Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tareda jefata daki kan gado ya dawo kusa da ita ta jingina bayanta da bangon toilet din dan matsawa baya tayi ta ce "a kashe wuta" ya harareta yana cewa "maganin me zai miki idan an kashe wutar? Kinga babu abinda zanmiki kuma jikinki ba bakona bane".

Hijab ya dauko mata bayan ta shirya gasunan a jere sunfi guda ashirin amma bata sawa saidai gyale kullum, saida suka shiga mota sannan tace "yau mama tace indawo inkarbi result din a koma wajen likita" cike da mamaki ya kalleta "yaushe kika je asibitin" ta ce "jiya naje dagacan ma na wuce gida aka samin ruwa bayan sun kare ne mama tacire sena dawo"  gyara zamansa yayi ya ce "saboda kina fushi dani shiyasa bazaki iya fadamin bakida lafiya ba? Nabila bana son fushi musamman a wurin karki sake bohemian ciwonki , shuru tayi bata ce masa komai ba, amma yaji haushi tunda har tambayarta saida yayi taki fada masa ruwa aka kara mata.

Yana rike da hannunta har suka karbi result din suka kaiwa mama ita tayi leading dinsu wajen likita, a tare suka shiga dakin har mama likitan ya duba result din yaga da akwai ciki 7wks bayan ya fada musu yayi mata tambayoyi tareda rubuta mata magani da shawarwari sannan ya dago yana dariya yace  "Na manta fa mamanki ma aikaciyar lafiya ce, zata baki shawarar data tace but pls you take care of your self and the baby" kunya ta kama ta sai ta sunkuyar da kanta kasa, bayan sun fita likitan ya tsaida Dr A.S suka sake gaisawa yace "kamar nasanka a dan fodio ko"? Dr ya ce "ba mamaki wane department kasan ni"? ya ce "nan wajen su Prof. Jabir" yayi murmushi yace "eh tabbas" likitan yayi kasa da murya yace "to a kula da yaron cikinnan dan baiyi kwari ba kar ya fita" murmushi kawai Dr yayi ya ce "nagode insha Allahu zan kiyaye" dan sosai ya fahimci abinda yake nufi. A zaune ya sameta wajen wani bench ya zauna yana cewa "tashi mu tafi sai a siya maganin kan hanya ko"? Ta ce "mama ta tafi ta siyo" ya ce "abin yayi yawa jiya tayi yau ma tayi bari ta dawo dai" suna nan zaune ta dawo ta mika mata ledar shikuma.ya ciro kudin aljihunsa da bashi da tabbacin ko nawa ne ya mika mata yana cewa "Mama ga kudinki don Allah ki karba" tayi murmushi tace "aikam ko zan karba sunyi yawa dan maganin dubu takwas ne da dari uku" nacewa yayi saita karba yasan kila bazasu wuce dubu sha uku ko sha biyu ba dan 20k ne yasa mai 5k ya siyo cream 1800 da sleepers din toilet guda biyu.

Chicken Republic ya tsaya ya siya musu abinci da kaza da sauran tarkace sannan ya wuce gida, suna shiga ya ajiye ledodin hannunsa ya rungumeta yana fadin "sannu Aisha Nabila sannu, nagode Allah ya biyaki ya miki albarka, kiyi hakuri Abubakar ya bata miki rai shekaranjiya kiyi hakuri yar kanwata kiyi hakuri matata, Allah ya sauke ki lafiya"....

 



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_ 

SHAFI NA GOMA SHA TARA




Lafewa tayi a kirjinshi saboda turarensa ya mata dadi, ga bacci da take ji, hannunta guda daya ta saka ta zagaye bayanshi, ajiyar zuciya ya sauke saboda wannan shine karo na farko data kai hannun ta jikinshi da son ranta, raba jikinsu yayi ya kalli fuskarta yace "badai bacci ba"? Komawa tayi ta kwanta tace "bacci da yunwa" kan doguwar kujera ya sauke Su a tare ya ce "tashi to ga abincin kuma ni bantaba ganin bacci a tsaye ba" murmushi tayi wanda itama batasan dalilinshi ba saida dimple dinta guda daya ya lotsa ta bude idonta tareda cire hijab dinta ya kalli fuskarta data dan kode saboda zazzabi da rashin kwalli a ido, dining table ya nufa ya dauko plate tareda daurayeshi ya dawo kusa da ita ya zauna, juyewa yayi sannan ya tura mata gabanta yace "don Allah ki cinye shi kinji" tana kallon plate din bakinta ya cika da miyau ta saci kallonshi taga ba ita yake kallo ba, sai taja plate din gabanta ta fara ci, shikuma mama yaketa kira a waya bata dauka ba ya nace saida ta daga tareda fadin "malam ko uwarka na kashe bazaka dameni da kira haka ba, salla nake yi fa kar in makara idan shabiyu tayi ka azzabe ni" dariya yayi mai dan sauti sannan yace "Mama kiranki nayi fa in fada miki yanzu muka dawo daga asibiti kin kusa samun jika" kunyar maganar taji ta ce "kaikam bakada kunya ko? Ina diyar tawa take? Kwana biyu bata kira ba ashe babu lafiya" ya dan kalli gefen Nabila yaga tana tsakurar naman kamar bata son ci ya ce "gatanan Mama abinci take ci kwana biyu bata samu taci ba sai yanzu" Mama tace "to ka gaisheta anjima zan sake kira" yana sauke wayar ya kalleta suka hada ido sai ta marairaice fuska da hannu ya mata alamar menene a hankali tace "pls ja daina fadawa mutane" ya zaro ido ya ce "Akan wane dalili" tadan turo baki "kunya mana nidai ka barsu inya fito zasu gani" dariya kawai yayi ya bude nashi takeaway ya fara ci, itakam daukar nata tayi ta wuce daki kafin minti goma ta cinye tasha ruwa sannan ta kwanta, ya leka dakin dan yajita shuru yaga tana bacci, shima wucewa dakinshi yayi ya kwanta saboda baccin da yake  ji.

Gaba daya week din bata je school ba sai wani satin tana gida tana hutawa, kullum sai mama ta kirata taji lafiyarta, itako batada wata matsala sai dan zazzabi da take kwana dashi kuma da safe sai ya gudu, abin nema ya samu ci ya karu nan take ta cika ido, cikin da baifi wata biyu ba kana kallonta zaka fahimci akwai Sam bai rufa mata asiri ba.

Ranar data koma makaranta ranar sai karar fitar motarta yaji ko sallama batai masa ba, dole shine ya rufe gidan yabi bayanta, takai minti ashirin da isa sannan shima ya iso dan saida ya fara shiga office sannan ya nufi class din, dukansu natsuwa sukayi sunan kallonshi kafin ya fara abinda ya kawo shi, yana kallon wani saurayi a gaba da wani littafi ya kura masa ido sai yayi pointing dinshi tareda umurtarshi daya bashi littafin, bayan ya kawo masa ya tsaidashi nan gaban class sannan ya mika masa littafin yace "read that number 1, I mean you read it out loudly I want the whole class to hear you" yaron ya soma karantawa the biological needs for individuals or members of an organization, the need for air, water, food and sex, yana zuwa nan ya katse shi tareda cewa "so bros you like sex ba" gaba daya ajin aka dau ihu, shi kanshi seda yayi dariya tareda fadin "you know what? Morocco is very good in this harmattan, the weather ehn..." class din suka sake ihu wasu na kiran Marlians, yayi shuru saida ajin ya nutsu ya ce "Marlians never graduate, bros go and sit down but pls concentrate for you own Good" lokacin ya hada Ido da Nabila ta harare shi tareda turo baki, ci gaba yayi da lecture dinsa yayi yana dora idonsa akanta lokaci zuwa lokaci har period dinsa ya kare ya fita bayan ya tura mata massage yana cewa "let's meet in my office I'm Hungary and I want to kiss those your soft and sexy lips" tana karantawa tayi murmushi tareda kallon Nana ta ce "ya zanyi in saki jikina da mutumin nan" Nana ta kalleta lokacin da take harhada kayan babynta acikin jaka tace "kamar yaya"? Ta danyi shuru daga baya tace "ina son mutumin nan yanzu, bana son yadda nake yin dari-dari dashi, ina son nima in nuna masa soyayya" Nana ta danyi dariya tace "rufe idonki zakiyi awurin da kike jin kunya, idan kina bari kunya ko shakkarshi na rabarki to zakiyita cutuwa ne, daga yanzu idan ya taba ki kema ki taba shi, sannan ki ringa yi masa hira ki gani idan bai miki responding cikin jin dadi ba" nazari ta danyi sannan ta mike ganin ya kira wayarta ta ce "bari na tafi yace yana jin yunwa" sallama suka yi Nana ta nufi mota dannyanzu mijinta ya siya mata tare da mai reno take zuwa.

Saida ta kwankwasa ya bata izinin shiga sannan ta nufi can lungu ta zauna bisa carpet tareda ajiye kular abincin data dauko daga mota "a daina maganar sex a class sai a ringa sawa yan aji suna kallona" daga nesa da yake da ita ya wurga mata wani kallo tareda tasowa yazo ya zauna kusa da ita ya hade bakinsu, kokarin cire mata hijab yake saboda gudunmawa daya samu daga gareta sai aka kwankwasa kofar, tashi yayi ya gyara zaman hular sa wacce ta gangara tayi bayan keyarshi ya dawo da ita daidai sannan ya ce "come in" tareda zama kan kujera, bude kofar tayi ta shigo yau tasa straight gown data matukar bayyanar da surarta anyi wani huda ta gaban rigar kirjinta ya leko ta wurin take kamshin turarenta ya mamaye office din dan karamin bakinta yasha Jan baki maroon, maida kallonsa yayi kan system yana karanta ayoyin alqurani da suka zo kansa da adduar neman tsari daga sharrinta, sam bata lura da Nabila a office din ba ta soma cewa "Dakta na sake dawowa da kokon barata, ni bai dameni da kayi aure ba dan nasan wannan busashiyar da aka nuna min tayi maka kankanta a gado bazata oya daukar nauyinka ba, ni kuma fa da wannan kadai sai ka iya biyan bukatarka, idan baka yadda ba mu gwada aure na yarjejeniya koda wata shida ne na tabbata randa ka ratsani wata mace bazaka sake jin ta a mace ba saboda nayi musu zarra" tunda ta fara magana ya fara aikinsa harta kammala zance ko daya bai kama ba, hasali ma wani sako yake kokarin turawa.

Nabila data daskare a wurin jin wannan mummunan batu gabanta ya ci gaba da faduwa, dama akwai matan da kewa malamai irin haka tayi sake? Tab... ta furta a zahiri cokalin hannunta ta saita ta kasan table dinda ke kusa da ita ta jefa sai a kafar yarinyar, tayi saurin rike kafa tana cewa washh... Nabila ko daga kasan da take zaune ta cire hijab da dankwali ta mike tsaye tana sanye da straight gown ta material tabi jikinta daya murmured ta kwanta gashinta dayasha gyara ya sauka kan kafadunta, durkusawa tayi ta dauki wukar data hado masa da ita da wani spoon taje direct ta zauna kan cinyoyinsa.....





*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN

Kamar zaiyi mamaki sai kuma ya fasa ya tsaya sauraren abinda take cewa a kunnensa "turarenta yayi karfi da yawa kace ta fita, kamar turaren aljanu" shima daidai kunnenta yayi magana "Ni ma sam baiyi min dadi ba bari in kore ta" ya fara kokarin dagata taki kafarta ta saka tayi rolling din kujerar sai ya kasance iita ke fuskantar yarinyar, spoon din hannunta ta jefa mata tanayi mata murmushi tareda nuna mata kofa tace "dan bamu wuri don Allah" ta fada tana dora bakinta kan nashi, ganin abin yafi karfinta ya sata mikewa tareda fadin "an saba da karuwancin kenan, batayi darajar da zakuje ba sai a office kuke lalacewa mtswww" taja dogon tsaki tareda rufe kofar da karfi bayan ta fita, sukam basuma fahimci surutunta ba, sai bayan ta fita Nabila ta tashi daga jikinshi tareda saka hijab dinta gudun kar wani malami ya shigo ya gansu, Dr kuwa jiki a mace yake kallonta murya kasa-kasa yace "Ashe kin iya" daure fuska tayi tace "wacece wannan"? Murmushi yayi ganin wai ita kishi take ya ce "yadda kika ganta nima haka nake ganinta, ban taba kulata ba haka take zuwa ta karaci surutunta ta fita" ta sauke ajiyar zuciya sannan ta zuba masa abinci bata sake cewa komai ba saida ya gama ci sannan ta dauki kayan tace "Bari in wuce gida sai ka dawo" paper ya dauka da marker yayi rubutu ajiki sannan ya dago mata "Honey idan na dawo yau pls kiyimin irin yadda kika min yanzu yayi dadi, I love you" murmushi tayi irin najin kunya sannan ta fita yadade yana kallon kofar yana dariya sannan ya maida hankali ga aikin da yake yi, yana cikin aikin aka kwankwasa kofar tareda turowa, assistant exam officer ne ya leko tareda cewa "shege dama haka kake so" dan bata rai Dr yayi sannan yace "kaifa ka bala'in raina ni, wai ba oganka nake ba" karasa shigowa yayi yace "yanzu naga yarinyar nan daka zubar mana da girma ka aura naga tayi kiba ciki gareta ko" juyowa yayi yana kallonsa yace "meyasa baka tambayeta ba da kuka hadu yanzu, ai gara ni dakai dan kaniyarka kai mai mata uku" Dariya sukayi a tare sannan suka zauna suna tattaunawa akan dora result din dalibai na semester dinda ta wuce.

Nabila bayan ta isa gida ta rage kayan jikinta nan ta fara shara tareda kiran wayar Nana sule tana dagawa bata jira wani amsa sallama ba tace "Nana don Allah ina yarinyar nan da muke ririta kyaunta da shigarta har muka ce tana nuna tsiraici gata da jiki mai kyau"? Nana tace "Eh ko yau ma na ganta bayan kin wuce wai wane department take"? Nabila tayi dariya tareda rike haba tace "department din ubanwa ko? Yarinyar nan fa yau office din Dr take bata san ina ciki ba tana masa karuwanci, harda fadin inya kusanceta bai sake jin dadin wata mace" Nana sule ta zaro ido tareda matsawa nesa da yarinyar dake mata aiki ta bar kitchen din gaba daya tace "Nabila! To me kika yi" Nabila tace "kora shegiya nayi na jejjefeta da cokula shikuma na haye jikinshi na mamayeshi, ahhh ashe duniya ana yan iska irin haka" Nana tace "zauna nan kina tsoron miji kigani, wanann yarinya mai shegen kyau da kayan aiki ai wallahi inbaki tashi tsayeba bakisan yaushe take zuwa ba zata iya janye masa hankali" Hankali a tashe Nabila tace "kayan nan da kika bani ranar ruwan nan me ake dashi rubutun is not clear" Dariya Nana tayi tace "ahh dan uban yarinya yau ta nemo su, tsarki zaki ringayi dasu kamar wanann ne da mama ta baki lokacin aurenku" kashe wayar tayi ta ruga daki ta nemosu sanann ta dawo da sauri ta gyara gidan tayi girki, sannan ta kwanta la'asar nayi ta tashi tayi wanka da salla ta saka riga da skirt ta debi abincinta taci kadan ya rage bata koshi ba sannan ta dawo ta zauna tana kallo a haka ya shigo ya sameta lokacin daya turo kofar ta tashi zaune tana kallonshi tana murmushi saida ya iso kusa da ita sannan ta tashi tsaye babu komai a hannunsa sai wayarshi, ta rasa mai zatayi sai shine ya rungumeta yana cewa "Haka zaki ringa yimin idan na dawo" sai ya soma tafiya da ita yana cewa "sai ki rika hannuna ki kaini daki ki rage min kayan jikina ki hadamin ruwan wanka, dalilin dayasa bazaki min wankan ba yanzu saboda kwalliyarki tayimin ta samu wurin a zuciyata ta zauna" bayan sun shiga dakin ya raba jikinsu saita nade hannyenta ta kalleshi tace "kodai kai abokin Alinuhu ne"? Janta yayi jikinshi a kunnenta yace "Abokin Nana Aisha dai" toilet ta wuce ta hada masa ruwan wankan sannan ta koma palo ta hada abincin a palo ta lura bai cika son zama dinning cin abinci ba, ya fiso ya zauna kan kujera palo ya janyo small side table ya dora abincin a kai yaci. Fitowa yayi da waya a hannunsa yana cewa "gata" ya makala mata wayar a kunne kafin tayi magana taji ance "Anty Ina yini, Anty munauwara ce, Babanmu ya kawo mu tambuwal jiya anty kice uncle yazo ya daukeni yau" tayi dariya tace "lafiya lau munauwara, sannunku da zuwa amma ki bari sai gobe dan yanzu yamma tayi yanzun nan ma ya dawo daga wurin aiki" munauwara tadanyi kasa da murya alamar bata ji dadi ba tace "To anty gobe don Allah da sassafe kuma na kawo miki tsaraba" godiya tayi mata sannan sukayi sallama, ta ajiye wayar tana cewa "sune yaran margayiya ko"? Ya gyada kai yana cewa "Aini yanzu ni zasu gwadawa bone, itafa munauwara ta gama secondary school shekarar nan ina gaya miki ta kwaso kayanta duka karatu zatayi tace school of nursing take so" Nabila tayi dariya tace "bakomai ai tazo idan Allah ya bata sa'a nan take zata kammala" abincinshi ya fara ci batareda yayi magana ba, saida ya gama sannan ya koma kusa da ita ya ce "ina alkawarina, kinsan kince zaki min tanadi mai kyau" dan rike baki tayi sannan tace "to ina zuwa" duka hasken palon ta kashe ta sauke labule sai ya kasance babu haske sosai ta dawo kusa dashi ta ce "rufe idonka to" cike da son sanin me zatayi ya rufe idon, ya dan jima da idon a rufe sannan yaji tana cire T-shirt din jikinsa kafin yaji ainahin fatar jikinshi da tata a hade (To ni iya nan na tsaya bansan abinda ya faru daga nan ba 😄).

Gefen gado yake kwance yana kallon yadda take kai kawo tsakanin madubi da wardrobe, daga baya taja ta tsaya tana kallonshi tace "don Allah ka daina kallo na haka kana sa inajin wani iri, kuma kana ji Ankira sallar ishai kana kwance" da hannu ya mata alamar tazo tana zuwa ya ce "na rantse da Allah i need more, i want us to spend the whole night doing it" zaro ido tayi taja baya tareda cewa....


 


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA

"Aradu cikina ya fara ciwo ka bari sai gobe" shi har ya manta da batun cikin ma, dan marairaice fuska yayi yace "gobe fa ko anjima" ta harare shi irin na wasa ta ce "sai naji sauki kuma" tashi yayi ya shiga toilet yayi alwala, sanann ya wuce masallaci.
Washe gari karfe goma ya tafi tambuwal ya dauko munauwara, koda suka shigo tana kitchen ji tayi an rungumeta, juyowa tayi tana cewa "sannu da zuwa" yarinyar tana sanye da wando jeans baki da top pink sai gyale karami kafarta da takalmi masu kyalli half cover tana ta zuba kamshi a ranta tace "to yaran bariki kenan" jan hannunta tayi tace "kin tada uncle tsaye ko" munauwara ta yi dariya tace "aina fada mai tunda aka hanamu zuwa bikinku to nan zan dawo gaba daya kuma dadynmu ya yadda" shikenan Nabila tace ta shiga kitchen tana kwaso kayan abinci tana tunanin yadda zata zauna da yarinyar dan dole tana bukatar gyara bazata iyaa da wannan duniyancin ba.
Sai da ta ajiye warmers din da ruwa sannan ta kalleta tace "shiga kitchen nauwara ki dauko plate da spoon" mikewa munauwara tayi cike da rashin sabo amma batada kyuya ta wuce kitchen din ta dauko, da dare daki daya ta kaita na kusa da nata ta tsaya kanta duk saida ta jera kayanta inda ya dace sannan tace "kiyi wanka kizo palo idan bakijin bacci" munauwara ta dan turo baki tace "Nidai na gaji wallahi basai nayi wanka ba" Dariya Nabila tayi tace "to zo muyi kallo amma yakamata kiyi wanka" bi bayanta tayi tana cewa "ai babu inda naje yau gashi nayi aiki na gaji" Dr yaga har shabiyu suna kallo ya kallesu yana cewa "kai ku tashi ku kwanta kallon ya isa haka" munauwara ta mike tsaye tana hamma tace "uncle sai da safe" girgiza kai yayi yana kallonta yarinya duk dabiun sangartattun yara take yi gashi dai ta girma ko aure akai mata tsaf zata zauna, kallon Nabila yayi yana kashe mata ido daya, murmushi tayi ta kalli dakin da Munauwara ta shiga taga har ta turo kofa ta rufe bayansa ta zaga ta haye ya wuce da ita yana cewa "gaskiya karki biyewa wnanan yarinyar batasan dadin aureba kar a shigarmin hakki da lokaci a cuceni" lafewa bayanshi tayi tana cewa "ni wallahi bacci nake ji" Saida ya sauketa kan gadon yace "ai ban hanaki yi ba".
Washe gari karfe tara ta fito ta shiga dakin nauwara ta tada ita tace "muje ki tayani mopping nikuma inyi shara" cinyarta ta dora kanta tace "Anty bacci be isheni ba gashi dazu kin tadani salla" Nabila tace "eh idan muka gama aikin kikayi breakfast da wanka saiki kwanta abinki kiyita bacci" tashi tayi tana layi ta shiga toilet ta wanko bakinta sanann suka fara aikin, tanayi kamar batada karfi dagangan Nabila ta kyaleta, bayan sun gama sai ta nufi kitchen bata kirata ba dan tasan tunda bata saba ba idan tace zata loda mata aiki zai iya sawa gidan ya fita a ranta, ita da kanta ta zauna ta fere doya ta tafasa tana kokarin dakawa ne Munauwara ta shigo ta tsaya gefenta tana cewa "Anty me zakiyi"? "Yam balls" ta amsa mata, murmushi tayi ta karba tana cewa "ki kawo na iya" Nabila ta sakar mata tana cewa "to idan dai baki iyaba kika lalata abincin uncle dinki ne" "idan yayi dadi me zaki bani" Nabila tace "ki shiga dakina duk abinda kikeso ki dauka" kayan miyan data deba ta shiga wankewa dan yau bata jin karfi a jikinta, so take tayi ta kammala abinci ta ajiye har dare, ganin yadda munauwara ke aikin ya nuna mata ba shine farkonta ba amma dai sam babu sauri cikin lamarin har sai da Dr ya shigo kitchen din yaja kujerar roba ya zauna bayan ya hada tea da kanshi, tana tsame zubin farko ya ajiye mata plate ta juye masa bai fita kitchen dinba sai da ya cinye yasa hannu a aljihunsa yace "Munauwara ki fadamin gaskiya inke kikayi girkin nan duk abinda na ciro a aljihuna naki ne" juyowa tayi ta lasa yatsanta manuni ta nuna sama, dariya yayi dan ya fahimceta ciro abin dake aljihunsa yayi dari bakwai ne aciki da wani pen dayake mutuwar so da yake yanada irinsa sai ya mika mata duka ta karba tana tsallen murna, Nabila ta girgizai ta ce "to ai kuma ni na fere doyar na yanka na tafasa, abani nawa kaso" dariya yayi yace "to ke uwar diya naki kyautar daban ne ki biyoni dakina in baki" "Na rantse da Allah ba irinshi nake so ba kuma in baka biya ba kasan sauran" tashi tsaye yayi ya fita waje yana cewa "Ni ai ba bakon tsanani nake ba, inada canji bari na baki" "Ahto gara ka kawo dai" babu dadewa sai gashi ya dawo rike da kudi ya mika mata tana dubawa taga dari hudu yan canji ne ya tarkato harda nera goma aciki" gabanta ta ajiye tace "bakomai na gode ai ba a maida hannun kyauta baya" bayanta ya tsaya tareda fadin "hannun kwace dai danni banganki kike fere doyar ba diyata na gani tana aiki har ta bani naci" dariya tayi tace "duk abinda zakace nidai an bani kudina Anjima da yamma zan kashesu, Nauwara ai zaki rakani cikin gari in siyo gumbar kwai da kwai ko" Munauwara tace "wallahi ko zan rakaki Anty dama sau daya naci tunda nazo tambuwal" mika mata kudin tayi tace "karbi kaimin daki ki boye su dakyau kafin ya dauke abinsa" kashe gas din tayi sannan ta fita da sauri tana amsawa da to, juyowa tayi ta kalleshi tace "Oya na kora mata ita rungumeni yadda ka saba" hadawa yayi da bakinta ya kuma rungumeta yace "shiyasa nake sonki kina ganewa" ya sake hada bakin su, Munauwara data dawo daga ajiye kudi ta shigo tana fadin "Anty ga wayarki ana kira" saurin komawa tayi tana fadin "lahhh" saurin raba jikinsu sukayi Nabila ta zaro ido waje tace "rashin hakuri kesa a tauna alewa, yanzu dai gashi yarinya ta gani" tsaki yayi ya juya ya fita a tsaye ya ganta dan nesa da kofar kitchen din harararta yayi ya ce "ke bakisan ana sallama in za a shiga wuriba ko a kwankwasa? Allah yasa in sake ganin kinshiga inda mata da miji suke baki jira sun baki izinin shiga ba" cike da mamaki tabishi da kallo saida ya shige daki ta tura baki ta shiga kitchen din, kasa kallonta Nabila tayi ta karbi wayar ganin Anty Maryam

Please Login or Register in order to submit comment