Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jikinta yake Amma zuciyar maamah yake ci Dan kuwa maamah bazata sake walwala ba sai 'yar uwar tata ta samu lafiya.

Wanka kawai AmatulMaleek ta iya hadawa Maamah din ruwan zafi tayi Amma ko abinci Bata ci ba ta kwanta,

Bata iya cewa maamah din komaiba sbd tasan Babu abinda zata iya cewa bayan adduar data yiwa madame Abeeda ta samun sauki a bayyane.

Shima Abdul dayayi bacci ya Farka daga baya ya tambaya jikin Madame din Amatu tace yayi shiru kawai.


Husnah kukan datasha Jin ciwon mahaifiyarta Saida ta Saka maamah kuka itama sbd kasa riqe kanta tai Dan ganin kawai sukeyi mutuwa zatayi ta barsu.

Amatu komawa tayi Husnah da maamah din take kulawa dasu sbd halinda suka shiga ahaka Kuma take zuwa makaranta ga aikin maamah da dole itace ta karba tanayi tinda maamah din Takoma asibiti itace take jinya.


*****Kwana biyu madame tafara Jin sauki Dan tana Dan iya komai da kanta hakama maamah komai itace take mata bautarta da sadaukarwa ya ninku Dan haka dole Amatu ta dauke idanuwanta da zuciyarta daga Hakan Dan kuwa ta yarda ta sadaqar kaunar maamah din da Madame din bazata iya Hana maamah bauta mata duk abinda zatai sbd maamah ta riga ta sadaukar da kanta ga Madame din da duk abinda ya shafeta.

Ayau asibitin suka taho tareda Husnah dasu Haydar da ita AmatulMaleek din wadda harta San fada sbd ayyukan maamah data maye gurbin kusan rabinsu ita keyi.

Koda sukazo madame din tana zaune kan kujera maamah na hada mata ruwan wanka a toilet na dakin.

Shigowarsu ya Saka Madame dago idanuwanta dasukai haske ta kallesu Daya bayan Daya tana Jin tausayin 'yayanta da duk sukai sanyi tinda sukaji ciwonta.

AmatulMaleek ce ta nufi toilet din Mai tsaye cikin sanyi da nutsuwa bayan sun gama gaida Madame din da yi mata sannu Dan ta taimakawa maamah aikin datake ta yi a toilet din takasa fitowa.

Wanke toilet din takeyi Wanda baida komai fes yake sbd tsadan asibin tsaftansa na musamman ne bare su dasuke kaman vip room a can sama.

Kallan maamah din tayi tareda Dan lumshe idanuwanta ta qaraso ta Kai hannu ta kama hannun maamah din Dake goge ruwa da mopper sbd kada Abeeda ta taka ta zame.

Dagowa Maamah tayi ahankali ta kalleta da idanuwanta dasuka fada itama
Ganin AmatulMaleek ce ta saki Wani sanyayyan murmushi tana ambatar sunanta da cewa

"Yaushe kuka xo??

Numfashi mara sauti Amatun ta sake tareda karban mopper din tana sake kallan maamah da fararen idanuwanta masu maiqo aciki ta Bude Baki a natsenta tace

"Bari na qarasa kawai kije ki huta tareda su Husnah harma dasu Abdul mukazo."

Murmurshi maamah ta sake zatai magana AmatulMaleek ta girgiza mata Kai a hankali tareda lumshe idanuwanta ahankali tace

"Maamah zan qarasa kije ki gaisa dasu"

Murmurshin kaunar ta sakarwa Amatun cikeda kulawa tace

"Shikenan ki kula kada ki zame yanada santsi sosai"

Gyada Kai ahankali Amatu tayi tana kallonta harta fice toilet din.

Hannun doguwar rigar jikinta ta Dan nade kadan sbd kada ya jiqe ta fara mopping toilet din da maamah tariga ta gama wankewa.

Cikin nutsuwa takeyi gogewan harta gama ta Dan dauraye mop din ta ajiye gefe ta wanke hannuwanta liquid soap din dayake toilet din tafara kokarin hadawa Madame din ruwan wanka.

Wani qamshi ne da Bata taba Jinsa ba a ruyuwarta sbd fitarsa daban da Kuma yanda qamshin yake daban a hanci harma da yanda yake sauka a zuci,
Qamshine me sanyi da Dan haka ta Kalli kayan wankan madame Dake Jere a gurin tana Dan sauke numfashi me sanyi mara sauti sbd sanin wani abu daga cikin kayan wankan ne yake wannan qamshin,

Ruwan wankan ta qarasa hadawa tareda sauke wanke hannunta kafin ta nufi kofa ta Bude ta fito ahankali tana Dan warware hannun rigarta data janye.

Qamshin Daya shiga hancinta a cikin sanyi na nutsuwane tareda Jin tsit din dakin ya Sakata dagowa ahankali idanuwanta Basu sauka a koina ba sai akan the grt ASH TALBA Dake zaune tareda Abeeda a kujera Daya fararen dogayen yatsun hannunsa na sarke da nata tayi shiru a gefen jikinsa kwance.

Firgita da mamakin da Bata shirya musu bane ya Sakata shiga faduwan gaba da shock lokaci Daya sbd ba kowa adakin kowa ya fice hakama tinda ta taso a gidansa suke rayuwa a cikin gidansa yaune ranar farko data fara ganinsa gashi ga ta,Dan kuwa idan ma ya Santa to a iya Baki ya Santa 'yar Asmau takwarar matarsa Abeeda AmatulMaleek.

Rikicewa ta sake shiga sosai Dan Bata tsammanin fitowa Taga ba kowa ba Kuma Bata taba kawo tinanin zata fito ta ga the grt ASH TALBA a gabanta ba yau bayan ganin nesa Suka Saba masa hakama Wani irin zama ne sukai Shida Abeedan wadda tayi shiru a jikinsa da yanda shikuma nasa hannuwan suke sarqe da nata Dan haka duk ta sake rudewa cikin sauri ta nufi kofa tana furta Ina wuni batareda ta dago ta sake kallan inda suke ba.

Amsawa kawai Shima yayi da muryarsa me kauri da tarin nutsuwa da Kwanciyar acikinta batareda ya duba waye ba Dan kuwa gabaki daya tinaninsa da hankalinsa na kan Matarsa dayake Jin kaman ya bar qasar da ita a ranar.


Ita Kuma tana fitowa dakin Kai tsaye gurin da maamah ke zaune ta nufa ta zauna gefenta batareda ta furta komaiba,
Haydar Dayazo ya zauna gefenta Shima Yana kallanta cikin tsananin kulawa da kaunarta da Baya hadawa da komai sbd Allah ne ya Saka masa Hakan tin Yana yaronsa Amma yanzu daya fara zama saurayi Jin yakeyi kamar son dayakewa AmatulMaleek kullum qaruwa yakeyi batareda yasan wane so ne zuciyarsa ke kamuwa dashi ba tin Bai gama zama cikakken saurayi ba.

Jinsa a gefenta ya Saka Amatu juyowa ahankali ta kallesa da fararen idanuwanta Dake sakashi qure kallansa akanta koyaushe sbd kyanta dayake Gani fiyeda duk Yan mata tsaransa da wainda suka girmesa sosai kaman Amatun.

Ajiyan zuciya suka sauke atare tana dauke kallanta akansa sbd sai yau data taba ganin daddynsu a Fili ta fahimci daga Husnah harshi da ake cewa Yana yanayin mahaifinsa duk ba Hakan bane duk da kallo Daya tayi masa ta sauke Kai Amma a Hakan ma zata iya qararda Haydar ba Wani kama yakeyi dashi ba sosai sbd shikam ASH TALBA din batama San tayaya ake fassara kamanninsa ba.


Cikin kulawa Haydar ya sake kallanta yace

"Lafiya dai??

Sake juyowa tayi ta kallesa Dan itama har cikin ranta kaunar Haydar daban ce sbd jinsa takeyi kamar Abdul da uwa Daya Uba daya ya haifesu Kuma qarin girman kaunarsa a ranta shine yafi kowa Bata kulawa da tattali duk da Yana qasa da ita a shekaru Amma sosai yake nuna kulawansa akanta fiyema da Husnah Dan haka kaunarsu take da qarfi.

Bayan ta sake kallansa ahankali ta Sakar masa Dan murmushi tace

"Lfy kalau,Yaya Akai ne??
Ko mu tafi yanzu tinda dad dinku yazo babu me sake komawa ciki Seya tafi."

Kofar dakin ya kalla kafin ya Maida kallansa kan Husnah Dake waya da Uncle Naufal dinsu tin dazu ya dawo da kallansa kan Amatun yace

"Mu bari Dad ya fito mu sake dubata saimu tafi din."

Gyada Kai tayi tana cewa shikenan ba damuwa Allah yabawa mommy Abeedan lafiya.

Amin"kawai yace Yana kallan Abdul Daya dawo daga reception.


Zaman Jira suka fara suna Dan fira sama sama har kusan awa uku kafin ya Bude kofa zai fito.

Qamshinsa ne yafara gauraya gurin Wanda kowanne hancin dayake shaqan qamshin zai bambamta tsadan qamshin da wasu qamshin sbd Kai tsaye qamshin cikin sanyi me nutsuwa yake shiga ya wuce zuciya da itama qamshi me dadi ke isar mata.

Dayake Personal person dinsa Jameel na gurin Yanata waya Shima wanda kusan wayar duk ya harkar businesses na ASH dinne,
Shima ana Bude kofar ya kashe wayarsa ya qaraso kofar ya qarasa Bude masa Yana yiwa Madame sannu da jiki.

Fitowa ASH din yayi Haydar da Husnah suka bisa suka wuce Husnah na riqe da hannunsa Daya data kama Shima cikin kulawa yake Dan kallanta a da idanuwansa da idan ba iyalansa ba baayi kalla sbd tsananin kwarjininsu da haiba.

Maamah da ita ce kawai yayi magana da ita sosai kafin ta fito dakin su barsa ta miqe tafara komawa ciki kafin Amatu da Abdul suka bita.

Maamah Dake zaune har lokacin Amma da alama tayi wankan suka kalla suna sake mata sannun ta amsa tana kalla maamah da itama ita take kallan lura da jikin Abeedan din yayi sanyi idan Kuma ta canka abinda Abeedan take tsananin gudu da tsoro ne yake Shirin faruwa zaa dauketa daganan din zuwa Neman lafiyanta zata rabu da 'yayanta.
#MAMUH#


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


13
YAR UWATA TSAYA KIJI KAYANDA SISTER NA KE SAYARWA BAZAKI RASA ABUNDA KIKESO BA A CIKI IN SHA ALLAH 🙏💪

Sis Kinason siyen maganin Kara girman hips da breast kodai rama ce damuwarki❓kinaso kiyi kiba ki ciko kiyi kyau KO KUMA KAYAN GHT KIKESON KISIYA Na gyaran skin fatarki tayi kyau❓ko maganin infection ❓asthma ❓ ulcer ❓ rashin haihuwa ❓ hepatitis ❓ diabetes ❓ ko Kuma kiba ce da tumbi suke damunki❓ to tanada magani da yardar Allah ❓ga group link din sister na🥰 kiyi joining 👆👆👆👆Zaki samu fiyeda yanda kikeso Kuma kayanta nada sauki ga kyau tested and trusted 👍💪

Idan bakyason shiga group kiyi saving number dinta👉 https://wa.me/+2349038090328 👈kimata magana kice kinyi saving itama zatayi saving taki🥰 zaki godemin na hadaki daita danayi in Sha Allah 🤗



*************
Ganin AmatulMaleek da Abdul na gurin yasaka Babu Wanda yayi magana a cikinsu kowa shiru yayi jiki a mace sbd tafiya ce da Kila batasan ranar dawowanta ba.

Amatu data lura da dukkaninsu jikinsu yayi sanyi Kuma Babu me magana acikinsu kowa yayi Nisa a tinanin,
Ajiyan zuciya ta saki a boye kafin ta miqe tsaye tana kallan Abdul Dake amfani da wayar Haydar tace masa su tafi waje su Jira su Haydar su dawo su wuce gida.

Miqewa yayi a tare sukaiwa mommy Abeedan adduar samun sauki suka kalli mahaifiyarsu sukai mata sai anjima suka fita maamah na bin bayansu da kallo cikeda tausayinsu sbd tasan zuciyarsu na cikin radadi da Jin ciwon wahala da bautan datakeyi Amma Kuma abinda Basu saniba shine duk wannan sadaukarwa ba iya Abeeda bane kawai sbd sune,sbd su samu ingantaccen ilimi da rayuwa me kyau ne Abisa ga sharadin mum Aisha data shimfida mata sharadin idan 'yayanta zasu samu ilimi me kyau ita zata maye aikinta da iliminsu.

Numfashi Amatu data fita ta sauke kaman yanda Suma bayan fitarsu Amatun maamah ta Dan sauke numfashi me sanyi a boye.

Su Amatu suna saukowa qasa cikin saa lokacin ASH TALBA yabar asibitin Husnah tabisa Dan haka Haydar kawai suka samu zai hawo saman Dan haka suka Jira yaje yayi bankwana da mahaifiyarsa ya sauko suka tafi gida.


Tsawon lokaci da tafiyar kowa har dare yayi maamah tayi maga komai na Shirin bacci ta kwanta Amma bacci ya kasa zuwa idanuwanta Dake cikeda yanayi na ciwo na irin Wanda yake Jin jiki,

Tanason magana Amma Sam Bata iyawa Dan kuwa zuciyarta tariga tayi Wani irin sanyi da saddaqarwa akan rabuwarta da 'yayanta tazo,

Wasu hawayene masu tsananin zafi suka gangaro daga cikin idanuwanta dasukai fari fes irin na ciwo.

Saukowar hawayenta akan idanuwan maamah suka sauko Dan haka tayi shiru batareda tace komai ba sbd duk abinda ya Saka Abeeda kuka yakai qololuwar raunana zuciyarta.

Tin hawayen na gangarowa cikin rashin sauti har kuka me sanyi da radadin zuciya ya kufce mata ta rintse idanuwanta tana yin sa sosai har lokacin Bata iya Bude bakinta ba.

Wani irin sanyi da mutuwa jikin Maamah yayi itama nata idanuwan suka ciko da hawaye sosai sbd Babu kalman da zata iya fadawa Abeeda yanxu ta sanyaya mata abinda take ji din.

Shiru dakin ya dauka bayan kukan madame Abeeda Babu abinda yake tashi cikin tsananin qunci da damuwar da tasan Allah ne kawai yasan Yaya rayuwa zatai da ita kodai ta dawo ga yayanta a Raye kokuwa a dawo musu da gawarta.

Duk yanda maamah taso daurewa kasawa tayi sbd maraicinsu dasuka taso aciki kowannensu batareda iyayensa ba dakuma yanda rayuwa tayi da kowannensu shine ya dawo musu zuciyarsu ta karye itama tafara gangaro da hawayen tana rufe fuskarta da mayafin Dake jikinta sbd yanda kukanta ya qara ingizowa da yanda ta rasa kowa nata daga iyayen har mijinta Abeeda kawai ta rage Mata itama gasu a Wani hali na fargaba da tsoron me zai iya faruwa sbd ciwonta.

Ita Abeeda kukanta me tsanani dayake sake karya zuciyar maamah na yanda zata bar yayanta duk da tasan suna cikin gata gaba da Baya Amma rabuwa da yayanta da mijinta ASH Wanda take Jin zuciyarta kawai Neman bugawa takeyi idan ta Tina tana tafiya shikenan zai iya shiga Wani hali na damuwar da zai iya nesanta kansa da kowa harma 'yayansa Dan kuwa ayanzu ta tabbatarda soyayyarta data Dade tanason tabbatarwa a zuciyarsa.


Haka suka kwana Babu me dadin zuciya sai tinanin da kowa ya zurfafa aciki qarshe Hakan ya tayarwa madame Abeeda Wani ciwon Amma ta daure sbd tanason kwanakin da zasuyi kafin tafiyar tayi su tareda yaranta cikin kauna da kulawa.

Ita kanta maamah daurewa tayi sbd damuwa na Neman tayar mata da nata ciwon zuciyar Amma batason kwantawa sai take dannewa da daurewa.

Washe gari qarfin halin da Abeeda ta nuna yasa aka sallamesu
Ko wannan Karan ASH da kansa ya dauketa ya tafi gida da ita.

Babu Wanda ya samu ganinta sai washe gari ta dawo bangarenta anan duk suka zo sukai mata sannu 'yayanta kuwa suna tareda ita,
Ko baqin dataita yi mutanenta masu zuwa dubiya matan manya basa Wani jimawa suke tafiya sbd an Hana abarta ta gaji sosai.

Tinda ta dawo kulawan da akeyi da ita ta ninku sbd wannan Karan duk Wanda ya kalleta yasan ciwo ne a tareda ita sosai Dan gaba Daya Takoma fara tafara sauya kamanni hakama ko magana tayi sosai saita gaji Dan haka ko magana baa son ta cika yi.

Daga yayanta har masu aikin gidan a yanzu kowa jikinsa a sanyaye yake Babu me doguwar walwala a gidan kaf Dan kuwa me gidan kansa Baya cikin walwala da dadin zuciya ko kadan sbd halinda matarsa take ciki.

Husnah data tabbatarda ciwon mahaifiyarta akwai yiyuwar takewa akwai yiyuwar tafiyarta tabarsu yasa take depression yafara kamata sbd ko karatu ta dena ganewa,
Gashi kowacce safiya suka tashi jikin mum din nata ba sauki gaba abin yake sake yi,
A Koda yaushe mum din yanzu magarsu nasiha ce gareta,
Haydar ma dayake namiji depression din kamasa yayi.

Gidan ASH TALBA tini ya tashi daga gidan farin ciki sbd zuwa yanzu Madame abeeda tayi Nisa gashi tafiyar da zaayi da ita Bata kammaluba
Gashi ita kanta Abeedan ta shiga mummunan damuwa da Saka abin a ranta Dan haka sai hawan jini me tsananin gaske ya shigo ciki da ciwon zuciya Dan haka jikin ya kasa dauka.

Maamah datake Jin danginta daya data rage Mata zata barta kusan ASH da 'yayan Abeedan ne kawai suka fita shiga damuwa Amma itama tini jikinta yake Neman rikicewa sbd damuwa Amma su Amatu nata kokarin kulawa da ita sbd ita idan ta kwanta basuda me kulawa dasu Dan haka suke lallabata duk da Suma suna cikin damuwa da kukan halinda madame Abeeda take ciki.

Madame abeeda takai matakin da ko magana Bata iyayi Amma ko acikin hali na tsananin ciwo maamah take sake bawa amanar 'yayanta sbd kaf duniyarta tasan bayan dad dinsu Babu Wanda zai kaunacesu ya kula dasu fiyeda nasa yayan sai maamah Dan haka Babu abinda take iya daure ta furta sai amanar yayanta ga Asmau wadda itama cikin kuka sosai koyaushe take tabbatarwa da Abeeda zata kula dasu Husnah da Haydar kamar itace ta dauki cikinsu ta haifesu wannan alqawarine datai mata zata kula dasu har inda nata karfin da rayuwar ta qare.


Ciwon Madame Abeeda Wata babbar jarabawa da kaddarar familyn ASH TALBA ne Dan kuwa tini labari ya yadu sbd tayi Nisan da kusan duk sun fidda Rai,
Kuka da tashin hankali irin Wanda familyn suka shiga baa magana Dan kuwa shi kansa ASH din isolating kansa yayi sbd sai yanzu ne zuciyarsa take sake tabbatar masa da tsananin so da girman Abeeda a zuciyarsa hakama yanda yayansa abun ya tabasu musamman Husnah da tini kanta yake Neman tabuwa da lamarin da Basu tana sanin meye rashi na dukiya ba bare na Rai tinda Basu taba rasa Wanda yake shaqiqinsu da wayonsuba.

Husnah batasan cewa idan mum din tasu ta rasu ba ita shikenan batada uwa batada Uba da Kila abin saiyafi haukatar da ita,
Haydar Amatu sosai ta tsayu akansa tana kulawa dashi ta hanyar rage masa damuwa itada Abdul Wanda Shima harda Husnah Yana kulawa da ita hakama ta bangare daya maamah Kam ciwo ya kwantar da ita Amma ahakan take daurewa,

Mum Aisha tashiga damuwa Amma ta rashin dawowan Naufal a daidai lokacinda yakamata ace familyn gidan duk suna Nan tareda ASH wadda duniya ma ta tabbatarda yanda yake tsananin son matarsa Madame Abeeda Talba.

A lokacinda tafiya da Madame Abeeda yayi ta kwana biyu da fita hayyacinta Dan haka kamar gawa aka gama komai aka tafi da ita tareda mum Aisha da yayanta suka tafi.


Bayan tafiyarsu kusan gidan kwana biyu Akai ana zaman da zaa iya cewa kaman na makoki,
Maamah da abin ya Dan tabata dole su Amatu suka dage gurin kulawa da ita sai ya zamana kusan ragamar gidan ta dawo hannunta tinda a hannun maamah take khaltume yanzu ta dawo karkashin maamah Dan haka yanzu da maamah din batada lafiya sai komai ya dawo hannun Amatu.



*****Bayan kwanaki da tafiyar mutan gidan da addua da dagewa da kulawa suka samu maamah tafara samun sauki tana warwarewa yanda ya kamata.

Ganin karatun yaranta na Neman tabuwa yasa maamah din Saka qarfin hali tana warkewa Dan kada ta daqusar da yayanta.
Cikin wasu kwanakin ta warware gaba Daya ta koma ayyukan gidan da kulawa da Gidan Dan kusan kowa gidan a qarqashinta yake yanzu itace aka barwa amanar gidan da kulawa dashi sbd shi kansa ASH TALBA ita yabarwa kula da kowa na gidan.


AmatulMaleek kuwa tini Takoma bakin karatunta Daman tana zuwa ne tana skipping wasu kwanakin sbd jikin Maamah Dan haka yanzu da maamah ta warke saita dage tinda gamawa zasuyi watanni kadan masu zuwa.


****Sati hudu su Husnah sukai suka dawo gaba dayansu jiki a sanyaye batareda mahaifiyarsu ba wadda komai ya tsaya a duniyarta dama tasu duniyar Dan kuwa jiki dai ankai inda baason Akai,
Ana Saka ran paralyze ya shiga ciki Amma baa tabbatar ba sbd gaba Daya tayi slipping into coma Dan haka baa San ranarda zata Farka ba,hakama akwai yiyuwar daga coma din bazata tashiba shikenan ta tafiyarta Dan haka a cikin mummunan tashin hankali sukai kwanakin da sukai suka tattaro gaba dayansu suka dawo Dan qanwar mahaifinta Dake Greece din da zama zata kula da ita duk da asibitin Wani Baya zama sune suke kulawa da komai monthly ake zuwa duba patient sosai suke kulawa dasu tinda kudi masu yawan gaske ake zubewa gasu da qwararrin likitoci.


Bayan dawowansu ASH TALBA Babu Wanda ya sake ganinsa Sam Babu ma Wanda yasan yana qasar ya sanar da Personal person dinsa Jameel Baya buqatan ganin kowa da kowannen irin aiki sai bayan kwana biyu Dan haka Jameel ya sanar da securities na gidan kwata kwata ma baqi yanzu idan ba family ba kar Abar kowa yashiga mansion din.

Mum Aysha kuwa Basu fi sati biyu da dawowa ba ta bar qasar zuwa Spain sbd Naufal Dake Neman buga mata zuciya da baqin cikinsa da bacin Rai yaqi dawowa duk kira da massages din datake aika masa Dan haka a yanzu da ASH zaiyi rayuwa ba tareda matarsa ba abu biyu take buri da buqata a wannan bagiren Amma Naufal din da Allah yayi da jinin ubansa data Jin ranta na quna idan tana ganin halinsa yaqi dawowa sbd anan Yana ganin bazai samu mata yanda yakeso ba yana biyan buqatansa,Dan haka gwara taje ta taho dashi da kanta.
##MAMUH#


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


14
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096



**********
Husnah bayan dawowarsu komai tsayawa yayi a rayuwarta sbd duk yanda aka dauka zata iya riqe abin takasa sbd kanta da zuciyarta Sam basa iya daukan abinda Bata Saba gani ya faru a rayuwarsu ba Dan haka sai abin yafara yawa Yana bawa maamah tsoro da Haydar harma dasu Amatu Dan kuwa cikin kanta depression din yafara tabawa Dan kuwa a yanzu rayuwa ce sukeyi kamar mahaifiyarsu dai ta riga ta rasu Dan kuwa dukkaninsu sun saddaqar da ba tashin zatayi ba San haka take Jin ita mum din ma ta riga ta rasu.

Dad dinsu sosai ya Maida hankali akan kulawa da lafiyarta sbd kada abin ya taba kwakwalwanta sosai duk da yariga yafara tabawa Dan haka ya tashi tsaye Shida maamah ne suka tsayu a gun kulawa da ita da yawon ganin likitocin da aka ringa yi da ita harta Dan fara samun sassauci tukuna Dad din yakoma harkokin gabansa maamah ta ci gaba da kulawa da ita.

***Maamah ta zama uwa ta zama kusan Uba ga 'yayan Abeeda da nata yayan Dan kuwa Dad dinsu Bai fiya zama ba kusan youshe Yana hanyar zuwa dubo Abeeda duk da Babu Wani alamar nasara ko zata Tashi din Amma Bai cire tsammani ba kamar yanda yake Jin idan Abeedan ta tafi tabarshi zuciyarsa zata samu raunin da Babu healing har abada.

Babu abinda Ba'a wadata maamah da 'yayanta a yanzu da komai na ragamar gidan yake hannunta,
Babu duniyar da basa samu,

Lalurar Husnah itace Mafi wahalar da maamah Kesha a rayuwarta sbd tamkar me ciwon qwaqwalwan gaske Takoma mata Dan haka sai take Shan wahala da azabar kulawa da ita Dan kuwa itama abin sai yake Neman taba ta Dan ganin takeyi idan AmatulMaleek dinta ce Hakan ya sama duk abu Daya zata ji gashi kusan ayanzu marayu ake daukan su Husnah din.


Ahankali ahankali lokaci yaja sosai Husnah tafara samun lafiya sosai bayan lokaci me Dan tsayi data dauka a halin na wuya da tausayi,
Maamah nata yayan sun hakura sadaukarwa Husnah da ita Dan kuwa tin bayan shigar Husnah wannan halin maamah Takoma abin tausayi itama sbd kula da Husnah din,
Ta wahala iya wahala akan Husnah,
Wani tsufa da qanqancewa tayi sbd rayuwar data samu kanta aciki,
Daidai da rana Daya Bata taba Jin gazawa ko jin ba 'yarta ce ta jini take dawainiyar da ita ba,
Husnah da ita maamah din sun samu Wani irin shaquwa da bond me karfi dayasa AmatulMaleek dole ta barwa kanta yarda da Babu abinda zai wanke ko rage kaunar da maamah kewa Abeeda da iyalinta,

A yanxu Husnah data saddaqar ta rungumi rayuwa a yanda tazo musu ba magaifiya sai maamah da a yanzu itace take wa kallan uwa ta gasken gaske harka tana Jin kamar ta Fi Amatu so da buqatan maamah a rayuwarta Dan kuwa kauna da so me tsananin gaske maamah ta nuna make a babu sirk,

Haydar kuwa Amatu ce ta cike masa gurbin uwa,Kuma 'yar uwa harma da masoyiyar dayake fata a gaba Dan itama duk da karatun datake harta gama ta tsayu akan kulawa dashi da debe masa kewa da hanasa shiga kowacce irin damuwa itada Abdul Daya zama kamar twin brother dinsa Dan kuwa komai nasu a yanzu Daya ne Babu bambamci.

A bangaren ASH TALBA kuwa a zuciyarsa Wani matsayi me girman gaske maamah ta samu da Babu abinda zai iya biyanta dashi har abada,
Itace ta tsaya akan gidansa da 'yayansa a lokacinda Babu Wanda zai tsaya masa,
Alokacin da 'yayansa suke buqatan uwa,
Alokacin da Shima yake buqatan macen da zata tsaya masa gidansa,
Ta sadaukar da rayuwarta da karfinta da lafiyarta harma da 'yayanta Bata bari gidansa ya shiga maraicin matar gidan ba,hakama yayansa Basu shiga maraicin da zai illata kuruciyarsuba, haka ma dashi kansa da itace ta tsaya tsayin

Please Login or Register in order to submit comment