Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ban fargaba.

A firgice na farka sakamakon mafarki da nayi mai ban mamaki. Cikin mafarkin na ganni cikin wani d'aki mai masifar kyau da akayi shi da gwala-gwala. Kuma abun mamaki kaina nake kallo zaune kan gado kaman yanda itama ke kallo na. Murmushi tayi ta miƙo min hannu kafin naji ta kira sunana 'SULTANAAH'. A firgice na farka ina maida numfashi bakina d'auke da Addu'a. Wane irin mafarki ne wannan kuma?. Gani a zaune gani kuma a tsaye?. Kai na girgiza na yunƙura da sauri na tashi saboda jin yanda masarautar ta d'auki shiru alamun dare ya tsala sosai.

Zama na gyara sosai ina tunanin ta inda zan fara. Ajiyar zuciya naja mai k'arfi na yunƙura da sauri na d'auki bakkona na mak'ale shi cikin k'irjina na nufi k'ofar a hankali ina Addu'a. Turus naja na tsaya bak'in k'ofar na kasa buɗewa saboda zuciya ta data ce 'idan ki ka tafi wane hali ki ke tunanin Mama Maria zata shiga?' .wannan tunanin ya kashemin gwiwa matuƙa na kasa motsi. Hak'ika idan na samu nasarar fita daga nan bansan inda zan fad'a ko hannun wanda zan fad'a ba. Duk rashin dad'in nan yafi dana fad'a hannun wani mugun da ban sani ba. Ko ba komai ina ci ,nasa sutura da gurin kwanciya.

To idan na fita kuma fa?. Numfashi naja mai k'arfi na juya a sanyaye na koma na zauna ina tunanin Mama Maria. Inama dai ina da halin da zanje naga yanda take. Da na samu nutsuwa ko ya ya ne. K'ofar d'akin nawa naji an tab'a kaman ana laluben sai kuma naji an d'an bugata a hankali. Da sauri na miƙe tsaye ina kallon k'ofar. Waye kuma cikin daren nan? Ban gama tunanin ba aka bugu k'ofar a hankali amma sai gata ta balle . Ga dukkan alamu wanda ya daki k'ofar maji k'arfi ne duk da cewa k'ofar dama ba wata k'ofar kirki bace.

Wasu mutane suka shigo cikin bak'aken kaya sun rufe fuska da bak'in abu. A razane na ja baya na buɗe baki zan kwala ihu d'aya daga cikin su ya k'araso cikin hanzari ya toshemin baki da hankici. A take naji numfashi ya d'auke na tafi lu na zube a k'asa.

ANONYMOUS POV.

Baya suka ja suna kallonta kafin d'aya daga cikin su ya fito waje ya yi fito. Saiga wata mace ta bullo daga mab'oya sanye cikin bak'aken kayan kaman nasu ta rufe fuska da mask. Tana shigowa d'akin kallo d'aya tayiwa Nadine dake yashe a k'asa tace

"Ku fito da ita"

Wani irin k'amewa suka yi ta juya zata fice daga d'akin har ta kai bak'in k'ofa ta juyo.

"Ku had'o da wannan tsummar jakar ta ta"

Baki suka had'a wajen cewa "aye captain "

Juyawa tayi ta fice ta barsu suna kici-kicin d'auka Nadine. D'aya d'aga cikin su ya sab'ata a kafad'a D'aya kuma ya d'auke ki kayan nata. A biye suka fice da ita kaman yanda suka shigo a b'oye. Wata hanya dake k'arkashin k'asa suka bi mai tsayi sai gasu sun fito daga cikin masarautar ta can k'ofa baya. Dankareriyar motar da yarinyar ke jiransu suka jefa Nadine bayan booth da kayan ta kafin su buɗe motar su shiga baya . Matar dake ciki taja motar da mugun gudu suka bar gurin.


NADINE POV.

Ruwan sanyin da aka kwaramin shi ya yi sanadin farkawa ta na tashi firgice ina ihu amma baya fita saboda manne bakina da sukayi da salatif. Ban gama farfaɗowa daga sumanmen ruwan da suka shekamin ba naji an d'auke ni da mahaukacin mari da saida naga wuta a take habo ya b'allemin. Gashin kaina aka fincika da mugun k'arfi aka dago kaina. Dishi-dishin da nake gani baisa na gane wake tsugunne gabana ba saida na runtse ido na da k'arfi na buɗe sannan ganin nawa ya fara dawowa daidai. Fatar bakina na furta sunan Anita da babu sauti.

Wani murmushi tayi mun na tsananin mugun da samun nasara

"Me nace miki idan har ki ka sake yin abu da zaki ja hankalin Azrah kan ki?,yau Azrah saboda ke ya yiwa baiwa dana sata aiki hukunci?. Duk irin abunda nake bai taɓa d'aga kai ya nuna ba dai-dai bane sai a kan ki. Wacece ke? Ke ba kowa bace face baiwa kaman sauran bayi. Aina gaya miki idan hakan ta kasance sai kin kwammace mutuwar ki"

Sosai hawaye ke gudu kan fuskata da nake jin b'arin data maren ya kumbura sumtum dan ido na guda d'aya bana gani dashi sosai. Bayan rufe min baki da sukayi harda hannu na da k'afafuwana suka d'aure. Wace irin kiyayya ce wannan? Me yasa ta kasa gane cewar King Azrah babu abunda ya had'ani dashi face tsantsan kiyayya?. Me yasa ta kasa gane kishin da take a kaina duk aikin banza take. Nikam me yasa bani da sa'a a rayuwata ne?. Had'uwa ta da KING AZRAH babu abunda ya jefani ciki sai masifa da tashin hankali.

Lokacin da baisan da zamana ba ina rayuwa ta cikin kwanciyar hankali aikin da nake ba komai bane kan masifar da nake had'uwa ta dashi. Duk abunda ya sameni saboda shi ne. Miƙewa tayi tsaye tana murmushi sai a lokacin na samu damar ganin inda nake. Bakin teku mu ke. Yau garin babu haske ki taurari babu bare hasken wata. Ruwan ya yi bak'ikki'rin baka ganin komai yanzun ma saboda y'ar torch da suke haskawa ne yasa naga fuskarta.

"Ku yi abunda nace daga bisani ku jetafa cikin tekun"

A razane na ke kallonta ina girgiza kai ko zataji tausayi na amma sai ta juya abun bayan ta bini da wani last kallo ta wuce ta barni da wad'annan kartan mazan. Tana b'acewa suka juyo kaina suna wani sinister smile da mummunan fuskar su. Tuni na k'arawa kuka na gunji na fara Jan jiki nan k'asa. Ina jin dariyar su suna bina harda tafawa alamun hakan ya yi musu dad'i. Saida suka bari na wahala duk na kurje ciki da k'afafuwana sannan suka kama k'afata kee suka jani zuwa bakin tekun inda ruwa ke haurowa.

Juyo dani sukayi d'aya ya hau kan ruwan cikina irin ya sani tsakiyar sa bawai zama ya yi ba. Kici-kici na fara ina gunjin kuka sosai sai dariya suke ya kawo hannu kan mad'aurin rigata zai warware. Sosai nake girgiza kai ina kuka na fitar hayyaci. Kiris ya rage ya kai hannu wata irin iska mai k'arfi ta kad'a sai wuff ta d'auke shi tayi jifa dashi can gefe. A rude na d'ago ina kallon d'an uwan nasa daya kai masa d'auki shima iskar ta d'auke sa tayi jifa dashi gefe.

Da wani irin tsoro da firgici suka tashi da mugun gudu suka bar ni nan kwance ina neman d'auki. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Allah ka kawomin d'auki kaga halin da nake ciki. Ka tseratar da rayuwata daga nan. Wossh naji iskar ta kad'a saman kaina kafin naji sunana saitin kunne na dama

"SULTANAAH "

A guje na runtse ido ina kuka sosai . Na shiga uku ni NADINE. Flash rayuwata tamin sanda ina yarinya da nayi experiencing irin wannan abu na d'auka ba komai bane yarinta yasa naji kaman hakan ne.

"SULTANAAH, kar ki damu ina tare dake a ko da yaushe. Buɗe idon ki bazan cuce ki ba"

Maimakon nayi abunda naji sai na k'ara runtse ido ina furta duk Addu'ar data zo bakina. Tabbas yanzu na yarda nayi gamo tun ina yarinya wanda yarinta yasa na kasa gane hakan. Ji nayi kaman anyi sama dani cikin iska kaman hannu yasa ya d'auke ni. Jikina in banda kakkarwa babu abunda yake kafin naji an kwantar dani cikin zunzurutun yashi. Shiru ban k'ara jin wani motsi ba bayan hakan har wajen sakan uku. Jin babu wani motsi kusa dani na fara k'ok'arin buɗe ido.

Kan wata kyakkyawar fuska mai tsananin kyau na sauke kwayar ido na dake durkushe kusa dani. Ido na zaro sosai ina k'ok'arin ja da baya. Wannan idon nasan wannan idon. Idon da nagani a bak'ar ranan da bazan tab'a gogewa a rayuwata ba. Ranan da narasa komai nawa na rasa farin ciki na . Ranan data janyo na shiga cikin k'angin rayuwa. Tsananin firgice yasa na sume.


✿︎✿︎✿︎✿︎


THE PALACE.


A zafafe ya juyo kan dakarun sa dake tsaye tsakiyar fada sun durkushe kansu a k'asa.

"What did you mean she's gone?"

Murya na rawa d'aya daga cikin su yace

"Mun duba kaf cikin masarautar nan bamu ganta ba. Har can b'angaren da take muka je suka ce rabun su da ita tun ranan da aka d'auko ta daga can. To sai kuma wata take ce mana ko taje wajen Maria ne duk da bata tab'a fita ba. Muka je gidan Maria dan mu duba itama bata can"

Da wani irin zafin rai ya sauko daga kan karagar Mulkin sa da yake zaune. Kaman dai koda yaushe fararen kayane a jikinsa riga da wando sai ya dora wata shegiyar alkyabba doguwa da aka kwata da gwals mai madaurai ya had'a madauren gefen kugunsa ya kulle sai k'afar sa dake sanye cikin takarmi sau ciki flat anyi masa ado shima da gwal. Gashin kansa tufke tsakiyar kansa an tufke shi da wani irin band kaman zube dake dauke da crown.

Kai tsaye ya damki wuyan Gaurd d'in dake masa bayani. Da grith teeth yace

"Tell-me- ta ya aka yi ta iya fita daga nan ba tare da an ganta ba?, kuna me?"

Da kyar Gaurd ya iya yin magana saboda shak'a ya yi masa bata wasa ba

"Kayi hak'uri King Azrah kuskure aka samu"

"Kuskure. Kana so kace min sakacin ku yasa ta gudu?, for the first time in history an samu wata ta iya guduwa daga masarautar nan under mai rolling?"

Shiru fadar ta d'auka kace babu dubban mutane a cikin ta sai kakari da Gaurd d'in keyi yaji shak'a barzahu nayi masa sallamad
Tun daga kan King SAIFULMULK, Queen Aira, PRINCESS SOPHIE da Kuma ANITA har zuwa the only one childhood best and brother d'in Azrah, General ALEE . Shi kaɗai yake iya tolerating Azrah idan yana cikin irin wannan yanayin.

"Azrah"

"Azrah"

A zafafe ya yi wurgi da Guard d'in ya juyo kan ALEE dake kiransa. Murmushi Alee ya yi ganin ya samu nasara ya saki Gaurd d'in. Yau kaf masarautar babu wanda baisan Kings Azrah na cikin matsanancin bacin rai ba. Da wani irin k'araji Azrah yace yana kallon su

"Find her, duk inda take ku nemomin ita fad'in duniyar nan. Kar ku kusura ku dawo babu ita , do not come back without her inba haka ba ku d'auki kan ku a matsayin matattu"

Gaba d'aya suka amsa banda Anita dake ji kamn za tayi bingida zuciyar ta zata fashe saboda bak'in ciki. Tabbas zargin ta kan Azrah ya zama gaskiya. Yanzu saboda baiwa yake wannan abu haka. To idan yaji cewar tasa an kashe ta fa?. Kafin nan za tayi duk abunda za tayi ta nuna masa soyayyar ta. Babu wata mace data dace dashi sai ita. Saboda shi ta sadaukar da rayuwarta ta jindaɗi take k'arkashin sa matsayin mai bashi kariya duk saboda so. Bazai yiwu ace wata can k'ask'antacciya ta samu gurbi cikin zuciyarsa saba.

" wai Wacece ne wannan baiwar da duk ka tada hankalin mutane haka Son?"

Bai bawa mahaifin nashi amsa ba ya juya a fusace yabar fadar Alee ya bishi da sauri. Murmushi Sophie tayi ita dama tasan za'a rina.



✿︎✿︎✿︎✿︎



NIGERIA


KANO TA DABO.


"Wai wannan baiwar Allah barci take bata san nunzo bane?, ke baiwar Allah, baiwar Allah..."

Sama sama nake ji......



Book 1 End.


WAI SHIN BAI YI MUKU KAMA DA FARKON PAGE 2 NAMU BA ?🤔😂 . KAMAN YANDA SUKA BUD'E IDO SUKA GANSU K'ASAR EGYPT . GASHI YAU MUN TSINCE MU A 9IGER OO🤣🤣.


YA BATUN KINGA AZRAH?
ZAI GANO ASALIN ABUNDA YA SAMU NADINE?

IDAN YA GANO INDA TAKE ZAI BITA NE KO A'A?WANE MATAKI ZAI D'AUKA?.

NADINE ZATA SAN ASALINTA?

SHIN ABBU DA INNATI IYAYEN TANE NA ASALI?

MENENE ALAK'AR NADINE DA WANNAN MYSTREIOUS ABU DAKE BIBIYAR TA?


YA LABARIN SOYAYYAR AZRAH DA NADINE ZATA KASANCE?

Duk zamu samu amsoshin wad'annan tambaya idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo k'arshen BOOK 1 NA SULTANAAH. Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi babu su littafin SULTANAAH Naira 500 ne kacal babu yawa.

Ga duk mai son biya zai tuntub'eni a wannan number

👇
08140754777

Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin

👇

3078293374
Aisha Sani Danjuma
First Bank

A turo shedar biya ta wannan number

08140754777




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment