Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xaku nisha dantu kuma xaku ji dadin wannan labari, nawa BUDURWAR ZUCIYA.)
Kwanan Ismat biyu aka sallamosu taji sauki sosai tamkar ba itace aka kai ranga ranga ba, saidai jikin alhaji sanam asanyaye nahangosa bayan sundawo gida sunyi masauki afalon gidan Ismat najikin mama tana wasa da hannayenta yayin dawasu siraran hawaye ke bin gefen idaninta mama ce takalli alhaji tana cewa
Nifa alhaji naga duk jikinka yayi mugun sanyi tunda Dr yafadamana Ismat nadauke da juna biyu naga dai yanada uba aibadamuwa ko da wata m..........
Tashin da Ismat tayi axabire ne yakatse wa mama maganarta takarshe
Inna nillahi wa inna ilaihir raji un mama ciki? ciki kuma? Mama nashiga uku
Saita fashe dawani firgitaccen kuka tana xubewa kasa
Mama nashiga uku mama yauni Ismat nashiga uku banji dadin rayuwataba mama, wannan rayuwa nayi asararki kaicon kaicona mama yasunan matsayin dancikina mama dahna wai? Inna nillahi wa inna ilaihir raji un Allah ka kasheni nahuta
Tafada jikin mama wacce saikallonta take tana mamakin kukan namaye tunda dahn da ubansa
Nuna daddy Ismat tafarayi da yatsa tana magana cike da fitar hayyaci
Kacuceni ka cuceni ka cuci rayuwata ka wulakantani ka toxartani wlh sai kaga yadda xakai mutuwar wulakanci kai..............
Tauuuuuuuuuuuu kakeji fuskar Ismat ta amshi bakuncin marikan da mama ta jerasu har biyu reras alafiyayyiyar fuskarta,
Rufe min baki sakarai shasha sha wacce batasan meyake mata ciwoba ke baki da mutumci wlh dahar xaki iya duba fuskar alhaji kirinka fadamasa irin wadannan maganganun masu tafe cike darashin da ah, menene laifinsa dan yaxabamiki mijin aure idan cikin ne bakyaso aibasai kin tadawa damutane hankali ba saimu xubar tunda ba mutumin kirki bane ubansa bakida laifi donkinki abindaya dangancesa, amma kisani alhaji har kullum ubanki ne kuma dole kicigabada ganin mutumcinsa indai har kinaganin mutumcina amatsayin uwarki.
Ya isa maman kamal kyaleta
Dagudu Ismat tamike tana kuka harta kai kofar falo saikuma taja ta tsaya tana sharar kwallah yayinda bugun xuciyarta kedada karuwa tanaji tamkar tafadi tamutu kawai tahuta dawannan irin masifu dasuke faruwa da ita daga wannan sai wannan kwatakwata rayuwar ta batasamu hutu ba,
Mama kiyi hakuri amma gaskiya dole nafadamiki ita sbda bana fatan abinda xai faru dake ranar gobe kiyama yafaru dani ranar da Allah xaitambayeki amanata daya baki kika gaxa iyariketa KO kula da al amuranta xaitambayeki wanna irin riko kikamata xaiki kuma gane kuskuren dakika tafka akan rikona aduniya lokacin dabaxai miki amfaniba, haka kikeso tafaru dani idan banfadamiki gaskiya ba? haba mamana kigane mana ayanayi koda labbaina basu motsa ba domin fadamiki, shi munafukin mutum ko aruwan sanyi gumi yake meyasa bakya ganesa dasannu xaki yi irin kukan da yanxu ninakeyi kikejinsa tamkar wasa, wlh baxanchi gabada xama daku ba yaudinnan xanbar cikin ku kuma narantse da Allah mama baxanbar gidannan ba saida Ayman kanina,
Takarasa fita aguje tana kuka,
Mama jikinta yayi mugun yin sanyi sannu ahankali nadamar marin Ismat tafara kamata tare dayin naxari nalokaci guda, amma tsayawa tunanin yanxu batata bace tafuta tabi Ismat dakin ta shine kawai xaifi mata kafin tahada kaya tabar mata gidan.
Kina ina salamu alaikum nace salamu alaikum kina ina karimatu
Dasauri tafuto alhaji sanam na mara mata baya shima sbda jin yadda kawu bala ke kwala mata kira cike darashin mutumci yau toh dame yaxo
Yana kwa ganinta yadora da ga inda yatsaya
Kinga karimatu yaufa bada arxiki naxo ba wallahi saikin futo min da yarinyar mutane domin naga ne kitsaf kindn dali arxiki kinji dadin kudi har giyar kudi tajaki dasai da amanar hannunki kin amshe kudin, domin kuwa da Ismat 'yar cikin kice dabaki bada ita gawani katon banxa ba wanda bakisan kowanene shiba dama kuma nafadamiki cewa ko bayan ran salama baxan taba barin 'yar ta tawulakantaba kinga karimatu bakallona xaki tsaya yiba kina xubar kwallar munafunci xuwa xaki muje kukaina har gidan shi mijin dakuka aura ma Ismat tadole Wlh ko na makaki kotu kara.
Mama jikinta rawa kawai ganin yadda ismat dake kokarin futowa adakinta tatsaya tsaf saidataji komi
Karya kake bala yaukuma tanan ka bullo kadade atsaye mutumin banxa kawai
Xaikuma magana tadaga masa hannu tare dacigaba da mgn
Kaga bala kashiga hankalinka shifa shuru shuru daka ke gani batsoro bane gudun maganane karkasa ke kace xaka xo katadamana dahankali akan abinda kaikasan bakada hurumi akansa toh kasani cewa duk wanda yajawo ruwa shi ruwa kan duka kuma idan xaka gewaye duniya kanafadar ismat ba 'yata bace bamai sauraronka sbda kowa yasan wanene kai wajen son xuciya da sharri.
Hmmm kawu bala yamotsa gashin bakinsa
Karimatu kenan nine mai sharrin da son zuciya inaso kisani cewa abayama shishshiginki ne yahadamu dake har haka tashiga tsakaninmu dake kuma nasha fadamiki cewa baxaki taba nasara ba kuma ke kinsan ismat ba'yar ki bace dole kuma duniya tasani kifuto da yarinya ko ki fuskanchi hukunchi wlh,
Daddy wanda yaji maganar banbarakwai ganin abinxai wuce gona da iri yasa yatakawa kawu bala birki sannan yanuna masa Ismat tare danunamasa kofar get alamun yafuce masa agida tunkafin yasa adaukesa awuya afitar dashi
Masifa yake tukuru sannan yafuce dayake awaje yabar direbansa amota
Shuru kakeji tsakanin daddy da mama sai Ismat wacce tayar da akwatunta arelan gidan tabiyosu falon ganin yadda mama ke gursheken kuka iya karfinta tana dukan kujera lallai hakan yatabbatar mata da xarginta akan maganar kawu bala mama kenan ba itace mahaifiyarta ba kukan datake kadai ya isa ya tabbatar wa da me sauraro amsar tambayarsa,
Mama dan Allah kifadamin gaskiya awurinki kadai nake da tabbacin samun amsar tambayata mama dagaske ke ba mahaifiyata bace
Kwarai makuwa Ismat!
Mama tabata amsa tare da mikewa tsaye
WA CE CE ISMAT?
Mahaifiyarki sunan ta salama takasance kuma 'daya daga cikin 'yan gudun hijirar wannan lokacin,
Gidan da aka sauki 'yan gudun hira yana kallon gida na kuma nice mace tafarko da salama tayarda da ita take kuma fadamata dikkan wata damuwarta tana yawan shigowa gidana miyi tahira sabo maikarfi yashiga tsakanina da ita domin kuwa dik da halin talaucin da muke ciki alokacin dani da mijina hakan baihana idan muka dansamu na aje mata ba idan taxo taci ko na aika mata ahaka har wajen shekara daya kenan watarana bala kanin umar mijina yaxo gidan saiyaga salama bayan kwana uku yasameta yasanar mata yanasonta kuma aurenta xaiyi
Datasameni daxancen saina yi shuru tace ba matsala nace akwai domin kuwa tsakanina da salama babu rufa rufa baxan iya boyemata komai ba musamman akan abindaxai iya cutar da ita. Nan nasanar mata irin halin bala na shaye shaye da bin mata yana da arxiki amma baya taimako kuma baya tausayin talaka burinsa ya toxarta mutum daxarar dan wani abu nasabani yashiga tsakaninsu dashi nace aurenta dashi baxai yuwuba tace shikenan dama itama hankalin ta baigama kwantawa dashi ba amma acikin maxajen dasukayo gudun hijira tare akwai wani maisuna mustafha yanuna yanasonta kuma balaifi yana danfita gareji gurin wani Alhj yanadansamu ashagon gidan yake axaune itama kuma tana sonshi
Nace tayarda da shi takuma tabbatar da hankalin sa tace kwarai makuwa nace tohm hakan xa ayi
Bala najin labarin maganar auren salama da mustafha hankalin sa yatashi yayo gidana bashiri ranar yayi mun rashin mutumci sosai bantaba tsammanin bala xai iya goge idaninsa yaxaxxageni ba akan maganar auren dayasan kaf halayensa danafada bawanda nayimasa sharri yana aikatawa
Nayi kuka sosai daga karshe na hakura nabawa xuciyata hakuri, umar ne yashige gaba aka daurawa salama aure da mustafa , gidan haya aka kama musu tsakaninmu dasu layi biyune tatare dataimakon umar aka dan sassayamata kaya na amfanin yau dagobe
Tundaga wannan lokacin tsakanin da bala sai fada da habaici da bakaken maganganun har sai da umar yagaji yatakamasa birki daxuwa gidanmu kuma yace karya kara shiga harkata, sannan nasamu hutu amma ko ahanya muka hado sai harara
Bayan shekara daya darabi da auren salama tahaihu 'yarta mace itace ke, 'ya taci sunan babar mijinta wato zainab sai akamata lakabi da Ismat
Akwana atashi bala yaje gewayen gidajensa wadannda yabayar haya kwatsam yasamu mustafa na haya adaya daga cikin gidajensa, yaji dadin hakan domin kuwa dawannan damar yayi amfani ya yi musu korar kare yasa akayo musu watsi dakayan su waje, rana tsaka naga salama dakaya niki niki shima mustafan haka tana kuka tafadamin dik abindaya faru, lokacin umar nagida dakansa yafuta afasace yaje gidan bala yasameshi yayi masa magana amma fir bala yace baxai ba dagidan saba haka umar yahakura yadawo dankaramin kichin dinmu shi muka basu suka xauna da,'yarsu mai wata biyar aduniya
Bayan sati biyu salama da mustafa suka shirya domin komawa garinsu sbda sunsami labarin anfara daddawo wa sabda abin yalafa bayan tafiyarsu banji dadiba domin kuwa nasaba da Ismat sosai kullum adakina take yini shan mama ne kadai ke maidata wurin ummanta,
Kwana biyar datafiyarsu salama tadawo itakadai kuma awani yanayi nalarura nan take sanar mana ankashe mustafa ahanya itama batasn yaya akayi takubutaba taganta kawai awani kauyene anan tayi kwana biyar dinma kwana biyu da dawowarta ta rasu nashakuka naji mutuwar salama kawata aminiya mace mai hakuri da hankali, haka nadauki amanar ki narike gam nai alkawarin rike ki tamkar ninahaifeki acikina. Lokacin bala yasa ido akanmu har aikowa yake inbasa ke nikuma nahana hakan yasa yakara kullatata,
Kina shekara daya darabi aduniya muka tashi daga unguwar dabai muka koma kainuwa, sbda anrabawa su umar gadon su anbamu namu daki daya muka gina muka koma rayuwa yau asamu yau arasa, babu wanda yasan ke ba 'yata bace domin kuwa wasu cewa masuke har kama mukeyi, shekarar ki shida aduniya nahaifi Ayman, baifi wata uku ba aduniya umar yarasu, lokacin rayuwa yakara mana tsanani haka nacigaba da rainonku Allah nataimakona inasamun abindaxan baku idan nafuto nema nayi aiki agidajen masu kudi nayi tallan ruwa nayi sana ar kosai nasai dakayan miya tohm wannan shine labarinki Ismat kigafarce ni banso kikasan keba 'yata bace inasonki wlh.
Tamkar anwatsa Alhaji sanam ruwan sanyi axuciyarsa haka yaji wani sanyi maitafe da wani daddadan yanayi don haka yakalli mama xai magana Ismat dake jikin mama tana ta gursheken kuka tace
Wayyo Allah mama yanxu wannan shine labarina allahamdulillahi danasamu kaina acikakkiyar 'ya kamar sauran 'ya'yan halas mama nagode da irin kulawar ki gareni da soyayyarki. Saidai ma.........
Daddy yakatse mata magana
Gaskiya dai maman ayman kincancanci ajinjina miki Allah kuma xaibaki lada akan abindakikayi nima naji dadin yadda nasameki mace tagari mai tsantsar bada taimako arayuwa datausayi Allah yasaka miki da mafificin alkhairi
Amin Alhaji nagode
Mama tafada bayan yagama tasa maganar
Mikewa yayi yana kallonta
Tohm muje ciki xanshirya office kinga yau harnayi ma let
Murmushi tayi
Tare dashafa kan Ismat dake jikinta
Tamike tare da ita
Kije dakinki kidan kwanta kihuta kinji karki sadamuwa aranki balle wani abu yadameki
Tajinjina kai tare da tsayawa ganin mama ta juya gurin daddy da dan saurin ta dab dasuka kusa hayewa saman mama tace
Humm Allah dama ai ninamayi xaton yau week end
Yakalleta dawani irin kallo kamar na soyayya
Murya kasa kasa yamata magana
Aa aa fa kedai kawai kicemin mijinki kike so yaxo xauna kusa dake amma inbanda haka yau monday fa
Dariya suduka sukayi tare da karasa hayewa saman
Sam hankalin su bai kai daganin Ismat a down ba sbda yadda suka shagala amaganar tasu
Ismat kuwa da ido tabisu tare dajin wasu xafafan hawaye na silalowa Ahankali lallai daddy bakaramin dan duniya bane sam yahanata fasa kwan duk wata hanya idan yaga tabi toshewa yake yanxu yaxatayi da cikin jikinta tabbas xata nemi gidan hussaina taje tagaya mata komai dayafaru tsakanin ta da daddy sannan su yanke shawarar yayaxatayi da wannan cikin. Da wannan shawarar ismat ta hakura ta sawa xuciyarta salama xuwa gobe ko jibi.
Bayan kwana biyu Ismat yau tashirya tatafi gidan hussaina bayan takirata awaya taturo mata address
Game da Alhaji sanam kuwa can office din Alhaji nura yawuce domin su tattauna akan matsalarsa yagaji da hakuri tunda dai aurensa da ismat yahalas ta yanxu toh yanason matarsa yanxu taxama tasa axahiri kawai kowa yahuta
Bayan gaisuwa dadan tsokane tsokanen junansu dasuka sabayi komai yalafa nan Alhaji sanam yakwashe labarin abinda yafaru kaf yasanar ma Alhaji nura game da labarin Ismat ashe ba, 'yar matarsa bace, Alhaji nura yatayasa farinciki sosai ganin yadda yasamu fita har ga Allah sakamakon yadda da suke kallon abin babban xinibi wanda babu tsarki acikinsa.
Yanxu kai wacce shawara kayanke toh abin nufi anan shine game da kuma auren naku shin xaka lallaba kasaki Ismat ne asalama kareematu batasani ba ko kuma yaya?
Alhaji nura yajefawa daddy wannan tambaya,
Nifa ba maganar saki tsakanina da Ismat domin kuwa maganar gaskiya itace kafa tuna abin dayafaru yafaru ne sbda inasonta yasa na aureta abisa wata hanya wacce baidace ba saikuma yanxu dana samu wannan kakkyawar fatawar sai kuma nasaki damata karfa kamanta Alhaji nura yanxu aurena halas taccene irin kowanne aure
Alhaji nura yakalle sa
Eh hakane kam amma ai ana barin halal dan kunya ko?
Humm inji masu iyamagana kenan amma sudin baxa su iya yimaka maganin muguwar matsalar damutum xaishiga ba bayan barin donhaka tunda ba Allah ne yace ba xan xauna damatata
Alhaji nura yasaki dariya sabda yadda daddy duk yabi yabirkice akan maganar
Tohm shikenan Allah yasa haka yafi alkhairi amma yaxakayi da kareematu kuma tayaya xaka fadamata wannan al amarin?
Humm karka damu yanxu kai yakake ganin xan fito mata da maganar domin kuwa ni akan haka ma naxo nasan baxakarasa dabaru kala daban daban ba don nasanka sosai abokina
Alhaji nura yace
Kawo kunnenka kaji yadda xa ayi
Yarada masa wasu maganganu kafin suyi dariya atare daddy yakashe masa ido tare da dukan table yana dariya
Kai kai mutumin nan kana wuta fa shikenan wannan shawarar yayi haka xa ayi yanxu abin daxa ayi shine ka taso muje wajen likitan naka mu amso magungunan dayakamata ko?
Alhaji nura ya nunasa dayatsa yana dariya kafin yace
Humm abokina wlh naga sai wani axarbabi kake darawar kai saura kuma kaje kayi over action tabaro jirgin naka
Allah ma yakyauta kaidai bari kagani tashi muje
Tare suka fuce xuwa babban hospital din dake kainuwa can kusa da xa abar gari duka suka shiga tare da faka motar dasuka xo da ita
Sauran bayani kuma saisun fito
💚ku ci gaba da kasancewa tare dani Shamsiyya Adam yumnah acikin wannan littafi nawa BUDURWAR ZUCIYA insha Allahu xancigaba da sabbado muku shi yanxun nan kudai muje xuwa 💚

Game da Ismat bayan taje gidan hussaina tayi farinciki sosai daganin irin daular da kawar tata tashigo duk dakasancewar ta diyar masu kudi amma wannan gidan nata yaninn nanka na iyayenta sau hudu kyau da haduwa ga kayan kudi da aka xuba tamkar baxa amutu ba gidan ga girma ko ina daukar ido yake
Abudaya yatakawa abindaya kawota birki wato neman shawarar kawartata shine yadda hussaina take kaudakai daga gareta tana wani yimata fuska fuska dakuma kamar tanajin kunyar ta
Bayan tagama yimata tarba dakayan ciye ciye da lemuka masu tsada sannan taxauna kadan Ismat tataba kafin ta dubi fuskarta dake kasa tana danna waya Iphone 11,fara sol sai sheki take da walwali
Niko besty nakasa gane wani abu danake gani yanxu game dake kuma fuskarki take kara tabbatar mini dan Allah kifadamin ko dai naimiki wani abunne daya batamiki rai harkika canjamin haka kokuma iftila in daya gama mamaye rayuwata ne yaxama tabo har ya kasance agoshi na tayadda kowama xai iya gani yasan ni wacece
Tafashe dakuka kafin taci gaba da magana
Kece kadai wacce nake da tabbacin xan iya dosa da damuwata kuma kiban shawara naji sassauci kece kadai nake maxaton baxaki juyamin baya ba idan kikaji kuskuren dana aikata amma menene yachanja minke hussaina?
Itama hussaina kuka tafarayi ganin yadda kawarta take yinkuka sosai baxata iya hada ido da ita ba kasancewar ta auri saurayinta duk da kaddarar aurence tashiga amma dole taji kunyar Ismat
Dan Allah kiyi shuru besty kudaina kukan haka wallahi babu wani abi dakikayi min saidai ma ni danayimiki kuma natabbata baxaki karbi uxirina ba koda nafadamiki yadda abin yafaru kawai xaki kalli abin cin amana da wulakanci shiyasa dole naxamar miki haka
Cike da mamaki Ismat ke share hawayenta tana kallon hussaina
Me kikamin harkike jin baki kyauta min ba besty babu wani abu daxakiyimin nakasa yafemiki wlh kinfi haka aguna nidake aimun xama daya tun muna yara har kawo girmanmu danhaka kicere komai dakike tunani kisaki jiki dani kiji damuwata wacce nasan ke kanki saikin kusa binneni agurinnan sabda haushina lallai hussaina nakasance mace mara wayo mai toshashshiyar kwakwal wa
Hussaina ta toshe mata baki da hannunta
Aa besty kidai na aibata kanki da munanan kalamai wlh duk abindakika fada baikama dake ba kuma baxai taba xama tare dake ba kome nene xakifada min kibarshi sbda nawa yafi muni Ismat kinsan kwa wana aura?
Ismat tagirgixa kai tare dacewa
Aa menene yafaru?
Ismat Mihran na aura shine mijina yanxu wlh bansanshine ba ya yaudare tawani salo....... Kaf takwashe labarin tabata
Gamamakinta murmushi tagani afuskar Ismat tare dawasu siraran hawaye
Wannan shine kike kira laifi haba hussaina saikace bai halatta ba ai baharamin bane don Mihran yataba sona yaxo yasoki ya kuma aure ki ba, kinga kimanta wannan watakila ma dama ke yakeso bani nidin wani abinne yarinjayesa gareni bayan yarasa ni kuma yagane ashe soyayyar ke yakeyiwa ni kawai birgewa ce,
Hussaina tadamke hannun Ismat anata tare da kara jin wani nauyi
Aa aa Ismat Mihran yanasonki amma nikaina bansan mehakan ke nufi ba sunkasa gane cewa ke bakida laifi
Bakomi duk yadda duniya takalleni besty domin kuwa daddy shine silar komai dayafaru darayuwata besty daddy ashe mugun nufi ne dashi akaina daga karshe yacika burinsa hussaina daddy ya aureni yanxu haka cikin sane ajikina wata biyu
Dasauri hussaina tamike tana dora hannu aka
Nashiga uku Ismat karki kuma fada dn Allah karki tabbatar min dawannan maganar
Dagaske ne hussaina bari kiji..........
Nan takwashe duk abin daya faru dakuma labarin da mama tabata cewa ita ba uwarta bace
Kuka suke tare anrasa me rarrashin wani acikinsu haka suka yini cikin wani hali najimami da takaichi daga karshe suka yanke shawarar xubar da cikin amma acikin sirri bawanda xaisani dayamma tadawo gida
Yaukam tunkarfe tara nadare takwanta bacci da asuba bayan tatashi tayi sallah kaitsaye kitchin tanufa domin taya mardiyya sukarasa hada break fast suna kammala wa tadawo dakinta gabdaxata shigo taga kamar gilmawar mutum yafito kafin takarasa taga bakowa sharewa tayi tana shigewa dakinta tare da makala sakata sbda tsaro tun data tashi dama taji tana sha awar freesh milik donhka tasaka afirij din dakinta dankarami wanda daddy yasiyamata tun farkon xuwansu domin tayi sanyi daukowa tayi tare da cop tanemi gefen gado taxauna tare da bude freeshmilik din taxuba cikin cop in tashanye tare da bin lafiyar gadon takwanta ko rufe wa bataiba sai bacci ne yadauketa maikarfin gaske.
Musalin karfe takwas da rabi mama ce da daddy sai ayman xaune bisa kujerun dani table yayin da mardiyya keta iso da break fast din bayan tagama ne xata futa mama takira
Wai ina Ismat ne kinga fa bata futo ba har karfe takwas da rabi lfy kuwa?
Mardiyya taikasa dakanta cikin ladabi
Lfy klau mama daxu bayan sallar asuba aitare muka kammala girki saita komadakinta amma bari naduba ta naga
Tohm shikenan jeki kice mata tafito muyi break tunda ita kullum Allah keda kullum sai antaso ta
Mardiyya tafuce tana mai nufar dakin Ismat ai da gudu tadawo tana kuka shabe shabe
Subhanallahi inna nillahi wa inna ilaihir raji un mama mama Ismat mama Ismat
Mama da daddy tare suka tashi suna rufawa mardiyya baya tare da kallon yadda take nuna musu cikin dakin Ismat
Fadawa ciki sukayi mama ma kuka tasa tana rumgumo ta jikinta itakuma sai fisgewa take yi tare da wani irin kumfa dake fita abakinta ba abindata kecewa sai fige fisge datakeyi tunkarfinta
Subhanallahi Alhaji Alhaji kaga abin datakeyi
Hannunta yarike kamar yayi kuka shima
Menene yasameta toh jiya ai lfy lfy naganta agidan nan
Mama tana share hawaye tace
Bawanda yasani tunda kaga mardiyya tace tare sukayi aikin abinchi da asuba kagakenan bayan tadawo dakin komenene yasameta muje hospital Alhaji
Aa wannan ciwon yafikama dana jinni saidai muje gurin wani malamin
Alhaji nibansan wani malami agarin nanba saidai mutafi rigar kawu shehu yadubata can kadai nasani
Tohm shikenan amma kuma bakyaganin xata galabaita kafin muje tunda akwai nisa tsakanin mu dubayadda take ta fisge fisge kinga muje nan wurin malamina bayan makarantar alhakku babban malamine yana rukiyya ma sosai
Shikenan Allah yataimakemu nidai
Alhaji ne yadauketa akafada yasamamama ita gidan baya tariketa kam sai hawaye ke futa a idaniyarta tabbas tana tausayawa Ismat sosai gata marainiya amma kaddarar rayuwa sai afko mata take Allah yakawo miki sassaucin wannan lamari
Mama tafurta afili bayan ta kara rumgume Ismat.

INA MA'U?
Tun lokacin data dawo nigeria hankalin ta amutikar tashe jikinta kuma yayi sanyi sosai da duniya abinda Alhaji sanam yayiwa 'yar matarsa yasa taji wani tsoron Allah sosai duniya tafara bata tsoro lallai mutanen yanxu imanin wasunsu baicika ba kana sallah amma inkayi wani katon xunibin baxa ace kasan alkibilaba kaitsaye taji harkar bariki tafita aranta ta tufa hadakayanta tayitakoma kauyensu dake yola
Bayan tasayar da gidan datake ciki wanda Alhaji nura yasaya muta dasunanta akan milion uku dari biyar tasa a acount inta sannan tachale.
Cikin mota tafara tunanin yadda xata kalli iyayenta domin kuwa duk halin datafada sune sila dasuka kawota aiki birnin kano tafara tuno abin dayafaru baya.
dama aikine yakawota kano daga aikatau dangidan matar yafara lalata da ita hartasa ba yaxama kodayaushe idan hajia batanan saitashiga dakinsa suyi ta lalatarsu har watarana hajia takamasu taimata duka takuma koreta tace karnasake dawo mata gida tunda ni 'yar iskace gashi na lalata mata dah kwanana uku atasha nake kwana watarana kasan gada dahaka harnagamu dawata mandiya tadaukeni takaini gidanta tacigaba dakuladani ganina kyakkyawa farasol cikakkiyar bafulatana mai matsagacin tsayi nagoge nakarayi kyau haskena yafuto sosai dahaka mandiya tabude min harkoki da manyan alhaxawa masu xuwa daga gari gari har muka hadu da Alhj nura kwanan mu uku dashi awani hadadden hotel namanyan masu kudi yace shifa sona yakeyi donhaka bayaso nacigaba da harka dawasu maxa nace baxai yuwuba domin kuwa hakan shine sana ata yace xanxama daduron sa xai mallaka min gidan dazai ajeni dasunana xaikuma rinka biyana duk bayan wata uku dubu dari biyar xaidauke min dik wasu bukatun rayuwa da dawainiya na amince mandiya kuwa sai daya ajemata milyan daya darabi sannan yasamu ta amince tabasa ni nan mukadasa sabuwar rayuwa nida alhaji nura naxubda ciki sama da bakwai nasa duk da kwayoyi damuke banka nahana shigar ciki amma wani xubin basa amfani
Nasauke numfashi lokacin danaxo nan atunanina lokacin da nashiga kauyenmu nasha mamakin yadda yagyaru yaxamu city mama na da babana dakyar suka iya ganeni domin kuwa shekara wajen bakwai kenan rabonsu dani bansamu masala ba domin kuwa murnar dawo wata aketayi mahaifana da 'yan uwa saidaga baya naba iyayena labarin irin rayuwar danayi sunyi kuka sosai kuma sunyi dana sanin turani aiki wani gida nan gida nayi istibura i, kodayaushe inacikin daki ina laximi istigifari nake yi kodayaushe dasalatin Annabi
Bayan wata uku nasa aka gyara gidanmu yaxama sabo dakuna shida kuma akasa manyan kyawara irin nacikin binni kofar gidanmu kuwa get akasa naba mahaifina jari yafara futa cikin garin yola yanayin sana ar masarufi babban shago nakama masa haya ababbar kasuwar gari yafara xuwa kayan masarufi yana sayarwa dandanan cigaba yaxo masa
Bayan wata biyu nasamu masoya sosai naxuwa guna amma haryanxu bawanda yakwanta min saiwani mutumi dake xuwa daga maiduguri cinkasuwa watarana naje wajen babana muka hadu maisuna Abubakar munfahimci juna sosai na amince kuma xan auresa har yaturo magabata antsaida magana yanxu haka saura kwana uku daurin aurena shiyasa naga chanchantar nafasa kwan Alhaji sanam tunda matarsa haryanxu batasaniba yaukam inaxaune bisa lallausar kujeran dakina naduba waya na nalalubo numbar kareematu wacce nasata awayar Alhaji sanam sbda nasan watarana xatayi amfani kamar yau kenan kaitsaye nakira.
Ba adagaba har sau uku ina kira amma ba adagaba saikawai natura mata dogon sako yadda xata fahimchi komai sanann naxare layin nakarkarya sa nasa Sabo wanda yanxu nake amfani dashi asabuwar rayuwar danake mai tsafta.

MUJE XUWA MASU KARATU
Mama ce da daddy xaune gaban malam gambo wanda yadauko wani koko daruwa agabansa yadasa kunnensa dai dai kokon kafin wani lokaci yadago yanaduban su Alhaji tare

Please Login or Register in order to submit comment