Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dining.

Dawo da kallanta tai kan Maamah din cikin yar kulawa tace

"Asmau meye kikeson ci??
Me zaa dafa Miki kici a cikin gaggawa?

Dan dagowa Maamah tayi tana kokarin Hana damuwa da sanyinta bayyana ta saki Dan numfashi tareda yaqe ta Bude Baki tace

"Kowanne irin abincin ma yayi basai sun wahala ba"

Juyawa khaltume tayi da kallanta kan Madame dinsu tana jiran umarnin abinda zaayi din.

Abeeda Bata juyoba ta kalleta tace

"Kije koma me Akai a ajiye mata ta taso taci batareda Bata lokaci ba."

Murmushin yaqe Maamah ta sauke tana dagowa ta zubawa Abeedan Idanuwanta cikin kulawa da ganin yanda itama Abeedan ta fada sosai tayi Wani irin haske kamar na Wanda beda jini ko kadan.

Numfashi ta sauke kafin ta Bude Baki cikin kulawa tace

"Abeeda Yaya muka sameku?
Yaya Husnah da Haydar?
Duk suna lafiya?
Yaya labarin su hajiyar porthcrt?kowa lafiya dai ko?

Numfashi Abeeda ta sauke kawai fuskar Asmau take kalla wadda magana takeyi Amma bakin dayake bushe da wuyanta ne suke kashe mata jiki Dan haka Bata iya Bude Baki sosaiba ta gyada Kai ahankali cikin sanyi tace

"Kowa lafiyansa kalau,
Asmau meya sameku haka keda yaran kuka koma kamar wainda ke rufe a kejin wahala?
Meyake faruwa ne?
Kuma cikin qunci da wahala ne?
Bakwa samun abinci ne?
Andena Kai Miki abincin da ASH yasa aringa kaiwa duk wata ne?

Shiru Maamah tayi tareda Dan sake sakin murmushin yaqe tana cewa

"Ana kaiwa kinsan gidan taro dakuma rayuwar kauye baka samun abu ka ringa cinyewa Kai Daya Se iyalinka,Idan ankai ana bawa kowa ya Dan Saka albarka,Allah dai yaci gaba da biyanki keda Mijinki har karshen rayuwarku,ai Kunata kokari....

Katseta Abeeda tayi da cewa

"Asmau bayan yunwa wane masifar kuke ciki haka da kika koma kaman wadda take kwance tana jinya??
Asmau Kin ganki kuwa?
Kinga 'yayanki kuwa?

Sake sauke numfashi maamah tayi tana Dan son Hana kanta da zuciyarta bayyanarda abinda zai damar da Abeedan Dan haka ta sauya tambayar ta Abeeda da jefa mata tata tambayar idanuwanta akan Abeedan tana cewa

"Yaya maigida ASH TALBA? Yana lafiya?
Yakuma akaji da hakurin rashin Alhajin??

Numfashi itama Abeedan ta saki sbd sanin zurfin ciki da iya shanye damuwa da duk abinda ya wuce na Asmau Dan haka tasan ba komai zata fada mata ba ayanzu din sai kawai tayi Baya ahankali ta gyara zamanta a lallausan Luxury kujeran Dake palon nata tana cewa

"ASH lafiyansa kalau yau da safen Nan yayi tafiya Dan Daman rasuwar Nan ta tsayar dashi,
Alhaji kuwa lokacin yayi Se fatan Allah yayi masa Rahama da samun Jin qansa.

Shiru sukai dukkaninsu kowanne zuciyarsa a sanyaye Banda Abeeda Dake jin bazata iya fadawa Asmaun damuwarta datai niyaba a duk randa suka Hadu sbd Bata taba tinanin ganinta a wannan mummunan halin itada yayantaba kamar wasu gawar dataqi Rami.


Ita Kuma maamah Jin tayi itama jikinta na sanyi tareda Jin nauyin fadawa Abeedan damuwarta sbd kada ta damu sosai gashi da alama Sam rayuwarta da alama batasan meye ma damuwaba Dan haka bazata lalata mata komaiba da tata damuwar zasuyi kwana biyinsu su koma salin alin zata bar damuwarta a cikinta ta duqufa da yiwa yayanta addua.


Abincin da akace a jera mata khaltume ta gama jerawa ta matso ta sanar musu angama jerawa.

Kallan maamah Abeeda tayi tace mata taje taci abinci tukuna.

Miqewa maamah tayi ta nufi inda abincin yake a Jere cike da table din da tasan zamansa yafi karfinta Dan haka sai kawai ta Kalli khaltume Dake ajiye kulan farfesun qaton catfish akan dining cikin nutsuwa da mutintawa tace bazata iya cin abincin anan ba akaita kitchen ko can dakin da aka saukesu taci.

Abeeda Dake waya cikin nutsuwa da Wani irin sanyi na Wanda Hutu kawai ya sani batasan me suke fada ba har khaltume din ta fita da Maamah din suka dauki kayan suka fito dasu har zuwa sashen masu aikin.

A lokacin AmatulMaleek tayi bacci hakama Abdulhameed Amma shi suna shigowa dakin ya Farka Yana ganin maamah din ya tashi zaune Yana kallanta tareda matar Dake bayanta Yana Jin son komawa gida gaba Daya na shigarsa.

Ajiye kayan sukai a qasa gefen Dan madaidacin gadon Dake dakin tayiwa khaltume data juya zata fice Godia sosai cikin Nutsuwa.

Bayan ajiye kayan da ficewar khaltume kallan Abdulhameed maamah tayi tana qarasowa gadon dayake kwance shida AmatulMaleek ta miqa hannu ta fara taba AmatulMaleek taji jikinta zafin Kai a sauka sosai ba laifi take ta sauke ajiyan zuciya me sanyi kafin ta Maida kallanta na Abdulhameed Shima ta tabasa taji ba zafi Sam Kwata kwata a nasa jikin Dan haka ta kamosa ya sauko gadon Yana kallan kayan abincin Dake ajiye kasa Yana cewa

"Maamah yaushe zamu koma gida?"

Zaunar dashi tafara yi a qasa kafin itama ta zauna tana cewa

"Kwana biyu zamu insha Allah mu koma,
Kaci abincin dai tukuna kafin Amatu ta tashi itama taci."

Doya da dankalin turawa ne da aka cakudasa da kwai dasu pepper sai kamshin spices yakeyi.

Wani mugun yawu me kaurin gaske Abdulhameed din ya hadiye harda ita Maamah din Amma dayake sunada dangana sai jikinsu Bai Wani dauki rawa ba.
A natse ta zuba musu kafin ta sake Bude dayar kulan sukai arba da farfesun kifin Shima ta zuba musu duk a cikin guri Daya sbd kada su Bata plates din dasuke qal tasan Se sunyi tsada,
abinda ma ita Bata saniba shine ko spoon da matar gidan take amfani dashi baa bari Koda wasa yazo bangaren masu bare kayan abincinta Wanda wainnan din daga yau sun tashi daga kayan cin abincin madame Abeeda sedai Kuma a ajiyesu Dan baqin da basuda wani mahimmanci,
Shi oga kwata kwata kuwa Sam bama kowa ke taba kayan da ake masa amfani dasu ba sbd Wani irin qyanqyaminsa da tsaftarsa data Baci tayi yawanda idan Yana gari aikinsa na musamman ne da ake taka tsantsan da kiyayewa dashi.

Abdulhameed duk da Yana cikin kulaficin son komawa gida a take harma da tsoron inda yaga sunzo din Amma sosai ya saki cikinsa ya ringa cin cimar da Bai taba cinta arayuwarsa ba Dan kuwa baitaba ganin ko dankalin turawa da idanuwansa ba bare ci hakama doya har gwara kifi suna Gani a masu siyarwa na kauyensu da masu zuwa ruwa su kamo.

Dadin dahuwar wadda take ta musamman Dan kuwa duka masu aikin gidan wainda suke da karatu akan aikinsu ake dauka Dan haka masu girkinsu komai nasu kamar a 5star restaurants kake,
Hakama masu aikin tsafatace gidan Suma kusan sai wainda suka samu training me kyau ake dauka sbd kusan gaba Daya rayuwar taurawan datake cikin ASH TALBA tagama kama iyalinsa da kusan gidan komai a daki daki akeyinsa kan tsari da rashin tarkacen da zai damesa.


Ita kanta maamah taci abincin sosai ba laifi suka sha Wani homemade drink da ko zaa kulla musu bomb ya watse dasu basusan dame dame acikinsa duk da fruits ne zalla Amma dai Sam basusan meye shi din ba sudai sunci Kuma sun koshi.

Suna gamawa ta rabe kayan gefe sbd na Amatu da suka rage Mata.

Toilet dayake dakin suka shiga
Dayake ta iya amfani duk da irin wainnan abubuwan sbd tasowa gidan masu arziki Dan haka Bata manta yanda ake amfani da wasu abubuwan ba da yawa.
Wanke musu hannuwansu tayi nata Dana Abdulhameed daketa lashe hannun.

Sabulun tasaka ta wanke masa hannu da kyau itama ta wanke nata kafin ta goge musu bakinsu suka fito tana ce masa ya koma yayi bacci kafin azahar ta qarasa yi ya sake warwarewa.

Hayewa yayi gadon Yana cewa

"To Amma bazaki fita koina ki barmu anan ba ko?

"Babu inda zani Ina Nan zaune harku tashi Nima Dan rintsawa zanyi kafin lokacin yayi."

Yana Jin Hakan ya sauko daga gadon Yana cewa
"To zan kwanta a gurinki"
#MAMUH#
#ASH TALBA
#LA HOT
#FRIENDSHIP
#LIFE
#AMATULMALEEK
#NAUFAL TALBA


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
YANCI DA RAYUWA
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at๐Ÿ‘‡
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest #


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


6
A qasa kan tiles Maamah tayi kwanciyarta kan daddumar sallah tareda Abdulhameed Daya shige jikinta tin tana jiran farkowan AmatulMaleek har bacci ya Dan fixgeta itada Abdulhameed din.

So biyu ana Aiko khaltume dubasu ko sun tashi Amma Basu tashi ba Kuma Madame tace kada a tashesu Dan haka aka barsu sukai bacci sosai batareda Maamah din ta san ta dauki lokaci sosai haka tan baccin ba.

Sanyin tiles ya dayayi musu yawa ya farkar da ita dole lokacin karfe biyun Rana harda minti talatin da takwas Dan haka cikin sauri ta tashi tana janye Abdulhameed Daya cukuikuyeta sbd sanyi ta miqe tsaye tana kallan gadon Taga AmatulMaleek din itama tana motsawa alamar tashi zatayi Dan haka toilet kawai ta wuce Tayo alwala ta fito tayi sallah tana idarwa Amatu na farkawa Dan haka itace ta kamata da kanta takaita toilet tabarota.

Ita kanta Amatu ta Dan iya aiki da wasu abubuwan bandakin sbd zuwan da suka taba yi tafara Dan wayo lokacin.
Fitsari tayi Tayo alwala itama ta fito ta tsaya gefen Maamah tayi sallah tana idarwa Abdulhameed na na tashi daga baccin Shima.

Da sauri Maamah ta miqe ta rakasa toilet sbd fitsarin dayake cewa ya matsesa.

Bayan fitsari harda zawo yayi sbd abincin Daya Dan fara tabashi kasancewar ciki Bai Saba da wannan dadin ba,
Fitowa yayi bayan Maamah ta wanko masa hannuwansa da kyau da sabulu
Gefen AmatulMaleek ya zauna Yana kallan kayan abincin Dake gefen ajiye yafada mata nata ne sunci sun rage Mata tin dazu.

Kallansa Amatun tayi bayan ta Kalli kayan abincin Amma Bata motsaba sbd ba Maamah ce ta Bata ba.

Maamah kuwa toilet din tahau wankewa sosai sbd kada su lalata musu guri Dan tasan tsananin karfin tsaftan masu gidan sbd duk Wanda ko kalilan sani yayiwa ASH TALBA yasan inda qazanta take da inda yake akwai Nisa me yawa da zurfi.

Sosai ta Saka karfinta ta wanke toilet din tayi masa fes ta fito tana kallan Amatu Dake zuru tana kallan Abdulhameed Dake ta fada mata dadin abinda suka ci din tana bacci.

Wani sanyayyan murmushi maamah tasaki tana qarasowa fuskarta a sake ta kallesa tana cewa

"Gashi Kuma bazaka sake ci ba yanzu sbd yafara lalata Maka ciki."

Dariya yayi Yana maqale kafadarsa Yana cewa

"Zan sake ci mana ai idan munkoma bazan sake ci ba shikenan."

Daga Maamah har Amatu da batada karfin jikinta qaramar dariya suka saki sbd yanda yake matse da a dauko abincin.

Maamah ce ta janyo abincin bayan ta zauna itama a tareda su qasan.

Bude abincin tayi da kanta ta zubawa AmatulMaleek komai kaman yanda suka hade tana cewa

"Ki cinye tas sbd Kinga ba karfi jikinki ta yanda zaku samu kuzari sai muje akaimu ku gaida mommynku Abeeda harma da sauran mutanen gidan."

Gyada Kai kawai AmatulMaleek tayi tana Saka hannu a abincin sbd itama ya shiga ranta sosai duk da batada kwadayi Amma shi abinci irin wannan basama ganinsa bare.

Abdulhameed ma dole tareda Amatun ya sake cin abincin itama Maamah hannu ta Saka sukaci abincin tare su uku Abdul naci Yana tambayar AmatulMaleek idan tanajin dadin dayake ji a abinda sukeci din.

Dariya Amatun ta Dan ringa yi masa tana cewa

"Maamah wlh 'dan Nan naki duk ya haukace sbd cin abinda be taba ci ba."

Itama Maamah din yar dariya tayi tana cewa

"Kyalesa yaci ai na kwana biyu ne muna komawa kaman yanda ya fada shikenan."

Cikin kulawa da tsananin so da kaunar juna sukaci abincin su uku suna Dan magana Sam sama,Maamah kusan duk Rabin cin abincin nata su take gyarawa kidin tana ja ye musu qashinsa abubuwan data San bazasu iya ci ba tana musu fira cikin kulawa da kaunarsu.

Suna gamawa wannan Karan su ukun suka shiga toilet suka wanko hannuwansu Maamah na fitowa ta tattara gurin tareda kayan ta fito dasu ta nufi hanyar kitchen tana isowa khaltume da Masu aikin abincin Dake girkin dare kallanta sukai tareda karban kayan hannunta.

Kallan khaltume tayi tana cewa Ina zata wanke kayan saita wankesu da kanta.

Karban kayan khaltume tayi tana cewa ta barshi kawai.

Kasa tafiya maamah din tayi sai data taimakawa khaltume gurin wanke kayan kafin ta koma.


Zama sukai a dakin shiru daga ita Se su Amatu suna Dan firarsu sama sama sbd daga Amatun har Abdulhameed sun warware kamar ba'a nade aka shigo dasu ba ba lafiya sosai Daman yunwa ce da wahalar hanya Se iska da sanyin kwanan Tasha.

Har yamma Babu Wanda ya shigo inda suke aka nemesu Suma haka sukai zamansu.

Koda Akai sallan magrib Wani abincin aka sake kawo musu Basu ci ba sai da sukai sallah tukuna suka zauna sukaci a plate Daya su dukansu dayake wannan Karan farar Basmati rice ce da brown chicken stew wadda Babu Mai sosai acikinta sbd lafiyansu da suke kulawa da ita sosai a gidan.

Kazar Dake cikin miyan zata Kai guda harma da Rabi Kila Dan kuwa duk yanda sukaci ta Basu cinyeba hakanan suka tattara kayan Maamah dince ta sake fita dasu takai kitchen ta dawo.

Har Akai ishai baazo antafi dasu can gurin masu gidan ba sbd umarnin da Abeeda ta bayar na a barsu suyi kwana biyu suci su huta yanda ya kamata kafin su fara Dan zagayawa sbd sam Bata kaunar ganinsu a yanda suke din.

Da daddare maamah barwa Abdulhameed da Amatu gadon tayi sbd baida Wani girman da zai daukesu su uku Dan haka tayi kwanciyarta qasa tabarsu a saman sukai bacci.

Bacci sukai sosai Wanda suka jima Basu irinsa ba sbd samun gurin baccin me nutsuwa ba sauro ba komai Dan haka har Akai asuba Basu saniba Saida gari yayi haske Maamah ta Farka tana tashi zaune kafin ta miqe ta nufi toilet Tayo tsarki da alwala tana fitowa kafin ta tada sallah ta tana Amatu tana Kiran sunanta a nutse.

Cikin baccin dabe saki Amatun ba ta Bude idanuwanta masu Dan girma tana cewa

"Maamah baccin be sakeniba"

"Tashi kiyi sallah Se ki koma tinda Babu aikin da zamuyi anan din."

Sake Dan juyawa tayi tana Bude idanuwanta tareda Kai hannuwanta duka biyu tana ture kafafun Abdul Dake kanta cikin Wani shegen mugun bacci Wanda ko a gida haka suke kafin safe ba qaramin shuri takesha a gurinsa ba sbd Mayen baccinsa.

Saukowa tayi gadon tana murza idanuwanta ta nufi bayin ta shige tana Bude idanuwanta dakyau sbd kada ta zame.

Koda ta fito Maamah tagama sallah tana zaune tana Dan kokarin tada Abdul Shima cikin kulawa da rarrashin ya tashi yayi sallan.

Sallah tayi tana idarwa itama ta zauna gefen maamah din wadda da kanta takai Abdul toilet yayo fitsari da alwala,
Inda ma Allah yayi mata babban rufin asirin dukkaninsu yayan nata Babu me fitsarin kwance da batasan ya zatai ba.

Bayan sun gama sallah Amatu ce ta kwanta qasa Maamah din Kuma da Abdul suka koma kan gadon suka kwanta dukkaninsu baccin ne ya sake daukansu hankali kwance.


Se qarfe Tara aka kawo musu abincin breakfast Wanda Tintini Daman sun tashi har sunyi wanka sbd kada Azo a taddasu da kowacce irin rashin tsafta.

Ayau ma lafiyayyan breakfast suka sake karyawa dashi Wanda kusan iri Daya Dana jiyan ne sedai yau tareda Wani Irin tea me shegen kauri Daya Saka Abdul ringa fadar akwai Madara sosai a cikin shayin.

Haka suka sake wuni guda Babu Wanda yazo ya tafi dasu sedai abincin da aketa kawo musu da lokacin cinsa yayi.

Bata damu da cewa Se sunje gurin Abeeda ba sbd tasan tana sane dasu Kila wata hidimance ta riqeta Batada lokacin ganinsu yanzu.

Abdul kuwa Jin yayi shikam yafara son gidan sbd dadin dasuke ci Kuma basa komai bayan kwanciya da Shan AC Wanda sanyinsa yafara taba Amatu ita Dan Sam Bata son sanyi duk da tana yarinya yanzu ne ze tabata.


****Kwanaki kusan hudu masu kyau aka Basu suka huta yanda ya kamata bayan ci me kyau da sha me kyau Babu abinda suke Samu,
Hatta yar suturar sakawa anbasu dukda ba masu yawa bane Amma sukam a gurinsa me yawan ce,

Abdul sosai a yanzu yaji bayason su koma gida Dan kuwa shi ko wannan ci a koshin da abinci mekyau aka barsa ganin yakeyi duniyarsu ta gyaru Dan haka tini shi Kam ya fara kumatun Kwana biyu,
Amatun ma ta Dan yi kumatun duk da batada jikin kiba ko kadan Amma dai ita cima me kyau da wuri take nunawa,
Maamah kuwa sosai ta dage da kulawa da inda aka ajiyesu din sbd karsu lalata inda aka ajiyesun kafin su tafi hakama duk takai kayan abincinsu kitchen seta Dan taimaka musu da Wani aikin sbd Bata Saba da zama Babu aikin komai ba Jin takeyi duk ba dadi sbd su Basu Saba da Hutu ba da wahala suka Saba.


Ranarda suka cika kwana biyar da zuwa aka Aiko khaltume ta tafi dasu cikin asalin gidan inda masu gidan suke,
Kai tsaye sashen Abeeda aka nufa dasu khaltume na gaba suna biye da ita.

Abdul na hannunsa na riqe cikin na maamah sbd kada yanda yake kalle kalle,
Amatu kuwa tana gefen maamah din itama tana Dan kallan koina.

Babban palon Abeeda ko yau aka nufo dasu suka zauna 'yayanta na gefenta matse da ita suna Dan kallan makekiyar flat screen tv din Dake aiki a palon ba murya sosai.

Abdul sai taba Amatu yakeyi Yana nuna mata abubuwan da duk idanuwansa suka Gani na mamaki ita Kuma tana gyada masa Kai sbd batasan me zata ce masa ba.

Basu Wani jimaba Abeedan ta fito fuskarta dauke da murmushi me yalwa da kulawa tareda kauna a Fili tana kallansu ta qaraso sanye cikin Wani milk dry lace Daya gama bayyanar da kudinsa sbd yanda take a kwance kamar cotton.

Zaunawa tayi idanuwanta dasuka fada suna kan AmatulMaleek wadda gabaki daya Babu abinda ta baro na mahaifiyarta Asmaun sai haske data Fi Asmau Amma komai na maamah dinne.

Manyan idanuwanta farare ta kalla tana mamakin Irin kamannin Asamun da Amatu ta koma sak,
Numfashi ta sauke ahankali tareda sake fadada murmushinta da kulawanta tana miqa hannunta ta Kila Abdul Wanda yake kallanta Amma ya kasa zuwa sai maamah Daya kalla wadda cikin murmurshi ta gyada masa Kai tana cewa

"Jeka ka gaida mommyn UK da kaji Amatu na fada"

Amatu kuwa cikin nutsuwa da girmamawa itama ta Bude Baki ta gaidata cikin Dan sakewan fuska da ganin mommyn.

Amsawa tayi itama tana Jin kaunar yaran tace

"Asmau AmatulMaleek ta fara zama budurwa Ashe,
Allah yasa dai kada iyayen Nan nasu Maza suyi tinanin yimawa auren kauye da wuri sbd bazamu yarda ba Sam da wannan dabiar ta kauye"

Dariya mara sauti maamah tayi tana cewa

"Toh ai sedai ace Allah ya tsare Amma Kam Kila Hakan zaa samu"

Dan kame fuska Abeeda tayi tana sake qarewa Amatun kallo Tana cewa

"Sam wannan bazai yiyuba sbd zasu kashe rayuwarta ne,Ina Sam Sam,wannan ai rashin hankali ne da cutatar da rayuwar Yara qanana sbd wasu shekarun nasu da gaske Basu kaiba."
#MAMUH#
#AMATULMALEEK
#ASH
#ROMANCE
#NAUFAL
#FAMILY
#WEALTH
#LA HOT


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at๐Ÿ‘‡
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

7
Maamah kasa cewa komai tayi sbd batasan mema zata ce din ba idan Akan wannan maganar ne Dan kuwa ko ita bazata taba son ayiwa AmatulMaleek auren wuri na kauye ba Amma Babu yanda zatayi idan su kawu suka Yanke mata Hakan.

AmatulMaleek kuwa da Abdul dasuke gurin Basu Wani Maida hankali ga abinda su maaman ke magana akaiba Dan kallo sukeyi,

Ganin Hakan Abeeda takira khaltume ta tafi dasu palon Husnah da Haydar suyi kallon acan.

Bayan antafi dasu AmatulMaleek din zuwa can Abeeda kallan Asmau tayi a natse tana son jin da gaske idan auren kauye din zaawa AmatulMaleek.

Shiru Maamah tayi sbd batasan me zata fada ba Dan kuwa kota Bude Baki ta fada ko kada ta fada Abeeda tasan batada ta cewa akan Hakan,

San numfashi kawai ta sake tana cewa

"Tinda Bata karatu Kam ai auren dole ne da wuri Koda bamuso Hakan ba"

Cikin mamaki da Dan takaici Abeeda tace

"Ke Zaki yarda kenan ayi mata Hakan?
Kuma Asmau me zaisa ki bari 'yarki taqi karatun Boko?
Yanada mahimmanci fa kema kinsan Hakan.

Fada Abeeda ta hau yi sosai Wanda ya Saka maamah yin shiru kanta a qasa batareda tasan me zata ce ba Dan kuwa fada ne Abeedan keyi kamar tanayi da 'qanwarta ko 'yar aikinta.

Abeeda ji tayi duk haushin Asmau ya rufeta Dan haka ma ko firar kirki basuyiba saita damuwa da takaici.

Su Amatu kuwa suna can zaune palon su Husnah duk da Husnah din Bata Nan tana can tareda mum Aisha tin da Akai rasuwar Basu dawoba tkuna Haydar ne kawai anan.

Kallo sukasha sosai hankali kwance sai kusan magrib maamah ta jasu suka koma inda suke wato bangaren masu aiki.

Kwana sukai Abdul na firar abinda suka ringa kalla a TV ita Kuma Maamah cikin damuwa ta kwana sbd Abeeda datai mata fada da maganganu dasuka Saka zuciyarta rauni akan rayuwar datake ciki da 'yayanta.

Amatu kuwa data fahimci damuwa a tareda mahaifiyarta itama sanyi jikinta yayi Dan haka dukansu a sanyaye suka kwana.

Koda gari ya waye maamah data Dan fara sabawa da fitowa Taya masu aiki ayyukansu,fitowa tayi ta nufi dakin khaltume ta kwankwasa mata ta tambayeta idan akwai aikin da zaa Taya dashi.

Ba musu khaltume ta nufi kitchen da ita ta tayasu da aikin fere dankali da doya harma da wasu ayyukan Dan kuwa maamah din tanada nutsuwan aiki da tsaftan Daya sakasu Dan bari tana Saka hannu a aikin.

Dayake kowa ya samu Rana shanya garinsa yakeyi sai gashi cikin kwanaki kalilan masu aikin gidan Kokuma ace khaltume datake babba a cikin ma'aikatan gidan sun mayarda Maamah din kamar me aikinsu Suma kusan duk wasu ayyukan kitchen din Banda girki itace take yi musu,

Ita Kuma Bata taba Jin gazawa ba ko jin an Renata ko wulaqanci ne sbd dadi ma takeji ganin tana yiwa Abeeda da Ash hidima a gidansu da karfinta tinda batada abin biyansu da tarin alkhairansu gurinta Dan haka da zuciya Daya take aikinta.

Abeeda batasan tana aikinba sbd sam Bata zama sosai yanzu da asmaun iyakacinsu suzo su gaidata ta danyi fira sama sama da asmaun su koma.

AmatulMaleek ma data ga dai aikin na gaske ne itama sai tana biyo maamah din kitchen tana kama wasu ayyukan Dan kuwa zuciyarta Bata nutsuwa ganin mahaifiyarta na wahala duk da aikin gidan Sam bama zasu kirasa da aikin wahala ba tinda komai a tsare akeyinsa yanda yake a tsare.

Sunanan Babu cikakken sanin matsayin zamansu Wanda ake nufin jiran dawowar Me gidan sukeyi da mum Aisha maamah tayi musu gaisuwar rasuwar data sakota zuwa Amma ba alamar zasu dawo kusa hakama ita kanta Abeeda tafiya kamata tayi zuwa porthcrt ta kwana biyu Dan haka tana tafiya suka sake zama Wani iri a gidan.

Abdul dai tini ya koma Dan masu aikin gidan sbd maamah aka barwa Haydar Dan haka akace su koma can cikin gida suna kwana sbd Haydar din kafin maamah ta dawo duk da akwai masu aikin Dake kulawa da cikin gidan dama Haydar din Wanda kusan shekarunsa Daya da Abdul.


****Acikin kwana biyu da tafiyar Abeeda Haydar yaji dadin zama acikinsu maamah da Abdul da AmatulMaleek sbd su Kam tsananin son junansu da kulawa da juna sukeyi tareda wasa,
Duk da Amatu ta girmi Abdul sosai Hakan Bai hanata zaka qawarsa ba abokiyar wasansa Kuma abokiyar fadansa ba hakama itama Maamah sosai take sakewa da yayanta tana San biye musu wasu lokutan musamman idan ba kowa sbd idan akwai mutane tana bayyanarda kunyarta ta haihuwar fari ga AmatulMaleek sosai sosai shiyasa a duk lokacinda Abeeda tace mata "yarki AmatulMaleek" Jin Kalmar takeyi ta mata Wani irin nauyi.

Tsakanin Abdul da Haydar harma da Amatu cikin kwana biyu sunyi wasa da 'yar sabuwa Dan haka Koda Abeeda ta dawo tayi mamakin yanda Haydar yake wasa sbd sam Baya wasa Baya Wani fara'a kamar 'dan dayake cikin qunci,
Husnah ko tana Nan Sam Bata Wani sake masa sbd son girma da ganin batada lokacin wasan banza dashi ita datake zama 'yan mata,
hakama masu aikin gidan Babu me Dan wasa dashi kulawa kawai suke basa Dan haka Sam shi rayuwarsa ta yarinta Bai ganewa komai na Jin dadi da sakewan qananun Yara ba,
Idan ya Dan samu wannan sakewan to Brother Naufal dinsa Yadawo hutun daga school Yana Nan Dan haka shi wata sabuwar rayuwar ya Gani a tattareda su Amatu da maamah.

Abeeda bataji komaiba saima dadi dataji Haydar din ya sake Yana wasa sosai Dan haka saisu Amatu da Abdul suka samu sake da Daman zuwa sashen aduk lokacinda sukaso ganin Abdul din haka Shima da Bai taba sanin tayaya ma ake zuwa sashen masu aikin gidanba sai gashi yana zuwa a duk lokacinda yaso.

Dawowar Abeeda ma ta fahimci maamah na aiki cikin masu aikin gidan ko datai mata magana maamah ta nuna

Please Login or Register in order to submit comment