Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokarin matsawa inda take

game da Nilfa kuwa koda tagama tabbatarwa dakanta cewa miftahu ne samin kanta tayi ame jin haushi da bacin rai batasan lokacin daxatsaki yafita abakin taba afasace taja hannun Aysha suka fuce tana kokarin fashewa dakuka kullum tagansa saitaji kamar kallon ta yake ba kaya ajikinta bataji xata iya yafemasa akan wawtar daya nuna agareta.

"menene haka Nilfa waye shidin miyasa.....

ranta awani cunkushe tasa hannu abakin Aysha yayin da hawayen dake makale aidaninta suka samu damar sulalowa cike da raunanniyar fuska takalli Aysha
"shi... shine miftahudeen

idanu Aysha tagwalalo waje tana kara waiwayar inda suka baro kozata hangi wannan sambalelen saurayi da Nilfa ke ikirarin shine miftahudeen. wanda suke jin labarinsa, toh miyasa kuma taimasa haka inshine

murmushi Nilfa takuma saki hawaye nakara sulalowa a idaniyanta

"mamaki kikeyi ko to xan warware miki komi yadda yafaru acikin sati biyu kacal danayi agidan mama kawar Abbu na atakaice miftahudeen dan mamane bansani ba shima baisan nice fatima ba, sakamakon bamu taba haduwa ba, sannan abin daya hadani dashi shine.πŸ™„..........................

hannu Aysha tasa tanarufe baki tare daxaro ido kafin takuma mai da kallon ta kan Nilfa bayan jin karshen labarin abindaya hadata dashi din tunkafin tasan shine miftahudeen dinta,
"😍 kai amma gayen nan kyakkyawa ne yasalm barakallahu kaijama ah waidama akwai maxa masu kyau harhaka kuma awannan karnin tab gaskiya miftahu yahadu kawata abi sa xancen gaskiya daxan miki shine kihakura haka kibar komi ya wuce ajone tunda yayi nadama akan lefinsa kuma yafadamiki ba halinsa bane mexaisa baxaki hakura ba Nilfa?

tnda Aysha tafara maganar Nilfa ke tadankara mata uwar harara tamkar idaninta yafado
"baxan iyaba kuma niyanxu nariga dana gama bawa kb soyayya ta banajin inada lokacin wani garan dan iska
dariya Aysha tasa tana rike ciki

"hyyyy heee hyyy tab Ahakan ke yanxu dan faduwar bakar tasa kinji kinagani bacutar makanta bata kuturta amma kike kokarin tabka wannan babban kuskuren toh wlh bari kiji xakisaki reshene ki kama ganye ke ana babbakar giwa ma waye xaijiyo kaurin xomo humm ai tun wuri kima seta tunaninki miftahu kunfi dace wa

tana gama maganar tayi gaba tana dariya Nilfa tajuma agun tana tunanin maganar da Aysha tayimata kafin tadage kafada tafita agurin duka tayi waje bakin get dah taso tsaya wa tajirasu amma xuciiyarta babu nutsuwar hakan kaitsaye damuwarta dayace miftahudeen hankalin ta yakasa kwanciya
kewarsa take da daddadar muryarsa maidadi dasa nutsuwa dik yadda ta ke tunanin ganinsa axahiri ai haryafi haka kyaune dashi tamkar ba bahaushe ba mutkar ba magana yayiba baxakataba cewa ba balarabe bane ko irin kyawawan juruman nan na india
halinsa ne kadai baimtaba tayaya maxan iya manta wannan abin dayamin kenan dawata ce ma banibadin xai iya ganin tsiraicinta haka πŸ˜† kaiiii wayyo kaiii na aa aa miftahudeen nawane nawane nikadai xai iya gani akowanne yanani .

tasa duk hanyenta tatoshe kunnenta xuciyar ta tafarfasa take tamkar tafuto waje wani xaxxafan son miftahudeen ne yakara ninkuwa acikin xuciyar ta gawani nauyi datakeji akirjinta kanta yadau chaji ba abindatake so yanxu sama da hutu.

miftahudeen ne yabiyo bayanta mahmud yarikesa amma yakwace hannunsa yabiyota duk maganganun datake wsu afili take yi ba tuna ni bane kamar yadda take tsammani
kokarin raba jikinta da jikin get din take kabeer dashima futowarsa kenan yayo wajenta
"Nilfa meyasameki
ahankli tabude idaninta wadanda suka kada sukayi jaxur sbda tsananin damu
miftahu dake dan nesa dasu kadan tahango lafin ahankli tamaida hanklinta kan kb

"kaini gida kb kaina keyimin ciwo

"subhanallahi sannu baby gidan su bilky ko gida kawai xan wuce dake

"aa gidan su bilky idan nakoma gida abbu baxai bari gobe nadawo ba ai bawani ciwo kankeyimini ba kadanne kuma dama bacci sbda jiya bamuyi bacci sosai ba

"ok ok muje

dakyar ta iya hawa bayan mashin din nasa kirar liform baki daxanen ja da dan fari fari ajikinsa

miftahudeen bakaramin bacin rai yajiba kenan kb saurayinta ne yanxu dama akan wannan guntun take masa wulakanci yanxu har yayi lalacewar da agunta yakai matsayin tachanja sa kenan dama ita abotar ne tadauka kawai tsakanin su ba ta sonsa da soyayya yau da idonsa yagani tahau bayan wani amashin yasalm 😭😭 yafurta axafafe kaitsaye motarsa yanufa dake fake agefe dashi wasu xafafan hawaye nakokarin xubo masa amma yana danne xuciyar sa
bayajin xai iya xama namiji mai rauni baxaitaba bari yaxubar da hawayen sa ba mata basu da tabbas basu dakirki....

yana kokarin tada motar imam yakaraso dagudu gudu ya bude gidan maixaman banxa yaxauna kafin yakarasa rufewa miftahu yaja motar amilyan.

"me yasameka ne Dr wai meyasa baxaka rinka nutsuwa akan lamarin nan nakuba nifa yanxu har kunfara bani haushi yakamata kadai daita tunda kunsan ko suwaye ku a ma amalance

agefen hanya miftahudeen yaja wani wawan birki wanda saidayasa hantar imam takada yarike kansa ganin sun kusa tunkusar wata rumfar mai shayi
"😑 mata basu da burin daya wuce suga suna disgamu imam Nilfa dama batasona damacan tunkafin tagane waye ni batasawa ranta sonaba abota kawai tarikeni da ita bantaba tsammanin hakaba imam bantaba xaton haka ba saiyau ashe Nilfa na xata iya soyayya dawani baniba dama sotake taxurmani daga karshe tabani sonta yakasheni tariga datayi nasara akaina sonta yagama illatani imam babu komi akirjina face ita da Soyayyar ta.
ruko kafadunsa duka biyun imam yayi cike da lallshi yafara masa magana
"ohhh sorry! naji naji amma ina maitabbatar maka cewa Nilfa tanasonka kuma duk abinda kaga tanayi badan tanason kb bane kai takeso kabarta xuwa wani lokaci xata hakura

"aa baxan iyaba imam tayaya xanbarta dawani kato yana janyemin hanklinta baxan iyaba inason my Neel banason wani yarabeta daxu danagansu wlh jinayi kamar xanmutu dan Allah kaje kafadamata inasonta imam rasa Nilfa tamkar rasa rainane
dafe kansa yayi hawaye suka xuba bisa fuskar sa
"😭😭imam xafi kirjina yakeyi muje kasaukeni agida

"ya rabbi?!! aboki dan Allah ka kwantar da hankalin ka xanmata magana insha Allahu
"ok
kawai miftahu yace tare da dindikawa yakoma back sta yakwanta tare da kankame jikinsa sakamakon wani bakon sanyi sanyi daya xiyarcesa lokaci daya kafin sukarasa gida kuwa xaxxabi maxafi yarufesa sai hosptal suka wuce daganan imam yakira mama awaya yafadamata halin da miftahu yake ciki

hankali atashe taxari key ta fice lokacin kaka tumma na makota taje jajen yaronsu daya bata kwana biyu tsakani akagansa.

bayan sallahn la asar Nilfa tafarka daga nannauyan baccindayayi nasarar saceta lokacin da kb yakawota taxo takwanta adakin bilky wanda ba mutane dakyar baccin yasaceta sakamakon tunanin daya dawo mata sabo dal.

musalin karfe tara akagama shaga gurin walima awa uku darabi akagama komi yayin da akafara daddauko jama ah ana dawo dasu Nilfa natare da kb amma hanklinta nakan jama ah tana dubawa koxataga miftahu amma har kawo yanxu da ake haramar tafiya bataga koda maikama dashi ba yagifta hanklinta bakaramin tashi yayiba shin ina yake? meyasa baixo ba? lafiya ma yake kuwa? tamkar tayi kuka haka takoma gabadaya takwance daurin dankwalin da akamusu agidan kwalliya saimayafin tadora akanta dankwalin kuma tahada dajakar ta duka ta rumgume akirjinta rantaduk adagule.
kb yayi rarrashi har yagaji amma taki sakin ranta haka koda yadawo da ita gidan su bilky batasaki raiba sai ma shigewa datayiwa cikin gida tabarsa anan ko sallama babu.

Aysha da meenal sunkasa gane kanta su ma haka suka kyaleta kowa yakwanta amma idonta biyu. wanka taje tayi sannan tasa doguwar riga na bacci tahaye gadon bayan meenal takwanta tare da rumgumar wayar ta
tanaji tamkar ta rumgumi miftahudeen.

washe gari suka kai amarya cikin garine gidan ta yahadu sosai bakaramin kokari mahmud yayiba
khalil naganin antyn nasa yarugo dagudu yana dariya

"anty anty kindawo ko

tadaga masa kai tare da rumgumar sa
"nadawo kalil amma banajin dadi dan cikani naje naga mami
hannun ta yarike sika shiga harcikin dakin mami dake kokarin tada sallah
"au har an gama bikin ai tundanaji ehunsa nace toh kece hala.
"wlh mami angama har ankaita gidan yayi kyau kuma

"haka akeso ai maxa kije kiyi sallah don kexamu mabari agidan nida abbun naku fita xamiyi

ashagwabe Nilfa ta fuskanci mami tana kokarin yin hawaye

"daga dawowata mami inakuma xaku dan Allah ni wlh banaso abarni jiran gidan nan nidaya wani lokacin inajin tsoro musamman irin lokacin nan bayan mangaruba

"toh maye nakuma yin kuka aciki uwar tsoro da anmagana kice ke tsoro kikeji ke tsoro kikeji ai shikenan saiki bada himma watarana dai aure zakiyi kuma dole kixauna agidanki, kuma kinajina dama hosptal xamuje dubo muftahu idan kuma xaki toh aisaiki je kiyi sallah kafin abbun naku yashigo daga masallaci
"tohm mami

tamike tana sharar hawaye fisabilillahi dik shagwabar ta kam ba maganar xa abarta jiran gidabane yabata kuka aa tunanin muradintane yakaryar mata da xuciya yasa hawaye fara xuba a idaninta tabbas tanasonsa miyasa baxata yafe masa ba hala akanta yake kwance a hosptal idan har wani abu yasa meshi baxata taba yafewa kanta va .

game da mami kuwa girgixa kai tayi bayan futar Nilfa tana mai mamakin shagwaba irinta ta ko me kuka take masa da abin kukan da wanda baikai ayi kuka ba abikankani kuka yake sata ko magana ce kuma koda da khalil abuyahadosu yanxu xata mike kafa ta hau kuka tamkar anmata mutuwa badan mami na kwabarta bama da yaya uwaisu

abbune yatarota da gudu tafada kansa tana murmushi

"shigowar yaushe ne fati

murmushi tasake yi tana gyara xamanta akan kujera

"daxu abbu ai lokacin katafi masallaci nashigo gaskiya nayi kewar ka abbu gaskiya baxan sake yadda nayi tafiya irin wannan ba nabarku har kwana uku taf

dariya abbu yayi yana shafa kanta

"aa fa domin kuwa aure xanmiki nan da dan wani lokaci kuma inaso kiyi xaman ki agidanki lfy ba yawace yawace nixan rinka xuwa naganki

kuka tasa tana diddira kafafu

"wayyo abbu wayyo abbu raina batason wannan maganar ni banason auren fa abbu daku da mami da khalil xanxauna pls karkamin aure abbu na

damamakinsa yakalleta ganin da gaske take yasa yace

"ohhhh toh ya isa ya isha shikenan yanxu kam xanbar maganar kinji kafin kigama girma ko ai yayimiki ko

tayi murmushi tana linshe idaninta
mamice tafito tanasanya hijabi sannan suka fito dukansu suka nufi farfajiyar gidan can bangaren jera motoci domin tafiya.
kaitsaye gidan mama suka nufa domin tasanarwa da abbu sundawo gida aikwanansu biyu ma a hospital din kwata kwata.

suntsaya gurin maikayan marmari suna saya dayawa sannan abbu yashiga wani shopdrinks yakwasa kayan roba da manya manya bosket sannan yasama suma iyalin nasa nasu kason sannan yadawo suka cigaba da tafiya Nilfa da khalil na gidan baya suna shan ascrim

πŸ‹πŸ‹πŸ‹
ke ba ai wlh kikiyayi son maso wani bakyadaukar shawara kokadan koda xankwana inafadamiki baxaki dauka ba ban san wacce irin xuciya ce dake ba safna

safna ahankli tadaga kai tana kallon yayarta marwa dake tsaye akanta tana mata maganar da alama ranta abace yake donhaka baxai sabu ba taxo tace xata xaxxage kwandon haukanta akanta ba don itama ba dadin takejiba

"kina kallona ko anmiki karyane bahaka bane ehhye toh wlh yaxama dole kinutsu kiba Saheel hankalinki tunkafin kijajamana asara inba wahalalliyaba me xakici ma agurin wani likiti duk da bansansaba amma nasan kwata kwata albashinsa nawane watakilama wani mugun gajane ma ko toh koma maye nafadamiki wlh baki isa kimana asarar arxikin daxamuciba agurin Saheel dan minstan kudine fa yoke wacce irin dakikiyace ma wai safna

kyakyacewa safna tayi dadariya harda bugun kujera dariya take sosai harda hawaye kafin marwa tabige da kallonta xuciyar ta fal tunanin ko dan shegiyar mayen likitan nan data likewa ne sonsa ya haukata mata kanwa. gamamakinta saitaga safna lokaci daya tatsaya da dariya tana kallon ta sama dakasa tana murguda baki kafin tace me marwa ta dane mata lebina da hannunta cikin xafin nama
rike bakin safna tayi tana mike waranta abace

"wlh kifita aharkata mutkar kina neman girmanki idankuma bakyanema toh wlh xanhau kansa na tattake ina ruwanki da rayuwata kitattara taki mana kiji da ita amma xaki bage da hakkewa tawa toh banason Saheel din nafada ke kisoshima na idan harkinji haushi dariya kuma nayi dole nayi tunda naji wani abu dakunne baxai dauka ba wai Dr muftahu na ne gaja harkina kiransa maikaramin albashi hhhhhhhhhh

bakisan sa bane shiyasa amma amsarki tana nan xuwa saikintaba ganinsa saiki samu amsarki atare dashi bari narage miki nauyi sbda karkita tambayar kanki kowaye shi Dr miftahudeen yafi ajin kanwar ki safna nice nake sonsa haryau banajin Dr yafara sona inadai kokarin dik yadda xanyi nayi domin ganin na samesa sbda inasonsa dani yadace ba Nilfa fa kamar yadda naji yana yawan fadar wannan sunan idan muna waya baruwanki dani anty marwa kibar harkata inbaha ba kuwa hummm wl.................

"inbahaka me?? ishashshiya? cigaba kinsata agava kinamata rashin kunya ko akan wani vanxan baxara ko toh cigaba nace kinji

momynsu kenan dake sakkowa daga benan tai maganar cike da fushi tare da tsare safna da ido wacce tai shuru tana jabaya marwa kuwa kuka tasa tana fadawa jikin momyn

"bakuka xakinayiba idan wannan tabbatacciyar mara mutimcin tamiki wulakamci ki dakamin ita tayi laushi tafahimci kece gaba da ita har yau ba don ta fiki tsayi tagane bashine yake nufin tafiki shekaru ba donshashanci kuma kin shigemin jiki kina kuka.

marwa tadago
"MOMy xagina fa takeyi yanxu kamar ni safna ke xagi haka ma shekaranjiya sbda suna waya dashi nakwace wayar kokawa takamani dashi saidana bata wayar sannan ta cikani haba momy yanxu kuna kallo yadda take abindatake so agidan nan

safna ta murguda baki tana fadin

"anyi din ke uban wa ke maki magana idan kinkawo samarinkan banxanki naga har futa kukeyi dasu kuma waya miki magana ehhye toh.......

momy ne tadau chaja tayi wurin datake aida gudu safna tarugu tana kunkuni tare dafadin

"wlh baku isaba bamai hanani auren Dr muftahu kaf gidan nan.

"don ubanki nice kuwa domin kwa bakida miji face Saheel banxa shasha sha ina matsayin uwarki ina magana kinayi sbda neman albarka toh bari abban naku yadawo wlh ko bakyaso saina sa ankawo kudin.

marwa tai murmushi tana kama hannun momyn suka xauna kan kujera tana fadin

"yawwa momy dakin kyauta ai kawai sukawo kudi atsai da ranar aure awuce gurin natabbata munfito gari muma acikin manyan mata xamushiga gidan minista muyi yadda mukeso

"shiyasa ai nake sonki sbda kece kikayo irin halina maganarki dutse 'yata kinga da angama wannan saimu fara shigo dakaya muna rabawa matan manya manyan nan

suka fashe da dariya.

WACECE SAFNA.

'ya ga Alhji ashir mutum maikiriki maitarin rufin asiri domin kuwa dan kasuwane yanasamun kudi sosai aharkarsa ta atamfafi da less da shaddoji anan cikin kasuwan kwari gidansa mekyaune domin kwa yakashe kudi wajen ginasa
matarsa asma u wacce sukayi auren saurayi da budurwa macace mai son kudi dahange nagaba dakai bata da aiki sai hangen matan masu kudi wadanda suka fisu komatan sanatoci da ministoci tana da shishshigi da son abin duniya yaransu uku da alhji ashir nafarkon shine Auwalu watansa uku da haihuwa yamutu bayansa ta haifi marwa da shekara uku tsakani sannan ta haifi safna.
kokadan batadora yaranta aturba tagari kullum hudubarta shine tasa su roki abvansu kudi ko kannan babansu insunxo dadai sauransu tunda kwa suka girma tadora buri akansu saimai mulki ko sarauta xataba yaranta musamman safna datafi marwa kyau

samari dadama masu kudi sunxo gurin marwa amma ta koresu tace sai manya masu nera sosai gashi har marwa tagirma yanxu shekarunta 27,
maxan sinja baya gashidama batada farinjini kamar safna
safna shekarunta 23, sun hadu da Saheel tun kafin tayi canday suke soyayya sosai tana sonsa yanasonta maganar aure harta ratsa ciki amma watarana taje bikin kawarta wani anguwa toh gidan su kawartata na kallon gida su muftahu yafito kenan xashi masallaci sallar la asar dama ranar ba office takasance lahadi
tunda tayi arba da shi takwarewa Soyayyar sa taji duk duniya inba shiba saidai amutu tundaga ranar duk lahadin duniya saitaje unguwar har tafara masa magana tunbaya kulata har yakulata
sbda tace ita 'yar uwar su halisa c e ma ana makotan nasu kenan sam baidauki abun soyayya ba don koda ta furtamasa bai aminceba saidai yafadamata akwai wacce yakeso bayajin xai iya jera soyayyarta da tata tayi hakuri
safna tacigaba da naci amma ina hhh abin yaci tura hargwara ma yanxu yanadan sauraronta awaya suna magana kamar MASOYA dik dayakance mata shifa dan Allah tabar maganar soyayya tsakanin su.
WANNAN KENAN
MUJE MAXA CIKIN CIGABAN WANNAN LABARI YANXU AKAFARA KAFCENFA DOMIN KUWA NILFA BAXATA BAR MA SAFNA miftahudeen BA GEFE KUMA GA KABEER TOH YAYA DAI YAYA DAI MUJE XUWA πŸ˜‚πŸ˜‚

mama taji dadin yadda abbu yadebo gidansa duka domin xuwa duba dan lelenta miftahudeen

afalo suka same ta da kahka tumma suna kallo bayan angaisa ne tarike hannun Nilfa tana tambayarta karatunta
mamice take tambayar ina miftahudeen din

mama tamike tana yimusu jagora xuwa dakin nasa gabadaya Nilfa saitaji kamar takwace hannun ta daga na mama amma ina mama tama manta da tarike hannun Nilfa sai hira sukeyi da abbu tayaushe gamo suna tafiya gab daxa sushiga dakin Nilfa tadanja hannunta tana fadin

"mama bari nadauko wayana nabarsa amota

kafin mama taimagana na xare hannuna najuya dasauri ina sakin ajiyar xuciya lallai na auna sa ah yau kam domin bashakka dana sake naje baxan iya boye damuwa taba akansa, tabbas xanbada kaina hala shi bayamin irin wannan axababben son danakemasa
"aa Nilfa yadai xakiyi ciki dani kina gani kuwa anya kawata

maganar kahka tumma ta dawo da ita hayyacinta

"am umm ammm laaa aibanganiba sannu inasauri induba wayana ne

"aa bakomi ai xauna muyi hira kafin sufito barshi cutar gulma ne ai ba wani abu ba shida mamansa su sunsan komenene matsalar tasa amma ba wani ciwo bane nadamuwa

Nilfa tayi murmushi
"Allah sarki
"humm niko ina kabeer ne fatima kinaban labarinsa kuma kikatafi gida 'yar nan gashi nikuma har yau bansamu muftahu yakawoni ba

"yana nan ai watarana xan kawosa yagaidaki saimun samu hutun islamiyya

"toh aikwa danaji dadi kyajimu da 'yar albarka kinga ke aurenki xakiyi ki huta shiko wannan sangartaccen jikan nawa bai da aiki saiwaya da kuma wannan abun da akeyi yanxu ana rubutu din yadukufa wai da kawarsa yake ni yama take ne neel ko meef kai namanta aikinga baidau hanyar arxiki ba

Nilfa takusa dariya tana murmushi tana kallon tumma dake tafama da farfeson kaji tana bata lbari
tunda suka shigo aka kawo musu farfesun da abinci amma kadan suka taba.

sunata hirar su taga fitowar mama da mami da abbu sai khalil hannunsa na cikin na muftahu mikewa nayi dasauri xanrigasu fita sai sallama nakeyima tumma muna murmushi

muftahu kwa ya kafe ta da idanu jiyakeyi tamkar yakamota jikinsa sbda yadda wutar sonta ke ruruwa acikin xuciyar sa

badama cigaba da ganinta kuma tana sharesa bakaramin tada masa da ciwo yake ba ganin yana kokarin faduwa yasa kawai yayiwa su abbu sallama yakoma dakinsa yana dafe da kirjinsa mama takula sosai da yadda yake kallon Nilfa dakuma yadda takixuwa dubasa take kuma kakkau dakai tabbas itace matsalar dan ta kuma xata yi duk maiyuwuwa domin tajawo masa hankalin ta,
duban Nilfa tayi tana fadin

"aa lfy kuwa Nilfa banga kinje kinga jikin yayan nakiba kodai fadan aka kumayi? ku sarakan fada

murmushi tayi tana sunne kai abbu yace

"jeki maxa kidubasa kifito bari mujiraki

bayadda ta iya sun sata atsakiya dole ta fara jan kafafinta tanufi dakin

miftahudeen dake kokarin shiga tolet karaf wadannan maganganun akunnensa donhaka yafasa shiga yakoma yaxauna kan gadonsa

ta isa kofar amma bata budeba saidataga abbu yakusa juyowa bangaren sannan ta bude tdan tsaya kadan da nufin iya nan xata tsaya sannan tadawo kawai kamar daga ciki take

miftahudeen yana hango mayafinta amma bata shigo ba ganin xata koma yasa dasauri yamike yarikota gabadaya yajawota ciki tafado kansa.

"kingani kekike jawowa harnake tabaki miyasa miyasa menayimiki har yayi xafi kixo kidubanin kawai yagagara baxan iya hakuri ba kinsan ina muradin son ganinki baxan iya hakuriin ganinki ki koma batare danasa idanuna acikin naki ba haba my Neel sonawa kikeso nafadamiki ninefa miftahudeen naki nine fa nell yah muftahu naki
πŸ€”πŸ€” ikon Allah
Nilfa tayi lamoo jikinsa tana sakin ajiyar xuciya tamkar wacce tayi gudu tagaji

janye jikinta tafarayi tana kara diddintse idaninta sbda kunyar hada ido take dashi tabbas taji wani abu jikinta sosai gabadaya gajiya tarufeta bata bukatar komi face tacigaba dajinta afaffadan kirjinsa saidai xatai abin kunya sabda rauninta baxata dauki wannan dabi un da miftahudeen ke kokarin koya mataba
kokarin futa take amma
yakuma jawota wannan karon batabarin ya hadata da jikinsa ba ta kwace da iya karfinta
. "ya isa ya isa miftahudeen baxantaba sauraronka ba kaje karike irin taka rayuwar xanrike tawa baxakataba daina taba jikina ba haka xalika nima baxantaba tsayawa domin sauraronka ba

"xaki kashe ni kuwa domin baxan iya daukar hakan ba soyayyar ki abincinace jin na kusanta da jikin ki kuwa tamkar mahadin numfashi nane ki guji nikuma tamkar kinrabani da dikkan farin cikina ne Nilfa inason ki

"bana sonka,

tafirta tare da ficewa aguje. kadan tadan dai daita tafuce afalon kowa yadawo da hankalin sa kanta kawai ganin ana kallonta yasa tasaki wani kuka tare da ficesu da gudu tabar falon gani take kamar sunji abindayafadamata kuma kamar suna kallon yadda ya rumgumeta ajikinsa kukanta yakarune tina yadda takuma baro miftahudeen batare data amincewa soyayyar sa ba hasalima tafadamasa ta tsanesa bahaka bane inasonka wlh inasonka tafada afili tana makarasawa jikin motarsu tajingina hawaye basu fasa xuba ba.
don me xakaxama haka bazantaba auren maxinaci ba

mama da duk wanda ke falon sunyi mamakin yadda tafuto ta. kamar wacce aka tunkudo gashikuma ankalleta tasaki kuka tafice abbu xai magana mama ta daga hannu

"soyayya ce atsakanin su amma har yanxu sunkasa fahimtar junansu naso sundaidaita sannan nasanar maka da maganar amma yanxu yakamata muyi maganar kawai

komawa sukayi akaxauna abbu murna sosai yakeyi mami ma tayi farin ciki kumadama tafahimci hakan agurin Nilfa kawai tabari taga gudun ruwansu,
tumma ma tayi mamakin jin fatima ita ce Nilfan Dr muftahu sun daga karshe mamace tafuta tataho da Nilfa tana lallashinta
miftahudeen takira suka hadasu guri guda mama tace
"wai miyasa idan har ka gamo da fatima saikasa ta kuka babana fadamin dalilin hakan bayan kaidakanka kafadamin soyayya kukeyi kanasonta tun lokacin baya datake matsayin Nilfa wacce kuka hadu online
yasunkui dakai
yanajin kunyan abbu da mami
"nifa mama ban mata komiba kawai shagwabar tace

mami ta ce

"kifa dena titsiyesa dan Allah waye babba ita dashi kuma kema fa kinsan rigimar Nilfa magana mai dadi ma kuka takesata danhaka yanxu komi yawuce tunda kunason junanku toh kudai daita duk wata rugima tawuce kawai

mama tai murmushi
. "aa kintare wa danki kawai ni ba atambayi yarinyata me yayimata ba take fushin dashi ba
. abbu ya harareta

"rabu dawannan 'yartaki hafsa ai bataji rigimar ta sai ita sannan kuma kai miftahudeen naji dadin wannan abu xuminci yayi dadi tunda har anje ga irin wannan mataki saika dauri kayi hakuri dakanwar ta ka Allah yabamu sa ah ko

sosa kansa miftahudeen yake kansa duke Nilfa kuwa tamkar ta kurma ehu sbda angama daddaureta da jijiyoyin jikinta kama hannun mama tayi tana kuka tana girgixa kai amma ina abbu yamike mami ma haka ana ta farin ciki musamman kaka tumma sai tsokanar miftahudeen take amma baikulata satar kallon Nilfa kawai yake

koda ahanya dawowa Nilfa batace ufam ba tanaji mami da abbu namaganar

bacci yakauracewa idaninta batada nutsuwa kokadan mutkar ta auri miftahudeen yaxamana cewa bata yiwa kb adalci ba batakayauta ba taxama mayaudariya kenan?
wayanta ne yafara kuka da neman dauki
sabon numba ne kuma batasan kona waye ba ankira yafi sau biyar sannan tadaga
"😚hello
"πŸ€—my Neel bakiyi bacci ba ashe
hummm tasaki ajiyan xuciya😏
"banajin xakataba samun abin dakake tunanin samu miftahudeen daxaka saukakawa kan ka wahalar dake gabanka tahanya mafi sauki kasanarwa iyayenmu baka sona domin kabar ginin tum ran xane kb nake so baxan taba amin ta dakaiba niba irinka bace

"😣hmmm shikenan toh naji amma maye dalili yayi maganar kamar yayi

Please Login or Register in order to submit comment