Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BABBAR HUJJA 1

NA

FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA 📖📚


Wannan littafin na suyarwane,gamai bukata .
Akan kudi naira dari uku N 300

Account Number zada ka/ki sa kudin.
1527970269
Access Bank
FATIMA DAHIRU

Ko kuma kasa katin MTN na naira Dari uku akan wannan Number
09162526909
Gamai bukatar cigaban labarin sayyayi magana ta wannan number
09162526909

Don Allah kada kadauki Number ta kayi Mani magana idan baka tashi siyen littafin ba.





Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai daya sake hadamu cikin wani sabon littafin.
Mai suna BABBAR HUJJA! Tsira da Amincin Allah sukara tabbata ga shugabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya.
Narubuta wannan Dan littafine domin farkar da mutananmu ,musamman. 'Yan mata da samari akan kalubalan da yake acikin soyayya,kawai mutum yayi imani da Allah,akan dukkan abinda baisamekaba,to daga Allah ne,kuma komin son da kakeyima Abu idan ba rabonka bane sayya tseremaka,yafi kyau dukkanninmu mukoma ga mika All amarimmu ga Allah kawai,musamman akan soyayya,domin akan ta zan rubuta wannan Dan littafin.
Sodayawa zakiga mutum kina sonshi,kokuma shi yana sonki,amma karshenta abin ba Alkairi bane a tsakaninku,to mafi yawan 'yammata da samari idan hakan tafaru a garesu ,sai kaga suntada hankulansu,har ananeman rasa lafiya.
Don haka samari da 'yammata asa hakuri acikin zuciya,komai daga Allane.
Wadda kake hangen ko Wanda kike hangen,karshenta ba shine mujin ba.
Amma bazance komai ba akan haka ,kubiyoni acikin wannan littafin na BABBAR HUJJA kuji yadda soyayyar wasu masoya zata kasance.
Fatanadai a dauki abinda yakeda kyau acikin wannan littafin .
Sannan littafin BABBAR HUJJA kagaggen labarine,bawai yaru akan wani ko wata bane,AA kirkirarsa nayi,don haka koda kaga wani Abu kowani hali yayi kama da irinnaka,to bakaidin bane,don WATA kilamani bansankaba ko bansankiba,kirkirar labarinne kawai yazo da haka,don haka idan abin gyarawane ,saika gyara .

DAGA
FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA

GARGADI
Banyadda ajuyamin wannan littafin ta WATA sigaba har saida izinin marubiciyar.
Gaisuwa ga dukkannin masoyayana,aduk inda suke,ina sonku kamar yadda kuma kuke sona .
Ayi karatu lafiya

Dasallama tashigo falon fuskarta dauke da tsararriyar kwalliya ,wadda yayi mata kyau sosai,tasanya Dan madaidaicin hijabinta ,Wanda yakara fitomata da kyawun fuskarta.
Sannu da zuwa yaya Ahmad,tafada dai dai lokacin da take Neman wurin zama nesa dashi kadan.
Yadago kai yakalleta,sannan yace:bayan kingama shanyaniko?har nayi niyyar intashi intafi,donnayi zaton ko bakida lokacin da zaki futo inganki.
Tace tuba nake yaya Ahmed, Nina isa kazo ince bazan fitoba,kayi hakuri don Allah bansan sauri kakeba,amma kuma yaya Ahmad konakai dare ban fitoba,aibaka iya tafiya bakaganniba,kumafa tsayawa nayi inshirya kawai,amma shine harka gaji da zaman jirana.
Yace: yo shirimme kikayi?abinda kwalliyarma ba kyau tayi makiba.
Tayi dariya tare da fadin yabawa kayi kenan,lallai yau na tabbatar kwalliya ta taburge yaya na.
Yace:haka dai kikace.
Tace :kaima haka kagani,tare dasa gefen hijabinta tadan rufe fuskarta.
Yace:Hafsat dama nazone insanar dake cewa rana itayau zantafi kano,kuma idannaje akalla zanyi sati acan,shiyasa nace bari insanar dake tun yanzun,don kifara shirin yin kewata.
Cikin shagwaba tace yaya Ahmad yanzun nan harsai nayi sati ban gankaba?Ashe kana shirin ka azabtar da zukata biyu kenan,yaya Ahmad bazan iya tsawon sati gida bangankaba,don Allah kasaukaka tafiyar,yaya Ahmad karage kwanakin.
Humff!!yayi ajiyar numfashi ,sannan yace:nikaina saida na jinjina tafiyarnan,domin nasan haka saita faru,Hafsat nikaina inatunanin yadda zanje wani wuri inyi sati guda ba tare danazo nayi tozali da wannan kyakykyawar fuskar takiba,no kaina nakan tambayi kaina shin sai wane irin sone muke yima junanmu?Wanda dai dai da kwana daya bama iya hakurin bamuga junaba.
Hafsat inasonki,wani lokacin har nakema kaina azarbabin cewa na kagara inga na mallakeki a matsayin matata,awannan rana zan tasaki inta kallonki,karkicefa har saina gaji,a'a bazan taba gajiya da kallonkiba,bazaki taba gundirataba.
Yadaga hannayensa sama tare da fadin.
Ya Allah ka nuna Mani ranar da Hafsat zata zama matata.
Acikin zuciyarta ta amsa da Ameen,sannan afili tace:mezakaje yowa kano?
Yace:Abbane ya shaidamin cewa diyar kaninsa.
MARIGAYI ALHAJI KABIR take dawowa daga Englar karatu ,to shine waini zanje in tarbeta,daga Air port.
Cikin muryar kuka tace amma shine harsai kayi sati.
Yace:banda wannan akwai wani aiki dazan yimasa akamfaninsa,to zai daukeni tsawon kwana biyar.
Tace:nigaskiya saidai katafi Dani "
Yace:kiyi hakuri Hafsat akwai sauran lokacine,idan lokacin yayi ko abayana kikace inzagaye garin Kaduna to inhar zan iya zanyi,to amma yanzun mudan kara hakuri kadan,kokinaso insanar da Abba cewa kince adaura mana Aure dake kafin intafi,sai intafi dake?
Tace:Ahh!!kajika saboda nice sarkin marasa kunya?
Nina yanzumma zanyi Aureba ,sai nayi digri.
Yayi dariya tare da fadin kinjiki ahakadin,sukasa dariya baki daya.
Haka sukaita firarsu cike da kaunar juna,hadi da soyayyarsu maiban sha'awa.
ALHAJI SALISU mahaifin Hafsat tare da matarsa HAJIYA FATIMA,suna zaune afalonsu.
Hajiya Fatima tace:Al-amarin yarannan Alhaji,abin gwanin babsha'awa,sunason junansu sosai,karkaga yadda Ahmad yake diki akan Hafsat ,itama da ance gashi yazo karkaga yadda jikinta ke rawa,kaih!mudai wannan Al amari Allah ya tabbatar mama dashi,kagansu da wasa da dariya,komai sunayinsa gwanin bansha'awa.
Alhaji salisu yace:shi Allah haka yake hada siyayyar 'yan Adam,gashi dai mutane dadama suna gudun Auren Zuminci ,amma mudai yarammu Allah ya had a kawunansu,kafin mahaifitar Ahmad din tadawo daga kasar saudiyya ai yaran sungama dai saita Kansu ,wannan Al amari aiba Wanda zaifini jindadinsa.
ALHAJI SANI DA ALHAJI SALISU DA MAHIFIYAR AHMAD HAJIYA AISHA,mahaifisu daya ,indashi Alhaji Sani da Alhaji SALISU mahaifiyar su daya,ita kuma HAJIYA Aisha ita kadai mahaifiyar ta ta Haifa,kunga. 'Yan uba Duke kenan.
HAJIYA Aisha tare da mujin ta ALHAJI SULAIMAN da daya kawai suka mallaka wato Ahmad ,sunaji dashi sosai,dama kuma ga arzikin.
Shi kuwa yayanta Alhaji SALISU yanada 'ya'ya dadama,cikinsu harda Hafsat ,Wanda a yanzun yakeda shekara goma sha Takwas da haihuwa,lokacin da take zama budurwa,sai Allah yahada soyayyarta da Dan uwanta Ahmad,Wanda yazamana Abokin wasantane (kamar yadda mu hausawa mukecewa)
Domin kuwa da Babantaba da innarsa mahaifinsu daya,saidai uwace kowa data shi.
Alhaji SALISU da kaninsa Alhaji Sani sunyi farinciki da wannan Al amari sosai,domin koba komai zai kara donkon zuminci atsakaninsu,wannan kenan.
Ranar Alhamis kuwa dasafe tadauki motarsa,yatafi kano,acikin zuciyarsa cike yake da kewar abin kaunarsa Hafsat.
Yasauka gidan,su biyu ya Tatar kamar yadda ya tsammata ,daga kubura sai khadija,sai masu acikin gidan da suketa kaida komowa,sunayimasu hidima,
Cikin farin ciki suka tarbi yayan nasu,suka kaishi masauki,tare da kaimai da dadan abinci kala-kala,saida yagamaci sannan suka shigo,India yake domin susake gaisawa.
Yace :aah!kanbaina!yakaratu?
Sukace lafiya lau yaya Ahmad,yaya wajen acikin ka?
Yace :lafiya lau,Abba yace in gaisheku,kuma yace:idan yayarku suhailat tadawo,inkoma daku,don yace yanson ganinku.
Kubura tata hannayenta tare fadin Allah sarki!Abbanmu!!inaso Nina inganshi.
Khadija tace amma dai ba dadewa zamuyibako?Donni bànso inje wani gari indade.
Ahmad yace aidukkece matsalar dama,bakison mutane.
Tace yaya Ahmad bahaka bane karatuna.
Yace to Al huda huda!karatun guduwa zayyi?komai menenedai tunda Abba yacekije saikin je,inba haka ba kuma injaki da karfina inkaiki.
Sukasa dariya baki daya.
Tace saikace WATA 'yar yarinya,aibaka iya jana,.
Yace Atashi tafiyar kice baki zuwa kigani,da karfi zansanyaki cikin mota,alokacin zaki gane ke yarinyace,suka shekararki nawa?
Yayi saurin cewa goma sha shidda!
Yace kaji barauniyar shekaru!yaushe kikakai haka?
Tace Allah yaya Ahmad bakai,ya kake maidani bayane?
Yace:don kinga kinyi jikin girma.
Kubura dai dariya takeyumasu,harsai tagaji tace:yaya Ahmad idan kabiyema autannantamu,nanzaka shiririce,ko hutawa,bazaka samu kayi ba,
Gashi kuma gobe Aunty suhailat ke dawowa, yakamata kadan huta kasha hanya,sannan ta kamo hannun khadija suka fita,shikuma yasamu Dakar kwantawa bisa luntsumemen gadon dayake cikin dakin.
ALHAJI SULAIMAN mahaifin Ahmad,shima su biyune iyayensu suka Haifa,daga shi sai ALHAJI KABIR.
Shi Alhaji Kabir 'ya'yansa mata uku,da matarsa HAJIYA RAKIYA,wadanda Allah yayi masu rasuwa asanadin hadarin jirgin sama,Wanda sukabar 'ya'yansu,BABBAR itace SUHAILAT wadda a yanzun ta kammala karatun ta,kuma take shirin dawowa Nigeria daga kasar Engiler.
Maibimata itace kubura,wadda itama yayi karatun sosai,amma yanzun harkar kasuwancin mahaifinsu,yadawo hannunta,sannan sai 'har autarsu khadija,wadda a yanzun take shirin kammala makarantar secondary.
Su biyu Duke rayuwa acikin gidansu,sai ma aikatansu da suke tare dasu,maganar dukiya kam!!akwaita,dama iyayensu sun mutu sun barmasu ita,kuma kubura nakara tafiyar da harkar dukiyar cikin kwarewa da kuma ilimi.
Shekara suhailat biyar a kasar Engiler ,run bayabayan asuwar iyayensu,bata kara dawowa Nageriyaba,saida yanzun data kammala karatun ta,takeso tadawo gida dun!din!!dunn!!!
Yayan Babansu Alhaji SULAIMAN,mahaifin Ahmad,yasyaso yaran sudawo wurinsa,amma suka nuna sudai subfiso suzauna inda suka saba,dama ga kubura na harkar kasuwanci,khadija kuma tana karatunta.
Was he gari kuwa tunda safe aketa aikaxe-aikace,na hidimar tarbar Aunty suhailat,gidan yadau kanshin gurke-girke da soye soye,kowa magani cikin murna yau sunada babbar bakuwa!!!
Kubura da khadija sukayi wanka sukasa kaga masu kyau da tsada,
Haka shima Ahmad kana nan kayane yasanya. Sunyi masa kyau sosai,sannan suka Shiga mota,Ahmad yaja suka nufi aanyar cikin jirgin malam Aminu kano.
Basu jima sosai ba jirgin ya sauna gaba daya duk sun kosa suganta.
Cikin shigar Mayan turawane ajikinta,gawata hular gashi data Sanya akanta,kayan jikinta sun kamata sosai.
Ahmad baiji dadiba dayaga 'har uwarsa acikin irin wannan yana yin,tamkar ba 'har musulmibarigarnan tata hatta cibiyarta a wane,ga wani da mammen Wanda dayake ajikinta.
Cikin murna tabi. 'Yan uwanta tana rungumarsu,tanayimasu kiss,suma murna Duke sosai da ganinta cikin kishin lafiya.

Ahmad bai ankaraba sai jinta yayi tafado cikin jikinsa,ta kankamesa tana fadin ,oyoyo!ya Ahmad,ta kaimai sun bata akumatunsa,shikau yana ta kokarin tureta,amma bata fahimcima hakanba,murnar ganin. 'Yan uwanta kawai take.
Tace:YA Ahmad ki irin. 'Har ziyararnan?baka taba zuwa inda nakeba.
Cikin 'har dariyarsa dabatakai cikiba,domin ranshi baisoba,ganin kanwarsa da irin wannan shigar,yace:
Tuba name Aunty suhailat kiyi hakuri,yakara rungumarsa cike dajin dadin ganin Dan uwanta.
Shikuma yace kushuga mota muwuce gida.
Sannan suka shigo mortar Ahmad Yakuma tukawa suka tafo gida...................🖊️
Fatima Dahiru Funtuwa Binta,don Allah idan baka shirya siye ba kada kadauki Number ta kabari saika shirya
Suna isa gida Ahmad yawuce dakinsa cikin sauri,don yagaji da ganin suhailat airin wannan yana yin.
Aranar gidan ya kasance cikin annshuwa da farin ciki,bayan anci ansha,sannan suhailat tashiga yo wanka,tayi kwalliya,sai dai haryanzun wasu kayan turawanne takarayin kwalliya dasu.
Suna cikin falon gidan sunata fira irin tayaushe gamo,an hadu da 'yan'uwa.
Suhailat tace wai ina YA Ahmad banganshiba?duk gamu munfito falo anata fira,inayashige?
Khadija tace yanadaki nakaimai abincine,kila baigama Ciba.
Suhailat tamike tsaye tanufi inda dakin Ahmad din yake.
Zaune tatarar dashi yanata shafa wayarsa,ga Abincin da akakawomai nan ko tabashi bayyiba.
Tana isa kusa dashi tasa hannu takarbi wayar,tace bakaci abincinba.
Yabata ransa yace aizanci.
Takallai sosai tace YA Ahmad meke faruwa?
Yayi banza daita
Takumacewa naga bakaci abincinba lafiya daiko?
Yace lafiya lau,ya amsa mata adakile.
Tace fushi kakeyi ya Ahmad?
Yadaure dai yace kekika batamin rai.
Saita zauna daf dashi,tace menayi kuma daga dawowa ta?
Yadago ido yakalleta sosai gata zaune daf dashi,yace duka shekararki nawa akasar turawan?dahar zaki juyar da dabi'arki irintasu,karki manta kefa musulmace 'yar bahaushe,amma kidubi irin shigar datake jikinki,sannan kuma aikinsa niba muharraminki bane ,domme zaki rika kai hannunki ajikina?tashi kibani wuri.
Tabishi dawani irin kallo,sannan tace to ya Ahmad kacemani ba 'yar uwarkabace,shikenan daga dawowa ta saika fara fushi dani,inwani abunnayimaka aibatahaka zaka bullominba,saidai ingaba daya nidince bakason gani,kokuma katsaneni.
Yace batsanarki nayiba,amma natsani irin wannan mummunar dabu'ar dakikaxo da ita,kidubi kanki kigani mana,haka kikazo kika tarar DA sauran 'yanuwanki?meyasa kika manta datsarin Addininkine?nida kike gani ba muharraminki bane,ballantana inkin hada jikinki danawa kikeganin kamar ba laifi.
Tace ya Ahmad daga dawowa ta zakatirkeni dairin wadannan maganganu?basaikanunamin cewar banida wata daraja awurinkaba,nasani,shiyasa kafara fushi dani don injanye jikina daga gareka,bakomai,tamike cikin hanzari zata fita.
Yakira sunan ta dakarfi SUHAILAT!
Tajiyo takalleshi.
Yace banaso kidauki magana ta dawata manufa,kawai dai gyarawa nakeso kiyi,kisani kinbaro waccen kasar,kindawo cikin 'yan uwanki hausawa,toyakamata ace shigarkima tacanza.
Tafita tana fadin nidai takuramin kawai zakayi ya Ahmad.
Sannan takoma falon da 'yan uwanta suke sukaci gaba da firarsu.
Anan kubura keshaidama Aunty suhailat cewa tare zasu tafi da yaya Ahmad Kaduna,saboda Abba yace yanason ganin su,
Ammakinsan abinda nake gudu Aunty Suhailat?damunje zacen aure zaitada mana,don tunbakinan yaketayimin nacin inyi aure nikuma nakafamai HUJJA dacewa saikindawo,toninasan dalilin kiran kirankenan.
Waitunda yanzun bakaratu nakeyiba,yakamata inyi aure,nikuma Aunty suhailat ganinakeyi idan nayi Aure yanzun kasuwancinnan gaba daya nakasu zaisamu,idanba adalin muji nasamuba,shiyasa naketazullema auren.
Aunty suhailat tace to aikuma aure yazama dole,tunda dai baki isa kikafamai HUJJA dacewa kasuwanci zaihanaki aureba,kadai Allah yazaba abinda yafi Alkairi kawai.
Ahaka sukaita firarsu harlokacin sallah yayi sukatashi gaba dayansu sukayi Alwalla sukayi sallah.

Misalin karfe Tara na dare,alokacin kowa yashige dakinsa,haka kawai saitaji takasa zama dakinnata,tamike tanufi dakin kanwarta kubura ,tayi sallama tashiga,ita kuma tana zaune gefen gadonta,hankalita nakan Televition din datake kallon.
Tajiyo dasauri taredafadin,Aunty suhailat Ashe bakiyi bacciba?nadauka zaki kwata kihuta,saboda tafiyar dakikasha.
Suhailat ta zauna kusa da ita,tare da fadin bankwantaba,kubura nakasayin baccine kaya nazokibani,donnalura bazamu shirya da Ya Ahmad ba,muddin bandainasa wadannan kayanba,karkiso kiji irin fadan dayayimani dazun,wai inayin shiga wadda bata daceba.
Kubura tace aikunfi kusa,saikije kiduba irin kayandakikeso,aikindawo kuma zakufara,kinsan dai shi yaya Ahmad baya gani ya kyale,donhaka kirika kiyayewane kawai Aunty suhailat.
Haba kubura amma daga dawowa ta!aiya kamata yabarni inhuta.
Kubura tace to aidai kinsan halinsa tuntuni.
Aunty suhailat tace keni bama wannan takawoniba,maganar dakikayi dazun,gaba daya nakasa samun nutsuwa,tunda kikafadamin.
Kubura tace wace magana kenan?
Suhailat tace tafiyar dazamuyi Kaduna,wallahi maganar Abbace banaso,kinsan shi inyaso Abu,kobaka shirya ba,baburuwansa,yanzun ni daga dawowa ta yaushema nanutsu bawanda zan aura.
Kubura tayi dariya,tace humf!baki saniba Aunty suhailat,akwai lokacin daya matsamani sainayi aure,yagadai inata gocemai,kawai sayya kawo Mani wani,waiyazo yaganni innayi masa,kinjifa Aunty Suhailat saikace wata haja!gaba dayama Abba tamkar Neman kai takeyi damu.
Todayazo wurinadin nasaki jiki munyi fira dashi sosai,sai daga baya cikin hikima nanunama Abba nifa inada Wanda nakeso,cikin ikon Allah kuma sayya amincemin sahakan,sai cewa yayi to intura Wanda nakesidin,sai kawai nayima Ishak magana.
Tofa Abbana yanason ganinka,muka shirya nakaisa suka gaisa,Abbafa saiya bijiromin dazancen aure,A yanzun haka Is'hak yakai kudinneman aurena wurin Abba,nikuma nakibada hadinkai ayi auren yanzun.
Har saida yazama na cewa muna wasan buya nida Abba,nidai nadaina zuwa Kaduna,shikuma inyazonan damun gaisa,magana tadaya-tabuyu to taukunsu zancen aurene,shiyasa nikuma damun gaisa zangudu,bana karayadda muko hada hanya dashi.
Daga baya saina kafamai HUJJA dacewar inajira saikin dawo,sannan kayi baki daya.
Nikuma Aunty suhailat inason kasuwanci na.
Aunty suhailat tace ammadai aibazai auri kasuwabako?Allah yakaimu Kaduna lafiya.
Washe gari Aunty suhailat tayi wanka tasanya leshi maukyau,dinkinyayi mata kyau sosai,amma saiji tayitayi daban dukkayan suntakurata,batadamu da kyawun dakayan sukayi matmata.
aganintadai duk Ahmadne yamatsa mata.
Tana zaune a falo tanata latsa wayarta.
Ahmad yashugo,cikin yabawayace:haba suhailat kinga yadda kikayi kyau kuwa?gaskiya kayan sunyi maki kyau!
Tayi murmushi tace nagode ya Ahmad,amma dai duknaji natakura.
Yace ahankali zaki saba,kidaure kici gaba dasawa,amma dakinasa wasu damammun kaya,aikinsan bazamu shirya ba,amma yanzun kin gyara naji dadi sosai kanwata.
Cikin jin dadin yadda yakulata,tamike tsaye tare DA fadin fita zakayine?
Yace e zanfita aikine,kozaki rakani?
Tace mezai hana? Kagama sai inkara ganin garin sosai,inga irin cigaban da aka samu bayan tafiya ta.
Yace aiko zakigani,don ansamu cigaba sosai.
Tadauko gyalenta tayafa,sannan tabiyo bayansa suka tafi.
Suna tafiya yanakara nunamata garin,dakuma irin cigaban da aka samu bayan yafiyarta,don wasu guraremma bataganesu,sayya sanar daita.
Kawai saita takaleshi dacewa,yaushe zaka koma?
Yace sauran kwana biyar,amma Abba yace daku zankoma,don yanaso yaganku,saboda yarabu dazuwa,kuburace tabatamashi rai,shiyasa yadauke kafarsa dazuwa kano.
Aunty suhailat tadanyi murmushi tace kubura tafadamani, waisoyakeyi tayi aure.
Yace toke mekika gani?
Tace lafiya lau ai,yin auren aishine darajarta,Allah ya tabbatar da Alkairi.
Yace Ameen,dama kekawai muke jira,don kubura tafiyar da mujinta tuntuni,nimakuma nafutar da wadda nakeso,kinga sauran ke kawai,Allah tafito maki dashi kafin lokacin,sai ayi gaba daya.
Aituni taji wata zufa natsatstafo mata agoshi,cikin karfin hali tace:INA kua kasamo mana matar?
Yace diyar wan mamanace,kuma nima munkusa shigar da maganarmu wurin su Abba,nasan dalilin daya yace yanason ganinku kenan.
Suhailat taciro Tissue tafada share zufar datake Neman tabbata mata kwalliyar fuskarta,yarasa kuma dalilin DA yasa tatsinci kanta airin wannan yana yin,domin jitake gaba daya karfin jikinta yakare,gawata masifaffiyar kasala data dabaibaye dukkan ilahirin jikinta,batada karfi kwata -kwata,kamar anzare mata lakka,tarufe idanunta,tare da kwantar da kanta bayan kujerar mortar,wani matsanancin tashin hankali yaziyarceta,bata kara fahimtarsa abinda yake fada mataba,saidai tabishi da ummf!kawai,harsukakai inda zasukai,yanaba ta labarin irin shakuwar datake tsakaninsa da 'yar uwarsa Hafsat.
Bawani irin yanayi suhailat bakasance,a wadannan kwana kin,koda yaushe tanazaube cikin dakinta,harbatasoma wani yakusanceta,saidai ita kanta batasan ainihin abinda kedamuntaba,itadai yanajinta wata sukuku da ita tsawon kwana uku.
Misalin karfe biyar na yamma,kubura tanufi dakin suhailat,kwance tasameta bisa gado tana rungume da filo akirjinta,hartayi sallama batasan tashigo ba,don haka tata bata tana fadin lafiyarki lau kuwa Aunty suhailat?
Aunty suhailat tatashi zaune tare satin murmushi,tace lafiya ta lau mana baccine yakeso yadaukeni.
Kubura tace acikin kwana ki ukunnan naga kinshiga wani yanayi nadaban,Wanda bansanki dashiba ada,dafarko nadauka cewa futawa kike,amma yanzun nafahimci bahakan bane,Aunty suhailat meke damunki???????????
Maukaratu biyoni apage nagaba
Daga maison farin cikinku
Suhailat tadafa kafadar kubura,Tace bakomai,kuma nagode da kulawarki agareni,amma ni ba abinda yake damuna.
Ya za'ayi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

2 Comments On BABBAR HUJJA
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Yes

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment