Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta wannan hatta numfashi idan akayi a
bayana, indai kece sai na gane domin ba
idanuna bane kawai suke ganinki ba Badawiyya,
hakika duk wani shashe na jikina ganinki yakeyi
musamman ma zuciyata".
Wannan tunani shiya dada sa Badawiyya ta
sakankance cewa Nuraddin baya dakin.
Wata zuciya tace da ita fita ki nemi mijinki a
waje. Badawiyya, domin dakin da take tsaye shi
kadai ne bashi da kwan wuta. Dama ba wata
tsiya bace a cikin dakin, kilishine kawai
shimfide da kujeru kanana guda biyu, tuni
daman Badawiya ta sanar da mahaifinta cewa
gidan fa ya musu girma ita da mijinta Nuri,
domin dakuna sunyi yawa aciki.
Badawiyya na nan dai tsaye tana son ta juya,
amma tsigar jikinta sai wani yar-yar take yi.
"NURADDIN". Ta sake kiran sunan cikin wata
rarraunar murya, shi ta dada gaishe da
kunnenta. Wani sassanyan gumi ya fara sartu a
gefen fuskarta. Badawiyya tayi sauri tasa bayan
hannunta ta share, babu abinda ta tsana irin
ace tayi kwalliya, amma gumi ya fara kokarin
bata mata kwalliyar musamman ma wannan
rana data shafe sama da sa'o'i biyu gaban
madubi tana shafe-shafe da goge goge, duk dan
mijinta Nuri.
Idanun Badawiyya sun fara sun fara sabawa da
duhun dakin, hakan ita tasa ta fara hangen
duhu-duhun wani abu kamar kullin kayan
wanki acan kuryar dakin.
Abu na farko data fara tunani shine inda
makunnin lantarkin dakin yake, duk da dai a
iya saninta, har lokacin da suka zo duba gidn
ita da Nuraddin yana daya daga cikin dakunan
da basu da kwan lantarki, amma tasan tun
shekaranjiya mahaifinta ya turo ma'aikata
domin susa duk wani abu da babu shi a gidan.
Wannan shiyasa Badawiyya ta dada matsawa
kadan jikin bango ta fara laluben makunnar
lantarkin dakin.
Adaidai lokacin da hannunta ya tabo makunnar
wutar lantarkin ne to taji kafarta ta zunguri
wani abu. Gabanta ya fadi ras! Abinda ta
zungura yaso yayi mata kama da jikin mutuma.
Badawiyya tayi tsaye nan sororo hannunta akan
makunnin wutar. Tsahon dakiku tana nan tsaye
zuciyarta na harbawa, daga inda take tsaye
tana jiyo haniyar samari da 'yan mata dake
shagali da sowa a farfajiya gidan. Ba zato ba
tsammani sai taji abinda ta shura da kafarta ya
dan motsa. Badawiyya taji kamar ta saki fitsar
a wando saboda kaduwa, kwatsam kuma sai taji
an fara wani gurnani marar dadin ji, gurnanin
yaso yayi kama dana namun daji, hantar
cikinta ta kada.
maryam Ellelah
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.29}
"Na shiga uku" Badawiyya tace gami da rike
numfashi. Cikin gaggawa tayi niyyar ja da baya
domin ficewa daga dakin, rabon sai tayi
mummunar gani, sai dan yatsanta ya janyo
makunnar kwan lantarki batare da ta sani ba
nan dan dakin ya gauraye da haske.
Da farko Badawiyya bataga komai ba har sai
bayan dakiku uku lokacin da idanunta suka
saba da hasken sannan ta lura da dan sauran
abin da ya rage daga jikin masoyinta Nuri.
Dan tsurut acikin babbar rigar kafar a shanye
hannu a shanye kyakykyawar fuskar da ganinta
kan jefa Badawiyya cikin nishadi da farin ciki
duk ta yakune kamar matsatstsen lemon tsami,
hakoransa sun fito sarari gayau! Dasu babu
kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa dasu
babu kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa
kamar gonar kasusuwa, kan yayi kato tim
kamar dan tulu, idanun sun zazzaro waje
gwara-gwara kamar idon kwado. In banda
agogon dake daure a shanyayyen hannunsa
wanda ya nuna mata a daren jiya yace dashi
zaije wajen shagalin bikinsu, da har abada
Badawiyya bazata taba imani wannan
shanyayyiyar halitta mai kamar aljani a
matsayin Nuri dinta ba.
Da farko tsabar kaduwa da girgiza tasa
Badawiyya ta kasa motsi da zurawa mutum
mutumin Nuraddin idanu tayi can kuma sai ta
dora hannu aka ta kwala ihu.
"Wayyo Allah! Nuraddin na shiga uku"! Ta dada
kwala ihu.
Dakunan gidan da basu sami isassun kaya ba
suka amsa kuwar ihun kukan Badawiyya. Tun
kafin amsa kuwwar ta dusashe Badawiyya ta
fadi gefen Nuraddin sumammiya.
A can kuryar gidan daga bangaren gabas, wasu
motoci ne a jere marsandi fara, honda shudiya
da kuma dankwaleliyar jeep launin rawaya.
Wadannan motoci guda uku kyautace ta
musamman daga mahaifin Badawiyya. Tun ana
sauran kwana uku a daura auren yasa aka kawo
musu. Da yawa daga cikin bakin da aka gayyata
babu wanda zai iya kallon motocin ba tare da
ya sake kallonta ba, domin sababbine fii-fil
hakan ce tasa wasu daga ciki masu karancin
wayewa har hannu suke sawa su dan shafi jikin
motocin suji yadda suke kome suke ji a jikin
motar? Allah masa. Dayake tsakanin inda
motocin suke zuwa inda ake shagalin bikin da
'yar tazara, sa'ar da aka sami damar gyara
wutar sai duk baki suka bar inda motacin suke
suka nufi can cikin gidan. To amma fa banda
wasu samari biyu wadanda ke boye a bayan
motar suna shawagi, lokaci guda kuma suna
mahawara.
"kaga Yusuf, tunda dai kanada Aysha a hannu
kamata yayi ka barmin bakuwar nan". Saurayin
dake magana sunansa Abbati, dan gajerene baki
kakkaura, fuskarsa tana da kyawun gani, sai dai
kuma kansa yafi uban jikinsa girma, wannan
shiyasa da yawa daga cikin abokanansa suke
kiransa da Abba kwandal.
"zance banza kenan", yusuf yace dashi yana
harararsa. "Me kake nufi da inada Aysha a
hannu? Aysha da kullum saita gasamin aya a
hannu ita ce har kake kokari kafamin hujja da
ita? Kaga Abba kwandal nifa *bebe* din nan
babu mai rabani da ita sai Allah".
Abbati kwandal ya fashe da dariya. "yaufa ake
zukin mazallako wai da daga ciki yana rokon
uba kwabo. Yusuf meye kuma na wani fusata?
Babe din da ko sunanta ma bamu sani ba".
Yusuf ya girgiza kai yace. "kaine dai ba san
sunanta ba, amma ni na sani".
Abbatai kwandal ya dafa motar da suke boye a
bayanta da hunnunsa na hagun. "To menene
sunanta idan ka sani"?
Yusuf da wasa yake yiwa Abbati, domin shima
kamar sauran duk mazajen dake gurin yau ya
fara ganin kyakykyawar budurwar ballantanama
har yasan sunanta, dan haka sa'ar da Abbati ya
tambayeshi sunan sai ya daga kai sama kamar
wanda yake kokarin tuno sunan.
"sunana Amal". Wata sassanyar murya
busasshiya mai tayar da tsigar jiki, maral
alkibla tace dasu daga baya.
Samarin biyu suka juyo firgigit cikin mamaki-
mamaki tsoro-tsoro, domin basu taba jin irin
sautin muryar ba. Koda suka juya sai sukaga
wayam ba kowa abayansu.
Yusuf ya dubi Abbati, sannan Abbati ya dubi
yusuf a rude.
"ma...magana naji anyi a bayanmu ne? Yusuf ya
tambaya bakinsa na rawa.
Abbati ya gyada kai a tsorace. "Magana ce...
Magana ce akayi wallahi".
Samarin biyu sukayi mutuwar tsohuwa a gurin
jikinsu na bari kamar mazari, gashi dai inda
suke tsaye suna iya hangen samari da 'yan
matan a can wani bangare na gidan ta ciki
gilashi motar da suke tsaye a bayanta, amma
tsoro ya hana su motsawa daga gurin, ko
shakka basayi maganar mace sukaji gashi
basuga mai maganar ba.
Abba kwandal ya mirgina katon kansa mai
kamar masaki gefe guda kana ya karkata
kunnuwa yayi fakare kamar zakara yana
kokarin ya sake jin daga inda muryar ta fito.
Yusuf na nan tsaye kusa dashi bayan rigarsa ya
jike sharkaf da gumi, a zuciyarsa yanata zargin
kansa da wautar rabo kansu daga cikin jama'a.
Shi daman tun farkon shigowarsu gidan sai
daya ayyana a ransa cewa yanzu haka acike
yake da kwankwamai domin girmansa yayi
yawa.
"mu bar gurin nan". Abbati yace da yusuf cikin
rada yana magana da gefen baki. A daidai
wannan lokacinne fa suka ji daga can cikin
gidan an kwalla ihu da karfin gaske.
Time up.

ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {PART
31}
Dakta sulaiman yayi fakin da motarsa kirar honda
a farfajiyar asibitin, sai ya bude kofar motar cikin
gaggawa ya nufi cikin asibitin. Akwai alamun
farin ciki da nishadi karara a fuskarsa, wannan ce
matasa aranar da duk leburan da yayi masa
barka da zuwa sai ya juya ya jefe shi da
murmushi. Wani sa'in ma har tsayawa yakan
danyi ya danyi musu wasa da barkwanci kana
yaci gaba da tafiya.
Wannan sabuwar dabi'a da Dakta sulaiman ya
shigo da ita asibitin aranar ta baiwa kowa
mamaki, musamman ma kananan leburori
wadanda su dama Dakta sulaiman bai daukesu
komai ba, baya da dillalan kashi.
Dakta sulaiman Bafillatanine dan kimanin shekaru
talatin a duniya, dogo fari sosai, yanada fashin
goshi, amma bai fito sosai ba. Yana da farin jini
mai tarin yawa a gurin mata duk kuwa da cewa
sun tsani tsabar girman kansa. Dakta sulaiman
ma'abocin sa farin tabarau ne, tunda ya fara aiki
a asibitin, ba'a taba ganinsa ba tabarau ba. Wani
makaryacin ma ya rawaito cewa wai Dakta
sulaima da gilashin yake bacci. Da yawa yawan
mata abinda ke burgesu ga surar daktan shine
fararen kwayar idananunsa da kan fito
rangadadau ta cikin farin tabaran. Abinda basu
sani ba shine, duk kyawun idanun farinsu da
girmansu gululun banza ne domin baya gani sosai
sai da taimakon farin gilashin nan.
Wannan ya samo asali ne saboda tsabar karatu
da hana idanu barci gami da kallon farar takarda
acikin hasken rana zamanin da yake karatun aikin
likitansa a jami'a.
"Barka da zuwa wani yankunannan tsOho dake
faman goge tayil da tsumma yace dashi.
"yauwa baba tanimu, har yanzu baka tafi gidaba?
Karfe tara saura na dare fa".
Tsananin mamaki da kaduwa ya hana tsohon
kara cewa uffan, sai kawai ya bi dakta sulaiman
da kallo. Tunda tsohon yake aiki a asibitin sama
da shekaru ashirin da doriya baitaba ganin likita
mai tsabar girman kai kamar iblis irin sulaiman.
Ai a tunaninsa ya gaishe da Daktan sama da dari
uku amma bai taba amsa masa ba.
Duk wannan bata hana tsohon cigaba da gaishe
da litkitan ba, domin ko banza lokaci lokaci idan
Dakta Sulaiman ya bushi iska, yakan mika masa
naira dari zuwa dari biyu ba tare da yayi masa
magana ba.
Dakta sulaiman yaci gaba da tafiya cikin sauri
yana duban agogo tara saura kwata. Ai nayi sauri
ma. Yace cikin zuciyarsa kana ya yiwa kansa
murmushi.
Duk da yake dai ba dadin rai ne ya kawo shi
asibitin ba, amma cike yake da farin ciki. A cikin
shekaru uku da yayi yana kula da al'amuran lafiya
na iyalan Alhaji Danbaba kullum addu'arsa itace
Allah ya kawo dalilin dazai sa ya sami damar da
zai duba wannan kyakykyawar budurwa. Amma
bata taba ko ciwon kai ba ballantana ya sami
damar ganawa da ita, sai gashi yau a banza
sa'arsa ta haska, mahaifinta da kansa yayi masa
waya yace wai yayi sauri yaje asibitin ya duba
Badawiyya.
Sulaiman ya yi tsaye jikin farar kofar na 'yan
dakiku yana nazarinta, kana daga karshe sai ya
tura kofar a hankali ya shiga dakin zuciyarsa na
harbawa das! Das!
Dakin da dakta sulaiman ya shiga yana daya
daga cikin dakuna na musamman da aka tanada
a asibitin don kwantar da masu hannu da shuni.
Dakin bashi da girma sosai, gado daya ne jal a
cikinsa sai wata kujerar roca guda daya.
Lokacin da Dakta Sulaiman ya shiga cikin dakin
bai damu da yayi sallama ba, haka nan kuma bai
damu da ya kalli matan dake ciki dakin ba, domin
gaba dayan hankalinsa yana kan gadon da
Badawiyya take kwance. Dakta sulaiman ya
mayar da kofar ya rufe. Ya matso da a hankali
kusa da Badawiyya ya rankwafa hannayensa akan
bakin gadon ya kurawa Badawiyya idanu baya ko
kiftawa.
Kai wannan yarinya da kyawun sa dauke
numfashi take. Sulaiman yace a cikin zuciyarsa.
Tsahon lokaci yana rankwafe yana ta nazarin duk
wani bangare na jikin Badawiyya sai hadiyar
yawu yake kamar tsohon maye.
"Ta farka kuwa"? Sulaiman ya tambayi jerin
matan dake cikin dakin a karo na farko. Inda a
lokacin za'a tambayeshi bai san mata nawa ne a
cikin dakin ba.
A gaskiyar Al'amari mata biyar ne cikin dakin
akwai mahaifiyar Badawiyya, sai kakarta ta wajen
uba hakan nan kuma akwai kanwar babanta.
Sauran matan biyu dangin uwartane, wannan iya
wadanda ke ciki kenan amma farfajiyar asibitin
akwai 'yan uwa da abokan Arziki sama da guda
ashirin.
Sa'ar da Dakta sulaiman yayi tambayar bai sami
amsa da gaggawa ba domin matan babu abinda
suke yi sai sharbar kuka. Tsohuwar nan kakar
Badawiyya ita tayi karfin hali ta dago kai tace
dashi.
"Ta farka harma ta bude idanunta... Sai dai kuma
shi... Tsohuwar ta sake fashe wa da kuka sauran
matan suka rufe mata Baya...............................
Dafatan kunajin dadin labarin matasa maza da
mata???????
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABBN LABARI {PART
33}
"Kaine likita sulaiman"?
Yawun bakinsa ya kafe, dan haka sai kawai ya
gyada mata kai kamar kadangare.
'yar budurwar ta dada bude kofar sosai, sannan
ta matsa gefe guda. "zo muje na rakaka, yana
ciki yana jiranka".
"To nagode". Dakta sulaiman ya fadi a karo na
farko.
Budurwar ta wuce gaba tana rausaya kamar
dawisu, shiko dakta na binta a baya, a zuciyarsa
yana tasbihi ga sarki mai komai mahaliccin
kyawawa.
Budurwar ta tsaya dab da wata kofa launi kasa-
kasa mai sheki kana ta juyo ta dubeshi da
murmushi tace. "kana iya shiga.. Yana ciki kai
yake jira".
Dakta sulaiman yaji dadin murmushin dan haka
shima ya haskaketa da fararen hakoransa. "kefa
baza ki shiga ba"?
Budurwar ta girgiza kai. "maganarku ce kai
dashi".
Suka danyi shiru na 'yan dakiku suna tsaye suna
duban juna. Daktanne ya fara magana.
"kinso ki yimin kama da wata kawata A'isha da
mukayi jami'a tare.
Budurwar ta gyara tsayuwa tana murmushi tace.
"Allah ko"?
Sulaiman ya gyada kai.
"To, ni dai ba Aisha nake ba".
Sulaiman yaji zuciyarsa ta harba shin wannan
dama ce agare shi ta ya tambayi sunanta"?
"Me kike to"?
Budurwa tayi dariya har da tafa haNnu. "Au!
Kaima wato irin maganata kake kwaiKwayo ko?
To sunana Badawiyya". Ta danyi shiru kana sai
ta dada da cewa. "Ko kuma kana iya kirana ma
da Badawiyya Nuri".
Dakta sulaiman yaji kamar ta watsa masa wuta a
doron zuciya. Yayi sauri ya boye kishin dake
ruruwa a zuciyarsa ya dubeta cikin mamaki yace.
"Badawiyya Nuri"?
Ta gyada kai. "Kwarai kuwa shine mijin da zan
aura insha Allahu".
Tun daga wannan lokaci har zuwa yanzun nan da
Dakta sulaiman ke tsaye akan Badawiyya bai
daina Addu'ar Allah yasa wata dama ta sake
hadasu ba, saboda tun bayan wannan al'amarin
bai sake samun damar tsayawa da ita daidai na
minti guda ba, sai dai gaisu a tsaitsaye.
Dakta sulaiman yayi firgigit, tunaninsa ya katse a
daidai lokacin da yaji tsohuwar nan kakar
Badawiyya tana cewa.
"Badawiyya... Badawiyya bude idanunki".
Dakta sulaiman ya lura da cewa ashe Badawiyya
ta farka. "ku kyaleta sannu a hankali zata
wartsake". Yace dasu a sanyaye lokaci guda
kuma ya mike tsaye yana duban matan guda
biyar wadanda motsin Badawiyya du yasa sun
mike.
"kuyi hakuri ku dan jirani a waje zan dubata".
Cikin biyayya ba musu, matan suka nufi kofar
fita, kakar Badawiyya ce agaba sauran matan
biye da ita. Mahaifiyar Badawiyya itace ta
karshen fita sa'ar datazo fita saita dubi sulaiman
tace bakinta na rawa.
"Don Allah likita.... Ka dubamin ita da kyau...
Bana son ta mutu..." zuciyarta ta karye sai ta
fashe da kuka.
Dakta sulaiman ya matsa dab da ita, ya tausasa
murya gareta, wani abu da bai taba yiwa wani ba
yace. "kada ki damu kaduwace kawai ta sata
sumewa". A haka ya lallabata ta fice daga dakin.
Fitarta ke da wuya sai idanun Badawiyya suka
bude. Sulaiman ya kurawa kyakykyawar fuskar
idanu baya ko kiftawa. Tsawon lokaci suna nan a
haka. Ga shi dai idanunta wayam a bude, amma
basa kiftawa. Sulaiman ya fara tunanin tabbas
har yanzu tana cikin tsabar kaduwa ne. Ya matsa
kusa da gadon sannan ya daga dan yatsansa na
dama da niyyar taba gashin idanunta.
"Kada ka tabani ina ganinka". Rarraunar muryar
Badawiyya ta katse masa hanzari.
Hannunsa makale a sararin subhanahu, a wannan
karon shine cikin kaduwa.
"Badawiyya... Sannu yaya jikin naki"? Ya sami
kansa yana mai fadi.
Shiru bata amsa masa ba. Can kuma ba zato ba
tsammani sai ta mike zaune zumbur ta dafe kirji
tace ciki karaji.
"Na shiga uku! Ina Nuri... Nuri... Nuri"! Ta sake
kwalla kara.
Cikin gaggawa sulaiman yayi waje ya dagawa
wasu daga cikin matan da suka fita hannu, suka
shigo cikin gaggawa.
"ku rikemin ita". Likitan ya basu umarni.
"wayyo Nuraddin! Dan Allah ku kyaleni na nemo
shi wallahi kashe shizata yi bata da imani. Dan
Allah ku kyaleni wallahi bata isa ta rabani dashi
ba, wayyo"! Ihunta ya kashe sa'ar da taji tsinin
allura ya soketa. Ba'a kara minti guda ba barci
ya saceta.
Dakta sulaiman yaja baya ya tsaya yana haki
cikin kaduwa. Bawai ihu, ko abubuwan da
Badawiyya keyi bane ya sashi kaduwa ba,
wannan yasha jinsu a baya amma maganganun
datake yi su suka jefashi cikin tunani. Nuri? Mijin
da zata aura kenan, shin wacece ke son rabasu?
Dakta sulaiman ya tambayi kansa.
*** *** ***
wani katon zakara mai jar cera yabi wata 'yar
karamar kaza aguje suka fara tsere a tsakar
gidan. Kai! Amma dai anyi girman banza.
Nuraddin yace cikin zuciyarsa sa'ar da yabi kajin
da kallo sun nufi zauren gidan aguje.
Kallo, numfashi da cin abinci mai ruwa-ruwa
sune kadai abinda Nuraddin zai iyayi tun bayanda
masifar ta sameshi.
Sannu a hankali kusan watanni shida kenan da
faruwar al,amarin. Acikin watanni shidan nan
abubuwa da yawa sun faru wadanda mafi yawa
daga cikinsu na bakin ciki ne. Alal misali tun
sa'ar da aka kawo Nuraddin gida mahaifiyarsa
bata kara samun lafiya ba, yau cuta gobe cuta,
kullum ta dubi Nuraddin a kwance akan katifa a
tsakar gida nannade kamar igiya sai ta sashi
gaba tayi ta kuka.

ALJANI YA TAKA WUTA
CIGABAN LABARI {part34}
Dakyar da ban baki da
rokon Allah 'yan uwa
suka shawo kanta ta
fara cin abinci kadan- kadan. Abangaren abin
da ya shafi magani
kuwa ya zuwa yanzu an
sami bokaye kusan
talatin, malaman tsibbu
arba'in da sauran 'yan bani na iya sama da
goma sha uku amma
duk a banza. Duk wanda
yazo ya dubi Nuraddin
sai ya girgiza kai yace.
Wannan sai dai abinda Allah yayi. Duk wannan
dawainiyar kashe-
kashen kudi da ake ta
faman yi ba wani ke
yinta ba sai mahaifin
Badawiyya. Ganin kullum sai kashe kudi
akeyi a banza babu
alamun sauki shiyasa
mahaifin Nuraddin wata
rana yaje har gida ya
sami mahaifin Badawiyya yace dashi.
"ya kamata ka daina
kashe kudinka haka
nan, abinda kayi Allah
saka maka da alherinsa,
Allah yaga niyyarka kayi kayi iya yinka Allah
ne dai baiyi zai samu
sauki ba".
Alhaji Danbaba ya dubi
Dattijon mahaifin
Nuraddin ya girgiza kai cikin tausayi kana yace.
"A'a malama ina fa zai
yiyu a kyale yaro acikin
irin wannan hali babu
magani ai bashi yiyuwa".
Mahaifin Nuraddin ya danyi shiru na wani
lokaci kana sai ya dago
kai yace. "Abinda nake
son ka fahimta shine
wadannan bokaye babu
abinda zasu iya yiwa yaron nan, shiyasa nake
ganin kawai mu mika
komai ga Allah a sami
malamai suci gaba da yi
masa addu'a kullum".
Tun daga ranar sai suka ajje zancen bokaye a
gefe, Alhaji Danbaba ya
sami wasu amintattun
malamai wadanda duk
kwana ukun duniya sai
sun karantawa Nuraddin Al-qur'ani mai
girma su kuma yi masa
addu'ar Allah ya bashi
sauki.
Tunda Badawiyya ta
sami sauki sai ta tare a gidansu Nuraddin, anan
take kwana sai dai
akawo mata suturunta
da abincinta nan. Ita ke
taimakawa mahaifiyarsa
suyiwa Nuraddin dinta wanka, ita ke bashi
ruwan zuma ko madara,
da sauran dangin abinci
masu ruwa-ruwa. Haka
Badawiyya ta kasance
acikin wannan hali na tsawon lokaci, kullum
haka zatasa masoyinta
agaba tana cewa cikin
kuka.
Nuri darling nida kai
alkawari ne babu mai rabani da kai sai
mutuwa. Wani sa'in da
zarar ta fadi haka, saita
tallabo kwandalelen kan
Nuraddin ta dora akan
cinyarta tana kuka kuma tana cewa...
"sannu Nuri kaji... Kayi
hakuri Allah ne ya dora
mana, idan yaso yau ma
saiya yaye mana". Aikin
kenan ba dare ba rana. Wani sa'in idan
Mahaifiyar Nuraddin ta
jiyo Badawiyya tana
fadin irin maganganun
sai tayi sauri tabar guri
saboda tausayi, ta koma can cikin dakinta tayi ta
kuka a boye.
Wata rana a cikin
ranakun da suka biyo
baya, Badawiyya na
zaune tana durawa Nurin ta ruwan madara,
sai mahaifiyarsa tace da
ita cikin sanyin murya.
"Badawiyya ina ganin da
komawa kika yi gida da
kwana, kinga kwana anan bana irin naki
bane.. Makwancin bashi
da kyau kuma muddin
kina ganinsa a kullum
hankalinki bazai taba
kwanciya ba". Badawiyya ta sunkuyar
da kai gami da
murmushin yake lokaci
guda kuma ta fara yiwa
Nuri fifita. "Baba... Idan
na daina kwana ma anan ba daina tunaninsa
zanyi ba, gara dai ina
kusa dashi idan mutuwa
ma zaiyi gara mu mutu
tare".
"mema ya kawo zancen mutuwa, abinda nake so
dake shine ki koma
kwana a gidanku inya
so in ma zuwan zakiyi
kya ke zuwa da safe,
amma yanzu kullum kina nan, gashi babu
ranar warkewa ki
barwa Allah Badawiya
nasan yadda kike ji a
zuciyarki to amma sai
hakuri". Tun daga wannan rana
ne Badawiyya ta koma
gida da kwana, yau
wata hudu kenan daidai
amma duk da haka
kullum karfe takwas na safe take baro gida tazo
gurin Nurin ta bazata
koma gida ba sai goma
na dare.
Adaidai lokacin da
katon zakaran mai cara yabi kazar da gudu ne
Badawiyya ta shigo
zauren gidan
hannayenta dauke da
jakankunan leda guda
biyu wadanda ke cike da kayan shaye-shaye
iri-iri.
"salamu alaikum".
Badawiyya tai sallama.
Mahaifiyar Nuraddin
wacce ke shara a tsakar gida ta amsa sallamar
gami da mikewa tsaye.
"Badawiya har kin iso"?
Badawiyya ta gyada kai.
Sannan idanunta suka
nufi inda kuturturan Nuraddin yake.
"ina su Hajiya da Alhaji
ina fatan dai suna
lafiya"?
"Lafiyarsu kalau".
Badawiyya ta amsa, kana ta nufi inda Nuri
yake ahankali tana
nazarin yanayin jikinsa.
Akwai tsammanin dake
damun zuciyarta,
akullum idan tabar Nuri tunani take yi kamar
gobe idan ta dawo zata
same shi ya warware.
Amma sabanin
tunaninta duk sa'ar data
zo saita tarar dashi jiya ya yau.
Suturar dake jikin
Badawiyya ba wata ta
kuzo ku gani bace
doguwar riga ce baka
kafarta kuwa takallamine silifa, tun
ranar da Nuri ya
nannade ta daina
kwalliya.
Badawiyya ta matsa
dafda katitafar da yake kwance ta ajje
jakankunan ledar a gefe
guda, sannan ta fara yin
abubuwan data saba yi
masa na al'ada tun
tsawon watannin shida da suka shude.
"Nuraddin ina kwana".
Tace a tausashe tana
duban fuskarsa, tasan
bazai amsa mata ba
domin babu bakinsa an rufe, amma duk da haka
akwai alamun da take
ganin a fuskarsa ta
gamsu da cewa lallai ya
amsa gaisuwarta.
"ya jikin naka"? Idanuwansa suka motsa
wannan shi ya tabbatar
mata da cewa ya amsa.
Tun a mako na farko da
faruwar al'amarin
Badawiyya ta fahimci cewa duk abinda aka ce
da Nuraddin yana
fahimta mayarwa ne dai
bazai iya ba.
======ALJANI YA TAKA WUTA CI GABAN LABARI
{P.35}=======
Wannan tunani na Badawiyya gaskiya ne, domin
tun ranar da aljana Amal ta shanye shi, duk
abinda ake cewa yana ji, sai dai bashi da ikon
magana. Bakin cikin dake kunshe a zuciyar
Nuraddin yafi bakin cikin bayan tukunyar dahuwar
shayin bakin kasuwa. Yaya za'a ce kullum sai
Badawiyyarsa tayi masa magana amma shi baida
ikon maganar. In banda tunanin da sa ran
akullum zai iya warkewa, su sake ganawa sosai
da masoyiyarsa Badawiyya da tuni ya hadiyi
zuciya ya mutu.
Akwai lokuta da dama da Amal kan bayyana
gabansa tayi ta kyakyata masa dariyar mugunta.
Zuciyar Nuraddin takan tafasa ta kone saboda
bakin ciki. Badawiyya ta dada matsowa kusa da
Nuri ta tallafi kansa ta dorashi bisa cinyarta,
kana ta bude daya daga cikin jakankunan ledar da
tazo dasu ta dauko wata doguwar kwalba mai
dauke da tacacciyar madara sannan a hankali ta
bude ta fara baiwa Nuraddin a baki.
*Bani da kamarki Badawiyya, Allah ya bani sauki
na rama miki abinda kike yimin*. Nuraddin ne ke
fadin haka cikin zuciyarsa. Duk abinda Badawiyya
ke masa yana gani kuma yana ji.
Tsahon lokaci suna nan a wannan hali, Badawiyya
na bashi madarar shiko yana shan rabi, rabin na
kwararewa ta gefen Bakinsa.
"Bari inzo in gogge masa jikin". Mahaifiyarsa ce
ke cewa da Badawiyya hakan.
Badawiyxa ta girgiza kai cikin ladabi. "ki bari zan
goge masa".
Mahaifiyar Nuraddin tayi tsaye tana dubansu ta
tuna da cewa kwana daya kawai da daura
aurensu, masifar ta sameshi amma dubi yadda
take fama dashi kamar daman sunyi shekaru
masu yawa amatsayin ma'aurata. Hawaye ya
kwace mata. Cikin gaggawa ta juya ta nufi dakin
girke-girke domin bata son ta tashi hankalin
Badawiyya.
Wani yaro ya shigo tsakar gidan a guje, kaji da
tattabaru suka yi tsalle gefe guda. Kwakwazon
kajin shiyasa mahaifiyar Nuraddin dake dakin
girke-girke fitowa cikin sauri tana share hawaye
ta tari yaron.
"lafiya ka shigo a guje? Kufa bakwa rabuwa da
kiriniyar banza".
Yaron yaci gaba da tsalle-tsalle agabanta.
"wallahi wai...wai ana kiran Badawiyya..
Badawiyya taji abinda yaron yace cikin mamaki ta
dago kai ta dubi mahaifiyar Nuraddin .
"wai ke ake kira". Mahaifiyar Nuraddin tace tana
duban Badawiyya. Akwai alamun mamaki karara
a muryarta.
Badawiyya ta ajiye tsumman data gama goge
jikin Nuraddin, kana ta dada gyara masa
kwanciya ta dubi yaron. "wanene ke kirana"?
Kwakwalwarta ta fara tunanin gaggawa, a iya
saninta ko a gidansu babu wani mutum in ba
kawayenta ba da yake zuwa nemanta, sai gashi
yanzu wani na kiranta a waje. "ko kuwa dai
macece"? Ta kuma tambayar yaron.
"Wani ne... Wani mutum ne a mota yazo".
Sukayi jim na dan lokaci, mahaifiyar Nuraddin ce
ta fara magana.
"Ai sai kije ki gano, Allah sa dai lafiya".
Badawiyya ta mike a hankali, ta dubi Nuraddin
tace. "Ina zuwa Nuri yanzu zan dawo minti daya
kawai". Ta daga danyatsa akan fuskarsa kana ta
jefe shi da murmushin karfin hali idanun Nuraddin
suka kifta alamun ya fahinta.
Cikin gaggawa ta nufi kofar gidan don kawai
biyayya ga mahaifiyar Nuraddin bawai don taso
ba.
Badawiyya na fita tayi turus kamar ta fada cikin
fasassun tukwane.
A tsaye a jikin wata shudiyar marsandi sanye da
jaket da wando shudaye, kafarsa sanye cikin
takalmi baki mai walwalin dauke idanu. Idanunsa
boye a bayan farin tabarau, wani dogon saurayi
ne fari mai dan siririn fashin goshi.
Saurayin yayi mata murmushi yace "ki gafarceni
Badawiyya ina fatan kin ganeni"?
Badawiyya ta zura masa idanu kamar biri da
kararrawa tana kallonsa ko kiftawa batayi tsawon
lokaci bata dauke idanunta ba ita ko bace dashi
kala ba.
"Badawiyya ko baki ganeni bane"? Saurayin ya
kuma tambaya.
Badawiyya tayi firgigit kamar wacce ta nutse a
kogin tunani sannan saita sunkuyar dakai tace.
"Na ganeka mana ba kaine Dakta Sulaiman"?
Dakta Sulaiman ya laltbi kwibin aljihun rigarsa na
dama ya zaro wani rawayan kyalle na siliki
sannan ya fara goge fuskarsa. Tabbas gumi yake
yi. Akwai wani yanayi na ko in kula da lumbu-
lumbu dake kan fuskar Badawiyya, wannan shiya
sashi rauni, kana yaji gumi ya fara sartu akan
goshinsa. "Yaya gidan lafiya"? Ya sami kansa
yana fadi.
"lafiya Badawiyya ta amsa a takaice kana sai ta
dan juya masa baya tace.
"Sai kayi sauri ka fadi abinda kake son ka fada
domin minti daya na nemo izni.
Dakta Sulaiman yaji duk gwiwowinsa sunyi sanyi.
Ya dada share gumi yace muryarsa na rawa.
"maganganuna da nazo dasu suna da yawa
Badawiyya, domin sama da shekaru uku kenan
ina fatan Allah ya kawo mu wannan rana dazan
Amayar miki abinda ke boye a zuciyata".
Badawiyya ta juya a yatsine sannan ta gyara
tsayuwa tace. "Ina jinka amayar".
Dakta sulaiman ya gyara Tsayuwa ya jingina
bayansa jikin motar kana ya fara.
"Tun sa'ar dana fara dora idanuna akanki nake
kaunarki Badawiyya kuma nauyin mahaifinki da
nake ji su suka hanani na furta miki manufata
tun farko". Yayi shiru kana ya gyara farin tabaran
dak idanunsa yaci gaba.
Abdullahi Yusuf Maitama.
====ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI
{P.36}====
"Badawiyya ayau ciwon dake cikin zuciyata ya
tsananta, tun ina boyewa gashi har ya fito fili.
Badawiyya ina sonki sani cewa ayau bana ganin
komai sai ke haka banajin komai sai muryarki, sai
abinda kika yi dani".
Dakta sulaiman yayi shiru akwai alamun
taraddadi ta karaya karara akan fuskarsa domin
bai san irin amsar da zata fito daga bakinta ba.
"kagama"? Badawiyya ta tambayeshi a yatsine.
Jikinsa na rawa sulaiman ya dubeta kamar ya
fashe da kuka ya daga hannayensa biyu ya dora
akan cinyarsa yace. "Babu zance gamawa
Badawiyya sai da ace wannan shine mafi
mahimmancin abinda ke tafe dani".
Tsahon lokaci matasan biyu na tsaye suna duban
juna, akwai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment