Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu abun yabo da bauta sai Allah. Shike bayarwa kuma shike hanawa ga wanda yaso.Gaskiya dole su shagala da duniyar da Allah ya basu su manta cewa zasu koma gareshi.

Ji nayi kawai sun tankad'ani nayi taga-taga kaman zan fad'i Allah ya taimake ni na tsaya da k'afafuna. Tsawa suka daka min

"Wuce mana kinja kin tsaya. Ko kinsan illar barin KING AZRAH zaman jira?"

Bance komai ba na cigaba da tafiya bansan inda zanyi ba don yaune karo na na farko dana shigo cikin wannan Palace. Lura da hakan da suka yi suka k'ara wuce ni na cigaba da binsu a baya. Katon gini muka shiga mai masifar kyan gaske da doguwar hanya kaman corrido. Shima saida muka yi y'ar tafiya sannan muka bulle wani irin Garden mai tsananin kyau dayafi na b'angaren mu. Ta cikin sa muka shiga sai gamu mun bullo Royal Palace.

Ido waje nake kallon ginin. Kunne nayi baki nayi. Sosai na zama y'ar kyaune na hangame baki ina kallo. Tankamemen falo muka shiga da ke dauke da kujerun gold da garden cikinsa kai harma da kwani na ruwa a tsakiyar sa ga wasu tattaburu farare dake shawagi kansa. MashaAllah hak'ika Allah ya basu duniya saura lahirar su kuma.

Glass staircase dake can k'arshen falon ya kewaye shi ta ko ina suna nufa na rufa musu baya. Kaman dai yanda ko ina yake zagaye da dakaru haka shima falon yake tun. Saboda yawan benen saida na gaji na d'an yunƙura zan hutu suka k'ara dakamin tsawa na miƙe da sauri na cigaba da binsu. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na dafe gefen cikina ganin mun kawo k'arshen benen. Kai wannan wahala da yawa take. Mutum in mai k'iba ne ai cikin kwana biyu zai ya zazzage gaba d'ayan sa. Hanya muka bi doguwa nan ma kaman corrido mai d'auke da kofofi wajen shida ko wacce a gark'ame da matakan tsaron a bakin ta. K'ofar dake tsakiya warda tafi ko wace girma da kyau tana fuskantar mu ,mu ka tsaya.

Kai na d'aga ina kallon jibgegiyar k'ofar da aka yi kaman da gold sai shek'i take saman ta an rubuta EMPEROR EZKE'IL CHAMBER da stone's na crystals abun sai ya k'ara armashi sosai. Dakurun dake zube gaban k'ofar na maida hankali kai ina kallo cikina na bada sauti saboda matsanancin tsoro. Sai yanzu nake jin irin bugun da zuciyata take da mugun gudu kaman zata tsaga kirjina ta fito. Gyaran murya d'aya daga cikin dakarun da suka titsiyoni nan ya yi nayi saurin maida hankali ina kallon su. Kai ya jinjina ganin na maida hankali ina sauraran shi ya fara magana.

"Idan an buɗe kin shiga kar ki kuskura ki d'aga kan ki har sai ya baki umarnin hakan. Ki kiyaye kallon sa ba tare da izni ba kinji ko"

Sakato na tsaya ina kallon Gaurd d'in. Wane irin abu ne kuma haka? Tsawa ya dakamin

"Kinji abunda nace?"

Da sauri na d'aga kai cikin firgici. Kai ya d'aga ya juya. Ina kallo yaja numfashi mai k'arfi kafin ya d'aga hannu ya buga k'ofa sau biyu ya koma baya ya wani k'ame ko motsin kirki baya yi kaman an zare masa laka bashi kad'ai ba gaba d'aya dakurun sun k'ara k'amewa kaman basu numfashi. Tun daga nan na fara hango makomata. Tsawon minti goma muna tsaye babu alamun za'a amsa bugun k'ofa bare a buɗe. Kafafuwan har sun fara gazawa na fara k'ok'arin sunkuyawa sai kawai naji wata irin murya mai shegen gard'i da sanyi gata so, so Deep tayi magana daga cikin d'akin a kasalance kaman wanda maganan kewa wuya.

"Minnnn ?" (Waye?)

Ai tuni hanjin cikina suka k'ara kad'awa na gyara tsayuwata da sauri kaman yanda naga dakarun sunyi. Jiki na rawa ya bashi amsa.

"Mune KING AZRAH. sakon da kace a kawo maka gashi mun tawo dashi"

Sak'o? Ban ma isa a kirani da mutum ba kenan?. Nan ma dai sai da ya d'auki sama da wajen minti goma kafin ya bada amsa. Wannan wace irin rayuwa ce?. Wace irin isa ce wannan?wai shin da mai kuɗi da mulki, arziƙi ,talaka duk ba d'aya suke ba gurin Allah?. Me yasa wasu mutanen idan sunga Allah ya basu duniya sai su dinga ganin kaman sunfi kowane?. Bafa dabara ko iyawa tasa Allah ya basu wannan matsayin ba. Duk wani abu da zai samu bawa a wannan duniyar jarabawa ce a gareshi. Wani zata kaishi wuta wani ta kaishi Aljanna. Ga wad'an da suka fifita duniyar su kenan a kan laharir su. Sun manta cewa duniyar nan ba komai bace.

Maganan gaskiya iya fusata nayi. Wannan wulaƙanci ya yi yawa. Yasa an kawoni ba tare da nasan abunda nayi ba. Nazo kuma sai iko yake mana. Anya kuwa zan iya jure wannan isar?

A kasalance naji ya yi maganan da saida na kasa kunne sosai naji. Cikin harshen nasara yanzu yace

"Let her in"

Kallo na gaurd d'in ya yi ya matsa k'ofar da sauri don ya buɗe yana cewa

"Kar ki manta gargad'in da nayi miki. Kar ki d'aga kai har sai ya baki umarni"

Ban bashi amsa ba na d'auke numfashi bayan buɗe k'ofar da ya yi duhun d'akin ya yi min sallama da wani irin kamshi da sanyi mai ratsa bargo da kashin mutum. Da kyar na d'aga kafata da suka yi nauyi na tura kai cikin d'akin bakina d'auke da siririyar sallama. Bana iya ganin komai saboda duhu sai y'ar fitilar dake can kan wata tebir katon gaske mara haske. Ido na buɗe sosai ina kallon kaman mutum ne zaune gaban tebir din ya d'an jingina dashi. Cikin duhun na fara bin kafafunsa da fitilar ta d'an haska min da kallo. Kaman wando ne na suit a jikin sa daya dan kama shi sai farar riga mai botira da kusan gaba d'ayan su a balle suke hannuwansa harde a kirji ya tattare hannun rigar zuwa gwiwar hannun nasa. Cigaba nayi da kallon nasa na d'aga ido na zuwa wuyan sa dake sanye da wata irin sarkar data kwanta kan faffaɗan kirjin sa dake a murd'e sai shining yake ga gashin kansa dake zube wajen kafad'unsa wasu sun zubo kan kirjin nasa sun kwanta.

Ido na k'ara d'agawa zuwa dogon wuyan sa wajen Adam Apple nashi (makwalato) na cigaba wajen fuskar sa sai diff wutar ta d'auke gaba d'aya. Tuni na dawo cikin hayyaci na na tuna da gargad'in da aka yimin. Innalilllahi meke damuna na ne? Nashiga uku ni Nadine. Rarraba ido nake saboda matsanancin duhun d'akin baka ganin komai. A mugun hankali naji kaman takun tafiya na kasa kunne inda nake jin takun da baya fita kaman wanda ke sand'a sai kuma naji diff shima ya d'auke. Yanzu nake jin ciwon rashin ganina cikin duhun da banayi. Da Sam ban damu ba amma yanzu saboda wannan mugun naji ina ma ya dawo ko na samu naga abunda yake kar naje ya kashe ni a banza.

A hanzarce na kai hannu na kare ido na saboda wani irin haske dal da dakin ya dauka lokaci d'aya. Murmushi (chuckling) naji anyi mai birkita lissafin mutum nayi saurin juyawa inda naji sautin. Sai da na kusa zubewa a k'asa lokacin da kwayar idon mu suka had'u jikina ya hau kyarma bansan sanda na d'aga hannuna na nuna saba. Yana zaune yanzu kan kujerar katon glass tebir irin ya dogara duka gwiwar hannun sa kanshi ya talleb'e hab'ar sa da yatsun sa daya had'a su guri d'aya.

Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Baza kuso kuga irin matsanancin tashin hankalin dana shiga ba wannan lokacin babu abunda ke yawo a kwanyar kaina sai kalmomin dana furta ranan kaman

" 𝒎𝒖𝒈𝒖𝒏 𝒎𝒖𝒕𝒖𝒎 𝒏𝒆 𝒎𝒂𝒊 𝒌𝒂𝒏 𝒂𝒈𝒘𝒂𝒈𝒘𝒂 , 𝒎𝒖𝒎𝒎𝒖𝒏𝒂 𝒎𝒂𝒊 𝒌𝒂𝒕𝒐𝒏 𝒄𝒊𝒌𝒊, 𝒂𝒛𝒛𝒂𝒍𝒖𝒎𝒊 𝒎𝒂𝒓𝒂 𝒊𝒎𝒂𝒏𝒊"

Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un shi ne King AZRAH. Shine na gama zagin sa kan idonsa cikin rashin sani duk da cewa wasu kalmomin da hausa na fad'e su. Na shiga Uku, Na shiga Uku.

Da kyar na d'aga ido na na kalle shi har yanzu yananan yanda yake fuskarsa babu wani expression a kanta. Kwayar idansa da ke da girma gata baka sid'ik kaman midnight dake bada wani calm expression ya zubamin kaman mai ganin hanjin cikina. D'aga gira ya yi gefen bak'in sa shima ya d'aga (smirk) da alama tsoron sa da ya gani kwance kan fuskata ya bashi enjoyment. Magana ya yi a kasalance muryar sa a kausasashe

"Masmik?"

Saboda firgici na kasa bashi amsa sai kai kawai da nad'aga. Gira ya k'ara d'agawa da alama kaman yin hakan nature nashi ne. Da sauri yanzu nace murya na rawa

"NADINE"

A d'ai-da'i ce ya kira sunan nawa "NA-DI-NE.. hmm"

Sunayen Allah kawai nake kira cikin raina da duk wata Addu'a data zo baki na. Murmushi ya k'arayi na lura da double dimples nashi a ko wane kunci. Tun daga sama har k'asa ya kalle ni sai kuma ya tashi daga zaunen da yake ya zagayo gaban tebir d'in ya zauna kaman yanda ya yi d'azu dana shigo.

Kuttt na had'iye yawu ina kallon sa na matse kafafuwana dake rawa guri d'aya. A take yanayin fuskarsa ya chanza zuwa wani deadly calm expression. Magana ya fara da calm voice cikin harshen turanci

" what is that you say?"

Kuttt na k'ara had'iye wani yawun, naji kaman na juya a guje na fice. Ga mamakina sai naji yana maimaita abunda nace harda hausar da nayi.

" Kayi hankali cikin masarautar nan idan kai sabo ne. Tunda har ka shigo masarautar nan nasan kasan wane KING AZRAH. Ba sai na tsaya ina maka dogon bayanin rashin mutuncin sa da rashin Imanin saba,amma dai kayi hankali da takun ka "

Yana dasa aya na kusa zubewa k'asan gurin. Duk irin matsanancin sanyin na d'akin wanda tsab mutum zai daskare cikin sa zufa na had'a kaman wadda aka zubawa ruwa. Gashin kaina dana tufke shi a tsakiyar kai na d'ora hula a kan nawa ina jin yanda gumi ke biyowa ta cikin gashin yana bin wuyana da goshina. Shi kanshi gashin ya jike jagab. Ban gama shiga tashin hankali ba sai da naji ya k'ara magana yanzu da Hausa.

"Ko kinsan tsawon lokacin dana d'auka ina koyan wannan yaren naki saboda na gane ma'anar kalman MAI KAN AGWAGWA DA KATON CIKI?"

"You dare to insult me like that?, mene ma ki ka ce .Bani da Mutunci da Imani?, why not na nuna miki rashin Imanin nawa zahiri yanda zaki ji dad'in bada labari da kyau?, . You disrespect me in the worst way possible. I know you have being told not to look at me, amma gaki kina kallo na ido cikin ido?"

Da azama na sauke ido na k'asa jikina na rawa kaman mazari. Wani murmushi naji ya k'ara yi da nasan babu alkhairi cikin sa.

"So Nadine. Daga yau zaki zauna a nan don ki sheda rashin imani na da rashin mutunci na. Aikin ki ya dawo cikin masarauta daga yau. Know Dismiss.."

Baima k'asara ba na juya a sukkuwanne na fice da mugun gudu daga d'akin.













♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔


Ashanty love.






☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
21/25.




Bansan inda nake sa gaba ba saboda firgici saida na sadu da k'ofar da zata fitar dani daga cikin masarautar. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi bayan na tsaya bak'in k'ofar na sunkuya rik'e da ciki ina maida numfashi. D'agowa nayi saboda idon da naji a kaina. Gaba d'aya hankalin dakarun yana kaina babu kuma wata alama da take nuna zasu buɗe min k'ofar na fita. Banyi k'asa a gwiwa ba na k'arasa ina kallon jibgegen Gaurd d'in dake tsaron k'ofar kaman yanda shima yake kallo na. Jarumta na aro na saita nutsuwa ta kafin nayi magana.

"Uhmmm ka buɗe min k'ofar zan koma b'angaren mu"

Kallo ya watsa min irin don't mess with me d'innan ya kauda kai gefe kaman da iska nake magana. Ai kuwa na k'ara tunzura a fusace na k'ara buɗe baki zanyi magana muryar mace ta katse numfashi na. A hanzarce na juya inda naji muryar. Kyakkyawar yarinyar ce da a kalla baza ta gaza haura shekaruna ba ashirin da hud'u ko biyar ba sanye da suit riga da wando da Air Bluetooth sakale a kunnen ta. Fuskarta dake d'auke da katon glass daya cinye rabin y'ar fuskar ta ta da babu wani annuri ko kaɗan a tare da ita. Bayanta wad'annan Gaurds d'inne yanayin ta ya nuna ita ce gaba dasu.

Tsawa ta daka musu da kausassar murya tace

"Me ki ke tunanin ki ke shirin yi?. You damn idiot gets her"

A hanzarce suka yo kaina dan cika umarni nayi saurin d'aga musu hannu.

"Kar wanda ya kuskura ya tab'a ni, zan tafi da kaina"

Na fad'a cikin tsawa. Saurin gimtse baki nayi. Ni kaina bansan inda na samu wannan kwarin gwiwar ba har na iya yin magana cikin tsawa haka. Shiru gurin ya d'auka kaman anyi ruwa an d'auke. Kallon da naga dakarun nayi min na k'ara shiga damuwa matuƙa. Da alama babu wani mahaluki daya tab'a tsayawa ya yi ja-in-ja da ita a matsayin ta na mace. Ga dukkanin alamu kuma tana da matsayi mai girma wajen King Azrah da sahalewar sa take duk abunda taga dama.

Da wani irin izza ta tako inda nake tsaye . Glass d'in dake fuskarta ta cire ta watsamin manyan blue eyes d'inta da suka k'ara fito da asalin kyanta. Da wani irin sinister voice ta fara magana

"Kar kiyi tunani ko na sakan d'aya saboda Kin dawo aiki k'ark'ashin Azrah kiyi tunanin matsayi ki ka samu. Ke d'in baiwa ce kaman sauran bayi babu wani chanji ko mahaluki da zai chanza hakan matsawar kina numfashi cikin masarautar nan. Dan haka ki kiyaye harshen ki in har kina son ki cigaba da rayuwa dashi a doron k'asa. Your nothing but a slave so stay within your limit"

Ta k'arasa maganan tana jifana da wani k'ask'antaccen kallo kafin ta mayar da glass d'in ta kan fuskar ta ,ta wuce da tafiyar izza wasu daga cikin masu tsaron suka rufa mata baya wasu suka tsaya don tafiya dani. Duk cikin kalamanta babu abunda nake juyawa cikin kwanyar kai na sai sunan King Azrah data kira gatsau babu sakayawa. Tun daga nan na tabbatar da lallai ita d'in macece mai babban matsayi a nan tunda har ta iya kiran sunan sa haka babu shakka babu komai. Tabbas ita d'in na daga cikin list d'ina da zan gujewa in har ina son zama cikin salama.

'Ya Allah babu abun bautawa da gaskiya sai kai, baka d'orawa bawan ka abunda bazai iya d'auka ba, ina rokon ka, ka bani ikon cinye wannan jarabawar.'

Addu'ar dana tsinci kaina ina yi kenan k'asan zuciyata data sama min nutsuwa. Numfashi naja mai k'arfi cike da kwarin gwiwar daya ragemin na fara takawa a hankali ina kiran sunan Allah nutsuwa na ratsa dukkan gabban jikina.

Sab'anin d'azu yanzu wata hanya muka bi y'ar siririya sai gamu mun bulle wajen bayi dake aiki cikin masarautar. Babu wani banbanci tsakanin b'angaren su da damu sai dai girma kawai. Guri ne har guri gari gudu ma'aikata nata kai kawo kace kasuwa ce.

Bakin wata matacciyar k'ofa na hango budurwan nan tsaye da wasu mata sanye da kayan bayi. Muna k'arasawa ta fara magana cikin izza

"Nan ne d'akin ki daga yau. Wad'annan zasu nuna miki aikin ki da kuma dokoki da zaki dinga bi. Dan haka ki kiyaye "

Bata jira amsa ta ba ta wuce bayan ta flipping gashin ta baya. Ban d'auke ido na daga kanta ba harta b'acewa ido na. Saida ta b'ace sannan naji matan sun sauke wani gauran numfashi na maida hankali kansu. Babbar cikin su wadda nake tunanin za tayi Mama Maria ta matso kusa dani da murmushi d'auke kan fuskarta.

" zo muje ya'ta. "

D'akin ta buɗe muka shiga. Wani irin wari da k'ari ya yi min sallama. Da alama an dade ba'a yi amfani da d'akin ba ga wata uwar yana da kura a kursurwoyin d'akin. K'aramin dakine dake dauke da wani tsohon gadon karfe duk ya mutu gefe masai ne ya yi bakikkirin ga wasu uban kyenkyesai suna yawa. Duk rashin wadatar b'angaren mu yafi nan sau dubu. A take naji amai na taso mun. Tabbas na yarda koma wace wannan yarinyar bata kauna ta.

Aiko mak'iyin ka baza kaso ya zauna cikin wannan a kurkin d'akin dake d'auke da abun cutar wa haka ba. Muryar matar naji tana magana da tsantsan tausayi cikin ta

"Ke kuwa y'ar nan meya hadak'i Anita? Babu wanda yake so yaga ya shiga cikin bakin littafin ta don bata da mutunci. Tana da karfin iko cikin masarautar nan saboda alak'ar ta da King Azrah . Gashi naji ance ke sabuwa ce kuma King Azrah ya zabe ki da kanshi. Tabbas sai kin jure don Anita babu abunda baza tayi ba kan EMPEROR EZKE'IL . "

Idan na fuskanci maganan ta Anita nasan King Azrah shima kuma yasan da hakan shi yasa take abunda taga dama?. To ni meya shafeni da hakan?. Kasa jure warin d'akin nayi na fito da sauri ina kakarin amai. Biyoni tayi tana d'an buga bayana ta cigaba da cewa

" wannan d'akin babu wanda ke amfani dashi saboda kazantar sa. Ni kaina nayi mamaki danaga ta ce nan ne d'akin ki. Sai kinyi hak'uri zamu taya ki gyarawa muje na nuna miki wajen karb'an abinci da sauran b'angarori. Layher ku da'n fara gyara mata d'akin kafin mu dawo"

Hannuna ta kama muka hau zagayawa tana nuna min b'angarori dake cikin gurin kafin daga karshe mu yada zango wajen cin abinci. Faranti ta dauka nima ta bani muka k'arasa gaban kanta da aka d'ora abinci . Wani irin fatan wake ne kaman gudawa sai wani ganye da farar shinkafa a gefe.

Yatsina fuska nayi ina bin abincin da kallo. Tabbas indai wannan ne cimar da zan dinga ci kullum na hak'ura da cin abinci. Wannan ai in kanaci kullum sai ka mutu a banza. Kallon yanda matar ke deban abinci take babu wani damuwa a tattare da ita alamun sabo da cimar. A take naji ashe mu kan a aljanna muke dan gaskiya mun fisu wadata suda ma suke cikin masarautar kenan fa.

Karb'an kwanon nawa tayi ta zubamin ganin na tsaya na kasa tab'uka komai. Ita ta d'auko mana abinci muka dawo k'ofar d'aki muka tarar da Layher har sun gama aikin.

Shiga d'akin nayi da ya yi kal yanzu sai warin aizil yake har zanin gado suka dan shimfiɗa kan a kurkin gadon.

"Kinga ya yi kyau ko?"

Kai kawai na d'aga dan gaba d'aya bakina ya mutu tunanin Mama Maria da mak'omata kawai nake. Ko wane irin aiki ne zanyi tunda ba'a sanar dani ba har yanzu.? Matar da na san sunan ta a yanzu da Layher ke kira da Mamee suka yi min sallama suka fice nayi musu godiya. Numfashi naja mai k'arfi na zauna bakin gadon ina bin a kurkin d'akin da kallo.

Hannuna na kai na ciro sark'a ta dake wuya na. Tun sanda Mama Maria ta cire min sark'ar ban k'ara sawaba sai bayan tafiyar ta. Shima kad'aici ne ya dameni na saka ta na tura kasan rigata. Sai nake ji kaman Abbu da Innati na tare dani a koda yaushe hakan yake d'an ya ye min damuwa. Kiran salla azahar da naji anayi na miƙe na fito dan neman fanfo nayi alwala.

Karo mukaci da Layher tana k'ok'arin shigowa tayi saurin ja da baya.

"Yauwa dama Mamee tace nazo na nuna miki inda fanfo yake sai ki samu bokiti da zaki dinga zuba ruwa kina kaiwa d'akin ki"

Kai na d'aga mata na bita ina tunanin wannan wace irin rayuwa ce?. Wajen fanfo ta nunamin nayi alwala ta bani bokiti na d'ibi ruwa na wuce dashi d'aki. Saida nayi salla na d'auko flat d'in abinci na zuba masa ido kafin na runtse ido na tura shi da kyar. In badan ina jin yunwa ba babu abunda zaisa ni cin wannan abinci.

To ranan dai haka na wuni cikin wannan a kurkin d'akin da tunani kala-kala da suka yimin kawanya. Har dare ina zuba ido ko za'a kirani naji matsayin aiki na ,amma shiru har nayi salla isha na takure kan gado bayan nayi Addu'a. Bazan iya cewa k'arfe nawa ba don babu agogo cikin d'akin amma nasan na dade banyi barci ba. Saida na daina jin motsin kowa da komai duk girman gurin ya yi tsit baza kace akwai dubban jama'a a gurin ba.









♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔


Ashanty love.







☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
26/30.




Bansan sanda barci ya d'auke niba ,haka ban dade da fara barcin ba na farka a firgice kaman zan shid'e sakamakon ruwan k'ank'ara da naji an zubamin shi a ka. A firgice na farka ina maida numfashi jikina ya fara rawa a take wani irin sanyi mai ratsa bargon jiki ya yimin salla. Nasan babu makawa sai na kwanta ciwo dan sam bana shiri da sanyi.
Maganan Anita naji a kaina

" barci ki ke?,bakiga ta barci ba. Ki tashi maza ki fito ki same ni a waje. Azrah na neman "

Bata jira abunda zance ba juya ta fice daga d'akin. Da ido na bita zuciya ta na suya. Wane irin wulaƙanci ne wannan kana barci a zuba maka ruwan k'ank'ara a jiki?. Da kyar na miƙe ina rawar dari saboda zazzabi daya rufeni lokaci guda hak'orana har kakkarwa suke. Da kyar na iya cire kayan jikina na tsaya ina tunanin to kayan da zansa fa tunda basu bari naje na deb'o ba. Kaman kuwa taji abunda nake cewa cikin zuci sai gata ta dawo riƙe da y'ar bakko na da nake ninke kayana a ciki.

Tsayawa tayi tsakar d'akin tana k'aramin kallo. Tun daga kan jikakken gashin kaina daya bazu har zuwa gwiwar kafata ya zubo gaba d'aya ya rufe ni. Har zuwa k'afafuwana dana rufe da doguwar rigata dana kare k'irjina da ita. Allah kad'ai yasan abunda ke cikin ranta dan jefo min jakar tayi ta juya ta fice daga d'aki a fusace. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na sunkuya da kyar na buɗe jakar ina rawar d'ari na d'auko doguwar rigata na saka kan jikakkiyar shimita da underwear d'ina da suke a jik'e.

Sosai nake jin zazzabi amma saboda gudun tashin hankali haka na daure na fito da kyar. Karo naci da ita bakin k'ofar sai cika take tana batsewa. Wani banzan kallo ta jefamin tana cire glass dake fuskarta.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment