Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zama.

Bayan sun zazzauna suka shiga gaishe da Inna ta amsa musu tana musu faɗan basa son zumunci wai rabon da ta gansu tun da suka je yi mata gaisuwar Malam. Haka sai suka ɗan kare kansu a kan aiyuka ne suka musu yawa.


Bayan shiru ya ɗan gifta Inna tana raya ta inda za ta fara sai kawai ta ji Kamal ya fara gyaran murya ya fara magana.

"Inna dama mun zo ne a kan wata muhimmiyar magana, da su Umar suka same mu da ita, a kan mu zo ko Allah zai sa a sasanta mu shawo kan lamarin" Ya faɗa cikin ladabi yana kallon Inna wanda tun da ya farw magana ta wani yatsina fuska tare da mere baki tana kallonsa dan tun kan ya kai aya ta gama harbo jirginsa ta ƙyaleshi ne kawai ya ƙarasa dan kar ta katse masa hanzari.

"Haka ne Inna ai maganar aure ma bai taso ba, haƙuri za ki yi tunda kin ga yanzu Baba Malam ko cikon shekara ba a masa ba, babu zancen cikon shekara tun da ko wata biyar bai ƙarasa ba, kai koda ma a ce ya yi shekaru goma ne da rasuwa bai kamata a ce kin yi wani auren ba tun da kin riga kin manyanta, bare kuma a ce ko jimawa baki yi da kammala takaba ba wannan sai ya zama abin faɗa a wurin jama'a kuma ko ba komai ko dan ƴaƴanki ai kya janye maganar auren nan" Rabilu ya kai ƙarshen maganar a dai dai lokacin da Maryam ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, amsa mata suka yi ta gaishe da su Rabilun ta nemi wuri ta zauna tana jin wani daɗi a ranta dan ta san dai magana ta ƙare tun da dai Inna ta ga abokan su Abba.

Tun da Rabilu ya ɗora daga inda


Kamal ɗin ya tsaya Inna ta yi tagumi da ɗaya hannunta ɗayan kuma tana riƙe da gutsuren kankanarta da ta riƙe mamaki ma ya hanata magana. Ganin da suka yi ta kifa uban tagumi duk tunaninsu maganar da aka yi ce ta shigeta har sun fara tunanin tsuntsunsu ya kama tarko.




Sai da Rabilu ya kai aya Inna ta ɗauke hannunta daga tagumin da ta yi, ta kai kankanarta ta saka a bakinta har da lunshe ido, sai da ta tauna ta haɗiye abinta ta suɗe yatsunta ta maida kallonta gare su ta ce

"Kamalu, Rabilu, kun gama jawabin naku, in ce dai duk a kan magana ɗaya kuka kwaso ƙafa kuka zo nan?" Kallon kallo aka shiga tsakanin su Baba da su Rabilu ita dai tun da ta jefa ayar tambaya bata sake cewa komai ba.

"Bani amsa mana" Ta faɗa tana ɗan muskuwata a kan kujera.

"Eh Inna" Cewar Rabilu jiki ba ƙwari dan bai ga alamar akwai sauƙi a tattare da Inna ba.

"To duk cikinku babu wanda ya isa ya dakatar da ni, wato su sun kasa shawo kaina shi ne suka je sula taho daku, ku kuma kuka ɗakko ƙafa ya sillen kara, kai kana tura ƙeya kamar gafiya ta so shiga rami" Ta faɗa tana kallon Kamal da ya sunkuyar da kai tsabar ba ar da Inna ta masa.

"Kai kuma ka ɗauki fuska kamar farantin tallar kukar kaɗi, kana ɗaga dogon wuyanka mai kama da mariƙin lema "Unbrella) Tambayar da zan muku uwaku Talatu bayan mutuwar ubanku aure nawa ta ƙara?" Ta faɗa tana tsare su da ido, babu wanda ya tanka mata dan haka sai ta ɗora da cewa

"Tunda ba za ka bani amsa ba, dan na ga ba niyya ango ya kwana da wando, tun da kun ƙi magana kun ƙunshe baki kamar amaryar da bata kai budurci gidan miji ba, bari ni in baku amsar, Talatu bayan mutuwar ubanku sai da ta yi aure-aure, sai da ta ƙara aure uku rigis, fir taƙi zama a gidan mijin da ta aura na farko bayan mutuwar uban naku, taƙi zama ne kuwa dan bashi da kataɓus a wajen gabatar da sunna. Bayan ta fito daga gidansa ta sake sabon aure amma saboda mijin baya gamsheta(Gamsar da ita) Ta fito dan cewa ta yi shi da lagwanin fitila babu banbanci yo cewa fa ta yi abar tasa ce jalele kamar hanjin ɗan tsako. Sai a gidan mijin na uku ne ta zauna har yau tana can dan cewa ta yi zama daram ita da shi mutukaraba takalmin kaza yo ai a can ne ta samu abin da take so me ya hana ku hanata lokacin da take aure-auren ? Shi ne dan rashin ta ido ni kuka zo za ku mini sagegeduwa wato in ƙare a gantale ba aure, na zo a sadaka in koma a alakoro, to wallahi haka ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa dan aurena da Jauro kamar an ɗaura taminjau" Ta faɗa tana binsu su duka da kallo.

"Dan Allah Inna ba dan mu ba" Baba ya faɗa kamar zai yi kuka.

"Kai rufe mini baki, ba waɗannn ka ɗakko ba kana ganin kamar su za su saka ni abin da ban yi niyya ba, to duk cikinku babu wanda ya isa ya tauye mini haƙƙi, ni babu wanda na hana ya ƙara aure a cikin ku ko mata huɗu kuke so babu mai hana ku, amma duk wanda ya ce ni zai hana rawar gaban hantsi, to mu zuba shege ka fasa ɗan halak sai yanka, kuma duk wanda ya ƙara yunƙurin hana ni aure sai na saka ya saki matarsa ya zauna a gauro ya ji idan zama haka ba aure da daɗi" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki kankan ɗaya ta kai bakinta har ruwan na gangarowa daga bakin nata ta saka harshe ta suɗe. Tun da ta yi maganaar sakin matansu sai duk suka shiga taitayinsu, babu wansa ya ƙara magana.

"Ke ma kuma in sak naki mijin ya sake ki sai ki dawo mu zauna a tare" Ta faɗa tana kallon Maryam da gabanta ya buga jin furucin Inna na saki.

Haka sai su Rabilu suka yiwa Inna sallama suka fice sumi-sumi su da su Abba, Maryam kuma bedroom ɗin Inna ta kwanra tana jiran mijinta ya zo ya ɗauketa su tafi, dan sun yi magana ya ce zai zo bayan magriba saboda ta gaji da abubuwan nan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, dan har alla alla take a gama maganar kafin mijin nata ya zo dan bata so ko ɓurɓushin maganar ya tarar a barta da abin kunya. Inna kuwa ko ta kanta bata bi ba dan ta yi alƙawarin babu wanda za ta saurarawa matsawar dai babu wanda zai goyi bayanta.

BAYAN MAGRIBA

Zaune suke a falo su uku Inna tana kan sallaya ta miƙe ƙafafunta tana jan carbi dan tun da ta idar da sallar magariba bata tashi daga wurin ba. Sai Maryam da Amna da suke cin abinci a falon suna hira abinsu, bayan sun kammmala Amna ta kwashe kwanukan ta kai kicin ya cewa Maryam

"Aunty bari in je zan yi karatu"

"To my Amna a yi karatu da yawa, sai yaushe za ki je gidan nawa kuma?"

"Sai dai idan na samu lokaci dan yanzu makarantar boko da islamiya babu hutu amma zan zo"

"To Allah taimaka ya baku sa'a sai kin zo ɗin ina zuba ido" Cewar Maryam tana kallon ƴar wan nata. Fita Amna ta yi wanda hakan ya yi dai dai da shigowar mijin Aunty Maryam ɗin sa sallama cikin ɗan sakin fuska Inna ta amsa masa saboda ta san ko ba komai idan zai tafi yana bata kuɗi sababbi Inna kuwa akwai son sabon kuɗi dan wano lokacin ma sai ta yi ta ajiyarsu kamar wanda za ta rataya a wuya wai bata son kashe sabon kuɗi.



MAMAN AFRAH😍 09030283375


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA


MAMAN AFRAH


FCW

*NI CE DAI NA NISHAƊANTAR DA KU A LITTAFINA ƳAR ZAMAN WANKA YANZU NA DAWO DA ƘARA'IN INNA DELU*

ƳAR ZAMAN WANKA TA TAFI MAI ƘARA'I TA ZO
😂😂😂😂😂😂


Page5⃣➡6⃣

Ƙarasowa ya yi ya zauna Inna tana ta washe baki tare da masa marhabin. Bayan ya gaisheta take tambayarsa ɗan nasa ɗan gidan Maryam ɗin yake sanar da ita ai daga makaranta gidan mahaifiyarsa ya kai shi.

"Yo ke ko ruwa bakya kawo masa ba kika zauna kina wani muzurai tamkar wacce ta yi wa sarki ƙarya sai wani zumu-zumu da baki kike kamar shazumamu ya samu sikari" Cewar Inna da ta lura da ɓacin ran da maryam ɗin ke yi tun shigowar mijin nata ita dai ta san dalilinta na yin hakan. Fuuu ta tashi ruwan ta tafi ta ɗakko masa da ido ya bi ta yana mamakin sauyin da ya gani a tare da ita, a plate ta kawo masa tare da masa sannu da zuwa cikin sakin fuska ya amsa yana ɗaukan ruwan ya tilla ya sha ya mayar da ledar kan plate ɗin da yake pure water ne.


"Wannan matar taka ta koyi mugun hali wallahi"

"Mugun hali kuma Inna?"

"Eh mana kai baka lura da muzuran da take ba tun shigowarka in ba mugun hali ba mene ne, da kuma baƙin ciki ta rasa abokiyar hassadarta sai uwar da ta haifeta ai ko idanunta ka kalla za ka ga sun yi luhu-luhu, to kuka ne ta yi ta garƙamawa kamar dai ranar da ubanta Malam ya bar duniya"

"Subhanallahi mai ya yi zafi Inna" Ya tambaya da mamaki.

"Maza Maryama ki yi ta hararata amma wallahi harararki ba za ta hana ni faɗin abin da ke raina ba" Cewar Inna tana wani gatsina fuska ta maida kallonta kan mijin Maryam ɗin.


Jin haka Maryam ta tashi da sauri ta shige ɗaki dan ta san yunzu Inna za ta fara ɓaran-ɓaramar magana kuma babu mai taka mata birki sai ta kai aya sai dai ta san yau abin kunya ne za ta gama ja mata a wajen mijinta.

"Inna idan laifi ta miki ai sai ki ja mata kunne...

"Yi shiru ɗan nan bakinka alekum, ai ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗa maka komai da komai,dama tun tuni nake jiran zuwanka in yaso ko addu'a ce sai ka taya ni a kan Allah ya mini mafita ya ganar da yaran nan gaskiya gaskiya ce ƙarya kuma ɓata ce" Ta katse shi tana rattabo bayaninta.

"Yarinyar nan Maryama da ƴan uwanta ne suke son yin kisan kai...

"Subhanallahi, kisan kai fa Inna amma dai na tattabara ko?"

"Kai dallah ja can, ana maka maganar mutane kana maganar tsuntsaye, to bari na maka gwari-gwari dan na tuna kisan zuciyoyi ya kamata in ce"

"Inna ban fahimta ba, sai ƙara ɓatar da ni kike, kin ce kisan kai kin ce na zuciya...

"Na gama shiryawa" Cewar Maryam da ta ɗakko jakarta ta fito daga ɗaki dan duk abin da ake faɗa tana jin su.

"To uwa gwadaga babu inda zai je sai na gama faɗa masa abin da ke raina wato shi ne kika ɗakko wata shegiyar jakarki mai kama da zabirar aski, wai kin gama to sai dai ki jira shi ya gama shi ma"

"Haba Inna ki bari mu tafi mana yana da uzuri fa "Ta faɗa tana zunɓura baki tare da komawa ɗaki dan ta ga mijin nata ya saki baki cikin rashin fahimtar takamaiman abin da ke faruwa.

"Uzuro, na ce uzuro, ko uzuri gare shi ba ya ƙi kin nawa uzurin ba ai" Ta faɗa tana hararar Maryam ɗin har ta shige ɗaki.

"Ɗan nan ina kai ka, kana jina, Maryma da Yayunta su ne suke so su daƙushe zuciyoyi guda biyu haka kawai fa dan na ce zan yi aure, saboda son tauye mimi haƙƙi da kuma neman dalili suke so su dakatar dani wai na tsufa, dan na tarasu na sanar musu tunda na kammala takaba in yi aure, ni ma in huta idan da rabon haihuwa ma ba sai a yiwa mai ɗakin naka ƙanwa ko ƙani ba, to fir suka ƙi, yo daɗi ta musu ake lissafani cikin zawarawa bayan ga ƴan matan nan da zawarawa sun rasa mazajen aure amma ni Allah ya bani mijina a hannu amma dan kawai su shiga haƙƙina sai su ce babu maganar aure wai sai dai in zauna in ke sallah da salatin annabi kamar da can ce musu aka yi ba na yi. Ni a ganina ai gwara dai in mutu a ɗakin aurena, in banda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, meye a ido banda ruwa, abu lami ba ɗaci ba, banda ma ɗaukan alhaki ɗanka ya hanaka sunnar ma'aiki, to shi ne na ce ko kai za ka mini WALI (Alwali) Tun da su banga kyan wuri a kunnen jaka ba, sai in baka sadakin ka je ka tara mutane su ɗaura mana aurenmu ni da Jauro, ai dai in an ɗaura cikinsu babu mai sincewa tun da igiyar sakin tana hannu Jauro, shi kwa na san ko duniya za ta taru ko ana ha maza ha mata kai ko da wuƙa aka saka wa Jauro a wuya ba zai sake ni ba gwara ka je a ɗaura dan bana fatan na shiga jerin wanda za su rataye kansu saboda soyayya su mutu a jefa su a wuta ko ya ka gani Sammani meye laifina a nan" Cewar Inna tana kafe sirikin nata da ido, dan shi tun daga lokacin da ta ambaci aure ya saki baki yake kallonta dan har ta gama rattaba bayaninta mai kamar almara leɓɓansa basu haɗu ba suna nan a buɗe, tsabagen mamaki.

"Kai ko kaima mijin ta ce ne, yo ya za a yi in zaunar da kai ina faɗa maka magana sai ka saki baki sharam ya layar mai tafiya kana kallona, ko baka fahimci inda maganar ta dosa bane na maka gwari-gwari"


"Eh Inna haka ne dama ai"

"Sammani anya kuwa cikin hayyacinka kake ko dai ka fara shaye-shaye ne, ya za a yi in taƙarƙare in zabgo maka bayanai rututu sun fi shurin masaƙi amma ka kasa bani gamsashiyar amsar da zan ji sanyi a ratsa zuciyata tare da ƙarfin gwiwar yin aure sunnar ma'aiki, yanzu ba gashi ni kaɗai k tarar a sashena ba da a ce ina da mijin ai tare za ka ganmu kuma sai ka fi ganin kimata idan da mijina saɓanin ina zaune bazawara amma babu wata amsa sai ka ce wai eh Inna haka ne" Ta faɗa tana mere baki tare da maimaita abin da ya faɗa ta hanyar kwaikwayar muryar tasa.

"Ko ɗaya Inna babu abin da nake sha" Ya faɗa a taƙaice dan shi ya ƙosa ya tafi ya daina jin wannan labarin ƙanzon kuregen marar kai da ƙafafu.

"A'a yo ni ai ban ga alamar hakan ba, wannan ai ba shawara bace, ba kuma mafita bace ka bani Allah na tuba wannan magana taka akwai ya babu kakar wajen uba, ina so in ji ka zage kana rattabo bayanai wanda zan ke murmushi ina gyaɗa kai kamar ƙadangare ya ga manja amma sai kawai ka ɓige da eh Inna haka ne, tashi ku je Allah bamu alheri dan na ga kai da matartaka halinku ɗaya bakwa son ƙaruwata tun da kuwa haka ne sai ko ka ga katin gayyata dan aure babu fashi ko ana ha maza ha mata" Ta faɗa tana kauda kai gefe dan kallonsa Sammanin ma ɓata mata rai yake ita duk a tunaninta zai goya mata baya ashe duk kanwar ja ce.

Sammani kamar jira yake ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa, dan shi gabaɗaya yadda kansa ya ɗaure da maganar Innar idan da a ce mahaifiyarsa ce ta zo da wannan maganar ai sai dai ya zauna ya yi ta girka kuka saboda bai san mafita ba a ce mace tsofai-tsofai da ita tana maganar ƙara aure daga mutuwar mijinta.

Haka dai ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyu ya ajiye mata a gabanta ya ce

"Gashi Inna kya sayi goro"

"Ikon Allah yo kai kuma Sammani a yi haka, har da kuɗin goro kamar yadda aka saba ai da ka barshi a haɗu a gaba tunda ga abu nan ya taho kar wahalar ta yi yawa"

"Menene ya taho"

"Yo har ka tambaya ma kai da yanzu na gama baka labarin zan yi aure ai ko dan saboda haɗa gudunmuwa da ka bar na goron a haɗu a gudunmuwar dan ƙura'anin Allah biki zan karɓa babu babbba ba yaro ba ɗa ba siriki...

Kafin ta kai aya Maryam ta fito fuuu tamkar wata kububuwa ta fice saboda takaici.

"To Inna ai duk ba zai gagara ba" Cewar Sammani cikin ɗan jin nauyi.

"Allahu akbar kabiran to ai shikenan Allah nuna mana dama da na ga ba wani lokaci za a ɗauka ba, na fi so a yi kwana kusa tun da har kwana sha huɗu na ƙara a takabar fa, tun da aka yi bakwai ɗin mutuwar Malam na irgi ƙanana duwatsu a ƙwarya yawan kwanakin takabata kullum in ɗauki ƙwaya ɗaya rak in jefar gudun ma kar in yi gaga a wajen irge in je in ƙara wani kwana a kan wanda Allah ya gindaya a yi takabar. Tun daga ranar da duwatsun suka ƙare na san babu takaba a kan nan nawa, sai na fara son na fesar fa maganar da ke guntse a bakina dakyar dai na bari aka yi kwana sha huɗu gudun karnin faɗa su ji ba daɗi amma yanzu da na faɗa sai suka ƙeƙashe ƙasa suka ce a'a hmmm ɗan yau!"Ta faɗa tana damƙe rafar sabbin kuɗinta tana taɓe baki.


Sammani dai bai sake cewa komai ba ya saka kai ya fice.


Da dare Inna ta sanya aka kira mata matan su Abba mamar Amna da Mamar Abubakar, bayan sun zo sun gaisheta cikin girmamawa ta kalle su a shelaƙe ta ce

"Na kirawo ku ne dan in sanar da ku abin da baku sani ba, idan ma ku ne kuke son shiga tsakani na da ƴaƴana to ku sani watan komawarku gidajen iyayenku wato ƙauye ya yi ƙauye za ta ɗauke ku"
Cikin rashin fahimta suke bin Inna da kallo wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana musu kallon ɗai - ɗai

"Inna mai ya yi zafi kuma shi ba wuta ba"

"Kwa santa munafukan banza, wato kuna can ɗakunanku kun ƙule da mazajenku hankula kwance ni ina nan a matsayin mai muku gadi yo Allah na tuba in ba dai dama su Umaru sun so su ja mini raini ba ya za a yi ina zaune da sirikai gida ɗaya amma a ce ina matsayin bazawara ai dole ku raina ni ina bazawara kuna matan aure, shi ne kuma na ce zan yi aure suke neman hana ni, to tunda haka ne kowane ɗan banza zan sanya ya saki tasa matar su ma su zauna a gwauraye idan zaman haka da daɗi"

Tunda ta fara zuba suka saki baki cike da mamaki suke kallonta, dan sai ma yanzu suka fahimci inda maganar tata ta dosa.

"Inna wallahi bamu san da wannan maganar bama babu wanda ya faɗa mana Allah ne shaidarmu, mu ya za a yi mu hana sunnar ma'aiki abin da Allah ya halatta miki duk wanda zai hana ki ai bai so zaman lafiya ba" Suka haɗa baki wajen faɗa cikin girmamawa dan sun san kaɗan daga aikin nata ta sanya a mayar da su ƙauyen ko a a sake su baki ɗaya.

"Allah sarki ƴaƴan nan ku yafe mini wallahi duk zatona da haɗin bakinku"

"Wallahi babu Inna ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne kowace mace za ta so ta mutu a ɗakin mijinta"


"Kai Allah sarki daman an ce mace ita ta san damuwar ƴar uwarta mace, da a ce ku ne na haifa da tuni an ɗaura mini auren ba za ku mini gardama ba amma wannan yarinya Maryama kai kamar kwakwa taƙi fir sai kuka take kamar matar marigayi, amma na san abin da zan yi ku tashi ku tafi Allah muku albarka" Ta faɗa tana share hawayen takaici.

"Amin Inna" Suka haɗa baki waje faɗa suka mata sallama suka tafi, amma a hanya suna ta jajantawa junansu a kan abin da surikar tasu ke shirin yi ko kunya da nauyi bata ji.

Shiru ta yi duk abin duniya ya dame ta ta rasa ta ina za ta ɓullowa al'amarin ƴaƴan nata su amince da buƙatarta. Tana nan zaune ta tashi kamar an tsikareta ta shige cikin ɗaki a gaban mudubi ra tsaya bayan ta cire rigarta ta shiga ƙarewa ƙirjinta kallon ƙwaf.

"Ni dama ban yi ƙarya ba ni ƴar gaskiya ce, shi ya sa na faɗi gaskiyata, ai na ce mashayar ɗa ta saka tun da gashi nan ni ma ina gani ya yi jalele"Ta faɗa tana kama breast ɗin nata ta ɗaga shi har ƙasan sai da ta leƙa duka ta ga ya yamushe ya yi yaba duk ya cukurkuɗe amma haka ta saka hannu tana ɗaga shi sama tana cewa.

"Ai ina ga su nufinsu sai sun gashi a tsaye bai rufta ba(Kwantawa) Sannan ne za su yarda ban tsufa ba amma ban da abin su Umaru ta yaya zan shayar da Sa'adu shekara biyu, in shayar da Umaru haka ma Maryama amma har a yi zaton ganin nono yana tsaye ƙiƙam ai wallahi sun ci ƙarya sun kwana da yunwa amma idan suka bi ta tawa ai gyara babu abinda ya bari duk da dai an ce gyra ba zai yi kamar kari ba. Haka ta ƙara ci ɗaɗɗagawa sai ta saka riga hallaw sai ta cire rigar ta koma gaban mudubin tana sake duba wa ita ala dole bata ga aibin ta ba da har za a ce ta tsufa da aure. Ta cire rigar ya fi sau biyar wani lokacin ma sai ta koma falo ta zauna sai ta dawo ta ƙara cire rigar ta riƙa juyawa tana kallon gefe da gefe.
Har ta zauna zancen zuci ya hanata sakat ta tashi ta shiga ɗaki wani ƙaramin mudubi ta ɗauka ta shiga bayi.

zaninta ta cire tare sa ɗan tofinta ta rataye, tsugunnawa ta yi ta haska ƙasanta ta ƙare masa kallo ta tashi tsaye.

"Ni wallahi ban ga aibun wurin nan a ai dama na faɗa musu yana nan tsut da shi a tsuke amma suka ƙi yarda yanzu a nan ina maganar wani tsufa abu kamar sabo" Ta faɗa tana ƙara komawa ta tsugunna ta ƙara haskawa da mudubin.

"Yo Allah na tuba ni idan na duba ma kamar tantanina yana nan (Tantani wata tsoka ce da take rufe da budurcin mace wannan naman tantanin yana nuni da mace bata taɓa sanin namiji ba)

Haka ta gama dube dubenta ta saka ɗan tofinta da zanin ta fito daga bayin tana ta kumfar bakin an shiga haƙƙinta da aka ce ta tsufa dan ita ta san komanta yana nan zam-zam da ita, balle aka sha gyara abin

Please Login or Register in order to submit comment