Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata taba ganin bacin ran daddy irin haka ba,
Ta sake fashewa da kuka tana hada hannayenta
Bankula shiba daddy wlh bance masa komai ba
Tai maganar cikin shagwaba da sharar kwallah yanayin dayafi kowanne yanayinta daukar hankalin alhajin don haka bakidaya yakasa jurewa so yake kawai yajita ajikinsa donhaka jawota yayi jikinsa yana rumgume ta da sunan rarrashi
Duk dataji matsewar tayi yawa amma haka tayi lamo sbda fatanta yanxu kawai daddynta yahuce aranta ma addu ar hakata ke
Game da Alhaji kuwa jin saukar 'yan matasan berest dinta ajikinsa yakara hura wutar kaunar ta da muradin ta acikin xuciyar shi, diminsu ke masa naso akirji yanajin tamkar daganan yawuce da ita daya daga cikin gidajensa ya huta da ita amma bayanxu ba akwai lokaci idanunsa duk sun chanja kala matsa hannunsa tayi
Daddy na kayi hakuri baxan sake ba in sha Allahu karma kafadawa mama don Allah karta min fada itama
Tohm yace
Kawai cikin daure murya tare dajanyeta daga jikinsa yana kau da fuskarsa daga gareta sbda karta gane halin dayake ciki yafara tuki suka tafi gida,
💚
Taku akullum Shamsiyya wacce kukafi sani da UMMU ARYAN
Kucigaba da kasancewa tare dani awannan labari nagode
💚
Washe gari dataje makaranta tana xaune sai duba karatuttukansu nabaya take sbd jarabawa xasuyi nan da one week hussaina ce tashigo class intana baxa ido taga ta inda xata hango kawarta ta aikuwa can ta hangota da sauri takarasa tana dala mata duka abaya
Kee besty amma wlh kina da whiteblood gaskiya
ATsorace Ismat tadago, tana dafe gun da hussaina tadaketa sbda bakadan taji xafin dukan ba daurewa kawai tayi sbda akwai rigimar su da ita akasa dama,
Xaikwa hadani da daddy na
Tai maganar tana hararar hussaina
Ita ko xama tayi tana kallon Ismat akaikaice
Ban fahimta ba besty menene laifina don annuna anasonki nakarfafa gwiwa ga mai nemanki?
Sauke numfashi Ismat tayi tana kama hannun hussaina
Laifi kikayi mana sbda nasha fadamiki ai cewa niban isa yin soyayya ba kwata kwata shekara na nawa 17 fa kacal kuma bayan hakama daddy yace karnasake nafara kula samari har sai ya fadamin dakansa tukunna amma yanxu gashinan garin danbanxan surutu na jiya nake fadama daddy nayi saurayi karkiso kiga yadda yafasata har yanxu danake baki labari fushi yake yi dani nabasa hakuri nabasa hakuri yaki saurarona, kuma idan nagayama mama itama fada xata min narasa menene yake damuna hussaina daddy na shine farinciki na sbda wlh nashaku dashi tamkar mahaifina daya haifeni.
Tana gama maganar tadukar dakai kasa tafara kuka
Hussaina banaso nabatawa daddy rai sbda shine gatanmu yarike mu tamkar shine ya haifemu wlh hussaina yadda daddy yake sona yake bani kulawa baya nunawa cikin mama daddy dik abin dana keso yake yimin shi meyasa xanbata masa rai dan Allah kibani shawara
Dago mata kan hussaina tayi tana share mata hawayen dadik yabata mata fuska sam ita batadamu dasauran class mate insu dake kallonta ba
Subhanallahi nibanyi tsammanin abin xaikai haka ba wlh nifa dalilin dayasa nabasa numbar ki danaga mutumin kirki ne kuma yanada yanayin kamilan mutane da alama kuma ba irin samarin nan bane 'yan abi yarima ashakida, amma yanxu dan Allah kibar kukan nan haka kiyi shuru Allah yakaimu atashi aschool sai muje narakaki office in daddyn mubashi hakuri saina masa bayani
Murmushi yabayyana afuskar Ismat tafara share hawayen tana kankame hannun hussaina tare da cewa
Yawwa besty wannan yayi nasan indai kikaje kika masa bayani xai hakura yadaina fushi da dotar tasa,
Lakace mata hanchi hussaina tayi tana cewa
Ke wallahi shagwabarki tayi yawa shiyasa kuka baya miki wahala
Eh anji din nidai dan Allah kitabbatar min xamu wurin daddyn
Ismat tai maganar cikin muryar rauni da son kuka
Eh karki samu masala Allah xamuje
Tagyara xamanta ganin anty maryam tashigo duk suka mike class din sunagaisuwa kafin ta amsa suka xaxxauna akashiga karatu.
💚
Sakatariyar Alhaji sanam ce tashiga office din nasa tare dasanar dashi yayi baki yabata damar yimusu magana akan sushigo
Ismat da hussaina ko wacce narike da hannun jakarta dake goye abayanta saman kan dan karamin hijabin makarantar nasu kalar blu riga milik wandon ma blu ne amma irin blublack.
Suka shiga kowacce bakinta dauke da sallama
Sakin murmushi yayi ganin Ismat sbd mutkar xaiganta xaiji xuciyar sa tayi haske dik wata damuwa tawuce masa daga rai
Gaisawa sukayi sannan hussaina tashiga yimasa bayanin dik yadda akayi sannan tace hakan baxaisake faruwa ba,
Bakomai ai yawuce dama nafiso tamaida hankali akaratune kulekulen samari kuma baxai barku kuyi karatu yadda yakamata ba har afito dasakamako mekyau to kungani akiyaye nahakura
Jin haka yasa Ismat yin murmushi kyanta yakara fitowa
Daddy tnx and kuma baxankara ba narantse
Karki damu my dota ainasanki da alkawari
Duka sukayi dariya harda hussainan
Tohm antashe kune aschool din ko kuma kun gudo ne
Ismat takalli hussaina suna murmushi
Daddy Allah antashe mu kuma duba time kagani ai yau friday shiyasa kaga kamar yayi wuri
Yatsare ta da idanunsa tun datafara maganar yana kallon dan karamin bakinta mekyau wanda tashafawa manlebe saikyalli yake, hussaina ce tadago tana kallon sa amma shi sam baikula ba da tagannsa ba Ismat kuwa tana tawasa dajakarta kanta akasa hussaina ce tamotsa muryar ta kamar wacce wani abu yamakalewa amakogoro, sannan yadauke idaninsa dagakan Ismat yana magana adan waske sbda yaga hussaina nayi masa wani kallo dakokarin gano ainihin manufarsa.
Ok ok gud aishikenan kidauko muku ruwa mana a freezer saikusha kudan huta kutafi
Mikewa tayi tana nufar freezer din tare da shagwabewa
Nidai gaskiya daddy yau ina nan harka tashi mutafi gida tare
Dasauri hussaina takalleta cike da mamakin ta
Kuwa gogan naka murmushi yayi yana cewa
Bakya ganin kawarki ita agida xa amata fada ace tadade karki ma kawarki tawaye sbd kinga daddynki
Tai dariya tana mikawa hussaina ruwan aglass cop itma taxauna tanasha
Aa ai mommyn hussaina baxata ce komaiba idan har tace mata muna tare a office wurinka
Hussaina ce tai saurin amsar maganar
Aa gaskiya Ismat akwai inda xanje daxararr nakoma gida yanxu don haka xantafi kawai kekitsayadin saimun hadu school ran monday,
Rike hannun hussainan tayi
Kai dan Allah hussaina yanxu baxaki xauna ba
Allah Ismat unguwa xani naga nafadamiki a class harnace xaki rakani kuma kinga aiken na mommy ne kinga badan haka ba ai xanxauna karki damu besty Allah kinga kuma dakinxo kema kawai muntafi tunda dama kinga kince xaki rakani sai dai bansaniba kokin fasa tunda nashiryaki da daddyn ki ko
Daddy yadanyi yake sbd baikai ciki ba Ismat tajuyo takalli daddy tare da shagwabe fuska shiko tunda yaji ta inda hussaina ta bullo ransa yabaci yaji tsanar ta kuma da alwashin rabata da ismat
Daddy na kagadai hussaina taci mu da yaki ko
Wani murmushi yayi wanda yatsaya iya fuskarsa baije cikin ransa ba
Shikenan aidama rigimar kice dota ungo wannan kuhau napep
Ta amsa tana masa bye bye suka fito
Gidan su Ismat suka sauka sunko tarar mardiyya mai aiki takammala girkin lunch anan suka cika tinbinsu
Ismat tayi wanka tashirya cikin bakar doguwar riga mai duwatsu sama dakasa tai rollyn namayafin rigar asaman kanta sukayi wa mama sallama saigidan su hussaina dama tayi wanka agidan su Ismat don haka shiryawa kawai tayi mommy tabasu aiken suka tafi
💚
Ahanyar su tadawo wa dai dai masallacin shehu aka saukesu me napep hussaina nadago kai tahango Mihran amachen insa kirar liform yanufosu dasauri ta dauke kai tana kallon Ismat dake sallamar dan adai daita sahun.
Muje inkingama basa kinga magrub nadosowa fa
Tana cusa chanjin ajaka tajuyo ga hussaina fuskarta dauke da murmushi kamar yadda take kenan ba araba Ismat da fara ah sam ita batason bata rai ba ko fushi tanada fara ah sosai shiyasa take dashiga rai
Dai dai lokacin dayakaraso wajen nasu sukuma xasuciga ba datafiya yatare gabansu
Assalamu alaikum Dan Allah kuyi hakuri natare muku hanya wallahi tundaga tsallaken titi nahangoku ansaukeku napep nace bari nakaraso mugaisa tunda tunwancan lokacin dakikaban numban Ismat batashiga kodayaushe nakira sai ace akashe baiwar Allah barka dayamma
Yakai karshen maganar yana kallon Ismat
Harara takwala masa tana kama hannun hussaina
Kinga malama xo mutafi kintsaya muna wani saurarensa saikaudi yake ma mutane
Hussaina tadan ja birki
Dan Allah kayi hakuri wlh daddyn ta yahanata kula samari donjiya har kusan dukanta yayi atunaninsa ta saurareka
Subhanallahi yace yanakallon yadda suka gewayeshi suka wuce kafin yakuma cewa wani abin, bin bayansu yayi dakallo yanakara jin yadda soyayyar Ismat ke tinxirasa yabisu kirjinsa har wani xafi yake sbda baxai iya jure yarasa ta ba itace mace tafarko daya fara gani takwanta masa yaga xai iya auren ta kuma har ummansa yafadawa donhaka dole yasamo wata hanyar amma baxai rabu da ita ba,
Kwance take akan lallausan gadonta wanda yasha bedshit blublack yau kam tanajin son kunna wayarta tunda sungamu anfadamasa batafara kula samari ba kuma da alama yahakura tunda baisake yunkurin biyo suba, dama takashe wayar tane sbd tunanin xaitakiranta yadameta yaje yakuma hadata da daddy
Jawo dirowan dake gefen gadon tayi tanadauko wayar takunna dama dayake akwai chaji kusan 80 pasent lokacin data kashe, maida falon tayi fuskar gadon tana jingina bayanta dashi tare da bude data tahau whaspp, kaitsaye hussaina tafara tabawa
Hey besty yakikaje gida
Sannan ta tura tacigaba da duba sauran sakonni na mutanen ta sai na groups daga sama taga wata bakuwar numban anturo mata stica bata bude ba taduba amsar da hussaina ta turo mata yanxu
Wlh besty lfy klau kinga fa har nafara bacci umar yakirani awaya yace nahau online akwai maganar daxami dashi dole nahau kai soyayya dadi Ismat saikin ji yadda yake min wani hira medadi
Tabe baki Ismat tayi tanajin haushin soyayya duka sbd kamar bata lokaci ne kawai
Bayan taga ma karantawa sakon tafara tura mata amsa
Uhumm wlh danice baxantashi nafasa baccina ba akan wani saurayi tafdi nifa besty kina bani mamaki yadda kike wani makalkalewa umar dinnan bakida xance sainasa
Dariya hussaina tayi bayan tagama karanta sakon Ismat tatura mata da cewa
Hum Ismat kenan wlh harkin bani dariya bakisan soyayya bane shiyasa kike fadamin haka kuma kike ganin xakewata amma da sannu xaki fahimci yadda take daxarar kinfara
Itama Ismat dariya tayi mai isarta bayan tagama karantawa tana ganin wautar hussaina naganin xata mato asoyayya atarihin ta tab
Tafara tapin in amsar
Aa shugabar 'yan soyayya nibayanxu ba kuma nikinsan saurayina nadabanne domin kuwa daddy na yace sai munxaba dan gayu maikyau wanda ya isa tukunna xanfara soyayya yanxu nayi karama dayawa kema tsaurin idone irin taki
Hussaina tayi dariya tana turo mata ansha
Shikenan baxaki ganeba amma mukum ai munwuce yara shekarar mufa 18 tab nikinga yanxu inayin candy Abba yace aure xaimun kuma umar ma yasani sbd yaturo har manya sunxauna anmagana nikawai yanxu yake jira nayi candy adamra,
Ismat nagani tace
Nataba mata inda yake mata kyaikyayi baxa ta kyaleniba
Tai maganar tana bude sakon takaranta tana bata amsa kamar haka
Zamu sha biki kinga time din muncika 20 yes cif cif naxama cikakkiyar budurwar kekuma matar aure hhhhh
Tayi dariya tana tura mata tabude sakon wannan bakuwar numban bayan siticar saiwani rubutu kamar haka
Allah yakara miki lfy da nisan kwana ranki shidade barkanki da dare mai cike da albarka
Maimaita sakon take har yafi takirga kuma takasa dauke ido daga kan sakon saiwani asirtaccen murmushi datake yi wanda ita kanta batasan namaye ba ita dai tasan cewa wannan shine karo nafarko da akataba mata girmamawa kuma taji dadin hakan donhaka taji dadin abin tatura wata situka mai nuni da yatsa alaman an amsa gaisuwa
Game kuwa da Mihran haka yasa yayi wani tsalle tare da harbin iska lallai hakana dab yake da cimma ruwa
Nagode gimbiyar mata lallai yau ina cike da farinciki marar musaltuwa
Tanagani ta tura masa amsa da
Menene dalili?
Yace
Sbda kawai nagaisa da macen datafi kowacce budurwa cancantar ta mallaki dik yanmata sbda tafisu takuma yimusu nisa kwarai
Murmushi tayi daga karshe tahade rai sbda me xaitamata yabon watanta kuma maye mahadinta dashi tayi tsaki tana ce masa
Humm amma kaidai danjarida ne ko malam? kuma sannan ma wacece wannan macen da tamkar tafi kowa kakemin xancenta?
Kuma ni menene alakata dakai dawannan banxan hirar naka?
Yana ganin amsar tata yafuskanci ranta yabaci dan haka yakara tsukewa domin xuba mata wasu da dadan xancan daxai sauko mata da bacin ran
Nine wani mutm kuma kinada alaka dani dakuma maganata sbda kece gimbiyar kuma abar so ga kowa ciki har dani daso samune kinga dana more mata amma kash! Wlh kingirmi ajina Ismat shiyasa nake neman alaka dake maikarfi dake sbda naxama wani bangare naki daxaki iyatinawa dashi, nayarda nakasance koda maibaki nishadi ne daxantika iri daban daban
Wani nishadine yalillibeta sbda sai yanxu tafara jinta amace sosai irin sauran mata waye wannan haka toh kai karfa yahuren kunne nabijirewa daddy wannan kalaman nashi gashi tunyanxu sunfara tasiri akaina kai baxan sake nasabama daddy akan umarninsa ba
Gama wannan tunanin yasa tai saurin kashe datar tana cillar dawayr nesa da ita tare da janyo bedshit dake gefenta mara nauyi ta lillibe jikinta
Dik yadda take xaton abin yafi haka domin kuwa takasa bacci kalaman mutumin ne kawai ke yawo akwakwalwarta kuma saikokarin tasiri suke agareta sbda tana jindadin su har cikin xuciyar ta dakyar tasamu bacci barawo yasace ta
💚
Akwana atashi asarar mai rai inji hausawa sannu ahankali dai Mihran yasace xuciyar Ismat har sunfara soyayya amma a whatsapp domin kuma idan yace xaixo saita hanasa tace yajira tai candy lokacin daddy xaibarta xance amma yakasa hakuri yace xairinka xuwa bayan makarantarsu suna haduwa yaganta kullum tace ta amince haka kuwa akayi ta silale taje sugaisa yatafi harwatarana tace ita gaskiya kar malamansu suganta acoreta yabari xatai tunani tasamar musu wata mafitar yace shikenan
Tagumi tayi tana kallon wayarta axahiri kuwa tunani tatafi maixirfi akan soyayyar ta da Mihran yaya xata bullowa abin ita yanxu tanasonshi kuma xata iya aurensa toh tayaya xata samu daddy da maganar kai wannan abu nadamuna tace afili tana mike danufin taje kitchin ta taya mardiyya aiki,
Mama ce ta fito cikin shin anguwa tana gyarawa ayman hularsa
Kina ina Ismat xantafi fa kikula sosai
Dasauri tafito daga kitchin din tana goge hannunta
Mama harkin fito saikin dawo
Umhum ai inagama sai gobe xandawo sbd kinga baba shehu shine komai namu ace bikin yarsa baxan kwana ba tohm xandai sake fadawa daddynki tawaya koxai barni ke sbda jarabawa dakuke badan haka ba aida duka xamu tafi sainadawo
Tohm mama adawo lfy
Musalin karfe tara nadare da rabi inaxaune afalo ina kallon shirin So alkhairi ne duk hankalina yatattara agurin bana kuma fatan wani Abu yaxo yakatsemin kallo na sbda wata xaxxafar soyayya da akeyi ne ta amutu afilm din tunanin mihran ne yafado min nayi murmushi ina kara hangoni watarana ni da mihran yaxo gidanmu muna axaune muna hira
Kiransa ne yashigo wayata dake gefena dasauri nadaga ganin sunan MIHRAN nayawo asanson wayan
Assalamu alaiikum
Saidana danyi shuru nasaurari daddar muryar tasa tukunna na amsa
Wa alaikum salm
Yayi murmushi
Kunjifa manya komi naku dabanne hatta maganarku kina magana tamkar bakyaso sbda mulki lallai naji dadi tunda naga tabbaci kin amshi tayin mulkin komi nawa
Nai dariya
Kaji kafa kaji kafa ko mihran abindake hadani dakai kenan bakagajiya da yabona ko jerantani cikin mata isassu
Aa ba jeraki nake ba kinfisu ai bako shakka matar mihran yadaren kuma
Humm lfy klau ya momina nadaifadamaka daxu ka gaishemin da ita Allah yasa kuma baka manta ba kafada mata
Haba 'yar momi karki damu ai aikenkine nafadamata inadawowa daga kasuwa danashiga ciki nasameta afalo sainafada mata tace tana amsawa yaushe ne xakixo kigai sheta
Narufe baki da hannu
Woooo mihran wannan xai wahala kam sbda kasan daddy na baisan mafa ina soyayya dakaiba aboye nakekulaka kaima kuma kasani kaga kwa xuwa gidanku baxai yuwuba yanxu sai lokacin damuka xama free dan Allah kagayama momi xanxo nagaisheta amma bayanxu ba
Dariya yayi mata ganin yadda tabi tarude duk da awayane amma har yanxu batagama sauke numfashi ba shikuma yariga dayagama yanke hukunci acikin xucuyarsa nanda wata uku xai je yasami daddyn nata ya fadamasa yana neman Ismat
Ok bamatsala xansake kiranki yanxu bari naje wurin Abba yanason ganina
Tohm shikenan tace tanasakin murmushi
Mihran kana raina
Dariya shima yayi tare da katse wayar bayan kalmar alov u dayacike kunnenta da ita tana sauke wayar daga kunnenta daddy nakarasa shigowa falon ransa abace tamkar mai shirin yin ehu sbda yadda yaji tana soyewa baxato batsammani baitaba tunanin xata tsallakewa maganarsa ba lallai tayi kuskure domin kuwa zai nunamata ainihinsa xaifito mata da maitarsa akanta muraran domin ko dayayi asarar ta gwara ya cika burinsa akanta lokaci guda awuce gurin
Dasauri tamike tsaye tana sakin wayan kan kujera
Daddy
Takira sunansa darawar murya
Dakata dota duk abundakikeyi inajinki kuma banyi mamaki ba dayadda kika shure magana ta kike soyayya dasamari abayan fage kinaganin kingirmane balaifi
Idanunta rau rau xatai kuka
Wlh daddy saurayi dayane nake kulawa kuma shima yashiga min rai daddy kuma yafadamin cewa aure na xaiyi
Harara yakwala mata
Ok wanda kuma naxaba miki fa
Kasa takai gwiwoyinta tana sakin kuka
Wlh daddy babu dawanda xan iya rayuwa bayan mihran dan Allah kafahimta nasan kanason komi dotar ka keso
Wani annamimin murmushi yasaki yana cewa
Shikenan dota yau anwayi gari kinfara son wani samada daddynki yau gashi saurayi yabude miki ido harkinajin yafi miki daddy shikennan dota shikenan nagode kin nunamin cewa banine nahaifeki ba
Sai hawaye dasauri yayi sama dakinsa yana share kwallar dake ta xirara aidaninsa baison yaya xaiyi da sondayakeyima Ismat ba yanajin kishinta kamar yakashe shi
Ganin kuka baxai yimata ba yasa tamike tabi daddy dakinsa duk da xuciyar ta cike take da tsoron abin daxata tarar don kwa ran sa yabaci taga haka axahirin fuskarsa amma shine mafitar ta din taje tabasa hakuri
Xagaye dakin yake tayi hannunsa goye abayansa mafita kawai yake nema
Taturo kofar tashigo
daddy.................
Yadaga mata hannu tare da tsareta da ido
Kinga tashi kifita
Yafada yana nuna mata hanya
Dan Allah daddy ka saurareni b...... .....
Xaki tashi kifita kosai nadauke ki da mari da gudu takwasa hade da fashewa da kuka kodata koma dakinta layin Mihran tafara kira yana dagawa muryar ta cike da kuka tafara magana
Kagani ko kaga irinta ko dama abindanake gudu kenan gashi kuma yafaru
Menene yafaru kifadamun dan Allah kinga bar kukan haka haba Ismat ko menene kifara fadamun mana kinsan kokadan bana kaunar damuwarki ko kinaso nima natayaki kukan ne,
Um um kawai ni yanxu karabu dani tunda daddy bayasona dakai yace yamin miji banason bacin ransa niyanxu bansan menene ma yake damuna ba
Ket takatse wayar takife kai bisa fulo tafara rusar kuka.
Game da Alhaji sanam ma haka take yadda yaga dare haka yaga rana
Yau kwana goma kenan ismat bata daga wayar Mihran idan yadameta da kira kuma takashe watarana hawaye ke xuba a idaninta tamkar ba gobe amma baxata iya cigaba da karya dokar daddyn ta ba,
Kamar kullum yau ma tana xaune afalo wayar sai kuka take amma taki ko kallon ta saima kokarin tashi datake yi
Mama dake rike da hular Alhaji sanam sunfito atare domin yin breaka fast yafice office
Takalli Ismat dake kokarin sakai tafita xuwa dakinta
Ina xaki kuma kina kallon munfito akarya kuma wannan wayar dakika bari tana kuka meyasa?
Kamar mai ciwon baki tace
Mama hussaina ce kuma nafadamata yau banajin dadi baxan iya xuwa school ba amma tadameni shiyasa nakyaleta
Tohm ai shikenan amma dakikaji xaxxabin kije dakin daddyn ku kisha magani mana saiki xauna da ciwo Alhaji kajimin yarinyar nan dawani shirme
Murmushi Alhaji sanam yayi yana ruko hannunta
Ayya my dota sannu kinji bari tayi breaka fast saita sha maganin kona kaita hospital kawai
mama jan kujera tayi taxauna tafara saven insu
Alhaji sanam yakula da Ismat sosai bacin abincin takeba sai rarraba ido take wani lokacin kuma tatafi tunani wayar tace aka sake kira komotsi batai ba balle taikokarin dagawa mama ce taharareta
Kinga Allah kikashe min wayar nan tadaina damuna da kara kinsan fa kwarai banason kara ko
Dauko wayar tayi tana sata ameeting mama takalleta
Ismat wulakanta samari kikafarayi kenan ko?
Dasauri tadago idanunta tana xubawa afuskar mama tare da girgixa kai wanda batasan ma tayi ba
Mama taci gabada maganar ta
Tohm kidai kiyaye kinga dai yanxu saura wata daya kiyi candy kuma dama shine lokacin dani da daddynki muka yanke domin mu aurar dake ba wulakanta mutum sbda bakisan rabonki ba wani nagari ne idan kafuskanci hakan kuma kikaga yamiki xaki iya cewa yajiraki amma banason irin wannan abun akiraka awaya kaki dagawa ko ka kashe wannan ba da ah bace
Harta gama maganar Ismat batasauke ido daga kanta ba sai lokacin data tuna daddy nawajen kuma yaji duk abun da mama tafada sannan tafara kokarin duban yanayin tasa fuskar kamar kwa takaranta dai dai tana dubansa ransa ahade tamkar ya sheke awurin
Wata dabarace taxo mata tai murmushi tana kama hannun mama
Hmm ba wulakanta samari nake ba mama ai akwai wanda nake tare dashi yanxu kuma mun fahimci juna sosai toh amma kinmanta daddyna yace yamin miji tun kafin yanxu saidai nasan cewa mama daddy na xai fifita xabina daxaran yagansa.
Yay gyaran murya
Maman yara xami wannan maganar dake idan nadawo daga office dota tashi muje nakaiki kiga likita, yaduba jikin naki karki damu dasannu xaki fahimci xabina shine yafi alkhairi gareki banason naimiki aure da sauri ga yaran xamanin nan dabasanin darajar auren sukayi ba
Mama tace
Wannan kam hakane Allah dai yaxaba mafi alkhairi
Amin
Yatashi bayan yakammala breaka fast jakarsa yadauka dake kan kujera Ismat dauko hijabinki muje na ajeki hospital ko
Tohm tace kawai sbda tasan tunda yace saitaga dr tohm fa baxai taba yarda xaxxabin karya ke damunta ba
Wayarsace tashiga ringin yadaga tare dayin kofar futa
Bayan yagama daga wayar yadawo
Am tana ina
Tashiga dakinta dauko mayafin
Ok basaima nakaitaba dreva ya kai ta niyanxu ammin kiran gaggawa office sainadawo
Tohm adawo lfy Alhaji ayman yadaga masa hannu shima yana murmushi daddy ya mayar masa martani dacewa my boy saina dawo
Ismat kam tana shiga dakinta kwanciya tayi bakwa juma bacci yakwasheta sakamakon jiya batasamu tayi ba
Mihran da hankalin sa yagama tashi duk yadda xai suhadu da ita ta toshe hanyar yaukam dakyar yasamu yaga hussaina dayake hargidan su hussainan yasani
Bayan sungaisa yake fadamata yadda sukayi da kawartata kotasan wani abu akai
Ehto kaga dai daddyn ta mai xafi ne kuma shi yahanata kula kowa xan iya rantse maka cewa Ismat bata taba soyayya dakowa face kai kuma tasha fadamun cewa ita mutkar bata aure ka ba tohm baxataji dadin rayuwa xata rayu da xuciya biyu koda kwa a inane, yanxu abun daxa ayi kaxo gidan mu da yamma xankira ta awaya saiku hadu musam yaxamu bullowa abin
Yawwa hussaina amma naji dadin abinda xakiyin nan kuma kin kwarara min gwiwa akan raunin datayi kwana goma sha biyar kenan bansa Ismat aido na ba bankuma ji muryarta ba da ita nake kwana araina nake tashi ba abindayake mun dadi hussaina Allah yamiki Albarka Allah yabaki abindakike so nagode yanxu bari natafi saikuma nadawo dayamman.
Amin nagode tohm
Tace tana shigewa gida yaja liform dinsa cike da murna ransa har fuskarsa tanuna irin farincikin dayake ciki axahirin gaskiya yana masifar son Ismat shikansa baison iya yadda sonta yake axuciyarsa ba burin daya shine mallakarta matsayin matarsa tasunnah.
Hussaina kenan kince min naxo kuma saifada kike min da wa axixxika kala daban daban haba ko masallaci naje yakamata adagamin kafa ahalin da xuciyata take ayanxun
Hum Ismat kenan ba wai natsareki da wa'axi bane abin dayakamata kisanine wani kuma kinsani tuna muki akayi amma kinsan sarai cewa abinda kike kokarin aikata wa bame kyau bane ko tohm miyasa xakiyi?
Cike da rauni Ismat tarike hannunta kam
Hussaina yaxanyi yayakukeso nayi dole hakan shine abin daxanyi na auri xabin daddy yace shine wanda yafi alkhairi agareni
Tohhhh tab Allah ne kadai yasan wanda yafi hakan amma baxan hanaki kiyiwa daddy biyayya ba saidai karki manta shi wanda yake cikin ranki yaya xakiyi dashi?
Tana matse wata mulmulayyiyar kwalla data tataho xubowa
Xan hakura dashi nabi daddy amma tsawon rayuwarsa datawa xamiyita ne afadar xuciyata nisa daya xamiwa juna shine na xahiri
Kamar badabara bace wannan

Please Login or Register in order to submit comment