Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, kiranta tayi bayan ta daga sai taji kukan jariri cike da farin ciki tace "Anty meramu na ta sauka lafiya ko" Anty Maryam tayi dariya cike da karfin hali tace "ga babynki nan Nabila ko gogeshi ba ayi ba" "Alhmdllh anty sannu kuna asibiti kenan ko" maryam tace "Eh tareda Mama muke da anty nusaiba inaji sukace kar a kiraki se an sauka, kidaiyi kokari kizo kinji" Nabila ta ce "yanzu kuwa zaki ganni ina sauke tukunya" kashe wayar tayi ta leka dakinshi tana fada kanshi tana cewa "sweety na Anty meri na ta sauka suna ma asibiti" "Haba Nana yanzu wannan fadowa haka idan kika yimin barna fa" ya fada yana gyara mata kwanciya ajikinshi "yi hakuri, nidai yanzu zan tafi idan na sauke abincin dana dora" "Eh zan kaiki amma ki daure kibani minti talatin ajikinki dan gaskiya akwai matsala" tafa hannayenta "don Allah kabari in tafi" tabe baki yayi yace "inkin barni nayi inkaiki inkin hanani musha zamanmu cikin gida" Komawa tayi ta kwanta tana cewa "Ayyah baby kar a sallamesu ban je ba" bai kulata ba ya fara debar garar shi.

Munauwara ita ta sauke shinkafar data dora taje tayi wanka bayan ta rage wutar gas din.

Tana kallo a palo suka fito Nana da shirinta shima ya shirya ta bisu da kallo Nabila tace "jeki dauko mayafinki amma ki canja kaya ko ki saka rigar datafi wannan tsawo" kallon kayan tayi tace "Anty saboda me" Nabila tace "katuwa dake bazan fita dake a haka duniya na kallo ba, kiyi dressing decently" dakin ta koma tana turo baki dama saida ta samu matsa da mama ta tambuwa akan kayan da take sawa, riga da skirt tasa na atamfa ta dauko mayafi suka wuce, tunda suka je Nabila tana rike da Babyn itako Munauwara tana like da ita har aka sallamesu suka wuce gidansu Nabila, Maryam ta kalleta ta ce "saura ke Nabila kiji yadda ake ji, wallahi nakuda ba karamin azaba gareta ba, jinai kamar raina za a cire" Nabila tayi dariya tana cewa "haka kowa ke fadamin nidai inaga zuwa zanyi idan lokaci yayi ayimin CS acire babyn" anty Nusaiba dake kusa da ita ta daki kafadarta sosai tace "ubanki zanci idan na sake ji, wallahi saima in fadawa yaya wannan shegiyar dabarar ina kika samota? Haihuwa ibadan Allah itace baki so kiyi da kanki? Tun wuri kisan halinda kike ciki, kiyi addua Allah yasa ki sauka lafiya bawai a fedeki dan raayin kanki ba" shuru Nabila tayi tana sosa kafadarta nan fa Maryam da Anty nusaiba suka sata a gaba, suna yi saiga matar yaya ta shigo ita an taba yi mata CS din haihuwarta ta farko dakyar ta sha saboda jikinta be saurin warkar da ciwo, anan dai sukayi ta bata shawara har ta sake da kuwa taji haushin yadda anty Nusaiba tayi mata.

Anayin magriba Dr ya je ya dauko su yana cewa "To ya zamuyi da munauwara gobe gashi zaki je makaranta"? Ta ce "Abu mai sauki muje tare" ya girgixa kai yana cewa "lecture zaki shiga da ita"? Tace "A'a saita zauna a mota" hannunta ya rike yace "Ni zan kaiki tunda lecture daya ce sai dai ta zauna a motata idan kun gama ku kirani na maidaku gida" ta amsa masa da to.

Haka kuwa suka ringa yi har ranar da za'ayi suna kullum daga makaranta sai ya kaita gidansu, Munauwara nan take ta sake tayi kawa diyar kawun Mama kusan shekarunsu daya sai watanni suka banbanta sunan yarinyar Hauwa, ran suna sai dare Nabila ta saka su a idonta daga gidan ko har hauwa binsu tayi saboda kawancen na farko ana daukin juna, gashi Hauwa tanada waya itako Nauwara batada waya sau biyu babanta na siya mata daya wajen dambe da kaninta wanda ke binta aka fasa na biyu a makaranta aka kwace koda aka dawo dashi wai engine ya mutu kallo sukeyi da wayar da chtn da samari yan yara kamar su ba hirar iskanci suke ba amma wai soyayya suke da surutu mara kan gado.

Sai da Babanta ya kira waya sannan ta koma gida, bayan ta wuce Dr yace to sai su shirya aje tambuwal ayo kwana hudu, Nabila ta shirya harda kayan abinci ta deba suka tafi.

Mama tayi farin cikin ganinsu, koda suka shiga gidan Nafisa tana zaune kofar palon Mama sanye da riga da zani complete kanta ba dan kwali, babu gashi duk kitso ya tsufa, Nabila ta gaida ita taki amsawa, dama baccin kirki bata iyayi tunda taji Nabila nada ciki a wurin kanwar Dr Farida, Nabila bata damu ba ta wuce part dinta bayan ta karbi makulli saida suka huta sannan ta dafa musu abinci dan ba asan da zuwansu ba da suka zo ma ba wanda taga zai basu abincin, bata jin dadi dole ta kwanta da wuri kuma bata ci abincin ba, Dr kuwa dakin Nafisa ya shiga yana neman izinin ta barshi ya kwana inda Nabila dan batada lafiya "kam bala'i! Wallahi ban yadda ba ina ruwana da ciwonta, tama mutu ko cikin ya zube wallahi ko a jikina, Allah yasa ma cikin ya zube dan naga saboda shi take wani iyayi da iya shege" ransa yayi matukar baci ya kasa cewa komai dakinshi kawai ya shiga yayi shirin bacci koda yaje tana zaune ta rasa abinda yake mata dadi ko kwanciyar ma ta kasa yi ga cikin ya fito radam kamar yafi wata hudu, lallashinta yayi ya kwantar da ita yana dannna mata jikinta har yaga alamar bacci ya dauketa sanann ya koma dakinshi.

Washe gari cike da karfin hali ta tashi suka gyara part din girki kam tace Nauwara ta dafa abinda take so shi banan zaici ba "Anty ke me zaki ci to" nauwara ta tambayeta "babu shi, duk abinda za a dafa a part din nan ban iya cinshi" munauwara tace "bari inje gidan Alhaji Husaini in samo miki" dayake tana so bata hanata ba, tana fita ta hadu da kaninta Jamil tace "kai baku koma ba ko" ya harareta yace "kizo ki maida mu yar iyayi" kwafa tayi ta wuce shi tana zuwa gidan suka dinga tsokanarta matan gidan dayake kakanninta ne kanin Babansu Dr, matar dansa ta samu ta dafa musu taliya da manja da yaji ta zauna ita da danta guda daya zasu ci ta ce "anty Raliya don Allah ki samma Anty Nabila taci ta kasa cin komai tun jiya" rufe plate dinta tayi tace "ai ko akwai saura bari in zuba mata, kinsan ance jiya kunzo inata so inshiga mu gaisa" a tare suka shiga gidan tana zaune Nabila ta cinye abincin suna Hira nan munaura ta fada mata abinda taji Nafisa na fadawa Dr, tayi shuru sai daga baya tace "Munauwara ki daina fadamin abinda kika jiyo irin wannan daga waje kinji, bani ba ma ko a wurin kowa babu kyau kibari randa ta fada a gabana zan bata amsa" munauwara ta ce "to kiyi hakuri bazan sake ba anty" Raliya ma Nan ta sake daukar darasi dan taso fadawa Nabila irin zagin da Nafisa ke mata idan taje gidansu amma sai tayi gum da bakinta jin wannan ma ba gulma ba an gwasale wata balle ita koda gyara tayi ba gwasalewa bane.

Nabila kuwa batun ya tsaya mata arai har idan suka hadu da Nafisa take kasa dannewa saita bata rai ta kuma daina kulata shikuma Dr bai lura ba har suka koma sokoto, tun daga ranar shikadai yake zuwa hankali a kwance yake barosu skt ya kwana daya ko biyu ya koma, har saida akayi exam sannan ya sake zuwa dasu, wannan karon cikin Nabila har baya boyuwa yayi girma sosai dan ya shiga wata bakwai, ta sake yin kiba, lokacin kuma Baban Munauwara yazo daukarta dan tuni kannenta sun koma, da kuka ta bishi saida Dr yayi mata Jan ido itama Nabila saida tayi hawaye dan Ta saba da ita sosai, bayan ta wuce ita kadai ta kwana ranar, a daren Nafisa take ce masa "wai nikam ko wani abin akacewa matarka nayi ta daina kulani" cike da mamaki yace "kamar yaya"? "To nidai tun wancen zuwan naku bata sake yimin magana ba har kiranta nayi a waya bayan kun koma a kayimin rejecting kq tambayeta don Allah dan ni yanzu banson tashin hankali gara mu zauna lafiya kaima hankalinka seyafi kwanciya, amma don Allah kar kai mata fada" shuru yayi yana jin ransa ya baci akan abinda tayi amma dare yayi da sai yaje ya asketa dan bata kyauta ba...


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanch_

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU

Koda ta tashi yau sai a hankali saboda wani nauyi takejin cikin yayi mata abubuwa dai wayanda bata san zata iya hakuri dasu ba saboda yanayin masu ciki da wayanda bata saba dasu ba har wani kumburi take ganin kafafuwanta sunyi, gashi Sam ta kasa komawa bacci dan inta kwanta ma ba dadin takeji ba sai a ringine gashi Mama ta fada mata ba a son mai tsohon ciki na irin kwanciyar, ta lallaba ta shiga toilet ta watsa ruwa ta shirya tana ta tunanin Munauwara gashi ko waya bata da balle suyi magana taji ya suka isa, dakin ya shigo da sallama a bakinsa amma fuskarshi babu walwala, ita ta saba ganin wannan fuskar amma ba a gida ba saidai a makaranta duk da haka bata damu ba ta share yanayin ta gaidashi "lafiya lau me kike yi a zaune baki koma bacci ba" murmushin karfin hali tayi tace "bakomai yanzu na gama shiri dai nayi wanka" ya gyada kanshi tareda zama kusa da ita yace "meyasa bakiwa Nafisa Magana"? Ta danyi shuru tana nazarin maganar amma bata ce komai ba "bakiji ni bane"? Ya dora da "Sabon hali kika tsiro dashi wanda zai tayar min da hankali a cikin gida? Koba komai Nafisa ta girmeki ko bata girmeki a shekaru ba itace babba acikin gidan nan meyasa ba zaki bata girmanta a zauna lafiya ba" saboda yadda maganganunsa sukai mata zafi yasa ta ce "kayi hakuri, banyi tunanin wurinta aka kawo ni dan in girmamata ba" ya fahimci magana ta gaya masa a hasale yace "karki raina min wayo dan kinga ina kyaleki, Nafisa Matata tace bazan yadda ki wulakanta ta ba dan ni bakiga na wulakanta taba, duk abinda take ji har ta fahimci baki mata magana ta kiraki a waya ki ringa rejecting call dinta sannan in miki magana yanzu ki maidamin bakar magana, bana son Gaba na kashe wannan maganar" dakyar ta hadiye abinda takeji a makogoronta ta danne shi kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "bamu taba yin haka dakai ba, ban taba kai maka karar matarka ba, koda zakayi fada ya kamata kayi bincike, Sau nawa muke zuwa garin nan taki kulani inshiga har dakinta in gaida ita taki amsawa idan zamu shekara agidan nan bazata taba kulani ba ko ciwon da nayi last zuwanmu bata taba cemin yajiki ba se yanzu dan na kyaleta itace mai bakin kai kara? Sannan yaushe ta taba yin numberta da zata kirani inki dagawa, ka dauki wayata ka gani bana goge call logs idan akwai number dinta aciki Kuma ni inada dalilin kyaleta badan na hada miji da ita ba, kyaleta nayi saboda sakonta ya iskoni kiyayyar da take min takaiga tayimin adduar Allah yasa na rasa cikin dake jikina ko kuma ni na mutu, me zanyi da kula matar dakemin wannan mummunar kiyayyar" tunda ta fara magana yake kallonta sai da ya ji tayi shuru sannan yace "bafa danki nake ba balle ki ajiyeni kina yimin surutu, sannan wanene yazo ya fada miki wannan maganar? Ko labe kike mana"? Duk kokarin tare hawayen da take su zuba ta kasa bata sake ce miki komai ba "na fada miki koma menene bana son sake jin maganar gaba a tsakaninku ki tashe kije ku shirya" dafa gadon tayi ta mike tsaye tace "Allah yana gani wanda yake karya tsakanin nida ita Allah ya isa, babu inda zani wallahi bakuma sai ka nuna min kiri-kiri ita kake goyon bayanta ba" tsawa yayi mata amma saboda idonta ya rufe itama ta daga murya tace "ka manta bana tsoronka yanzu, ya wuce ka dakeni ko ka sake ni, kayi daya ka gani idan rayuwa ta zata daina amfani, kuma ko baka sakeni ba saina bar maka gidanka ka fara kin gaskiya tun yanzu nan gaba sujada ne kawai bazaka sakani nayi mata ba" tana gama fadin Haka ta ja Hijab dinta dane kan gado ta dauki wayarta, tana tafiya a hankali ta nufi jikin madubi tana neman purse dinta, fita yayi daga dakin bayan mintuna biyu zuwa uku wayarta tayi ringing ganin numbern Yaya yasa ta daidaita nutsuwarta ta dauka tayi zaton normal kirane kamar yadda ya saba yaji ya take, gaidashi tayi ya amsa yana cewa "idan a tsaye kike zauna zamuyi magana" wuri ta samu ta zauna tana cewa "to yaya na zauna" "Nabila kiyi hakuri kinji mu maza haka muke don Allah babu wacce ta taba yin yaji a gidanmu kiyi zamanki dakinki nasan kinada hakuri amma aure ko shekara baiyi ba zaki fara yaji" kuka ta fashe dashi dakyar tace "Yaya baya bincike basusan me nakeji ba, babu mai kishiya acikinsu karya da kazafi Yaya kuma yaki fahimta ta, wallahi zuciyata zafi take yimin" yaya yadan sassauta muryarshi cike da lallashi yace "haba Nabila nasan fa bakida gardama kiyi hakuri kinji kinsan yanayinki ba a son mai ciki da damuwa ki kwanta ki huta kinji Allah ya miki albarka" godiya tayi masa sannan ya kashe wayar, ajiye wayar tayi taje ta rufe kofar dakin tare da barin key ajiki ta kwanta kuka tayi har saida taji kanta ya fara ciwo sannan ta hakura, batayi bacci ba dan dama sama-sama take jin kanta.

Dr kuwa lokacin daya fita hankalinsa ya tashi jin zata bar gidan shiyasa ya kira yaya tareda rokon shi don Allah ya bata hakuri karta tafi, yanayin wanka yabar gidan ransa duk abace.

Sai wuraren a zahar ta fito dan yunwa dayake mai tsohon ciki bata fushi da abinci, dakyar ta sake wanka saboda fuskarta da ta nuna damuwa da kuka ta shafa kwalli da hoda harda jan baki ta saka doguwar riga da hijab ta sa takalminta ta fita, gaida mama tayi ta dan zauna Mama tace "Nabila lafiya kike ko" murmushi ta yi tace "angode Allah dai mama dakyar na taso yanzu ma na rasa me yake min dadi" Mama ta tausaya mata tace "sai hakuri ai Nabila insha Allahu kun kusa rabuwa lafiya ciki idan yakai yanzu ai dole sai da hakuri" mikewa tsaye tayi tace "mama inaso inshiga gidan Baba indan mike kafa"  mama tace "yanada kyau ai sai kin dawo nima fita zanyi yanzu can gida zani" Nabila ta amsa mata "ina gaidasu Mama idan naji sauki zanje ai ingaidasu" daganan ta fita bayan ta gaisa da mutanen gidan suna jajanta mata tafiyar da akayi da Munauwara anbarta ita kadai ta nufi kofar Raliya tana shiga kuwa ta is kota ta sauke tukunya kenan, jollof din shinkafa tayi da wake da alayyahu, ta sa mata nan ta zauna tanaci suna hira har ta gama anan tayi laasar taci gaba da zamanta.

Karfe shida ya shiga gidan direct part dinta ya wuce yana tura kofar yajita a rufe ya dawo part din Nafisa tana shara ya shigo dan yau sai iyayi take da neman gindin zama tunda ta hada fada shiyasa part dinta har kamshi yake bata san shi ya saba da wannan ba nata ba wani d'ad'a shi da kasa zaiyi ba, ya ce "Nafisa ina Nabila"? Ta dago ta kalle shi tace "matar da bata min magana ina zata fadamin inda tayi" tsaki yayi hankalinshi a tashe ya fara lalaben numbernta ya kira ta.




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

*Bazan boye muku ba gaskiya naji dadi kuma ina ci gaba da jin dadi musamman mutanen da basu gajiya da yimin addua mai kyau tare da fatan alkhairi Nagode sosai nima kuma ina yi muku Fatan alkhairi tareda adduar Allah ya hada fuskokin mu a aljanna madaukakiya*

Tana ganin kiranshi ta mike tayiwa Raliya sallama, a tsaye ta ganshi kofar gidan ta daure fuska kamar bata taba dariya ba, kura mata ido yayi har ta karaso kusa dashi, can kasa yajiyo muryarta tana cewa "Sannu da zuwa" ya kasa amsawa daga baya yace "Ina kika je"? Ta nuna masa da hannu tana cewa "Gidan can" ya gyada kai "Amma ban fada miki bana son yawo ba"? Cikin idonsa ta kalle shi ta sauke nata kasa saboda ganin irin kallon dayake mata ta ce "ba yawo na je ba, An bata mini rai dole inshiga mutane dan bazan zauna kunci ya murkusheni nikadai a daki ba" tana gama fadar haka ta wuce ta barshi, bayanta ya biyo har suka shiga daki ya riko hannunta ya zaunar da ita "Nabila zauna muyi magana" cire hannunsa tayi daga nata tace "ni bana son wata magana" ya danyi shuru daga baya yace "mijinki fa nake, kina ganin ya kamata inringa yi miki magana kina yarfa ni" shuru tayi gabanta na dan faduwa dan tasan batada gaskiya ta soma kauce hanya, "kiyi hakuri na fahimci ban kyauta ba rashin bincike ko ince rashin saurarenki da banyi ba, amma ba shi zai baki damar yimin magana any how ba Nabila ban iya tolerating ko dan ina mijinki ina neman abu a jikin ki kina ganina tsirara zaki rainani? Wannan ma shi ya kamata yasa kiga girmana kisan irin maganar da zaki ringa fadamin" shuru tayi taki magana dan har lokacin haushin shi take ji daga karshema data tuno akan Nafisa ne ya saka ta samu matsala dashi sai ta fara kuka, tashi tayi ta shiga toilet ta barshi anan yana jiyo sheshekar kukanta ganin bazata fito ba yasa shi mikewa ya fita jin an fara kiran sallah yana mamaki da jin haushi ashe dama haka take.

Tunda ya fita bai dawo dakinta ba, bata damu ba dan gaskiya bata son abinda zai sake hada su, tun daga ranar ya daina matsa mata da zancen sai dai ya leko su gaisa ya fita, takan debi kayan abinci takai irinsh magi da kayan miya dan tana ganin idan ta aika shinkafa zasu iya jin haushi tu da mijin Raliya yace a ringa saka abinci da ita, idan zaman ya isheta takan shiga part din mama suyi hira, acan kuma take isko Nafisa amma bayan tayi sallama bata ko kallon gefen da take.

Ganin dadewa zasu yi sati biyu gashi yayi kwana biyar a dakin Nafisa sai ya shiga dakin Nabila ya sameta a zaune cikin duhu babu wuta, zama yayi ta gaida shi ya amsa yana cewa "Zaki karbi girki yau tunda ba yanzu zamu wuce ba sai a raba kwana daddaya" kamar zata ce bata so sai kawai ta gyada masa kai, ya kalleta yana haskata da fitila yace "Me kikaci" nan ma kai ta girgizai masa alamar bataci komai ba, fuskantar ta yayi yace "Nabila bakison in zauna dakin ki ne in fita"? Saurin kallonshi tayi taga fuskarshi ya gyada mata kai ita kuma sai ta girgiza tana sauke kanta kasa "Nabila kwana hudu fa kenan, Baki gaji da fushin ba? Inata magana amma saidai ki amsa mini da kai bazaki bude baki kiyi magana ba" muryarta tana rawa dan har yanzu bata daina jin zafin abin ba tace "kayi hakuri" Rungumeta yayi sai ta fashe da kuka, Abin mamaki ma ya bashi yayi shuru yana saurarenta daga baya yace "don girman Allah karki sake furta min kalmar saki ko dukan matata acikin gidan nan, duk abinda zai faru tsakaninmu karki sake cewa zaki tafi gida, Allah yasani ina sonki na saba dake rashinki zai cutar dani" tana kukan tace "ka daina daga mini murya akan matarka, Babu ruwana da ita bazan iya shiri da ita, cewa fa tayi Allah yasa cikina ya zube, kasan ni bazan taba tsokanarta ba saboda ina kishi da ita bana rigima da kowa ban iya fada ba" dagota yayi yana kallonta "nikuma bana son kuna zama a haka babu shiri ko dan saboda yarana, ba dabia bace mai kyau karsuma su tashi suna gaba da juna kuyi hakuri don Allah kuringa mutunci bance sai anyi shiri ba amma a kwatanta karki biye mata kinji" haka ya ringa yi mata dadin baki irin nasu na maza aka dawo da wuta, kallonta yayi sosai yace "Naga kina kumburi anya bazaki ga likita ba" ta kalli kafafuwanta tareda cewa "kuma karuwa yakeyi" riko kafar yayi yana dan dannawa sannan ya lalibo numbern Likitan dake aiki asibitin tambuwal, ya fada masa yana da emergency ko yana asibiti likitan yace eh to amma suyi sauri san so yake ya wuce gida "saka hijab dinki muje" ta girgiza kai tana cewa "ba sai munje ba bacci nake ji" tada ita tssye yayi yace "kika barni na kirashi kuma? Kiyi hakuri muje" hijab dinta ta saka suka fita bayan sunja kofar, suna zuwa BP dinta ya fara aunawa yaga ya hau shawara ya bata akan ta kwantar da hankalin ta jinin ya sauka dan ya hau sosai ba a son kuma jinin yana hawa ta ringa samun isashen bacci, godiya yayi masa har suka rage masa hanya dan motarshi tana wajen gyara, koda suka shigo gidan har sha daya ta dan gota, kwantawa sukayi Dr yana sake lallabata dan ya gano yayi barna tunda har jininta ya hau.

Washe gari garau ta tashi sai dai bata kaunar dafa abinci, dole bread ya siyo suka sha tea da rana Raliya ta aiko da abinci, tun daga ranar iyakarta gaisuwa da Nafisa har suka gama hutunsu suka dawo, Munauwara taso dawowa amma acan babanta ya sama mata admission zata fara zuwa makaranta sai dai ya mata alkawarin kawo ta idan Nabila ta haihu.

Bayan wata daya da sati biyu ya shirya zuwa tambuwal a ranar ya dawo daurin auren wani kanin abokinsa yana kokarin fita yace "kinga na makara gashi ke baki shirya ba, ki kira Maryam tazo ko idan zaki iya kije gidanta karki zauna ke kadai" ta amsa masa "zanje gidan Anty Maryam din idan na samu nayi wanka" bata ma raka shi ba ya fita yanata sauri kar ya rasa daurin auren, kwantawa tayi bacci ya dauketa sai karfe goma da rabi ta tashi tana kokarin shiga toilet tayi wanka taga wasu ruwa suna mata zuba tayi mamaki dan batasan na menene ba sai ta shiga wanka harta fito basu tsaya ba ta shafa mai bayan tasa pad ta dauki waya ta kira mama bata daga ba, sai ta kira Nana sule itama bata dauka ba, ajiye wayar tayi ta dauki hijab sai taji kamar tana jin fitsari, tana shiga toilet din taga ruwan harda kalar jini nan hankalinta ya kara tashi ta fito da sauri batareda tayi fitsarin ba ta sake kiran Mama amma har lokacin bata dauka ba, daga nan ta fara jin wani ciwon azaba daya sa dole ta ajiye wayar tana fadin "Innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un" kamar wasa sai gata a durkushe tana jin kamar ranta zai fita, cikin karfin hali ta sake gwada kiran mama Da Nana amma duk ba wanda ya dauka, Dr ta kira shikuma not reachable, ajiye wayar tayi ta fashe da kuka irin wanda bai da hawaye, tunda take a rayuwa bata taba jin ciwo makamancin wannan ba.

Mama lokacin tana can sunyi baki a asibiti ward dinsu dan haka wayar ma a office ta barta suna zagawa tare dasu, Nana kuwa tana can suna hidima matar kanin mijinta ta haihu bata sokoto ma shiyasa dukansu bata same su ba.

Sai bayan kusan awa daya Mama ta dauki wayarta tayi mamakin ganin kiran Nabila yakai goma, da sauri ta kira amma batayi packing ba dan lokacin zata iya cewa ma bata hayyacinta...





*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_ 

SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU 




A lokacin Dr ya fito daga kauyen da sukaje daura aure ashe ba cikin garin tambuwal bane yarinyar babanta dan wani kauyen cikin tambuwal ne da ake kira Shinhiri kuma basuda network din MTN shiyasa tayita kiransa bata samu ba shikuma bai je da mota ba dan hanyar babu kyau ya shiga motar ango suka tafi shiyasa saida ya jira ango ya gama gaisawa

Please Login or Register in order to submit comment