Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamun damuwa karara a fuskarsa,
meyiyuwa su basu lura da hakan ba domin
kawunansu a sunkuye suke.
"Biyo ni mu shiga ciki in nuna maka wani abu".
Dakta sulaiman ya dubeta cikin mamaki, daidai
lokacinne wani katon kuda kore ya yiyo hijira
daga kan bawon ayabar da yara suka jefar ya
nufo kunnen Dakta sulaiman yanayi masa Bu!
Bu!! Dakta sulaiman yakai duka ya mari fuskarsa
a banza.
"Banjiki sosai ba kina nufin mu shiga ciki"?
Dan abu zan nuna maka yanzun nan zamu fito ko
minti daya ba zamu yiba". Tana gama fadin haka
saita juya ta fara tafiya ta nufi zauren gidan.
Sulaiman yayi kamar kada ya shiga gidan domin
baisan abinda take nufi ba gashi kuma uwa uba
babu alamun dake karfafa masa gwiwa. To amma
sa'ar da yaga gadan-gadan shigewa zatayi, sai
sulaiman ya bita a baya cikin sauri har da
sassarfa, kadan ya rage ya taka wuyan wata
farar kaza. Badawiyya ta rage sauri sa'ar dataga
yana biye da ita. Tana tafiya tana tunani. Acan
wani bangare na zuciyarta gani take yi abinda
tayi daidai ne domin ahalin da ake ciki a yanzu
itace hanya mafi sauki da zata kirkira domin ta
rabu da wannan sabuwar masifar da ta kunno
mata kai. Ta sani cewa duk tsayin lokacin nan
zuru kawai akayi mata saboda tausayin halinda
take ciki, amma da tuni an fara tunanin araba
aurenta da Nuri tunda dai babu ranar
warkewarsa. A gareta duk wani abu da zai rabata
da Nuri dinta masifa ne.
Tauraron da sa'ar Badawiyya ya haskaka sa'ar
da suka shiga tsaka gidan domin mahaifiyar
Nuraddin ta zagaya bandaki. Dan haka cikin sauri
sai Badawiyya ta wuce da sulaiman kai tsaye
zuwa inda Nuraddin yake kwance. Badawiyya ta
dago ta dubi sulaiman da niyar nuna masa
Nuraddin, amma alamun kaduwar data gani
karara akan fuskarsa. Sun isa ta san yaga
Nuraddin.
Tsawon lokaci likitan na tsaye ya kurawa
Nuraddin idanu, can sai yayi ajiyar zuciya ya dubi
Badawiyya yace. "wannan shine abinda kike son
nuna min din"?
Badawiyya ta gyada kai sannan tace. "zo mu
koma waje".
Dakta sulaiman ya bita a baya zugum-zugum
kamar rakumi da akala, duk ilahirin jikinsa rawa
yake kamar mazari. Suna fita kofar gidan sai
dakta sulaiman yayi sauri ya jingina da jikin
motarsa, domin ji yake yi kamar kafarsa bazata
iya daukarsa ba. A tsahon lokacin da yayi yana
aikin likita ya sha ganin munanan abubuwa,
kamar irin su gawar hadarin mota da sauransu,
amma sa'ar da yaga Nuraddin, sai da hanjin
cikinsa ya yamutse, gashi a kanannade babu kyan
gani amma wai da rai.
Badawiyya ta dubi fuskar Dakta Sulaiman taga ta
hada gumin sharkaf. "Ina fatan ka kare masa
kallo"?
Dakta sulaiman ya gyada kai lokaci guda kuma
yayi ajiyar zuciya yace bakinsa na rawa. "Menene
dalilin nuna min shi"?
Badawiyya ta dubeshi ido da ido tace. "Wadanda
suka kwatanta maka kazo nan ka sameni basu
baka labarin abinda ya mayar dashi haka ba"?
Dakta sulaiman ya girgiza kai, yawun bakinsa ya
bushe. Tsawon lokaci suna duban juna, can sai
tace dashi.
"wannan mutumin da na nuna maka mijina ne,
kwana daya da daura mana aure aka mayar dashi
haka".
Dakta sulaiman ya dubeta a rude. "mijinki fa kika
ce"?
Badawiyya ta gyada kai. "Kwarai kuwa, da
lafiyarsa kalau, kamarka yake a dalilin wai saiya
rabu dani yaki wata aljana ta mayar dashi haka.
Me yiyuwa bazaka yarda da wannan labarin ba,
amma haka dai abin yake". Ta danyi shiru kana
saita dubeshi. "shiyasa na nuna maka shi domin
na sanar dakai cewa duk da haka din da yake, a
duniyar nan babu wanda nake kaunar gani
kamarsa. Akan sai ya rabu dani aljana ta mayar
dashi haka, don haka nake son ka fahimta aljana
ma tayi kokarin raba mu bata samu nasara ba,
ballantana kai mutum mai 'yar kankanuwar
soyayya, babu mai rabani da Nuri darling sai
mutuwa". Tana gama fadin haka sai ta juya da
sauri ta koma cikin gida. Wata sassanyar iska ta
fara busa fuskar Dakta Sulaima. Abin yayi
matukar kadashi bai taba jin labari kamar
wannan ba.
Da sassafe misalin karfe shida saura 'yan
mintuna, Badawiyya ta tashi zaune akan gadonta,
domin lokacin yin wankanta yayi, sai taji kanta
ya fara sarawa. Dama tunda asuba kan nata ya
fara alamun zaiyi ciwo. Badawiyya ta janyo
matashin kan dake kusa da ita ta tura shi a
bayanta kana ta jingina da bango, lokaci guda ta
zura hannunta da dauko hoton Nuraddin dake kan
wani teburi dafda gadonta ta dora hoton akan
kirjinta sannan ta zura masa idananu.
Abdullahi Yusuf Maitama.

ALJANI YA TAKA WUTA {p.37}
Ba'a fi ko dakiku ashirin ba da fara kallon hoton
sai hawaye ya fara sartu akan kyawawan
kumatunta shar-shar.
Wannan sabuwar al'ada da Badawiyya ta tarka ba
karamin konawa mahaifiyarta rai take ba. Tun
tsawon watanni shidan nan, haka Badawiyya
kanyi aduk safiyar duniya.
Ga al'adarta kullum karfe shida take tashi na
safe, ta dauki hoton Nuraddin ta kura masa idanu
tayita kuka. Haka nan zatayi ta fama har zuwa
bakwai, wani sa'in har sai idan mahaifiyarta ta
shigo ta lallasheta, sannan zata bar kukan ta
wuce zuwa bandaki tayi wanka.
Dan haka wannan safiyar sai taji hawayen da
yake zuba yafi na kowacce rana domin in har
ciwon kan yaci gaba da takura mata zaiyi wuya in
har zata iya zuwa gurin Nuraddin dinta, wannan
kuwa yafi komai kona rai a gareta.
Aka kwankwasa kofar a tausashe. Badawiyya ta
dubi kofar cikin gaggawa, haka nan lokaci guda
ta ajiye hoton dake kan kirjinta akan katifar
gadon. Kofar dakin ta bude ahankali mahaifiyarta
ta leko, sanye take da doguwar riga baka kanta
daure da dan kwali na zani. Koda Badawiyya ta
dubeta sai taga alamun damuwa karara akan
fuskarta wannan shine yasa ta mikewa zaunen
sosai ta dubi mahaifiyarta, har yanzu akwai
sauran hawaye akan fuskarta.
"kukan dai kike Badawiyya"? Mahaifiyarta ta
tambaya. Adaidai lokacin data zauna a bakin
gadon ta fuskanci 'yarta Badawiyya.
"Ina ganin lokaci yayi daya kamata ki sallamawa
ubangiji dukkan abinda ke damunki kada ki bata
rayuwarki a banza".
Badawiyya taji gabanta ya fadi, domin bata taba
tsammanin haka daga bakin mahaifiyarta ba.
"yanzu ace mutum Badawiyya bashi da aiki
kullum kwanan duniya sai koke-koke da kuncin
zuciya, wannan ai sai hawan jini ya kamaki. Ina
ganin ya kamata ki rage zuwa gun Nuraddin haka
nan domin ganinsa shike jefa ki cikin damuwa".
Badawiyya taji kamar an watsa mata wuta a
fuska, ta dafe kirji cikin razana, rashin ganin
Nuraddin yafi kowacce irin masifa azaba a
gurinta, sai gashi kuma yanzu mahaifiyarta da
kanta tana cewa wai ta rage zuwa gurin Nuraddin
dinta. Nan da nan taji hawaye ya fara yi mata
sartu akan kumatu sar sar kamar ruwa.
"Ba kuka zakiyi ba, hankalinki yaki bani nan na
fahimtar dake abinda nake nufi". Ta danyi shiru
na wani lokaci, kana taci gaba. "Ba wai ina nufin
ki daina zuwa gurinsa bane kwata-kwata, amma
ya kamata ki rage . Ina laifin kina zuwa gurinsa
sau daya a sati. Amma ki tafi can ki tare kullum
sai kinje, watanni shida kenan fa. Kuma banda
wannan ma kina nufin zaki yi ta zama da shi
ahaka kenan har abada bazaki sake aure ba"?
Numfashinta ya dauke akaro na farko ta dago kai
ta dubi mahaifiyarta tace cikin rarraunar muya
tana kuka. "shi kuma fa.. Yaya zanyi dashi? Shi
ba mijina bane"?
Ganin halin da Badawiyya ta shiga shiyasa
mahaifiyarta ta matso kusa da ita sannan ta
dafata tace. "Nasan mijinkine Badawiyya, kuma
har yanzu da aure a tsakaninku amma yayi
muguwar nakasa, nakasar da bashi da wani
amfani agareki. Yanzu ke kya iya zama da
mutum a kanannade haka har abda? Sai dai ki
bashi abinci kiyi masa wanka ki kwantar ki tayar,
haka zata yiyu kuwa Badawiyya".
Badawiyya taji zuciyarta na neman tsagewa, irin
wandannan maganganu na mahaifiyarta sun fara
isarta domin basu da wata ma'ana agareta.
"mama saboda nifa Nuraddin ya shiga halinda
yake ciki ayanzu, da yabi umarninta ya gujeni da
yanzu yana nan lafiya klau kamar mu. Nikam
bazan iya rabuwa da shiba domin koda na rabu
da shi din ma zuciya da duk wani bangare na
ruhina suna tare dashi". Ta sake fashewa da
kuka.
"ke har yanzu yarinya ce ana rabaki da kiwon
akuya kina kwalla ta haihu abin da baki gane ba
shine kada ki kasancd mai yawan son kanki ke
kadai ki tunafa ni mahaifiyarki be, kuma kina da
mahaifi, ki sani kuma babban burinmu a duniya
shine mu sami jikoki muyi alfahari dasu kamar
kowanne kaka aduniya, to yanzu Badawiyya ta
yaya wannan buri namu zai cika idan kuna tare
da wannan yaro wanda a yanzu mutuwarsa tafi
rayuwarsa"? Tadan saurara tana nazarin fuskarta.
"ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki kuma
fahimci abinda nake kokarin yi miki. Kinga yanzu
akwai yaro dake masifar kaunarki kyakykyawa
dashi, shi baima san kinada aureba sai daga baya
tunda kullum a gida yake ganinki, kamata yayi a
raba aurenku da Nuraddin sai a hadaki dashi".
Badawiyya ta zabura ta dago a tsorace ta dubi
mahaifiyarta cikin kuka. "Bana fatan Allah ya
nunamin wannan rana... Arabani da Nuri"?
Mahaifiyarta ta harareta. "shashar banza, kinsan
dawa nake nufin za'a hadaki? Wannan likitanne fa
daya dubaki alokacin da kika suma, dakta
sulaiman. Kuma in kin aureshin dinma wayace kin
rabu da Nuraddin har abada, sai insa mijin naki
duk sati yana kaiki kina dubo shi".
Badawiyya ta zuro kafafunta kasan gadon kana
ta sunkuyar da kai tana shasshekar kuka tace.
"Bani da wani mijin da ya wuce Nuri, bazan iya
rabuwa dashi ba, tunda ya shiga masifa saboda
ni nayi alkawarin babu mai rabani da shi sai
mutuwa.
"zakwa ki ci ubanki 'yar banza sokuwa inkayi
wasa wallahi saina hana ki fita koda nan da
tsakar gidane".
JANI YA TAKA WUTA {P.38}
Awannan ranar saboda abinda ya faru tsakaninta
da mahaifiyarta bata sami damar dawowa daga
gurin Nuri dinta ba sai baya karfe goma sha daya
da rabi na dare.
Lokacin data dawo gida maigadi ya gaisheta,
sannan ya janyo kofar gidan ya rufe. Tsahon
watanni shida kenan kullum itace karshe shigowa
gidan saita shigo za'a rufe. Maigadin yan
matukar tausaya mata domin laraba mai dafa
abinci a gidan ta taba yi masa gulmar duk
abubuwan dake faruwa akan Badawiyya.
Cikin sauri Badawiyya ta nufi dakinta. Ta riga
tasan kullum da anyi sallar isha'i mahaifiyarta
take yin barci koda yake dai koda tsakar darene
sai mahaifyarta ta leko dakin ta tabbatar ta dawo
sannan zata koma ta kwanta.
Badawiyya ta tura kofar dakin ahankali sai taji
gabanta ya fadi ras, domin tana budewa sai wani
haske ya kashe mata idanu. Kusan dakiku biyar
tana tsaye kafin idanunta su saba da hasken dake
dakin. A lokacinne to Badawiyya taji gabanta ya
fadi. Hasken daga kan gadonta yake bullowa. A
zaune a bakin gadonta tasha kwalliya da kayan
kawa na gaske, fuskarta na kyalkyali kamar
madubi acikim rana Amal ce 'yar sarkin Aljanu.
Tun wani lokaci daya shude Amal ta daina baiwa
Badawiyya tsoro, dan haka a wannan irin yanayi
da ita kanta Badawiyya ke neman abokin mutuwa
sai taji ko kankani Amal ta daina razanata.
"Me zaki yimin kike jirana? Ko zuwa kika yi nima
ki nannade ni? Idan wannan ce niyyarki to
bismillah domin wallahi bani da kaico don kin
nannadeni tunda dai kin mayar da Nuri na haka
macuciya"!
Amal ta dubeta tana murmushi. "Bakaken
maganganunki na iya sawa kiyi nadama".
"Babu wata nadama da zanyi, domin a yanzu
bana tsoron komai, tun daga ranar da kika
nakastamin abin begena, naji na daina tsoronki
bana tsoron kowa a duniya inba Allah ba. Na riga
na kuna bana tsoron kauri dan haka a yanzu ina
umartarki dan Allah ki mayar dani kamar
Nuraddin dan uban da ya haifeki makira"!
Amal ta dubi Badawiyya cikin mamaki dan bata
taba tsammanin irin wannan taurin kai daga
gareta ba.
"Abin bai kai da zagi ba Badawiyya sasin kanki
ne idan inaso yanzun nan ina iya marayar dake
KARAS ko kuma TUNKIYA, amma ni ba wannan
ce ta kawoni ba, abinda ya kawo ni shine zuwa
nayi na baki dama ta karshe, domin ina tausaya
miki a matsayinki na 'yar uwata mace".
Badawiyya ta dubeta cikin rashin aminci, dumbin
tsana karara akan fuskarta. "Wacce dama kuma
zaki iya bani, tunda kin nannade abin kaunata"?
Amal ta mike tsaye daga kan gadonta ta nufo
inda Badawiyya take tsaye, a tsakar dakin.
Badawiyya tayi tsaye kikam ko gezau bata yiba,
duk kuwa da cewa ta lura da farin takalmin dake
kafafun Amal na farar azurfa ne. Badawiyya tayi
mamakin abinda ke cikin takalmin shin tafin kafa
ne ko kuwa kofato".
"kin cika taurin kai Badawiyya kamar Nuraddin".
Amal tace da ita tana dubanta.
"Wannan shiya tabbatar da cewa irin jininmu daya
da mijina Nuri". Badawiyya ta bata amsa. Mijina
din data ce shi yafi komai konawa Amal 'yar
sarkin Aljanu zuciya fiye da komai.
"zabin da zan baki shine na karshe, in kin yarda
kin tserar da shi, idan kuwa kinki to haka
Nuraddin zaiyi ta zama har abada ni kuwa baza
ki kara gani na ba".
"Allah ya fiki makira, kuma ko yaushe naga
damar ganinki saina ganki shin ko kin manta ne
da zoben dake hannuna"? Badawiyya ta daga
danyatsanta sama.
Amal ta dubi zoben da ta baiwa Nuraddin cikin
takaici, tasan duk cika bakin da take na banza ne,
do muddin Badawiyya na tare da zoben nan, ko
babanta mai hancin karas bai isa ya tabata ba
ballantana Amal.
"kinga Badawiyya irin halinda Nuraddin dinki ke
ciki, kashi da fitsari duk a kwance, amma idan
naga dama yanzun nan saina mayar dashi kamar
yadda yake ada in har zaki yimin alkawarin abu
daya". Badawiyya ta dubeta cikin rashin yarda.
"wane alkawari"?
Amal ta dubeta tace "ina so kiyi min alkawarin
indai na warkar dashi zaki bar min shi na aura.
Ke kuma ki sai ki auri wannan sulaiman din da ke
son ki yaya kika gani"?
Badawiyya ta harari Amal tace. "Amal idan zaki
yarda da kaddarar mahalicci, to ki yarda kawai ki
warkar da Nuraddin amma zancen na bar miki shi
baima taso ba' domin babu mai rabani da Nuri
darling sai muuwa.
Amal 'yar sarkin aljanu ta fashe da dariya tace.
"kada ki cuceshi ki cuci kanki, na baki daga yau
zuwa gobe kiyi tunani, in dai har dagaske ne kina
kaunarsa, ki bari mana na warkar dashi na
aureshi domin zamansa lafiya baya tare dake yafi
zamansa a nannade tare dake, ko kuwa me kika
gani"? Ta danyi shiru sannan taci gaba. "Gobe
zan dawo da daddare kiyi tunani da kyau
Badawiyya kawata".
Kafin kiftawa da bismillah Amal ta bace. Dakin
yayi shiru dif! Kamar makabarta. Badawiyya jiki
na rawa ta jingina da bangon dakin sannan ta
lumshe idanunta tace a fili.
"ALLAH kayi min maganin wannan masifa".

ALJANI YA TAKA WUTA
part39
Washe gari tun karfe
tara saura kwata na
safe Badawiyya ta isa
gidansu Nuraddin.
A daren jiya batayi barci ba, zuciyarta cike da
abinda ya wakana
tsakaninta da Amal 'yar
sarkin aljanu.
Badawiyya ta yarda
cewa abinda Amal ta fada gaskiya ne, tabbas
da ace Nuraddin yaci
gaba da zama a haka
gara Amal ta warkar
dashi ta aure shi. Amma
tambayar da Badawiyya ta kasa kawo amsarta
shine, shin anyan kuwa
zata iya zama a duniya
ba tare da Nuri Darling
dinta ba? Ta kuma riga
ta san tsabar taurin kan Nuri ba dole bane ma
idan Amal din ta warkar
shi ya yarda ya aureta
ba. Wadannan
abubuwan su suka
cunkushe kwakwalwarta. Daga
karshe dai ta yanke a
zuciyarta cewa koma dai
menene gara ta amince
da sharudan Amal in har
zata warkar da Nuri, dadai yayi ta zama a
haka a nannade har iya
rayuwarsa gara ta bari
Amal din ta warkar
dashi ta aura din. Akalla
dai, badawiyya tace cikin zuciyarta, koda
mutuwa nayi, nabar
abin tarihi mutane na
baya masu zuwa idan
sunji labarin zasu san
cewa ban zalunci Nuri ba, kuma na mutu a
kokarin ceto shi daga
mummunan kangin
rayuwa.
Da wannan hukunci a
zuciyarta ta isa gidansu Nuri. Tana zuwa suka
gaisa da mahaifiyarsa
sannan ta wuce kai
tsaye zuwa inda Nuri ke
kwance kamar
kwarangwal, an lullube shi da farin kyalle kamar
gawa babu komai a
jikinsa sai diras.
Badawiyya tasa hannu
ta yaye kyallan zuwa iya
fuskarsa lokaci guda kuma ta ajiye jakar
dake hannunta ta zauna
kusa dashi ta kura masa
idanu.
"sannu Nuri... Allah ya
sauwakema kaji"? Tace dashi. Wani zazzafao
hawayen bakin ciki yayi
sartu akan kuncinta,
Badawiyya tayi saurin
dauke kanta gefe guda
ta goge hawayen saboda tasan duk da
yakedai Nuri baya iya
koda motsi, idan yaga
hawayen sai zuciyarsa
ta soye dan bakin ciki.
Badawiyya ta dubi agogon dake hannunta,
karfe tara daidai, lokaci
baiwa Nuri abinci yayi
tace cikin zuciyarta. Dan
haka ciki gaggawa ta
dauko kwanon farar tasar dake kusa dashi
wanda a cikinsa kulum
take juya madar kafin ta
bashi, domin baya iya
sha kai tsaye daga
kwalbar. Badawiyya ta zaro kwalbar madarar
mai sanyi daga cikin
jakar da tazo da ita, ta
juye madarar cikin
kwanon. Badawiyya na
kokarin bashi madarar kenan sai taga kamar
madarar tayi kauri da
yawa, sai ta dan kara
ruwa ciki, sannan tasa
dan yatsanta guda daya
wanda ke sanye da zobe ta fara gauraya
madarar, bayan ta gama
sai ta tsotse dan yatsan
da tasa cikin madarar a
bakinta, sannan sai ta
lura da cewa duk madarar ta bata zoben
dan haka shima zoben
saita sashi a bakinta ta
tsotse shi cikin jindadi
domin tasan zoben ya
taba zama a hannun Nuri.
Ahankali cikin
tausayawa ta tallafi kan
Nuri ta dora akan
cinyarta, sannan ta
dauko kwanon tasar da madarar ke ciki ta
dungura a bakin Nuri da
niyar ya sha.
"Kada ki bashi! Kada ki
kuskura ki bashi! Idan
kika bashi mutuwa zaiyi". Wata fikakkiyar
murya ce take fadin
maganar cikin karaji,
akwai alamar razana
karara a muryar.
Badawiyya ta juya a tsorace bata ga kowa
ba.
"kada ki bashi! Zai mutu
idan yasha"! Cikin firgici.
Badawiyya ta dubi
idanun Nuri abinda ta gani sun bata al'ajabi,
fuskarsa ta fara motsi
tana kokarin nuna mata
wani abu, tabbas
idanunsa nuni suke da
cewa abashi madarar yasha. Badawiyya bata
bata lokaci ba sai ta
durawa Nuri abaki.
Nuri ya hadiyi madarar
kut!.
"wayyo Allah na shiga uku na lalace wallahi
Badawiyya kin cuceni"
muryar ce ke ihu tana
kuka.
Ga mamakin Badawiyya
sai taji kamar jikin Nuri ya fara nauyi akan
ciyarta, da farko bata
gane abinda ke shirin
faruwaba, saida ta kura
masa idanu sannan taga
jikinsa ya fara rikidewa yana dada kumbura,
kifin kiftawa da
bismillah jikin Nuraddin
ya warware ya koma
kamar yadda yake abin
kamar a mafarki. "Alhamdulillah" nuri yace ya
tashi zaune.
Badawiyya ta mike
tsaye zumbur a kidime,
ta rungume Nuraddin
cikin Kuka.
"NURADDIN... Wayyo Allah Nuraddin ya akayi
ka warke"?
Nuri ya mike tsaye,
Badawiyya ta dubeshi
sai taga ya warke garau
babu sauran wata nakasa a jikinsa kamar
ma wani abu bai taba
samunsa ba.
Nuri ya kama dan
yatsan Badawiyya
sannan ya rike zoben daya bata yace. "Har
kullum kwanan duniya
nakan gwada miki da
idanuna cewa ki jikamin
zoben nan ki bani nasha,
amma kin kasa ganewa sai yau Allah yasa kika
gauraya madarar da
danyatsanki mai zoben".
Yadan yi shiru yana
duban jikinsa kana yaci
gaba. Wallahi daga yau dinnan makircinta ya
kare agaremu har abada
domin duk wanda yasha
wani abu da ya taba
zobennan bazata taba
iya cutar dashi ba, shi ya sa kikaga tunda farko
ta kasa tabaki, duk
karyar banza take fada
miki da ace tanada iko
da tuni ta nannade ki
kamar ni".

ALJANI YA TAKA WUTA KARSHEN LABARI.
"Nuri darlin! Wayyo Allah nurina"! Badawiyya ta
dada rungumeshi. Gaba daya nema take ta zama
mahaukaciya.
Mahaifiyar Nuraddin tana daki sai ta jiyo
hayaniyarsu a waje. Gabanta ya fadi sa'ar da taji
wata murya kamar ta danta Nuraddin. Wannan
shiyasa ta fitowa waje cikin gaggawa sai suka yi
ido biyu da Nuraddin. Atake a gurin ta fadi
summamiya.
"Nuri darling na godewa Alla daya warkar dakai,
don Allah zo mutafi gidanmu yanzun nan mama
ta ganka".
Nuraddin yayi murmushi "Amal ta fadamin labarin
komai, wai da wani mijin za'a aura miki ko"?
Gaban Badawiyya ya fadi ta dubeshi cikin
damuwa tace. "yaushe ta fada ma?
Nuraddin yace. Jiya da tsakar dare, kinsan kullum
saita kawomin labarin da zai konamin zuciya.
Yayi shiru gami da murmushi, sannan sai ya
kama hannun Badawiyya yace.
"zo mu tafi gidan naku mu bata mamaki me
yiyuwa ita ma idan ta ganni sai an zuba mata
ruwa saboda kaduwa".
Cikin farin ciki marar misaltuwa, Badawiyya ta
kama hannunsa suka nufi zaure. Koda suka zo
daf da kofar gidan zasu fita sai Badawiyya ta
rkeshi suka tsaya sannan sai ta dubeshi ta
kyalkyale da dariya tace.
"Nuri darling Duk mun rude dubi fa a yadda
jikinka yake har zamu fita waje. Ka koma gida ka
sako wandonka da riga sannan ka yayyafawa
mamanmu ruwa". Badawiyya ta sake fashewa da
dariya.
Nuraddin ya dubi jikinsa cikin mamaki domin
ganin abinda take yiwa dariya. Sannanne to ya
lura ashe tik yake tsirara daga shi sai DIRAS!.
KARSHEN LABARI.
ALHAMDULILLAH.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment