Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawabin muhimmancin ilimin Islam cikin harshen larabci inda labila take fassarawa cikin harshen Hausa"" hafsat takeyi cikin harshen turanci daki daki sukebin komai

Hakika nayarda
Ilimi wani abune maidadi hakazalika maisanya nishadi azuciya"ilimi gishirine narayuwa"dukkan Wanda yakeda ilimin Islam bazaitaba tabewaba duniya da lahirah Allah yabamu ilimi mai amfani

Bayan sunkammala khadija tayi Yar takaitacciyar nasiha gameda muhimmancin bin iyaye cikin harshen Hausa wadansu sunyi mamakin jinyanda take magana dahausa Dan Sam basuyi tsammanin tanajin hausaba

Birrul walidaini"" wato biyayya ga iyaye "" Yakamata yan uwa musan mahimmancin iyaye arayuwarmu musaman uwa!! uwa!! uwa!!!

Kasani komai kazama aduniya karkasake kawulakanta iyayenka babban abunda yake damun al ummarmu ayanzu dayawa mutane basusan darajar iyayensuba

Baka daraja iyayenkaba toballantana kuma iyayen wani"" shinkokasan dukkan cigaba yana samuwane idan harkabi Allah da manzonsa sannan kuma kabi iyayenka""

wasu yayan babu ruwansu sudai kawai suyi abunda yake gabansu karkumanta wahalarda uwa takesha tunsanda kake cikinta ranarda zata haifeka wahala cikin wahala harkazo duniya tayi dawainiyar shayardakai sukabaka ilimi Amman dagakarshe saikayi tamkar bakasan dawainiyarda sukai dakaiba"" shinkayiwa kanka adalci kuwa??? Kokadauka basuda hakki akankane??? Kamar yanda akace matarka aljannarta tana karkashin kafarka haka kaima taka tana karkashin ta iyayenka inhar kasaba musu bazaka shiga aljannaba.

Sukuma iyaye Susan tarbiyarda zasu baiwa yayansu domin suyi alfahari dasu"" abun alfaharinkane kaji ance wannan Wanda yacinye gasar musabaka aidan wanene bazakaso kaji ance ankama danka yana kanta daureba kokaji ance aidanka babban danfashine
Ku kyautata atsakanin Yaya yenku

Manzon Allah yanacewa awani hadisi""
وقال صلی الله ءليه وسلم ساووا بين أولادكم kusasanta "atsakanin yayanku a

Awani hadisi manzon Allah yabacewa وقال صلى الله ءليه وسلم إن من حق الولد ءلى والده أن يعلمه الكتا به و أن يحسن اسمه و أن يزوجه إذا بلغ رواه النجار

Yanadaga hakkinda yarataya akan iyaye bisaga yayansu ya karantardashi littafinshi ma ana alqur ani maigirma "" kokai zaka karantardashi kokuma kakaishi islamiyaya la ba asan"" '' ka kyautata sunansa"" sannan ka aurardashi idan yabalaga""





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




chapter 55
By
Gentle Lady💃🏽


وقال صلى الله ءليه وسلم من بلي من ه‍ذه البنات بشيء فاحسن اليه‍ن کن له ستر من النار Wanda yakeda Yaya biyu mata ya kyautata agaresu ma ana ya tarbiyantardasu harsuka girma ya aurardasu zasu zame masa sutrah daga daga wuta"""
Inakirah ga iyayena maza da mata dasu tsayu akan Yaya yensu kusan kalar tarbiyarda zakubaiwa yayanku domin duniya tayi alfahari dasu

Kukasance kuna ciyarda matayenku abinci na halat domin samun Yaya nagari masu biyayya agareku sannan kusa ido akan yayanku abokansu makotanku yanda suke mu amala

Musamman wannan zamanin damuke ciki wai uba zaiyi zina dayarsa Yaya. Yayi zina dakanwarsa makoci yayi zina da matar makocinsa da yayi zina da mahaifiyarsa wa iyazubillah waihartakai anayiwa kananun yara fyade kayiwa yarshekara biyar ko uku ko hudu fyade bisabillahi mezakaji??? Banda zalunci kuma dakai za ayiwa yarka ko kanwarka yazakaji??? wai wane irin lokacine mukeciki ayanzu babu shakka manzon Allah yayi gaskiya

Duk ilimi ya bace acikin alumma barna tayawaita adoron kasa tobala ine zaiyita shigowa gashinan kuwa munagani

Duk wannan tsadar rayuwar damuka samu kanmu aciki mune mukajawa kanmu"" kashe mutane sai yawaita yakeyi anmaida rayuwar mutane tamkar takiyashi kiyashima yafita daraja

Lalacewar Yaya iyaye sunada hannu dumu dumu yaro tunyana karami ake koyardashi yanda zaibi Allah Amman wasu iyayen koda sunga yaro yanayin badaidaiba wani yayi magana saisuce kukyaleshi kuruciyace

Wai kuruciya bayankuma ayanzune yadace kuginamasa komai tayanda zai zauna akansa

Manzon Allah yanacewa awani hadisi"" هفزل غلم سغرن كنكسن بلهحر .وهفزل رحل بااد ميغبر كل كتبت ألل ماء kiyayewar yaro karami kamar rubutune bisa dutse kiyayewar babban mutum bayan yagirma kamar rubutune bisaga ruwa

Idankukai rubutu akan dutse zai zaunane daram bazaitaba gogewaba sai idan zakusaka nakiya ne kufasa dutsen kodakuwa kunyi hakan za asamu wani gefen darubutun Amman bazaitaba goguwaba

Amman kugwadayin rubutu akan ruwa kugani shinzai tsayakuwa???? Tokamar hakane idan yaro yagirma babu abunda zai iyah tsayawa akansa

Hausawa sukance icce tunyana danyensa ake tankwasashi idankuwa yabushe bazai tankwasuba inharkuwa kamatsa saidai yakarye

Tokamar hakane idankukaga yayanku sunayin abunda baidaceba kutsawatar masu kuma kuzaunardasu kununa masu illar yin hakan kusanardasu irin azabarda akeyiwa mai aikata hakan tozasuji tsoron aikatawa

Kundarsa masu tsoron aransu dashikuma zasutashi""misali kamar yanda akecewa yara Karya haramunne maikarya Dan wutane

Zakaji yara harsunayi dawaka idansukaji wani yayi karyaa"" ya Allah kashiryar mana da zuriyarmu Kaine maishiryarda Wanda kaso idan kashiryarda mutum babu mai iya batardashi idankuma mutum yabace babu mai iyah ganardashi gaskiya sai idan kaso

Allah kakaremana yayanmu da jikokinmu yan uwanmu musulmai duka kabamu ilimi mai amfaninmu duniya da lahirah kadoramu akan tafarkin gaskiya"" kasadamu da rahamarka"" رب اغفرلي وتب ءلي إنك أنت التواب الغفور. سبحا نك الله‍م وبحمدك أشه‍د ان لاإله إلاأنت أستغرك وأتوب إليك

Tamikawa malamin lasifikar"" gabadaya akakaure wajen da kabbara
Cikin natsuwa suka karasacikin taron wajen muktar tatafi"" inda akarufe taro da addua"" akasoma watsewa saiyanzu labila taga dad inta"" yana nufosu"" da fara a afusarka""

Hajiya tace yan kaduna saukar yaushe??? Yace kafin afara nakaraso labila tagaidashi ya amsa yana tayata murna" Dukawa yayi yagaida hajiya ta amsa cikin sakin fuska yabawa Hafiz hannu suka gaisa yace kaga yarka ko banyi tsammanin haka takeda kokariba

Hafiz yace hakane Yaya ai ina shirye shiryen turata saudiya tayi karatu acen inshaa Allah sai anyi alfari da itah

Majeed yace uncle nikumafa??? Kansa yashafo yace sha kuruminka aihardakai za aje inajirane kaima kasauka kamar yanda tasauka saika miyarda hankali sosai idan kanaso katafiii

Hajiya tace tomuwuce gida ko"" labila tace nidai hajiya kukarasa nizan jirah sahibane mutafi tare"" Usman yace wainikuwa wacece sahibar nan???

Kullum maganarki sahibadai sahibadai yaudaikam inaso naga wannan sahibar
Tace zakaganta kuwa dad"" yace lallaikam inason ganinta dankam nalurah bakaramin so kike mataba

Hajiya tace inama kasan haka kayanda kasiyomata cewa tai bazata sakasuba saboda bakasiyo biyuba da itah da sahiba saboda Hafiz yasaba komai zaisiyo dolensa yasiyo biyu idankuma bahakaba bazatayi amfani dashiba""

Yace um lallai naga alama tokutafi muje gidan gabadayansu suka karasa wajen motarda Hafiz yazoda itah""

Labila kam wajen sahiba takoma tacemata suwuce gida"" dayake bawani nisa dasubane tsakanin gidansu da islamiyya Amman akwai yartafiya

Motar abokin muktar suka shiga zuwa gida"" anakaiwa gidan taja hannunta tace muje kigaisa da babana""

Juyawa tayi tace Yaya inazuwa yanzun zandawo yace to ba Matsala sukawuce cikin gidan gaban khadija sai yatsananta bugawa

Zaune yake shikadai acikin falon wayace ahannunsa yana latsawa tunda sukayi ido biyu da ita tasanne kwayar idonta kasa wani abune takeji yanamata yawo ajiki tareda harbawar kirjinta

Taresuka duka tace inawuni daddy wani sanyine yaji yaratsashi aransa yace ya salam badai khadija itace Kawar labilaba???

Labila takatsemasa tunani tahanyar cewa dad ga kawata sunanta khadija Amman yangidansu sunakiranta da safna saboda sunan mahaifiyartane

Nikuma inakiranta sahiba dad inasonta fiye dayanda nakeson kaina itah marainiyace mamanta tarasu tana zaunene ahannun kawunta tareda yayanta

Sannan takalli khadija tace sahiba ga babana""" abun alfaharina kuma maisharemun kukana"" yaudai kinga babana ko

Khadija tasake dago kai karaf sukasakeyin ido hudu dasauri tamike jikinta yana karkarwa"" tace sahiba bari naduba wani Abu

Tayi gaba Usman yabita dakallo hartashige dakin labila yasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya labila tana kallonsa Da kuma yanayinda yashiga

Yadawo dakallonsa wajen labila saiyaga shiitake kallo nantake yaji wata irin kunya takamashi"" murmushi labila tayi tace dad barinaje gurintaa





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 56
By
Gentle Lady💃🏽



Kasace mata komai yayi saboda kunyarda yaji"" mikewa tayi kawai tana murmushi tawuce abunta""

Bangaren khadija kuwa tanashiga daki tafada akan gado tadafe saitin zuciyarta inda yake harbawa tamkar kirjinta ne zaifaso zuciyar tafito

Tanacewa لاهولاولاقوت الابل لله kasa samun natsuwa tayi duk da jero adduarda takeyi bataji wani sauyiba azuciyarta "" tagumi tayi yayinda tashiga wata duniyar daban murmushi tasaki afili batasan sanda bakinta yafurta gaskiya kyakkyawane

Daidai shigowar labila tace baban nawa?? Kunyace takama khadija tace nifa badawata manufa nafadaba ina nufin yanada kyau Ashe shikika biyo ba ummaba"""

Nantake annurin fuskar labila yagushe"" khadija talurah dahakan tace meyafaru sahiba??? Kodai bakiji dadin abunda nafadabane???

Labila tace bakomai kawaidai naji raina yabacine!!! Tatari nunfashinta dakikaji na ambaci umma ko???

Waime yasaka kullum naketa jankunnenki akan muhimmancin umma agareki?? Tanisa kodayake tunda kinada itah araye bazaki gane mahimmancinta ba saikin rasata

Labila tace sahiba kenan wlh dama nice ke dama tun wajen haihuwana tamutu"" khadija tayi saurin rufemata baki tace a uzubillahi Allahumma izna min hazal kalamiki"" kinkuwasan mekike fada???

Kinaso yayanki sucemaki hakan"" wasu hawayen takaici tashare tace inhar banzama nagartacciyar uwaba bazanga laifinsuba koda jifana sukai da dutse

Khadija tadafata tace kome kikeji agameda ummah hakuri zakiyi itace dai mahaifiyarki kuma kinsan babu Wanda zai karkare hakan

Labila tanisa tace babban takaicina kenan danashigo cikin tsatsonta inama ace babana ba itah ya auraba har aka haifeni

Khadija tabata fuska tace sahiba waime yasakike hakane kin isah kisauya hukuncin Allah ne"" kisani kowa dakikagani aduniya bai isah yagoge kaddarar saba

Ballanata ummah batada wata makusa kawaidai dankina yarfarine yasa batajanki ajikinta tokuma bakece kawai akayiwa hakanba kigaggauta Neman tuba awajen Allah

Tashare hawayenta tana maineman yafiya awajen Allah astagfirullah wa atubu ilaihi"" aranta kuwa tana mamaki yanda take kasa sanarda wani damuwarta

Khadija ce tajawo hannunta tafada saman gadon"" tace kiyi hakuri kinji sahibata wlh banason inaganin damuwa atare dake kwata kwata kasa samun sukuni nakeyi

Labila tayi murmushi nadaina sahiba kinga ya muktar fa yana jiranki muje narakaki indawo wajen dad

Tace to tareda mikewa "" aranta tanata addua Allah yasa bayacikin falon labila tanagaba tana binta baya

Yana nan kamardai yanda sukabarshi Amman yadorah kafarsa daya akan dayaa sabanin dazun dayake danna waya yanzu idanuwansa kyam sunakan kofardasu labila suka shiga

Suna fitowa yatada kansa zuwa fuskarta take idanuwansu suka sarke cikin najuna dasauri khadija tasaki likaf yakarasa rufemata yan idanuwanta dama sune kawai abude

Wani iri yaji aransa kardai yarinyar nan tagano itah nake kallo??

Muryanta yaji tanacewa dady sai anjima""" yadago ahankali yakuramata ido saikuma yasaki murmushi yace to Khady kigaida gida" taresuka fita da labila yarakasu da ido

Khadija kafarta har sassarfa takeyi"" sunafita Usman yadafe kansa yace ya salam meyake shirin faruwa dani wannan wane irin abun kunyane zuciyata takeson kaini gareshi kawar yata!! Yayi saurin kawarda tunanin aransa tunkafin yasamu matsuguni

Wayarsa yadauko yakunna kira a yadorah akan kunnensa yadan kishingida saman kujerar babu jimawa barci yadaukeshi awajen

Hajiya yaji tana tashinsa yatashi yayi sallar la asar gashicen anyi kirah mikewa yayi tareda mika yawuce zuwa dakinsa dayake gidan

Yana nan tsaf dashi tamkar akwai mutum aciki toilet yashiga yawatsa ruwa sannan yadauro alwala yawuce masallaci acen yahadu da Hafiz

Bayan sundawo ahanya yake masa maganar yaushe zaikoma america yace wani sati ainakusa gamawa inhuta yawon nan basonsa nakeyiba

Usman yace Allah yataimaka aini namatsu kagama in hannan tamaku dukiyarku"" Hafiz yace habadai Yaya niba fa kasuwanci zanyiba aikin gamnati zanyi
Kawaidai kacigaba dakula dasu

Yana dariya yayi maganar Usman yace naki wayon nauyi yayimun yawa akaina bazaku ragemunba"" Hafiz yace aigirman Kane""Kaine fa babanmu dole kakarbi girman"" Usman yace naji waikai yamaganar auren inata zuba ido naji tsit karfa yarka tarigaka aure???

Kakuwasan dakaji kunya'' Hafiz yasosa kai yace aini karamin ubane bazanji kunyaba tunda Ban isah aureba"" Usman yaharareshi yace ahakan???

Tokodai kafitarda mata ko inhadaka da Abu mai kuli kuli da awara"" baki Hafiz yarike yace abun haryakai cen tokwantarda hankalinka dazaran nadawo zakaji komai

Usman yace sauran watanawa??? Hafiz yace bakwai koyanzu walimar labila tadawo dani danbanaso ayi bana nan"

Usman yace shikenan munadai zuba ido daidai sunkai kofar gidansu sukashiga tare sunafira suna raha hajiya bakaramin dadi takejiba idan taga yayanta cikin farinciki

Saman kujerah suka zube labila tadauko masu abinci sukaci sukahau firah sai shida saurah Usman yayi haramar tafiya harbakin mota suka rakashi yawuce yana daga masu hannu

Labila batakoma gidan sahiba ba saboda hankalinta yanakan yayanta shima washe gari tunda safe zaikoma""


Agogon Nigeria yabuga karfe biyu nadare alokacinda nasan kowa yayi nisa cikin barcinsa saikuma masu ibadar dare. Bakajin motsin komai saikukan karnuka dasuke cikin layin

Inkadauke Usman dayake tsaye yakai gwauro yakai mari tunsanda yabaro kano yakasa samun sukuni cikin ransa"" komai yakeyi fuskarta yakegani sanye cikin nikaf haryana ayyana suffarta yanda zata kasance

Gabadaya ta dabai bayemasa zuciya dakuma tunaninsa hatta abinci idan zaici fuskarta yake hangowa akan plate wanan wace irin makauniyar soyayya ce???? Kawar labila yafurta ahankali komawa yayi saman gadon yazauna yadafe kansa wanda yayimasa nauyi

Kai bazaitaba yuyuwaba wlh tunwuri dama kindaina son abunda bazakitaba samun saba dawanne ido zan kalli labila ince inason kawarta ???

Taya zata kalli maganata?? Yakamata inhana zuciyata afkawa inda baichanchanci yazama muhallinaba "" wata zuciya tace masa taya hakan zai yiyu kokamanta soyayya batayin shawara dakowa

Yayinda zatashigeka batadubà matsayi kochanchantar Abu"" yace idankuwa hakane gaskiya bataimun adalciba saboda abun nan bazaitaba yiyuwaba""


Wata zuciya tacemasa yiyuwa kai saidai inhar bakace kanasontaba koda kaki fada Dole sai zuciyarka ta tilas taka
Yace wlh karyane wannan abun kunyar badanibà ganin abun yanason haifarmasa da damuwa yayisaurin kawarda tunanin abun yafaskara tashi yayi yadauro alwala yasoma nafila yanarokoñ Allah yaciremasa sonta tunkafin yayinisa

Saikusan asuba yakwanta Amman abun mamaki maimakon yaga sauyi aransa saiyaji kamar ansake linka sonnata sau ashirin acikin zuciyarsa





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 57
By
Gentle Lady💃🏽




Har akayi kiran asalatu idonsa biyu bairuntsaba"" tashi yayi yasake dauro alwala yafita yatada lubabatu sannan yakarasa sauka kasa yasoma tashin yan aikin gidan kamardai yanda yasaba

Saida sukai alwala sukawuce masallaci baidawo ba saida haske yagama mamaye gari cikin masallacin ma zaune kawai yake tamkar mutum mutumi tundayake baitabajin soyayya irin hakaba

Waidama Ashe haka soyake??? Lallai Wanda baisan soba shine zai karyatashi baitaba tunanin hakan akejiba gameda abunda zuciya takeso tomeyasa banajin hakan lokacinda nahadu da lubabatu???

Kodai itakanta soyyyar matsayi matsayine da itah nasan Na auretane Dan inasonta towacce irin soyayya??? Kawaidai inajinta cikin raina yanda baxan iyah rabuwa da itah ba

Sauran matanda na aurah fa??? Sume yasa banajin haka atattare dasu??? Suma tasu kalar soyayyar dabantake

Khadija ce kawai lokaci daya soyyyarta tashiga harcikin barko dakuma jinin jikina"" tomeyasa hakan??? Saboda kanasonta"" !! Tomeyasa nakesonta alhalin kofuskarta banganiba ??? Saboda tarbiyarta to ai itama lubabatu tanada tarbiya meyasa banajin sonta kamar wannan ??? Wannan kuma daga Allah ne

Haka yayita yiwakansa tambayoyi kuma yanabawa kansa amsar tambayarsa haryabaro masallacin kwana biyu tsakani yakasa gane kansa abinci kansa yarage ci


Zaune yake office dinsa yana tunani yakamata insanarda labila halinda nakeciki nasan bazata zargeniba saboda tasan banine nasakawa kainaba"" kai anya zan iyah kuwa???

Tomezaihana kadai tsaya kallon ruwa kwado yayimaka kafa kawai kasanarda itah zata fuskanceka dawannan shawarar yayarda yadauko wayar yakamo lanbar Sannan yasoma jujjuya wayar

Yayi tsayin mintuna ashirin sannan yakirah"" tanafara ringing yaji gabansa yafadii rasss"" tayita ringing harta katse ba adaukaba yasake kirah hartakatse bata dagaba

Khadija tana kwance adakin wayar tasoma ruri harzata daga taga sunan wanda yakirah dadyna gabantane yabada rasss tadafe kirjinta tanamairufe idonta

Waimenene hakan kikeyi babananefa"" taja tsakii hartakai hannu tadauka kuma takasa saida yayi kiran saubiyu gana uku tadauka

Jikinta yanadan rawa cikin siririyar muryanta tace Assalamu Alaikum daya bangaren wani irin sanyine yaratsa zuciyar usman haryasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya


Yace Amin wa Alaikumus salam" Wani yanayi khadija tasamu kanta aciki jin muryarsa yasaukar mata da kasala cikin sassarfar murya tace dady ina kwana"" yace lafiya qalau kina lafiya tace umm sannan tace batanan taje gida tadawo batajirah mezaiceba taka she kiran
Tace wai tareda murmushi tanadafe da kirjinta dayake harbawa""


Yanajin taka she yajiwani iri cikin ransa Sam baijidadin hakanba"" yaso koda muryantane yaji yanatsaka da tunani saigakirah yashigo

Dasauri yadauka atsammaninsa itace tasake kirah yanadauka yaji muryan labila bahakan yasoba cikin sanyin murya ya amsa gaisuwarta tace dad tundakazo bakasake kiranaba

Yadan shafo kansa yace tubanake aikine yayimun yawa wlh "" tace shikenan yace yasu hajiyafa??? Tace qalau munga sako dani dasahiba mungode

Yadan murmusa bakomai tayidanjin dad akwai matsalane??? Yace ah yayi saurin cewa sorry ah ah babuwata damuwa kinga wani abune???

Tace dad aibahakan nasabajin muryankaba indai akwai damuwa kasanardani please"" yace bakomai dama nakirakiine naji idan kina lafiya

Tanisa qalau nake dad yace tosai anjima"" tace inasonka dad cikin sanyin murya yace nimahaka yakashe kiran yanamai runtse idanuwansa why why meyasa nakasa sanarda itah???

Bayankuma tatambayeni damuwata yayi wulgi dawayar yadafe kansa wani irin suracine yake fitowa tajikin zuciyarsa yanafita ta hancinsa tamkar suracin tafashasshen ruwan zafii


Labila tsuru tayi tana kallon wayar"" khadija tace yadai sahiba???? Ajiyar zuciya tasaukar tace bakomai tareda zaunawa saman gadon"""

Abu wasa wasa kullum saiyakirata kamar yasanarda itah saikuma yafasa itah tagano manufarsa Dantun ranarda yazo walima taga kallonda yakeyiwa khadija kawaidai yana jinjina sanarda itane amatsayinta nayarsa itakuma taraya aranta inhar bashine yafurtaba bazata taba nuna taganoshiba sai idan yatunkareta da maganar

Yau yakasance weekend ne karfe takwas nasafe Usman yakama hanyar kano yaukam zaisanarda labila abunda ke zuciyarshi saidai koma kunyar ne yajita danyagaji da ajiyar abunda yafi karfin zuciyarshi

Bangaredaya kuma yanason ganin khadija koda muryantane yaji zaiji sanyi "" koda yakarasa gidan hajiya bata nan"" dama kuma Hafiz Yakoma"" bayan yayi pkng suka gaisa damaigadi yake sanardashi yace bakowa gidan kenan???


Yace ah ah yar dady tana nan"" kamar yacemasa tareda kawarta saikuma yashare yawuce cikin gidan tanajiyo sallamarsa tafito dagudu tanamasa oyoyo

Yace labila waiyaushe zaki girmane aiyanzu kinwuce wannan saidai majeed "" baki taturo tace ah ah banwuceba sai anhaifamun Kanwa sannan

Murmushi yayi yanasamun waje yaxauna yacire hularsa yana fiffita kaiyaufa akwai zafi babu wutane???

Tace ah yanzun nan tadauke bari inkawo maka ruwa tayi maganar tana wucewa ruwa tadauko masa tareda cup tadauro akan wani karamin faranti maikyau taduka ta ajemasa tanayimasa ya hanya

Yace alhamdulillah ruwan tazuba masa Tamika masa yakarba yanasha wani sanyine yake ratsashi saida yashanye duka tace akarane dad??? Yace kara Amman kadan

Tasake Karamasa yashanye sannan yasaukarda ajiyar zuciya yace Alhamdulillah nagode"" inakuma hajiya taje baba maigadi yacemun tafita???

Tace ah wlh gidan wata kawarta akayi rasuwa shine tatafi gaisuwa"" yace ayya wayarasu mace ko namiji"" tace wlh bansaniba nima

Yace to Allah yajikan Wanda yarasu tace Ameen" Amman meyasa bakibita kuntafi tareba""??? Tace dad kusa da islamiyar munefa kuma zasuga banzoba saitace induba gida sahiba ma tatafi tundaxu

Shiru yayi baisake cewa komaiba gashi yanason magana Amman yakasa.......





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 59
By
Gentle Lady💃🏽



Yace nidai hajiya natafi"" sukayimasa Allah yakiyaye yawuce cikin farinciki gabadaya jiyake tamkar anyaye masa wani katon dutse daya taushe zuciyarsa fatansa kawai Allah yasa khadija zata ameence

Dawan nan tunanin yakarasa gida"" lubabatu tana zaune cikin falon kasa tana kallo yanashigowa tabishi dakallon mamaki

Kusa da itah yazauna yace yakina kallona bazakimun kosannu dazuwaba"" baki tatabe tace aibansan inda katafiba kaida bakafita koda kofar gidane idanhar ranar weekend ne Amman yaunaga bakon al amari

Yanisa yanashafar kansa yace kano natafi"" takalleshi dahanzari tace incekodai lafiya??? Yace qalau natafi ganinsune kawai yaunatashi dason ganin Ya'yana

Har abada baida niyar boyemata Amman yasamu kansa dakin sanarda itah dalilinsa nazuwa kano tundasafe dankoda yabarta bata tashi barciba shima saman hanya yasha lemu

Tace wlh harkasa gabana yafadi nadauka wani abune yafaru"" yace bakomai wlh hamma yayi yana Shafa cikinsa yace akwai ragowar abinci yunwa nakeji

Tace babu iyah cikina kawai nace agirka kuma nacinye inda kafito bakaci abinci bane??? Shiru yayi baice komaiba "" tace sai idan kanaso nasake sakawa adafa maka wani"' yace shikenan barshi kawai nahakurah inci dadare""

Baijirah jin mezatace ba yamike yahaura sama tabishi damugun kallo"" sosai tanason tarika juya Usman tamkar dancikinta Amman tarasa gane dalilinda yasaka duk aikinda akaimasa baicika tasiri akansaba

Wanda akayi cikin kwalbane kawai yakeyin aiki akansa kumashi zafin zuciya kawai yake sakashi idankuma takulle barta mutane har itah kanta bata tsirah da fushinsa

Abokanta duka suna juya mazajensu son ransu duk da batanemi komai tarasaba Amman tanason harta wanki shine zaiyi mata dagyaran daki

Tanajin tsoron sakashi tunda tasan yanada zuciya zata iyah sakashi yace bazaiyiba girmantama dayake gani yadaina gani kuma batason kowa yarika zargin wani Abu

Usman tunda yahau saman baisaukoba saida yaji kiran sallar la asar yasake watsa ruwa yadauro alwala yasauko tana nan inda yabarta yawuce abunshi batareda yacemata komaiba
Itama batadamuba Dan hankalinta yanakan TV datake kallo""

Kwance take dakin khadija itakuma tanazaune tana yankan kumba"" labila tace sahiba dama magana nakeso muyi dake""..

Tana yankan kumbar ta daina inajinki"" labila tanisa tace gameda alkawarinda mukaiwa juna yaudai inason nafurta maki sunan mijinda nazaba maki

Khadija tayi kasake tana kallonta sannan tanisa tace sahiba atsarina inasone muyi aure tare kinaganin baiyi sauriba idan kika zabamun miji ayanzu

Labila tatashi zaune tace nidai awajena baiyiba kuma nafison ayikomai dawuri"" Saidai idan zakiki zabinane

Khadija tace habadai Nina isah naki abunda kikazabamun nasan har abada bazaki zabamun abunda zaicutardaniba""

Nayarda kowaye zansoshi sahiba idan harkedai yayi maki bamasai kintsaya Neman yardataba kawai kicemasa Na amince

Labila tasaki fara a tace bahaka zamuyi dakeba inasone kifadi ra ayinki"" khadija tace inhar yayi maki wlh yayimun"" karkidamu


Labila tace shikenan Amman akwai bukatar kusamu lokaci domin kugana kafin nan zansanardashi yaturo iyayensa atsaida magana domin cikin kankanin lokaci za ayi bikin"" khadija tace haba sahiba karatunfa!??

Karkidamu da karatu zakicigaba agidanki"" tace shikenan Allah yatabbatar mana da alkhairi labila tace Ameen tarungumeta cikin jindadi
Bayan kwana uku kamardai yanda sukayi dashi saigashi yakirata tana falo tanayiwa hajiya tausa tamike dasauri tayi hanyar dakinta

Hajiya tabita da kallo tana girgiza kai labila waisai yaushene zatayi hankali"" Allah yakyauta

Tanashiga dakin tadauka tareda sallama ya amsa sallamar taredacewa lafiyadai naji shiru kodai kinmantane???

Nayita jiran kiranki gashi har dare yayi"" tace sorry dad wlh mantawa nayine""" idanuwa yakwalo aransa yace umm lallai bakisan abunda dadynki yakeji gameda itaba aida bazaki mantaba

Takatsemasa tunaninsa tahanyar cewa ta amince""" baki yawashe yace dagaske??? Tace sosai ma yace Amman tasan nine tayarda dawuri haka??? Tanisa ah ah batasaniba

Sai murnarsa takoma ciki yace mekikayi haka??? Taya zan aureta alhalin bakisanarda itah gaskiyar kowaye niba

Tace naso fadamata saitace koma waye inhar niyayimun tobasaina nemi yardar taba"" tayarda"" tasan bazantaba zabamata abunda zaicutarda itaba

Yayi shiru daga bisani yace ninasan bazata yardaba"" labila tace maisaukine dad yanzudai inaso kazo kasamu kawunta"" idan kungama magana"" saikazo danka ganta idan kaganta taganka komenene ninasan yanda zanyi

Amman fa akwai sharadi bayan amincewarta"" yanisa wanne irin sharadi kuma labila??? Tace awajena maisaukine bansaniba kodai awajenka dakuma matarka!!

Dif yayi shine illarfa kaso karamar yarinya kuma abokiyar yarsa yanisa shikenan kifadamun sharadin" tace bayanzu ba dad sai idan maganar ta tabbata yace shikenan

Sukai sallama yadade yana nazarin kalaman labila daga bisani yadaga kafadarsa alamar baidamuba kowanne sharadine zai yarda dashi matukar zaisamu hadinkan Khadija dawan nan tunanin yawuni


Bayan kwana biyu dazancen yaje kano hajiya yasamu yalabarta mata komai"" shiru tayi nawadansu lokutta sannan takalleshi tace anya khadija zatayarda idanhar tasan labila Kaine zabinda taimata???

Yanisa nikaina bansan yazata kayaba Amman banada mafita hajiya tunda kikaga harnayiwa labila magana kinsan abun nan ba karami bane

Kece mahaifiyata nasan bazakiso abunda zaitaba lafiyataba wlh inacikin damuwa sosai abun yana Neman taba lafiyar jikina likita yacemun nadaina shan maganie nayi aure

bansanarda ke bane kawai tunsanda kikaga inata aure Amman matanne duka kinga irin yanda suke kasancewa hardanacire son aure araina nabarwa Allah komai idan yazama shine ajalina Allah yagafartamun saigashi kwatsam naga wannan khadijar gabadaya narasa natsuwata"!!!

Tanisa shikenan bari zanyi maka kwatancen shagonsa danbaicika zama agidaba kafara tuntubarsa dazancen kanemi izinin ganinta idan hartaganka kuma tayarda zata aureka komai zaizo cikin saukiii yace shikenan

Tayi masa kwatance shagonsa akasuwa Yakuma sameshi yabashi hannu suka gaisa Ashe shima yasanshi"" Usman nekawai baiwayeshiba""






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 58
By
Gentle Lady💃🏽



Saiya kalleta kamar yayi magana saikuma yakasa itakuwa tana kallace dashi ganin yayi shiru tamike tace dad nikam bari nadan kwanta"" tayi maganar hartasoma tafiya

Yace amm dawo labila magana zamuyi""" tace to tareda juyowa tazauna kasa tana fuskantarshi saikuma yayi shiru

Yacije lebonsa nakasa yanasake jinjina nauyin maganar"" tace yadai daddy??? Yadan nisa yace bakomai tashi kije kikwanta

Murmushi tayi maidan sauti tace dad kadaina boye abunda yake zuciyarka hakan babbar illace atareda zuciyar

Komai nene kasanardani mana zanfuskanceka amatsayina nayarka banason damuwarka kokadan Kaine kawai kasan damuwana yanda zanfadamaka Abu bana iyah sanarda mahaifiyata

Kadaure kasanardani wlh batunyauba nalurah kanacikin damuwa kullum kakirah ni dankasanardani saikuma kafasa

Nifa yarkace menene bazaka fadamunba kaima kasani zanbaka goyon baya Dari bisa Dari idankuma abunda zanbada shawarane saina baka daidai sanina""

Yanisa yana kallonta yace hakane labila Amman gaskiya inajin nauyin fadamaki bukatata dankuwa tanada matukar nauyi.


Tayimun nauyi abakina hakazalika zuciyata takasa daukarta inaganin kamar bankyautaba kuma abun kunyane

Nayi nayi incire abun

Please Login or Register in order to submit comment