Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu irin hawaye masu dumin kayewan zuciya na ganin mace kamar Abeeda a kwance gabaki daya kamar ba itaba a cikin qanqani lokaci Allah ya Maida ita Hakan,

Tayi Wani irin haske tayi fayau kamar wadda Babu jini ko kadan a jikinta hakama fatarta kamar wadda aka shafe da yar farar Hoda.

Kasa riqe hawayenta tayi suka fara gangarowa tana Sauke idanuwanta daga kan Abeedan tanajin kaman zuciyarta bazata dauka ba sai kawai ta fashe da Dan kuka mara sauti tana Jin halinda Abeedan ke ciki har cikin zuciyarta.

Ita kanta mum Aisha duk tazo Jin takeyi zuciyarta na karyewa sbd abu ne dayazo lokaci Daya hakama ASH TALBA yakasa fada musu abinda likitoci sukace akanta tin ranarda aka kawota asibiti zuciyarsa ke cikin Wani mummunan hali Amma qarfin halinda yaqi nunawa,

Abeeda wata tsoka ce a zuciyarsa dayakejinta musamman duk da baisan Menene so ba,
Idan Hakan shine so to tabbas Abeeda tagama zama sonsa qwal Daya da bayajin zai samu sassauci akan Hakan.


Kuka sosoi maamah Tasha a asibitin Wanda yasaka nata ciwon datake dannewa tashi sosai sbd Daman ita Kuma matsala ce ta zuciya datake kumbura tsaban kunci da damuwar datake ciki.
#MAMUH#
For more pages follow me @Mamuhgee at arewabooks or join vip


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


10
Badan mum Aisha taso ba dole ta Bada dama likita ya duba maamah a asibitin sai gata itama anbata gadon sbd sosai jikinta ya rikice.

Bayan likita ya gama komai akan mamah din ansamu tayi bacci yayiwa mum Aisha bayanin ciwonta da hutun datake buqata ya tafi.

Babu abinda mum Aisha take tinanin tsayawa tayiwa maamah din Dan haka ta dawo gida saima data huta tayi sallah taci abincin ta Tina da maamah din tasaka khaltume ta hada Amatu dame aiki Daya aka kaisu asibitin gurin maamah.

Amatu karan farko tana ganin halinda mahaifiyarta take ciki Jin tayi komai nata yayi sanyi sbd Koda sukazo tayi Amai Amma Babu kowa adakin bare ya taimaka mata harta koma bacci ahakan.

Share hawayenta dasuka gangaro tayi ta qaraso tafara kokarin tsafatace maamah din batareda wadda aka hadota da ita ta taimaka mata ba duk da qarancin shekarunta ita kadai ta tsafatace mamanta ta gyarata zuwa lokacin jikin maaman ya sake rikicewa Dan kuwa kaman Wanda beso aka zo asibitin ba.

Tsoro dukkaninsu suka shiga sbd Dena numfashin da maamah tayi hakama yanda take fizga tini suka kirawo likita Yana zuwa akace su fita.

Suna fitowa dole Fatima ta tausayawa Amatu itama jikinta yayi sanyi sbd itama marainiya ce tasan suna rasa mamansu a yawon aikatau Kila Suma zasu qare.

Zaman Jira suka dasa a wajen dakin har likita da sauran nurses suka gama duba maamah din suka fito suka wuce Babu Wanda yace musu komai sbd ganin basune sukeda iKon Jin komai ba sai mum Aisha tazo itada ta kawota.

Ciki suka koma suka zauna shiru Babu me magana sai kallan maamah da Amatu keyi a Kai Akai.

Anan Amatu ta kwana tareda Maamah ita kadai sbd ana kawo musu abincin dare aka koma da ita.

Husnah ma taredasu Abdul da Haydar akazo dasu suka duba mommynsu da maamah din suka koma.


Acikin kwana biyu da wuni biyu maamah ta zabge itama Takoma kaman ba itaba ciwo ya sauyata,
Amatu ma sosai ta Dan sake figewa sbd Bata iya ko sabawa da dawainiyar asibitinba dukda Babu abinda sukasan ma Yaya ake biyansa komai Kai tsaye cikin bill na familyn ASH yake shiga.

Madame abeeda kuwa jikinta itama dai sai ahankali har lokacin Dan haka aka fara shirye shiryen fita da ita waje Amma saita farfado Dan haka ana Saka ran farkowanta kowane lokaci.


Maamah Saida tayi kwana bakwai tana jinya me wahala kafin sauki yafara zuwa lokacin Abeeda ta farfado itama jikin nata yafara sauki Kuma baa sanar mata maamah na asibitin tana jinya ba sbd kada a qara mata damuwa.

Koda Maamah tafara samun kanta dauriya da qarfin hali ta Saka sosai ta warware aka sallameta sai alokacin taje ta dubo Abeeda wadda ramarta ta bayyana sosai,
Ita kanta Abeedan dataga maamah sai data tambaya cikin sanyi da rashin qarfi cewan ko maamah din tayi rashin lafiya ne sbd yanda duk ya qanjame itama.

Murmurshin karfin hali maamah ta saki tana girgiza kawai tana qarasa zama a kujeran gaban gadon tareda Dan dafa bakin gadon tana kasa kallan fuskan Abeeda ta tambaya Yaya jikin nata.

Numfashi Abeeda ta sake ahankali tana Dan lumshe idanuwanta sbd gajiyan datake ji ta gyada Kai ahankali tana qure kallanta akan maamah din wadda take kasa kallanta.

Amatu ma da Bata samu zuwa duba mommyn ba sbd dawainiyar kulawa da maamah sai alokacin tayi mata sannu tana fatan samun lafiya.

Zuwansu Husnah tareda su Haydar ya Saka dakin Dan daukan hayaniya kadan sbd murnan ganin iyayensu sun samu sauki kowacce tana zaune da kanta sabanin yanda suke zuwa ganinsu a kwance Babu me sauki.

A Nan dakin suka wuni sai dare suka tattara suka koma gida gabaki daya sbd an sallami maamah,
Suna dawowa gida wanka maamah din tayi Amatu ta Sakata Shan maganinta kafin taci abinci ta kwanta hakama Haydar da Husnah na dakin nasu anan sukai dare kafin suka koma can cikin Mansion suka nufi dakunansu suka kwanta.

Washe gari wankin kayansu Amatu tayi nata Dana maamah Dana Abdul,
Bata gama ba sai Rana Dan haka tana gamawa sallah kawai tayi taci abinci itama ta kwanta ta samu baccin Hutu.

Sai yamma sosai ta tashi tayi sallan laasar lokacin maamah Dan karfin hali tabi masu zuwa asibiti zuwa dubo madame,
Amatu bataji dadin fitar maamah ba a halinda take ciki Amma Kuma batada abin cewa sai kawai tayi fatan samun lafiyansu su dukan.

Sai dare maamah ta dawo cikin ikon Allah tareda madame din suka dawo anyi sallama.

Madame din tareda daddynsu Husnah ta dawo Dan haka babu Wanda ya ganta sbd Kai tsaye bangarensa aka ajesu Kuma sun shige Dan haka Babu Wanda ya ganta sai washe gari Shima washe garin Se yamma ta fito sbd Babu abinda Babu acan da zata buqata,
Masu Kai abinci ne kawai ke shiga sashen Se masu gyara Suma suna gama abinda yakaisu suke fitowa.


Kowa yaje har palonta na kurya ya gaisheta ya mata sannu da jiki da fatan samun lafiya Mai dorewa kafin kowa ya fito aka barta dasu Husnah sai mum Aisha data shiga itama.

Maamah da Bata gama warwarewa ba haka ta ringa yawon kulawa da ita sbd Abeedan tafison maamah a kusa da ita akoda yaushe,
Tafi Jin sauki da qarfin jiki takeji idan maamah ce take kulawa da ita.

Ita Kuma maamah Sam bazata iya fadawa Abeeda batada lafiyanba tinda harta Nuna ita takeson ta kula da ita to tabbas zata danne tayi mata komaima.

Amatu a zuciyarta bataji dadin Hakan ba sbd maamah din kullum dare itama haka take kwana jikin Se ahankali.


******Da wannan kacokam lalurar kulawa da Abeeda ya dawo hannun maamah wadda har tsaftan bangaren Abeedan gaba Daya mum Aisha tasaka aka bar mata Dan haka sai maamah ta koma tamkar itace me aikin Madame abeeda a gidan.

Tafiyan da akaso yi da Abeedan ganin ta warware yasaka ta buqaci ASH din ya barta taci gaba da ganin likita anan,
Shawara yayi da likitoci qwararri suka ce zaa iya barinta Nan din duk ba matsala Suma sunada likitoci cancer masu kyau,,Hakan ya Saka ya barta din Badan hankalinsa ya kwanta sosai ba sbd bayyanar cancer a tareda Abeeda ya jijjiga duniyarsa da duk abinda yake cikinta sbd a ransa Abeeda wata haskensa ce da baya fatan rasawa a kusa Yana fatan su tsufa tare su mutu tare.


********
Amatu da Abdul sun sake komawa bakin karatunsu da suka bari a Nan din sedai wannan Karan harda Boko aka sakasu makaranta me kyau da tsada Amma ba wadda su Husnah keyiba.

Amatu Sam batajin kunyar girman data Dan Fi Yan ajinsu ba tace tafison tafara daga Js 1 din Daya kamata Dan haka anan aka Sakata akan idan anga kanta na budewa sosai sai idan zata shiga Js 2 a jefata Js 3 kawai.

Abdul ma nursery aka sakashi duk da yayi girma kamata yayi ace an sakasahi primary 2 ko 3 Amma dai sbd baida komai na karatun dole aka sakosa daga can.

Daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya damu da girman da yayiwa Yan ajinsu su farin ciki ma sukai da Hakan Dan haka suka dage tareda Maida himma musamman Amatu datasan wahalar mahaifiyarsu ce suke mora da karatun Dan haka bazata bari uwarsu tayi wahalar banza ba Dan yanzu aiki bana madame Abeeda kawai takeyiba kusan aikin gidan Rabi yana rataye ne akan maamah din Dan haka tsufa na dole yafara rufarta ga ciwo shiyasa kowanne dare a wahalce take bacci gari ya waye Takoma aikin kamar engine.


*****Fara karatunsu ya Saka sosai Amatu ke sake wayo da Jin damuwan mahaifiyarta da Babu ranarda bata kwana da abin,

Ta bangare daya Kuma Husnah na taimaka mata sosai da karatunta hakama Haydar shima Yana taimakawa Abdul Dan haka abin yake zuwar musu da sauki suna ganewa.

Madame abeeda kuwa jikinta yayi sauki sosai Kuma har lokacin Babu Wanda yasan Menene ciwonta daga ita sai ASH Wanda Shima a qurarran lokaci ya sani Dan haka a yanzu koyaushe cikin ganawa da manyan likitoci yake ana masa recommending qwararrin likitocin Cancer na qasashe da ze Kai Abeeda ayi treating dinta.

Maamah dai a taqaice Takoma chief maid ta gidan Dan kuwa yanzu hatta abincin da masu gidan ke ci itace take girkawa Dan takanasa aka ringa koyar da ita bisa ga umarnin mum Aisha Dan haka tana qwarewa aka sallami chiefs din Dake girka abincin ASH TALBA maamah tayi replacing dinsu Dan haka ta sauya sosai ta sake manyanta ba kaman Abeedan Dasuke Aminai ba ita duk da tanada boyayyan ciwon da Basu saniba jikinta yananan me kyau da Hutu kamar yarinya take sake komawa.


**AmatulMaleek karatunsu yayi Nisa ta sake zama Yan mata Dan ma karatu na cinyeta sosai sbd yanda ta qwallafa masa Rai,
Kamar yanda aka fada idan anga tana ganewa zaa mata jumping to lokacin nayi Akai nata tsallake maimakon tayi Js 2 Kai tsaye Js 3 aka kaita wadda har sunyi jlc tayi SS 1 hakama yanzu tana Ss2 lokacin Husnah tagama harta shiga university.


***Ita rayuwa tana zuwarwa bawa ne a yanda ubagiji ya tsaro masa bawai Kaine kake tsarowa kanka ba,
AmatulMaleek matashiyar budurwar Dake tasowa a lokacin,
Wata irin rayuwa ce take gudanarwa ta kadaici da kamun Kai a cikin gidan dasuka Dade da zama 'yan gida Kokuma tace gidan da suka Dade da zama 'yayan me aikin gidan Dan kuwa ayanzu ba 'yar uwa ko Aminiyar madame ake kallan maamah ba matsayin shugabar masu aikin gidan ake kallanta,matsayinta Daya da masu aikin,guri Daya da masu aikin gidan suke rayuwa,abinda ake bawa masu aikin gidan shi ake Bata,bambamcinta da masu aikin gidan shine Bata karban albashi hakama dauke ake da nauyin karatun yayanta Wanda zata iya qarasa rayuwarta a wannan wahalar sbd 'yayan su samu gobensu me kyau duk da har Koda yaushe duk abinda takeyi na wahala da abinda ake mata a gidan bata taba Jin haushi ko damuwa ba sbd Dan Allah takeyi dakuma kaunar datakewa Abeeda wadda itama zata iya dawwama a wannan wahalar datake mata batareda taji komaiba.

AmatulMaleek zuciyarta ta taso ta Ginu da damuwa da Jin radadin irin rayuwarda mahaifiyarta ke ciki wadda a yanzu ko tausayi Babu bare kauna a yanda yake treating maamah a gidan,
Hatta dawainiyar Husnah data Haydar itace takeyi Wanda Hakan ke sake lullube zuciyarta da tausayin mahaifiyarta wadda har lokacin zuciyarta me tsafta ce Bata Jin qyashi ko gazawa.
#MAMUH#
#MERAH HERBS


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


11
Rayuwa a Mansion din ASH TALBA tamkar rayuwa ne a wata aljannar duniya Amma Kuma ga AmatulMaleek ba Hakan bane sbd halinda mahaifiyarta yake ciki ya danne duk Wani farin cikin datake samu a gidan,
A tsawon shekarun da suka share a gidan kowa yasamu ci gaba ya sauya daga sanin da Akai masa,sauyi kuma me girman gaske Amma Banda maamah wadda ta koma tsohuwar qarfi da yaji ga ciwon kirji Dana jiki Dana qafafu da Baya Wanda kowanne dare Bata iya bacci me dadi,
Ita kadaice tasan halinda mahaifiyarta ke shiga kowanne dare,
Maamah a Koda yaushe boye mata gajiyawarta da ciwonta takeyi sbd kada ta sani ta nuna damuwarta Dan haka maamah din ta zabi ta ringa hadiye damuwarta da ciwon dayake cinta sbd ganin AmatulMaleek na ajiye kowacce damuwarta a ranta kada Hakan ya taba rayuwarta da karatunta Amma Kuma abinda Bata saniba shine hakan ya Riga ya zaunu a zuciyar Amatun ta yanda take musu kallan Yan cin alfarma da jiran komai akashe abasu kaman yanda Husnah ke fada mata tin suna Yara.


Su 'yayan me aikin gidan ASH TALBA ne Kuma bazasu taba tashi daga Hakan ba shine kalmomin da mum Aisha akoda yaushe take fadawa maamah a gabansu tin suna Yara haryanxu dasuka girma Hakan Bai taba canzawaba.

Ko mum Aisha da Husnah basa yawan tinatar dasu su din da matsayinsu Hakan a bayyane yake ba buqatan tini sbd haryanxu data zama budurwa Abdul yafara zama Dan saurayi a daki Daya suke su da mahaifiyarsu anan suke rayuwarsu.,
Jimawa sukeyii baa dinka musu sabuwar sutirar rayuwa ba kayanda su Husnah suka cire su ake Basu,
Basa shiga sashen madame Abeeda Sai Idan aikine ya kaisu Wanda tinda ta girma take kamawa mahaifiyar aikin gidan,
Har gobe abincin dasuke ci da Wanda mutanen gidan sukeci akwai bambamci,
Dan wannan matsayin dasuke Basai an tinanar dasu matsayinsu ba a cikin ASH TALBAs Mansion.

Abdul ma duk da kasancewarsa namiji har cikin ransa Yana tausayin mahaifiyarsu da wahalar datake sha Amma Shima kusan Amatun ne su dauko halin maamah na danne abu a zuciya tareda nuna ba komai bane Amma kusan Shima Yana taimaka mata da wasu ayyukan duk Yana gida kamarsu aikin kitchen Dan dole daga shi har Amatu sun iya aikin girki sbd taimakawa maamah.

Duk tsawon shekarun da sukai a gidan Babu abinda ya taba kaisu bangaren Mai gidan wato daddynsu Husnah sbd sam baa zuwa gurin hakama duk ganinda sukai masa daga nesa ne tinda ba mazauni bane sosai hakama Koda Hange Babu abinda ya hada bangaren masu aikin gidan da bangarensa bare su samu kusanci dashi.

Husnah anan Abuja take karatunta Dan haka wayewarta ta yayan masu kudin qasa suke bayyane gata batada hakuri ko saukin kai 'yar Kai tsaye ce Bata iya boye zance ko maganar Dake ranta ba shiyasa da dama ake mata daukan me wuyar shaani,
Kusan Tako wanne bangare halayenta Dana AmatulMaleek sunyi hannun Riga Dan ita kanta Husnah duk yanda taso ganin bacin ran Amatu ko fushinta Bata taba iya Gani.

Shaquwan AmatulMaleek da Haydar wata irin kaunace a tsakaninsu me girma Dan kuwa jinta yakeyi a ransa fiyema da Husnah hakama itama Amatu a cikin familyn TALBAs gaba Daya Haydar shine Wanda tafi so fiyeda kowa da komai na gidan bayan Maamah da Abdul Dan ma kusan yanda take Jin Abdul haka take jinsa a ranta.



*******
Ayau gidan ASH TALBA sun tashi da sabon tashin hankalin dawowan ciwon Madame abeeda wadda haka kawai aka wayi gari ta sake shiga mummunan halin data taba shiga kwanaki.

Babbar rashin sa'ar da akaci shine ASH Baya Nan Dan haka su mum Aisha suka kira ambulance akazo aka dauketa hankalin gaba Daya jamaar gidan a tashe aka tafi da ita.

Bayan antafi da ita asibiti lokacin dukansu suna makaranta Dan haka maamah da mum Aisha ne dole a asibitin.

Wayar ASH da mum Aisha keta kokarin kira Bata samu ta sake Saka Kiran Amma dai still Bata samu Dan haka suka zauna jiran tsammani.

Har yamma suna asibiti Kuma har lokacin baa samun wayar ASH Dan haka likitocin basuda zabi bayan sanarwa mum Aisha Cancer ce da Madame abeeda Kuma takusa kaiwa last stage.

Shiru mum Aisha tayi idanuwanta akan likitan Daya gama bayanin cikin Hausa da turanci sbd bahaushe ne.

Maamah kuwa dafawa tayi Takoma zaunen data miqe sbd nauyin da qafafunta sukai mata suna Gaza daukanta.

Shiru sukai dukkaninsu Babu Wanda yake motsi sbd tinanin dasukai Nisa a cikinsa na ba zata da tashin hankali musamman maamah da hannuwanta duka dauki rawa ahankali
Ta damqesu sbd rawar da sukeyi zai iya haifar da matsala babba gareta musamman ciwonta datakeji zuciyarta na Neman Dena bugawa.

Cancer" mum Aisha ta furta ahankali tana Dan share guminta Dan duk abinta tana tsoron mutuwa haka Kuma duk lokacinda aka ambaci Cancer ga mutum Babu abinda suke fara hangowa akansa sai mutuwa a kusa kusa.

"Innalillahi wainna ilaihirrajiun" maamah ta fada ahankali tana rintse idanuwanta dasukai nauyi suna son hawaye Amma sunma kasa haduwan.

Mum Aisha a gurin ta ciro wayarta Babu Wanda ta fara kira sai 'danta da kusan Babu abinda suke boyewa juna,kaf duniyarta shi kadaine Wanda takeso tsakaninda Allah da gaskia Dan haka ta tsaya akan karatunsa Dan yayi arzikin Daya kusa na ASH TALBA idanma har bazai fisa ba kenan.

Ringing wayar tasa takeyi harta katsae Bai daga ba Saida ta sake kira karo na biyu jikinta na rawa ta isar masa da zancen sbd damarsu tazo ta dawowansa gida ya baro turai sbd tabbas hankalim ASH TALBA zai tashi daga dukiyarsa da harkokinsa ya dawo Kan Abeeda sbd mahimmancinta da matsayinta yafi na komai daya mallaka so yanzu ne NAUFAL dinta zai samu matsayi da Daman shiga cikin huldodi da dukiyar ASH EMPIRE.


****
Madrid,SPAIN.

kwance yake akan lafiyayyan gadon dakinsa acikin gidansa da babu abinda ya rasa na Jin dadin rayuwa da Hutu,
Dagashi sai Men's tight Wanda baida bambamci da Babu komai a jikin nasa sbd kusan daga saman ya zame kadan hakama ya kamasa sosai ta yanda kana ganin shape na komai nasa.,

Fatar jikinsa Dake shining na qyallin Hutu da kyan fatar duk a Bude Dan bayan tight din baida komai a jikinsa,
Gefensa wata lafiyayyar blown skin mace ce da itama Babu komai a jikinta sai pant da bra wadda itama kusan a zame take,
Bacci sukeyi hankali kwance Wanda ke nuni da idanma da daddare idanma da safen to sungama mu'amalar mace da namiji ne kafin baccin.

Ringing wayarsa keyi duk da tana silent Amma vibration din na tashi sosai harya fara jinsa cikin baccinsa Dan haka ya Dan motsa Yana Bude idanuwansa ahankali daidai lokacinda Wani Kiran ya sake shigowa.

Akan fuskar sabuwar budurwarsa Dake kan jikinsa idanuwansa suka sauka ya Dan yamutsa fuska ahankali tareda janyeta daga jikin nasa Yana miqa hannu inda wayarsa take daidai kira na uku na sake shigowa.

Qaramin numfashi da tsoki ya Dan sake lokaci Daya kafin ya duba Mai Kiran yaga sunan Mum dinsa baro baro.

Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi tareda tashi zaune Yana zamowa bakin gado ya sauko da qafafunsa qasa ya miqe daga gadon Yana daukan wayar Kai tsaye tareda dorawa kunnensa ya nufi hanyar fita dakin Yana cewa

"Yes mum,good morning"

Kallan time mum Aisha din tafara yi gana su anan din ba safiya bane Amma dai koma yayane bashine matsalarta ba cikin kulawa da 'yar kamewa tace

"Morning,ka tashi lfy?
Ya karatun??

Ruwan dumi Daya zuba a cup ya jefa lemon aciki ya Kai bakinsa Saida yasha sosai kafin ya amsa da cewa

"All good mum,
Yaya Su Husnah and Aunt Abeeda?

"Husnah lfy kalau Aunt din taka ce dai take kwance asibiti batasan inda kanta yake ba."

Shiru yayi Yana ajiye cup din hannunsa ya nufi Daya daga tsadaddun kujerun palonsa ya zauna Yana cewa

"Meya sameta mum?
Wani abu ya faru ne?
Meyake faruwa?

Katsesa tayi da cewa

"Cancer ne da ita duk tsawon lokacin Nan Amma ba Wanda yasani sai yanzu..

Katsesa Naufal din yayi cikin mamaki da cewa

"Uncle ASH fa? Ya sani?

"Bansaniba ko ya sani Amma dai yanzu besan muna asibiti da ita ba bana samun wayoyinsa duka,
And duka bayan wannan ka saurare ni da kyau kaji......

"Heyy baby good morning" ...shine abinda mum Aisha taji daga cikin wayar tayi shiru zuciyarta na yin nauyi sbd bata buqatan kowanne irin bayani ta sani mace ce a tareda Naufal din a cikin irin matan dayake kawowa gidansa suna kwana,

Babban baqin cikin mum Aisha a duniya biyu ne zuwa uku,
Na farko dukiyar ASH TALBA data tsone idanuwanta ta Hana zuciyarta sukunu tsawon shekarun datake zaune a gidansa cikin dukiyar tana yanda takeso da ita hakama 'danta yake yanda yakeso da rayuwarsa tamkar shine magajin ASH TALBA din,

Na biyu shine Neman matan da Naufal yekeyi kamar bunsuru Sam Baya iya kwana a rayuwarsa batareda ya kusanci mace ba
Duk ranarda ya kwana biyu batareda mace a tareda shi ba to kamar zai zauce yake jinsa shiyasa gaba Daya Baya iya zama Nigeria sbd Jin Yana aikata irin wannan zinar haka kaman abinci zai iya Saka ASH TALBA nesantasa da ko inda zaibi ya wuce bare Kuma sakashi cikin dukiyarsa dasuke fata tin shekara da shekaru Shida mum dinsa.

Abu na uku kuwa shine Haka kawai takejin tsana da rashin Jin nutsuwar zaman maamah da 'yayanta a cikinsu sbd maamah din tamkar kariya ce ga Abeeda data Dade tana Jin qyashinta da kishinta ga Dan uwanta dayaqi qara ko kallan wata macen bare Wani tinanin qarin aure da babusa a tinaninsa ko rayuwarsa ma gaba Daya.,
Zuwan maamah yasaka duk yanda Husnah take renanta Kuma tarbiyarta harma da yanda takeson ta zama sbd amfani da ita gurin ASH sosai ya ruguje sbd komai rashin saukin kan Husnah da zafin kanta tana kaunar maamah da gaskia Kuma kamar yanda maamah din ke tsananin sonta kaman AmatulMaleek da Abdul, Husnah Takoma kusancinta da maamah da shaquwarta da ita yafi na kowa Dan haka Sam yanzu sedai ayiwa maamah duk abinda zaa mata na cin zatafi ko aikin wahala Amma baa iya canza matsayinta gurin Husnah da zuciyarta.
Wanna dalilin ne yasaka taji tayiwa shigowarsu Maamah rayuwarsu tsana me karfi.
#MAMUH#


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


12
YAR UWATA TSAYA KIJI KAYANDA SISTER NA KE SAYARWA BAZAKI RASA ABUNDA KIKESO BA A CIKI IN SHA ALLAH 🙏💪

Sis Kinason siyen maganin Kara girman hips da breast kodai rama ce damuwarki❓kinaso kiyi kiba ki ciko kiyi kyau KO KUMA KAYAN GHT KIKESON KISIYA Na gyaran skin fatarki tayi kyau❓ko maganin infection ❓asthma ❓ ulcer ❓ rashin haihuwa ❓ hepatitis ❓ diabetes ❓ ko Kuma kiba ce da tumbi suke damunki❓ to tanada magani da yardar Allah ❓ga group link din sister na🥰 kiyi joining 👆👆👆👆Zaki samu fiyeda yanda kikeso Kuma kayanta nada sauki ga kyau tested and trusted 👍💪

Idan bakyason shiga group kiyi saving number dinta👉 https://wa.me/+2349038090328 👈kimata magana kice kinyi saving itama zatayi saving taki🥰 zaki godemin na hadaki daita danayi in Sha Allah 🤗



**********
Naufal dayaji mum dinsa Tayi shiru batace komaiba ya tabbatarda taji maganar Cynthia haka Kuma yasan yanda ta tsani mace ta rabesa sbd sam Bata masa shaawan aure batareda ya tsayu a cikin dukiyar data tsaya mata a zuci da ido Tim kafin ta haifesa ma.

Ajiyar zuciya ya Dan sauke a boye Yana basarda abinda mum din taji Yana cewa

"Mum ki bari zan kira anjima idan Aunt din ta farfado na mata ya jiki and I will call the grt ASH TALBA Shima na masa sannu da jikin nata"

Numfashi me zafi mum din ta hadiye randa duk ya gama Baci da daukan zafin halin Naufal din Dan haka Kai tsaye ta kashe wayar batareda ta amsa shi ba Dan kuwa zuciyarta zata iya kumbura a gurin.

Tana aje wayar ta koma dakin ta Tararda maamah data sha kuka Mai tsima zuciya da tausayin 'yar uwarta datake Jin inama wannan kaddarar Bata sametaba Amma ko yanzu ciwo ba mutuwa ba.

Cikin dacin zuciya mum Aisha ta nufi gurin zama ta zauna tareda jefa wayarta cikin lv handbag dinta Dake gefenta aje tana Jin zuciyarta na kasa hucewa Dan haryanxu Naufal ya kasa girman burin dataci akansa kwata kwata halin ubansa yayo bayan mace Babu abinda yake gabansu kamar Babu wata rayuwar bayan ta kusantar mata.

Tsoki data ringa saki Akai akai batareda tayi magana ba ya Saka maamah da idanuwanta sukai jajir dagowa ta kalleta itama batareda tace komai din ba.

Sai dare sosai suka dawo gida kuma har suka dawo Amatu batai bacci ba tana jiran dawowarsu cikin damuwa da tausayin Madame abeeda wadda ta San ciwon

Please Login or Register in order to submit comment