Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biye dashi a
baya. Shigarsu keada wuya sai dalibai suka dauki
ihu baki daya 'boss! Boss! Suka daga Nafi'u
sama suna yawo da shi acikin ajin da kyar suka
ajje shi.
Nafi'u ya dubesu sannan yace "Ga Boss nan a
gabanku". Ya nuna Nuraddin da dan yatsansa
hannunsa na rawa. Har yanzu ganin mahaukaci
yakewa Nuraddin Nafi'u ya zagaya ya nufi gurin
zamansa, a ganinsa kowanne lokaci zai iya
hawansa da duka.
"A'a yau kuma guduna kake yi?" Nuraddin yace,
sannan ya fashe da dariya. "karyar banza ashe
dai gabama da gabanta wai Aljani ya taka wuta,
ka kake cewa wai ko shedan ne mutum baka
tsoronsa."
anya kuwa nima xan iya bin Nuraddin domin jiyo
muku abinda zai faru?
Sai kuma mun sake haduwa daga

Aljani Ya Taka Wuta!....6
-
-
-
-
Dajin yayi shiru bakajin komai sai motsin
ganyayyaki bishiyoyi dake gogayya da juna
sakamakon iskar dake busawa cikin wasu lokuta
kuma akwai jefi-jefin kukan tsuntsaye da sautin
ruwan dake gudana cikin koramun dake zagaye
da gurin.
-
Nuraddin yaci gaba da tafiya, amma har yanzu
jikinsa rawa yake, domin daya daga cikin
kawunannan masu gemu daya gani, yaso yayi
kama da kan malam mahmud, malamin
arabiyarsu, ni kuma wanda na gani yaso yayi
kama da kan mai karanta labarin nan hehehe.
-
Bai dade da fara tafiya ba sai yazo daf da inda
hanyar ta rabu gida biyu, hanyar datayi gabas,
itace zata kaishi har zuwa makaranta. A daf da
gurin tsakanin wasu bishiyoyi guda biyu, wata
katuwar tsamiyace mai duhun ganye. Anan ne to
Nuraddin yaga abin mamaki.Yana zuwa inda
hanyoyin suka rabu, sai ya mike cikin sauri yabi
wacce ta nufi gabas din ba zato ba tsammani sai
bishiyar tsamiyar dake tsakanin bishiyoyi biyun ta
girgiza sannan saita tunbuko daga cikin kasa,
jijiyoyinta a waje tsirara, sannan saita nufi
tsakiyar hanyar da Nuraddin kebi ta dasa kanta a
hanyar. Nuraddin yayi turus ya tsaya cikin
kaduwa, yayi kamar ya koma da baya, to amma
idan ya koma da baya din ina za shi? Jikinsa na
rawa sai ya karkata yabi daya hanyar data nufi
kudu lokaci guda sai bishiyar ta sake tunbukewa
ta tashi sama sannan ta sauka a tsakiyar hanyar
daya fara bi ta sake dasa kanta. Nuraddin ya
sake yin turus ya tsaya akaro na biyu, sai dai
wannan karon lokaci guda ya juya a razane zai
gudu, sai yaga bakin labulen duhun nan ya sauko
a gabansa da sama bakinkirin babu hanyar gudu.
Ga yamma tayi bakinkirin babu hanyar wucewa
ga gabas bishiya ta tare hanya. Nuraddin ya juya
nan, ya juya can yana neman hanyar gudu lokaci
guda kuma kwakwalwarsa nakokarin tuno addu'a
kowacce irice ma, sai dai rabonsa da rike addu'a
ma, tun yana karatun dare a waje babansa.
A dai-dai lokacinne wata katuwar mage ta keto
da gudu daga cikin bakin duhun daya rufe
bayansa, ta nufi kan katuwar bishiyar. Hawan
magen keda wuya sai bishiyar tayi girgiza nan da
nan ta rikide ta koma wata irin halitta mai zako-
zakon hakora kamar kibiya, gashin kan halittar
tamkar kayoyin aduwa. Halittar tana da kofato,
sannan abin mamaki kuma shine dukkan jikinta a
lullube yake da gashi kamar tunkiya.Nuraddin ya
dubi jibgegiyar halittar ya rufe idanunsa yana mai
fatan dama mafarki yakeyi, sai dai kuma arufe
idanun nasa ma bai hana shi ganinta ba. Ya sake
bude idanun nasa ma bai hana shi ganinta ba.
Yasake bude idanun har yanzu dai tana nan
shirim! A gurin tana dubansa da jajayen idanunta
masu kamar garwashin wuta."Bance kada na kara
ganinku a hanyar nan cikin dare ba"? Ta bugawa
Nuraddin tsawa hayaki na fita daga bakinta
kamar salansar mota."kai kafi kowa taurin kai
ko"?Nuraddin yayi tsaye yana kallonta, yana
kuma sauraronta. Tun abin na bashi tsoro harma
ya soma bashi haushi."shin baka ji kashedin da
nayi maka bane"?"Banji ba"! Nuraddin ya samu
kansa yana mai cewa. Bai san lokacin da kalmar
ta subuce masa ba, amma ya gama yanke kauna
cewa wannanitace kalmar karshe da zai furta a
duniya, jira kawai yake yaji tayi sama da shi ta
jefa a cikin wangamemen bakinta mai kama da
kofar gari.Shiru-shiru baiji komai ya faru ba, babu
kuma alamar motsin komai a dajin sai sautin
zubar yayyafar ruwan da har yanzu bai daina
zuba ba. Nuraddin ya bude idanunsa a hankali, ga
mamakinsa sai ya hanyar wayam babu matar
nan ta bace haka nan bishiyar tsamiyarnanma ta
koma inda take ta zauna. To amma lokacin da
Nuraddin ya waiwaya bayansa, saiya ga har
yanyu duhun dake bayansa bai yayeba. Wannan
shiya dada tabbatar masa da cewa har yanzu
yana cikin hadari, domin ya san mai zako-zakon
hakoran batayi nisa da inda yake ba.Daga inda
Nuraddin ke tsaye yana jiyo rugugin aradu jefi-jefi
a can wani bangare na cikin dajin. Ba'a dade ba
sai aka sake kwatsama wata aradun mai karfin
gaske wannan karon ma har tafi wadanda akayi a
can baya tsoratarwa. Walkiya mai hasken gaske
ta biyo bayan aradun. A cikin'yan dakikun ne to
Nuraddin ya fara ido biyu da wata kyakyawar
sura. Walkiya ta haskaka wajen, Nuraddin yakai
idanunsa ga ruwan dake gudu a gefen hanyar, a
cikin ruwanne to yaga kyakyawar fuskar ta tana
masamurmushi."Yau na gamu da gamona".
Nuraddin yace cikin zuciyarsa. A daidai wannan
lokacinne sai yaji wani irin ni'imtaccen kamshin
turare ya mamaye gurin, sannan ne to ta
bayyana a gabansa a zahiri kamar an jehota daga
sama, fuskarta na sheki da annurh, hasken
kyakykyawar fatar jikin budurwar shiya haskaka
dajin. Kyawun budurwar bashi misaltuwa ga dan
adam. Doguwa ce ba can ba'yar shafalfal mai
tsukakken jiki da kyawun girar idanu, fatar
bakinta narai narai dasu jajaye suna kyalli kamar
ka taba jini ya fito, gashinta abin kallo da daukan
hankalin duk wani da namijin duniya....

Aljani Ya Taka wuta!.....7
-
-
-
"Jarumi Nuraddin". Tace dashi tana haskaka
fuskarsa da tattausan murmushin Allah kashe ni
dan dadi.Nuraddin ya dubeta duban nutsuwa tun
daga sama har zuwa kan kafafunta. Hakika duk
halittar dake jikin budurwar babu makusa, tunda
yake bai taba ganin halitta mai kyawunta ba, ko
shakka baya yi, yasan ta ninka Badawiyya kyau
nesa ba kusa ba. Ga mamakin Nuraddin sai yaji
duk tsoro da fargaba sun sake shi lokaci guda
kamar cirar kaya.To amma fa duk wannan kafin
idanun Nuraddin ya kawo ga kasan kafarta ne.
Ko da idanunsa suka kawo ga kafarta, sai
kamannin sha'awar dake fuskarsa suka
sauya,suka rikide zuwa tsoro da fargaba. Ba wani
abune yasa jikinsa sanyi ba, sai ganin
kyakykyawar buduwar dake gabansa bata da tafin
kafafu irin na bil'adama, maimakon hakan, sai
kafta kaftan kofato irin na giwa.Kai Allah wadan
naka ya lalace. Nuraddin yace cikin zuciyarsa
lokacin da yaga kofaton. Ga doki hardoki amma
kofaton na sakainane. Ya sake cewa da
kansa.Buduwar ta dubeshi yayin data tabbatar ya
kare mata kallo, sannan ta fara matsawa kusa
dashi.Nuraddin ya yi tsalle gefe guda don gudun
kada ta taka shi da kofato."kada kaji tsorona
Nuraddin, domin yanzu tsakanina dakai babu cuta
ko cin amana, sai so da kauna da amincewa, duk
duniyar nan a yanzu babu wanda nake kauna sai
kai, ba dan komaiba kuwa sai dan ganin kaine
mutum na farko daya fara ganina a mummunar
kamata bai sume ba".Ta danyi shiru ga barin
daddar magana cikin murya mai kama da sarewar
mutanen hindu, sannan taci gaba da ce.Dubeni da
kyau Nuraddin, kyakykyawa ce kana sona?
Nuraddin ya dubeta tun daga kan kyakykyawar
fuskarta har zuwa kan kofatonta jikinsa na rawa
ya sake dubanta yace."Tabbas babu wani dam
adam dazai ganki yace baya sonki, amma idan
yana da hankali babu abin dazai sa ya kusanceki
ballantanamaharya soki da wadannan kaba-
kaban kofato a kafarki. Ya nuna kofaton dake
kafarta, sannan ya dada ja da baya kamar wanda
ake bi da wuta.Budurwar mai kofato, ta dubeshi
sannan ta hade fuska tace"da wani ne ya fadi
haka bakai ba saina tsotse jininsa na shanye
bargonsa, sannan na karairaya kashinsa na
watsar a bayan duniya.Tsohon lokaci buduwar
tana kallonsa kawai batace dashi komai ba. Jikin
Nuraddin ya fara tsuma domin tunaninsa rikidewa
zatayi zuwa jibgegiyar halittar nan ta dazu,to
amma ga mamakinsa sai budurwa ta haskake shi
da wani tattausan murmushi.Ka daina jin tsorona
Nuraddin, ai na riga nayi maka alkawarin bazan
taba cutar dakai ba, kuma ni mai kokari ce gurin
cika alkawari, ba kamar ku bane bil'adama.Budur
war mai kofato ta ja baya, sannan saita durkusa
kasa, kyakykyawar doguwar rigar dake jikinta mai
sheki da kamshin gaske ta sauko ta lullube
kofaton. Kusan tsahon dakiku ashirin, sannan ta
sake mikewa tsaye. Tun kafin doguwar rigar ta
gama dagewa sama Nuraddin ya hango santala-
santalan kafar kyawawan gaske, baitaba ganin
tafif kafar mace mai kyawunsu ba.Daman ku'yan
Adam gajen hakurine daku da tun farko ma kayi
hakuri, sannu a hankali zaka ga surar da baka
taba ganin irinta a jikin wata'ya mace ba a
duniyar nan. Ta danyi shiru tana karkada
awarwaron dake hannunta kan taci gaba da
cewa."sunana AMAL'yar sarkin Aljanu. Mahaifina
shike sarautar duk aljanun dake wannan nahiyar,
muba kananan Aljanu bane. Dan haka inaso ka
kwantar dahankalinka da sannu zan kaika ku
gana da mahaifina, mutumin kirki ne, kuma nasan
dole ne ma ya kaunaceka in dai na bashi
labarinkadomin yana son jarumi irinka.Budurwa
Amal ta daga hannunta sama, sai farantan abinci
da kayan marmari iri-iri na sauka a gabansu.
Ba'a dade ba sai wata katuwar rumfa ta alfarma
ta sauko daga sama ta kare musu ruwan saman
da har yanzu yake zuba kadan-kadan.Amal ta
zauna, amma Nuraddin yakimotsawa daga inda
yake, har yanzu gani yake kamar zata sake
rikidewa zuwa wata halittar mai ban tsoro.Zauna
mana Nuraddin, ko har yanzutsorona kake ji?
Haba nuraddin ka yarda mana da alkawarina, ai
ni dakai yanzu mun zama daya.Jin haka, shiyasa
nuraddin ya koma can gefe guda a cikin rumfar
ya zauna akan lallausan kilishin daya mamaye
duk cikin rumfar. Nuraddinya dan lallatsa kilishin
da hannusa, laushi tubus kamar katifa. "Matso
kusa dani mana Nuraddin". Tace dashi a
tausashe.Nuraddin yayi karfin hali ya matso kusa
da ita ya zauna jikinsa na rawa, har yanzu tunani
yake zata rikide.Amal ta dubi Nuraddin sannan
tayi masa murmushi, ta dada matsawa daf da
shi, har yana iya jin hucin numfashinta mai
kamshin turare a fuskarsa.Ashe suma aljanu suna
numfashi irin na dan adam. Nuraddi ya fadi cikin
ransa."Kayi min murmushi mana Nuraddin ko
baka sona ne"?A karo na farko da Nuraddin yayi
koka ri, ya jefeta da wani dan saurayin fatalwan
murmushi.Amal ta dafa kafadarsa tace."Nuraddin
kana sona kuwa"?

Aljani Ya Taka Wuta!......8
-
-
-
Wanene zai iya dubanki a haka yace baya son
kyakykyawa kamarki? Ai kowa yana son mai kyau
indai kafa babu kofato". Nuraddin yace da ita
yana duban fuskarta mai sheki.Amal tayi shiru
tana sauraronsa, sannan sai ta rankwafa ta dora
kyakykyawan kanta akan kafadarsa tace."Naji
dadi Nuraddin, wallahi nima ina sonka matukar
so, naji dadin cewar kaima kana sona". Ta danyi
shiru, tana wasa da gashin kanta akan
kafadarsa.Nuraddin ya dimauce, saboda ni'ima da
kamshin turare dake tashi daga cikin
gashinta."Ina so ka sani cewa daga yau kayi
sallama da talauci har abada, muddin kana tare
dani, ni'imar duniya kam ka hadu da ita, duk
abimda kake so ka ambace kawai ka samu
masoyina, sannan kuma nayi maka alkawarin
idan jarabawarku ta karshe tazo, kada ka dami
kanka da wani karatu, domin nida kai zamu yi
jarabawar zan bude maka tafin hannuna duk
abinda kake bukatar sani yana nan a rubuce, sai
dai kuma ina so ka sani cewa kai kadai kake da
ikon ganina."Amal ta danyi shiru sannan taci
gaba da cewa."To, Nuraddin nidai kaji alkawarina
saura naka Nuraddin, ina so kayimin alkawarin
idan duk nayi maka wadannan abubuwan dana yi
maka alkawari zaka aureni"?Amsa kuwar
tambayar ta daki dodon kunnensa a bazata,
hakika al'amarin ban mamaki na faruwa gareshi
cikin daren nan. Nurdaddin yasa hannunsa a karo
na farko ya dafa kyakykyawan hannunta yana
tunani. Ni Nuraddin yau da auren aljana? Ya fadi
cikin ransa. Koda yake ba aibu bane na aureta,
indai har zata mayar dani mai arziki, to daman
duk duniya ma me ake nemainba kudin ba? To
kuma gashi sun zomin a bulus, in kuwa hakane
mezai hanani aurenta. A lokacin ne to Badawiyya
ta fado masa a rai. Hakika yana son Badawiyya
matukar so, domin ta dade tana wahala akansa
iri-iri dan me yanzu dare daya zai mata haka, don
kawai ya hadu da aljana mai siffa biyu,
mummuna da kyakykyawar siffa, waya sani ma
ko nan gaba in ya sake ya aureta ta sake
rikidewa. Amma dai bari na fara cin bulus din
kafin na yanke shawara. Tabbas bazan taba barin
Badawiyya ba mai sona tsantsa, ba dan jarumta
ta ba, ko rashin tsorona. Yace da kansa a zuciya,
sannan sai yace a fili."Zan aureki Amal".Amal ta
dago kanta dake kan kafadarsa ta dubeshi
tace"da gaskeNuraddin? Don Allah da gaske zaka
Aureni"?Dagaskenake Amal, ai na fada miki babu
wani mutum dazai ce baya kaunarki a duniyar
nan Nuraddin yace yana duban fuskarta."Alkawari
fa Nuraddin, nasan halinku na'yan Adam baku da
alkawari.""To, shikenan Nuraddin, tunda ka
amince gobe saika shirya mutafi na kaika gurin
mahaifina ku gana, sannan kuma shima kayi
masa alkawarin zaka aureni". Gaban Nuraddin ya
fadi, jin cewa za'a tafi dashi gurin sarkin Aljanu,
ya dubeta a tsorace zaiyi magana sai ta daga
masa hannu."Nasan abinda kake tunani, indai
idan wannan ne, kada ka damu kanka, domin
babu wani aljani daya isa ya tabamin bakona
ballantana kuma masoyina". Ta danyi shiru
sannan tace."kayi kokarin rike alkawari Nuraddin,
domin bana son mai karya alkawari, kuma daga
yau bazaka sake ganinaba cikin mummunar
siffata ba ta farko. Nayi maka alkawarin hakan".
Amal tace sannan saita mika dan karamin dan
yatsanta na dama tace tana murmushi."mukul
la".Nuraddin ya mika dan yatsansa suka kulla
alkawari sannan sai Amal ta cire daya daga cikin
zoben zinariya ukun dake hannunta, ta kama dan
yatsansa ta sa masa zoben ta ce."Daga yau in
kana son ganina, sai ka murza wannan
zoben,zaka ganni nazo, sai dai kuma inason ka
sani cewa bana zuwa da goshin magariba,
bakuma na zuwa da asuba, dan haka kada ka
murza zoben a wadannan lokutan dan bazaka
ganni ba, sannan kuma babu wani aljani daya isa
ya tabaka inhar kana tare da wannan zoben koni
dana baka shh kafi karfina, nima daga wajen
mahaifina na gajesu. Guda ukune daman gashi
nan na baka daya ka kula dashi da kyau kada ka
sake ka baiwa kowa, domin yanada matukar
amfani da daraja. Mahaifina ya taba rantsewa
yace duk dan adam din da aljanu suka taba ya
haukace koya nannade, ma'ana sassan jikinsa
suka shanye, to dazarar anjika masa zoben nan a
ruwa yasha zai warke kamar wani abu bai taba
samunsa ba, sannan kuma in har kana tare da
zoben nan babu wani aljani daya isa ya tabaka,
koda kuwanice kamar yadda na fada ma tun
farko.Tayi shiru tana jujjuya kanta akan
kafadarsa, tana mayar da numfashi."Gobe sai mu
hadu dakai anan kamar wannan lokaci, sai mu
tafi nakaika wajen mahaifina, domin ya dade yana
damuna akan na samo miji, to gashi na
samu".Amal ta miki tsaye ta dubi Nuraddin zaune
tace". Rufe idonka".Cikin mamaki sai Nuraddin
yabi umarninta. Alokacinne yaji tace."To nuraddin
sai goben kenan, Allahbamu alheri kana iya bude
idanunka".Bude idonsa keda wuya ya ganshi
zaune akan gadonsa.

...ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI part
{11}...
Cikin mamaki, sai yayi sauri ya dirgo daga kan
gadon yana waige waige, domin a tunaninsa Amal
ce keson cigca da wasa da hankalinsa. Nuraddin
ya dubi sauran gadajen dake daki, sai yaga duk
abokan kwanansa ne wadanda ya sani kwance
suna bacci abinsu. Ya leka tagar dakin, sai ya
hango farfajiyar makarantar kamar dai yadda ya
santa, ciki mamaki sai ya dawo ya zauna a bakin
gadon, sannan ya rufe idanunsa da tafukan
hannayensa. Nuraddim ji yake kamar ya farka
daga wannan mummunan mafarki. Adai dai
lokacinne ya tuna da zoben data bashi, cikin
gaggawa ya dubi dan yatsansa. Tabbar zoben
nan yana sheki. Nuraddin ya murza zoben.
"Menene kuma"? Amal ta sake bayyana acikin
daren, sanye da doguwar rigar bacci tana
murmushi. Dakin ya game da tattausa kamshin
turare. "Ko baka jin baccine nazo na tayaka
hira"? Tace dashi tana murmushi.
Nuraddin ya juya ya dubi sauran yaran dake
kwance a dakin suna ta sharar bacci, gabansa na
faduwa yana ta addu'ar Allah yasa kada wani ya
farka ya ganta a dakin.
"kada ka damu dasu, ai baza su iya ganina ba,
bakuma zasuji hirarmu ba, koda wani ma a
cikinsu ya farka to a kwance zai ganka kana
bacci".
Tana gama fadin haka sai ta jefeshi da tattausan
murmushi ta bace.
Awashegarin ranar, acan kofar makarantar
misalin goma sha biyu na rana musa mai gadi ne
keta jayayya da wata kyakykyawar yarinya dake
tsaye a gabansa.
"Kacd dashi Badawiyya ce keson ganinsa". Ta ce
dashi cikin kaguwa.
Ai ba fadar sunan ne wahala ba, abin da nakeso
ki gane shine neman mutum daya ciki duban
dalibai cikin wannan uwar ranar mai kamar ta
tashi Alkiyama ba karamin aiki bane". Mai gadi
yace.
Badawiyya ta kule, sannan sai wani tunani yazo
mata nan da nan sai ta juya ta dubi direbanta
tace dashi. "Dauko min jakata".
Cikin sauri direban ya tura hannunsa ta cikin
budadden gilashin motar, ya laluba kujerar ta
baya ya daukowa Badawiyya jakarta.
Badawiyya ta bude jakar, sannan ta dauko "yan
wasu adadin takardun naira hamsin-hamsin tace
da maigadin. Ga wannan kasha ruwan sanyi,
amma don Allah taimaka ka nemomin shi".
"Ai dole ne tunda kin bada maganin rana!
Maigadin yace yana rawar jiki. "yaya kika ce
sunansa"?
"Nuraddin Abubakar". Badawiyya tace.
Maigadin ya ruga da gudu, ya nufi cikin
makarantar, zuciyarsa tana mai mamakin abinda
ya hada wannan kyakyawar yarinyar mai kwarjini
ga karfin mayen karfen kudi a tattare da ita da
wannan watsattsen shaidanin yaron Nuraddin.
Abin da ya faru a daren shekaran jiya ya tambara
Nuraddin a duk fadin makarantar kai harma cikin
gari, dalibai kuwa har kanana "yan aji daya babu
wanda baisan shiba, domin ko yau aka kawoka
dalibi makarantar sai an baka labarin Nuraddin.
Ba'a dade ba sai ga mai gadin sun dawo tare da
Nuraddin, sanye da kayan makaranta farare, da
koriya Hula.
Nuraddin ya dubi Badawiyya cikin Mamakin
abinda ya kawota bayan kwanansa uku kacal da
rabuwa, tabbas ba lafiya ba. Amma ga
mamakinsa sai yaga tundaga nesa Badawiyyi ta
fara masa murmushi.
"Wallahi Nuri tunda ka taho bana iya barci,
tunaninka ne ke damun zuciyata, shiyasa nace
bazan iya ba gara na lallabi direbanmu ya kawo
ni na ganka, yanzun ma kaga ko sani ba'ayi a
gida ba".
Nuraddin ya dubi abar kaunarsa cikin mamaki, so
da kaunarta suka dada kwarara a cikin zuciyarsa.
"kina nufin abinda ya kawoki kenan kawai ki
ganni"?
Badawiyya tayi murmushi, sannan ta gyada kai
tace. "Ai ya wuce kawai Nuri, domin tunda ka tafi
nake Mafarkinka, wallahi 'darling' duk inda zani
dakai nake yawo a zuciyata, gaskiya ni dai ina
ganin daka gama sakandire zamuyi aure, ko kana
sami damar ganinka kullum a kusa dani, inka
shiga jami'a ma take tafiya da matarka.
Nuraddin ya fashe da dariya. "Lallai kam kinyi
dabara, kinga naji dadin zaben kala-kala acan
jami'ar naji ance canne gidan mata".
Badawiyya ta harareshi tace. "kama fara mana"!
Ta danyi shiru, kana ta dubi dan yatsansa ta
girgiza kai tace". Koda yake ma dai nasan Maza
baku da tabbar. A ina kuma ka sami
kyakykyawan zoben nan, watace ta baka"?
Badawiyya tace tana murmushi. To sai dai kuma
lokaci guda murmushin dake fuskar Nuraddin ya
subuce daga fuskarsa, gabansa ya fadi.
"Au! Menene na wani bata rai, don kada nace a
bani, to duk abinka saina karbi zoben nan a kalla
dai inna dube shi yake tunamin dakai, ya dauke
min kewarka".
Nuraddin yayi shiru yana dubanta cikin taraddadi
da fargabar abinda zai biyo baya, lokaci guda
kuma maganar Amal ta fado masa
*kada ka rabu da zoben nan domin yana da
matukar daraja da amfani ga bil'ada".
To, amma ai Badawiyya ma masoyiyarsa ce,
kuma tayi masa wahalhalu da dama a rayuwarsa,
duk dayake dai haduwa daya kawai sukayi da
Amal amma ta mayar da shi mai arziki. Tun safe
yake kashewa abokansa kudi, dayasa Hannu a
aljihu sai kawai ya yita zaro kudi, kai duk abinda
yayi niya idan yasa hannunsa a aljihu saiya
dauko. To koma dai menene Badawiyya ita ta
fara wahala akansa kafin kowa.
saida yamma.

Aljani Ya Taka Wuta!......12
'
'
-
Hakika zoben kyakykyawane kamar Nurinta.
Tambayar kawai da har yanzu takasa ramun
amsarta itace. A ina Nuri ya sami wannan
kyakykyawan zobe? Ita dai ta san kudin da ta
bashi bai isa ya saya masa irin wannan kerarren
zoben ba. Amma bari ya dawo zan tambaye shi.
'
Badawiyya ta fadawa kanta kana ta kuma duban
zoben, sannan sai ta kama zoben ta murzashi
tana murmushi, a ganinta zoben kamar Nurinta
ne. Da ba goshin bane, da Badawiyya tayi
kaduwar da bata taba yin irinta a duniya ba,
domin tana murza zoben mai shi zata bayyana a
gabanta. Badawiyya tayi sa'a domin'yar sarkin
aljanu Amal bata bayyana da goshin magriba,
amma da zarar magriba ta wuce zata iya
bayyana a sa'ar da aka murza zoben, ta koma
kan daya daga cikin dogayen kujerun alfarmar
dake dakinta ta fara cire kayan dake jikinta tana
jefawa akan kujerarta.
'
Al'adar da ta samawar kanta a duk magaribar
duniya take son farawa.Al'adar a kullum kwanan
duniya shine wankan magariba. Koda yake wasu
lokutan in har bada wuri zata kwanta ba, ta kan
bari har sai lokacin barcinta yayi saita shiga
wankanta. Amma idan har Nuraddinyana nan Nuri
Darling a yadda takankira shi, wankan magariba
wajibi ne a gareta ba mustahabi ba. A duk sa'ar
da Nuraddin ya dawo hutun makaranta, takan
shiga wanka tun karfe bakwai na yamma.
Wankan da shafe-shafe da kuma kyale-kyalenta,
takan shafe akalla sa'a guda tanayi. Da zarar ta
gama saita nemi guri ta zauna cikin annashuwa,
annuri na fita daga fuskarta, yayin da daddadan
kamshi madaukaki ke hurowa daga jikin
kyakykyawar halittarta, taci gaba da jiran abin
kaunarta Nuraddin wanda idan yazo suka fara
hira basa rabuwa sai karfe goma shabiyu na
dare. Aikin kenan kullum kamar karatu, har kuma
sai Nuraddin ya koma makaranta sannan sai duk
soyayyar ta koma kan hotonsa.
-
Badawiyya ta fito a hankalin tana rangwada, ta
daura farin zani iya kirji, gashin kanta ya
warwatsu akansantalelen wuyanta mai kamar na
barewa. A duk sa'ar data motsa sai ruwa ya
fantsamo daga cikin gashinta. Fitowarta kenan
daga al'adarta ta wankan magariba.Ta zauna a
hankali akan daya da cinwasu kujeru takwas
masu numfashida suka zagaye dan madaidaicin
dakinta, kana ta janyo wan dan karamin teburi
fari mai tafiya akan kananan tayoyi. Wannan
teburin shine dan dakon kayan kwalliyar
Badawiyya. Sannu a hankali tana tafe tana
rausaya har takai ga wani tangamemdo madubin
kwalliya ta fuskanceshi. Daga cikin madubin tana
iya hango kofar dakin da zata kaika har falon
cikin gidan.Badawiyyata dauki wata 'yar doguwar
kwalbar rob, wacce ke dauke da lallausan man
shafawa mawadacin kamshi, ta matso man akan
tafin hannunta na hagun. Sannan tasa na dama
ta fara shafawa. Agogon dake jin bangon dakin
ya fara rera sarewa, karfe takwas na dare,
Badawiyya tayi murmushi data tuna da abin
kaunarta Nuraddin. Ta daga hannanayenta izuwa
fuskarta ta farashafa lallausan man, sannan ta
lumshe idanuwanta cikin annushuwa tace.NURI
DARLING!!! Bata dauke hannayenta daga fuskarta
ba, ba ta kuma bude idanunta ba, domin ji take
kamar hannayen Nuraddin ne ke lullube da
fuskarta. A haka taci gaba da tunaninta. Sabanin
al'adarta ta yauda kullum a ka'ida Badawiyya
bata wanka karfe takwas na dar har sai idan abin
begenta Nuri yana gari, amma yau sai gashi tayi
saboda dalilai biyu. Na farko mafarkin da tayi a
daren jiya na matar nan mai mummunar halitta
wacce ke kokarin kwace mata Nuri. Hakan shiya
sata wanka yau tun kafin karfe takwas na dare.
Domin a tunanin Badawiyya koda Nura baya nan,
kamata yayi ace tana raya lokacin hirarsu.
Wannan shine dalilin wankanta domin tayi
alkawarin zatayi kwalliya ta zauna tasa hoton
Nuraddin a gaba tayi ta hira koda kuwa bazai
amsa mata ba,ba kuwa zata daina kallonsa ba
har sai sha biyun dare wanda shine ka'idar
lokacin rabuwarsu da Nuri darling.Dalili na biyu
kuma shine tana tunanin idan takai sha biyu
batayi barci ba, da wahala ta sake mafarki da
mummunar matar nan mai kokarin kwace mata
Nuraddin. Hakika mafarkin ya tayar mata da
hankali. Domin Badawiyya bata da wani abokin
gaba a duniya da ya wuce wanda zai rabasu da
*NURI DARLING*.Da farko da tayi mafarkin mata
mummuna ce amma sa'ar data farka ta sake
komawa barcinta, sai matar tazo mata a siffar
kyakykyawa. Abin bakin cikin kuma ga Badawiyya,
surar matar a wannan lokacin tafi tata kyau nesa
ba kusa ba. Mafarkine kawai amma duk da haka
ya tayar mata da hankali.Tunaninta ya katse
sakamakon sauyin yanayi dataji a jikinta. Haka
kawai ba zato ba tsammani, sai taji jikinta ya
fara rawar sanyi sannan taji wani abu mai kamar
iska ya na kada gashin kanta, sannan abu
mafitashin hankali da figitarwa shine lallausan
man datake shafawa a fuskarta sai taji yayi sanyi
kalau tamkar tana shafa kankar adai dai lokacin
ne taji karar budewar kofa kuu!Ina vaxan iya
ganin wannan tashin hankalin ba. Wani abu yayi
ta kururuwa cikin kwakwalwarta yana cewa kada
ta bude idanunta, saidai kuma mai gargadi ya
makara.......
-


"""ALJANI YA TAKA WUTA CI GABAN LABARI
{Part 13}"""
Nuraddin yaci gaba da tunani, sai gashi kuma
lokaci guda Amal na barazanar zata mayar da
burin wani shudadden mafarki. Bazai yiwu ba,
yace a ransa. Nakoma matsiyaci, tabbas ba zata
sabu ba bindiga a ruwa.
Nuraddin ya dubi amal ya sunkuyar da kansa
kasa yace da ita a tausashe. "kin kasa fahimtata
Amal, abinda nake son ki gane shine, so nake mu
rabu da Badawiyya cikin salama, ke yanzu kina
ganin bayan abinda tayi min ya dace na watsar
da ita gefe guda"? Nuraddin ya girgiza kai sannan
yaci gaba da cewa. "Daga yanzu Amal zan rike
dukkan alkawarin danayi miki, kece baki san
zuciyata ba amma wallah tunda na doraki a
idanuna naji begenki ya lullube tsokar zuciyata,
dan haka ina son ki kwantar da hankali nayi miki
alkawari idan na koma gida, da zarar mungama
jarabawarmu ta karshe, zanyi kokarin mu rabu da
Badawiyya.
Ni kaina nasan ba dai dai bane ace "yar talakan
mutane tana takara da 'yar gidan sarkin aljanun
duniya mai kyawun sura kamarki".
jin hakan keda wuya, sai wani tattausan
murmushi na farin ciki ya subuce daga bakin
Amal. Ta sunkuyo da kai a hankali zata sumbace
shi, sai ta tuna she bai riga ya aureta din ba.
Cikin sauri sai ta dauke kanta ciki jin kunya, kana
tace dashi. "Alkawari fa Nuraddin"?
"eh alkawari, kada kiji komai ai sanin kanki ne ba
daya kuke da Badawiyya ba ai ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin bakin kaza, duk da yake dai
itama kyakykyawa ce acikin mutane, amma ai
gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta".
"tsokana fa kenan"? Amal tace tana dariya
wallahi wannan karin maganar taku ta mutane ta
fita daga bakinka".
Nuraddin ya fashe da dariya, sannan ya juya
firgigit yana leken taga don kada wani yaji sautin
dariyarsu ya shigo ya ganshi shida yar sarkin
Aljanu.
"kada ka damu da wadanda suke waje, domin ko
sun shigo ma baza su iya ganin mu ba, kai dai
kawai shirya mutafi mahaifina na can yana
jiranka.
Nuraddin yayi ajiyar zuciya hakika yana tsoron
zuwa garin da babu kowa sai aljanu, amma
yanzu ya tabbata Amal bazata bari a cuceshi ba.
Nuraddin ya mike tsaye a tsorace yace "mutafi".
Nuraddin yabi umarninta. Rufe idonsa keda wuya
yaji tace bude. Yana budewa sai ya ganmu a
cikin wata katuwar alkarya mai dauke

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment