Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

office ɗin tsuntsurewa da dariya tayi inda ya janyo hankalinshi zuwa kanta

Mamaki ne ya kamashi yadda ya ganta da wata ƴar ficik na mayafi sai kamar batayi Aurenda take faɗa ɗinba

Karasawa wajenshi tayi cikin shagwaɓarda ta saba tace "Abdul bakaje ɗaurin Aure na ba lafiya kuwa kodai lokacin bakayi sauki bane?".

Ko ɗagowa ya ganta beyi ba yace "anyi Aure lafiya?"

Meera tace "dama so kake ayi auren cikin tashin hankali?"

Murmushi Abdul yayi yace "bahaka nake nufi ba kuma bai kamata kiyi magana dani ba yanzu saboda ke matar Aure ce"

Meerah ce tace "don ni matar Aure shikenan bai kamata muyi magana ba?"

"Ehh saboda haramun ne"

Meerah tace "malam nafa je islamiyya kuma inada haddar Alqur'ani sannan inada hadisai dama sauran litattafai ya kamata kasan wannan"

"Big girl dake kina kanwar minista amma Kishiga islamiyya"

Murmushi tayi kana ta ɗaure sir Abdul da mari tace "ka rika gyara zancenka so kake ka sanya ni ta farki mara kyauu ko,kuma ni second lady ce ba kanwar minista ba yanzu"

Mamaki ne ya cika Abdul kana ya mike ya riko Hafsat da hannunshi biyu ya janyota wajen ɗaya table ɗin tana kokari kwatar hannunta tana cewa "ka sake ni nifa matar Aure ce"

Shiko ya juyo ya ganta yace "yanzu kikasan wannan?"

Table ɗin ya ajiyeta kai kanaya ɗauko wata dorina a durowar shi yace "kinga wannan bulala! To da ita xan rika cin ubanki kullum a makarantar nan i dai zaki rika shigarmin office"

Tsoro ne ya kama Meerah ta fara kuka tana bashi hakuri

Ɗaga bulalar yayi kamar zai watsa mata bata san lokacinda ta fara fitsari ba a wando kawai sai ji yayi ana tsula fitsari

Itako Meerah kara tsurewa tayi da taga ranshi ya kuma ɓaci

Sauke bulalar kawai yayi yace "matsoraciyar banza saiki tashi ki shiga toilet kiyi tsarki kibarmin office"

Cikin sanyin jiki Meerah ta wauce toilet ta wanke kayan duka ta jike tabar office ɗin dagudu

Shiko Abdul tana fita ya kwashe da dariyar kanwar minista yadda take wani kuka tana wani rokonshi kada ya dake ta

Tana fita ba inda tayi sai mota tayi saurin shiga tabar makarantar saboda bazata iya zama da jikakken kaya ba

Canja kayan tayi ta kuma dawowa cikin makarantar inda taga sir Abdul a ajinsu

Shigewa ajin tayi cikin rashin tsoro saboda tasan babu abinda zai yi mata don shine sila

Ya gama lesson nashi tas yana shirin fita yace "ko akwai wanda bai fahimta ba?"

Meerah ce ta mike cikin sauri tace bata fahimci komai cikin lesson ɗin ba

Ran Abdul ne ya matukar ɓaci saboda dole ne ya mai-maita sai yace.........

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
[10/10, 13:38] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 1️⃣5️⃣



_________📲Shiko Abdul bai tafi ba tsayawa yayi a gefe yana yi mata dariyar mugunta,.

Koda zugin ya ɗan kyale ta ta mike da sauri ta bar wajen bata yiwa sir Abdul magana ba,.

Yayi mamakin yadda akayi yau Meerah ce ya nemo faɗanta amma ta wani kyale shi ba magana.,

Bai yi Aune ba yaji kamar an watsa mishi wani abu a bayanshi,.

Juyowarda zaiyi yaga Meearah ce har taje shagon cikin makarantar ta siyo coloured exotic (exotic me kala) ta zo ta zuba mishi jikin kayanshi,.

Ji yayi kamar yayi ihu a wajen saboda bakin ciki dukda cewa ba mutane dayawa a wajen,.

Sai da ya gama ɓacin ran nashi tukuna ya juyo ya ganta gefe itama tana gefe tana yimishi dariya yadda yayi mata saida ya kulu iya kuluwa yabar wajen bai yi mata magana ba ga kuma sanyi saboda damunar da suke ciki yanzu,.

Saurin shiga mota yayi ya bar cikin makarantar,.

Ita kuwa Meerah cewa tayi "ko ba komai dai yau kaima ka ɗan jikewar da nayi irin na jiya yadda ka sani fitsari" kana ta kuma kyalkyalewa da dariyar Asara ta bar wajen

Yana shiga gida momynshi ta tare shi tana tambayarshi meya sameshi duk rai a ɓace, ce mata yayi "mom ba wancan shegiyar yarinyar bane" ya faɗa yana me shirin yin kuka

Mom ce tace "wai kanwar mininstar nan ba kacemin tayi Aure ba me haɗinka da ita a makaranta ko dai batasa darajar Aure bane?",.

"Momy ina tasan darajar mutum ma bare na Aure",.  ya faɗa kana ya wuce ciki ya canza kayan ya fito da wuri saboda yanada lectures dayawa yau


Yana shiga cikin makarantar yayi Aji beyi ta kan Meerah ba

Ita kuwa Meerah ta ganshi ya wuce tace "nifa banga me makarantar nan yake kara min ba gashi ni zama na kawai nake makaranta bata komai da ni ko kulani makaranta bata yi gwara ma kawai in fita a school ɗin shikenan"

Zuwa Ajin nasu tayi ta tsaya a kusa da sir Abdul tana fuskantar ƴam ajin gaba ɗaya tace "bayin Allah kunga dai zaman da nake a cikin makarantar nan Akwai mahassada na da dama da kuma da kuma wanda burinsu shine in fita,to insha Allah ni daga yau bazan sake zuwa makarantar nan ba na barku lafiya".,

Nan ta fice daga Ajin kowa da ido yake binta babu meyi mata magana saboda karamin Aikin ta ne taci ubanka da zagi

A kwana a tashi ba wuya Meerah ta kai wata uku,ta hakura da zuwa makaranta,  kullum bata zuwa ko ina sai zaman gida,Abinci kam kullum ana kawo mata daga gidansu Salaam amma ina ko sau ɗaya bai sake kiranta ba kuma baya mata magana ta instagram infact Abdul baya kulata,.

Tun Abin baya damunta har yanzu ya fara ci mata tuwa a kwarya ta wani zama wata kala gashi kuma bata da matsalar Abinci damuwa kala-kala ce take damunta

Gashi har yau yayanta  bai taɓa kiranta ba koda kuwa sau ɗaya ne

Duk tunani ma sun ishe ta sai ta ɗauki wayarta don rufe zafi,.

First abinda ta fara  gani  a notification(sanarwa) na gaban waya ba komai bane fasheee.....


Kuuu muje zuwa

Vote pls wattpad

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
[10/10, 13:38] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*


*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 1️⃣6️⃣

First Abinda ta fara gani a notification (sanarwa) ba komai bane fashe wani message na Salam da yace mata "kanwar minista kuma second lady ai sai naga zaman Borno ba zata karɓe ki ba don haka nake yanke shawarar kaiki kauyenmu inda zaki ɗanyi zaman Auren namu a can sannan ya kamata ki sani baki isa ki karya dokata ba",.


Meerah fe zufa ya fara keto mata saboda ta fara jin tsoron wannan gaye  gashi ƴan uwanshi basa zuwa mata ita kuma batada ƴan uwa kwata-kwata bare ma kawaye


Saida ta sharɓi kuka sosai tayi me isanta kafin ta samu ta ɗan yi wasu ayyuka kaɗan tayi wanka ta kwanta abinta


*BAYAN SATI ƊAYA*

Meerah ce zaune a ɗaki tana ƴan danne-dannenta bata ma buɗe data ba taji ana buga kofarta bisa ga mamakinta taga lokacin kawo Abinci beyi ba yanzun goma ne da rabi

Saurin mikewa tayi taje ta buɗe inda taga wasu sabbin bodyguards ne guda uku tsaye da bakaken kaya a jikinsu sun sanya bakaken glass sun rufe fuskarsu tufff sun haɗa fuska


Sai da ran Meerah yayi duuuum kafin ta iya buɗe baki tace "malamai lafiya kuwa?",.

Ɗaya daga cikinsu ne ya ce "yallaɓai ne yace mu zo mu ɗauke ki yau ne ranar tafiyarki kauyen!",.

Meerah ce ta sake ihuuu kana tace "bazan je ba kuje ku faɗa mishi ba inda zani"

Tana kokarin shigewa taji an sunkuce ta cak bata sake ganinta wani waje ba sai mota ihu take musu tana turjewa amma ina sunki sakinta


Haka tayi su saketa sunki saida suka shiga hanya ne suka barta dama sun sata a tsakiya ne

Meerah ce tayi tagumi tana ta kuka Allah ma ya taimake ta da waya ta fito kawai saita ɗan faki idonsu ta ɓoye wayar tayi taci gaba da kukan tana dana sanin wannan Aurw da tayi,.

Wani shawara ne yazo mata anya ba gwara ta kira yayanta ba yazo yanzu sai kawai ta fasa saboda kada suga wayar su kwace,.

Batayi Aune ba taji sun fara shiga gargadan hanya ɗago ido tayi Alamar tunda wuri haka sai kawai ta kara fashewa da kuka

Babu wanda ya kulata saima ɗayan da tasa headphone yana ta jin waƙarshi


Meerah ko sai ihu take tana a fiddata baza ta iya ba


Saida suka yi tafiya mai bala'in nisa kafin suka iso garin da yamma bayan la'asar,.


Suna sauka a motar Meerah ta fashe da sabuwar ihu saboda gari ne kamar bukkar fulanan jeji batada wani kyauuu sai Aukin gidajen ƙasa masu baƙaƙen fenti kuma gashi garin babu wutar nepa,.


Yara ne suka taru suna ta kallon Meerah da ke ta ihu abun su har dariya yake basu wai babba da ita tana kuka,.

Ita kuwa Meerah kota kansu bata bi ba ihunta take yi koya dameta can tana cikin ihun suka hango wani yaro wanda zai kai shekara Ashirin yazo wajen nan bodyguards in suka ce mishi ga Meerah nan,.

Yaron ne ya washe baki yace "bakuwarmu sannu da zuwa",.

Meerah cikin ɓacin rai tace "inma bakuwar uwarka ce ka rike sannu da zuwanka banza kazami ɗan kauye"

Zagin yayiwa hamma zafi amma da yake shiɗin mai hakuri ne sai yayi murmushi yace "kiyi hakuri ranki shi daɗe bakuwa",.

Meerah ce ta ɗago kamar zata dake shi dama wando ne a jikinta da wata ƴar ficikar riga tace "ai da ban hakura ba mari zakasha ɗan iska"

Nan ma yayi mata shiru bai bata amsa ba

Ita kuwa duba yaran wajen tayi tace "don ubanku wa kuke kallo shegu ku wuce ku bani wajen ƴan iska",.

Wani ne yake wucewa yace "kee ki shiga taitayinki faaa",.

Tunda Meerah ta fuskanci mashayi ne ta ja bakinta tayi shiru saboda ita batason fitina da mashayi,


Haka yamma yace babu wani kaya da za'a ɗiba muku

Ba tareda yayi maganabba ɗaya bodyguard ɗin yaje ya kwaso wasu kayayyaki a bayan mota ya kawowa Hamma yace "ga wannan gaba ɗaya na sawan hajiya ne"

Nan suka shiga mota suna shirin tafiya Meerah tayi gudu ta rike murfin motar tace basu isa su tafi su barta ba

Ɗayanne ya wani waina kan motar har saida Meerah ta faɗi ta ɗanji ciwo a kafarta nan ta ki tashi ta fara burgima a wajen Hamma ne ya samu waje yama jira ta gama su tafi......

*_🌹🏵️Oho dai masu son littafin kanwar minista a wattpad nafi update🏵️🌹_*

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
[10/10, 13:38] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 1️⃣7️⃣



_________📲Hamma ne ya samu waje ya tsaya yana jira ta gama su tafi tunda shi gidansu da nisa a ƙarshen garin ne,.

Saida tayi kuka me isanta ta gode wa Allah kafin ta mike ta dubi Hamma da yake ɗan nesa da ita tace "kazo muje gidankun don ubanka, kuma sai sun maidani gidan yayana kota yaya ne, mugaye kawai Azzalumai",.

Hamma bai kulata ba sam suka fara tafiya tana ta ɗingisawa saboda taji rauni gashi wajen yana jini sosai,.


Suna shiga gidan aka fara yimata sannu da zuwa ana zuwa kusa da ita sai a nan hankalinta ya fara kawowa ta gane cewa nan garin fulanai ne saboda hango wata kyakkyawar yarinyar  fulani da ta gani wacce ba zata wuce sa'arta ba  tana zaune tana girki nan yarinyar ta hango Meerah sai ta fara yi mata murmushi,.

Nan Meerah ta mayar mata da murmushi itama saboda yarinyar ta matukar burge ta sai kuma ta juyo ta fara kallon cikin gidan,.

Babu laifi an ɗan gyara nan ta fara tunanin cewa dama nan ne Asalin su ɗan shugaban ƙasar kai Allah ta tsine talauci ita bata taɓa ganin surukanta ba an kawo ta wajen wasu mugayen mutane,.

Kowa sai kallon Meerah yake yi da idanuwa ita kuwa ta fashe da wani kuka kamar yarinya karama nan ta roke su wai su bata *First Aid Box* zata wanke ciwon ta babu wanda yasan ma'anar abin sai kawai suka cigaba da kallonta gashi wando ne a jikinta da wata ficikar riga amma duk wannan bata dame ta ba ita kam saima kukarda take yi kamar yarinya,.

Nan ta ɗaga kafar ta nuna musu tana kukan,.

Ransu ne ya tsinke ganin Wannan ciwo na Meerah can sai ga Faɗimo da gishiri a hannunta da gudu tazo ta baɗa a kan ciwon Meerah,.


Meerah ce ta faɗo ƙasa tana ihu tana faɗin "wayyo zasu kasheni..... Wayyo zasu kasheni"

Nan sauran yaran suka shiga yi mata dariya manyan kuma sunta tausaya mata,.


Haka Meerah ta gama shirmenta sannan aka umurci Faɗimo da ta kaitq ɗakinta a can zasu zauna

Suna shiga ɗakin Meerah tace "ina zanga wajen sa caji"

Faɗimo ce tace "laaa kina da waya ne ai babu wajen sa caji kaf garin nan sai garin makwafta muke kaiwa",.

Meerah ce tace "to me sunan garin nan?",.

Faɗimo tace "Au baku sani ba kenan sunanshi Rumdakila "

Meerah ce tace "sunan gari kamar wani kashi ko daɗin ji babu",.

Faɗimo ce tayi shiru saboda su a garinsu suna mutunta bako ko yaya yake

Haka Meerah ta bukaci ruwan wanka nan aka kaimata akace tazo tayi wankar


Tana fitowa ba takalmi tayi toilet ɗin ita a zatonta irin nan birni ne saida ta fasa ihu ganin munin bangidar gashi babu tsari ta baya ma za'a iya kallonka,.

Nan tace bazata iya wanka a bangidar ba a ƙyar suka lallameta ta shiga da ido a runtse tayi wanka tana fitowa taga an ajiye mata wata takalmin fulani me kyauuu nan ta sanya a kafarta taga yayi mata kyauu sai ta fara murmushi,.

Suma murmushi suka yi da suka ga tayi sai kawai yaran gidan suka fara farinciki ganin iyayensu na murmushi.

Haka Meerah ta wuce ɗakin da suka bata ta samu ta shafa mai vaseline,.

Tana gama shafa man ta ɗauko ledan kayan ta fara buɗewa,.

Me za ta gani wasu mugayen takalma ta ne kundira irin na zuwa gona da kuma wasu kaya riga da zani irin ɗinkin fulanan jeji zannuwan yawanci kalan kore ne da kuma ruwan ɗorawa  kayan dai na fulanan jeji ne kala uku,.

Wani wawan ihu Meerah tayi kana tace "na shiga uku na lalace me zan gani Salam" nan ta fashe da kuka

Faɗimo ce ta shigo da gudu tana cewa "ƴar Birni me ke faruwa ne wai?",.

"Fateema don Allah duba wannan kaya da Salam ya siyo min"

Faɗimo ce taji daɗin sunanda Meerah ta kirata dashi kana ta fara dudduba kayan

Farinciki tayi kana tace "wallahi kayan nan sunyi kyauuu kamar ace tawa ce",.

Meerah ce ta ɗago kai ta harareta kana ta mika hannu ta ɗauko wayarta ta kunn,.

Faɗimo ce taki tafiya saboda taga babbar waya kememe taki barin wajen,.

Saida ya kawo kafin ta cire pin ɗin ta fara danne-danne,.

Ranta ne ya tsinke ganin ko Alamar network babu a garin,.

Nan tayi saurin juyowa taga Faɗimo da take ta leka wayar da doguwar wuyar tata,.

Dariya ne ya kama Meerah kafin tace "babu network ne a garinku"

Ina babu hankalin Faɗimo sam kanta yabi kan wayar..........


Kuuu muje zuwa

Vote d novel pls wattpaders

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
[10/10, 13:39] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮

  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 1️⃣8️⃣


_________📲Ina babu hankalin Faɗimo sam yabi kan wayar...

Saida Meerah ta ɗan darawa sosai sannan tayi tsawa tace "ke Fateemah tambayarki fa nake"

A ɗan firgice Faɗimo ta ɗago kai tace "ehhhh babu... Babu sam"

Nan Meerah ta ajiye wayarta a gefe ta fara kukan zuci wanda yafi na ido zafi babu hawaye cikin idanunta amma kana ganinta zakasan tana cikin matsananciyar damuwa..

Faɗimo ce ta mike taje ta ci gaba da Ayyukan da take Meerah kuma na nan tana kukanta,.

Can suka jiyo sallama Faɗimo ta mike da gudu ta taryi me sallamar tana murna wai ƙawarta ce Nafeesa ta ɗan je ƙauyen makwafta sai yau ta dawo,.

Faɗimo tayi matuƙar farinciki saboda Nafeesa ce kaɗai ƙawarta a garin inba haka ba kowacce sa'arta ta tsane ta saboda kawai ta fisu samun samarai,nan suka ciki Meerah na zaune a yadda Faɗimo ta barta.

Saida Meerah taji suna ta ihu ne yasa ta ɗago kanta don taga wacece wannan nan taga wata yarinya ce fara sol masha Allah da ka ganta kaga fulani usul saboda gashinta a bayyane yake an wani ɗaure shi tukur-tukur wannan fuska tata taji Ado na fulanai infact Nafeesa dai ta haɗu ta ko ina saboda ba irin siraran nan bane,.

Meerah ce ta washe baki tace "sannu da zuwa Nafeesa"

Sai a lokacin Nafeesa ta san da akwai mutum a ɗakin sai ta ɗago ta dubi Meerah tace "yawwa bakuwarmu fatan kina lafiya kamar yadda nake lafiya?",.

Maganar ce ta yiwa Meerah daɗi kana tace "ina lafiya kalau ya muka sameku a wannan ƙauyen?",.

Nafeesa ce tace "muna lafiya kalau",.

Nan suka zarce da hira kamar sun san juna har Abin ya baiwa Faɗimo mamaki tana ta kallon su,.

Haka suka gama hirar da Faɗimo zata rakata Meerah tace sai ta bisu itama nan suka tafi tare,.

Haka Meerah ta ci gaba da zaman ƙauyen nan ba yabo ba fallasa tayi wajen sati biyu tana shanawarta kayan da Abdul ya siya mata kuwa tuni ta fara sawa babu abinda ya shalle ta,.

Kamar kullum Meerah sai sun je rafi ɗebo ruwa haka yau ma ya kama Alhamis Meerah sunje ɗiba ruwa a rafi,.

Nan su Auwalu saurayin Faɗimo suka zo rafin su uku dama sunyi da Faɗimo cewa zasu zo,.

Kowa yaje wajen budurwarshi suka fara zance ɗayan kuma da ake kira da  Idi yaga babu sarki sai Allah yayi wajen Meerah yana mata magana,.

Tun tana ɗauke kai bata kallon shi sai yanzu ta ankare saida ta girgiza ganin kyauu irin na wannan gayen,.

Nan ya nemi soyayya a daga wajen ta tuni Meerah ta mance da wata aba wai Aure ta amince nan suka ɗaure da soyayya a wajen,........



_Masu karatu ku biyoni cikin sauran pages ɗan kaɗan da zan saki in gama novel ɗinnan saboda wannan littafi film za'ayi dashi insha Allah shiyasa kuka gabana saka wani love kamar film nake yinshi ku dai ku biyoni_

Kuuu muje zuwa

Vote d novel pls wattpaders

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 1️⃣9️⃣



_________📲Nan ta Amince a take suka ɗaurw da soyayya a wajen.

Koda kowanne daga cikin du yaci soyayyar ya koshi sai mazan suka daɗɗaukawa matan ruwa suka tafi ba tare da matan sun ɗauki komai ba Meerah sai kallon soyayya take yiwa Idi tana kara jaddada kyau irin nashi,.

Koda suka shigo cikin gari kowa ya amshi abunshi suka yi gaba inda Meerah da Faɗimo sukayi gidansu ita kuwa Nafeesa tayi gidansu.

Innar Faɗimo ce da sauran kishiyoyinta biyu zaune suna ta mamakin yadda Meerah take da hankali amma wai a zo a yaudare su ace bata da hankali be ake so ta koya tarbiyya sai kawai kowaccensu taji ba daɗi sam basu kyauta mata ba.

Meerah na juye ruwan tazo kansu dama cin Abinci suke sai ta wani kaɗa kai tace "kuma me kuka dafa?",.

Maman Faɗimo ce ta ɗago kai da wuri don ganin wanda yayi maganar cin karo tayi da Meerah kanta a ɗage ta rike kugu kamar me zuwa dambe,.

Mamaki ne ya cika fal a idanunta sai kuma ta wani dake tace "Ameerah ba wani abin kirki muka yi ba tuwon dawa ce da miyar kuɓewa"

Kuka Meerah ta saki cikin shagwaɓa tana bubbuga kafa tace "ni shikenan an kawo ni inda za'a kashe ni na shiga uku dana sani a bayan keya yake wallahi da ban Aureka ba Salam mugu kawai Azzalumi",.

Matan ne suka yi kasake suna kallon Meerah ira kuwa kallonsu tayi tace "to me kuke kallo mugaye kawai da ba dan ku ba ai da yanzu ina can Maiduguri amma gashi wannan baƙar ƙauyen bansan ma kasan wata state ce ba mugayen banza sai Allah ya tambayi Bakinku ai",.

Matan ne suka fito da idanuwa suna yiwa Meerah kallon tambaya wai dagaske ne Allah zai tambayi bakinsu Meerah ce ta fahimce su tace "wallahi dagaske nake muku",.

Da yake ba wani sanin Addini suka yi ba yasa suka Amince da maganar Meerah hae da hawayensu,.

Meerah ta zata cewa zasu bata kuɗin mota ta tafi sai taji sunce "kiyi hakuri ki yafe mana baɗɗo wallahi munyi kuskure kuma ba zamu sake ba"


Ran Meerah ne ya matukar ɓaci tayi ɗaki tayi ta kuka tana kiran umma da Abbanta amma ina babu mai taimakonta cikin wannan ƙauyen gashi dukda yau ne tazo kuma da yamman nan taje rafi to wallahi baƙar yunwa take ji gashi bazata iya cin tuwon dawa ba gaskiya saboda bata taɓa ci ba ma haka ta sa aka kira mata Idi Allah ya taimaka yana saida tsire nan da nan ya kawo mata suka shige ɗaka suka yi tass dashi ita da Faɗimo babu wanda suka baiwa gashi zai kai na ɗari biyar,.

Da yake Meerah bata saba ci ba sai taji ta koshi nak kamar Abincin dubu ta cinye sai kawai tayi sallah ta samu ta mike sai bacci.



Washe gari tana tashiwa ta idar da sallah tayi sake komawa bacci abinta wannan shine abinda yasa ƴan gidan mamaki don su basa haka sam sai kawai suka ja Bakinsu sukayi gum.

Can wajen sha ɗaya Meerah ta tashi ta fara neman ruwan zafi wanka ta keso tayi amma ina babu ruwan zafi sai dai ta tafasa,.

Sauran matan gidan babu wanda ya kuka Meerah sai mamar Fateema wacce take matukar son Meerah sosai domin ita haka kawai Allah ya haɗa jininsu tana matukar kaunarta tana jinta kamar ƴar'ta ta cikinta ne, haka ta tafasa mata ruwan wankan ta kai mata ita kuwa Meerah nan matar ta fara burgeta saboda karrama ta da take,.

Tana kammala wankan tazo ta shafa mai ta canza kaya tana kukan kalan kayan muguntarda Salam ya siya mata,.

Tana gamawa taga an aje mata karyawa buɗewa tayi taga ƴar tsame ne da kunuda kuma shayi,.

Saurin ɗauko shayin tayi saboda shi tafi so ta ɗan kurɓa kaɗan ta ajiye kofin nan ta ɗauki ƴar tsamen ta fara ci,.

Tun tana wani yamutsa fuska har tazo ta fara gabzar ƴar tsame kamar an saba ci,.


Sai da ta gama tass kafin ta ɗauko kunun, wani irin bala'in daɗi kunun yayi mata sai da shanye su tas kafin ta koma bacci ba tare da ta fitarda kwanon bama,.

Haka Meerah ta kai wajen sati biyu a Rumdakila kullum sai sun haɗu da saurayinta Idi sun sha hira ya kawo mata abincin rana da kuma na dare saboda na safe babu matsala tana iya cin na gida,mahaifiyar Faɗimo ta kan rika kallon Meerah kamar wata me nazari a fuskarta har Meerah ta gane ta kan ɗauke kai,  kullum sai Innar Faɗimo ta basu labarinta na gaskiya inda yau ma tace zata basu wani abu da bazata taɓa iya mancewa dashi ba a duniya,.


_Kuuu muje zuwa don jin labarin_

_Vote d novel pls wattpaders_

*_short Story_*

🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*
🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
 

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment