Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yaya anan yake Babu yanda zatayi da kaddara bayan dagewa.

Ko islamiyya Bata barin AmatulMaleek tafiya ita kadai kullum tare suke zuwa lokacin tashi nayi taje su dawo tare duk da ta Dan girma Amma dai hankalinta baitaba Kwanciyar tabarta taje ita Daya ta dawo ita Daya sbd yawun da samarin gidan suka hadewa 'yartata Dan haka tasan ko a hanya zasu iya binta.


Ita kanta AmatulMaleek tasan rayuwarta a gidan tana cikin hadari Dan haka take kiyayewa tareda kame kanta Babu inda take taba zuwa Dan haka wasu da yawa a kauyen Basu Santa ba sbd Bata fita koyaushe tana dakin maamah ana tsaronta kamar wata gwal me tsadar gaske.


Abdulhameed Daya kasance qaninta shi Kuma sai ya zama kowa shi ya sani sbd shi Kam yawonsa yake zuwa yi tinda bara yakeyi duk da Shima Maamah din na kokari akansa Amma dai tafi Maida hankali akan Amah,
Yaron ya kasance Yana so da shaawan karatun Boko Dan haka kullum saiyaje makarantar bokon kauyen ya shige cikin Yara
Wannan dalilin ne yasa ake yawan kawo kararsa ga kawu bello sbd sunyita korosa Amma Baya Dena zuwa Dan haka kawun keji Asmaun da 'yayanta sun ishesa Daman kuka aure yakeson qarawa duk da manyancinsa sosai Dan haka so yake Asmau ta tattara tabar gidan ya samu bangaren sbd ya aje yar bazawarar da zai auro.


*****
Asmau tayi shekaru sosai rabonta da Abeeda a idanuwanta sedai aike Wanda Wani lokacin har mantawa akeyi dasu kafin su samu Wanda daga Yan Aiken ne da aka aje duk wata sukai musu abinci Amma Sam basa kaiwa sai bayan watanni watanni suke kaiwa ganin madame din Bata qasar sai Suma suke tasu zalamar.

A yanzu da AmatulMaleek tafara zama yar budurwar yarinya tini hankalin maamah yabar jikinta Bata bacci Batada nutsuwa kowane dare Bata iya baccin kirki sbd tsoron rayuwar da 'yarta zata shiga a yanzu da samarin gidan da babu nagari zasu iya cewa suna son aurenta kuma tasan batada abinda zai Bata damar hanawa tanaji tana Gani zaa lalata mata rayuwar 'yarta gashi kowannensu yaga budurwa tafara tasawa a cikin gidan sai suce sunaso gashinan da qananun shekaru sunata Tara mata daga me mace biyu Se uku sbd suna cewa sunaso akeyin wuf ayi auren sbd karfafa zumuntar da Babu so ko jin qai a cikinta.


******
Iyalan ASH TALBA sun sauka a kasar Nigeria a bazata sbd rasuwar mahaifin mom Aysha wanda yake tamkar mahaifin ASH din Shima Dan haka dolensu suka dawo Nigeria.

Saukarsu da labarin rasuwar tasa yasaka Maamah shiryawa dole itada 'yayanta sukai Shirin tafiya duk da batada kudin mota Amma hakanan ta siyar da akuyoyinta guda biyu datake ta Reno sbd auren AmatulMaleek idan zaizo kafin lokacin sun qara hayayyafan da zasu isheta yiwa AmatulMaleek din Wani abu.

A wulaqance aka siyesu sbd anga tanason kudin amma Bata damu ba sbd zuciyarta Sam bamai Saka damuwa bace hakama Allah yayi mata sanyin hali da tsananin hakuri me yawa Dan haka baka gane ko ka quntatar da ita sbd tana hadiye komai da sanyin halinta.

AmatulMaleek da batajin dadin tafiyar tasu Sam Amma Bata nuna ba itama sbd kusan halin mahaifiyarta itace ta dauko sak na boye damuwa da hadiye kowanne bacin Rai da sanyin hali Dan haka itace da maamah din sukai wankin kayansu da zasuce tsumma ne ma Amma Kuma su suke dasu Dan haka dasu zasu.

Abdulhameed kuwa farin ciki yakeyi sosai sbd baitaba barin ko wajen kauyen ba bare zuwa babban birni ba dukda baimasan me birnin ke nufi ba Dan shi Kam asalin bafulatanin kauye ne.

AmatulMaleek din ma dai kana ganinsu kaga fulanin kauye sun fito Amma Kuma nutsuwarta ke Hana duhun kansu fitowa.

Ranar da zasu tafi gidan kaf murna sukeyi su tafi sbd bangarensu da kowa keso saikace ce musu maamah tayi bazata dawo ba,
To sukam Koda zata dawo din to idan ta dawo sedai ta koma zauren gidan da zama Dan kuwa duk Wanda ya shiga baida niyarnta gidan sbd AmatulMaleek dasuka qwallafawa Rai akan tana Isa aure zasu aureta su jefa cikin matansu.


Duk Wani Shirin tafiyarsu sun kammala Dan haka washe gari tinda asuba suka hau mashin Abdulhameed na gaba maamah da AmatulMaleek a Baya suka fita kauyen zuwa kauyen gabansu da acan ake Hawa motar zuwa babbar hanyar titi da acan Kuma zasu hau motar zuwa cikin state din kafin daga can su hau motar zuwa Abuja.

Tinda suka hau mashin din Abdulhameed ke washe Baki cikin tsananin farin ciki sbd Bai taba Hawa ko Keke ba bare mashin sai yau din.

Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa kauyen kurmawa,
Saukowa sukai daga kan mashin din maamah na ajiye jakar kayansu gefe
Ita Kuma AmatulMaleek Abdulhameed Dake zare idanuwa Yana kallan koina ta kamo hannunsa suka dawo gefen maamah din.

Kudinsa Maamah ta Ciro ta basa na mashin ya juya Yana musu Allah ya kiyaye Abdulhameed ne kawai ya amsa da Amin cikin murna da farin cikinsa da Baya boyuwa.

Wata motar a Kori kura suka nufa wadda ita kadai ce Daman a kauyen take fita da mutane Dan haka kusan Tama cika Dan haka ba Bata lokaci aka kama su Abdulhameed din da AmatulMaleek aka Dora a sama kafin Maamah ta miqawa Amatu jakarsu tukuna itama ta tattara zaninta ta kama motar ta Haye ta zauna gefen 'yayanta suna Dan gaisawa da sauran mutanen Dake bayan motar a Bude kowannensu kura ta gama rife koina jikinsu kaman anyi juyen yashi a jikinsu sbd iska da akeyi.

Tafiya suka fara Babu me magana acikinsu sai Abdulhameed Dake kalle kalle har bacci ya daukesa a jikin AmatulMaleek wadda itama tafara komawa kamar bokanya sbd iska da qura Dayake Kara sauya kamannin kowa Dake motar.

Tafiya me tsayi Nan ma sukai sosai kafin suka iso babban titin hanyar shiga kauyukansu masu shegen Nisa.

Saukowa sukai kowa qafafunsa sunyi sanyi gashi zuwa lokacin Rana tayi Dan kuwa sha Daya saura Dan haka komai Basu tsayaba ruwa kawai da biredi kawai maamah ta Siya musu suka fada wata motar da zata kaisu state acan su samu shiga motar Abuja.

Babu Bata lokaci motar ta cika Dan haka suka sake daukan hanya.

Biredin data Siya musu ta rarraba musu suka fara cin abinsu hankali kwance.

Abdulhameed duk rawar murnarsa fara komawa ciki tayi sbd zuwa lokacinda suka Isa babbar tashar yola tsoro kamasa yayi sosai sbd Bai taba ganin mutane hakaba sosai da hayaniya anata ihun Neman passengers ta bangare daya ga masu talla takoina suna ihun azo a Siya abinda suke tallan,
Hakama a Wani gefen fada akeyi sosai a cikin tashar..

Ba Abdulhameed ba AmatulMaleek ma kanta tsoro ne da firgici me tsananin gaske ya shigeta Dan Basu Saba haka da mutane da wannan hada hadarba Dan haka dukkaninsu qanqame hijabin maamansu sukai ita Kuma ta riqe hannuwansu gam tana Basu kariya har suka samu motar da zata daukesu zuwa Abujan suka shiga ta rungume 'yayanta tanajin hakanan zuciyarta na karyewa da tafiyar Kuma a yanzu sbd so da dama duk halinda take ciki a kauyen sai tanajin yafi mata nutsuwa akan zuwa birnin duk da wannan tafiyar taji hankalinta ya kasu kashi biyu zatayi ne sbd magana da Madame Abeeda ta rage nauyin zuciyarta da quncin Daya dabaibayeta akan rayuwar AmatulMaleek da batasan Yaya zatai da ita acikin zuriar Sanda Fulde ba.


Shiru tayi tareda Nisa a tinanin rayuwarta tin kuruciya da irin gatan data samu a Baya da rayuwar data taso aciki har kaddararta ta sauya mata hanya zuwa kauye da auren kauye Wanda ayau ta samu kanta a tsaka me wuya sbd rashi na Miji Kuma uban 'yayanta Wanda da ace Yana Raye da bazata samu Kanta a wannan halin na kakanikayi da 'yayanta.

AmatulMaleek Dake jin tsoro me tsananin gaske a duk Nisan da suke qarawa na tafiyar shiru tayi jikin mahaifiyarta tana Jin zuciyarta na shiga yanayi na rashin murna da tafiyar dakuma yanayi na sanyi Dan haka ta rufe idanuwanta tana barin baccin datake ji daukanta.

Kallansu maamah ta sake bayan dukkaninsu sunyi bacci jikinta ta shafa kansu su dukan tana Bude zuciyarta cikin amincin Allah tace

"Allah ya kawo madaukakin haske da girma a rayuwarki AmatulMaleek keda 'dan uwanki,
Allah yasa ki zama tauraruwar macen alfahari a duk inda rayuwa zata kaiki,
Yakuma Baki mijinda zai Miki Mafi girmamman so me tsaftan gaske..Amin"

Numfashi ta ajiye ahankali itama tana lumshe idanuwanta sbd zuciyarta Dake jin kaman tana gazawa da gwagwarmayar.


****
Tafiya yankin azaba kaman yanda aka fada,
Sai yamma lis suka sauka birnin Tarayya,
Daga maamah har su duka kafafunsu sunyi Wani irin nauyi da riqewa Dan haka daqyar dukkaninsu suka iya tsayuwa bayan sun fito motar zuwa lokacin Abdulhameed da AmatulMaleek sosai suke Jin tsoron mutane Dan haka a maqale suke da maamah wadda itama tasan bazata iya Kai kanta gidan ASH TALBA ba Dan haka numbern Madame Abeeda datake cikin kanta kamar hadda ta karanto aka kira musu ita cikin rashin saa akaita kira baa dagawa sbd basa daga bakuwar lamba Dan haka dole guri suka samu a tashar suka zauna ana sake kira lokaci bayan lokaci.

Yunwa da wahala ta Saka AmatulMaleek ringa Amai a gurin har Saida dole aka nemi guri aka kwantar da ita sbd take zazzabi ya rufeta.

Sanyi jikin Maamah yayi ga Abdulhameed Shima duk yayi laushi sbd azabar tafiya da yunwa Dan haka duk taji hankalinta ya tashi damuwa na rufeta ta zuwan nasu.

Sallar magrib ake kokarin shiga Wanda yaketa kira musu numbern ya ringa mata fada Yana cewa wayace suzo batareda sun sanar da inda sukazo din ba?
Basusan baa zuwa Kai tsaye gidajen manya ba batareda an sanar musu ba sbd basason damuwa da takurar talakawa da dangin kauye.

Shiru Maamah tayi sbd zuciyarta gabaki daya Bata mata dadi jikinta yariga yayi sanyi gaba Daya Dan haka batama San me zatace ba bayan sauke Kai kasa.

AMATULMALEEK
Regular 700
Vip 2k
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

#MAMUH#
#AMATULMALEEK
#ASH
#MADAME
#FRIENDSHIP
#LA HOT
#ROMANCE
#LOVE
#ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL
#MEERAH HERBS
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

4
Duk fada da masifar daya daga cikinĀ  ma'aikatan tashar yayi mata akan zuwan nata duk da baisan dalili ba bare Kuma alaqarta da Gidan ASH TALBA din datazo gurinsu Amma dai yasan Hakan datai na zuwan Kai tsaye nada hadari.

Kallanta yayi Kai tsaye yace ta Fadi sunanta ya rubuta Sako ya tura mata ga numbern,

Jiki a mace cikin sanyi ta fada masa tareda Dana 'yayanta wainda yayiwa Wani kallan qyama da takaicin yanda ta kwasosu kaman wasu almajirai sunzo garinda basusan koinaba ko tsoro bataji.

Kai tsaye sunanta Dana yayan nata ya rubuta a cikin sakon da cewan a taimaka a dauki wayar gasunan Tasha a zube harda mara lafiya.

Tafiyar sakon ya sakashi kallanta yace ta zauna ta jira idan ankira to shikenan idan Kuma baa kiraba motar asubar safe su koma inda suka fito.

Gyada masa Kai tayi cikin sanyi da nutsuwa tareda Bude Baki ahankali tayi masa godiya ta juya ta koma inda su Amatun ta zauna tana kallansu har zuciyarta bataji komai ba na haushi ko jin zafin rashin daukan wayar harma da fadan da ma'aikacin tashar yayi mata Dan kuwa Babu lefi a cikinsu saima uzuri datakewa kowa Wanda shine abin dayafi bawa mutane Daman cutatar da ita ko acan kauye sbd komai kayi mata a rayuwa tanai Maka uzuri Bata fushi Komai girman cutar da zakai mata.

Zaune suke cikin duhu da rashin mafita hakanan ta miqe tayi alwala a gurin tayi sallah har lokacin AmatulMaleek a kwance take jikinta yafara tsanani sosai Abdulhameed ma tini Shima yafara kamuwa da zazzabin sbd wahalar yunwa.

Har Akai ishai Babu Wani bayanin biyo sakon da suka tura da kira Dan haka ta Yanke komawarta da bin motar asuba Kila Wani uzurin ya Hana Abeeda ganin sakon Dan haka bazasu cigaba da damunta da Kiran ba akwai takurawa ga Hakan ta sani.

Ruwa kawai ta ringa bawa Abdulhameed da AmatulMaleek har kusan asuba anan suka kwana cikin sanyi a sararin iska ga sauri da duhu harma da qwari kala kala Dan haka asuba nayi sallah kawai tayi suka miqe Dan shiga layin bin motar komawa.

Koda gari ya fara haske AmatulMaleek kaman bazata tashi ba hakama Abdulhameed Dan haka sai hankalinta ya rabu biyu ga tafiyar sbd bazasu iya bin doguwar hanya a Hakan Amma Kuma Babu zabi na yanda zatayi Dan haka tayi shiru a cikin sanyin jiki Dana zuciya idanuwanta sunyi jajir da damuwar Dake riqe da zuciyarta.

Isowar ma'aikacin tashar na jiya ne gurinta Yana qwala kiranta ya Sakata dagowa ahankali cikin sanyi ta Dan kallesa tareda sauke Kai tana gaidasa da girmamawa.

Da farin cikin dayake tareda takaici ya kalleta Yana cewa tayi Maza tazo ana son magana da ita anbiyo sakon da kira yanzu.

Numfashi ta sauke me dumi kafin ta fito layin a sanyaye ta biyosa zuwa inda ba hayaniya ya miqa mata wayar wadda daidai lokacin aka sake kira.

Cikin nutsuwa ta Bude Baki tayi sallama nauyin zuciyarta na raguwa Jin amsa sallamar Abeeda cikin Wani irin nutsuwa ta wainda suke cikin duk wata ni'imar rayuwar duniya.

Jin muryar Asmau ya Saka Madame abeeda sauke ajiyar zuciya a hankali tareda sake Bude Baki tace

"Asmau kece??
"Meyesa Baki kirani da wayarki ba?
Yaushe kikazo?
Sai yanzu nake duba sakon sbd Banda time na duba wayar rasuwar da Akai ya Saka Sam bana samun Hutu yanda ya kamata.

Shiru sukai dukkaninsu sbd kowannensu da Wani girmamman quncin dayake mamaye cikin ransa Amma baisan tayaya zai tinkari Dan uwansa ba sbd Nisan daya shiga cikin kusancinsu da tsananin kaunarsu

Numfashi mara sauti maamah ta sake saukewa ahankali kafin ta Dan saki murmushi me sanyi tace

"Eh nice,jiya nazo sbd labarin rasuwar ta alhaji babba danaji daga bakin Dan gidan kawu bello dayake Dan shiga birni shine yazo ya sanar mun,
Allah yaji qansa yayi masa Rahama,
Munata damunki da kira ga fama da jamaa Anata zuwa gaisuwa."

Numfashi Madame abeeda ta sauke kafin tace

"Ba komai yanzu ku Jira ga driver Nan zan Aiko yazo ya dauko ku keda yaran ai gwara da bakiyi saurin juyawaba Ina buqatan ki Asmau,
Ina tsananin buqatan nawa a kusa Dani"

Shiru suka sake yi jikin Maamah na sanyi ita Kuma acan nata bangaren wasu zafafan hawayen da babu Wanda ya taba ganinta dasu ne suka taru a cikin idanuwanta Amma Bata bari sun taba saukowa kan fuskartaba bare yau din Dan haka ta sake hadiyesu cikin dauriya da karfin zuciya kafin ta kashe wayar ta ajiye gefenta sbd Asmau kamar rauninta ce sbd Bata iya boye mata komai duk dauriya da jarumtarta.

Ita kanta Asmau sanyi jarumtarta ke Neman yi Dan haka ta daure batareda ta dago ba tasake yi masa godiya tana koma gurin yaranta da suka koma kamar mahaukatan almajirai.

Zaunawa tayi tareda zuba musu idanuwanta da suke boye duk Wani abinda yake cin Rai da zuciyarta tana musu fatan hayewa matakin nasara a duk inda suke rayuwarsu.

Zaman jigum tayi tana sauke kanta qasa da jiran tsammanin Kuma Ina rayuwa da kaddara zatai dasu itada yayanta a gaba.

Zaman jiran awa kusan Daya da Rabi tayi zuwa biyu kafin Daya daga cikin Mahaukatan motocin gidan ASH TALBA ta iso tashar daukanta.

Da farko numbern da aka bawa drivern yazo daukanta ya kira shine ma'aikacin tashar ya kawosa har inda Maamah take zaune kaman almajira ita da yaranta yace "gatanan"

Kallanta drivern yayi dakyau kafin ya dawo da kallansa kan mutumin Dake nuna masa ita Yana wasi wasin idan wannan din ce akace ya dauka yakai gidan ASH TALBA sbd ko masu aikin gidan bazasu dauki wannan aikin gidajensu ba bare gidan ASH din da kansa.

Lura da fahimtar tinanin dayake gudana a zuciyar drivern yasaka Dan tashar sake basa tabbacin ita din dai ce,daga kauye ta fito shiyasa.

Kasa cewa komai driver yayi sai kawai ya dauki jakar kayanta ya Bude bayan black range Rover Din dayaxo da ita yana sake kallansu maamah din cikin danne mamakinsa da Dan shakkar idan ba kuskuren daukansu zaiyiba.

Maamah dasu AmatulMaleek ma da basusan inda kansu yake ba rakubewa sukai tareda dunqulewa guri Daya bayan motar Babu me iya motsawa sukai shiru Maamah din najin zuciyarta na Dan sake sanyi da taimakon gaggawar dasu AmatulMaleek din zasu samu Dan kuwa data koma dasu a wannan halin ba lallai ta samu Isa gida da duka yayanta biyu ba Kila ta rasa ran Daya a hanya kafin su Isa,sai gashi Allah ya dubi maraicinsu ya kawo sassauci a lamarinsu ta samun Kiran Abeeda.

Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa,
Koda suka Isa tini sanyin ac yakusan sankarar dasu Abdulhameed Duk da sun Saba da sanyin Allah Amma wannan din yayi musu karfi da yawa sosai.


Babban makeken luxury gate din gidan ASH TALBA aka wangalewa motar gidan dasuke cikinta suka shige harabar gidan datake da Wani irin girma da tsari irin na gidajen turai da Kuma masu abin duniyar qasa da qasa,

Motacin Dake harabar sunkai takwas koma fiye,
Motoci ne wainda babu me karamin kudin da zaka iya lissafawa bare manyan,
Dukkaninsu baqaqe ne sai farare guda biyu aciki sai Ash Daya.

Parking yayi daga gefen da ake ajiye duka motacin gidan Dana mutan gidan Banda na ASH dake gefensu daban sbd ta inda yake fitowa daga sashensa da Babu Wanda yake bin kofar idan ba shi ba Dan haka ta Nan yake fitowa ya shige motacinsa yabar gidan batareda ma kana gidanba bare kasan fitarsa.


Tinda Sharif driver yayi parking ya fito yake Dan Jin zuciyarsa na sake shiga shakku idan baiyi kuskuren dauko Wanda Basu aka aikesa daukowaba.

Bude musu motar yayi Yana kallansu yace maamah tafara fitowa tukuna idan ya tabbatarda sune aka sakasa daukowa saisu shiga.

Wayarsa ya fitar cikin nutsuwa ya Nemo numbern Madame din ya Saka kira.

Saida yayi mata kira biyu kafin ta daga Kai tsaye ya sake gaisheta Yana cewa

"Hajiya ga baqin na dauko Amma bansaniba ko na samu kuskuren daukowa wainda Basu ba....

Katsesa Abeeda tayi da cewa

"Bata wayar naji"

Da sauri ya miqawa Maamah wayar Yana cewa "yi magana taji"

Karban wayar maamah tayi tana sallama Abeeda ta kashe wayar tareda miqewa daga zaunen datake ciki lafiyayyan bedroom dinta sanyeda jallabiya ash da mayafi me Dan girma na sallanta ta ajiye wayarta tana nufar kofar barin bedroom din sanyeda slippers masu tsananin laushi da tsadan kudinsu zasu ciyar da maamah din da yayanta na sati uku koma fiye.

Tinda ta tinkaro babban palonta ta nufo kofa ma'aikatan Dake gyaran palon suka ringa gaisheta cikin tsananin girmamawa sun Dan sauke Kai sbd Koma me zai fitarda Madame din harabar gidan a daidai wannan time din me tsananin mahimmanci ne.

Sharif dayaji madame ta kashe wayarta Babu amsar komai Shan jinin jikinsa yayi sbd ta tabbata kenan yayi kuskuren dauko wainnan kauyawan dajin.

Kallan maamah yayi cikin sauri Yana cewa

"Kinga maza shiga na mayar daku inda na daukoku kafin na Rasa aikina"

Juyawa mota maamah tayi tana kokarin komawa batareda tace masa komaiba Dan itama batasan dalilin kashe wayar Abeedan ba.

Cikin fada da daga murya yaci gaba da yi mata sauri sauri Yana cewa

"Wai bazakiyi sauri ba muje?
Kema kinyi gangancin biyoni bayan kinsan Babu ta inda kukeda arzikin Azo daukanku da mota irin wannan Amma haka kawai kika biyoni gashi Kuma Kinga irin gidan da akazo bazaki Bude Baki kice bakuda Hadi da irin wanna guraren"

Shiga motar Maamah ke kokarin saiga fitowar Abeeda harabar gidan tini ta dagakata daga shiga motar tana tsayuwa a inda take gabobin jikinta na Neman saki idanuwanta dasukai Dan ja suna tsayuwa a kan Abeeda wadda itama nata idanuwan akan Maamah din suke tana kallan Wani irin mugun mummunan yanayin da Asmaunta ke ciki kamar wadda Tayo gudun hijira.

Suturar jikinta ta kalla taji hankalinta na mummunan tashi kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar Asmaun da sauran kadan takoma skeleton sbd rama da bushewa.

Maamah kasa kurar da nata kallan tayi kan Asmau sbd alkunya da muzantar dataji tanayi agaban Abeedan sbd yanayin datazo gidan dashi kamar almajirar data debo tafiyar qafa.

Qasa tayi da kanta lokacinda Abeeda ta tinkarota Kai tsaye jiki a tsananin mace da baqin cikin ganinta ahakan tana isowa hannunta take kokarin kamowa tana ambatar sunanta muryarta na rawa sosai.

Kasa bari maamah tayi Abeeda din ta a kamata sbd jikinta Babu inda yake da tsafta ita kuwa tamkar wata tauraruwar datafi taurari take komai nata na musamman ne sbd Jin dadi,Hutu da daular da Allah yayisu acikinta.

Sharif na ganin Hakan yasan ba kuskuren ne dai aka samu ba Dan haka a Jere ya Sako ajiyar zuciya Yana Bude mota da sauri yahau kokarin kamo Abdulhameed sbd AmatulMaleek bazata dauku garesa ba tinda ta fara zama yar budurwa.

Yanda Sharif ya dauko Abdulhameed kamar matacce ya Saka gaban Abeeda mummunan faduwa tana kallan Motar cikin tashin hankali tace

"Meya samesa?
Ina AmatulMaleek?
Meya samesu?"

Jiki na rawa murya na sauri sharif yace

"Ahaka aka daukosu daga Tasha inaga basuda lafiya sosai sunyi Nisa musamman ita macen ko numfashi ma batayi...""

Bai qarasaba Abeeda ta katsesa da cewa

"What??

Kallan maamah tayi tana Isa motar jikinta na rawa takai hannunta kan AmatulMaleek Dake kwance ba Rai ta janyota kafin tayi Wani yunkuri tini sharif ya kira masu aikin gidan mata su biyu suka iso gurin Dan daukan AmatulMaleek Dan baiyi tinanin Madame din tasu zata iya taba mutanenba.

AMATULMALEEK
Regular 700
Vip 2k
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

##MAMUH#
#LOVE
#ROMANCE
#INSIDELIFE
#ASH TALBA
#NAUFAL
#MADAME
#ABOKIYAR NISHADI
#MEERAH HERBS

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

5
Abeedan bazata iya daukanta ba Dan haka dole masu aikin ne suka dauki AmatulMaleek din maamah Kuma tana dauke da jakarsu suka dunguma zuwa ciki.

Kai tsaye sashen masu aiki aka nufa dasu dayake akwai daki na musamman acan aka Bade musu Daya aka kwantar da AmatulMaleek din gefen Abdulhameed Daya farfado shi Amma baida karfin iya motsawa sai tsoro Mai karfin gaske Daya shigesa ganin inda suke kaman baa duniya ba duk da baisan yanda aljanna take ba da lahirar.

Abeeda da kanta ta fice tana bawa masu aikin umarnin su fara yaran kafin a kirawo likita yazo ya dubasu cikin gaggawa.

Abdulhameed suka fara yiwa wanka fes suka dirji uwar dauda da kurar jikinsa kafin suka fito dashi.

AmatulMaleek kuwa kasa barinsu maamah tayi da kanta ta daure ta wanketa tsaf ta fito da ita.
Kaya aka Basu suka Saka Wanda AmatulMaleek din take aka karbo kayan Husnah Talba daga bangaren iyayen gidan aka Bata maamah ta Saka mata hakama Abdulhameed kayan haidar aka Saka masa take suka Dan yi kyan Gani Babu Bata lokaci likita tazo ta fara dubasu Duk da shi Abdulhameed ana basa tea me tsananin kaurin gaske ya shanye katan Kofi yafara Dan samun kuzari.

AmatulMaleek kuwa ana Bata tea din haka ta amayosa Dan haka dole aka sake gyarata kafin likitar tazo.

Ita kanta maamah ta tsaftace kanta cikin 'yar suturar da aka Bata Dan baayi qasa a gwiwar Kai kayansu store ba aka ajiye sbd Babu Wani sutirar arziki acikinsa.

Da farko sosai hankalin Abeeda ya tashi da ciwon na yaran Dan Bata dauka yunwa da wahala ne tareda iska Dasuka wuni suna sha a hanya ba tin asuba ya jijjigasu gaba Daya.

Likita Abdulhameed ta yara dubawa dakyau ya tabbatarda gajiya ce da azabar yunwa a tareda shi Dan haka ruwa kawai ya daura masa Dan karfinsa Daya tafi ya Dawo.

AmatulMaleek kuwa bayan yunwa iskane ya shigeta sosai Wanda Bata Saba sha ba sbd basa zuwa koina koyaushe suna kauye cikin gida a zaune,Se yunwa da wahalar hanya ta doguwar tafiyar da tinda tayi wayo Bata taba ba.

Itama ruwan ya daura mata tareda allura kafin ya tafi yace basa buqatan magani da sun samu hutawa sosai sukaci abinci wadatacce zasu warware Inshallah.

Sai bayan tafiyar likita Maamah ta iya dagowa ta Kalli Abeeda datafi nuna damuwarta akan ciwon nasu sbd Bata taba ganinsu a wannan halinba bayan ciwo ga wahalalliyar yunwa Nan a tareda su bayyane a jikinsu.

Kan maamah ta dawo da kallanta tareda qurawa Maamah din idanuwanta tana sake kallan qashin wuyanta Da kamar turosa Akai waje duk koina jikinta qasusuwanta a bayyane,
Jin tayi hankalinta ya ninka tashi tareda shiga tsoro Amma tayi kokarin dannewa tareda boyewa sbd kada ta muzanta Maamah din da kallanta dakuma mamakin.

Fitowa tayi maamah na biyeda ita kaman yanda ta umarta suka nufi sashenta sai alokacin maamah ta Dan saki numfashi sbd sanyin AC Daya gama kame koina na sashen da Wani irin kamshi na gidan kudi da basai anfada Maka ma.

A palonta na farko ta zauna ahankali kan kujera tana nunawa Maamah gurin zama tareda sakawa aka kira me aikinta ta kusanta.

Khaltume na zuwa ta Dan tsaya daga gefen Abeedan cikin girmamawa tace gata tazo.

Abeeda Dake kokarin dauke kallanta daga Maamah sbd kallan yafara damunta da alama ta Dan juyo ta kalli khaltumen Kai tsaye tace a hadawa Maamah abinci

Please Login or Register in order to submit comment