Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauran properties nasu dama an barsu sun fita ne saboda an san su sosai kuma suna kwana a nan,suna kwasowa suka biya kuɗinsu na yau sannan suka kora ƴammatan da suka ɗiba har huɗu suka ce baza su basu ko sisi ba,.

Suna fita Musayyaf yayi hanyar motarshi ya shiga sai gida,.

Shi ko Salam bodyguards nashi ne suka ɗauke shi dama shi yace su tafi baya bukatarsu sai gidan Khaleesad,.

Yana shiga ya ganta a falo zaune kan kushin two seater tana kallon hankalinta kwance babu wani Alamar damuwa a fuskarta sai hutu ɗago fuska tayi ta ganshi nan ta sake mishi ko murmushi maimakon yayi farinciki sai haɗe fuska da yayi ya shige ciki,toilet ya faɗa yayi wanka ya fito da towel a hannun shi yana tsane ruwan jikin shi, ji yayi an rungume shi ta baya yasan ba kowa bane zai iya mishi haka illa Khaleesad,.

Bakin ciki ne ya cika shi ya rasa me zai fara yi mata saboda duk ta wani cukwuikuye shi sai kuma yaji tace "Haba my one meya faru kuma babu Abinda nayi maka kafin ka tafi amma zaka wani shigo min babu fara'a",.

Kafin ya bata Amsa suka jiyo muryar su Eesha,da Teemah suna ta ihu suna kiran sunanta,.

Saurin sake shi tayi ta fita da gudu shi kuwa yaji daɗin hakan saboda dama da bata tafi ba yau ubanta zai ci don yanzu duk haushin su yake ji daga ita har Meerah ɗin yara sai rashin kunya a faɗarshi wai,

Tana fita ta daka tsalle ta rungume su duka biyu tana farincikin ganinsu sai kuma tace "na ma yi fushi ku rasa lokacin da zaku kawomin ziyara sai dare",.

Eesha ce tace "haba Leesad ƴar bakarmu ai kema kinsan halin dad baya so muke yawo shiyasa amma kiyi hakuri watarana zamu kawo zo miki tun safe",.

"Yawwa dai sai yanzu hankali na ya kwanta"

"Au daka hankalinki tashi yayi?",.

"Ehh mana ba dole ba ace zuwan dare sai kace masu gane min sirri",. Ta faɗa tana me ɗan kekashe ido ɗaya tana kallonsu,

"Zaki ci ubanki ai" inji Eesha suna cikin maganar ne suka ga giftawar mutum ta gefen su ɗago kai sukayi nan suka ga ashe Salam ne ya wuce su sanye yake da kananan kaya a jikinshi wanda yayi matukar karɓarshi saurin juyowa sukayi a tare suka haɗe baki suka ce "Lafiya kuwa ya ganmu ko sannu bai ce mana ba",.

Ɗan rikicewa tayi ganin a tare suka tambaya yasa tace musu "lafiya kalau kunsan mutumin nawa da shegen ɗaukar kai kamar basarake,jira yake ku ku fara gaishe shi",.

"Caɓ za'a jima" inji Teemah da tunda suka zo ta mayar da hankalinta wajen kallo saboda a na yin wani indiyan series da ta fiso (swaragini) bata bari ya wuce ta sam saboda yana matukar yi mata daɗi,.

Basarwa Leesad tayi kana tace "muje kuci Abinci ko",.

Saurin mikewa suka yi Eesha tace "dama ni a matukar jin yunwa nake" sai wajen dinning suka nufa,.

Salam na fita ya hau motarshi yayi hanyar gidan uwar gidanshi Meerah don ganin wane hali take ciki,.

Yana shiga ya tarar da ita tana bacci saboda bakin cikin da take tattare dashi har fuskarta ya nuna saida ya gama ganin fuskarta tsaf kafin ya fara tashinta daga bacci,.

A tsananin firgice ta mike gami da Addu'a a bakinta,.

Mamaki ne ya kama shi dama Ameerah ta iya Addu'a ne? Sai kuma ya basar yace "ke mike don ubanki magana nake son yi dake"

Ɗagowa tayi da wuri saboda tasan me muryar nan sosai ta saba ji sai kuma taga fuskarnan tashi rufe take da hular fuska (face cap) baka wanda ta mamaye ko ina na fuskar latsa wayarshi yake ko ya kulata,.

"Yi hakuri bacci nake,kuma shiɗin ya mutu baya raye",.

Tausayinta ne ya kama shi saboda yadda tayi maganar kamar zatayi kuka sai kuma yace "Allah ya jikanshi"

Tace "Ameen" sai kuma tayi shiru ta fara neman inda ɗan kwalinta yake, inda yayi caraf da ɗagowar fuskar shi nan yayi karo da gashin kanta kamar na indiyawa yana kan kallon gashin ta ɗaura kallabin ta juyo karaf suka yi ido huɗu dashi Meerah ta fara ihu tace "wayyo me nayi maka? Dama baka yafe ni ba sai ka zo gidana nashiga uku ni Aisha wayyo rayuwa ta wanu irin kunci nake ciki ne",.

Dariya ya fara yimata ganin haukar da take yi mishi sai kuma yace "dalla malama kimin shiru nine dai mijinnaki ABDUL-SALAM dama kinfi kowa wayo ne?kina tsammanin cewa kinfi kowa rashin kunya ne? to nayi Amfani ne da wannan dama na Auren ki domin ramakon Abinda kika yimin sannan ya kamata kisani har yanzu ban gama miki azabar da kika gwada min domin ke fuskata kika mara ni kuma rayuwar nake kan mara Ameera sai na kuntata miki yadda kika kuntata min domin bazan barki ba banza irinki" sai kuma ya fice ya barta a ɗakin baki sangame tana ganin Abin mamaki.......



_Kuuu muje zuwa_

_Vote d novel pls wattpaders_

_🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*_
[10/10, 13:39] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮


  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 2️⃣5️⃣

_________📲Sai kuma ya fice ya barta a ɗakin baki sangame tana ganin abin mamaki.

Haka ta mike da wuri ta bishi falo tun kafin ya bar gidan,ganinshi tayi zaune kan kushin me wajen zaman mutane uku,yana ganin kamar ya aikata abu me kyau ya wani ɗaura kafa ɗaya a bisa ɗaya sao murɗa kai yake.

Meerah ce ta karasa wajen shi ta rike kafarshi tace "ya kai mijina, bai kamata kayi min haka ba, abinda nayi nasan kuskure ne kuma na daina, sannan wannan sanin kanka ne a makaranta kace ka yafe min,to meyasa bazaka yafe min a gida? Muci gaba da zaman da nayi shirin ɗaura mu, nasan cewa a kwanakin baya kaɗan da basu daɗe ba ina da mummunar hali,amma wallahi na canza ba haka nake ba a yanzu,don Allah yaya Abdul ka yafe min". 

Ta karasa maganar ta fashe da kukan nadama,shiko Abdul jan kafarshi yayi yace "ke Ameerah bazan taɓa yafe miki ba,domin Abinda kika yimin bana yafiya ba ne sam,kuma kike ikirarin wani zama ai baki isa ba wallahi,sannan ya kamata kisan cewa na Auro Khaleesad ne ba don komai ba sai don in saki bakin ciki in ba haka ba sam ba sonku nake ba fatan kin fahimce ni".

Meerah da ta wani tsorata lokacin da yayi mata tsawa yasa tayi gefe abinta tana ta rera kuka kamar waka,

A daren ranar saida sir Abdul ya kusanci Meerah don ya kara mata bakin ciki da zafi-zafi yake yi mata, inda yayi mamaki wai har yau ita budurwa ce duk da rashin kunya irin nata amma Khaleesad da take nan shiru-shiru bai samu wannan budurcin ba kawai baiyi mata magana bane saboda yasan cewa ba wani daɗewa zaiyi da ita ba domin badon ya sanya wa Meerah bakin ciki bane yayi Aure haka kawai yaji cewa yana son Khaleesad shi gaskiya yanzu ya tsane ta ba sonta yake ba don haka yana gaf da rabuwa da ita,

Yana mikewa ya wuce toilet yayi wankarshi ya barta a kan gado,da kyar ta iya mikewa tana ɗingishi ta wuce ɗakinshi ta shige toilet nashi ita ma tayi wanka Abinta ta dawo ɗakinta,.

Hango shi tayi kan gado yana lulluɓe da blanket nan taji wata sabuwar soyayyar shi ya kuma shiga zuciyarta saboda yanzu ta tsani kuɗi tunda aka ce mata mahaifinta ba karamin me kuɗi bane da ya rasu an kora su ita da uwarta hakan yasan ita ma bata cire rai ga korarta da za'ayi ba idan Shi Salam ɗin ya mutu,.

Itama karasawa kan gadon tayi ta janyo blanket ɗin da ya saura ta shige ciki ta kwanta suna fuskantar juna,kowanne saukar numfashin sa a kan fuskarta yake yi ita kuwa sai murmushi take ta manta da raɗaɗin da take ji har bacci ya ɗauke ta.

Washe gari da safe tayi saurin tashiwa ta kuma yin wani wankan,tayi saurin zuwa kitchen don haɗa musu abin kari,kana ta koma ɗaki ta haɗa mishi ruwan wanka me daddaɗan kamshi kana tazo ta zauna a bakin gadon ta rasa yadda zata yi ta tashe shi,

Tana cikin zaman tagi ya tashi ya zauna shima yana kallonta,

Sunkuyar da kai tayi kana tace "dama ruwan wanka na haɗa maka shine da nazo banson taso ka daga baccin may be ba yanzu kake taso wa ba"

Murmushi yayi a cikin zuciyarshi kana yayi mamakin irin tausayi da juriya irin na Meerah gashi duk mugungar da yayi mata jiya batayi fushi ba, saboda indai Khaleesad ce da ta ɗaura mishi ruwan wanka ai gwara ya shekara kada yayi wankan, sai kuma ya mike ya nufi toilet ɗin ita kuma ta fita dagudu saboda kada girkinta ya kone,

Da ya fara wankan ya rika mamaki wannan wanne irin ruwan wanka ne me bala'in kamshi?shi tunda yake bai taɓa wanka da irin wannan ruwan ba sam-sam koda me ta haɗa oho,.

Yana gamawa ya fito da towel a hannunshi yana tsane ruwan jikinshi sai ji yayi an murɗa handle na kofar,.

Meerah ce ta shigo sai kuma ta juya saboda ita bata taɓa ganin mace ɗaure da towel ba balle ma namiji shi kuma sai kallonta yake yaga abin mamaki,sai kokarin murɗa handle take zata fita,.

Cewa yayi "idan kika sake kika fice min daga ɗakin nan ni dake"

Tsayawa tayi cak amma sam taki ta juyo saboda duk kunyarshi take ji ta kasa sakin jiki dashi,

Ayi maleji masoya na.

_Kuuu muje zuwa_

_Vote d novel pls wattpaders_

_🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*_
🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮

  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

*_Assalamu Alaikum sakon gaisuwa gareku masoya na masu jinkirin jirana Allah yabar kauna ya kuma sanya mu a Aljanna baki ɗaya nadawo fa da kokari kamar yadda kuka sani a kwanaki ina kokari wajen yi muku typing to yanzu ma insha Allah hakane_*

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 2️⃣6️⃣

_________📲Tsayawa tayi cak amma sam taki juyowa saboda duk kunyarshi take ji ta kasa sakin jiki dashi sam,

Karasowa wajenta yayi ya juyota suka fuskanci juna kana ya haɗe goshin su a waje ɗaya,

Meerah ce numfashinta ya fara sarkewa yana harɗewa saboda bata taɓa jin irin haka ba,

Shikuwa Abdul-salaam sake matsawa yake yi kamar zai haɗiye ta sai wani manna fuskar su yake a waje ɗaya yana shafa bayanta,  hancin nan nata da nashi duk dogaye ne kamar na indiyawa,

Meerah ce tafara kokarin kwacewa saboda tana so taje ta duba girkinta kada ya kone nan Abdul ya sake riketa da karfi,

Kokawa suka fara a ɗakin duk da dai tasan ba iya shi zatayi ba saboda yafi karfinta gashi kuma ya haɗu da tana da ciwon jiya sai kawai ta fashe da kuka,

Abdul ne yayi saurin mikewa ya ɗaura towel nashi da ya kwance, Meerah ta ruga da gudu ta buɗe ɗakin ta fice Abinta,

Tana shiga kitchen ɗin taga Abincin bai kone ba sai dai ya shanye ruwan tass alamar yanada shirin konewa tayi saurin saukewa ta damo flask ta jute ciki,

Bayan ta gama haɗa breakfast ɗinne ta rasa yadda zatayi ta kira Abdul-salaam ɗin saboda gudun kada ya sake yi mata Abun ɗazu, sai kawai ta daure taje kofar ɗakin ta rike handle ɗin kamar zata murɗa ne kamar bazata murɗa ba tana cikin tunanin taji an murɗa handle ɗin ta ciki nan tayi gaggawar matsawa daga jikin kofar,.

Sanye yake da farar shadda shampoo yadda taji ɗinki da zubi kamar ta sarauta yanayin zubin ne ya ɗauke hankalin Meerah saboda bakin zare akayi Amfani da ita kaɗai gashi kuma farar shadda ce kal,Abinka da mutum fari sai ya sanya glass baki da takalmi baki a gaskiya dressing nashi ya ɗauke hankalin Meerah sosai saboda ba karamin kyau yayi ba kamar ka sace shi domin Abdul-Salam ya kai matsayin da kowace mace zatayi burin ya kasance mijinta nan Meerah taci gaba da kallonshi ta mance a she serving spoon ne a hannunta,

Hure mata ido yayi da iskar bakinshi sannan yace "meyasa kike ta kallo na ko nayi kyau ne?"

"Gaskiya kayi kyau sosai kamar in sace ka" shine abinda Meerah ta faɗa a gigice itama batasan zata iya faɗar hakan ba,

Sai ji tayi ya rike hannunta yana nufar wajen dinning da ita ita kuwa ido take binshi dashi,

Saida suka zauna ne ya fuskance ta yace "ba dole nayi kyau ba tunda yau ni sabon Ango ne"

Kallonshi take tayi har yanzu bata iya taɓuka komai,.

Kara dubanta yayi ya kuma duban kanshi yace "lafiya kuwa nidai kada ki cinye min kyau don na lura ke mayya ce maza kiyi serving ɗina zan wuce office"

Batayi magana ba ta fara serving nashi kafin itama ta sa nata ta fara ci babu wanda ya sake yiwa wani magana har suka gama,.

Yana mikewa yace "Alhamdulillah nizan wuce office jakata na gidan Khaleesad don haka zan biya ta can in karɓa ki kula da kanki sai na dawo"

Meerah tace "To Allah ya kiyaye yasa ka dawo lafiya ya kuma kara buɗi"

Jin daɗin Addu'ar yayi sosai kana yayi shiru bai yi mata magana ba ya fice cikin farinciki,.

Yana fita yayi gidan Khaleesad yana zuwa ya tarar da ita sai kwasar bacci take da Alamu ko sallah batayi ba,.

Saurin karasawa yayi ya tashe ta yace maza taje tayi sallah shi zai wuce office,.

Yana ɗaukar jakarsa ya wuce dayake sauri yake,.

Haka yau ya gama wuninsa a office cikin farinciki da Annashuwa sai wajen karfe shida ya dawo cikin zumuɗin ganin wani kalar dressing Meerah zatayi yau kuma,.

Yana shiga me zai gani........... 

_Kuuu muje zuwa_

_Vote d novel pls wattpaders_

_🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*_
[10/10, 13:39] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮

  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

 

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* 2️⃣7️⃣

_________📲Yana shiga me zai gani wata mahaukaciya ce a kan kushin sanye take da wata riga guntu iya cibiya,sai takalmin ta kundura irin na zuwa gona,sai kuma ɗankwalin da ta ɗaura a kanta da kuma zani guntu,yanayin shigarta sak na fulanan jeji gashi duk ta ɓata fuskarta da kwalliya duk janbaki nan an ɓata fuskar dashi.

Tashiwa tayi dagudu taje ta rungume shi,kokarin zillewa yake da iya karfinsa amma ya kasa saboda da iya karfinta ta rike shi itama,.

Tsayawa yayi yana kallonta ido cikin ido,sai a sannan ya gane cewa Meerah ce matarsa,kara waro ido yayi kana yace "Ameerah kece?"

Cikin hawaye tace "Nayi kyau? Nace nayi maka kyau Abdul?" ta karasa maganar tare da fashewa da kuka kuma har yanzu taki sakinshi.

Juyowa yayi daga kallon gefe da yake yi yace "A'a baki yimin kyau ba nikam ko kaɗan,kinma yi kama da mahauta" sannan ya kuma ɗauke kai

Meerah ta ɗan goge fuskar ta da damtsen hannunta tace "dagaske banyi kyau ba? To wannan shine shigar da ka bukaci inyi tayi lokacin da ka kaini ƙauye,Abdul ka cuce ni, ka wulakanta ni,don kawai zaka rama menayi maka shine zaka kaini inda ban iya rayuwa cikinta ba,to gashi hakan da kayi shine dai-dai a gareni saboda gashi sanadin hakan da kamin yasa na samo Asalina da kuma mahaifiyata,nagode da Abinda kayi min" tana gamawa ta sake shi tayi ɗaki da gudu

Dukda yana cikin damuwa saida yayi dariya saboda irin gudun da takeyi bana wasa bane,

Cire babbar rigar shi yayi ya rike a hannu ya shige ɗakin shi ya aje,toilet ya faɗa yayi wanka kana ya sanya kananan kayanshi yaje kitchen ya ɗauko wani cup ya ɗebo fresh milk a fridge ta rike a hannu yayi ɗakin ta.

Bai tarar da ita a cikin ɗakin sai jin karar ruwa da yayi a bayi meshi kamar wanka yake.

Kwanciya yayi kan gadon da bayanshi kanshi na kallon silin sai tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake saboda yaga Alamar tayi fushi sosai.

Fitowa tayi da towel a jikinta babu ko ɗankwali nufar dressing mirror tayi ta zauna a kan table da yake kusa da mirror ta fara tsane ruwan jikinta da towel ɗin tana cikin haka taji an dafa ta a kafaɗa bata juya kallon meshi ba don tasan babu kowa a gidan sai shi,kai kawai ta ɗaga ta ganshi ta madubi ya wani tsaya yana yi mata kallom kurilla cikin madubin.

Sun ɗauki tsawon mintuna kafin Meerah ta buɗi baki tace "dilla malam ka daina kallo na kada ka cinye min Kyau na" tayi maganar cikin sigar shagwaɓa me jan hankali.

Abdul yace "wani kyau ne a nan kwail dake har kina da bakin cewa ni Abdul kada na cinye miki kyau, nida kowacce mace ke burin kasancewa tare dani,ai kamata yayi ki ririta ni gudun kada a kwace miki ni, amma kwaila dake kya tsaya kina wannan zancen" ya faɗa kuma be fasa kallon ta ba.

Meerah ce ta fusata da zancen shi ta mike a fusace tayi wajen wadrobe ta ciro kananan kaya saboda tafi sakewa dasu ta sanya wata jacket da wando jeans ta sanya hular jacket ɗin ta wuce falo don cin Abinci.

Ta zauna kenan tayi serving na kanta sai ga Abdul shima yazo ya samu kujerar da yake fuskantar ta ya zauna.

Bata ko kalle shi ba taci gaba da cin Abincin ta.

Shikuwa gogan naka sai kallonta yake saboda jacket ɗin ya matukar karɓe ta sosai kamar wata ƴar india sai wani sonta yake ji yana ratsa jinin jikinshi ji yake kamar ya maidata ciki tsabar soyayya.

Kara dubanta yayi yace "ni baza kiyi serving ɗina ba kenan?"

Ba tare da ta kalle shi ba ta mike ta zuba mishi komai ta kara komawa ta zauna,

Fara cin Abincin yayi yana santi sai ya kuma cewa "Ni wai in tambaye ki?"

Har yanzu bata dube shi ba tace "inaji" a takaice

"Wa ya koya miki girki ne da shegen girman kan ki da fitsara?"

Ɗago kai tayi ta harare shi tace "koya nayi ai Akwai wanda suke koyarwa"

"Mmmm yayi kyau amma gaskiya kin samu kwararriya"

"Ehhh hakane domin sakeenarth zam-zam ta haɗa komai wajen koyarda girki a online to na koya a wajen wata chef sai ta raina ni nikuma banason rashin kunya ne yasa na sille ta na tafi,shine naga post na sakeenarth zam-zam naga lalle zata iya min training hakan yasa na nemo number ta tayi Adding ɗina a group nata shiyasa na koya" tana gamawa ta mike zata tafi

Riko hannunta yayi yace "haba my princess ya zaki tafi kuma baki koshi ba"

Murmushi tayi a fili saboda har ga Allah taji daɗin sunan da ya kirata dashi sai kuma tace "ba kaine kake ta ɓata min rai ba"

Dariya yayi saboda yadda tayi maganar cikin shagwaɓa ya matukar ja hankalinshi sai kuma yace "to ba gashi na yabi girkin ba ai kwalliya ta biya kuɗin sabulu ko?"

Kallonshi tace "dagaske yayi daɗi?"

Amsa mata yayi yace "tunda nake ban taɓa cin girki me daɗin wannan ba"

Farinciki ne ya cika ta saboda ita tana son a yaba mata sosai,

Kamota yayi ya ɗaurata kan cinyarshi ya fara bata Abinci a baki haka har suka gama,

Suna kammalawa suka yi ɗaki suka idar da sallar isha'i suka yi Addu'a suka kwanta abinsu,a ranar saida Abdul ya nemi ta kara mishi amma fau-fau taki sai dai kawai yayi ta wasanni da jikinta har ya samu bacci.

Haka rayuwar su ta kasance kullum farinciki duk ranar girkin Khaleesad sai Meerah ta jita wani kala saboda batason rabuwa da shubbynta amma ya ta iya dole ne.

Meerah da Faɗimo sun saba kamar da sun san juna amma har yau akwai kunya tsakaninta da mahaifiyarta suna yawan ɓoyewa juna sirrinsu.

Khaleesad kuwa sai rashin kunya take zabgawa Abdul yana ɗan sarara mata ne saboda Meerah tace kada ya saketa bare ace ita ta fitar da ita.

Bayan wata huɗu Allah ya Azurta Meerah da samun cikin wata biyu.

Farinciki abun baya misaltuwa a wajen dukannin ƴan uwa da Abokan Arziki amma Khaleesad bakin ciki ne ya ishe ta fal inda tace kota halin kaka saita raba Meerah da cikin.........







_Kuuu muje zuwa_

_Vote d novel pls wattpaders_

_🎋☞Ⓦ𝔞𝔴𝔩𝔦𝔡𝔞𝔱𝔦𝔬𝔫 *¢ɛ✍🏻*_
[10/10, 13:39] +234 903 129 9157: 🔮🎋:• ´¸.•*´¨) .•´ (¸.•'* 🔮
     🔮🎋*.*.¸¸.*.*🎋🔮
  
  *🇰​'ᗅNWᗅℛ 🇲INIՏͲA*

   🔮🎋:• ´¸.*´¨)  (¸.'🔮
🔮ө🎋*.*.¸¸.*.*.¸¸🎋 🔮

  ༆𝐒тory&𝐖rῖttϵͷ༆
            *ʙʏ:*
     *Wαℓι∂αтισи*
         Ѕ. Мαρι
     ━━     ✍🏻     ━━

*©-Ꮓᴀᴍᴀɴɪ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
(wє ѧяє һєяє ṭȏ єԀȗċѧṭє ṃȏṭıṿѧṭє ѧṅԀ єṅṭєяṭѧıṅ ȏȗя яєѧԀєяś)

*ᴅᴏᴍɪɴ ɴᴇᴍᴀɴ sʜᴀғᴜᴋᴀɴ ᴍᴜ.*

*wαƭƭρα∂:*
*➠walidation_*

*Fᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ:*
➠zαmαní wrítєrѕ ᴀѕѕσcíαtíσn
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation/

*ɪɴsᴛᴀɢʀᴀᴍ*
➠zαmαní_wrítєrѕ_αѕѕσcíαtíσn.

*ʏϴῠ tῠbϵ*
➠zαmαní wrítєrѕ αѕѕσcíαtíσn tv

Assalamu Alaikum masoya littafin kanwar minista yau ne Allah yayi na karasa wannan gajeren littafin naku fatan kun nishaɗantu,ilmantu,kun kuma faɗakartu da wannan labari nawa,dukda nasan cewa wannan page bazata taɓa burge ku ba domin nasa Abu me ban haushi a ciki ku dai ku biyoni don jin ƙarshen kanwar minista.

*🎋Ⓟ𝑎𝑔𝑒➱* complete

_________📲Ya murɗa handle ɗin ya shiga ɗakin yace "naji duk Abinda kika faɗa munafuka,ki tattare kayanki gaba ɗaya kibar min gida na,na sake ki saki ɗaya"

Ihu Khaleesad ta sanya ta sunkuya ta dafa kafarshi tana neman yafiya.

Ture ta yayi yace "kada inzo in tarar dake a gidannan daga gobe" ya fice ya bar gidan yana huci.

Yana zuwa ya shiga ɗakin Meerah ya tarar har yanzu batayi bacci ba idanunta biyu tana kallon silin.

Karasawa yayi wajenta ya zauna kusa da ita ya kamo ta ya tallaɓo kanta ya ɗaura kan cinyar shi ya fara shafar gashin kanta,kafin yace "wifey kiyi hakuri da Abinda ya far,naje gidan Khaleesad ne ba'a son raina ba,ina shiga na tarar da ita tana waya shine naji komai da komai kan cewa ita ce ta sakamin maganin feelings har na kasa samun sukuni ɗazu a wajen Aiki,sannan ina me bakin cikin sanar dake cewa Khaleesad itace ta turo miki wannan kurajen na gabanki....."

Kamin ya karasa ta wani zaburo tace "what?kana nufin Khaleesad ce ke shirin cutar dani?menayi mata to? Menayi mata ka faɗamin!"tana gamawa ta fashe da kuka ta haɗa da kwantawa kan cinyar shi

Ya rasa ta ya zai fara Amsa tambayoyinta kawai sai ya dinga shafa gashin kanta yana bata hakuri har tayi bacci.

Washe gari ta fara ganin Aikin maganin saboda kurajen saura kaɗan su tafi  nan suka koma wajen malamin ya basu magunguna da Addu'o'i don neman tsarin jikinsu suk dawo gida.

Kushin me wajen zaman mutum biyu suka zauna suna fuskantar juna Meerah ce tayi shirin magana sai ji sukayi ana kiran Abdul a waya dubawa yayi yaga governor ne saurin ɗauka yayi cikin nutsuwa da ladabi suka gaisa Governor yake tambayarshi lafiya kuwa Khaleesad ta dawo gida tana kuka taki faɗan Abinda ya faru nan Abdul ya labarce mishi yadda sukayi tas.

Governor ne ya rafka salati kana ya bawa Abdul ɗin hakuri ya kashe wayar dubanshi Meerah tayi tace "lafiya kuwa?"

"Sakinta nayi" Abdul ya faɗa a takaice kana yaci gaba da danna wayarsa.

Batajin daɗin Abin ba harga Allah sai kawai ta dake taci gaba da bashi labari yadda tayi rayuwar ƙauye,nan itama taji ringing na wayarta sunan mom wato maman Abdul-Salam ya fito a jikin wayar saurin ɗagawa tayi suka gaisa tace ga driver zai kawo mata sakon turaren wuta data sa akayi mata a wajen Hajeeya Bilkeesu mai turare da murnarta tace "to mommy nagode sosai" "bakomai" mom tace a takaice kana suka katse wayar a tare.

Kallon Abdul-salaam tayi tace "kaga yadda mommy ke sona kuwa? Turaren wuta zata Aikomin yanzu Wallahi"

Farinciki ne ya cika shi don yana son yaga mahaifiyar shi da matarshi na shiri sosai.

Haka rayuwarsu ta kasance kullum cikin farinciki  gaba ɗaya dangin an haɗe waje ɗaya Meerah cikinta ya kai wata takwas inda mr.president yace bazata haihu a Nigeria

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment