Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[16/12/2022 11:21 AM] Zee Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWAN MAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA

1️⃣

YA ALLAHU,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA A KANKI BA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN ,,,,,,,,

YAR UWA DA BAZANKU MUKE RAWA IDAN BA MAKARANTA BABU RUBUTU GODIYA GAREKU HAR KULLUN DA IRIN GOYON BAYAN DA KUKE BAMU MUKE CI GABA KULLUN,,,,,,,,

Matashine ke tafene da sauri a cikin tashin hankali kamar yadda kowama a unguwar yake cikin sauri dan yanayin da gari ya nuna idan da rabo ruwane zai iya gwaucewa a ko wani lokaci a garin.
Saidai shi kana ganin shi kasan yanayin shi baya cikin walwala a lokcin don yadda yake tafiyan zaka iya fahintar hakan gareshi .
Sauri yakeyi a cikin tafiyan shi irin na mazan dake da karfin kira da zatin karfi inda yake dan hadawa da sarsarfa don kada hadarin daya game gari yana shirin saukoda ruwa ya sameshi a hanya lokacin.
Yayafi akafara dan sakewa haka yasa ya kara saurinshi a lokacin ba komai yakewa sauri haka ba sai don abu biyu zuwa ukku na farko don kada yan tufafin dake jikinshi su jike dan ko a gobe su yake da niyar mayarwa a jikinshi da kuma yar jakkar shi da yake adana takardun karatunshi a ciki wanda ke rataye a kafadan shi.
Sai abuna biyu tunawa da kakan shi Dije dake gida ita kadai a wanan lokacin yasan ba kafane gareta ba a yanzu saboda tsufa daya fara kamata kafan na dan rike mata lokaci lokaci don ko da zai fita da safe ya barta dashi dan ya taso mata haikan yana mata ciwo a cikin yan kwanakin nan sosai.
Da sallama ya fada gidan idonshi ya fara tozali da Dije dake tsakar dan gidan nasu tsaye tana tafiya da kyar tana kokarin kama dabbobin dake ta kuka saboda yanayin hadarin da suka gani suma a lokacin.
Da sauri ya karasa inda take ya karbi dabbobin daga hannunta ya nufi dan rumfar da ake dauresu ya fara turkesu ita kuma tana kokarin juya zuwa daki take mashi sannu .
Yana ciki yana dauresu yaji saukan ruwan da karfi wanda kafin ya fito ruwa ya fado sosai ta yadda sai ya jika jikinshi dole don karfin ruwan.
Dakin kwanan dijen ya nufa da sauri ya fara walwale ledan da suke tare ruwan sama dake diga a dakin idan ana ruwan sama sai sukanyi wanan dabaran a daura leda koda ruwan zai zobo ba zai taba yan kayan dake dakin ba sai ya tsaya iya leda kawai.
Bayan ya gama daura ledan ya dan fara samun natsu a lokacin kafin ya kai hannu saman rigan jikin shi da ruwan ya riga ya taba ya fara balle bottom din rigan a hankali yana kallon yadda ruwan saman ke zuba.
Kallon rigan yayi ruwan saman ya riga ya taba duk da baiso hakan ba a lokacin saboda ita din yake da niyar mayarwa idan Allah yakaimu washegari zai fita.
Duban ruwan yayi daga inda yake tsaye a cikin dakin yaga yadda ruwa da iska ke zuba da karfi lokaci guda irin na tsakiyan damana din nan mai barna ga mutane da kaddarorinsu.
Ajiyan zuciya ya sauke don yasan yau akwai barna idan ba Allah ya gyara ba ke nan dole haka ya ratsa ruwan ya fito a guje zuwa dan karamin dakin shi da yake kwana a cikin gidan tsohuwan kakan nasa da ita ke nan masa tillo dake kula da komai nasa .
Kayan ya sauya tare da baza wanda ya cire a jikin shi zuwa wani tsohon gajeren wandon shi da wata riga nasa daya tsufa har ya dan fara cacakewa don tsufa amma haka yake amfani dashi idan yana cikin gida.
Komawa yayi ya rakube a wuri daya kafin ya fara bin dakin da duba na dan lokacin yana sauke ajiyan zuciya a hankali tare da kara kai kallonshi gun kofa yana kallon yadda ruwan ke zuba da karfin Allah.
Wani ajiyan zuciya ya kara saukewa a hankali tare da lumshe idanuwan shi yana ci gaba da tunanen kuncin rayuwan da sukeyi a gidan dashi da kakanshi Dije.
Baida kamar Dije din yanzu a duniya don da Dije ya bude idanun shi da Dije ya taso a rayuwanshi yau duk abinda ya zama Dijene silla itace gatanshi a duniyan nan.
Don itace uwa uba kaka a gareshi tun tasowan shi bai san kowa na kusa nasa ba idan ka debe Dije dake bashi kulawa irin na mahaifa don a tare da ita ya taso ya bude idon shi.
Wani irin tsawa aka sake lokaci daya tare da walkiyan da yai sanadiyar budewan idonshi da sauri yana karanto addua a bakin shi subbuhul kudus wal,mala,ikatu walruhu,,,,,,
Ihun da yaji kamar a makwabtansu yasashi bude idon da sauri tare da kara dan firgitashi lokaci guda don yana ji yasan ihun bana lafiya bace.
Don kusan haka suke fama duk shekara sai sun samu wanan matsalan ruwan saman kasancewa gidanjen unguwar duk tsofin ginene ne irin nada can baya.
Wanan yasa duk shekara idan ruwan sama ya fado hannunsu a gaba yake don fargaban ruwan sama yadda zai kasance masu yawancin gidajen basu da sukuni idan ba sunga an dauke ruwa ba.
Gashi talauci irin na yan arewa yayi masu katutu ba zarahin gina wani a garesu sai wanda Allah ya tallafawa ya samu wani budi zai dan yiwa nasa kwaskwarima ko a fita ciki.
Wanan yasa ake kiran unguwan da tsohon gari don mafi yawan gidajen dake unguwar duk gidajen tallakwane a wurin matasa da masu kudi sunfi komawa daga bayan gari
suna ginan su irinna zamani.
Kakan wanan matashin gidanta na daga cikin jerin gidajen dake cikin wanan unguwar ta tallakawan dake fama da barazanan ruwan saman a duk shekara.
Duk da karfin ruwan saman da iska da akeyi a lokacin bai hana yan unguwan jin kururuwan wasu mazauna unguwan da iska da ruwan saman yayiwa barna a ranan .
Haka ya jawo hankalin sauran yan unguwan suka fara fitowa daga gidajen su don zuwa bada agaji kamar yadda suka saba bawa junan su lokaci lokaci.
Dakin kakanshi ya fara nufa inda ya samu duk da ledan daya daura mata don tare feshin ruwa dake diga a dakin yau karfin wanan ruwan bai tsaya a iya ledan ba kwarai ga tsohuwar tsugune tana faman tara yan tsummakara tana tare ruwan dake dan dinga daga saman dan rufin kwanon dakin wanda duk kwanon ya riga daya tsufa sosai a lokacin saboda dadewan da yayi.
Ihu nake ji a waje ya fada yana karban abinda take kwasan ruwan dashi dake hannunta bata kai ga mika mashi ba, take fadin jeka kakai masu agaji saboda Allah.
Tun ganin yadda aka hada hsdarin nan nasan yau unguwar nan sai yadda Allah yayi damu don wanan ruwan da karfi ga iska yake sauka ji dakin na duk da wanan dabaran saka mai ledan da kayi amma sai zuban ruwa yakeyi yau din nan.
Juyawa yayi da sauri ya fice ya barta a duke tana magana ita kadai yana fita abinda ya gani ya kara daga mai hankali don ruwane ko ina a kwance zakace a tsakiyan rafi gidajensu yake a unguwar.
Da sauri ya kara kai kallon shi gefen hagu gidan malam Tanimu mai faskarene yayi flat kamar ba a taba gina a wurin ba.
Gasu tsatsaye sai ihu iyalinshi keyi suna neman taimako ga jama,a da suka fito don kawo masu agaji ga kururuwan neman agajin da sukeyi.
Hankali tashe ya nufi wurin a gigice da alama akwai wani da ginan ya rufta dashi don yadda suke kururuwan taimako daga jama,a.
Gashi sai su biyu yake ganin sun fito don basu agaji don kowa na cikin gidansa a lokacin ya kasa ya tsare ana duban hukuncin ubangiji.
Malam suke fadi kawai don matar gidan daga ita sai zani daura gaba kawai a jikinta sai kai gwauro da mari takeyi a tsakiyan rubaben gidan nasu.
Dakin ya nufa gadangadan ya fara tono kasan dake wurin a cikkn sauri irin na bada agajin gagawa ga mutum ganin hakan suma suka taimaka mashi har Allah ya taimaka suka fara hango malam Tanimu din da kasa ya rufeshi a some suka zaroshi baya cikin hayacin shi.
Duk sun zuba ido suna kallon yadda yake bashi taimako a cikin gwanewa da hikima sai gashi ya fara dan motsi da hannayen shi a daidai lokacin aka kara sake wani cida mai karfi da walkiya.
Ruwane masu karfi suka kara biyowa bayan hakan wanda yasa hankalin kowa kara tashi don dare sukewa gudu Allah ya taimaka a lokacin yamma ne duhu bai riga dayazo bako.
Ganin mutane sun fara watsewa suna komawa gidajen su saisu da abin ya shafa sai Amadi da yake kan malam din yana bashi taimako.
Karan ruwan daya tun karo unguwar daga wani bangare na cikin gari ya kara daukan hankalinsu ya dago kai yana fadin wani ya taimaka min mu kamashi mubar wurin nan.
Sai gani yayi daga shi sai iyalan malam Tanimu din makwacin su kawai a wurin duk saura sun shige gidajen su a lokacin da taimakon iyalan malam din suka sam u suka kamashi zuwa dan kangon gidansu.
Su samu su fake har ruwa ya dauke asan abinda za ayi saidai suna tun karan cikin gidan kakanshi Dije ce a waje cikin ruwa yana dukanta hankali tashe tayi tagumi da hannu daya tana kallon ikon Allah.
Ganin su yasa ta nufosu hankali tashe tana fadin Amadi dakin nawa rawa yake yana jijiga kamar zai tashi sama yasa na fito na tsaya nan.
Duban dakin yayi hankali a tashe kafin ya juya inda malam tanimu yake tsaye rabin kafadanshi duk a jikin Amadi din yake bai ajeshi ba saidaya danganashi da dakinshi har kakan nasa suka kutsu gaba dayan su sun zubawa saurata Allah ido.
Manyan duwatsu ya dinga mirginowa zuwa bayan dakin har ya samu ya tangale ginan tsohuwan dashi ya koma ya zauna daidai ya daina rawa.
Sai lokacin ya sauke ajiyan zuciya kafin ya samu shiga dakin tsohuwar ya fake yana sauke numfashi a hankali wurin zama yaiwa kanshi saman kujera yar tsugunno dake dakin aje ya fara bin dakin da kallo yana tausayawa halin rayuwa irin nasu.

Duk ruwan saman da ake shekewa su sam gidan basu sanma anayi ba saboda yanayin ginan nasu na zamani da bai nuna hakan idan baka fito wajen gidanba ba zaka sanda ana wanan irin uban ruwan mai karfi haka ba garin.
Sai sha,anin su sukeyi a cikin gidan basu san wani wahala ko tashin hankalin da marasa karfi suke ciki a garin ba.
Hjy saude ne tashigo dakin yar nata tana saye da hijjab a jikinta mai ruwan toka farace mai dan matsaksicin tsawo mara jiki kallo daya zakai mata zaka gane bata da wani shekaru mai yawa.
Idanun ta akan yar nata dake kwance tana karatu duk rabin jikinta a waje ya kware don yar rigar zama gidace doguwa a jikinta.
Haba mamangida ace tun safe mutum yana kwance haka ko dan lekowa waje ina jin yau bakiyi ba tunda safe watau ke dai bakya jin magana dai maamah.
Wace aka kira da Maamah din ta dago kai tana murmushi tana dan dagowa daga kwancen tare da fadin wallahi yanzun nake fadin in fita in ganki sai karatun test din nan ya dauke min hankali.
Kiyi hakkuri ummah ta fada tana sauke kafafuwanta daga saman gado uwar tabi fararen kafafuwan yar nata da kallo tana fadin yau part din maman ku bakije kin gaida ita ba.
Irin wanan halin naki take na ko in kula bana son shi kisa ana dauka nice ke rabaki da mutane ko nake hanaki shiga yan uwa sam bana son irin wanan halim mutum ya dinga baya baya da kowa.
Ummah yi hakkuri yanzun nan zan fita na gaidasu ai karfe nawa kike tsamani yanzu din duban lokaci tayi ta hanyar daga kai ta kalli agogon dakin daya nuna biyar da rabi na yamma lokacin.
Au ashe da sauran lokaci amma naga wurin yayi duhu haka mana ruwan sama ake yau sosai a wajen kina nan ciki baki ko san abinda gari ke ciki ba wanan irin rayuwan baida kyai maamah ki dinga shiga yan uwa ki daina nisanta kanki da kikeyi da yan uwan ki bana son haka ummah ta karasa cikin nuna bacin ranta.
Ummah kiyi hakkuri ta juya ta fice daga dakin ban dakin ta shiga ta gyaro fuskanta kafin ta fito zuwa part din maman nasu sai a lokacin take jin yanayin sanyin ruwan saman da akeyi yana ratsa jikinta a hankali.
Tafiya takiyi kamar bata son taka katsa ta nufi wani dogon corridor daga barin gabas wanda ke kallon nasu part din kofan falon a bude yake haka ya bata daman sa kai ta shiga da dan sirierin sallama a bakin.
Duk suka juyo suna kallonta bayan sun karba mata direct wurin matar dake zaune saman carpet ta nufa har kasa takai kafin tace mama ina wuni.
Da mamaki a fuskan matar take fadin Maamah kina gidan nan dama ko a can wanan ruwan ya sameki haka ?
Dan murmushi ta sake kafin ta kai zaune kusa da matar tana fadin ai yau ban fita ko ina ba ina ciki ina karatun test da zamuyi gobe idan Allah ya kai mu.
karatu tun safe mutum yana kwance a daki wata kila ma ko abinci bakici ba tundazun son shiririra dazun nan nake maganan ki da ake fadin ruwa yau akeyi sosai garin.
Wallahi ina gida mama ban fita ba ta fada tana gyara zama kallon ganyen dake gaban maman tayi cike a plate daya ya sha kayan hadin gargajiya zogalene da kuli kuli sai su tumatur da albasa attarudu da aka zuba a sama.
Zakici ke nan uwar ta fada ta dan daga kai alaman eh a hankali zubo mata Yasmin matar ta fada wace aka kira da Yasmin din ta tabe baki tana fadin mama ba yawafa kuma ai kin aika masu part din su dashi.
Ina ruwan ki wanan din dai take son ci don haka ki dauko plate ki zuba mata ko kuma barshi nasan halin cin nata, ta dai saka hannu a nan muci tare kawai.
Duban hannun nata tayi kafin muryan maman yace kin san dai ba a cin abinci da cibi sarkin tsabta tashi ki wanko hannun kizo muci matar ta fada.
Mikewa tayi zuwa kitchen din part din bayan tafiyan ta matar ke fadin Yasmin bana son wanan halin da kuke son nunawa yarinyar nan wanan yasa yanzu take yawan jan baya damu na sani don ba halinta bane haka.
To mama ita din sa,arkice da zata dinga manne maki ko yaushe taje gun uwarta mana amma sai ta dinga wani shishigewa mutane a daidai lokacin yarinyar ta fito daga kitchen din.
zama tayi zuka zauna da mama din tare sukaci ganyen suna da hira jefi jefi wanda baifi sau hudu da takai ganyen a bakinta tana fadin ta gode ta koshi ta mike ta koma kitchen din ta wanke hannu sai gata da wani ruwa a roba ta kawowa matar tana fadin mama ga ruwa idan kin gama ki wanke hannun ki.
kai maamah badai tsabta ba shiyasa nake son ki ai bata zauna ba don ganin magariba ya kawo jiki tayi masu sai anjima ta koma part din ida nan ma bata zauna ba yan gyare gyare tayi kafin ta shige daki yin sallah zuwa lokacin sanyin damana ya hade dana iskan dake kadawa ya kade ko ina yana shiga jikin bawa.
Bata kara leko wajen ba sai washegari don tasan tana da exam a ranan don haka ta tashi da wuri ta shirya a falon su ta samu mahaifiyat ta da mai aikin suna magana yanayin fuskan mahaifiyan nata ys sauya.
Ummah ina kwana ta fada daga bayan ta hakan yasa uwar dan juyowa tana kallonta tare da amsawa take fadin kin fito ke nan ko me eh ummah ina son na isa da wuri don na dan taba karatu a can.
To ki karya don ba,a fita gida hakana ba, a karya Tani don Allah miko mata ruwan zafi ummah ta fada cikin rashin walwala a fuskanta har lokaci.
Ummah wani abune ya faru lokacin uwar ta juyo tana fadin bari maamah ruwan nan najiyane yayi barna a cikjn gari harda rasa rayuka mai aikin ce ta fito tana fadin hjy inaga ashanan mu ya karefa.
Haba Tani na hanaki yin hakkan idan abu zai kare ki fada min don Allah na sayo ummah barin wuce kawai kada in makara idan naje can zan ci a capterial.
Akwai kudi a hannun kine eh wanda Abba ya ban banyi komai dasu ba suna nan ta fada fatan alheri uwar tabi yar dashi ta fita duban part din mama tayi yana rufe ba a bude ba har lokacin yasa ta fice daga gidan kai tsaye.
Komawa ummah tayi ta zauna bayan fitar yar nata da take bi da adduan fatan alheri akoda yaushe al rayuwan ta.
Kasancewan su su hudu tillo suke a wurin ta auren ta shekara goma sha takwas kafin Allah ya azurta ta yarta Zarah wace taci suna uwar mijinsu Fatima wace ke raye har har yanzu da rayuwanta .
Rashin haihuwan ummah yasa bayan shekara daya da aurensu aka matsawa mijinta ya kara aure ida ya auro mama bata take wata ba ta samu ciki a gidan wanan ya jawowa mama dauka sosai ga kowa.
Nan soyayyan duniya ya hau kanta daga mijin har yan uwan miji ta zama abin lele a garesu sai ya koma kamar itace uwargida a gidan ba ummah ba.
Sai gashi wasa wasa har ta haifi yara maza biyu sai mata uku sai kuma maza da suke sa,an zarah a yanzu wanan yasa ummah ta sakewa mama duk wani girma dama kuma ita mama ta girmi ummah din don ita saida ta tsaya ta kare secondary din ta lokacin ana form five afita secondary.
Lokacin da Ummah ta gane tana da ciki a jikinta tayi ta boyon cikin jikinta na zarah lokacin don tana gudun azo daga baya ace marudiyace ya kasance ba cikin bane jikinta har saida cikin ya fito fili ya nuna kan shi ga jama,a .
Nan tsegumi ya fara tasowa wurin mutane har zuwa lokacin haihuwan zarah da wasu ke kiranta da Tuni don dadewan da akayi ba a sameta ba lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[16/12/2022 10:33 PM] Zee Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,,
2️⃣ZAINAB IDRIS MAKAWA
AR RAHAMAN ,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN ,,,,,,

💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫

*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI KYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327

_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_

Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻

Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata

Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki

Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci

Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji

Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar

Please Login or Register in order to submit comment