Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masani. Nima kuma tunda na mallaki hankalin kaina na watsar da komai bana son ma na tuna wannan bak'ar rana da baza ta tab'a gogewa a kwanyar kai na ba sai ranan da zan koma ga mahallicina.

A yanzu bani da komai sai wannan sarkar da Abbu ya bani. Duk lokacin da nake begen su zan d'auko sarkar ina kallon ta ina kuka. Ganin yanda sarkar ke sani cikin damuwa sosai Mama Maria ta sani na cire sarkar na ada nata. Ta hanani daukan ta sai dai in babu idon ta. Kuma hakan da tayi ya yaye min damuwar rashin su matuƙa.

Mama Maria babbar macece balarabiyar Egypt. Tana da aure da yara biyu, halin rayuwa yasa ta karb'i aiki cikin masarautar kuma Allah ya taimake ta macece ita mai gaskiya da amana ,dalilin da yasa sarki da sarauniya suka yarda da ita d'ari bisa d'ari. Duk irin wannan bauta da take musu basu amince da fitarta daga masarauta ba sai lokaci zuwa lokaci. Wato sai idan abu mai muhimmanci ya taso. Tace hakan ya yi mata matsawar mijin ta da yaranta zasu ci, su sha su kuma saka sutura mai kyau.

Babu laifi gaskiya ana bata albashi mai tsoka. Har mamaki nake idan naga yanda take yin komai saboda y'ay'an ta. Wata rana haka zan zauna nayi ta kuka idan na tuna Abbu da Innati. Zamana da Mama Maria yana d'an debemin kewar rashin su dan ta d'auke ni tamkar yarda ta haifa. Ta koyamin larabci duk da nima ina ji amma ba sosai ba. Yanzu idan na juye harshe baza kace nasan wani abu waishi hausa ba. Kusan mutanen da muke wannan b'angaren d'ai-da'i kune ban koyawa hausa ba. Wasu sun d'an iya wasu kuma har yanzu sun kasa cikin su harda Mama Maria da bata iya sosai ba harta sunana NADEEYAH bata iya furta shi sai kawai ta samin NADINE da harshen su.

Duk wanda ya sanni anan da sunan da yake kirana dashi kenan. Bayan wannan kuma sai harshen nasara da muke makaranta shi nan b'angaren mu akwai dogari (Gaurd) na musamman dake koyar damu turanci don ya zama kaman doka ne mutum ya koya saboda gudun had'uwa da wani daga cikin masu Mulki.

A yanda nake ji sunfi yin turanci a kan harshen su mai dad'i yaran Manzon mu Annabi Muhammad (S.A.W) saboda y'an boko ne. Kaf cikin su jinin sarautar basu cika zama ba a nan sai kasashen waje. Shi yasa ma ilimin addinin ya yi musu k'arancin.

Ina da shekara goma sha bakwai cikin masarautar Egypt KING SAIFULMULK da QUEEN AIRA suka sauka daga kan kujerar Mulki suka d'ora d'ansu da naji anawa lak'abi da EZKE'IL wasu suce AZRAH. A yanda naji ana labarin sa mutum ne shi mai masifar had'arin gaske. Bashi da imani bashi da tausayi. Maganan Mama Maria a koda yaushe nayi hankali koda wasa kar na bari hanya ta had'ani dashi. Kai ko hanya nabi naji ana labarin sa tace na chanza wata.

Ranan nad'in nashi kaf cikin mu babu wanda ya runtsa. Yanda muka ga rana haka muka ga dare. Wuni mukayi muna aiki babu kama hannun yaro. Musamman ma mu da muke b'angaren girki. Mama Maria har ciwo tayi saboda gajiya ga kuma girma dake k'ara kamata. Da yawa wasu abubuwan nike yinsu nace ta huta. Shi yasa aikin ya zame min jiki, Idan ka cire ciwon jiki da kai babu wani bayan hakan. A ranan ne zan iya cewa muka fito daga b'angaren mu ,muka mik'a abinci wajen da ake ajiyewa a shiga dashi cikin masarauta.

Tunda ake fita dashi ban taɓa karb'a na fito da dashi ba hasalima nan gurin mu dogarai ke shigowa su kwasa suyi waje da su. D'ai-da'i kun rana ne Mama Maria ke fita da abincin da kanta bata tab'a cewa nazo muje tare ba. Wajen had'a kayan ne muka had'u da Fahima. Rungume juna muka yi cikin matsanancin farin cikin ganin juna. Harna fidda ran k'ara ganin ta sai gashi Allah ya had'amu. Tun daga ranan muke d'an satar jiki muna haɗuwa.
Ita tana can b'angaren masu wanki.


✿︎✿︎✿︎✿︎


Yau ya kama ranan weekend. Tun dare Mama Maria ke kwance zazzabi mai zafi ya rufeta. Da kyar ta iya yin sallan Asuba don ko karatun Qur'ani da take koya min duk bayan sallan asuba kasawa tayi yau. Na shiga cikin matsanancin damuwa da ciwon nata hankalina duk ya tashi. Idan itama ta mutu bani da kowa yanzu a duniya sai ita. Ina yin salla na miƙe da sauri na fito katon kitchen d'in dake nan kaman gari masu aiki nata kai kawo sai kayi tunanin kasuwace. Da sauri na fara bin kayan ganye dake ciki kwanduna ina dubawa har Allah ya taimake ni na samo ganyan lemon. Shayi na had'a mata da ganyen da y'ay'an coffee.

Cikin y'ar k'aramar butar shayi ta silver na juye na d'ora kan plates da d'an k'aramin kofin butar. Ragowar abincin da aka kawo daga masarauta nabi da sauri ina d'an duba abu mai dan ruwa-ruwa. Kayan abinci ne gasu nan sunfi kala ashirin. Nama ne , kaza ce ,kifi ne, snacks ,kayan ganyayyaki ,fruits ne gasu dai bila adadin dan wasu ma ko tab'asu ba'a yiba. Haka kullum zamu dage mu girka a dawo da rabin abinci ba'a tab'a ba. Shi yasa babu yunwa mukam a gurinmu kaman sauran b'angarorin. Dan muna ci mu koshi har sai mun ture.

Kaza na hango katuwar gaske kan wani plate an shak'e da abubuwan ci wasu ma baka sanin mene. Da sauri na d'auki plate na yanka k'azar na d'ora a kai na kwashi romanta da yawa na zuba na hada da d'an snacks na koma d'akin mu da sauri.

A tsaye na tadda Mama Maria tana ta rawar jiki da babban d'anta da kanwar sa dake binsa. Huzaifa da Jalila. Kaya suke sa mata suna ganina fuskarsu su ta cika da fara'a. Ajiye kayan nayi cike da farin cikin ganin su nace

"Huzaifa , Jalila. Marhabanbikum, kaifal hal?"

A tare suka bani asma " Alhamdulillahi, kaifa Anty?munzo tafiya da Mama ne saboda yanayin jikin ta, zata koma gida ta d'anyi jinyar ta acan har Allah ya bata lafiya"

Ido na zaro tuni ruwa sun fara cika su. Idan suka tafi da ita zanyi zaman kad'aici. Babu yanda zanyi haka na taimaka musu muka shirya Mama Maria ina k'ok'arin hana kaina kuka. Duk abunda nake nasan Mama Maria na kallo na tasan kuma dakiya ce kawai nake saboda babu yanda zanyi. Muna gama shirya ta Jalila ta kwashi kayanta suka rik'e ta zasu fita da ita. Hannuna ta kama ta tallafo fuskata. Hawayen da nake ta k'ok'arin riƙewa suka tawo shar kan kuncina. Murmushi ta yi na wanda ke jin jiki tace.

"Ki kwantar da hankalin ki Nadine, da zarar na warke zan dawo kinsan babu yanda za'ayi nayi nesa dake sai in ta kama dole ne. Yanzun ma naso tafiyar dake ban samu wannan alfarmar ba saboda King SAIFULMULK da QUEEN AIRA basa k'asa sai EZKE'IL. Kinsan wane AZRAH yanzu ma da kyar ya amince wa Huzaifa da Jalila su d'auke ni saida ya ganni cikin matsanancin hali tukun. Nadine ki kula da kan ki har sanda xan dawo kar kiyi wani abu da zai jawo hankalin EMPEROR AZRAH kan ki don Allah Nadine"

Ina kuka na d'aga mata kai. Ba yau ta saba tafiya ta barni ba. Duk inda zata je kuma bata wuce kwana biyu ,yau d'inne kawai nake jin kaman wani abu na shirin faruwa idan ta tafi ta barni. Huzaifa da Jalila suka hau dariya suna tsokana ta dole na ware muka fito nayi musu rakiya har bakin k'ofar mu. Ban bar bak'in k'ofa ba saida suka b'acewa ido na na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi na koma ciki.

Ranan wuni nayi babu kuzari. Harta Fahima data saci hanya tazo muyi hira sai gajiya tayi ta tafi dan duk abunda tace sai dai na bita da eh,ko A'a.

Kwana biyu da tafiyar Mama Maria na kasa warware wa. Duk abunda nake ina yinsa babu kuzari. Wajen la'asar yau na fito dauke da kwando dana zubo kayan ganye daga lambu dake can bayanmu. Azeemah dake aikin Mama Maria duk lokacin da bata nan ta aike ni na deb'o mata. Tafiya nake ina y'ar wak'a ta larabci da Mama Maria ta koyamin duk kewar ta ta dame ni. Bansa ya akayi ba na fito wani katon Garden dake nan gari guda ga wasu irin bishiyu masu masifar kyau da suka k'awata gurin an kuma kewaye gurin da kujerun glass da aka yiwa ado da furanni masu kyan gaske. Turus na tsaya ina kallon aljanna duniya. Ban taɓa sanin da akwai gurin nan ba sai yanzu. Can gefen sa wani irin kwami ne dake zubda wani irin ruwa mai shegen haske kaman madara ga wasu irin fulawoyi dake zuba cikin sa da wani irn kamshi da kukan tsuntsaye masu masifar kyau dake shawagi a gurin.

Nikam ya aka yi bansan da wannan aljannr duniyar ba duk tsawon zamana cikin wannan masarautar?. Dube-dube na fara ina tunanin hanyar dana biyo ta kawo ni nan. Chak idon nawa ya tsaya kan wata hallita mai masifar kyan gaske. Tubarakalla MashaAllah, hak'ika babu abun yabo da bauta sai Allah. Bayansa kawai na gani nasan cewa koma wane wannan ba k'aramin kyakkyawan mutm bane.

Dogone mai faffaɗan kirjin duk da bayan nasa kawai nake iya gani yanayin zubin halittar sa ya nuna shi d'in maji k'arfi ne. Gashin kansa dake tufke tsakiyar bayan sa nabi da kallo baki sid'ik dashi har tsakiyar bayansa duk da ya tufke shi. Wata irin tsayuwa ya yi bak'in kwamin dake zubda ruwa hannun sa goye a bayan sa ga wata irin tsuntsuwa mai masifar kyau kan k'afad'ar sa. Kayan jikinsa riga da wando farare kaman na Pakistan mara nauyi nabi da kallo da basuyi nuni da shi ko wani mai muk'ami bane cikin masarautar. Murmushi nayi a raina nace ai dole ma na kulla k'awance dashi kodan saboda kyansa duk da ban taɓa ganin sa ba cikin masarautar. Wata kila sabon d'auka ne cikin bayin da aka d'auka satin daya wuce.

A hanzarce na k'asara inda yake tsaye cikin sand'a . Ashe yaji ni dan a wani irin slow ya juyo inda nake. Kalu'innalillahi. Chak numfashi na ya d'auke sanda nayi arba da kyakkyawar fuskarsa. Tunda na taso tsawon rayuwa ta naji yanda ake zuzuta kyau na, amma wannan bawon Allahn ni ba komai bace a kansa. Ban taɓa ganin mutum mai tsananin kyau kaman sa ba ,duk da ba fita nake ba nasan ko na fita da wuya a samu mutum mai masifar kyan sa. Wata kila ma yafi EMPEROR EZKE'IL kyau kaman yanda naji ana zuzuta kyawun nasa.

Murmushi nayi mai kama da yak'e nayi tsuru-tsuru dani kaman wadda aka kamata tana sata. Kwayar idansa dake bak'a sid'ik da ita ya zubamin ya d'aga cikakkiyar girarsa guda d'aya da suka kusa had'ewa . Cikin inda-inda da rashin sanin abun fad'a nace da larabci.

"Assalamu'alaikum. Ya kke?, hala kai sabon d'auka ne anan?"

Shiru bai bani amsa ba sai idon sa daya zubamin ga uban kwarjini da yake dashi kaman na zura a guje amma na dake don ina son gwada damata. To ko bayajin larabci?. Kai na gyad'a na juya harshe da turanci nace.

"Hey are you knew?"

Nan madai shiru bai bani amsa ba. Na fara tsarguwa da kallon da yakemin zuciya ta tace ki kama gaban ki Nadine. Shawarar zuciya ta na d'auka na juya da sauri zan tafi sai kuma wata zuciyar tace ki gargade shi ya yi hankali cikin masarautar nan ya iya takun sa. Juyowa nayi da sauri na fara magana ina yi da larabci ina had'awa da turanci kai harma da Hausa tsabar yanda na rud'e da kwarjinin sa.

"Kayi hankali cikin masarautar nan idan kai sabo ne. Tunda har ka shigo masarautar nan nasan kasan wane KING AZRAH. Ba sai na tsaya ina maka dogon bayanin rashin mutuncin sa da rashin Imanin saba,amma dai kayi hankali da takun ka dan mugun mutum ne mai kan agwagwa, mummuna mai katon ciki. Nasan yanda ake cewa yana da kyau ko yatsan ka bazai kama ba...."

'NADINE ' Zuciya ta ta kirani da k'arfi. Chak na tsaya da b'ab'atun da nake Ina zare ido. Wani irin kallo naga yana min da naji hanjin cikina sun kad'a. Shikenan na b'ata damata nasan zama abokiyar sa. Nasan yana min kallon mahaukaciya na tsaya ina ta b'ab'atu bana ko Jan numfashi daga haɗuwa da mutum bansan waye ba?.A guje na juya a sittin na bar gurin cikin matsanancin kunya.








♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔



ASHANTY LOVE.








☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
11/15.




Ban tsaya da gudun ba don burin kunya saida na tabbatar na sadu da sashen mu. Kitchen na nufa kai tsaye na ajiye kayan lambun dana deb'o kan kanta na durkusa ina haki hannuna dafe da k'irjina dake bugawa. Muryar Mama Azeema naji a kai na d'ago da sauri ina kallon ta da murmushi kan fuskata dani kaina na rasa dalilin sa.

"Ina ki ka shiga tun d'azu ki deb'omin kayan lambu kawai?"

Y'ar dariya nayi mai kama da yak'e nace

"Yi hak'uri Mama Azeema bansan zan dad'e haka ba. Na tawo ne na kauce hanya na b'ata "

Ido ta zubamin tana jiran k'arin bayani. Idan nace mata na had'u da wani hanyar dawowa ta zata ce babu wani b'ata da nayi da sani na ne. Ni ko yama sunan sa? Allah yasa gobe mu had'u na tambaye shi. Kai na sosa nayi saurin kawar da kaina daga kallon tuhuma da takemin.

"Wlh Mama Azeema b'ata nayi. Gani kawai nayi na bulle wani Garden mai shegen kyau. Ban taɓa sanin da akwai shi ba ,koda yake ba fita nake bane shi yasa babu lallai nasan dashi."

Ido waje naga tana kallona kafin ta kama hannu na da sauri taja ni gabanta.

"Me naji kina cewa Nadine?,kinsan inda ki ka tsinci kan ki kuwa?, wa ki ka gani a gurin ?,kin had'u da wani"

Kai na girgiza ina kallon fuskarta dake d'auke da tashi hankali k'arara.

"Babu wanda na haɗu dashi Mama Azeema amma me yasa naga kin shiga damuwa"

"Saboda wannan gurin b'angaren Sarakai ne . King Azrah yasa aka gina shi bayan nad'in sa. Babu wani bawa daya isa ya shiga gurin har saida iznin sa. Ko da ace ka shiga gurin ne cikin rashin sani sai ka karb'i hukunci. Akwai bayi da dama da suka samu b'atan hanya irin ki har yau babu wanda ya k'ara jin labarin su"

Shiru tayi tana maida numfashi na zuba mata ido ina tunanin mutumin dana had'u dashi cikin garden d'in. Suturar jikinsa na tuna da bata da banbanci da kayanmu na bayi. Mu mata muna sanye ne da doguwar riga mai d'an fad'i daga kasa wajen kugu an dan tattare ta kad'an ya zama kaman sket, sai saman rigar wajen k'irji da mad'aurai gudu uku. Rigar mai three quarter d'in hannu ce. Su kuma maza suna sanye ne da riga da wando ruwan toka mu kuma farare. Rigar kaman Y'ar Pakistan ce da wandon ta. Sai hula ko dan hankici da zamu daura a ka ga duk mai so.

Ance ko wane b'angare da irin kalan kayan su. Mu namu b'angaren kalan namu kenan. Ba'a chanzawa sai in ana cikin d'aki ko kuma ranan da babu aiki. Nikam ina dasu wajen kala goma da Mama Maria ke sawa ana d'inka min duk lokacin da aka samu yadi mai kyau.

Tunanina ne ya tsaya kan cewa shima bawan ne amma ba b'angaren mu ba. Yanzu haka ko shike kula da garden d'in shi yasa kayan sa suke farare kal . Gum nayi da baki na ban k'ara cewa komai ba na wuce na kamata aikin ina na taimaka mata da yanka kayan lambun dana kwaso. Har muka gama tunani na na kan wannan mutumin Mai Kyau. Sunan dana rad'a masa kenan. Saboda rashin Mama Maria nina fita da abincin da taimakon Mama Azeema da sauran mutane da muke abinci tare muka kai can inda ake ajiyewa. Shi kanshi gurin d'aukan abinci idan kaje kaman karka fita saboda kyau. Komai Allah ya wadata su dashi dole kuwa suyi abunda suka ga dama. Allah ya kyauta.


✿︎✿︎✿︎✿︎


Tsawon kwana biyu kenan da haɗuwa ta da wannan bawan Allah har yau kuma ban k'ara sashi cikin ido naba. Sai naji duk babu dad'i na saddakar cewa bazan k'ara ganin saba. Duk irin kashedi da Mama Azeema tayi min akan garden d'in nan ban fasa satar hanya ba nabi ko Allah zaisa na ganshi ta wajen don tunani na yafi k'arfafa ne a nan yake nashi aikin, amma sai naje na gama zagaye ne ban ga ko inuwar sa ba.


✿︎✿︎✿︎✿︎


Qur'anin dake hannuna na ina bitar karatun da muka yi da Mama Maria na rufe sakamakon bugun k'ofar da naji ana yiwa k'ofarmu. Agogon dake mak'ale jikin bango na kalla. Karfe shida da rabi ya nuna. To waye haka yanzu da sassafen nan?. Ko aiki bama farawa sai bakwai dan su kansu wanda muke yiwa bautar basa tashi sai wajen d'aya na rana sannan za'a kwashi abincin su nasafe a kai musu lokacin mun kusa sauke na rana. Kunga abunda yasa bama zama da yunwa.

Qur'anin na ajiye da sauri na tashi na ajiye gefe saboda bugun k'ofar ya yi yawa. K'ofar na nufa a hanzarce ina cewa gani nan. Da rawar jiki na buɗe k'ofar dan ganin masu wannan bugun. Matsanancin bugawa k'irjina ya yi ganin Royal Gaurd(dakarun Sarki na musamman) ba'a ganin su sai in mutum ya yi laifi. Laifin ma mai girma da zaisa King Azrah ya turosu da kanshi suzo su tafi da mutum. Ganin su babbar musifa ce. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Me ya kawo su k'ofar mu? Me nayi?. Ko an gano ina zuwa Garden d'in ne a b'oye? bugun K'ofar da suke ya fito da Mama Azeema da sauran mutanen dake nan b'angaren namu. Ina kallon yanda tashin hankali ya bayyana k'arara kan fuskar Mama Azeema da sauran Mutane gashi basu isa su tunkaro inda suke ba ko saji ba'a sin zuwan su nan.

Tashin hankalin dasu Mama Azeema suka shiga ba komai bane kan wanda nake ciki. Kad'an ya rage ban saki fitsari ba har wani gumi ke kyetomin tsabar firgici. Kallon su nake jiki na, na rawa na fara k'ok'arin buɗe baki nayi magana suka rigani da firgitacciyar murya d'aya daga cikin su ya yi magana.

"Anty NADINE ?" (kece Nadine?)

Jikina na rawa na d'aga kai dan bazan iya basu amsa ba ji nake kaman na fashe da kuka. Kallon juna suka yi suka k'ara kallo na kafin d'ayan ya cigaba da cewa

"Ana buƙatar ki cikin masarauta yanzu-yanzu"

Wani irin kullewa cikina ya yi naji kamn zan kifa saboda firgici. Nashiga Uka ni NADINE. Mama Maria kizo ki cece ni. Me nayi yau ake nemana cikin masarauta? Tsawon shekara goma sha takwas ban taɓa takawa cikin taba ko wani guri makamancin ta bare nayi laifin da za'a nemi cikin ta. Idan ka cire garden d'in nan. Shima kuma bana shiga saidai na kewaya shi tunda tunda katangar sa da wani irin glass aka yi shi. Kai ko King SAIFULMULK da QUEEN AIRA basu san da zamana gurin Mama Maria ba. Inma sun sani to sun manta dani dan ina bin duk wasu dokoki saboda gujewa wannan rana. Maganan su ta katsemun tunani

"Ki hanzarta kina tsaye. Umarni ne daga EMPEROR AZRAH "

Wai ai tuni naji fitsarin da nake riƙewa yana k'ok'arin kufcewa a guje na juya na koma d'aki. Tsawar su naji bayana sunyi tunanin ko guduwa zanyi. To in gudu inje ina?. Da gudu na fad'a d'an banɗakin mu dake cikin d'akin da muka kewaye shi da labule. Ina jin sawun tafiyar su bayana suna ganin na shige suka ja tunga bakin k'ofa suka tsaya suna jirana. Saida na rage marata na fito jiki a salube ina kallon su kaina. Wasu d'irka-d'irka dasu jiki duk a murmurd'e. Ga wasu kaya da suka sa na yak'i dake k'ara firgita mutane.

Gaba nayi suka rufamin baya. Ina fitowa na iske su Mama Azeema da sauran mutane tsaye k'ofar d'akin namu. Tana ganin na fito ta tawo da sauri ta rungume ni tana kuka.

"Me ki ka yi Nadine? Me ki ka yi da har King Azrah ya turo a tafi dake?"

Murya ta na rawa nace "nima ban sani ba Mama Azeema. Ke shedace babu inda nake zuwa cikin masarautar nan"

Kai kawai ta d'aga hawaye na bin fuskarta. Tsawa suka daka min

"Wuce muje mana kina b'ata mana lokaci "

A sanyaye Mama Azeema ta sake ni na wuce ina sharar hawaye kasan zuciya ta ina kiran Mama Maria. Da ace tana nan nasan sai inda k'arfi ta ya k'are wajen ganin ta hana sun tafi dani. Inma bata hana sun tafi da niba to tabbas babu makawa tare zamu tafi da ita.

Kome zan tarar kuma cikin masarautar da ban taɓa taka k'afata cikin taba??




♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔




ASHANTY LOVE.









☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆





Chapter
16/20.






Tafiya nake ina sharar hawaye suna biya dani. Tunanin mak'omata cikin wannan masarautar nake. Tsawon minti hud'u muka dauƙa muna tafiya kafin na fara hango tangamemen ginin daya raba mu da cikin masarautar. Dakarune kewaye da ita ta ko ina tun daga farkon ta har k'arshen katangar da baka ganin sa. Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi zuciya ta fal tsoron abunda zan tarar. Da sauri naga sun wuce ni zuwa bakin k'ofar suna wa katon Gaurd dake gadinta magana. Shi kaɗai ma ya isa yasa ka juya da gudu tun kafin ka k'arasa.

Katon gate d'in suka buɗe da aka yi da zallar Crystal stones. Baki na hangame na tsaya chak ina kallon wannan masarauta kaman aljanna duniya. Hak'ika

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment