Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gine
ginen alfarma iri-iri. Adai dai lokacin ne muka
kawo ga wata katuwar kofa tsayinta ya kusan
tokare. Sararin samaniya.
Amal ta dubeshi tace. "kada kaji tsoro, nan
gidanku ne babu abinda za'ayi maka".
Kofar garin tayi kara mai kamar rugugin aradu,
sannan sai ta bude a hankali wata shintimemiyar
halitta ta fito harshen halittar guda biyu ne
manya manyan kamar tabarma. Fitowarsa keda
wuya sai aljanin ya zuro harsunansa waje ya
shimfidasu gaban Nuraddin da Amal.
Nuraddin yayi baya cikin razana.
"kada kaji tsoro Nuraddin, hau daya harshen nima
na hau daya, akansa za'a kaimu zuwa fadar
mahaifina".
A dai dai lokacin ne to wata katuwar murya tayi
ihu mai tsanani sannan tace.
"Allah ya kiyaye wani dan Adam ya aureki bani
ba"!!
Kafin kiftawa da bisimillah sai wani farin hayaki
ya fara mamaye ko wanne sashe dake katuwar
kofar.
"Amal!!" Nuraddin ya kwala mata kira a gigice
domin baya iya ganinta saboda hayakin.
A dai-dai lokacin da duk wannan ke faruwa,
Badawiyya na can kwance male-male akan
gadonta tana barcin. Acikin barcin nata ne tayi
mafarkin wai suna cikin tafiya ita da Nuraddin
aciki wani kungurmin bakin daji, sai suka hango
wata mage ta nufosu da gudu tana zuwa
gabansu saita rikida da ta zama wata jibgegiyar
mata, mai zako-zakon hakora kamar kibiya,
jikinta duk gashi kamar na tunkiya. A lokacin ta
zaro tafka-tafkan hannayenta ta kama wuyan
Nuraddin zata yi sama dashi.
Badawiyya ta kwala ihu a rude sa'ar da taga abin
dake shirin faruwa.
A hakan hajiya habiba mahaifiyarta ta sameta ta
kankame matashin kai tana ihu.
"ke menene"?
Badawiyya ta yi firgigit ta tashi zaune, sukayi ido
biyu da mahaifiyar ta.
"momi, wallahi wani mummunan mafarki nake".
"kuma dan kina mafarki sai kiyi ta ihu, bazaki
ambaci sunan Allah ba? Duk abinda ya sameki na
masifa sai kice innalillahi wa inna'ilaihirraji'un".
Badawiyya ta sunkuyar da kanta tana tunanin
mummunar matar dake kokarin dauke mata
Nuraddin.
"kada na sake ganin kina ihu a mafarki, addu'a
akeyi ba ihu ba". Mahaifiyarta ta kuma fadi
sannan ta fice daga dakin ta koma dakinta. Karfe
uku na dare abin ya faru, to amma har gari ya
waye Badawiyya bata sake komawa baccin ba.
Washe gari da yamma misalin karfe shida
Badawiyya na zaune a dakinta. Sai tunani Nuri
'DARLING' dinta ya fado mata. Ta mike tsaye a
hankali ta fara suntiri a cikin. Oh! Nuri 'DARLING'
yanzu yana can makaranta ko me yake yi yanzu?
Ta tambayi kanta. Sannan ne to idanunta ya
kawo ga ZOBEN da Nuraddin ya bata.
Asannan nima lokaci yayi. Sai gobe da safe..

ALJANI YA TAKA WUTA!_14
'
'
Ko da Amal ta dubi idanunta saitaga kamanninta
sun fara sauyawa daga na firgita zuwa na wani
yanayi da ban.
"Badawiyya". Amal ta kira sunanta. "inaso ki
fahimci cewa koda ada can Nuraddin masoyinki
ne, to ki yarda cewa yanzu ya miki nisa, domin
na fiki sonsa, na kuma fiki daukaka, iko da karfin
mulki ballanta kuma uwa uba kyawu. Wannan
itace maganar data raboni da Nuraddin nazo
gareki na sanar dake cewa daga yau babu ke
babu shi"!
-
Badawiyya taji kamar Amal ta watsa mata wuta a
fuska. *NA RABU DA NURADDIN? Tab! Ai kuwa
sai dai mutuwa, kai ba 'yar gidan aljanu ba, ko
'yar gidan balbalin bala'i ce bata isa ba.
"kada ki bata bakinki"! Badawiyya tace cikin fushi
tana dubanta acikin madubin. "Bazan rabu da
Nuri ba, babu kuma wanda ya isa ya rabani dashi
sai Allah".
Ta danyi shiru tana duban Amal, wacce ke tsaye
acikin madubin cikin kaduwar ganin wacce keyi
mata magiya tana rokonta kuma yanzu ta birkice
take fada mata bakaken maganganu.
"kuma naji abin da kika fada 'yar gidan sarkin
aljanu, kince kin fini mulki, da iko da dukiya, da
kuma kyawu to duk naji na yarda, domin duk
Allah ne ke bada su ba mutum ba ko aljani.
Amma kin san dai cewa duk halittar ubangiji babu
wacce tafi mutum daraja, kuma kyawun da kike
takama dashi ai na karyane domin a siffarmu ta
'yan adam kika fito min, in gaskiyane ki koma
kirarku mana ta aljanu sai muyi takarar
kyawun...."
"Ke! Marar kunya kisan abinda yake fita daga
bakinki in kuma ba hakaba wallahi zakiyi
nadama". Amal tace a fusace.
"Rashin kunya ba gadonta akeyi ba Amal agurinki
na koya, wahala kuma ko nadama indai akan Nuri
Darling ne to hutuce agareni. Bazan barshi ba
kuma barin na maimaita miki babu abin da ya isa
rabani da Nuri sai ko mutuwa. Haba Amal tunfa
ina 'yar kankanuwa Allah ya dasa harsashin
kaunarsa a raina, ina girma itama kaunar na
girma cikin zuciyata, tare muka girma shine jini,
tsoka, kashi, bargo, ke shine rabin ruhin raina.
Shi bakiji sunansa ba ne Nuri? Ma'ana hasken
raina. Koma garinku Amal ki auri dan uwanki
aljani mai kan karfe, NURI kam nawane".
Amal 'yar sarkin aljanu tayi sororo cikin tsananin
takaici da kaduwa tana duban Badawiyya. Dakiku
ashirin suka shude Amal na tsaye ta kasa cewa
komai. Can sata nisa tace. "Nagode Badawiyya,
daman kunce jiki magayi to jikinki zai gaya miki,
kada ki tsorata domin bake zan taba ba, Nuri naki
zan nannade na mayar dashi kamar abinciku
alkaki, fitsari da kashi sai a kwance inyaso ki
aureshi haka ki nuna min kin fini kaunarsa ko"?
"Na daina tsoronki Amal kuma kada ki sake cewa
ina tsoronki, abinda ya dazuma nake baki hakuri
na dauka wani abune dabam ya kawoki, amma
indai zancen ki rabani da Nuri ne to bani ba
tsoronki har abada, nasan dai bai wuce kice zaki
nakasa shiba, ko ki kasheni, to bari kiji Amal indai
in rabu da Nurine, saidai kiyi duk abinda kikayi
niyya, domin rabuwa dashi sunfi mutuwa ko
nakasa zafi a gareni".
Badawiyya ta mike tsaye tana duban Amal, tawul
din wankan dake daure a jikinta rike a hannunta
na hagun.
"shikenan Badawiyya ma jiyi ma gani, a ga wanda
zai gaza". Amal tace. Sannan tayi shiru tana
duban zobenta da ta bawa Nuraddin a hannun
Badawiyya cikin takaici. Amal taji zuciyarta kamar
ta fashe da kuka. Mahaifinta yasha bata tarihin
zobunan guda uku, biyun da suke hannunta da
kuma wanda ke hannun Badawiyya a yanzu.
Mahaifinta yasha cewa da ita.
"Wannan zoben yafi shekara dubu biyar a gurina
tun zamani annabi sulaiman {A.S} yake, zoben
alkawarine, dan haka ki rikeshi da kyau kuma
kada ki sake ki cutar da duk bil'adaman dake
sanye da daya daga cikin zobunan guda uku, idan
kuwa kika aitata sabanin haka, to ki kuka da
kanki domin nannadewa zakiyi ki zama gurguwa
baiwa wulakantacciya a cikin jinsin aljanu, kiyi ta
yawo a kwararo da lungu-lungun duniya cikin
kazanta".
Tunanin wannan dogon jawabi na mahaifinta, da
kuma fargabar abinda zai biyo baya, shiya hana
Amal ta nannadewa Badawiyya kafafu da hannu.
Kai in ba don zoben dake hannunta ba, da saita
kakkaryata ta shanye bargonta.
"sai gani na biyu Badawiyya huduwar da ina
tabbatar miki da cewa bazata zamo alkhairi
agareki ba, kuma aure ni da Nuraddin kamar anyi
ne, kinga yanzu haka ma muna tare dashi a kofar
gidanmu zamu shiga su gaisa da mahaifina sai
kawai naji kinyi kirana".
Badawiyya ta dubi Amal cikin rashin fahimta tace.
"kamar yaya nayi kiranki, kufa Aljanu bakwa
rabuwa da karya da yawan son wasa, yanzu ke
ko kunyar fada bakya yi wai kuna tare dashi? To
Allah yasaa ma baya garinnan, yana makaranta.
Kuma da zaki ce nayi kiranki yaushe na kiraki"?
Amal ta dubi zoben dake hannun Badawiyya ta
girgiza kai. Zakisan yadda akayi kikayi kirana,
amma sai nan gaba, kuma sai kinyi nadama
marar kunya.

ALJANI YA TAKA WUTA!__15
-
-
-
...Wani bakin hayaki ya turnuke dakin sannan
lokaci guda sai ya washe.
Badawiyya taja da baya cikin kaduwa, sa'ar da
bakin hayakin ya washe, sai ta sake duban
madubin. Babu alamar kyakykyawar surar Amal
sama ko kasa ta bace.
Adaidai lokacinne kofar dakin ta bude, "keda wa
naji kina magana yanzunnan"?
Badawiyya ta nufi mahaifiyarta da gudu ta
rungumeta sannan ta fashe da kuka wiwi.
****
"Amal! Nuraddin ya sake kwalawa Amal kira karo
na biyu daidai lokacin da farin hayakin yaci gaba
da tunuke gurin.
Tuni Nuraddin ya fara zargin kansa da wautar da
yayi, wai soyayya da aljana, kuma dan karin
sabon haukama wai har ya amince ya biyota
garinsu, togashi nan yanzu ta kawo shi gaban
mai dogo harshe mai muryar jaki suna kokarin
hallaka shi.
Nuraddin yaji kamar akan iska yake ninkaya
domin kafafunsa basa taba kasa, amma duk ba
wannan bace tafi bashi tsoroba, sai muryar nan
da yaji mai amon kukan jaki tana cewa dashi
wai ya rabu da Amal ba mai aurenta sai ni.
Yanzu inba dan rigima ma irin tawa ba ina ni ina
takarar budurwar aljanu, kuma aljanun ma masu
muryar jaki? Nuraddin ya tambayi fuskars.
Adai dai lokacinne ba zato ba tsammani sai farin
hayakin ya washe tamkar ma ba'ayi shiba
Nuraddin ya dubi inda yake fuskanta cikin
mamaki domin har yanzu dai yana nan tsaye
gindin katangar nan, hakannan kuma dankareren
aljanin nan mai dogon harshe na tsaye yana zalo-
zalo da harshensa kamar tabarma.
"Kada kaji tsoro". Wata muryar tace da Nuraddin
wacce daga baya ya fihimci ashe muryar aljanin
nance mai dogon harshe. "kai bakonmu ne,
bazamu cutar dakaiba. Muryar daka ji tana yi
maka tsawa ta wani shaidanin
dan sarkin ce daga cikin kananan sarakunan
aljanu. Ya dade yana son ya auri Amal amma taki
amince masa, bata kaunarsa koda kwayar zarra.
Ya cika nacin tsiya, munsha yi masa kashedin ya
rabu da ita kuma kada ya sake
zuwa gidan nan amma yaki, to yau munyi
maganinsa, domin a yanzu haka yana can cikin
karkashin kasa mun daure shi, saboda tsawar
da yayi maka a matsayinka na babban bakon
sarkinmu. Don haka a madadin sauran aljanu
ni babban maigadin gidan sarkin aljanu inayi
maka barka da zuwa mijin gimbiya".
Koda aljanin ya gama dogon jawabinsa, sai
Nuraddin ya bude baki da niyyar ya tambayeshi
inda Amal ta tafi ta barshi. Kafin ya tambayane
to Amal ta sake bayyana a gabansa cikin sauri
kamar an jehota daga sama.
"kayi hakuri Nuraddin," Amal tace "Wallahi
kiran gaggawa akayi min shine na tafi, amma
daman nasan babu abinda zai sameka, shiyasa
na bar maigadinmu ya kula da kai kada
nacaccen nan ya tabamin kai".
"Ina kika je"?
Amal ta dubi Nuraddin sannan ta sunkuyar
dakai Bazata iya fada masa cewa daga wurin
Badawiyya take ba ballantaoa kuma azo ga
zancen alkawarin da tayiwa Badawiyya na
nannade shi. Don haka ba tare da ta iya hada
idanu dashi ba tace.
"Al'adar gidanmu ce duk lokacin dakazo da
bako mai mahimmanci kamarka, sai anyi
kiranka kayi bayanin cewa kun karaso, sannan
sai a shigo da bakon.
Nuraddin ya dubeta cikin rashin gamsuwa, ko
shakka babu yasan karya take.
Amal ta sake matsowa kusa dashi taci gaba da
cewa ina fatan ka gamsu"?
Nuraddin ya gyada kai baiyi magana ba.
"To ai sai mu tafi ko"? Tace dashi.
Kafin kiftawa da bismillah, katon aljanin nan
maigadi ya shimfida dogon harshensa mai
kamar tabarma. Suka hau sannan yayi sama
dasu ya tsallake katangar gidan. Har sa'ar da
aka ajiye Nuraddi agaban sarkin aljanu bai
daina zargin kansa da wauta ba, haka nan yayi
wa kansa alkawarin inhar ta mayar dashi
makaranta bazai sake binta ko ina ba. A wani
bangaren na zuciyarsa ma saida ya fara tunanin
anya kuwa zai iya ci gaba da soyayya da ita?
Nuraddin ya dago kansa a hankali cikin
fargaba, yana kallon aljanun da sukayi sahu-
sahu a fadar sarkin aljanu. Tun da yake, bai
taba ganin halitta mai ban tsoro da muni irin
tasu ba. Fadar cike take makil da jinsin aljanu
iri-iri, kuma tun daga kan bakake da fararen
aljanu zuwa kan masu faka fakan kunnuwa
kamar faranti, kai wasu babu kunnuwan gaba
daya, haka wasu zako-zakon hakora da manyan
kunnuwa, wasu kuma manyan kawuna kamar
goran kamun kifi, wasu kuwa 'yan kawunansu
gwanin ban dariya, domin 'yan kananane kamar
dunkulen fura, sai katon uban jiki kamar
giwaye. Nuraddin ya dubi surukinsa sarkin
sarakuna
mai mulkin Aljanu wato mahaifin Amal, sai
yaga kansa kamar an taka gwanda da tayar
mota, kunnensa daya ido daya haka nan
hancinsa dogone kamar karas.
"ka rike alkawari Nuraddin," sarkin Aljanu ya
fara jawabi, yayin da sauran aljanu sukayi tsit
suna da faman fifita da faka-fakan
kunnuwansu. "Muna farin ciki dakai, kuma in
dai zaka rike alkawari, to zan baka 'yata Amal
ka aura domin tace duk duniya babu wanda
take kauna sai kai, bisa wannan dalili dole ne
nin na kaunace ka, domin duk abin da take
kauna nima ina kaunarsa. Yaya kake gani, zaka
iya rike alkawari zaka kuma aureta??

Aljani YaTaka Wuta!....16
-
-
...abin da take kauna nima ina kaunarsa. Yaya
kake gani, zaka
iya rike alkawari zaka kuma aureta??
"Kuyi hakuri ansamu typin errors a wannan page
na littafin "
-
Tun fara hangenta daga nesa Nuraddin ya fadawa
kansa cewa lallai ba lafiya ba, domin fuskarta
murtuk! Take a hade, kuma abinda ya kara sashi
kaduwa ma shine harya kusa isa gurinta
Badawiyya bata saki fuskarta ba ballantama tayi
masa murmushin nan na alkawari data saba yi
masa maimakon haka ma sai harara.
Nuraddin ya matsa kusa da Badawiyya a hankali
wacce hannunta ke dafe da saman motar kirar
Toyota da aka kawota a ciki, fuskarta na duban
kasa, akwai wani yanayi dake kan fuskarta wanda
yasa 'yar autar hantar cikin Nuri kadawa.
"sannu da zuwa". Nuraddin yace da ita sa'ar da
ya dada matsawa kusa da ita.
"sannunka dai". Badawiyya ta fada a yatsine. Tayi
shiru bata sake cewa kala ba.
"Badawiyya meke faruwane ina fatan dai lafiya"?
Nuri ya tambayeta cikin damuwa.
"Lafiyar kenan". Badawiyya tace sannan tayi
ajiyar zuciya ta sunkuyar da kanta kasa tana
duban inuwarta ajin mota.
Nuraddin ya sake dubanta cikin tsananin damuwa
sannan ya dan dauke kansa gefe guda ya dubi
can cikin farfajiyar makarantar inda dalibai ke ta
harkokin gabansu.
"Badawiyya kada ki boyemin komai in wani abune
ki sanar dani mana kin barni cikin zulumi da
damuwa, ni kuma nasan ba wani abu na miki ba
tunda shekaran jiya-jiyan nan fa kika zo da farin
ciki da sanyi rai muka rabu dake amma gashi
yanzu kinzo ranki a hade ni...ni dai na kasa gane
wannan abu"?
"nace dakai babu komai, in kuma zuwa gurin
naka danayi baka so to sai nayi tafiya".
Badawiyya tace fuskarta a murtuke.
Cikin damuwa, Nuraddin ya lalubi aljihunsa ya
zaro kyalle daga goshinsa.
"kada kiyi min haka Badawiyya, alkawarin dake
tsakanina dake baice haka ba, ki tuna fa tun
muna yara muke son juna, wani sabani
makamancin wannan bai taba shiga tsakaninmu
ba, in kuwa hakane mezai sa yanzu ki rufe idonki
a kaina"? Ya danyi shiru yana mayar da numfashi.
"idan kuma laifi nayi miki batare dana sani ba ki
fada mana saina baki hakuri tunda dai Allah ya
halicci kaunarki cikin zuciyata".
Jin haka shiya sa Badawiyya ajiyar zuciya sannan
ta dago kai ta dubeshi da dara-daran idanunta
tace. "Nuri meye hadinka da aljana"? Numfashin
Nuraddin ya dauke. Daman ni nasa a rina wai an
saci zanin mahaukaciya. Ya fada cikin ransa.
"Ban fahimce ki ba". Ya fada a fili. Lokaci guda
kuma ya fara kokarin sa alamun rashin
fahimtarta akan fuskarsa duk kuwa da cewa
zuciyarsa ta dade da zargin abinda ya faru.
"Nace inda alkawarin kamar yadda ka gama fada
meye hadinka da aljana? Badawiyya ta sake
maimaitawa.
Wani sassanyan gumi ya fara sartu wuyansa ya
gangaro har zuwa ramin tsakar bayansa.
"Badawiyya waye inba mahaukaci ba zaiyi
soyayya da aljana," Nuraddin yace cikin karfin hali
yana girgiza kai. "Gaskiya nin Badawiyya duk kin
rudani...ni yau na kasa fahimtar inda kika sa
gaba".
Badawiyya ta dube shi tana kokarin karantar
fuskarsa sannan tace. Mu shiga daga cikin motar
in fahimtar dakai, labarin nada yawa". Tana fadin
haka sai ta bude gidan baya na motar ta zauna.
Nuraddi jiki ba kwari, ya shiga ya zauna a kusa
da ita yanata sakar zuci.
Badawiyya tadanyi shiru na lokaci tana hangen
direban daya kawota wanda ke can gefe guda
kusa da wata tsohuwar rijiya da dalibai kan dauki
ruwa idan ana wahalar ruwa a makarantar.
"Nuri" ta kira sunan a sanyaye, sannan taci gaba
da cewa. "wata aljana ce ta bayyana kanta
agareni tace duk duniyar nan ba wanda take so
ta aura sai kai".
Kusan tsawon mintuna arba'in kenan Nuraddin na
zaune yana sauraron abin al'ajabi daga bakin
masoyiyarsa Badawiyya. Ko shakka baya yi duk
abinda tace sunyi da Amal 'yar sarkin aljanu
gaskiya ne, domin ganau ne ba jiyau ba.
A daidai lokacin da Nuraddin ya fara jin kamar
kansa zai rabe gida biyu saboda firgicin labarin,
sai Badawiyya tayi ajiyar zuciya, ta kare zancenta
da cewa.
" shin to kai Nuri, a ina kuka hadu da ita?
Nuraddin yayi murmushin yake yace. "Nima
tambayar dana kewa kaina".
Badawiyya ta dubeshi cikin rashin fahimta "kamar
yaya kenan kake nufi"? Ta sake tambayarsa karo
na biyu.
"saboda ni ban san wata aljana wai ita Amal ba
ballantana ma harna iya soyayya da ita".
Nuraddin yace batareda ya iya hada idanu da
itaba.
Badawiyya ta dubeshi a rude amma babu alamar
zargi a fuskarta, hakan ya karwa Nuraddin karfin
gwiwar lallai zai iya jirkitar da zanceta, ya mayar
mata da duk abinda sukayi jiya itada Amal ya
zam kamar mafarki.
"To.... Kana nufin kace duk surutun da mukayi da
ita a daren jiya ba gaskiya bane"?
Nuraddin yayi ajiyar zuciya, sannan ya dubeta da
murmushi yace. "wallahi yau kin sani cikin
damuwa a banza, ni da na dauka ma wani laifi
nayi miki? Yanzu keda wannan dan abin duk
shiya rikitaki haka"? Nuraddin ya danyi shiru gami
da dubanta ido da ido.
"Bari na fada miki wani abu da baki sani ba,
aljanu ne kawai suke son wasa da hankalinki
saboda ganin irin tsabar kaunar da muke wa
junanmu.


-
Nuraddin ya kara cewa, kinga nima kaina a 'yan
kwanakinnan haka nake ta fama da 'yan
mafarke mafarken ban tsoro, fada mikine kawai
bana yi dan kada hankalinki ya tashi, amma ni
basu taba zuwa min a zahiri ba, kema dan
macece, shiyasa amma kada ki damu, ki
kwantar da hankalinki in kinje gida kisa a miki
rokon Allah kada suci gaba da zuwa miki a
zahiri".
Badawiyya ta dube shi gami da ajiyar zuciya
tace "Nuri darlin wallahi ni har na gama tsora
na dauka da gaske soyayya ka fara da aljana.
Nuraddin ya girgiza kai da dan murmushi.
"karya ce kawai da iya shegen aljanu kin sansu
da son wasa kamar daren sallah. Allah ne kawai
zai iya rabani da ke Badawiyyata".
Acan gefe guda, kimanin taku ashirin Daga inda
suke zaune, Amal ce 'yar sarkin aljanu ita da
fadawanta tana kallon duk abin dake faruwa
tsakanin masoyan biyu.
"shegiya nacacciya kya yi kya barshi saina
munana fuskarki"! Amal ta ce ciki zuciyarta a
fusace.
Saura kwanaki uku kacal su Nuraddin su fara
jarabawarsu ta karshe, wato ta kammala
karatun su a makarantar.
Karfe hudu da 'yan mintuna na yammacin
ranar ne Nuraddin ya shiga makarantar dauke
da farar leda ahamnunsa. Daga cikin gari yake
jakar dake hannusa kayan marmari ne da ire-
iren nau'in abincin gwangwani wanda a yanzu
sun abin shansa da cinsa. Wannan ba abin
mamaki bane domin duk sa'ar da yaso ya kashe
kudi hannunsa kawai zai tura cikin aljihunsa sai
yaji dumus, ya zaro iya adadin da yake bukata
ya kashe abinsa.
Yau kusan kwana arbain kenan rabonsa da
Badawiyya Amal kuwa tun sa'ar da ta dawo da
shi daga garinsu bai kara ganinta ba ido biyu
ba, amma takan zo masa a mafarki cikin dare
suyi hira abinsu. A ire- iren hirarrakin da suke
yine ma a daren jiya tace dashi yayi jiranta yau
zata zo gurinsa da yamma domin su tattauna
akan maganar fara jarabawar sannan kuma tace
da shi da zarar ya kammala karatu zata kawo
masa kudin da zai sai motar hawa shima ya
samin abin yawo a gari.
Wannan ita tasa Nuraddin shigowa makarantar
cikin sauri har yana sassarfa. Amma fa duk
wannan hira da ake sha tsakaninsa da Amal
'yar sarkin aljanu, har yanzu hankalin Nuraddin
a tashe yake zuciyarsa ta kasa tsayawa guri
guda.
A gaskia so kam ya fi kaunar gimbiyarsa ta
ainihi wato Badawiyya. Tasha wahala akansa
kuma a kullum idan ya kwanta barci yakan ce
da kansa da Badawiyya ce keda arzikin Amal, to
da ko raine tana iya saya masa idan tana da
iko, Amma Amal fa? Cewa tayi tana kaunarsa
saboda shi jarumi ne. Gaskiya ba kwanta min
ba soyayyarta bata da inganci. Yace da kansa.
Aljanun nan basu da tabbas, yanzu idan wata
rana ya aureta ta kuskure ta sauya kamanni irin
na mahaifinta mummuna mai dogon hanci
kamar karas yaya zaiyi? Tab!! Falcao! Kenan
yace a ransa sa'ar da ya tuna wani aljani da ya
gani mai manyan kunnuwa kamar takalmi.
Tambaya daya da Nuraddi yake wa kansa ita ce.
Idan Amal bata kwanta masa a rai ba meyasa
ya dau alkawarin aurenta? Arzikin da tace zata
baka. Wata zuciyar ta bashi amsar tambayarra.
Tabbas yana bukatar kudi. Wani babban sirri
dake boye a zuciyar Nuraddin shine, tun
farkon fara haduwarsu da Amal Nuraddin ya
amince mata ne duk saboda Badawiyya. Ya sha
fada ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba
cewa, wahalar da Badawiyya keyi masa ta isa
haka, domin abin yayi yawa, tun suna firamare
take wahala dashi, sau da yawa ma ita ke zuwa
musu da abincin ma da suke ci idan sun fito
tara, hakanan kuma ita ke bashi kudin kashewa.
A lokacin Nuraddin ma kazami ne bai fiye son
wanka ba, ansha fito dashi filin taron dalibai
ayi masa bulala a matsayin dalibin da yafi
kowa rashin tsafta. Amma duk wannan bata sa
daidai da kwayar zarra Badawiyya ta kyamace
shi ba. Wasu lokutan ma idan aka dake shi ya
fara kuka, ita takan zo tayi ta lallashinsa har
sai ya huce. A haka har suka zo sakandire, nan
ma taci gaba da wahala akansa, kudin
makaranta, na kashewarsa, littafansa da kayan
amfaninsa na yau da kullum. To irin wannan
dawainiya ita tasa tun nuraddin baya damuwa
har abin ya fara damunsa, ya fara tunanin a
duniya fa babu zaman wacce yake inba
Badawiyya ba, kullum burinsa a duniya shine
Allah ya azurta shi ya nunawa Badawiyya cewa
tofa shima dane. Don haka haduwarsu da Amal
keda wuya sai yaga cewa damarsa tazo na ya
saka mata na sama da abinda ta masa. Abinka
da takadiri irin Nuraddi, ko kusa ko alama
zuciyarsa bata taba tsoratar dashi irin hadarin
da yake kokarin jefa kansa aciki ba. Tunaninsa
kawai Badawiyya, tuni ya fara tunanin idan
Amal tazo bashi kudin sayan motar da tayi
masa alkawari zaiyi kokarin ya karbin kudin
mota biyu datasa da ta Badawiyya.
Wadannan tunane-tunane suke ta kai kawo
cikin zuciyar Nuraddin har sa'ar da ya kawo
cikin makarantar.
Lokacin da ya karasa bangarensu na Seniors
{manyan dalibai} gurin babu ko dalibi daya duk
sun tafi daukar karatu, saboda kusantowar
jarabawar da zazu fara nan da kwana uku, da
yawa daga cikinsu basa dawowa dakin sai waje
asuba Nuraddin ya nufi dakinsu cikin sauri sai
yayi
turus da....-

Aljani Ya taka wuta!....18
-
-
-
Nuraddin ya fara tafiya a
hankali baki bude cikin
mamaki. A iya sanin Nuraddin daliban da
suke cikin dakin basu
taba tafiya sun barshi a
bude ba, haka basa
barin wutar lantarki a
kunne tun bayan wata gobara da aka yi suna
aji daya, amma yanzu da
Nuraddin yaci gaba da
nufo dakin sai yaga
dakin a bude, haske ko
ina duk kuwa da cewa har yanzu da sauraran
hasken ran, kuma abin
mamaki hasken har
waje kamar kwaya-
kwayan wutar lantarki
dake dakin sunkai dari. Gaban Nuraddin na
faduwa amma ba wai
don tsoro ba sai don
mamakin da kuma
dokin ya shiga yaga
abin dake faruwa. A haka Nuraddin ya shiga
dakin.
Shigarsa keda wuya sai
sukayi ido biyu da ita
zaune akan gadonsa
tana haskake masa idanu da fararen
idaninta.
"Sannu da zuwa". Amal
tace dashi cikin
annushuwa.
"Haba ni fa nasan wani aikin sai ke". Nuraddin
yace shima cikin
murmushi, lokaci guda
kuma yana kallon
sauran zobunan guda
biyu da suka rage a 'yan yatsunta.
Nuraddin ya karasa
cikin dakin yana fara'a
ya zauna kusa da ita.
Duk kamshinki ya
mamaye mana daki" Nuraddi yace yana
dubanta.
"Naji dadin hakan".
Amal tace cikin fara'a da
jin dadi, duk mai hankali
idan ya dubi irin kallon da take yi masa zai san
cewa lallai tarko nan mai
magani daya ya mamayi
zuciyarta ya cafketa
wato S0!.
"Na bata miki lokaci ko? Cikin gari wallahi naje
siyan 'yan kayayyaki,
dan ma nayi sauri da
bazan karaso yanzu ba".
"Haba Nuraddin ba
komai wallahi, nima dai azarbabina ne ya kowo
tun wuri, kuma gashi
DUNDUMA baya kusa na
aike shi karas SIN
ballantana ma ya sanar
dani inda ka tafi, naso ma na biyo ta cikin gari
na daukoka muzo tare".
Nuraddin ya dubeta
cikin rashin fahimta yace
"wanene kuma
DUNDUMA"? "Bawa na mai kula
dakai".
Nuraddin ya dubeta
kirjinsa na bugawa cikin
fargaba. Ashe 'yar masu
dogon hancin nan han dan leken asiri ta
makalkalamin. Nuraddin
ya fada a ransa. Wani
sansanyan gumi ya fara
kwararowa a tsajiyar
gadon bayansa. Yanzu da magulmacin ya dauki
duk maganganun da
sukayi da Badawiyya ya
fada mata yaya kenan?
Maganar Amal ta katse
tunaninsa. "Tunanin me kake yine? Dan kaji nace
DUNDUMA? Ai tsaron
lafiyarka yakeyi, yaushe
zan bari tsautsayi ya
samar min kai Nuraddin?
Ai bazai yiyu ba, kai dai na san abin da kake
tunani, to ba leken
asirinka yake yiba".
Nuraddim yai ajiyar
zuciya gami da
murmushin yake kana ya dubeta yace "ke
kuwa kin cika zargi, to
ni tunanin da nake ma
bai shafi wannan ba".
"to Me kake tunani?
Nuraddin ya jefeta da tattausan murmushin
yaudara. "Ranar
aurenmu nake tunani".
Amal ta washe baki
cikin farin ciki, sannan ta
dan matso kusa dashi. "wallahi nima kullum
tunanina kenan.
Nuraddin yaushe zaku
fara jarabawar ne nina
matsu ku fara ko kwa
gama a fara zancen aurenmu".
"Ai ranar litinin dinnan
mai zuwa zamu fara. Yau
saura kwana uku".
Amal ta dubeshi tace
"kada ka damu kanka, saurara da kyau, idan
ranar litinin tazo zan
shigo cikin ajin daza
kuyi jarabawar, zan
buda maka tafin
hannua, zakaga duk amsoshin a jiki".
Nuraddi bai gaskata,
kunnuwansa ba ya
dubeta cikin kaduwa.
"kada ka damu, duk ajin
babu wanda ya isa ya ganni sai masoyina".
Ranar litinin, rana ta
faduwar gaba ga kusan
dukkan daliban da zasu
fara zan jarabawarsu ta
karshe a makarantar. Wasu daga cikinsu suna
fargabar ranar ne
saboda basu yarda da
kansu ba, domin sun
tabbata dan abinda suka
karanta bai isa sukai labari ba. Yayin da wasu
kuma suke fargaba
kawai saboda basu taba
zaman jarabawa ma
mahimmanci wannan ba
a rayuwarsu. Haka kuma basu san
wadanne irin tambayoyi
za'a kawo ba a wannan
shekarar.
Koma dai menene shi
Nuraddin ko a jikinsa wai an mintsini
kakkausa. Tun karfe
tara saura na safiyar
ranar suka fara
jarabawar. Basu dade da
shiga ba malaman suka shi rarraba musu
takardun jarabawa tare
da bakaken 'yan sanda
guda hudu dake binsu a
baya suna muzurai
kamar zasu hidiye mutum danye da ransa.
"kai gyara zamanka"!
Wani daga cikinsu ya
bugawa Nuraddin tsawa
sa'ar kafar Nuraddin ta
hagu ke kan teburin rubutunsa.
Sai da akayi kusan
mintuna arba'in da fara
jarabawar Nuraddi bai
zana alif ba. Yana zaune
yana tsammanin warabbuka wai malam
yaki yin Noma don
zakka. Adai dai lokacin
Nuraddin ya fara
zazzare idanu yana
tunanin ko bazata zoba, sai kawai ya kamar
daga sama yaji ance.
"Kada ka damu
masoyina, ina nan kusa
da kai. Da yardar Allah
yanzu zaka gama". Sannan sai Amal ta
bayyana kusa dashi
tana murmushi.
Nuraddin ya daga kansa
ya dubi sauran daliban
da kuma malaman dake tsaronsu, ko kusa ko
alama babu wanda
hankalinsa ya kawo
gareshi, ballantana ma
su nuna alamar sunji
abinda tace. "Dubi tafin hannuna,"
Amal tace dashi a
tausashe, lokaci guda ta
daga tafin hannunta
sama, kamar wasa sai ga
rubutu a jiki "fara kwafa wannan ce amsar
tambayarka ta farko".
Nuraddin jiki na rawa ya
fara kallon tafin
hannunta yana rubuta
abinda ya gani ba magana don gudun
kada a jishi a cikin aji.
"Idan kaso muna iya yin
hirar mu ma kana
aikinka. Domin babu mai
jinmu ballanta ganina.

Aljani

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment