Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinta tafi karfin ace wasune zasu tura ta gani sai dai ita ta tura, A lokacin Nabila baccinta take hankali kwance babyn kuwa yana hannun Dr yana bacci.

Munauwara da tazo hutu a ranar da akayi haihuwar washe gari ta gyara musu kayansu ita da Ramla tace sokoto zasu a motar Haya, ba yadda Mama bata yi ba taki zama dan haka ta kira Dr, sai ya shirya ya je tasha jiransu su iso, a lokacin ne ya kira Nafisa dan ya sanar da ita yaga bata ko kirashi ba....




*kuyi hakuri exam nake yi bazan iya hada typing da karatu ba, idan Allah ya kaimu on 4th February zan kammala exam dina sai mu dora daga inda muka tsaya, Nayi muku wannan ne dakyar saboda naga kunata Nema wasu basusan dalilin dayasa suka jini shuru ba sun damu sosai niko ban jure ganin damuwar don Allah ku kara hakuri nagode sosai da kulawarku a gareni*




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA BIYU




Tayi mamaki kwarai ganin wasu daga cikin course mate dinsu sun kirata sunyi mata barka wasu ma sunzo har gida amma har an wuni an sake kwana wani wunin yaci rabi Nana sule Bata kirata ba kuma bata zo ba, ta San kuma bawai bata ji bane, da wannan tunanin ta wuni har dare kafin ta samu natsuwar kiranta taji ko lafiya.

Babyn yana jikinta tana magana da Munauwara Dr ma yana zaune da abinci a gabansa yana tsakura haka kawai yake jin babu dadi saboda sabanin da ya samu da Nafisa har takai ga ya fada mata maganganu marasa dadi.

Nana sule tana kwance kan kujera mijinta yana gefe zaune yana kallo a system dan basuda wuta, wayarta ta fara ringing, karamin tsaki tayi dan bata so dauka ba ta kuma san halin mijinta bata shirya dogon surutu ba, daga wayar tayi tasa gefen kunnenta tayi shuru Nabila tace "Nana kina jina"? Sai ta amsa mata da "umm ya akayi"? Dan shuru Nabila tayi har kamar ta katse wayarta kila ko bata cikin dadin rai ne amma saitace bari dai inji "Nana lafiya najiki shuru ko baki san na haihu ba" kamar jira Nana take ta bata amsa acikin gatse "Na sani, gani dai nayi banyi muhimmancin da za a kirani a fada min ba shiyasa Naja gefe" Nabila ta daure fuska tace "Kamar yaya Nana? Yanzu ni na haihu kice har sai na dauki waya na kiraki zaki yi min barka"? Nana tace "ai su wayanda kika dauka da muhimmanci kin kirasu kin fada musu, sababbin kawayen naki yayan masu hannu da shuni sai dai naga khadija Isma'il ta tura hoton jariri to meye nawa na cusa kai inda ba a muradi na" Nabila ji tayi kamar ta dauke Nana da mari da ace suna kusa dan haka tace "na fahimta yanzu, tunda haka kika zama aje a hakan idan bakiyimin barka ba dubunki sunyi Alhmdllh, kuma yayan masu hannu da shuni dasu akeyi dan banga mai tsinta ajikin talaka ba" tana gama fadin haka ta kashe wayarta tareda blocking numbern Nana ta kuma goge ta, ajiye wayar tayi ta shimfide babyn ta mike da nufin shiga Daki Dr yace "ke? Waye kike fadawa Magana haka" juyowa tayi ta kalleshi tareda nufar dakin tace "wata ce baka Santa ba" ya gyara zamansa yana cewa "Nabila Sunan Nana fa naji kin kira shine zaki ce ban Santa ba" a hankali ta sake juyowa dakyar tace "Don Allah kabar maganar nan anan bana son sake jin koda sunan Nana ne" yana kiranta ta kyaleshi ta shige daki, daya ke shi baya barin ta kwana sai ya bita har dakin a tsaye ya sameta da pad a hannunta da pant yace "bakiji ina kiranki ba"? Ci gaba tayi da kokarin dora pad din a jikin pant kamar bata san da shigowarshi ba a tsawace yace "bakiji ina magana? Kinsan Allah ki kiyayeni? Kar iya shegenki yakaini bango inda bazan iya controlling temper ta ba" idonta da suka kada sukayi ja ta dago ta kalleshi tace "idan baka iya controlling temper dinka ka dake ni ka huce haushi? Menene na hakikancewa haka duk da bakasan meya faru ba? Pls kowa yaji da damuwar da take ranshi nida kai karka dauki laifin wani ka dora kaina ko kuma ya shafeni" a hasale ya turata kan gado da karfi yace "na fada miki kisan irin maganar da zaki ringa fada min Nabila, ina kiranki kinaji ki kyaleni naga wasu sababbin halaye kike ji tun jiya, duka kuma bawai dan bazan iya ba..." shurunsa ya katse lokacin da Munauwara ta shigo tayi tsuru tana kallon yanayinsu, tana rike da wayar Nabila, cikin basarwa Nabila tace "Yaya akayi Nauwara ko Ramlace ta tashi" ta girgiza kai muryarta na rawa tace "wayarki ake ta kira" mika hannu nabila tayi ta karba ita kuma ta juya jiki a sanyaye, har zata ajiye wayar kira ya shigo wayar true caller ya Nuna sunan mijin Nana sule a rubuce, dagawa tayi tareda yin sallama a hankali, ya amsa yana cewa "kina gida ko kina gidan Mama"  a hankali tace "ina gidana" yace ok kawai tareda kashe wayar, ta sauke wayar tana kokarin tashi daga kan gadon Dr yaki matsawa, dagowa tayi ta kalleshi tareda sauke idonta dan irin kallon dayake mata taga alamar ko dukanta zai iyayi, a hankali ta  rarrafa daya gefen ta sauka ta shiga toilet, zama yayi ya dafe kansa itako da ta kasa sabawa da irin wannan rigimar ta zauna kan toilet sit ta fashe da kuka, hawaye wani nabin wani takai minti goma sha biyar kafin ta fito da idonta sunyi wani iri saboda kuka, baya dakin amma lokacin taji sallamar su Nana dan haka ta sake wanko fuskarta ta fito palon tana kokarin sakewa, gaisawa tayi da mijin Nana sai tayi kamar batasan yazo da wata mata ba ya karbi babyn tare da yi masa addu'a yana dan kokarin yiwa Nabila wasa, yakai minti goma sannan ya kalli Dr yace "Dr ka binciki yaran nan kuwa anya sunada hankali, maganganu marasa dadi suke fadawa juna" Dr ya dan harari gefen Nabila data daure fuska yace "sun daiji kunya dukansu, a tunanina Nana zata kasance cikin mutane na farko da zaki kira ki fada mata kin haihu amma kin kasa yin hakan, lafiya lau kika haihu ko awa daya bakiyi da haihuwa ba kika fito sa kafarki balle kice bakida lafiya ne haka kawai kika zabi bazaki kirata ba kuma ta nuna miki baki kyauta ba zaki jefa mata kalamai son ranki" Najib mijin Nana yadan jinjina kai dan shima yasan Nabila bata kyauta ba yace "idan Nabila ta farayin laifi ai bai kamata ace Nana ta jira har sai ta kirata ba ko kuma tayi fushi dan ni wallahi banda labarin Nabila ta haihu, ni abinda yasa nazo yanzu shine ku Sasanta kanku abin kunya ne aji kunyi fada harda kalamai irin wannan, ku tashi ku shiga ciki dan mu tare muka ganku" Nabila ta mike a hankali tareda kiran munauwara ta fito dauke da Ramla da cup dinta na friso dan inbashi ba yanzu bata cin abinci duk ta tsuke "kawo ta nan ki kawowa bako ruwa da abinci" .

Zaune sukayia dakin kowa tayi shuru sai can Nabila tace "kiyi hakuri, amma kisan irin maganar da zaki ringa fada idan ranki ya baci, ni khadija ko layinta banda bansan ina taji na haihu ba, bata kaiki muhimmanci a wurina ba idan na yi miki abu kuma kiringa fadamin kai tsaye bana son gatse hassalani yake" Nana sule ta kwada mata harara tace "gaskiya nima karki sake yimin hakanan, kin bata min rai kuma bazan zaunaba yau sai gobe zan dawo" mikewa tayi ta fito Nabila na bayanta har lokacin basu saki ransu ba, najib ya tabe baki yace "Dr mu zamu wuce a kara hakuri kasan mata ba hankali ya ishesu ba a karkace suke" Dariya Dr yayi dan shi kadai yasan halin mata suka jefa shi tunjiya yake tunanin irin matakin da zai dauka akan Nafisa.

Nafisa wannan karon bata kirata ba sai ranar suna tazo da yamma kuma kafin magrib ta koma Nabila kuwa data fita iya shege sai ta hanata kayan biki sannan ta hada na Mama ta bawa Farida kanwar Dr tareda na sauran mutane da abubuwan da akayi kamar haihuwar Ramla.

Mamaki ya kama Nafisa dan batayi zaton zata hanata ba sannan kuma ta lura tunda suka gaisa bata sake ko kallon inda take ba saida zata wuce sukayi sallama.

Washe gari da abin ta kwana aranta dan haka karfe tara ta kira Dr bayan sun gaisa tace "dama cewa nayi ko wani abu aka cewa matarka nayi jiya ta wulakanta ni" ya hade fuska yace "kamar yaya" tace "Ahto, nidai ko ruwa bansha ba gidan nan sannan bayan gaisuwa ko kallona bata sakeyi ba wulakance muka yini nida kannena dana kwasa, anba kowa naman suna da abin biki ni an hanani gasunan dai tun daren jiya aka rarraba daga mai kofin glass sai mai jug sai mai bokiti na zamani abubuwa kala-kala" ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "zanji dalili" dan dafe kansa yayi dan yaga yanzu rigingimu na neman yi masa yawa bai san Nana da neman fada ba amma yanzu yaga tana so ta koya aikuwa duk wanda ya ke zugo masa ita sai ya hadu dashi.







*Nagode da hakurin da kukayita yi dani, har na kammala exam, har yanzu ina samun sakon gaisuwa da adduar samun nasara daga gareku bazan gaji dayi muku godiya ba akan wannan kulawar, daga yanzu zuwa duk lokacin da Allah ya bani iku zaku ringa jina har in na kammala wannan labari da yardar Allah*




EXQUISITE WRITERS FORUM 

*Dr A.S. Zaki*

*SAFIYYAHGALADANCHI*
SHAFI NA TALATIN DA UKU




Kura masa ido tayi bayan ta saurare tambayar da yake mata daga baya tadan gyara tsayuwarta tace "mara hakurin har takai karata kenan? Matarka wanzam ce bataso a jikinta amma tana yiwa wasu, ni badan idan na bata zai rage ni da komai bane kawai na hanata ne saboda in rama dan nima naji haushi data hanani na haihuwar yarta yanzu anyi 50-50 kenan" kallonta yayi yana nazarin wannan figaggiyar matar tashi sannan yace "Nabila da kika hanata mai kika karu dashi" yana rufe bakinta tace "kasonta na kara na bawa Nana sule" Cikin bacin rai yace "Nabila wannan rayuwa da kika dauko bazata haifar miki da mai ido ba, ni mijinki ina fada kina fada, Sam bakya bani girmana yanzu idan zugaki ake gara tun wuri ki dawo kan hanya bayan haka Nafisa ta girmeki in bataji darajar girmarki da tayi ba taci darajar girmarki da tayi a gidan miji saboda itace matata ta farko ban wulakanta ta ba duk yadda take kema bazan bari ki wulakanta mini mata ba, wace irin rayuwace wannan kina ganin kin kyauta kenan menene acikin abin biki da bazaki bata ba dan kawai ki barni na zauna lafiya, ban aureki ba saida naga kamar kece zaki kwantar min da hankali na ashe nayi kuskure na fada hannun da bai dace ba, tunda haka kika zaba yayi miki kyau kici gaba Allah ya baki sa'a tunda ni yanzu ban isa dake ba" yana gama bambaminsa ya fita, jikinta yayi matukar sanyi saboda batayi tunanin abin zai juye haka ba, tayi failing wannan jarabawar dan tasan halin matarsa Sam bata cikin wayanda hankalin mijinsu yake kwanciya ta dalilinsu, irin matan nan ne masu neman tada zaune tsaye koda yaushe, komawa tayi ta zauna kan kujera ta dafe kanta, idan har ya hango natsuwar da zata kwantar masa da hankali mai zai saka ta kasa nuna masa abinda ya hango hakan yake, gaba daya taji kamar zazzabi na neman kamata, jiki a sanyaye ta wuni gidan sai dare wuraren karfe goma ya turo mata massage "ku rufe gida ku kwanta bazan dawo yau ba" gabanta yayi mummunar faduwa kenan yama bar mata garin ba gidan ba.

Har zata kira shi sai kuma ta fasa haka washe gari ta wuni babu karfin jiki har wani ciwo take jin kanta yana yi, shikuma yaki kira da gangan, dayaje gida tambuwal kasa yi mata fada yayi tunda baisan bata bawa Nabila ko naman sunan yarta ba ya kuma san Nabila baza ta taba magana ba tunda sai ranar yaji amma sai ya girgiza Nabila ta dawo hayyacinta yafison ganinta kamar wata hudu da aurensu bata tsoronshi kuma bata raina shi ba.




Sati daya yayi a tambuwal sannan ya koma da sasafe ne sai ya wuce makaranta kawai sai yamma ya shigo tana kitchen lokacin da kofin kunu a hannunta da rabi ta dama mata dan saboda damuwa gaba daya ta kasa zama taci ta koshi yadda ta saba tunda yaje bai ko kirata ba, yayi sallama ba kowa a palon sai Ramla ita dinma barna ta samu dan ruwan pure water ta dauko leda daya ta fasa tana juyewa a cup duk ta jika jikinta karba yayi ya dauketa yana cewa "ina kika samu ruwa kike barnatarwa haka gaki da mura" dariya tayi tana masa yarenta da baya ganewa, dakinsa ya wuce da ita ya cire mata kayan ya zauna da ita a hannunshi yana cewa "jeki kiramin mamanki kice nace ta baki wasu kaya kisa" tsugunawa tayi gefen madubi ta janyo burner tana wasa da ita dan bata gane wannan  aiken ba,  daukota yayi suka fito lokacin Nabila tana zaune a palo da jaririnta tana bashi Nono ta rame amma fuskarta tadan kumbura saboda ciwon kai data kwana dashi kwana biyu taje asibiti akace jininta ne bai gama sauka ba tare da rubuta mata magani, "ina yini" tace dashi, ya dan kalleta sannan ya amsa "lafiya lau yagida, ya Muhammad" "lafiya lau, a kawo abinci"? Ya girgiza kai "na koshi dauko mata kaya dai dan ta jika wancen" mikewa tayi ta shiga daki ta dauko mata gown da hula da safa nan ya zauna ya saka mata, haka nan dai ba fushi ba ba kulawa ba suke zaune har ta kusa arba'in yana shirin fita da safe tace "wani sati muna so mu shiga school wajen karbar notification" ya danyi shuru sanann yace "ba matsala sai kiyimin magana idan ranar tazo" ta gyada masa kai ta fita daga dakin, bi bayanta yayi da kallo, ta rame sosai kamar ba Nabila ba kodan wannan  namiji ne yasa ta rame ko dan yanayin da suke ciki ne yanzu babu dadi zaman.

Ranar da zasuje yana shirin fita ta fada masa yace sai tazo, bayan ya wuce ta kimtsa ta dauki ramla da Muhammad zata kai ramla gidansu inda mama kafin ta dawo sai taje ta dauki Nana sule dake fama da laulayi.

Yana zaune a office dinsa akayi kwankwasa ya bada izinin shiga, hasken fatar ta ya kashe masa ido tana sanye da riga da skirt wani irin kamshi da bai taba jin irinsa ba yaji ya dauke office din, ajiye wayarsa yayi tareda da hada tagumi yana kallonta, saboda ta raina shi ko zama batayi ba ta zaga har kusa da shi ta tsaya.

Lokacin Nabila ta iso tacewa Nana "bari na leka naganshi yace in mun shigo inzo" ta fito da sauri tana sanye da riga doguwa da mayafi mai girma fuskarta daga powder sai kwalli da lip balm, wannan karon bata kwankwasa ba kawai tura kofar tayi tana dauke da Muhammad saida ta isa ciki ta yi turus tana kallonsu a hankali tace "kuyi hakuri ban kwankwasa ba" ta juya tareda fita, jikinsa na rawa ya biyo bayanta yana kiran sunanta amma saita tsaya ta hade hannunta biyu alamar roko tace "Don Allah ka tsaya can karka biyo ni don Allah" tsayawa yayi yana kallonta tana sauka kan stairs din har ta fice, a hasale ya koma ya dakawa yarinyar tsawa tareda nunata "Ranar dana sake hada ido dake nayi miki rantsuwa da Allah sai na san waye ubanki a garin sokoto, get out idiot kafin na illataki" ganin yadda jikinsa ke rawa yasa ta fita ya dafa table a fili yace "ta wargaza komai ta ina kuma zan dora"?.

Nabila ta saita kanta ta shiga mota yareda cewa "yace muje can ya same mu" karbar Muhammad Nana tayi tace "to" daga cikin jikinta take jin yadda jikin ke rawa haka ta daure suka gama abinda suke yi suka koma gida, tayi mamakin ganinsa gida lokacin dan ya daina zama. Tana shiga ya taso ya riketa yana hadiye miyau yace "Nabila ki saurare ni karki bari sharrin wannan aljanar yayi galaba akanki" a hankali ta durkusa gabanshi tace "Dr na gaji don Allah ka sake ni kaji, In koma inda Mama, can gidan kusa da ita yafi dadi babu damuwar kowa acan ko akwai batakai wannan ba, don Allah ko da saki guda ne kawai nauyi da hayaniyar auren nan sun miki yawa akai suna neman dakusar dani Nagaji" jikinsa ya kara daukar rawa yace "Nabila da bakinki kike cewa in sake ki kingaji dani da aurena? Bazan iya sakinki ba saboda ina sonki" hawaye suka zubo daga idonta tace "baka sona, dalilin dayasa ka aureni baya tareda ni yanzu, banida nutsuwa har yanzu hankalin ka a tashe yake, bana ganin girmanka bana girmama matarka da kake so baka yimin magana inji, nice fa nabila data sa kabar skt sati daya baka taba ko kirana ba ka gaji dani, ka dawo kuma iyakarka gaisawa dani, banda wani amfani anan pls koda saki daya ne inaso in sake jin banbancin rashin aure da auren shi kanshi" a tsawa yace "bazan iya sakinki ba koda rabin daya ne" ta mike da sauri tace "wallahi saina bar maka gidanka yau" dakinta ta shiga da gudu ta rufe da key ta fara hada kayanta a akwati dana ramla da Muhammad, saida ta daina jin motsintsa ta fito ta dauke Muhammad dake bacci taja akwatin tasa mota yana kallonta ya fita sai ya kira anty Nusaiba ya fada mata, saurin katse kiran tayi ta kira Nabila dan tasan idan ta isa gidan nan sai mama da baba sun sugar da ita cikin sa'a kuwa ta dauka harda gyara murya kamar bakomai anty nusaiba tace "kafin kice komai juya ki koma gidan mijinki" cikin kuka dayazo mata a lokacin tace "Anty nagaji" "ki koma nace wallahi kika je gidan nan idan naje na sameki saina yi miki duka irin wanda baki tsammani" ta kashe wayar, maimakon ta koma sai kawai ta mike bata tsaya ko ina ba saida ta ganta tambuwal, gyara fuskarta tayi ta shiga gidan Mama tayi murnar ganinta ta karbi Muhammad tana cewa "madu ina yar yaye ka barota, Nabila zuwa haka ba sanarwa" Nabila tayi yar dariya tace "aikuwa Mama naga anyi arba'in nace bari nazo na kwana biyu sai in koma" abinci mama ta kawo mata suna dan hira, Nafisa bata nan haka suke hirarsu har tadan tsakuri abincin dan babu kwanciyar hankali ga karyar data tsula wai waji kaninta ya kawota ya koma sai jibi zai dawo ya dauketa, part dinta ta bude tayi wanka ta kwanta baccin gajiya.

Dr kuwa hankali a tashe yake yaga yamma tayi babu labarin Nabila kuma anty nusaiba ta fada masa bataje gidan ba dan taje bataji ance nabila nacan ba.




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA HUDU

Waya ya dauka ya ringa jera mata kira bata dauka, daga karshe ma Muhammad ta goya suka shiga gidan Kanin  baba dagacan ta zauna wurin Raliya suna hira, ba karamin mamaki abin ya bashi ba saboda a iya tunaninsa bai ga abin daukar zafi da zai saka Nabila tayi masa haka ba, anya kuwa lafiyarta kalau? Sake kiran Anty Nusaiba yayi ta dauka tana cewa "wai karkace min har yanzu bata dawo ba" muryar shi cike da damuwa yace "bata dawo ba, bata gidan Maryam kuwa" maimakon ta bashi amsa sai ta katse wayar, Baba ta kira yana kokarin shiga gida ana kiran sallar isha'i a cikin motar ya tsaya tareda daukar wayar, ta gaidashi lafiya lau sannan tace "Baba dazu Dr ya kirani Nabila zata zo gida saboda sun samu sabani sai na hanata zuwa gida nace ta koma, Baba tun azahar ne lokacin dan karfe daya da rabi ne mukayi magana da ita to fa har yanzu bata koma gidan ba koya kira bata dauka" kafin ransa ya baci saida yace "ita Nabila din"? Anty Nusaiba tace "Wallahi ko Baba, mijin yace tun haihuwarta ta birkice masa, to ni bana son kiran wasu daga dangi inda zata iya zuwa kila bata can sai abin yazama tonon asiri" Baba ya sauke ajiyar zuciya yace "Bari inkirata" Nusaiba ta kashe wayar tana tausayin hukuncin da baba zai yankewa Nabila akan wannan iskancin.

Nabila sai lokacin ta koma part dinta tea tasha ta canzawa Muhammad kaya, tayi zaune tana tunanin abinda zai biyo baya, ganin kiran Baba a wayarta ya kara daga mata hankali amma tasan bata isa taki dauka ba, dagawa tayi tareda yin sallama amma bai amsa ba sai ma cewa da yayi "kina ina"? Ta kalli dakinta cikin faduwar gaba tace "Baba ina tambuwal" ya gyada  kai yace "yauwa to ki kamo hanya yanzu kizo ina son ganinki" ta zaro ido waje tace "Baba don Allah ka bari da safe" a hasale yace "Nabila wallahi yau zaki dawo idan kika kwana garin nan abinda zan miki sai ya zarta nazarinki" tana ji ya kashe wayar ta tashi ta maida kayanta data cire ta dauki Muhammad ta shiga bangaren Mama, ta sameta tana fada har lokacin Nafisa bata dawo ba, Baba yana zaune can cikin daki taje ta gaida shi sannan ta zauna jikinta a mace ta fada masa abinda yake faruwa har ya fara yi mata fada bata kyauta ba tace "Baba don Allah kuyi hakuri nidai a samomin driver da zai maidani saboda dare ne bazan iya komawa ba nikadai" ta bashi tausayi dan ya lura a tsorace take sai yace "kiramin babanki" har ta dauko wayarta sai tace "wallahi sai naje yau idan banje ba zai iya illata ni, nidai asamo min driver" mama tana tsaye tana kallon su cikin jin haushi tace "Amma Nabila bakiyi dubara ba, saika tashi ka kaita, ke kuma ki kiyaye kanki inbanda hauka ma fisabilillahi tundaga sokoto kawai dan ranki ya baci" ita duk bajinsu take ba hankalinta yana gida, Baba yace "Tashi muje" mikewa tayi ta fita da sauri, maimakon motarta sai ya janyo tashi, baya ta shiga suka kama hanya yana duba man dake ciki ko zai kaisu, suna tafiya yana mata fada har suka isa lokacin karfe tara da minti goma, jiki a sanyaye ta shiga gidan ko sallama ta kasa yi, Baba dama dakonta yake yana kallonta har ta shiga gida yabi bayanta dakin Mama ta wuce direct amma sai taga bata ciki, tana shirin fitowa baba ya shigo tayi ssurin shimfide Muhammad ta durkusa kasa tace "Don Allah baba kayi hakuri wallahi bazan sake ba" tasan duka a wurinsa bakomai bane sai in baiga damar yi ba, da girmansu sukayi laifi zane su yake amma ita dai tunda ta shiga jami'a bai sake dukanta ba tun wani party data taba zuwa bata dawo ba har sha biyun dare ya zaneta tsaf, sai kuma yanzu da take ganin dole ma sai ya zaneta din.

Hannunsa yasa ya dauko dorina acikin aljihu yace "ba kin iya jan mota har Tambuwal ba, bari ingani yanzu idan na zaneki ko zaki sake tunanin daukar mota kije koda babban titi ne da sunan yaji" Mama tana kitchen sai ihunta taji, ta shigo da sauri tana goye da Ramla, gefe ya koma ya kira Dr yana dagawa yace "zo ka dauke min matar ka daga gidan nan kafin nayi mata illa" gabansa ya fadi dan yana jiyo kukanta, kenan dukanta baba yayi, da sauri ya fito daga gida yana isowa ya samu Baba a kofar gidan "yanzu nake shirin kiranka" da mamaki ya tsaya ya gaida shi tareda cewa "Baba ya akayi kazo nan" ajiyar zuciya ya sauke yace "mu shiga dai kayi min kiran Alhaji akwai matsala ne, ni na kawo Nabila to naji shuru tunda ta shiga" babban palon ya nufa ya tura kofar cikin sa'a kuwa a bude take ya shiga tare da Baba sannan yayi sallama cikin gidan Baba ya leko yace "gata can fitar min da ita daga gidana" shuru

Please Login or Register in order to submit comment