Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled By Umar Dalha Funtua.


*_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*1*


_Bismillahir-rahmanirraheem_.


*B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,,

Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata,

Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki 'daya,

Ya rasu shida Mai 'dakinsa Fatima sunbar 'yaya hudu duka maza,,

Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa'da,
Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,

Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa kowa dadiba.
yanada mata biyu inna hindatu da iya lami,

Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda 'yaya bakwai, _zayyanu, auwalu, dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_.


Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu 'daya da baba malam illai shi Yana da'dewa baiyi fadan ba,
Matarsa 'daya shi,mama salamatu Sai 'yaya biyar duk mata,hafsat, Amina, hajaru, zainab da sumayya Kuma duk anyi musu aure.

Sai baba Yusuf Mai sanyin Hali da kawaici dakuma tsananin qaunar 'yanuwansa, shima matarsa 'daya fatima da 'yaya biyu _*AYSHA*_ da nuratu.

Alh Bello shine qaraminsu Kuma fitnannensu Dan masifa da son kansa a fili yake sbd ya 'dan taba yin arziki abaya Amma yanxu Babu shiyasa ko Abu ka'dan akai saiya maidasa babba akan fitina da fa'dansa.
Matansa biyu mama bilki da umma sakina.,
'yayansa bakwai _ahmad, isah, Umar, abbakar Sai saudat Salma da husna_


Dukkaninsu a gida 'daya suke Sai dai kowa da shiyarsa Amma yaransu maza kaf 6angarensu 'daya hakama matan.

Asalinsu buzayen qasar nijar ne malanci yakawo mahaifinsu garin gombe harya gina gida yazama mazauni.

Malamai ne kaf 'dinsu Kuma basuda wani aiki bayan malanta hakama ba wani arzikine dasuba Sai rufin asiri.

A rayuwar gidan Sam basa auren na waje saidai atsakaninsu sbd yawa dakuma tsananin kyamar wani yare daba nasuba na buzaye.

Qabilanci ne tsantsa acikin jinin kowane 'dan Adam dake rayuwa acikin gidan,
Basa qaunar ha'dawa da ko bahaushe bare wani yare har gwara Fulani.

Wannan aladace dasuka gado tun gurin iyaye da kakanni shiyasa duk kwa'dayi da maita ta kyau da 'yayan gidan sukedashi ba'a tunkararsu da maganarso,

Qiyayyar dasuke fitowa suna nunawa ta rashin son ha'da zuria da wata qabila a qarara yake Dan abin har tsoro da mamaki suke bawa na taredasu.


Yaran gidan kaf dinsu maza da mata ustazai ne kamilallu kullum jikinsu a rufe yake ruf ko qafarsu baka gani fuskarsu ma wani sa'ilin suna rufewa idan zasu fita.,

Mazansu da matansu sun haddace alqur'ani akansu da sauran littafan addini.

Ka'dan ne daga cikinsu sukai karatun Boko sbd bai damesuba sunfi riqe addini shiyasa layin gidan kullum acike yakeda motoci da mashina harda kekuna gurin 'daukar karatu a gidan.


Ayshah,husnah,saudat da Salma kusan sa'anin juna ne 'yan kimanin shekaru goma Sha takwas zuwa Sha Tara.

A al'adar gidan mata basa wuce gaba da secondary aure suke musu Amma wannan karon anbarsu Aysha sun wuce sbd ba'ayi Shirin aurensuba Amma antsayarwa kowaccensu da miji.

A university suke karatu yanxu suna two hundred level.,
Aysha medicine take karatu sukuma sauran gabaki 'daya Islamic sukeyi.


Yaya Umar shine Wanda aka ha'da Aysha dashi sbd sonta daya nuna yanayi qarara,

Ya Umar mutum ne Mai zafin Rai kamar iyayensu Dan kamarma ya zarcesu sbd baida hakuri ko ka'dan ga saurin duka dayakedashi bayada kar6ar uzurinta ko ka'dan shiyasa kullum idan sukai fira kwana kuka take sbd da fa'da suke rabuwa,

Sanyin halinta da sanyin jikinta tareda kasancewarta miskila Mara hayaniya shike wahalarda ita ko acikinsu saudat bare gurin ya Umar.

Halin umminta ne ta 'dauko Zak harma ta zartata sanyin halin shiyasa mahaifinta da ummin ke tsananin qaunarta da tausayinta sbd ganin kawaici da hakurinta sa6abin qanwarta nuratu dake da masifa ba'a ta6ata ko ka'dan.

Aysha kyakkyawace Mai kyan jiki Dana fata ko acikin gidan tafisu hasken fata da kyau sbd tafisu rashin son fita duk da dama kulle ake musu basa fita.




***********
Yau tun 6 na safe tafara shiri sbd anyi shifting lectures 'dinsu zuwa sabon site 'din university Wanda bakowane course ake maidawa can ba gashi yanxu an rabata dasu husnah dansu yanxu tsohon site suke.

Hakanan batajin dadin rabata dasu da'akai sbd batasan ya can 'din takeba,.

Tsaf tashirya cikin doguwar rigar atampha red Mai adon dark blue saita saka dogon hijab dark blue daya sauka har qasa yanaja danko kalar atampharta ba'a gani bare qafafuwanta,
Jakarta ta 'dauka tareda ficewa taje tagaida iyayensu kowane 6angare kafin tadawo 'dakinsu suka fito taredasu husnah.


A qofa suka hadu da ya Umar da ya Ahmad zasu shigo,

Har qasa suka durqusa su duka suka gaidasu
Ahmed ne ya kar6a Yana shigewa cikin gidan
Ya Umar ne ya amsa tareda kallon ayshah

Qasa tayi da kanta Tana wasa da Jakarta su husna kuwa tuni suka wuce sbd Umar 'din Sam baya wasa yanxune zasuji ruwan bala'i.

Kallonta yakumayi dakyau ahankali yace,

Meyasa baki saka safa ba?

Cikin sanyin murya kanta na qasa tace,

Sunyi dattine na wanke na shanya ruwan da'akayi da dare sun hanasu bushewa.

'daure fuska yayi yace,

Toki tabbatarda kin dawo kan lokaci.

To''''' tace a hankali tareda wucewa cikin sanyinta.


Ajiyar zuciya ya saki ahankali bayan ta wuce Dan hakanan yakejin Sam hankalinsa yakasa kwanciya da karatun Aysha sbd jiyake kamar zai rasata ne duk dayasan bazata kula kowaba.



A bus stop suka rabu dasu husnah ita ta nufi new site Banda faduwa ba abinda gabanta keyi sbd ita mutum ce Mai tsoron shiga jama'a batareda Wanda tasaniba.

Koda ta Isa kai tsaye hall 'din dazasuyi lectures ta nufa kanta a qasa cikin nutsuwarta take takawa Dan duk a takure take sbd yanayin students 'din data gani anan 'din kamarma 'yan iskan makarantar ne aka kwaso aka dawo Nan dasu Dan dukanin alamu sun nuna kusan hakan ne,


Lectures suke Amma Sam takasa samun nutsuwarda zata fahimci lectures 'din Dan wasu samari dake kusada ita suna dariyar shigarta.


Sai kusan six suka fito daqyar taga tafito ta iso gida Dan har wani zuru zuru tayi na fargaba data yini yau aciki.

Tana Isa gida ta tu6e tayi wanka tareda sallah kafin tazauna cin abinci Tana fira da umminta tareda Bata labarin wani fa'da dataga anayi kan hanyarta ta dawowa.






********

Babban gidane dayaji komai najin da'din duniya sbd girma,kyau dakuma haduwarsa..

Babbar mace ce 'yar gayu da hutu tareda ilimin Boko dayagama ratsata yasa manyancinta qin bayyanuwa sosai,

Babbar justice ce a babbar federal high court dake garin hakama Mai tsananin roqoce da addininta na christian Dan har muqami gareta a church sbd riqoda addininta Dan dukda zamanta babbar Mai kudi hakan bai hanata halarta da kula da aikin church ba kullum.. _justice queen aiden Bellamy_ kenan.

'yayanta uku rak a duniya,
*FINN* shine babba mum's boy kenan sbd shine ya 'daukota sawu da sawu Dan shima law ya karanta yanxu lawyer ne kullum tare suke zuwa office sudawo tare suje church tare,
Duk wani Hali nata ya 'dauko Dan harma ya zartata musamman yanda ta tsani kowace qabila da addini idan ba nataba toshima haka.

*_NIK_*,,,,Niklaus kenan, shine nabiyu Wanda shida qanwarsu *DAVINA* kwata kwata halayensu sunyi hannun Riga Dana mahaifiyarsu sbd Sam su Babu ruwansu da wani riqo da addini bare zuwa church,,

Nik 'dan gayune na qarshe daya ha'du iya ha'duwa sbd tun farko a hannun dad 'dinsu yake a qasar Germany danshi Sam bayason takura yanason yayi rayuwarsa a sake shiyasa yaqi biyo mum 'din dazata dawo Sai daga baya ta matsa tareda 'daga hankalinta akan saiya dawo Nigeria.

Gabaki 'dayansu suma farare ne tas bama kamarshi dayafisu son hutawa akoda yaushe kamar mace.

Davina ma kusan kamarsa take 'yar gayu kullum Tana tareda friends ana gurin shopping ko gurin hutawa..

Hutu da gata tareda dukiya sun ratsasu sosai shiyasa kullum cikin qara kyau Nik yake,
Duk wani son life 'dinsa mata basa burgesa tunda yadawo Nigeria sbd Sam bazai iya ko kallonsu ba bare ya iya kulasu yan matansa nacan sunfi burgesa sbd sune sukafi sakasa nisha'di.



Tsaf take cikin kayanta na aiki ta fito ta hawo sama bedroom 'dinsa Dan shika'dai ne 'dakinsa yake sama sbd tsananin so data fili ta nuna qarara tafisonsa fiyeda sauran 'yayan nata.

Tura qofar tayi ahankali sanyin ac da qamshin turarensa na signature hugo ya daki hancin takai kallonta kan lafiyayyan gadon dayake kwance Yana bacci dunqule cikin falin bargo qal.

Takowa tayi ta Isa bakin gadon tareda durqusawa ta rintse ido tafara kwararo masa adduarsu ta church Wanda kullum saitayi Masa kafin tafita office hakama da daddare komai Daren dazaiyi awaje saita jira yadawo tayimasa sbd ba qaramin so takeyiwa 'dan nataba.


Ahankali ya 'daga hannunsa 'daya ya janyo dayan pilonsa batareda ya bu'de idanuba ya toshe kunnensa dashi sbd damun baccinsa da mum din keyi da addua.

Jin ta qara 'daga murya tana fa'din,

Ohhhh Lord I pray for..........Jesu....


Cikin muryar bacci Yana qara tora kansa cikin pillow yace,

Mum pls I hate this...

Miqewa tayi bayan tagama tareda 'duqawa ta shafi fuskarsa bayan ta janye pillon cikeda kulawa tace,

Nik can pls promise me you'll......

Katseta yayi cikin qosawa yace,

Yes I promise I will.

Thank you sweetheart'''' tace tareda miqewa tafice tana murmushi.

'dakin Davina tanufa Kai tsaye daganan.

Kwance take tana bacci itama Amma ki'da ke tashi a hankali cikin 'dakin sbd ita Bata iya bacci Saida kida qaidarta ne.

Tada ita tayi itama kafin tafito ta tsaya Saida masu aiki suka jera komai na breakfast 'dinsu Nik idan sun tashi kafin takalli Finn dake shirye Yana jiranta suka wuce office.


WANNNAN KENAN.



Mamuh💋


_Dont forget to follow,vote and comments_ _@mamuhgee_..
*_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*2*


Yauma a sanyaye ta iso makarantar sbd duk jinta take a takure badan tana tsananin son karatunba da batajin zata iya cigaba da zuwa sbd wannan new site 'din yafi qarfin abinda qwaqwalwarta zata iya 'dauka.


Lectures biyu tayi yau Dan haka da wuri tagama Tana fitowa hall ta fiddo niqaf 'dinta ta rufe kyakkyawar fuskarta sbd kallo dayayi mata yawa Wanda tasan bai wuce na suturartaba sbd har ja hijabinta keyi.


Sauri takeyi ta tafi gida duk da niqaf 'din data saka kanta a qasa yake bazaka ta6a cewa sauri takeyiba sbd cikin nutsuwa take tafiyar kaman yanda addini ya koyar.

Tsayawa tayi cak tareda juyowa ahankali sbd sunanta dataji ankira daga bayanta.

Ajiyar zuciya tasaki sbd ganin wata ayshar ce ake Kira ba itaba.

Juyawa tayi zata wuce batareda sanin isowa mutumba sukai wani irin karon dayasa wayar hannunsa da car keys 'dinsa zubewa qasa.

Ya salam'' tafada ahankali cikin sauri tareda ja da baya jikinta na matuqar rawa sbd jikinsu daya 'dan ha'du Wanda wannan shine karo na farko da jikinta ya ta6a ha'duwa da jikin wani 'da namiji.

Tsayawa kallonta yayi sbd ganin yanda jikinta ke tsananin rawa abin dayafi basa takaici ma kenan,

Samanta zawa qasanta ya kalla cikin qyanqyamin shigarta sannan shibaiji baqin cikin ha'duwar jikinsuba shida yakeda komai na rayuwa musamman kyawunsa dake fuzgar mata Sai itace da fuskarta ke rufe qilama nakasasshiyace shiyasa ta rufe fuskar.

Dafasa abokinsa Murphy yayi bayan ya 'dauko Masa kayansa dasuka zube Yana cewa,

Let's go Nik we're getting more late..

Wucewa yayi tareda qara juyowa ya kalleta yana 6ata fuska.

Hawayen datake dannewa ne suka gangaro mata ta 'dago Kai ahankali takalli inda sukabi dai dai yakuma juyowa manyan idanuwansu suka ha'du da juna.

Atare gabansu ya Fadi yayi saurin 'dauke Kai sbd tsoro da idanuwanta suka bashi danshi mutum ne Mai tsoron mutane sbd bai cikason ko kallon wasu mutanen ba.

Ita ma cikeda tsoro ta juya jikinta na tsananta rawa ta fice tabar makarantar.

Harta Isa gida nutsuwarta bata gama daidaita.

A qofar farko ta ha'du da ya Umar gabanta yakuma yankewa ya Fadi sbd ganin Yana qureta da kallo tai saurin tattaro nutsuwa tareda qaqalo murmushi cikin sanyin murya tace,

Ya Umar ina yini?

Cikin Jin da'di da tsananin qaunarta ya amsa tareda cewa,

Ayshah da gani kin 'debo gajiya ko?

Eh'''tace tana sauke Kai qasa.

Bata hanya yayi ta wuce batareda yakuma wat maganarba.

A 'dakin umminta ta yada zango ta cire hijab 'dinta tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.



Washe gari jiki a sanyaye ta shirya ta nufi makarantar duk da yau ya Umar da kansa ya rakota har bus stop tashiga mota.


Tunda suka shiga first lecture 'dinsu taga tamuqar ba tattaro nutsuwa tayiba to bazata fahimci komaiba shiyasa ta 'dan nutsu ta karanto addua tareda maida hankali saigashi tana fahimtar komai.


Sai four suka fito a gajiye take sosai ga yunwa datakeji sbd Sam basa cin abinci a waje komai rintsi shiyasa ko ruwan makarantar Bata ta6a siya tashaba.

Sam bazaka kalleta kace yunwa takejiba sbd acikin nutsuwarta take tafiya.


Saukowa take daga sama Dan hall din dasukai lectures yau a sama yake.

Wasu samari ta hango qasa a tsaye suna sheqa dariya suna nunota
Tasan da ita suke Dan idan da sabo yakamata ace tasaba da tsokanarsu Dan kullum idan zata fita Sai sun tsokaneta suna kiranta da ninja lady Wanda sunan tuni yafara binda acikin makarantar Dan gabaki 'daya yanxu ba Wanda yasan fuskarta sbd kullum rufe fuskarta take cikin niqaf,,
Ba kalar mummunar halittar daba'a kiranta da ita sbd kawai ta cire niqaf 'din aga fuskarta Amma Sam ta danne duk da sau tari idan an mata tana Jin zafi harda hawaye musamman idan matane sukai mata.


Ihu suka 'dauka suna Kiran,

Here comes our ninja lady..hahhhhhhh

Sunkuyar da Kai tayi tacigaba da saukowarta sbd Bata ta6a kulasuba.

'daya daga cikinsu mace taci ado ta matse cikin qananun Kaya kamarba musulma ba ta 'daga musu hannu tareda miqewa tsaye cikin 'daga murya tace,

Yau dai Kam dole muga fuskar ninja lady sbd bamusaniba Koda aljana muke tare,,wat do you say guys????

Ihu suka 'dauka cikin shewa suna cewa,,

Yesss ohhhh..

Cak ta tsaya gabanta na tsananta fa'duwa ganin yarinyar ta nufota ana mata kirari gurin na da'da 'daukar ihu sbd kowa dakeson ganin fuskarta ta.

Ayshah mutumce Mai tsananin tsoro da rashin qwarin zuciya sbd Sam batada kuzarin dazata iya qwatar kanta Sai kawai tafara hawaye ahankali tareda rintse idonta tadan ja baya daidai lokacinda yarinyar takai hannu zata bu'de mata niqaf taja baya ka'dan cikin rashin sa'a Ashe takai bakin qarfen stairs 'din ta fa'da.

A tsorace kowa gurin ya 'dau ihu..



Sanye yake cikin wasu tsadaddun designers qananun Kaya blue jins da blue shirt datayiwa farar fatarsa kyau bazaka kallesa kallo 'daya kace christian ne ba sbd yamafi Kama da akirasa bafulatani sbd komai nasa Mai kyawu ne.,

Shigowarsa kenan tareda amininsa nako yaushe Murphy.,Sai Davina dasuka ha'du yanxu cikin school 'din ta maqale Masa wai wani lecturer 'dinsu ya hanata shiga lectures yau shine suka shigo department 'din yayiwa lecturer 'din magana sbd baya tsoron kowane lecturer shi duk da shima student ne Yana final year 'dinsa...Amma ba ruwansa duk Wanda yatakasa takashi yake sbd gata da sakewa daya samu daga uwarsa.


Ba zato yaji saukar mutum akansa saigasu sun zube qasa atare..

Holy Christ...yace da qarfi daidai itama tace,

Ya salam''''..

Da sauri Murphy da Davina sukayo kansa ya miqe Yana yarfa cikin tsananin azaba yace,

Oh God she broke hand..

Wat'''''Davina tafada tana yamutsa fuska.


Zafi yakeji sosai Nan danan student 'yan neman fada suka 'dauko kujera aka zaunar dashi Sambatu yake sbd jiyake baitaba Jin azaba irin wannan ba duk da ba wani ciwo bane.

Mum Davina takira tana 'dauka tace,

Hello my little princess,,,,,

Mum your Nik meet wit an accident his hand and leg got sprained....

Wat,,,, where and how?

One stupid ninja lady fell on him,her face was covered she probably doesn't see where she was going so......

Take him to hospital now I will be there soon.

Kamasa sukayi zasu fice ya juyo cikin azaba yacewa murphy hand her to school authorities she did it on purpose.


'dagowa tayi idanuwanta sunyi jajir sbd kuka Dan tunda tafado takasa tashi sbd qafarta da hannunta sun bugu matuqa Amma ba'a ganiba zaa miqata ga hukumar makaranta sbd tafadowa 'dan gata.

Hannu ta zura cikin niqaf dinta ta share hawayenta tareda dafawa ta miqe tabi securities dasukazo tafiya da ita.


Sai gaf da magriba ta iso gida sbd tajima kafin subarta tatafi dukda sun mata gargadi Mai kyau akan karta Kuma ko lallon hanyarda Nik yabi bare takuma karyasa Dan mum 'dinsa tace next time aka qara bazata yarda ba.


Kodata dawo gida hankalin 'yan gidan tashi yayi dasuka ganta tana 'dingisawa..

Karo na farko data fara qarya arayuwarta kenan Dan cewa tayi 'dan adaidaita ya fa'di da ita.



Zazzafan zazza6i tayi tareda 'yar qaramar jinyar qafarta Dan satinta kusan 'daya rabonta da school Sai yau dazataje.

Sam yanxu tadaina Jin da'din makarantar Kuma takasa fadawa kowa sbd kada ahanata Dan tana matuqar qaunar karatun.


Asanyaye take shiri harsaida husna ta lura tace,

Ayshah lafiyarki kuwa?
Kodai jikin ne?

Safarta ta jawo tana sawa cikin muryar karaya tace,

Lafiya qlau kawaidai inajin kasalar zuwane.

Daria husna tayi tana saka hijab 'dinta tace,

Kodai kin gaji da karatun ne so kike ku zarge keda ya Umar''''ta qarasa zancen cikin tsokana.


Murmushi ayshan tayi tareda tuno fuskan ya Umar,,
Tabbas tana qaunar ya Umar halinsa ne bataso na rashin haquri da zafin zuciya Dan da'ace komai zai rage da tafi sha'awar auren nasu yanxu sbd ta huta da karatun Dan tuni yafara fita ranta sbd jikinta na Bata ba alkhairi a karatun Nan gaba.



Kwana goma ya share ko cup 'din ruwa baya iya 'dagawa da hannun duk da Dr ya tabbatarda ba wata karaya 'yar bugewace Amma sun 'dauki ciwon wani irin babba Dan mum har hutu ta 'dauka Dan kula dashi kawai ko dad 'dinsu Saida yazo yadubasa Yakoma Germany and yanda suka 'dau ciwon wani babba.



Koda ya warke Yafara zuwa makaranta Sam hankalinsa bai wani kwantaba sbd ayyanawa ransa da yayi Sam ita ba mutum bace aljana ce shiyasa ko mace Mai hijab ya gani koba niqaf Sai ha'diye yawu
Yanxu ko bakin gate baya iya zuwa Saida Murphy sbd tsoron karya ganta.



Yau suna fitowa lectures din farko ta fito ta nufi ladies toilet 'dinsu sbd period take tanason canza pad Dan ita Sam Bata iya wuce two hours da pad ajiki Bata canzaba.

Restaurant ta nufa danta siyo ruwan dazatayi amfani dashi.

Ku'di ta miqa aka miqo mata ruwan tajuyo kenan yakawo kowannensu cak ya tsaya cikeda tsoron 'dan uwansa yanda jikinta ya'dau rawa haka shima nasa Murphy yayi saurin riqesa tafara takowa ahankali jikinta na tsananta rawa zata bar gun sbd tarigada ta tabbatarda ganinsa ba alherineba.

Ganin ta nufo gurinsu yayi saurin sakin Murphy cikin tsoro da qarfi yace,,

Ghost,,,,
Ghost, ghost...

Aikuwa bashi kadaiba duka sauran mutanen gurin da gudu aka watse Sai ihu ake wasu harsuna fa'duwa.


Tsayawa tayi cak tareda duqawa ta fashewa da wani irin siririn kuka jikinta na sakewa.

Murphy dake tsaye shika'dai ne bai guduba Nan take yaji tabasa tausayi ya tako ahankali ya tsaya akanta cikin tausaya mata yace,

Ki daina kuka Kuma karkiji haushinsu sbd basusan Mai suke taredashiba acikin lullu6inki.

Miqewa tsaye tayi tareda ra6ashi ta wuce kukanta na tsananta.






Mamuh💋



_dont forget to vote, follow and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*3&4*


Toilet tashige da hanzari tareda rufowa tasaki wani sabon kuka ahankali,

Gabaki 'daya rayuwarta a makarantar ta zamar mata masifa Wanda take danganta hakan da qaddararta.

Rarrashin kanta tayi daqyar kafin ta zare niqaf dinta ahankali takalli fuskarta jikin mudubi taga baiwa ta kyau da tsarin halitta da Allah yayi mata rashin sani yasa ana mata 'daukar mummunar halitta.

Share hawayenta tayi tareda maida niqaf dinta tafito tawucewarta gida gabaki 'daya batareda ta tsaya attending sauran lectures 'dinta ba.


Da daddare bayan sunci abinci itada su husna tareda sauran yaran gidan suka nufi babban palon baba malam gurin 'daukar karatun dare Wanda qaidar gidance kullum da dare saisun 'dau karatu.

Awa 'daya da rabi sukayi sunayi kafin aka gama.

Gyara Zama baba malam yayi tareda gyaran murya
Nan kowa ya nutsu sbd sauraron Mai zai fa'da.

Kallon sauran dattijawan qannensa yayi kafin yace,

Mustapha 'dana ne Kuma ya 'dauko zance Mai girma Don kuwa ya take akidar gidan Nan daya tarar tun kakanni tunma kafin ni mahaifinsa a haifeni..
Ma'ana dai bayan mun tsayarda maganar ha'dashi aure da yar uwarsa jininsa ya tsallake waje yana neman auren wani yaren ma'ana bahaushiya.

Wani yawu iya lami ta ha'diye Dan kuwa tasan mummunan hukunci 'danta zai fuskanta Dan anta6a irin haka can baya abun baiyi kyau ba sbd Saida aka rasa rayuka.


Tsit palon yayi babu Wanda ya motsa sbd jinjina girman laifin da mustaphan yayi.

Cigaba baba Mal yayi da fa'din,
Mustapha kaje kashirya gobe bayan sallar juma'a za'a 'daura aurenka saudat a goben zaka koma gida nijar tareda matarka Kuma bamu yafe katako qafarka Nigeria ba kokuma Kiran 'daya daga cikinmu Sai bayan shekaru biyar.

Sunkuyar da kansa yayi hawayen baqin ciki da damuwa suka ciko idanuwansa sbd hukuncin da iyayensa suka yanke Masa bazai iya jadasuba Wanda wannan tarbiyace da'aka ba zuriar gidan kaf tun suna yara.

Saudat kuwa wani irin kukane ya kufce mata ahankali batajiba Bata ganiba laifinsa ya shafeta bayan auren bazata an datse mata karatu gakuma nesa dazatai da gida bako waya har tsawon shekara biyar.

Jikin kowane yasaki Banda iyayensu maxa dake da'da nanata yi musu fadan kowa ya kiyaye aikata irin hakan,

Baba Mal ma fa'da Mai tsanani ya 'dora dashi sbd ran iyayensu ya 6aci matuqa.

Umma sakina kuwa Jan 'yarta tayi cikeda tausayawa suka fice kowama ya fice jiki a sanyaye.

Ayshah kuwa 'dakin ummi tashige ta kwanta jiki asanyaye tana tsiyayar hawayen tausayin saudat da yaya mustapha.

Kallo 'daya umminta tayi Mata ta 'dauke Kai sbd Bata cika kulata kasancewarta 'yar farin..

Cikin sanyi da karyewar murya tace,

Duk lokacinda Abu yasamu 'dan uwanka Mara kyau to kayi qoqarin nesanta kanka da abun Nan sbd gujewa mummunan sakamako irin wannan.

Zuciyata takasa nutsuwa da zuwa makarantar ki Dan haka ki guje afkawa cikin irin wannan mummunan halin.

Tsit tayi tana sauraron nasihar umminta duk datasan Sam ita bazata iya fadawa soyayya da wani yarenba bayan nata Dan itama gwargwado tana

Please Login or Register in order to submit comment