Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafito yayi cikin gidan dasauri kaitsaye hawa nahudu yahaye yabude dakinta anan yacikaroda bargonda ta lullube ahankali yakarashi ahancinsa yashaki kamshinta yalumshe ido jiyake tamkar yanzun khadija tayafashi saboda kamshinda yakeyi"" dakin yasoma dubawa yana kwalamata kirah harcikin toilet yagama bade bagarenta danema Amman baigantaba cikin falon Yakoma yarumgume bargon yafashe dakuka

Damadai Usman kuka bayayimasa wuya kamar mace su hajiya suna shigowa basu ganshiba hajiya tace to inakuma yayi lubabatu ce tace yana saman duk tare suka rankaya saman sukasameshi yana kuka

Labila takurah masa ido sannan takalli hajiya tace waimeyake faruwane haryanzu banga sahiba ba??? Meyasa dady yake kuka??? dukkansu takebi dakallo tanayimasu tambayar akarasa Wanda zaibata amsa Usman ne yamike kamar Wanda akatsakurah yayi waje hajiya tanakiransa yace policetetion zaitafi muktar ne yabi bayanshi waje sukasamu su habu suka dunguma zuwa opishin yansanda wajen abokinsa idris yatafi dayake DPO ne bayan sungaisa Usman yasanardashi

Yace wlh yasamu labari Amman sunanan sunayin iyah bakin kokarinsu kuma insha Allah duk inda take za aganta sundade cen anayiwa Usman tambaya tareda ma aikatan gidan Amman usman yace baya zarginsu dantare sukaje sallah

Towama za adorawa laifi haka sukadawo gida jiki sanyaye hajiya tace asanar masallaci domin atashi da addua Allah yabayyanàta duk inda take

Lubcy kam dagekawai take kallonsu saiyanzu labila tasan mekefaruwa taci kuka harma yasake jawomata wani zazzabin kullum cikin addua take Allah yabayyana sahibarta yanzukam Sam batadorawa lubcy wannan aikinba

Kawai tahakikance akan waninedai maijin haushin babanta"" rayuwa kenan Usman cikin sati biyu karkuso kuga yanda yazama kullum yazauna baidawata magana saita khadija saikuma yawan tunaninta
I

Kullum zakasameshi bangarenta yatasa kayanta agaba yana kallo watarana yayita surutu saikuma kasameshi yana kuka"" labila makusan hakan saida lubabatu tayita basu baki tuni muktar Yakoma sannu kan hankali labila taware Usman mahakan yasama mata admission tawuce London dantacigaba da karatunta Usman mayakoma bakin aikinsa!"

Khadija sannu sannu hartasoma sabawa dagidan abunda yake yawan bata mamaki kullum saitaji kamar anayimata motsi acikinta tun lokacinda tacika wata daya agidan takejin hakan

Saikuma yanzun taji motsin ya yawaita gashikuma mararta tasoma tasowa kamardai maiciki yanzun balaifi tanayin hargirki taci kuma dazaran kayan miya sunkare saikawai tasake ganin wasu

Bayan watanni uku alokacin kam khadija tasan cikine da itah tashiga tashin hankali ita dabakowa agidan towaye zai taimaka yakaita asiviti gashi bakowa agidan"" koma adadin watannin cikin batasaniba nidai inakan kirgamata watansu uku wajen yawon shakatawa yanzun tayi hudu anan cikinta Yakama kwata bakwai kenan

Karkuso kuga kirmansa kamar gobema zata haihu danyagirma sosai duk dayake cikin budurwane!"


Usman zaune cikin falonsa suna firah da lubabatu tanacewa yakamata yadauko Abdul majeed yadawo hannunta"! Yakalleta da mamaki yace yanzun kuma kefa kikace bakyason hayaniyar yara

Tarausayar dakai tace toyanzun gidan nan yamun fadi nidaya!! Shiru yayi daga bisanie yace shikenan zanyiwa hajiya magana kometace shikenan"" tace harsaika tambayeta haba usman to indai bazaka daukoshiba kasamamun Yar aiki wacce zanrika ganie kuma tana tayanie aiki


Yace shikenan kamar dayaushe kikeson ta??? Tace umm
Nifa tafiyama zamuyi namanta bansanar dakai ba Usman yakalleta kamar zaiyi magana saikuma yafasa kansa yajingina jikin kujerah yadafe saitin zuciyarsa dayakeyi masa ciwo lubabatu takalleshi tace yadai kociwonne??? Kaiyagyada mata tace sannu yadaga mata hannu alamar yauwa"" tace kai ni wlh ciwon nan naka yasoma isata ayi Abu bayajin maganie

Ya murmusa yana lumshe ido yace baisamu ingantaccen maganinda yadace daciwonba"" tace kamar wanne maganie kenan ai atunanina babu maganinda zai gagaremu siyensa komai tsadarsa

Yayi saurin tarar nunfashinta yace akwai mana ai maganin ciwona khadija ne muddin baxan gantaba ninasan nayi bankwana da lafiya harkarshen rayuwata Nina San sonta shine zaizama ajalina

Ahankali lubabatu taja siririn tsaki wannan abun na Usman yasoma Kaita makurah ko kwanciya sukayi duk ranarda yasamu tabashi hakkinsa babu sunan wacce yake ambata sai khadija

Idan yakwanta kwana saidaifa kowa nagidan yadade kunnuwansa dan sunanta yaketa kiran hargarin Allah yawaye abunda yakekuma bata mamaki Sam Usman yanzu baidamu dayakwanta da itah ba

Dantun bayan batan khadija yanzu tsayin wata hudu Usman saudaya yakwanta da itah koshi ita tajashi dankuwa haka kurum taji tana ra ayinsa ranar taci kuka Sam kashe khadija baiyimata ranaba tunda gashi haryanzu Usman baidaina sontaba

Kuma baimanta da itah ba dukda abunda boka yace Amman kamardai shidin abun baiyimasa aikiba"" Amman su labila kam aiyayi masu""

Mikewa tayi tahaura sama ranta abace Usman kam baidamuba saima yasake mirginawa yasoma tunanin ruhinsa duk da haryanzu yana tunaninta Amman baisan yazaiyiba Sam yakasa tuhumar kowa yabarwa Allah komai"""


Akwana atashi hasarar mai rai cikin khadija yashiga wata Tara komai dakyar takeyiwa kanta"" zaune"" take cikin falo" kamar""daga sama taji muryar Usman yana kwalamata kirah zunbur tamike tasoma waige " jin kiran yayi yawa kawai tafita harabar gidan tunda take bata taba kaiwa harabar gidan ba

Hartasa kafa zata fita tatunoda maganar wannan aljanar jiki bakwari tajuya zatakoma taji yasake kwallah mata kirah batareda shawarar komaiba tasakai tafitaa








Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠




Chapter 99
By
Gentle Lady💃🏽




Tana fitowa sukayi ido hudu da Usman bakinta tadafe tana kuka tana dariya alokaci daya shikuma murmushi yakeyi tace dad Kaine yaushe kazo nan wayafadama ina nan??? Yace haba Deejarh duk inda kike aidole zuciyata tasanardanie

Kizo maza mubar dajin nan mugun dajinie"" batareda shakkar komaiba tatunkaroshi gabanta taji yayanke yafadi saikuma tatsaya chak

Zuciyarta tanacewa wannan ba Usman bane kaitasoma girgizawa tana jadabaya """ cikin sansanyar murya yace menene kuma khadija kizo gareni mana kinkuwasan halinda nakeciki sanadin kewarki

Cikin daga murya tace karyane kaiba dady bane kaiwayee? Meyakawoka wajena "" meyasa kakeson cutardanie""

Jinhakan keda wuya kawai sai aljanie hayyanul zairi yarikida yakoma katon jemage"" mai fika fiki sosai yayi mamakin da khadija ta iyah ganeshi dariya yasoma kyakyatawa wacce tasaka khadija Dade kunnuwanta saboda karar muryarsa dakuma rukukinta yatsaya da dariyarsa yace ke yarinya baki isah kisan koni wayeba abudaya nakeso kisani kafin nashanye maki jini shine nine nan zanzamo ajalinki

Yau ina wacce zata taimakeki kikirata kokuma kikirah Wanda zai ceceki daga hannuna yauba makawa zakikwana lahirah

Aini taimakoma akamun yauzanyi murna bayan kema Ashe harda kari nasamu yau zanmore dajikinku

Khadija tace karyane jinina bazaitaba zama abincinkaba in Allah yayarda yaunice zanga karshenka Allah bazaitaba baka sa a akainaba

Tanagama fadin haka tajuya daniyar komawa cikin gidan kamar walkiya yasha gabanta babban kuskurenda yayi kenan shaf yamanta khadija tanayin azkar dasafe babu wani mahalukin aljaninda ya isah yarabi jikinta batareda yakoneba

Iska yazama tayanda bakaganin komai face iskan yakai hannunsa yadankota alokacin khadija tasomayin addua dakarfi

Hayyanul zairi yarigada yariketa wata wahalalliyar kara yasaki yafada gefe daya hannunsa yasoma dayewa kamar yasaka hannunsa jikin dalma tuni Dan fiffiken dayake gadara dashi yafincike

Hakan baisa ya daddaraba kawai yataso gabadaya yayi mata baran makauniya yasake kwamtsa wata uwar kururuwa cen nesa da ita akayi wurgidashi take dukkan ilahirin jikinsa yasoma cidawuta

Khadija haryanxu batadaina addua ba cen taji iska yana kadawa maidadi ahankali tabude idonta tayi Arba dashi cen yashe bayako motsi wasu hawaye masu zafii suka saukomata mararta taji tafara ciwo

Dakyar ta iyah daga kafa zuwa cikin gidan tanajan kafa tanashiga falo taduke tasoma kuka danciwonda bata tabajin irinshiba""" nantakama murkususu

Haryanzu bakinta baidaina ambaton sunan Allah ba""Allah yabata ikon yin numfashi maikarfi saiga kan danda yafito sallama tajiyo cikin gida duk da bushi bushi takeganie

Wata dattijuwa ce tashigo dasauri takaraso wajen tataimaka mata tajaye yaron saigakuma wata dabuwar nakuda bajimawa tasake suntulo wani Dan wannan tsohuwar tayanke cibi tawanke yaron tahadamata ruwa tayi wanka

Duk wani taimakonda za ayiwa maijego itah tayimata tea tahadamata maikauri tasha takwanta babu jimawa barci yadauketa

Saidai tafarka tana tunanin mafarkinda tayi wai wani aljani yaso kasheta Amman sunyi fada baici nasaraba kuma tahaihu harwata mata tataimaka mata tatuno damaganar aljanin dayake cewa yasamu Karin Jinie

Hannu tasaka tashafo cikinta kwalelen batagama rufe bakiba taji cikinta wayam dasauri tamike daga kangadon tace innalillahi badai shiru tayi saikuma tasoma dariya ganin jarirai guda biyu cikin shigarsu ta alfarma kowannensu hannunsa yana bakinsa yanata tsotsa

Dukawa tayi takuramasu ido kamarsu daya da sahiba kenan Usman sukabiyo murmushi tayi najin dadi kenan ba mafarki tayiba Alhamdulillah

Dayan tafara dauka takurama ido tsirarun hawaye suka sauko sai akan kumatunsa saiyabude idonsa yana kallonta yana lumshe ido kamar yasan dalilin kukanta

Saman gadon takoma takwanta tarungumesu tafashe dakuka kowanne uba zaiyi gurin a Haifa. Masà yaransa gabansa yakallesu yaga kyautarda Allah yayimasa

Tashare hawaye kutaku kaddarar haka tazodashi babanku baisan mada cikin kuba saiyanzu take tuna in tsohuwarda ta tai maketa kowacece

Tana kwance harkusan magrib saiga dattijuwar tadawo tasake hadamata ruwa tayiwa yaran wanka tashiryasu takawomata lafiyayyen abinci yaji kayan yajie saida tagama komai tatafi

Khadija dakanta tayiwa yaran huduba" takirasu da sunayensu hassan da husainie yaran akwai hakurin yunwa danko alama basuyi kukaba saiwashe gari da tsohuwar tadawo ta umurceta data basu nono

Kullum haka takezuwa harsukai sati ranarkuwa tana zaune dasafe tsohuwar tazo bayan tagama shiryasu khadija tace innah matar takalleta da murmushi tace na am"" tace inaso ingodemaki akan taimakonda kikamun

Tayi murmushi tace bakomai yata aiyiwa Kaine"" khadija tace innah wanne gida kike?? Tasake murmusawa tace Niger nake kokintaba zuwa cen ne???


Khadija tace ah ah kafin tasake jehomata tambaya hartafita hakadai sukacigàba dazama damatar hartayi arba in

Tasoma hadamata maganie akwai nasha nawanka dakuma nahayaki cikin sati biyu khadija tagoge tayi haske fatarta sai sheki takeyi

Su hassan sunada wata bakwai sannan dattijuwar nan tayiwa khadija sallama tace itah zatakoma khadija tatambayeta sunanta murmushi tayi tace Hauwa u kafin khadija tayi magana dattijuwar tafita khadija tanata nanata sunanta acikin ranta itakuma wannan aljanace ko mutum???

Amman naga aikinta kamardai irin na mutane sosai khadija tasaba da itah duk da bawai fira takeyi da itah ba Amman tanajin dadin zaman gidan tunda akwai mai tayata zama kuma koda yaran tana rikemata itakuma tayiwa daya wanka sa arta daya basuda kuiya basa kuka yanzun harsun soma tashi tsaye batareda sunrika wani abuba"" khadija idan tana karatun Qur anI saitaji sun natsu kamardai sunsan abunda take karantawa "" bayan watanni biyu datafiyar dattijuwar alokacin su hassan sun iyah tafiya idan kagansu zaka rantse da Allah sun shekara biyu domin jikin girmane dasu gakuma wayo dansun fara magana


Khadija Sam tasaba dazaman kadaicin itah Kadai acikin gidan zaune take cikin falon tazaunarda su hassan tanayimasu karatun qur ani

Sukaji anyi sallama Kusan tare suka kalli kofar danganin maiyin sallamar wannan aljanarce tashigo cikin murmushi dakuma fara a tanasanye cikin lifaya fara tayafa farar alkibba""" khadija bazata taba mantawa da fuskar taba ta amsa sallamarta tatashi dasauri ta isah inda take tarungumeta saikuma tafashe dakuka


Hannu tasaka tana bubbuga bayanta alamar rarrashi cikin kuka tace dan Allah kimiyardani gidan mijina nagaji dazama wajen nan "" tajayeta daga jikinta tariko hannunta suka dawo wajenda su hassan suke tazauna tana kallonsu sannan tayi murmushi tamiyarda kallonta kan khadija tace yagidan ya yaran""" ahanzarce tace qalau muke Dan Allah kifadamun yaushe zaki kaini gida bansan halinda yan uwana sukeba da mijina atakaice inason Yayana suga mahaifinsu

Tanisa tace hakane zaki iyah tambayata nikuma ashirye nake inbaki dukkanin amsoshin tambayarki"" Amman kidaure kiyimun tambaya daya daya domin insamu damar baki amsa gamsasshiya""

Khadija tace meyasa aka kawoni nan??? Aljanar tace ai ina tunanin kinsan wannan amsar Amman zansake tunamaki ankawoki nan ne domin akasheki hasalima banan yaso yakashekiba zaikaiki duniyar aljanune datake kasar Iraqi wajenda babu wani mahalukinda zaije cen yadawo daransa saiwanda Allah yanufa kuma yakeda Karin kwana anan gaba

Lokacinda yaratso tawannan jejin sakamakon Neman tsarinda kikayi ga Allah lokacinda kika farka shiyasa yafado daga sama kuka fado wannan jejin

Khadija tace nandin wacce kasace??? Tace kasar sin"" inajin kintabajin labarinta ko acikin tarihi"" khadija tagyada kai tace tome naimasu sukeson kasheni???

Aljanar tasake gyara zama tace yanadakyau kisan asalin tarihin shugaban wanan aljanin wato *hatsabibin boka*

Khadija tace menene alakar tambayata dakuma wannan bokan ina Neman tsarin Allah daga sharrinsa dashi da shaidanun aljanunsa

Aljanar tasake murmusawa tace tambayarki tanada alaka da labarinsa zaifi kyau kisaurareni kiji ainahin koshi waye daga cikin labarinsa zakisamu amsar tambayarki shiru khadija tayi batace komaiba

Aljanar tasoma kamar haka

Tarihin *hatsabibin boka* mukoma bayà wadansu shekaru Dari biyu baya anyi wani kasurgumin matsafi Wanda aduniyar lokacin babu wani boka mai tsananin tsafi dakuma siddabaru kamar shi sunan wanann bokan haiiiiranu wàsu suñamasa lakabida uban shaidanu👹👹👹






Aisha
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 100
By
Gentle Lady💃🏽



Bashida imani kokadan sannan kuma yashahara" harwadansu matsafan sukanje wajensa yakowaya masu siddabaru da bokanci azamaninsa babu wani wanda zaijadashi yanada aljanu dayawa wadanda sukaimasa hidima yanada yaro daya sunansa kanzaru"" yanakoya masa yanda akeyin tsafi

Lokacinda ciwon ajali Yakamashi"" yatattara dukkanin kayan tsafinsa yabashi amatsayin gado yakara dacemasa karike wannan aikin domin shine kawai abunda zanbarmaka gado

Kowanne da yakanyi tutiya dacewa ubansa yamutu yabarmasa gado kudine gidajene filayene dakuma kaddarori tonikuwa wannan din shine abunda nabarmaka kamardai yanda nima nagaji wannan awajen babana shima yagada awajen babansa danhaka karka kuskura kawatsarda wannan Sana a Dan acikinta aka haifeka

Lokacinda haiiiiiranu yamutu wadansu bokaye da matsafa sunyita murna saboda Ya addabesu gabadaya aljanunsu suna shakkar sa danhaka ba kasafai suke samun aikiba kowa yafiso yaje wajensa sunyi murna sosai da mutuwarsa aganinsu sunhuta zasu sake suci karensu babu babbaka saigashi kanzaru yazo yakere ubansa da mugunta iyah tsafi siddabaru zalunci harsuke ganin karama ubansa dashi

Lokacinda kanzaru yayi nisa yana damawa acikin tsafinsa saiyayi bincike yagano maciji shine zaiyi ajalinsa kuma bazai Dade aduniyaba

Yashiga Neman inda zaisamu matarda zatahaifamasa dan da danbayaso yamutu baibar wanda zaiyi gadonsaba""

Acikin bincikensa yagano wata diyar sarkin yan bori akasar Igbo kiristance sosai tayimasa aljannunsa kawai ya umurta suka daukomasa itah yacigaba da amfani da itah batareda andaura masu aureba

Saida tashekara biyu sannan tasamu ciki tun cikin yana karami yakeyin tsafi wacikin kuma baiyarda matarsa taci nama dafaffeba saidai danyen nama cikinta yana shiga wata tara"" tasoma nakuda"" yana ganin hakan yatsafeta tasandare dakansa yadayeta yafitarda jinjirin dake cikinta yakwashe jinin jikinta sannan yabawa aljanunsa masu cin nama suka cinye gangar jikin

Hikimaryin haka awajensa yanaso Dannasa karyayi tausayi danmuddin yasha nonon uwarsa zaizama maitausayi gawasu

Jininta shiyatsafe yadinga baiwa yaron yanasha amatsayin nono lokacinda yaron yasoma girma yalaka masa suna *hatsabibin boka* aikuwa yaci sunansa dankuwa tunyana danshekara biyar yakanyi wani kalar tsafinda ko ubansa bai iyah shiba alokacin yacika damurna danyasan koda yamutu yabar wanda zaicigaba da daukaka gadon gidansu

Ko ina na kogonsa akwai hadiman aljanu masu kulamasa dankar maciji yashigo tunda yaga maciji shizaisama ajalinsa yasa akashirya masa wani gado maikyau

Kullum zakasameshi akan gadon baya yarda yaje ko ina dangudun haduwa da ajalinsa abunda baisaniba dukkan abunda aka kaddara shine zaiyi ajalinka baka isa ka kaucemasaba

Shiwannan boka abincinsa nonon shanu Wanda aka tatsashi yanxu yanzu kuma baya yarda yasha nonon awani guri kohannun wani aljanie sai hayyanul zairi danshi kawai ya amin dashi watarana ya aiki hayyanul zairi diban madara bayan yadibo yanakan hanyar dajin zaikaimasa toshikuma yanajin yunwa saiyayi katari dawadansu fatake sunsamu hatsari akan hanya saiya yanke shawarar zuwa yasamu jininda zaisha

Yasamu guri yagirke kwaryar nonon yatafi bayan tafiyarsa da sa o i biyar saiga wani maciji yafito raminsa yanajin kishirwa yanaganin kwaryar nono kawai yakafa bakinsa yasha asheyazuba kuma dafinsa aciki

Yayi tafiyarsa hayyanul zairi yana dawowa yadauki nono yakaiwa shugabansa bawani tunani yakafa kai yasha

Bayan shudewar rabin awa saidafin maciji yasimayimasa aiki yanajin yanayinsa yasauya kawai yadauko madubin tsafinsa yasoma bincike yagakomai saninkuma ajalinsa Yakama yakirah *hatsabibin boka* yadamkamasa gadon

Kujerar mulkin bokanci yasake jaddada masa karyayi wasa dashi danshine zaiyi tinkaho kobayan ransa take yasoma shure shure bakinsa yana fitarda kumfa harrai yayi halinsa

Tanisa tana kallon khadija tace daga lokacin *hatsabibin boka* yafara shuka mulkin bokancinsa cikin zalunci dakuma cin amana

Bayajin tausayin kowaye akabashi yayiwa aiki saikuma akasamu mutanen yanzu sunada rauni sosai akan addu a karancin ilimi dakuma rashin tarbiya

Kezan iyah cemaki babu wani aiki daza abawa *hatsabibin boka* ya gagareshi babu wani aikinda yabashi Matsala samadanaki

Tanisa tanamai kallon hassan tace Ku mutane kunada sakaci yawanci sakacinku shine yake jawomaku matsala

Ansanardaku tayanda zakunemi kariyar Allah daga dukkan wani abun cutarda hakan yashafi aljanu da mutane irinsu *hatsabibin boka* dankuwa sharrinsa yakere duk wani sharrin aljani

Yayi nazari dakuma tunani Dan Adam baida tsawon rai kamarmu aljanu Dan adam duk dadewarda zaiyi yayi tsawon rai bazai haura shekara Dari da ashirin ba

Wannan dalilinne yasaka abincikensa yagano wata Yar sarkin aljanu tanahiyar kudancin Nigeria yaturah bakaken aljanunsa suka daukomasa itan

Yanaso yayi amfani da itah yahaifi danda zaigajeshi yazamana jinsin aljani yafi yawa atare dashi danhaka zai Dade aduniya yanashuka tsiyarsa

Itakuma taki aminta dahakan dankuwa musulmace duk da dagabaya takarbi musulunci tayiriko dashi sosai wannan dalilin yasaka yakaita kurkukunsa dayake karkashin kasa yana ganamata azaba harzuwa yanzu baisamu yardartaba

Kuma atsafinsa yagani aladole saida yardarta idanba hakaba bazaisamu danda yakesoba zaisamu yaron jinin bil adama yayi yawa ajikinsa

Yanzun haka tana tsare acikin kurkukunsa karkidauka itah kadaice akwai mutane da aljanu dayawa awajen wadanda yakeganawa azaba idan suka bijiremasa acikinsu harda bokaye babu Wanda yasan mabudan kurkukun saifa shi danbaiyarda dakowaba yakance shiko kansa baiyarda dashiba ballantana yayarda dawanie khadija tanisa tace ni wannan gimsasshen labarin ya isheni babu wani abun dadi acikinsa menene ribata tasauraren labarinsa tundashidin ba wani malamibane baikafa tarihin komaiba saina zalunci tanisa haryanzu banji amsar tambayataba saidai kawai cikamun kunne dakikai dawannan tatsuniyar banzar


Aljanar ta murmusa tace munkusa ai kisake hakurii

Dajinda yake acikin taraba yake Amman yatsafe dajin tayanda kodamutum yatafi bazaiganshiba
Saifa idan wajensa kikaje sannan zakisamu damar shiga
Shikuma dalilinda yasa yatsafe dajinda yake saboda yagano wadansu yara biyu shune zasu zama ajalinsa
Wadan nan yarankuwa sunzo duniya






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 001
By
Gentle Lady💃🏽




Tamurmusa wadan nan yaran bawasu bane face yayanki"" jin hakan yasa khadija tawatsa mata wani mugun kallo tana jansu hassan ajikinta tace wannan aizancen banzane akan wanne dalili zanbar yarana suje wajen wannan azzalumin

Wanda bai maida rayuwar mutane abakin komaiba"" Yarana basa bukatar hada idoma dashi

Aljanar tace khadija kenan kisani tunkafin kizonan nasanda zuwanki wacce *hatsabibin boka* yadauka kanwatace

Khadija tayi saurin Tarar numfashinta tace aiho kicedama dabiyu kika taimakeni ni atunani kinyine saboda Allah Ashe akwai wata mummunar manufa axuciyarki game damu

Tace kisaurareni khadija dazan iyah aikin nan wlh datuni nagama da matsalar khadija tasake wurgamata wani kallon tace saikuma akace dole Yayana suzasuyi??? Dayake sune kawai ubansu baisan dasuba??? Toni inason yayana bazantaba turasu wajen wannan mugunba kudakuke aljanu ma yagagareku saiwadan nan yaran dako abinci basu iyah baiwa kansuba

Aljanar tace khadija kifuskanci maganata wannan abun banikawai yashafaba hardake
Khadija tace nibanda Matsala dashi bansanshiba bansan inda yakeba danhaka kinunamun hanya inkoma gida"" tayi maganar tana mikewa tadauki su hassan

Aljanar tace nibazan hanaki tafiyaba Amman kishirya domin yatura bakaken aljanunsa duk inda wadan nan yaran suke adaukomasa su aka she inadai kinason yaranki nandin shine maboyarsu

Khadija nasan zakice akan Karen bukatata nataimakeki shinkokinsan wannan bokan shine yayi sanadin mutuwar mahaifiyarki Fateema??? !!

Kirjin khadija ne yaharba dasauri tajuyo dahanzari tace waike waye yafadamaki hakan?? inakuma kikasan mahaifiyata???

Tamurmusa gazahiri kuwa dattiijuwar nan wacce takarbar maki haihuwa maisuna Hauwa u to kakarkice"" !!! Dam gaban khadija yasake faduwa haba tadade tana tunanin kamar tasan mai fuskarta ashefa da mamantane suke kama

Dasauri takarasa tazauna kusa da itah murya narawa tace toyanxun ina take Dan Allah "" tadafata karkidamu zakije inda take khadija komai dakike gani kaddararrene kakarki tabison zuciyarta

Ga abunda iyayenta suka zabamata Amman takafe sai kakanki takeso dasukace tazaba kosu koshi saitace tazabeshi tayi wauta mezaihana talallabasu harsu amince

Wannan abun datayi mahaifinta yayita fushi da itah sanadin hakanne kishiyarta taimata magani tabargidan takoma Niger duk da batakoma wajen mahaifintaba saboda furucinda yayimata

Akan komai yabiyo baya kartanemeshi gata yargidan sarauta dankoda takoma babantane akan karagar mulki lokacinda tatafi tatafi daciki wata uku haka tayita rainon cikin hartasauka tahaifi yara biyu Mace danamiji

Tasake maida sunan mahaifiyarki fateema idan kikaganta bazakice kedin nan bace dankuwa babu abunda yarabaku

Namijin kuma Muhammad sunansa duka sunyi aure sun hayyafa Amman basacikin jindadi duk tasanadin abunda mahaiifiyarsu tayi abunkuma saiya shafeki keda kike jikanya"" sumacen din kusan hakane

Ranarda nabar nan naturah hadimina yasamoman cikakken tarihinki shine nasamu kakarki nafadamata hadarin rayuwarda kike ciki dukta dalilin kin biyayyarda tayiwa mahaifinta tayita kuka aranar kuma nasanarda itah mutuwar kakanki dakuma kishiyarta

Aranar namatsa mata saida takoma gidan mahaifinta tasamu yayanta shine sarki bayan tatafi wajen mahaifiyarta tanemi tayafe mata tasanarda itah duk abunda yasamu yayanta gashi haryanason taba jikarta batajiba bata ganiba mamarta takaita wajen mai martaba bashikoda lafiya

Yanaganin Hauwa yasoma hawaye shikanshi yayi wauta baidace danyarsa tayi badaidaiba yayimata wannan horon dama saida yayansa yace baidace aimata hakanba"" yadade abun yana damunsa saidai baisan yazaiyi yanemotaba tunda baisan inda take aureba

Dakyar yatashi zaune yayimata alama tazo cikin Dari Dari takara inda yake taduka saikuma tafashe dakuka tana neman yafiyarsa yace shikam aituni yadade dayafemata

Yace ina maigidanta?? Anan tadanardashi labarinta tunbayan barinta garin dakuma halinda kike ciki yajinjina Kai lallai wannan abun saiyazama izna ga iyaye dasuke nuna isa akan yayansu yanzu kuduba ba itah datai abunba yashafi yayanta harda jikokinta kuskure gudadaya data aikata

Inagamu masuyiwa iyayenmu kallon hadarin kaji kallon gidadawa aimu munwaye"' kallon basu isah ba aini bayaro bane dazasu nunamun Abu maikyau nasan abunda yadace ga rayuwata

Waisu dansunyi lokacinsu ana takuramasu muma saisun takuramana subarmu muci zamaninmu mana"" hmmm yammata samari yawancinku duk haka kuke

Kusani duk abunda kukaiwa iyayenku lallai kukwana dashirin karbar sakamako kukalli abunda Hauwa tayi kuma da abunda yasameta agurinka zakaga kamar abun bakomai bane nankuwa babban laifune.

Tacigaba karkiso kiga yanda ake murna sainunata akeyi gadangi "" satin tadaya agidan mahaifinta yarasu bayan kwana uku mamanta tabi Allah mai iko ashedai darabon zasugana ne

khadija tace Allah yajikansu tace Ameen "" khadija tanisa tana kallonta tace haryanzu magana kike akan dangina haryanzu bakibani amsataba menene dalilinda yasaka wannan bokan yakeson kasheni
..
Tace bashine yakeson kashekiba shima aikine akabashi tatari nunfashinta tace wayabada aikin akasheni??? Bana fada dakoma bantabacin zalin waniba bantaba hayaniya dawaniba to akan wanne daliline za ace akasheni??? Tayi maganar tana kallon aljanar

Murmushi tayi tace bakodaya Amman itah wacce tasadin akasheki tanaganin kintaremata wani jindadin duniya

Khadija tatareda dacewa wacece wannan??? Batareda shakkar komaiba tace kishiyarki lubabatu""

Khadija tace ban...ban.banfahinci mekike fadaba"" aljanar tamurmusa tace nace kishiyarki lubabatu khadija tace never wlh nifa kinsani aduhu wacce lubabatun???

Tace ina tunanin bakisan wata lubabatu bayan Itaba kuma Usman bashida wata Mata ayanzu sai itah akan me kike tantamar anya itane kuwa???

Khadija tace saboda itah ce mahaiifiyar labila kinga kuwa nasan bazata cutardaniba"" aljanar tamurmusa tace ke yarinyace khadija ai lubabatu ba itah tai nakudarkiba dahar zataji tsausayinki barimadai infadamaki bayan batanki tasa akaturawa yarta kuma kawarki aljani yahurah mata iskar barci Na sihiri kwananta biyar tana barci yanzun haka bata kasar anturata karatu kuma duk bacikin hayyacintaba

Gabadaya yan uwanki sunmanta dake kamardai yanda lubabatu tace bokan yayimasu "" nasan bazaki yardaba saboda kinyarda da itah idan zaki iyah tuna kalaman yarta datake maki zakigane hakan domin itah tasan abunda uwarta take aikatawa

Khadija kam bakibude take kallonta"" tace waima kinsan usman yanada da saurayi babba yayan labila ne Amman ba lubabatu tahaifeshiba sunansa kaleed

Bayan lubabatu tasa ankashe mamarsa ameenatu tasa kuma boka yakashe kaleed saidaikuma abunda basu saniba acikin aljanunsa akwai wani maisauran imanie saboda lokacinda ana tsoratarda maman kaleed hardaashi cikin masuyimata gizo suna zama kadangaru







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 002
By
Gentle Lady💃🏽


khadija ce tayi saurin Tatar nunfashinta tace waiikina nufin dadyn labila?? Tace sosai kuwa lokacinda lubabatu takeson miji taje wajensa kuma itah tasakashi akashe matar Usman"" shine yatura aljannu sukarika tsoratata karshe aka sakomata ciwon zuciya tarasu bayan nan kuma tasakecewa akashe kaleed saidai aljaninda yaturah yakasheshi kafin yaje wani dagacikin aljanunsa yayi saurin zuwa yadauke kaleed din tareda kayanshi

Aka idar *hatsabibin boka* kuma duk yabawa aljaninsa aiki kuskure banaka bane kuma rashin aikata aikin zaijamaka mummunan hukunci

Lokacinda yaje gidan baitararda kaleed dinba saikawai yakama bakinshi a zuwan shine yadaukeshi domin bayan yadawo yana taraddadin sanarda *hatsabibin boka* saikawai akabashi kayan aiki saikawai yakarbe kayansa yayi shiru

Takai kwarshen maganar tana kallon khadija"" khadija wacce hawaye sukebin fuskarta"tanisa toke taya kikasan dukkan labarinsa??? Aljanar tamurmusa tace kakana shiyayiwa kakan *hatsabibin boka* aiki lokacinda yamutu sai kakana yatuba dalilin wani malami anturashi jikin wata mata domin yahanata zaman aure

Awajen rakiyyya da malamin yayimasa wa azi saiya tuba Amman bayada hujjar sanarda kakan *hatsabibin boka* haka"" shine yagudu zuwa makka yayita tura mayakan aljanunsa Amman sunkasa samun nasarar shiga inda yake

Please Login or Register in order to submit comment