Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanadaura agogon hannunsa tace ina kwana

Batareda yakalletaba yace lafiya yadauki takardunsa da key din motar sa yafita"" dasauri tabishi tana kiransa kowaigenta baiyiba harsuka sauko kasa

Labila tsaye da itah da majeed sunyi shirin skull cikin uniform
Lubcy tasauko kamar tafadi tace abban majeed Dan Allah katsaya

Afusace yajuyo yace wai lafiya??? Idan natsayà mezanyimaki"" gabanta saida yafadi tadan dake tace bakomai naga zakafita bakayi break ba

Yace nakoshi yasakai yawuce labila""tabishi dasauri zuwa waje tanakiràn sunansa kamar karya tsaya bayaso labila tafuskanci hàlinda yakeciki ya juyo tareda kirkiro da fara a

Takaràso tace dady morning"" yace morning my doter kintashi lafiya tace kalau idanuwanta sunakawo kwallah

Yace menene nakuka labila" yayi maganar yana dago habarta tace dad nagakamar kanacikin damuwa

Dariyar yake yayi yace bakomai banada damuwa maza Kira majeed insaukeku makaranta

Tace dad kabeer fa??? Yadanyi Jim sannan yadago yace bayajin dadi yatafi gida maxa kirashi karku makara

Tace to sannan tajuya cikin gidan yabita dakallo yacije kasan lebonsa""

Lubcy kuwa tunda yafita tayi tsaye sakeda bakiii suwaiba wacce tasauko duk akan kunnentà komai yafaru dasauri takoma saman tanakuka





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




chapter 36
By
Gentle Lady💃🏽


Tana shiga batako kalli wajenda mom dinta takeba tadauko jakarsu tariko hannun majeed sukawuce

Murya asanyaye tace inakuma zakuje baku karyaba"" batareda tajuyoba tace munkoshi tafita abunta driver n dady ne yatukasu yafara kaisa company sanan yabiya yakai labila yakai majeed shima

Lubcy guiwa a sake tahau saman ta takasa tsaye takasa zaune karfa wannan abun yashafeta ranarda aka kawo Amarya aranar tasanarda *hatsabibin boka* bayanin labila da abunda tafada

Yace kwantarda hankalinki nasan mezanyi mata"" cikin saurii tace karfa aimata wani abun nacutarwa yatace

Yamurmusa yace nasanda haka bakomai zanyimata ba zankullemata bakine koda tayi niyar sanarda wani abunda kikeyi zatakasa magana

Kodakuwa akan idonta kikai kisan kai bazata iyah sanarda kowaba tamurmusa yauwa hakan yayi saikuma maganar wannan shegiyar matar wlh boka banason tadade gidan nan

Inatsoron karwani Abu yashiga tsakaninsu kasanshifa dashegiyar lakuwa"" yakece da dariya yace abunda naimasu wlh koda dagashi sai itah ne acikin duniyarsu bazaitaba kusan tartaba

Yace gobe kiduba cikin drower dakike aje madubinki Zanbada wani magani akawomaki dazaran kinji kina ra ayin tabar gidan kizubamata a lemu abunshadai tasha

Toranar zatanemi namiji mukuma zamu turata wajen driver ngidanku Dan tsohon saurayintane idan bakimantaba nafadamaki
.
Tagyada kai dazaran kinji gabanki yafadi to sunacen tare saikiyi yanda zakiyi kifitardashi harkuje dakinsa

Inda za akawo maki maganin zakiga wani Abu cikin kwalba saiki daure bakin kwalbar bayan kin tabbatar tasha maganin daganan komai zaifaru zakigani

Godiya tahauyimasa sannan tamaida madubinta"" watan suwaiba biyu yanzu agidan saitazuba mata maganin kuma takulle bakin kwalbar

Shine dalilin abunda yafaru tadan nisa akwai matsala watakil nayi kurene gashi laifinta yana nema Nina yashafeni gashi dasafe bahalin kiran *hatsabibin boka*

Ranar babuwanda yakarya agidan tana ganin ranatayi takulle bangarenta tadauko akwatin tadauko madubin bayan tagama kiransa saigashi yabayyana tazayyana masa komai

Saida yayi dariyarsa wacce yasaba sannan yace laifinkine keda nacewa kidaure bakin kwalba shine kikadaure tamau kisani zuciyarsace kika kulle babu inda iska zaishiga danhaka kuncine yaketa mamayar zuciyarsa

Bayajin sanyi kokadan wannan dalilinne bazakiji dadinsaba idanma kika matsa hukuncinda zai yankemata yashafeki

Ido tawaro tace nashiga uku to yazanyi yanzu??? Yace abune maisauki kisassauta kamunda kikaimasa shikenan zai sauko

Tasaukarda nannauyan ajiyar zuciya nagode boka ahuta lafiya tana miyarda nadubin tadauko abun ta sassauta daurin tamiyar ta aje saiyanzu taji hankalinta yadan kwanta


Baidawo da ranaba koda dare baidawo dawuriba"" yanashigowa dakinsa yanufa bangarensa yayi wanka yasaka kayan barci yafeshe jikinsa da turare yasauko zuwa dakin lubcy

Kwance takesaman gado abun duniya yashamata kai tunaninta daya karfa reshe yajuyeda mujiya?? Duk da tayarda da boka tasan bazaiyi abunda zai cuyarda itaba

Da sallama yashigo dakin Amman batajishiba saman gadon yahau tabayanta yarungumota yasunbaci wuyanta

Kamshin turarensa tareda sunbatardà yamata sukadawo da itàh duniyar gaske ahankali yaradamata akunne juyo kikalleni

Shiru tayi komotsi batayiba hànñu yasaka yajuyoda itah dakansa
Tasanne kanta kasaa hannu yasaka yatallafo fuskarta yace meyasamu gimbiyata????

shiru taimasa haryanzun take yasoma aikamata dayan sako tuntana share shi hartasoma maidamasa martani

Sundade suna wasa dajunansu saida yasamu yar natsuwa yasake jawota jikinshi

Tadago tana kallonsa idonsà yanarufe kamar maibarci tace baban majeed murya atausashe yace inajinki akwai matsalane???

Tace akan kanwat batagama rufe bakiba yàsà hannu yarufematà bàki yace barci nakeji night

Baisake dago kai yakalletaba yajata jikinsa yacigaba dà barcinsa itama ahakan barcii yadauketà
.
Tundaga ranar baisake haduwa da suwaiba ba itakuma batada aiki saikuka duk tarame saboda tunanin makomarta
.
Girki yanadawo wà hannuñta lubcy tace tashirya susameshi dàkinsa tabashi hakuri dadare lubabatu dakanta tashirya suwaibà

Cikinwàni bugaggen less tanajin dawowarsa tariko hannuntà sukai bangareñshi kirjin suwaiba sàifaduwa yake

Lubabatu cegaba taturah kofar da sallama yàña xaune saman kujeràh yana danna laptop lemune ahannunsa yanasha

.yadago yakallesu kallodàya yamiyada hankalinsà wajen abunda yakegabansa






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Chapter 37
By
Gentle Lady💃🏽



Lubabatu tace barka da hutawa yace yauwa barka batareda ya dagoba"" tadanyi jim sannan tace dama dama wajenka mukazo

Yace inajinki to"" tasake gyara zama tace akan kanwata ne Dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru

Tayi shiru tanajiran taji mezaice yace yakiikeso ayi yanzu??? Saida gabanta yafadi karfa yace ya yafemata saikuma tadake tace kayi hakuri karkayanke mata hukunci mai tsaurii

Sai wannan karon yadago yakallesu suwaiba tunda suka shigo kanta yanakasa saikuka takeyi wani mugun kallo yawatsamata yace munafuka kawai aransa

Yamaida kallonsa wajen lubcy yace wane hukunci zanyimata bayan tazabi abunda yazama daidai arayuwarta

Saiyanzu taimagana cikin kuka tace Dan Allah Alhaji kayi hkuri wlh bahalina bane wannan shairin shaidanne

Baki yatabe yace ban iyah ganewa yace waima menene dalilinda yasaka kika shigomun da itah dakina??? Wlh banason ko kallon fuskarta dazaran naganta raina baci yake

Lubabatu tace nasan ranka zaibaci Amman hakuri zakayi tunda babu abunda yafaru tsakaninsu kadaure kahakurah Dan Allah badan halinmuba

Yace waikina nufin incigaba da zama da itah??? Hmm abunda bazaitaba yiyuwa bane tunda aka kawo yarinyar nan agidan nan ko hannunta bantaba rikawaba

Amman hartayi wayonda zaraje wajen yarona waitabashi kanta tatube agaban wani katon banza suna aikata masha a kuma batsoro aranta batajin tsoron Allah ballantana na mutane tace Dan Allah kayi hakuriii alhaji cikin kuka take maganar

Yamike afusace tashi kibarmun dakina banason sake sakaki acikin adanuwana nayi bakincikin aurenki wlh danasan haka halinki yake tunfarko bazan kai kainaba

Bata tashiba yasake daka mata tsawa wacce tasakata mikewa dasaurii tajuya lubabatu tace meyasa kakehakan nifa nasanka da hakuri

Yajuya mata baya yace banda irin wannan sannan kema ina gargadarki karki sake zuwada itah gurinda nake

Tace wannan bahujja bace to akanme"" yace nasaketa itace kalmarda suwaiba taji aidasauri takara wucewa tana kuka

Jikin lubabatu yayi sanyi batasake cewa komaiba tajuya tafita abunta farinciki fal ranta amman idan kakalleta zakadauka tanada damuwane sosai

kaitsaye bangaren suwaiba tanufa tasamu tanakuka tana hada kayanta "" lubabatu takarasa dasauri tace inakuma zakije suwaiba???

Inazanje bayan inshiga duniya kinsan sarai bazankoma gidan mahaifinaba Dan muddin yaji ansakeni kuma yaji labarin dalilin sakin nawa kashina yabushe

Dan wlh zai iyah kasheni"" lubabatu cikin alamun tausayawa tace toki zauna anan mana"" harkisamu miji saikiyi aurenki

Tagirgiza kai tace Anty duk yarda kikesona dole kibarni natafi saboda gidan nan"" bawajen zamana bane

Lubabatu tace nasani Amman aidarene kibari mana hargari yawaye"" tace bazan kwana agidan nan ba wlh Anty tafiya zanyi

Jakarta tadauka tayi gaba lubabatu tabita dasauri tana kiran sunanta Amman takasa tsayawa hartakai bakin kofa sukaji muryansa

Yace ina zakije??? Tsaye tayi chak! Batareda tajuyowa tace zanshiga duniyane amsarta saima tabashi dariya

Aikuwa yasoma dariya harsuka juyo suna kallonshi cikin mamaki yatsagaita dariyar yace idanma shizakiyi kece kika zabarwa kanki hakan

Amman kafin nan dole kizauna kiyi idda adakinki idan kingama idda daganan komai kika yankewa kanki daidaine dagahaka baice komaiba yajuya dakinsa""

Tsaye tayi itah bata fitaba kuma bata komaba saida lubabatu takarbi Jakarta tamiyarda itah

Tundaga lokacin suwaiba takoma rayuwar daki saidai idan bayanan lubabatu taje suyita firah yawancin abincima taresukeci

Hartayi idda yabata takardar sakinta tareda motarda zatakwashe mata kayanta lubabatu ce tarakata hargida

Tabawa babanta hakurii akan karya daketa dantuni dama yasamu labarii makudan kudii tabaiwa suwaiba sukarabu kowa yana kukan rabuwà saidakuma Innar suwaiba takoma rarrashinsu

Tace aibasu rabuba tunda mutuncine yahadasu saikusan magrib lubabatu taimasu sallama tawuce Dan gidanma taci abincin dare

bayan kwana uku dafaruwan hakan sunayin break dasafe labila tace dady magana nakeso muyi takai karshen maganar tanakallon lubabatu""
Itakuwa saida gabanta yafadi

Yamurmusa to yarlele kyabaridai nagama cin abinci tundayau bafita zanyiba kaitagyada masa"" bayan sunkammalà

Sukadawo cikin falon sannan yacemata inajinki maganar mezakiyi tanisa tace inaso kasa a kaimu gidan hajiya murmushi yayi yace saboda wannan kawai?? tokushirya zanyiwa Sunday magana yakaiku

Tace dady idanfà mukaje badawowa zamuyiba yagyara zamacikin rashin fahimta yace wani Abu mom dinku takemaki Wanda bakyaso???

Tadanyi Jim sannan tagirgiza kanta bakomai dady nidai nafison zama agidan hajiya kabarmu mukomacen islamiyar nan basucika karatu sosaiba cendin zamufi jindadi kuma uncle Hafiz zaikoyamana karatu

Yajinjina maganarta sannan yakalli lubcy yace kinji abunda tace menene ra ayinki???

Tace mefa tunda ita tazabarwa kanta kabarta tatafi duk inda zataje mana Amman tabarmun Dana"" tagallàwa labila harara aikuwa majeed yafasheda kuka yace
wlh dady nidai wujin Anty nakeso "" yace daina kuka zakabita jikin labilà yalake tasoma bubbugar bayansa cikin lallashi

yace tozuwa yaushe zakuje tayi karaf tace harnashirya kayanmu gobe zamutafi yayi murmushi to Allah yakaimu"" hajiya zatayi manyan bakii labila tayi murmushi yace Amman zanyi kewarku tace mumahaka

Washegari sukawuce wannan shine mafarin zaman labila kano





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 38
By
Gentle Lady💃🏽



Acen aka sakata islamiyya dakuma boko rayuwarsu sukeyi cikin jindadi dakwanciyar hankali tabbas tasan mamanta ce tayi sanadin mutuwar auren mahaifinta

Amman batada halin sanarda wani koda tasofadawa dadynta saita kasa fada"" lubabatu tacigaba da zamanta sai yanda taso gida yakoma nata

Saikuma tatsiri yawace yawace kasashe wajen kasuwanci Sam tadaina zama gida babu yanda Usman baiyiba dantadaina taki yace mena rageki dashi mekika nema kikarasa tace bannemi komai narasaba Amman kasuwancin nakeso saboda kawayena duka mazansu sunbarsu suna kasuwancinsu

Dayake babanza akabarshiba duk da yanadan cijewa karshe dole yasaka mata ido wasu lokutan tanagida Amman kawai wasa zaiyi da itah

Aibashiri yasoma azumie domin gojewa fadawa zina watarana dadare bayan sungama abunda yasaba akullum tajuya daniyar yinbarci

Yakira sunanta tadanjuyo tanakallonsa tace yadai??? Nisawa yayi yace waimezaihana muje kasar waje adubaki ni wlh nagaji hakurina yakare ina gudun infada ga hakala

Tace toyazamuyi hakurindai xakacigaba dayi" cikin daga murya yace kullum maganarki kenan hakuridai hakuridai shin hakurin haryanzu yabani abunda nakesone???

Sokike garinyin hakuri infada ga aikata zina??? Wlh ninasan Allah yanakareni dayanzu nadade na afkawa ga aikata alfasha

Dakudina dakomai "" Amman abunda baifi karfinaba yana nema ya gagareni haba
Tace toya kakeso inyimaka inda lafiyata qalau zaka furta hakan to banda lafiya ai

Yayi saurin gwaceta yace naji bakida lafiya Amman Allah dayasaukarda cuta saida yasaukarda maganinta

Koda banida kudi wlh zan iyah yinrance domin samun lafiyarki Amman inadakudin nan bawai banidasuba Amman kinnace dole sai anan kikeso aimaki aiki

Dafarko nayi tunanin kobakyason zuwa wata kasane toyanzu gashi kinazuwa kasuwanci Amman Neman lafiyarkine bazakiba to wlh nagaji kara infadamaki gaskiya nadaina cutarda kaina

Tamarairaice fuska tace abban majeed kayi hakuri tomezai hana kayi aure kodan samun abunda kakeso

Yace wanne irin aure zanyi agaban idonki komai yafaru nayi auren Amman baikareni dakomaiba saitashin hankali""haba wannan wace irin rayuwace

Komawa yayi ya marairaice fuska please lubcy kitaimakeni badan niba dangirman Allah kiyarda aimaki aikin nan

Baki tatabe tace nifakoda anyimun aikin Nan bazandauki lakuwarkaba kullum acebawa yanakanyin abudaya kamar abinci haba

Wani mugun kallo yawatsamata yace nafuskanceki kenan duk abunda kikemun dagayya kikemunshi ko??? Anya lubabatu kinatsoron Allah?? Mijinki yanason abu amman dantsabar mugunta kihanashi abunda kuma yazama halalinsa ranar gobe kiyama mezaki fadawa mahaliccinki

Hannu tadagamasa tace dakata usman shiruna bashine zaibaka lasisin gayamun magana son rankaba "" nihaka Allah yayoni banada jimirin daukar lalurarka danme zakaga laifina tunda banice nayokaina hakanba

Zan iya juran komai amman banadaukar bakar magana"" da mamaki yake kallonta
Baki budee yace umm lallai yaukinfito mun da ainahin halinki dakika koya wajen kawayenki danni bahakan nasankiiba
Kuma
Nagode inhar kudi suna biyawa rai bukata kibani sati daya zanbaki mamaki nidakaina bazansake cewa kije ayimaki aikiba
Kiyita kumuiniya da kayanki indai jikinkine nadaina rabarsa ballantana abunda kike takama dashii

Yatashi daga kan gadon yadaukii kayansa yawuce fuuuu yabarmata dakin"" kallo tabishi dashii ta daura hannu aka tace nashiga ukuna🙆🏿 menene yakeshirin faruwa dani haka""???

Dasauri tadirko daga saman gado tadauki zani tadaura tafito""dakunan dasuke bangarenshi tahau bidaya bayan daya"" kowanne tabuda saitajishi bude

Aranta tace kenan bayanan dasauri tasauko zuwa kasa falon kasa tahango haske ta matakala tasauko kasan

Chak tatsaya sakamakon abunda kunnuwantà sukajiyo mata"" tasake saurarawa kodai karya kunnuwanta sukejiyomata

Yana kwance saman kujerah yadaura kafadaya akan daya alamu sun nuna yanajin dadin firarda yakeyi yalumshe idonsa yace ninedai bawaniba

Daya bangaren akace haba ammandai batan hanya kayi nikuma awa daza a kirani cikin wannan lokacin

Dariya yayi yace aikinwuce komai awajena kingakuwa kinada mukami azuciyata dannakiraki bawani abubane

Tace hakane Amman inakabar uwargidan taka"" bakiyadan mere yace inajin tayi barci nikuma banajin barcii

Tasaukarda ajiyar zuciya tace bakaji yanda najiba lokacinda nagakirankà dannituni nafiddarai dasamunka

Dariya yasakeyi yace togani nasake dawowa tamurmusa najidadi sosai inasu labila??? Yadan shafo kansa yace suna kano

Tace kana nufinwai haryanzu basu dawoba??yace eh yanzu aisunyi shekara acen sukandanzo suganemu tareda hajiya

Tajinjina kai Allah yataimaka yace Ameen





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 39
By
Gentle Lady💃🏽




Shirune yabiyo baya nayan dakiku sannan yakirah sunanta samrat tace na am"" yanisa maganafa nakeso muyidake bata wasaba

Tadan gyara kwanciyarta tace inajinka yace inaso gobe naturo gidanku maganar aure
Baki tarike tace dagaske tareda kalalo ido

Yalumshe ido yabude tamkar tana ganinsa wani nishadine yakeji aransa cen kasan makoshi yace dagaske kuma banaso auren nan yawuce sati daya inafatar dai ashirye kike
.tarausayarda kai sosaima kuwa"" indai katashi " yace wlh sosai natashi inamatukar bukatarki atare dani

Wani mugun dadi taji aranta tace maganina yayi aiki kenan"" dasannu zan mamaye zuciyarka"" yace yanaji kinyi shiru kodai barci kikeji???

Tace barcin lafiya inatare dakai kawai inaganin kamar mafarki nakeyi wainice zaka aurah"" yagyara kwanciyarsa yana fuskantar kasa yace kwarai dama kinsan kamai lokacine yanzun kokacin auren namu yayi bakiji yanda nakejinki arainaba

Lubcy wacce saboda tsabar tsurewa batasan sanda fitsarii yasoma bin kafartaba tunda Usman yasoma soyayya da suwaiba baitaba kiranta awayaba

Haka zakila baitaba furtamata wata Kalmar soyayya ba waisaigashi yautaji da kunnenta yana fadawa wata kalamai masu sanyaya zuciya Wanda rabon dayazauna yana koramata kalamai masu sanyi tun tana amarya

Nikuwa nace kece kiKajawo bakibashi abunda yakesoba taya zaibata lokacinsa wajen fadamaki kalamai bayankuma babu abunda kalaman zasu kareshi dashi

Shin mezaihana ke idan bakyada juriyar daukar lalurarsa kibarsa yayi aure mana yasamu wacce zata daukemasa lalurarsa

Amman kinhanashi kanki sannan kinhanashi aure kenan sokike yaje ya aikata zina bakyajin tsoron cutar zamanine???

Idan ma baikwaso maki cutaba wlh kincutardashi kinkuma zalunceshi saikisan amsarda zaki kare kanki ranar gobe kiyama agàbàñ mahaliççinmu

Dayawa akwai mata masu irin wannan halin musamman matanmu nayanzu inhar bazan baka farincikiba bazan hanaka aureba

Watafa tahanashi hakkinsa idankuma yace zaikara aure tace ba aimata adalciba"" aikoda yayi auren bazaiyi adalciba dan Allah jama a kunga laifinsa??? Wlh konine shi inda nakesamun kulawa nan zanmaida shekata kuma komai tanema zanyimata tunda nima tanabani abunda nakeso

Daga hakan saikuma tafara surutu tace anmaganceshi gashinan yanabin ta kamar bantee

Kullum yana manneda itah kamar jela dasafe bayafita aiki dawuri dadare kuma saiyadawo dawuri Amman bayahaka ranar girkina "" shinwai intambayeki wayajawo hakan??? Kome kikagani kece kikajawo kuma wlh dole kiga banbanciii
Kedakanki kinsan dole asamu banbanciii
Inakirah ga iyayena yayuna abokaina kannena mata muji tsoron Allah musan yanda zamutafida lalurar mazajenmu mukuma ji tsoron Allah musani komai mukayi sai antambayemu yazamanmu na aure gobe kiyama karmu manta da kwancin kabari tsallakar siradii sannan kuma karmu manta gida biyune alahirah akwai wuta akwai aljanna dole kasamu kanka adaya Allah yasamuna cikin tawagar yan aljanna Ameen Allah yasamufi karfin zukatanmu

Gabadaya hankalin lubcy yagama tashi jinyanda Usman yake furtawa wata Kalmar soba itaba wani wawan zagi tafurzar Wanda nikaina bansan ta iyashiba

Dasaurii tayunkura domin komawa aranta tana ayyana bamazata bari wannan tashigo gidan ba"" santsin tayes dakuma sanyin fitsarinda tasaki suka kwasheta tafadii jikake kuuuu

Tasaki wata kara wacce taisanadin dawoda hankalin Usman saman aikuwa dama bakin bene take hakan akafara gangaroda itah kamar kwallon magwaro sai ihu take tana kawowa kasa tabuga kanta dakarfe take tasuma kantaa yasoma fitarda jini daidai kawowar usman wajen

Sam baijiwani damuwa Aransaba kodan tabata masa raine oho"" atsanake yafita yakirah driver dakyar ya iya Kaita mota akawuce da itah hospital

Taji mugun rauni akai akayimatà gyara takuma goce akafa"akasamata Karin ruwa"" washe gari akagyara mata kafar

Usman yasanardà doctor idan dahali suwuce ayimata aiki kasar waje"" yace aikin mene ai matarka batada wata matsala
.
Yadubeshi darashin fahimta yace bakagane menake nufiba kwanaki sunsamu hatsarine akan hanya towajen gyaranne doctor yace tanada kari agabanta shine dalilindà yasaka takasa haihuwa dakanta

Yabata wadansu magani yace tayi amfani dasu kafin aimata aiki" doctor yayi murmushi yace tanada kari agabanta kuma harka kusanceta tasamu ciki???
.
Inhar agabanta yake bazaka iyah kusan tartaba Usman shiru yayi dankansa yadaure"" doctor yalura dahakan yace barinasa akoremaka kokonto

Nanyakirah wata nurse yace takiramasà doctor Asma.u tace to tafità babu jimawa sukadawo tare yayimata bayaniñ komai itama yanda doctor yafada hakan tafada

Yajuya wajen Usman yace kadaijiko"" yasake kallonta yace kije rum 11 kiduba mana saikizo kimana bayani tace okay tareda fita

Doctor yacigaba da rubuce rubucen shi Usman kuwa saisake sake yakeyi aransa yanata jinjina maganar doctor





Aisha✍🏼
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 40
By
Gentle Lady💃🏽


Bayan kamar mintuna talatin tadawo taturo kofar tareda sallama"" Usman yana ganinta yadago kansa"" kujerar kusa dashi taja tazauna

Tanafuskantar doctor Wanda shima ya aje alkalamin hannunsa yana saurarenta tace nadubata batada wata matsala""

Doctor yace shikenan kina iyah tafiya"" tace to tareda mikewa tafita" doctor yanisa yana kallonsa yace dama ninasan babu wannan ajikinta kamanta a hospital din nan tayi haihuwa biyu inda munga wannan matsalar aidatuni mun maganceta

Kodama tanada wannan karin ai a take zamucireshi basai andau wani dogon lokaciba haihuwa dabata iyah yidakanta yadanganta dayanayin jikinta sannan kuma yaranta sunada matukar girma kofar jikinta bazata ishesu fitaba

Idan munga kamar za arasa wani acikinsu shiyasa harmuke mata aiki"" yakai karshen maganar yana kallonsa

Usman yanisa yace nagamsu da bayaninka Amman meyasa doctor yasanardani hakan???

Yace wacce asiviti kenan??? Usman yace abuja"" doctor yanisa yace baxaicemaka hakanba inhar ba ita tace yasanarda kaiba ai itah tanajin yanayi ajikinta koda yafurta zata iyah karyatawa

Usman yadago da alamun damuwa afuskarsa yace meyasato zatamun haka??? Doctor yace to wannan amsar abakinta zakajita kabari idan tasamu sauki kuka koma gida saikaji abakinta akwaidai manufaryin hakan

Yanisa shikenan doctor nagode bari Nayi waya yabashi hannu suka gaisa sannan yafito hajiya yafara Kira yasanarda itah sannan gidansu lubcy din

Ranar hospital din yawuni sai marece su hajiya sukazo labila kinzuwa tayi waisunada harda islamiyya washe gari yangidansu lubabatu sukazo harda kanwar mamanta anan suka barta suka koma

Hajiya kwananta daya takoma washe gari aka kai kudin auren Usman gidansu samira mahaifin abdul tareda abokansa sune suka nema masa auren ko hajiya baisanar mawaba danyasan zatace yabari sai matarsa taji sauki shikuma yanason bata mamakine

Ranar litinin aka kai sadaki akasa bikin sati daya duk da bahakan Usman yasoba Amman sunce sunason yin shirye shiryene

Sai anasaura kwana biyu daurin auren yasanarda hajiya itadai fatan alkhairi kawai tayimasa"" labila dataji labari murna tahauyi harsaida hajiya tabuge ta tace waikinji abunda akafada kiketa faman tikar rawa??

Tace najimana hajiya ba dad ne zaiyi aureba??? To idan banji dadiba mekikeso nayi??? Sainafadawa sahiba muhada faty na musamman
.hajiya takaimata duka taruga tana dariya tace banda shashanci mahaifiyarki tana gadon asiviti harta faty kikeyi??

To naga yanda zakihada Fatyn labila tayi cikin daki tana dariya tace aikuwa zakigani"" tunda lubcy tafarfado tamatsa akaita gida batason zaman asiviti

Doctor yakibata sallama yace takara hakuri hartaji sauki"" saida kanwar mamanta ta rarrasheta akan takara hakuri Usman yanazuwa Amman bainuna mata yasan komaiba saiyayima kamar babu abunda yashiga tsakaninsu
.
Wata zuciya tana rayamata kodai yafasa aurenne watakuma tana karyata hakan dole tanason taga *hatsabibin boka* totaya gata agadon asiviti wazatace yadaukomata madubin

Takaicii yabi yadameta nan take jininta yahau saida akaimata allurar barci dantasamu natsuwa
Washe gari kuwa da azahar akadaura auren samira da Usman akan sadaki dubu Dari hudu lakadan

Ranar samira tamkar tazuba ruwa akasa tasha saboda murna"" wai itace matar Usman" mutumenda yace bazai auretaba hmm gaskiya dolene tagodewa aminiyarta datakaita gun bokanta

Gashi tasamu soyayyarsa acikin ruwan sanyi yanzu dazaran tashiga gidan saikuma tayi yakin fitarda kidahumar matarsa wani murmushin mugunta tasakii

Saina rabaka da itah yazamana bakowacce mace agabanka faceni tasakeyin murmushin jindadi

Da marece motocin kai Amarya suka dauko samrat zuwa gidan Usman ranar ko asibiti baikomaba tunda yaje dasafe
Ranar Usman kam yahuce takaici dankuwa samrat batahanashi kantaba saida yabarshi Dan kanshi koshima yatausaya matane ganin tawahala sosai

Bayan yayi wanka yayi sallah yanamai godiya ga Allah daya sharemasa hawayensa yabashi samrat

Lubabatu tana asiviti batasan wainarda ake toyawaba"" yakanje dasafe kuma yajemata da abinci sambata kawo yayi aurenba Amman tagayanzu kullum cikin fara a yake kamar tatambaya saidaikuma takama bakinta

Kachar tabari takara sati tamatsa dole aka sallameta ta tattara takoma gida ranar kanwar mamanta tatafi

Tunda Usman yafita baidawoba saidare"" lubabatu tana bangarenta kaitsaye bangarensa yanufa yayi wanka sannan yatafi bangaren samrat

Cikin falonta yasameta tachanchade cikin adonta tayi kyau tana ganinshi tamike tatarboshi kiss yamata akumatu yace Amarya Kinsha kamshi

Tayi farida ido tace andawo lafiya"" yace qalau dauko mayafinki muje bangaren maman majeed kidubata tace to tareda wucewa tadauko sannan tafito suka jerah sunayar firarsu ta ma aurata

Tunda lubabatu taji muryan mace gabanta yayanke yafadiii" shine gaba tanabayansa yaturah kofa da sallama lubabatu ta amsa fuskanta tanakan matar da sukashigo tare

Usman ne yanuna mata waje yace tazauna kusa dashi tazauna tareda gaidata Anty inawuni yajiki

Duk daharyanzu lubabatu takasa yarda dagaske usman aure yayi tanakan gadon asiviti tace qalau naji saukii yagidan

Tace Alhamdulillah "" usman ne yace maman majeed ga zainab amaryatace yajuya wajenda zainab take yace zainab ga matata kuma farincikina itace ni nine itah inasonta fiye dakomai banason abunda zaibata mata rai inafatar zakitayani wajen faranta mata rayuwaa

Baki tatabe cikin ranta tace basaika fadamun yanda kakeson matarkàba jinhakan bazaihana inrabakuba

Amman afili murmushi tasaki tace karkadamu zanyima fiyedakai murmushi yayi yace nagode yajuya wajen lubabatu yace ga kanwakinan dan Allah inhar tayi badaidaiba kitsawatarmata kiyita hakuri kuma dukda nibanida matsala ta bangarenki

Tasaki murmushin yake tace karkadamu bazantaba sauyawa ayanda kasanniba fatanadai Kanwata tarikeka amana""" takai karshen maganar tanajifartà dawani kallo nikam nace dàbiyu kenan

Kusa dàkunnenta yaradamatà magana kigodewa kanwarnan taki tanaji dani sosai nasamu abunda nakeso gaban lubcy yabada rass tace nashiga uku😳 ya akài hakan tafaru????gabadaya tashiga tashin hankali Amman dayake yarduniyace saita wayance





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 41
By
Gentle Lady💃🏽



Tace kai Amman naji dadi sosai hakan nakeson ji """ Allah yabarmun Kanwata"" yace ameeen itakuma samrat kunya duk takamata tamkar tanutse agurin

Fuskarta yashafo yace to yamaganar raba kwana tunda yanzu hartayi sati daya"" rausayarda kai tayi tace kaga banada lafiya haryanzu dasaura

Kawai kabari sai nanda satiii biyu kafin nan nawarke kaikuma kaci amarcinka sosai"" wani dadine yakamshi baisan sanda ya makaletaba yasakar mata kyakkyawar sunba abakinta

Wani mugun kishi yaturnuke samrat kamar tasaki kuka"" lubcy talurah dahakan"" cikin ranta tace ke kenan dakika tsinceshi darana tsaka inakuma gani da nayi shekara shabiyar tare dashi"" mekiike tunanin zanjiii

Afili kuwa saita dantureshi " murya kasa kasa yace please kibarni naji dimin jikinki Sam shiya manta yana tareda samrat lubcy ce tace baban majeed Kanwata kaifa takejirah naga alama kamar barci takeji

Sai alokacin hankalinshi yadawo jikinsa wata uwar kunyace takamashi yadan Sosa kai sannan yamike yace mujeko samrat"" mikewa tayi tadan kirkiro murmushi tace Anty saida safe Allah yasauwake

Tace ameeen Amarya nagode saida safe gaba tayi abunta yana bayanta harsuka bude kofa tafita shikuma yadawo dasaurii yasunbaci lubcy abakinta nadan tsayin lokaci sannan yadago yalunshe idonsa yabude fuskarta yashafo yana kallon cikin kwayar idonta kamar mai karantar wani Abu
.
Tace kabarta tsayefa"" murmushi yasaki sannan yace saida

Please Login or Register in order to submit comment