Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shiga ya kaisu Airport din suna isa lokacin jirgin yana sauka...




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI

Kallonshi tayi ya daure fuska tamau yana danna waya, hannu tasa ta dungure wayar ya dago da murmushi yana cewa "sweety lafiya" kusa da kunnensa ta kai bakinta tare da cewa "thankyou" a hankali yar dariya yayi ya ce "kardai bakauya ce ke baki taba shiga jirgi ba"? Ta turo baki tana komawa kujerarta ta gyara zamanta tace "waya fada ma? Babu adadi ina raka mama yawo ai munje Lagos tare munje ibadan, munje Abuja kai har Dubai naje" hararar wasa ya mata yace "zo dai yau inhaskoki a jirgi yarinya" ya fada yana saita musu camera, dariya yayi sosai ganin yadda ta yamutsa fuska "Haba sweetheart murmushi fa zakiyi" ta turo baki tana cewa bazatayi ba, haka suke ta wasansu da dariya har jirgin ya daga.

Bayan sun sauka driver yazo ya dauke su lokacin duk su Muhammad sunyi bacci, babban palon gidan suka zauna Nabila tanajin kanta a takure, anan suka ci abinci suna dan hira da matar gidan da yaranta, Yaya Ali ganin Nabila ta kasa sakewa tunda ya shigo ya kalli Dr yace "Abubakar ka raka maman Muhammad daki ta huta kun isheta da surutu" Dr ya kalli Ramla dake murmushin yake yace "ai da magana zakiyi idan kin gaji Goggo, dauko Muhammad muje Ramla ko ki barta nan" ta saci kallon yaya sannan ta kalli Dr ta ce "ba tare zamu kwana ba ko" ya sake baki yana kallonta Matar yayan ta kallesu tace "ya akayi Nabila" ta girgiza kai tace "A'a ba komai" Dr ya kallesu yace "wai bazata shiga dakina ba"  yaya yace "ahh tashi kuje ku huta tafiya akwai gajiya kinji, karki damu nan ma duk gidane, kayanku ma suna can" a kunyace ta mike tabi bayanshi, suna shiga ta taka masa kafa tace "bakaga ina maka signal ka fara wucewa ba" cikin mamaki yace "to maganin me idan na fara wucewa" ta cije lip dinta na kasa tana zaro masa ido tace "ba kunya ka sakoni gaba" dariya yayi yace "yarinya wallahi soyayya muka zo yi nan kinsan Allah, yanzu zamuyi amarci kima shirya" ta zauna kan kujera tana lumshe idonta saboda palon ya dau sanyi, shikam daki ya wuce yadan watsa ruwa yasa kayan bacci ya sauyawa Muhammad, itakam baccinta take hankali kwance, acikin baccin taji ya daga ta, ta bude idonta tana zagaye hannunta wuyanshi yace "yarinya fa bacci bai ganki ba" murmushi tayi tace "idan karfe hudu tayi ka tashe ni sai in baka abinda kake so" ya sauketa gefen gado yana kunce mata igiyar rigar yace "to inkina son kiyi bacci me dadi kiyi wanka" towel dinda ya ajiye kan gadon ta dauka ta shiga toilet din, saida ta karewa toilet din kallo sannan ta fara wanka, yayi kyau sosai kamar ba toilet ba.

Washe gari tun karfe bakwai ta tashi zata fita yana kwance yace "wai ina zaki"? Ta dauki hijab ta saka tace "fita zanyi mana na kama aikin gidan" ya rike hannunta yace "ke nan fa ba sakkwato bane gida barrister kike, ba mamaki tundazu an gama aikin gidan kedai ki hutawarki" komawa tayi ta kwanta tareda fadin "shiyasa mama bata son rayuwar Abuja nan ta bariki" yayi dariya yace "to kinsan kana zama cikinsu dole kayi adopting wasu daga cikin dabi'unsu nan gidan ma naga shi mai gidan yana tsawatarwa kuma matarshi tana kulawa" ta gyada kai tana cewa "to bari nikam inyi bacci kafin Muhammad ya tashi" kashe wutar yayi yace "ko mu koma ruwa" dariya tayi tace "Gulbi zamu koma ba ruwa ba" shima dariyar yayi dan yaga yanzu gaba daya gudunshi take bai san dalili ba.

Sai karfe goma suka tashi, itace ta fara tashi tayi wanka ta shirya sannan ta fita lokacin yana wurin wanka, a palon ta samu matar zaune da yan yaranta da Ramla suna cin abinci cike da Mamaki take kallon Ramla ta daddage tana cin Irish da kwai harda wani munafukin cup gabanta da tea aciki, yarinyar da ko farar shinkafa bata ci ko kunu bata sha itace zaune da kanta tana dura Irish anty tace "sannu Maman Muhammad sai yanzu kuka taso" tayi dariya tace "wallahi ko, yau yar gidanki nake gani da abinci tana ci, har ina cewa kila tana nan tana kukan banza na manta ban fito na bata friso ba" Anty tace "gashinan dai tana ci kuma batayi kuka ba sai karfe tara ma nace Hamdiyya ta tasheta tai mata wanka" shuru palon ya dauka sai motsin yaran Anty sake cewa "gafa abincinku can kan dinning" Nabila ta kalli dinning din tareda isa wurin ta bude warmers din ta kalli Irish din ciki wai nasu ne su biyu, ita wannan ai ko ita ta cinye bazai isheta ba tace "Anty, ina kitchen" Ta nuna mata tana cewa "wani abu kike so ne" Nabila tace "Ni wallahi koni saina cinye wannan Irish din, bari na dafa indomie shi sai yaci wannan" Anty tayi dariya tace "ke wallahi na mance goyo gareki, bari Hamdiyya ta dafa miki zo ki fara shan tea" kallon mug din dake jere wurin tayi ta samo babba ta hada tea ta dawo palonta zauna, bada dadewa ba Dr ya fito dauke da Muhammad yana kuka sosai, ta karbe shi da sauri tana cewa "Anya ba muntsininsa kayi ba" Anty tayi dariya tace "ba dole ba kun sashi raino, wai nikam Abubakar ina Nafisa ne baku zo tare ba" ya zauna yana facing dinta yace "wannan matar inaga aljanu gareta aini ko sokoto ban iya zuwa da ita" Anty tace "last zuwanmu fa bata yimin magana bansan me na mata ba sai Farida ke fada min tace ina bin bayan Nabila shiyasa itako duk me son Nabila bata kula shi" Dariya Nabila tayi tace "wallahi Anty kinga hannuna har ya kumbura jiya janyoni tayi ta wurgani na fada kan hannun" Dr ya kalleta tareda riko hannun yaga da gaske ya fara kumburi yace "meyasa baki fadamin hannun yaji ciwo ba" tace "nifa yau kawai naji yana yimin zafi amma ba sosai ba" Anty ta girgiza kai tace "Allah dai ya baku hakurin zama da ita amma tanada matsala" Dr ya mike tsaye ya nufi dinning ya fara cin abincin shi sai time din aka kawo mata indomie sunata hirarsu sai kusan la'asar sannan yace ta shirya su fita.




Bangaren Nafisa kuwa kuka ta ringa yi bayan sun wuce kamar wacce aka yanka abu ukku da goma sha ukku sun hade mata, Na farko ga kishi antafi da Nabila an barta, nabiyu ta bata ran mijinta har yayi abinda bai taba yi ba gashi duk kurin da take yana sonta yau ya kora ta gida me zata cewa yan gidansu yasa ya koro ta, akwatin data shirya aje Abuja sai gashi taje dashi gidan ubanta, karya ba kalar wacce bata yiwa Dr ba lokacin da aka zauna da ita dan jin abinda ya dawo da ita gida, ta ce yana dukanta sannan yafi son matarshi har mota ya canza mata wayoyin Nabila ukku sannan ko kayan daki taji kyashin-kyashin zai canzama Nabila duk inda zashi tare suke zuwa, sannan idan yana sokoto sai ya share wata har biyu bai zo Tambuwal ba idan ma zai zo seya kwaso Nabila yazo da ita sai ya lura tayi bacci ya Salale ya tafi dakin Nabila ita batada amfani, karshe tace ta manta rabonta dashi ko cikin Diyarta Allah yayi da rabon a same shi, iyayenta dukansu shuru sukayi kowa ya cika da takaicin Dr suna ganin dan ya auro yar masu kudi zai wulakanta musu yarinya, mamanta karshe tace "Bazata taba bari Nafisa ta koma ba" nan take cikin ta ya duri ruwa dan ita kam bata ga mai rabata da mijinta ba tana son abinta.

Dr da Nabila soyayya suke kamar lokacin ne farkon aurensu, ya kaita wurin yawo yayi mata siyayya kala-kala daga can kuma ya sauya mata waya iPhone inata leko inga wace iri ce amma ban samu gani ba.

Last shagon da suka je siyayya yara kawai ta daukarwa kaya indai na mata ne zata duba size ta dauki babba da karami baice komai ba dan wasu da kudinta ma ta siya, satins biyu a Abuja suka shirya dawowa.

Lokacin Nafisa ta ishi kowa gidansu ita bata wanka bata yiwa yar ta sai taga dama, zani sai ta jera kwana uku dashi, bata aikin komai sai chtn da kallon film din su Adam Zango da Ali nuhu kaf industry din kanywood ba wanda bata sani ba haka ma India Hausa duk jaruman nan tasansu tana zaune bakin kofar dakin Mamanta tana tsaststage hakori farce yai mata zaro zaro ga diyarta Nana kusa da ita ko pant ba tada Baban su ya shigo yace "Ance mijinki zai dawo gobe dan naje can gidanku idan ya shigo nace yazo ina son ganinshi dan gara kisan matsayinki" ta hadiye wasu yawu masu kauri tana tunanin yadda lamarin zai kasance dan tasan ta tafka barna. 




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS

Tsaki ta danyi ganin ta kusa awa daya a zaune tana jiranshi yana upstairs palon Barrister Ali yaya kenan wai magana suke yi, tashi tayi ta dauki Muhammad suka koma daki ta shimfide shi itama ta kwanta, tasan ba maganar zuwa wani wurin kuma idan ya gama ya tasheta kawai su wuce airport, ta dade kwance bacci yaki daukarta duk tunanin ta maganar Nafisa suke yi da zancen maida ita dan taji jiya da dare yana magana da Baba kuma lallashinsa yake karya saketa, sai time din ma tasan Nafisa bata gidan.

Ta rasa wane kalar yanayi take ciki kawai bata jin dadin yanayin, wayarta ta dauka ta kira Nana sule tana dagawa tace "lallai duniya tai miki dadi keda Dr dazu IG naga wani Vd Northern blog sunyi posting dinku" Nabila ta tashi zaune tace "raba kanki bamu bane danni ko hoton mu bansa ko dp din WhatsApp ba balle IG" Nana tace "tab...to billahillazi ku nagani a airport vd dinku har kuka hau jirgi" Nabila ta dafe kirji tace "ina zuwa ban minti biyar naje na gani danni tunda nazo ban leka IG ba" Nana sule ta kashe wayar tana mamakin to waye idan basu ba.

Nabila kuwa account din ta shiga tana searching har lokacin vd din yana nan kamar ma kusan guda uku ne aka hada waje daya, tunda Dr ya zaga ya bude mata mota ya dauki Ramla ta fito da Muhammad, har lokacin da suke tsaye kafin su shiga ciki tayi mamaki sosai, comments ta shiga taga mostly yabawa akayi sai wayanda suke fadar magana son ransu dan baza a rasa su ba, wani ma cewa yake "Allah ya bamu kudi muyi auren nan muma, matan nan masu kyau yaran masu kudin nan sai kwashewa suke mu an barmu da masu hakora kamar kaca" wani yace "Ina ma zai sakar min yarinyar nan in aura" tsaki tayi ta fita tana jin haushin wanda ya daukesu wannan vd din suna zamansu yaja musu surutu, sake kiran Nana tayi ta dauka tana cewa "me kika gano" Nabila tace "hmmm... ke wallahi mune kuma na rantse bansan waya dauke mu ba" Nana sule tace "Nima nayi mamaki, koda yake ba abin Mamaki bane yanzu mutane da shiga abinda ba ruwansu" haka dai suka ci gaba da hira sai ga Dr ya shigo tayiwa Nana sallama ganin yana shigowa wurinta yayo ya rungumeta tareda sauke mata kiss a kumatu tayi dariya tace "Nana fa tana jinka Dr" ya zauna yana cewa "tashi ki maida kayanki mu wuce amma dan samin ledar nan cikin jakar can" ta karba tare da bude jakar ta saka yace "kudine idan mun isa can ma ki adana min su" ta gyada kai tareda "fadin Allah ya bani ikon kiyayewa, Amma Ramla fa naji Barrister na cewa abarta nan" Dr yace "munyi magana yanzu nace ya bari sai zata shiga makaranta yanzu wahala kawai zata basu" Nabila tace "Nima abinda na gani kenan, nama yi mamaki yadda bata damuwa dani tunda muka zo" taimaka mata yayi ta maida rigarta yace "kani take so ayi mata" wata dariya tayi tace "ciki yanzu? Ai kama daina wannan maganar kaji Mubar maganar zuciyata tashi take" hularta ta karasa sawa ta dauki kayan da zata iya dauka a hannu suka fito, driver din gidan ya kaisu airport bayan sunyi sallama da mutanen gidan la'asar a sokoto tayi musu direct gida suka wuce. Kudi ya bata ta siya abubuwan da zasu iya bukata yayi mata sallama zai je tambuwal, tayi mamaki sosai dan bai fada mata zai tafi ba daga isowarsu amma ta danne zuciyarta dan yanzu duk abinda zatayi zai yi kamar bata son Nafisa ta dawo ne" bata yi kokarin siyan komai ba dan bazata iya fita ba kuma wa zata aika ma yanzu, dan haka sai tayi zamanta bazata rasa indomie da zata dafa ba.




Mashin ya hau ya tafi gidan Hajiya luba ya dauki motar shi dama ta Nabila can gidansu yasa aka kaita bayan an daukota daga tambuwal, gidan mai ya shiga yayi full tank sannan ya kama hanya.

Yana zaune yana sauraren su mama kamar ruwa ya cishi nan kuwa zuciyarshi wani kuna take mama tace "Ka rufa min asiri ni yanzu bakin tambuwal bisa kaina yake ance nayi maka auren dole, na lalata matarka nasa bata ganin girmanka sai abinda nace, ka kara aure Na koma wajen amarya na barka kana gallazawa uwar gida, Abubakar ka rufa min asiri karka sake ta kaje ka dawo da ita" Baba ya karbi zancen da cewa "Ni abinda ya hadaku ma banga yakai ga saki ba kayi hakuri dan bazan taba bari ka saketa ba kaje kaji me zasu ce maka" ya gyada kai da kudurin idan yaje zaice ta dawo idan ya kwana biyu sai ya koma.

Suna zaune a palon Babanta kowa yayi shuru, Babanta yace "Nafisa maimaita abinda kika fada yana miki dan ayiwa tufkar hanci" ta hadiye miyau ta kasa cewa komai, ya dago ya kalleta yanada tabbacin ta kwana biyu bata watsa ruwa ba yana jiran yaji me zata ce, ta sauke kai kasa babanta ya sake maimaitawa sai ta daga ido ta kallshe tareda matso hawayen karya tace "Baba ai ba sai an maimaita ba, indai ya gaji dani ya sallameni" Mama a hasale tace "wane irin inya gaji dake, in kuma bai gaji da zaluntarki ba sai ya maidake ya karasa ki ko? Kana zaune da miji yayi wata biyu baizo inda kake ba sannan ya fifita wata akanki yana mata abubuwa harda sayen mata mota da wayoyi da kayan daki keko naki na nan watse Marfin wardrobe baifi shekara kasa ba"  ya daga kansa ya kalli Nafisa dakyau wato karya tazo tana yi masa kenan amma sai yayi shuru Babanta ya fadi duk abinda ta fada musu daga karshe yace "wanda ya mutu dai akewa karya gatanan ita ta fada muna da bakinta kuma gabanta yanzu na maimaita in ko hakane Abubakar wannan zama akwai zalunci da take hakki ciki" Nafisa ta fara yan kame kame tana son yin magana Dr yace "Baba tunda nayi aure indai kaga nayi sati biyu ban zo garin nan ba to tabbas aiki yamin yawa office, sannan kayan dakin Nabila dabi'ar gidansu ce babanta yakan sauya musu idan yaga kayan su dauki lokaci bayan haka mota tunda na fara ganinta da motarta na ganta babanta kuma shi ya canza mata wallahi ko mai bana sawa motar Nabila se idan na dauki motar na fita da ita sai in saka mata mai tunda a karkashi na take dole na kula da ita, waya kuwa tunda tazo gidana bantaba siya mata ba har wayarta lalacewa tayi ta ajiyeta ban gyara mata ba ban siya mata wata ba bata taba yimin magana ba amma ke ko shekarar nan waya biyu kika banzatar aka dauke babu ta kasa da dubu saba'in kuma ni nake siya, shine zaki zo ki shirya min karya bayan rashin kunyar da kika min kuma kika turemin mata ta fadi da jariri a hannunta" iyayenta sukayi shuru kowa jikinsa ya mutu Dr ya kalle su yace "Baba raina ya sake baci bazan iya maida Nafisa ba yanzu abarta ta kara hankali, duka dabiarta sunsha bambam da nawa, Baba nafisa bata wanka bata wanki bata shara, har takai abokanaina in sunganni zasu gane nazo garin nan saboda ramewa nake babu abincin kwarai dan bata bani bata ma dafawa nikuma Allah yasa bana iya cin abinci awaje, wace irin macece wannan da muguwar kazanta a haka ma zata ga laifi na dan na dade banzo ba, don Allah kuyi hakuri ku barta ta sake hankali"  Babanta ya kalleshi yace "kayi hakuri amma karkace bazata koma ba, ni nasan maganinta, kabarta ta koma zansa ido akanta tareda tsanani in bata gyara ba ka sake koro ta to babu hannuna aciki Kuma karma a neme ni" Dr ya gyada

saboda yana jin nauyinsu ya mike tare da yi musu sallama bayan yace ta shirya ta koma duk sanda take so.

Gidan yakoma ya musu sallama tareda wucewa Sokoto, gara yaje inda yafi wayo koba komai zai shaki kamshin turaren jikinta dana gidanta, zata bashi yaci ya koshi kuma ya kwanta bacci bisa gado irin na alfarma, zai tashi da safe ya kalli fuskar da take shiga damuwa in yana cikin damuwa, fuskar da take saka nishadi a ranshi, zaiga matar da tafi kowace mace iya wanka da jiki mai daukar hankali, kasa hakuri yayi ya dauki waya ya kirata, tana zaune taga kiranshi ta dauka ta gaida shi sai yace "Baby ina hanya zan dawo karkiyi girki zan kawo miki kaza da madara"  tayi dariya tace "inace can zaka kwana" shima dariyar yayi yace "ai baki bari, nafison zama kusa dake, kiyimin kwalliya zanzo ingani in kalleki inkara sonki kuma inyita sonki".



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA TARA

second to the last page 

Murmushi ya kasa barin fuskarta har bayan ya kashe wayar, dakinta ta shiga ta kira Anty Maryam tana daga tace "Hajiya Nabila mutanen Abuja" dariya tayi a fili tace "Anty mun dawo dazu" anty Maryam tace "iyyee shine ba sanarwa, ya kuka baro mutanen can" ta bude wardrobe dinta tana kallon kananan kayanta da bata cika sawa ba tace "lafiya lau Anty, Tambayarki zanyi don Allah" Anty Maryam ta ajiye wukar hannunta ta samu wuri ta zauna tana cewa "Allah yasa na sani" Nabila ta danyi kasa da murya tace "Dr muna dawowa daga Abuja yaje tambuwal bikon matarsa to da can zai kwana yanzu kuma ya kirani wai yana hanya to wata kila matsala aka samu, niko ina son in Faranta masa amma dai yace kar inyi girki ya zanyi" Maryam tayi wata irin dariya sannan tace "yarinya kin fara abin arziki kenan? Bari billahi ganinan zuwa in kawo miki wata hadaddiyar humra da turaren wuta ki baza a gidan da jikin ki, na fasa girkin sai na dawo" Nabila ta zaro ido tace "Anty Maryam dare fa ya fara yi isha'i ake batu" Maryam ta ja hijab dinta ta kalli mijinta tace "sweety na fasa zuwa gida don Allah it's urgent zan kaiwa Nabila abu in dawo" ya kalleta daga sama har kasa yace "na hanaki tuki da dare ai ina zama na karki sake zuwa ki afkawa express" ta bude baki zatayi magiya yace "muje in kaiki amma da yaran zamu" tayi dariya tareda cewa "Ba matsala ai" Nabila tana juyosu tayi dariya tareda kashe wayarta, wanka ta shiga tayi da sauri, tana fitowa suna isowa Hijab tasa taje ta bude kofa Maryam ta shigo tana cewa "ya kusa isowa ko"? Nabila tace ya kusa gaskiya dan kafin magrib mukai waya yace ya taso kuma tafiyar awa daya ce" Maryam ta bude kayan ta mika mata harda kayan bacci tace "karbi wannan rigar jiya dana irinta ba karamin girma ta siya min ba, yau ko fita yaki yi, zan wuce ki gyara dakyau kinji yar kanwata karki mance ki aje ruwan zafi na gashi bayan an gama" Nabila ta jefa mata rigar tana cewa "haba anty Maryam kina sani jin kunya" fita tayi tana cewa "Nabi kunyar dagudu kinji" biyo bayanta Nabila tayi amma ta samu har ta fita gate rufe kofarta tayi ta dawo cikin sauri tayi shirinta ta kunna turaren wutan kitchen ta nufa tana cewa "kafin ya iso bari insamu insha koda tea ne dan nasan bai wuce kayan kwalama niko Allah ya gani ba yimin suke ba" tana bude gwangwanin madara taji karar bude gate, ta sauke ajiyar zuciya tana rufe gwangwanin tana fadin "inban koshi ba dare zanbi insha tea gaskiya" daki ta shiga tacire hijab din jikinta ta sake goga yar hoda da turare ta fito, direct zuwa tayi ta bude masa kofa lokacin har yana shirin kwankwasa tayi dariya tana cewa "yaushe zanji karar bude gate kuma ace sai na jira ka kwankwasa sannan in bude"? Ya shigo yana cewa "ahh tunaninki mai kyau ne kullum, ya akayi naga kamar bayan gida babu wuta" ta karbi ledar hannunshi tana cewa "banma lura ba dan ban zaga bayan ba" ta kalli bayan shi tana sake cewa "Niwai dama ba kwana zakayi ba kodai koroka akayi" sai da ya zauna kafin ya bata amsa, ransa yakejin babu dadi irin kazafin da Nafisa tayi masa Allah yagani yaso kyautata mata amma halayenta basa bari, kallon dressing dinta yake yaga yadda kayan suka karbi jikinta skinny jeans ne a jikinta dark blue, da farar riga mara kauri yana hango farar bra dinda ta saka tanada dogon hannu amma bata da tsayi cibiyarta a waje, kanta a bude babu dankwali tayi parking gashin tsakiyar kanta ta dunkule shi,  hannu ya mika mata yana cewa "adduar ki Allah ya karba, sai kizo ki gwadamin irin murnar da kika yi tunda kinsa an koro ni" ajiye ledar tayi kan center table ta nufi daki tana cewa "Naki wayon dan samari sai nayi sallar isha'i" mikewa yayi har zai shiga daki ya kalli Ramla tana wasa a tsakiyar palon da Teddy ta Muhammad ko yana kwance yana tsotse yatsansa, fasa shiga dakin yayi ya tsaya nan palo yayi sallar shi har shafa'i da wutiri, hular kanshi ya cire ya ajiye yana kiran Ramla aikuwa tazo tana zuba masa surutu, yaja hancinta yana cewa "sweety ya akayi bakinki har yanzu yaki budewa kusan shekara biyu amma baki iya magana ba" Nabila da fitowarta kenan daga dakin tace "wallahi nima naga ta dade bata iya magana ba, mai ka siyo mana tunda ka hanani girki" jingina yayi da kujera yace "zoki duba ki gani" karasowa tayi ta duba, batayi magana ba ta shiga kitchen ta dauko plate da cup guda daya ta dawo ta zauna, tana cewa "Dr ni nake da daya ko" harararta yayi yace "yaushe zan kawo miki rabin kaza bayan nasa ke kura ce, nidai bani yunwa nake ji" gwalo tayi masa ta dauke dayar ta ajiye gabanta.

daga nan kallo sukayi suna hira tana tambayarshi son zuwa gida da takeyi jibi, shikuma turarenta yaketa shaka yana rufe ido acikin kunnenta yace "idan kin fadamin acikin sunning waccece tafi dadi zan miki kyauta" tayi dariya tace "me zaka ban idan na fada maka" ya kura mata ido yana nazari sannan yace "zan baki dubu hamsin kyauta kisha ice cream" saida ta tashi zaune sannan tace "Aure" ya girgiza kai yace "bakici ba" yana kokarin tashi ta rike shi tace "to fadamin waccece" gefen kumatunta ya rike yace "wannan wanda akeyi oza room" "iyyyee ai duk maganar daya ce Allah saika bani 50k dina" daukarta yayi ya nufi dakin da ita yana cewa "ai baki bani amsa mai gamsarwa ba" wuntsila kafafuwanta take tana kokarin sauka tace "ka taba ganin anyi wannan abu ba aure an kira shi da sunna? Malam dubu hamsin dina cas" ya ajiyeta ta nufi kofa da sauri ta fita, kaya ta sauya ta dawo dakin ya kura mata ido kafin yace "meyasa kika ciremin kwalliya" ta kalli jikinta tace "Nagaji dasu ne kasan kuma bazan iya bacci dasu ba" ya rike hannunta tareda cewa "gara da kika cire wannan wando dan Haramun ne matar

Please Login or Register in order to submit comment