai watarana sai labari,Nina tabbatar maki nan gaba saikun zama dai dai,amma saikin. Shanye damuwarki.
Suwaiba tace to aishine Abu maiwahala,nagaji! Farida nagaji!!!bazan iya ganiba,kibarni dashi kawai,tundashi baisan Alkunyaba,saimunyi fito na fito dashi ,kafin mudai daita.
Misalin karfe Tara nasafiyar ranar Asabar,yayi shirinsa tsaf!,zaifita,tataso dasauri tanufo wurinsa,tare dafadin fita zakayi?
Yace:e fita zanyi wani Abu?
Tace dama inaso zani gidammu,ko inshirya saika saukeni?
Yace yikiyi sauri kada kibatamin lokaci.
Tace to shikenan,sannan tayi sauri tashirya tafito,tabiya tayima Hauwa'u sallama,tare dafadin zamu fita,,sai mundawo
Hauwau tace saikun dawo,takalli Nasser tace love bye bye kadawo lafiya Allah yatsareminkai,sannan takalli suwaiba tace Aunty saikun dawo.
Suwaiba tace Allah yasa,sannan suka fita,acikin motarsa sukashiga,yaja suka fara tafiya
Yace kinsan wani Abu suwaiba?
Tace saikafada.
Yace:Abokina Ibrahim na funtuwa shine yake gayamani zayyi aure,watanni uku masu zuwa.
Tace ikon Allah komai da lokacinsa,saiyanzun zayyi aurefako?
Yace:e saiyanzun Allah yakawo lokacin,kingakenan inada biki.
Tace kwarai kuwa kaga saikatafi da Hauwa'u,itace bata taba zuwa funtuwaba.
Yayi dariya yace itama wannan maganar tayice koko?
Tace wane irin tayi kuma?dagaske nake katafi da ita.
Yace to ai inagudun kada amaimaitane,halinnakune na mata saiku,kuzakuce ayi Abu kuma daga baya yazo yadameku.
Tace:toaini gaba daya Nasser mamaki kabani,daga cewa jekayi wata daya,shikenan ko gaddama bakayiba kaje kayi abinka hankalinka kwance.
Yace toaini nasha irinhalaccinnanne naku namata kikayi Mani,ganinke shekara Hudu muna tare dake,shine kikatausayamata kikabata wadannan kwanakin,shiyasa banyimaki gaddamaba,
To yanzun kuma ga tafiya tatashi,kince intafi da ita,kinga aidole insan kyautar taki iya bakice koko har zuci?
Tace dagaske nake kutafi .
Yace a'a duk wadda aiki yafada kanta ranar da ita zani,shikenanko?
Kafibtakarayin wata magana wayarshi tayi ringing yasa hannu yadaga.
Hello babyna yayadai?
Tace love yaya hanya?
Yace hanya gatanan munatabi,kinfara missing dinako?
Tace aiko kamar kasan abinda zan fada maka kenan.
Yace tokiyi hakuri kinji,yaumuna tare,indai nine ki kwantar da hankalinki,zandawo dawuri,duk abinda kikeso dani kinga saikiyi,yayi kissing din bakin wayar tare da fadin bye kijirani inanan dawowa.
Sannan ya yanke kiran,tare da kara maida hankalin sa abisa titi,yace wai haryanzun bamukai bane?
Ita kuma datake gefensa zaune tariga tagama cika makil tace:
Aiwai dama Nasser kaiya irin wadannan kalamanni bansaniba?waikokadauka kai kadaine acikin matar nanne?
Yace wani Abu kuma nayi?
Au!bakamasan abinda kayiba?tobari infito maka a mutum!!Nagaji!cin kashin karen dakukeyimin kaida Amaryarka ya isheni!!! Waini meka maidanine?dani da babuni duk daya!!kainifa nalura tunda kakara aurennan dokinnaka yaki karewa!adadin kwanakin dana Baku yatafi abanza kenan??tunda abin yakici yakicinyewa!!to gaskiya nibazan iyaba!!!
Yace yakikeso ayi?
Tace saukeni anan nafasa tafiyar!domin tafiya dakaima ba abinda zai haddasamin banda bakin ciki!kasaukeni nace!tafiyar nafasa!!!!
Yaja jirki yatasaya tare da kallonta yace waini suwaiba narasa abinda yake damunki,gaba daya kincanza.
Tace nicema nacanza?kaibakaga irin canzamin din dakayiba!aikaine kafara canzawa,nima nazame maka haka,kuma muddin badawowa kayi yadda nasanka daba,to haka zakaita ganina nima babu ranar dazan canza!!Aida bahaka kakeba!aurennan dakayi shine yadabarbartaka!!kuma indai bazaka dawo yadda nasankaba to haka zamuyita zama dakai!!babu ranar canzawa! Tabude marfin motar tafita dasauri,tare da tare mai adaidai ta tahau yajuya da ita gida.
Shikuma yana zaune yadorakansa akan sitiyarin motamar,yana tunanin irin wannan hali na Suwaiba ,shidai yasan sanda yake Neman aurennan dagoyon bayan ta akayishi,amma yanzun gaba daya tacanza,bata taba nunamai wani bacin rai ko rashin yadda sanda yake Neman aurennanba ,saiyanzun da Amaryar tashigo gida,kodadai haryanzun bata bude baki tacemin aurenne batasoba to ammani miyene na Abu akan saitahau ?shima yana nufin kishi take daitakenan?kodani bantaba ganin ko sa in sa tashiga tsakaninta da Hauwa'uba,suna zaune lafiya ,to ammani meyasa takeyimin haka?wane hali nacanza matane???
Tagirgiza kansa,tare dajin tafiyarma duk tasiremai,don haka yajuya kan motarsa shima yakoma gida.
Dakin suwaiba yawuce,yasameta zaune tayi tagumi da hannayenta,hawaye naci gaba da gudu afuskarta,gabanta yazo yatsaya tare dafadin.
Innalillahi wainnailaihirrajiun!Suwaiba menayimaki?miyekikaga nacanza maki?Wanda ada nakeyimakishi,yanzun kuma nadaina?menene yake tadamaki hankali gamedanine?
Tadago kai takalleshi idanu jajur tace:baikamata kayimin wannan tambayarba,yaya zakudaukeni sakarya dakai da Amaryarka sannan kazauna kana tambayata!inba wulakanciba aitasan inatare dakai dommiye zata kiraka?Kai kuma kasaki jiki kana fadamata wasu kalamai dani tunda nake bantabajin sunfito daga bakinkaba,ai abinda kukeyimin baro-baro yake afili,kaimakasani,basaikatsaya tambayataba.
Yace to intakirani ba matata bace?
Tace dama haka nakeso kafada!!yadda akaraba kwana,maganarma zan iyasawa Araba!!irin wadannan maganganun tahakura inkun shiga daki can kuyi abinku!amma ba'agabanaba,wannan aicinfuskane!!!taya za'ayi inajinka kana fadamata kalamai wadandani tunda nake bantabajin kafadamani irinsuba!bammasan ka iyaba,sai kawai dalilin ka kara sure saika bijire kacanza dabi arka da halayyarka!!dommiye hankalina bazai tashiba,?
Yatsugunna gabanta tareda dafa kafafunta,yace:kiyimin uzurin abinda zaifito daga baki na yanzun,yace wallahi suwaiba haryanzun nakasa gane laifina awurinki,saboda duk abinda nakeyi ganinake dai dai nakeyi,banayin kuskure,amma kuma ban fahimci manufarkiba.
Tayi saurin ture hannunsa daga jikinta,tace: aibazaka fahimtaba Nasser!soyayyar Hauwa'u tarufemaka idanu,baka ganin kowa sai ita!itakadaice 'yar lele awurinka,itakadai kakenunama tsantsar soyayyarka agareta,nikuma shikenan kagama yayina!!!
Humf!yayi ajiyar numfashi,tare dafadin,meyasa kikeso kifitomin da tsantsar kishinki ta haka?meyasa kike dafani da ruwan Dana kasa fahimtar na sanyine kona zafi?karki manta suwaiba,babu Wanda ya isa yaci zamaninsa sannan yaci nawani,shekara Hudu mukayi nidake muna soyayya,dommiye ita don taxo tayi na WATA DAYA rak!zaki tada hankalinki?kuma naga wata dayannanma aike kikabani shi,bada niyyar kaina nayishiba.
Tace nasan haka saita faru!waimeyasa kodayaushe Ku maza Azzalumaine???kai tsakaninka da Allah abinda kakeyima Hauwau a yanzun shi kayimin ada?
Yace harwandama yafi nata nayimaki.
Tace Toni bansaniba!kuma ban ganiba!ai abinda kuka iya fakewa dashi kenan?dazararkun kara sabon aure!sai kuyita wulakancinku darashin kunyarku agaban matanku,idan mace tanuna ranta yabaci,sai kuce Aida itama anyinata,haka,kuma naga Aida tawuce!inkuma ka isa KATARIYOTA tadawo baya!!
Yace to nadai gane manufarki,yanzun kwanakin dakikabani nayi adakinta,sunesuke damunki?toko maida makisu zanyi inkashe wannan wutar?
Saijin muryar Hauwau sukayi tadago labilen dakin,tare da fadin:
Dagabaya kenan!aiwadannan kwanaki tariga tayi asararsu!inbanda karamin tunani irinnaki,tayaya donkinbani kwana TALATIN da mujina zai gundureni?aisaidai mukara son junanmu!
Idan kuwa har Uwar gida zatayi tunanin tadauki kwanakin ta tabama Amarya waidon su gunduri juna ,totayi kuskure!ita meyasa tsawon shekarun dasukayi da mijinta ba sugundiri junaba?sai watace datake sha sha sha!!zata gunduri mujinta?!Toni da Nasser daram dam!!soyayyama bakiga komaiba,
Yayi saurin dakatar da ita tare da dagamata hannu cikin tsawa yace:kifita!!kifita nace!!mema yakawo ki dakin?
Suwaiba tace barta ta idasa abinda zata fada,koma miye nikai kajawomani!tadakatadimme?bayan tagama fadin abinda zata fada!!komadai nikai kajawomani!kaika fara zubarmin da mutuncina awurinta,shiyasa tasamu damar abinda take gayamin yanzun!!laifin gaba daya nakane!kaika bullo da hanyar da gidanka zaikasa samun zaman lafiya!saboda wallahi kaiba ADALUN MUJI BANE!!!kagama tozartani awurin Amaryarka!tunda hargashi tasamu damar datakeyimin labe.
Hauwa'u tace:nibazan iya baki mujina yayi kwana TALATIN adakinkiba,kidai dauka cewar wadancan kwanakin kinyi asararsu,tuna...........
Nasser ya katseta tare da turata waje,yace:fita da Allah!wayema yasakoki cikin maganarmu?yakoreta tabar dakin,sannan yajuyo ga suwaiba,yace:aiga irintanan!gashi nan..........
Tace kada kakatayimin magana!fita kaima!!kafita kabarmin daki!!niyanzun ba abinda zaka gayamin insaurareka!!!
Yace:amma ai..............
Tace kafita nace!!!!!
Cikin fushi yabar dakin,itakuma tazauna wani irin matsanancin kuka maisauti ya kwacemata.
Afusace yashiga dakin Hauwau yana fadin,waiwane irinneman fitinane wannan?yakukeso kumayar danine?meyakaiki dakinta Alhalin kinsan inaciki?wane irinneman tashin hankaline was nan??
Takaraso inda yake cikin sanyin jiki,tace:
My love bahakabane,takama hannayensa cikin shagwaba tace:,kwantas don Allah,samu wuri kazauna kaji.
Humff!yayi sassanyar ajiyar numfashi ,tadago ido takallai cikin fari,sannan tajawoshi tazaunar dashi bisa kujera.tace:
Nasan kumfita,amma bansan dawowarkuba,shine naji hayaniya adakin,koda naje kofar dakin zan shiga sainaji kana cemata.
To nadai gane manefarki,yanzun kwanakin dakikabani nayi adakinta sune suke damunki?toko maida maki suzanyi inkashe wannan wutar??
Tobansan sanda naji hankalina yatashiba,domin kuwa babu abinda natsana irin kayi nesa dani,inayimaka wani irin sodaban iya nisa dakai NA tsawon sati guda,to amma sai injikana zancen zaka maida mata KWANA TALATIN,gaskiya nibazan iya wannan hakurinba.
Yace hakane,amma inaso kifahimta,wannan matsalar bataki bace,tsakanina daitane,batasakaki cikiba,kifita harkarta,babu ruwanki,rigimarmuce nidaita,karki karasa bakinki,tunda take tashin hankalin ta bata tabasakokiba,kinsan kotunyaushe muka fara wannan rigimar ?tunda bata sakaki cikiba INA abinda yadameki?karki kara nagayamaki!!
Tace to shikenan
Yace tashi muje ki bata hakuri,domin banason rigimarnan tahada dake.
Tadanyi jimm!!sannan tace to muje,suka tashi sukanufi dakin suwaiba,
Azuciyarta tana fadin ,badon itazaniba,dondai kawai incika umarnin mujina,koba komai zaikara yadda dahankalina,yakuma kara sona amatsayina nameyimasa biyayya,inkuma kara saima kaina daraja awurinsa .
Yana gaba tana biye dashi har kofar dakinnata,ya bubbuga dominkuwa tarufeshi GAM!!
Yace suwaiba kibude!tareda bubbuga kofar,kubude suwaiba!!!
Tace bazan budeba!!saboda babu abinda zakagayamani yanzun !!!!abinda dai kakeso aikayi!don haka katafi kabarni inji da abinda yake damuna!!!
Yace kibude kiji abinda yakawomu mana!
Tace bazan budeba!!bana bukatar jinkomai daga gareku!!!
Yajuya yakalli Hauwau yace tojeki shikenan.
Axuciyarta tace Alhamdulillahi!dama haka nakeso hakanan kawai asa inje inwaniba kishiya hakuri,garama dataki budewa.
Afili kuma tace:toshikenan love muje ai anjima nanan,sai inbata hakurin.
Yace kirabu da ita kawai,kardai kikara shiga tsakanina da ita,kinjiko?
Tace to shikenan,in Allah yayadda za'akiyaye.
Data gaji dakukanta,saita lalubi wayarta takira Farida.
Hello Farida yau anbatamani rai!!kishiyata waitake gayamani nayi asarar kwanakina!
Farida tace garinyaya?
Suwaiba tace waiharni take cema soyayyama banga komaiba!!wallahi farida laifin Nasser ne kawai!!shine yabata damar tayimin hakan.
Farida tace waime yakawo tagayamaki hakan?
Suwaiba tace:Nasser ne yace zai maida Mani kwanakina,sabodayaga hankalina yaki kwantawa.
Farida tace toke meyasa kika kasa kwantar da hankalinki?abinda yawucefa yariga yawuce,saikuma adubi gaba,kiyi hakuri kawai ki kwantar dahankalinki,wata rana zakiga abin yawuce kamar ba'ayiba.
Suwaiba tace tayaya za'ayi hankalina yakwanta farida?kinji yadda suke magana harwani suna suka sanyama junansu,ninaga iskancinnasuma bakarewa yakeba!
Farida tace tokema basaiki sanyamai sunanba.
Suwaiba tace don tace inagasa daita?kenifa Allah nema yataimakeshi badakinayakeba,yauda saimun kwana tashin hankali!amma bakomai zaidawo ai!!
Farida tace kafin yadawo dakinnaki kinhuce,don Allah kirika danne zuciyarki suwaiba,bakomai kedamunkiba ki shine kawai,amma kiyi hakuri komai zaiwuce.
Humff!!suwaiba tayi ajiyar numfashi tace:to shikenan sai anjima,nagode.
Harmisalin karfe goma sha biyu darabi nadare,yana zaune afalo,tunanin halin matarsa dakuma mene yasauya mata hali lokaci guda,kuma duk iya tunanin sa akan yagano wani Abu dayakeyimata Wanda badaidaiba yakasa.
Shimmenakeyima suwaibane?bahaka takeba da,meyasa tasauyamin yanzun?wane laifi nakeyimata?duk yakasa samun amsoshin tambayoyinsa.


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment