Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba a cewa komai.


*WASHE GARI*

Tun da garin Allah ya waye take ta saƙa da warwara tana son ta samu mafita dan dole auren take so a ɗaura mata. Sai da yamma ta fito lokacin babu kowa a waje ta fito tana ta waige-waige kamar marar gaskiya mai gadin ma yana bayi ta sulale ta bar gidan, titi ta tsallaka abinta tana ta saƙa abin da za ta faɗa
idan ta je.

A hanya ta haɗu da wani mai tallar maganin sanyin irin na gargajiyar nan da ake siyarwa a jiƙe a robobi. Tsayar da shi ta yi ta siyi roba biyu ta bashi kuɗinsa a wani gindin maina ta tsaya ta shanye roba guda ɗayar ma ta fara sha ta ji ta ƙoshi ta rufe ta jefe da robar da ta shanye.


"Maganin matan nan ba ya aiki indai da sanyi a jikin mace gwara in fara shan maganin sanyin kafin in yi aike ƙauye a ciro mini saiwoyi fa su sassaƙen ɓaure in dafa tsumi gwara in fara rage hanya da gyara kar abin ya zo dab wuri ya ƙure amma idan na fara sha tun yanzu sai in tsumu abuna Jauro ya ji abin ba dama, dan ina so ya banbance tsakanin aya da tsakuya, ya gane akwai mata akwai muna mata dan babu abinda ba zan iya ba amma wannan matar tasa Kande wataƙila ma bata da ƙwarewa a wajen sunna, tana bar mini masoyi a gantale ai gwara in je in kula da abuna dan na san in ya jini zamzam ɗin nan ba ƙari yo wace mata zai ƙaro kuma ai sai dai ita ma ya bata fara(Takardar saki)" Ta faɗa a ranta tana sakin wata ƴar dariya a fili ta cigaba da tafiya abinta hankali kwance tana riƙe da robar sauran maganin sanyin.


Masallacin juma'a wanda yake unguwar ta nufa duk da ranar ba juma'a bace tana zuwa ta samu mutane daga can gefe zazzaune a bishiyar da samari ke zama suna shan iska, wurinsu ta nufa ta musu sallama suka amsa mata.

"Dan Allah limamin masallacin nan nake nema" Ta faɗa tana kallon matasan da su ma ita suke kallo.

"Gashi can shi ne wanda yake fitowa daga cikin masallacin" Ɗaya daga cikinsu ya bata amsa. Bata sake bi ta kansu ba ta nufi wajen mutumin wanda zai kai Abba a shekaru rike yake da carbi a hannunsa sai ganin Inna ya yi ta nufoshi tana zuwa ta ce

"Gafarta malam wajenka na zo"

"Ikon Allah to sannu iya ina saurarenki"

"Wallahi mijina ne Allah ya masa cikawa, ya rasu yau watanni kusan biyar...

"Allahu akbar kabiran Iya abinci kike buƙata" Ya katse ta,cike da tausayawa duk da bata yi kama da mai jin yunwa ba

"Haba ɗan nan wane irin abinci ana maganar babban abinci, kana maganar shinkafa"


"Babban abinci iya? Wanda bashi da abu duk abinda ya samu ai karɓa yake dan babu wani babban abinci"

Ka bari in mutu ka binne ni mana, aure ne nake so in yi shi ne ƴaƴana suka hana ni, shi ne na ce bari na kawo maka sadakin ka ɗaura mini tunda ba haramun bane" Ta faɗa tana share hawaye tare da saka hannu a aljihun ɗan tofinta ta zaro kuɗi.


"Aure iya"

"Yo aure mana ɗan nan ku ma da kuke malaman kana tantama da maganar auren bare kuma wanda ba malamai ba"

"Ba haka bane Iya"

"To karɓi nan, ka kirawo matasan can na zaune su zo ku haɗu ku ɗaura mana aure, ka mini Wali (Alwali) Su ma a cikinsu wani ya karɓa wa Jauro aurena"

Galala ya saki baki yana kallonta amma sai ya danne mamakinsa ya ce


"Ina angon"

"Yana can ƙauyenmu, yo ai yana so na ba sai yana nan ba duk abinda na zartar daidai ne"

"Iya ki riƙe kuɗinki mu je gidan ƴaƴan naki sai a musu nasiha su barki ki yi auren"

"To ba a ƙi ta mutum ba wai an ce da ɓarawo ya gudu amma ina so ka sani na sha fama da su an kai ruwa rana amma sun ƙi da daɗi"

"Za a yi ƙoƙarin shawo kansu, tun da har abin ya kai ga ki kawo sadaki masallaci a ɗaura miki aure to ai abin ya girmama ba ƙarami bane"


"A yi zancen ma ai dama ba ƙarami bane da girmansa"

Haka suka tafi ta shiga gaba yana binta ashe dai ya san gidan ya yi mamakin ganin gidan Alhaji Umar da Alhaji Sa'adu ne ashe mahaifiyarsu ce mai son yin aure tsofe-tsofe da ita sai ka ce a shirin film.

"Yo ko a film ai wannan ta saduda da wani aure yanzu a yadda take jiki duk yaba duk girma ya kamata kuma ma wai watanni ne da mutuwar mijin" Ya faɗa a ransa yana kallon yadda take tafiya cunkus-cunkus abinta ga wata jarkar da ya rasa ta meye a hannunta daga sun yi ƴar tafiya sai ya ga ta tsaya ta buɗe ta kurɓa ta rufe.

Haka aka sha ɗauki ba daɗi da liman da su Abba da Hajiya Inna suna ta kawo hujjoji ita kuma tana ta sharar hawaye ta dage a kan za ta gudu ta shiga yawon duniya a neme ta a rasa idan ba a ɗaura mata aure da Jauro ba a haka dai suka amince ba dan sun so ba sai dan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ta dage a kan sai a gidan nan za ta zauna ita da Jauron haka suka amince ba dan ransu ya so ba.

Bayan an daidaita da Jauro ya yi matuƙar jin daɗin zaman da za su yi a birnin Kano dan haka ya ce zai siyar da komai nasa dan su dawo nan da zama ko Kande matarsa da ta tada masa hankalin ba zai tafi ya barta ba Inna ta saka an bata inda za ta zauna a cikin gidan.

Dan haka aka tsayar da ranar ɗaurin aure Inna ta saka Shattu aminiyarta ta gayyato mata ƴan ƙauyensu dan su zo su sha bidiri.


MAMAN AFRAH😍


LITATTAFAN MAMAN AFRAH

*RAYUWAR MARYAMU free

*GIDAN MIJINA free

*ƳAN UBANCI free

*ƳAR ƘANWATA paid 300

*SANADIN KISHIYA NE free

*ALAƘAR YARINTA free

*Beelal buk 1 free

*Beelal buk 2 paid 500 cmplt

ƳAR ZAMAN WANKA paid 500 cmplt
AND NOW👇

ƘARA'IN INNA DELU


MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
https://chat.whatsapp.com/C7Bm5rzpp10K96WEUGHPE0


ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

FCW


PROMO! PROMO! PROMO💃💃💃

*ƳAR ZAMAN WANKA COMPLETE 500 NE DAGA YAU 6/9/2023 ZUWA 10/9/2023 ZA KU SAME SHI A KAN 400 MAZA HANZARTA KAR A YI BA KE NISHAƊI ZALLAH😂😂😂*
*IDAN 10 GA WATAN YA WUCE ZAI KOMA YADDA YAKE 500 A TUNTUƁENI A NUMBERTA 09030283375*


MAI ZAMAN WANKA TA TAFI MAI ƘARA'I TA ZO
😂😂😂😂😂

*DAN ALLAH DUK WACCE TAKE CKN GRP 1 KAR TA SHIGA GRP 2 SBD YA CIKA AKA BUƊE WANNAN SBD MUTANE SUNA SON SHIGA*


Page7️⃣➡️8️⃣


Zaune take ita da Lantana a falonta suna ɗan taɓa hira bayan fitar Lantana Inna ta dulmiya kogin tunani. Jim kaɗan ta miƙe kamar an tsikareta, tashi ta yi ta shiga ɗaki ma'ajjiyar kuɗinta ta je ta ɗakko dubu ɗaya da wata ledar viva.

"Gwara dai in ba mai gadin nan ya je ya samo mini dan da zafi-zafi a kan daki dutse kar in zauna wuri ya zo ya ƙure ita mace ƴar gyara ce musamman ma idan aka ce tana da kishiya sai ta tashi tsaye sosai da gyara sannan za ta samu kan miji" Ta faɗa a zuciyarta tana fitowa daga ɓangaren nata ta nufi bakin get. Mai gadi da ke zaune a kan benci yana sauraren rediyo ganin Inna ta tunkaro shi ya ce a ransa.

"To wannan jaru jarabar kuma da mai ta zo ita da bata son zaman lafiya duk ta bi ta addabi mutane tana kaɗe musu hankali da maganar aure magana kamar cin ƙwan makauniya abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kullum abu ɗaya"

"Mai gadilo"
Ya ji ta kira shi da wata murya mai sanyi ba kamar da ba da take masa gadara.

"Na'am Hajiya Inna barka da fitowa"

"Yawwa, na ce dama saƙo zan baka"

"Mai za a siyo miki Inna"

"A'a mai za a ciro dai, wato dama cewa na yi a ina za ka samu bishiyar bagaruwa da ta magarya, ina so ka ciro mini ganyen magarya da bagaruwa da kuma tumfafiya"

Kallonta kawai yake jin furucinta sai ma ya rasa abinda zai ce mata su da suke a unguwar masu hannu da shuni a ina zai samu wannan abubuwan.

"Inna wallahi ban san inda zan samo ba, kuma kin san ni da nake gadi kar fa in fita masu gida su ga laifina...

"Kai dalla dakata! Ina maganar kaya masu muhimmanci kana maganar wasu masu gida in ce dai masu gidan ƙarƙashin ikona suke to ka je dan kanka, kuma ka yi wa arziƙi dundu dan har da naira dubu guda na taho da ita zan baka lada" Ta faɗa tana juyawa sai sababi take ta koma ɓangarenta. Tana zuwa ta ɗauki wayarta ta dokawa wani jikan aminiyarta Shattu ta ce ya haɗa ta da ita.

"Ƙawalliya romon jaɓa" Cewar Inna tana washe baki.

"Amarya, amarya, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Wata dariya Inna ta yi jin an kirata da suna mafi soyuwa a wajenta.


"Ke dai bari ai ina hango yadda amarcina da Jauro zai wakana ai akwai ɗan jijjiɓin kata'i dan wallahi Kande sai ta rufe idanunta in kuwa ta ce ba za ta ƙi ji ta ƙi gani ba, za ta yi gigin hana mu rawar gaban hantsi to aradu riɗin amarci zai sa Jauro ya danƙara mata saki uku" Inna ta faɗa tana dariya. Itama Shattu dariyar ta tuntsure da ita suka shiga tdara yadda komai zai kasance.

"Amini ni fa na kira ki ne in ce ki bayar da bagaruwa himili guda da ganyen magarya cikin ledar viva sai kuma tunfafiya ita ma mai yawa a kawo mini yau ɗin nan zan bada kuɗin motar"

"Ikon Allah Delu mai za ki yi da kayayyakin nan?"

"Oh ke kuwa Shattu kullum kamar kanki a cikin tukunya yake(Rashin wayewa) Ni da nake shirin zama amarya har a tambayi mai zan yi da su to bagaruwar dai dafawa zan ke ina zama a ciki, ganyen magaryar ma in ke dafawa ina shiga kinsan shi ma yana wanke gaban mace yana kuma gyarawa ya matse sannan ya ƙarawa mace ɗumi. Tumfafiyar kwa ruwan jiki zan shafa a nonuwa na dan su yi kuɓul-kuɓul da su kin san gyara yana da daɗi"

Dariya sosai Shattu take yi daga nan ta mata alƙawarin yanzu za ta sa a ciro a aiko mata.

Tun da aka kawo take babbakawa kanta bagaruwa, da ganyen magarya tumfafiya kwa ta shafa ya fi sau shurun masaƙi amma dai tana ganin ƙirjin nata jiya iyau fatar ma ta ƙi sakawa daga yamushewar da ta yi bare a yi zancen tasowarsu amma saboda ta sa a ranta yana mata gyaran har cewa ta yi gani take suna wani ƙalli da sheƙi. Haka ta ringa yin amfani da su har ranar ɗaurin auren.


RANAR ƊAURIN AURE

Zaune take a kan kujera mai mazaunin mutum biyu, sanye take da atamfa ja wacce aka yiwa kwalliyar manyan ganye koraye, riga da zani sai ɗankwalin atamfar da ta tufka uban gwaggwaro irin nasu na tsoffi, hannayenta sanye da awarwaraye ƙafar nan ta sha jan ƙunshi dagwal har wajen ƙwaurinta. Kwalli ta rambaɗa da janbaki kai har ma da jagira ta zana abinta jagirar tamkar wanda aka zana da muciya gashi ya haɗu da yamutsatstsiyar fuska. Shattu aminiyarta ce a kusa da ita, ita ma irin kayan Inna Delun ne a jikinta sai washe baki suke kamar wanda ka yiwa albishir da tafiya aikin hajj bana.

Mata ne cike a ɗakin ƴan ƙauyukan su, suna zazzaune a falon suna ta cin abinci wasu tuwon shinkafa da taushe sai rangaɗa hira suke ana yi ana suɗe hannu, da alama ma dai akwai abin da ke faruwa na fari ciki.

"Wai ni Shattu har yanzu auren nan bai ɗauru ba, tun daɗewa aka tafi amma har zuwa yanzu ban ga ana shigowa da goro da alawa ba bare in tabbatar da zamana matar Jauro, karfa a yi mini sakiyar da ba ruwa, dan wallahi kwarankwatsa dubu matuƙar su Sa'adu rufata suka yi ba ɗaurin aure aka tafi ba, to a yau ɗin nan ba sai gobe ba zan ɗagawa kowannensu nono, tsinuwa kwa sai na tabbatar sun gama tsinuwa zan daina ja musu ita, ace na tara jama'a dan taya ni murna amma an shanya mu kamar wasu kaya a igiyar shanya"Inna Delu ta faɗa cikin raɗa dan kar mutane su fuskanci me ke faruwa, jikinta babu ƙwari dan duk ta gama sarewa daga samun cikar burinta.

"Haba Delu me yasa kike da gajen haƙuri ne? Ai duk gaggawar asara ta jira samu ko, sai ki bari ki ga gudun ruwan yaran nan amma ba wai kike ikirarin ɗaiɗaita musu rayuwa ba ta hanyar ambata musu tsinuwa bayan kin tursasa musu su aurar da ke, ai duk lalacewar naka nake ne, kuma naka sai naka daɗin zama sai bare, sannan ma ba da ni ba gaɗa a hurumi, in goyi bayanki da tsinewa ƴaƴan cikin ki yo Allah na tuba kika tsinewa su Umaru ina muka kama kuma" Cewar Shattu cikin ƙarfin hali dan ita ma gabaɗaya ta sare da ɗaurin auren aminiyar tata.

"Haba Shattu bakya tausayina yanzu a ce shekarata 70 amma sai yanzu zan yi auren soyayya, amma ina shirin rasa maƙwallaton zuciyata kuma marurun raina Jauro kina wata magana, na lura yaran nan kishin mataccen ubansu suke" Cewar Inna tana fakar idanun ƴan ɗakin ta share hawayen da ya taru a idanunta

"Ki dauri ki jure Delu, dan rabon kwaɗo ba ya hawa sama kuma duk nisan dare ai gari zai waye, in har kuna da rabon aure to za a ɗaura in kuma babu to sai...

"Bakin ki ya sari ɗanyen kashi Shattu, ai rabon aure ma kamar an yi an gama...


"Aure ya ɗauru, tsakanin Aisha (Delu) Tare da Jabiru (Jauro) A kan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba" Maganar da wani maroƙi da ya shiga faɗa a lasifika


"An ɗaura, an ɗaura na zama matar Jauro Allah na gode ma" Cewar Inna Delu da ta tashi tsaye ta fara taka rawa tana waƙa, ita ma Shattun tsaye ta tashi suka shiga taka rawar a tare gabaɗaya falon ya karaɗe da guɗa kowa ƙoƙarin tofa albarkacin bakinsa yake na guɗar dan duk ɗakin kowa ya san cewa Delu tana mutuwer son Jauro haka shi ma yana ƙaunarta.

Shattu ce ta ɗakko ƴar pos ɗinta ta buɗe ta ɗakko ƴan biyar-biyar sabbi dal ta shiga liƙawa aminiyar tata tana yi tana cewa

"Alƙawari ya cika amarya, alƙawari ya cika amarya, in angonki ya shigo amarya ki yi masa fifita, amarya ki bashi ruwa ya sha, amarya alƙawari ya cika amarya" Tana yi tana mata liƙi ita kuma Imma Delu sai rawa take tana juyi, gabaɗaya matan falo ma tashi suka yi, suka haɗu da Inna ana ta rawa ana ranbaɗa guɗa ko hannu basu wanke ba da suke cin abinci.



Inna! Inna!! Inna!!!" Cewar Abubakar cikin ɗaga murya rai a ɓace yana wani muzurai da cin magani sai wani harare-harare yake yana musu kallon ɗaya saura kwata. Cikin kiɗima Inna da Shattu kai har ma da ƴan ɗakin da ke ife-ife da guɗa suka dakata kowa ya maida hanklinsa kan Abubakar ɗin da ya shigo kamar an koro shi.

"Habubakar kar dai ka ce mini maroƙin nan ƙarya yake ba a ɗaura ba ya karaɗe gida da sanarwa? Idan kuwa har ƙarya yake to wallahi sai na ɗaureshi daga shi har danginsa har sai igiya ta yi saura, a kan ɗaga mini hankali da ya yi" Cewar Inna cikin tashin hankali, burinta kawai Abubakar ɗin ya bata amsa bata ma lura da manyan ledojin hannunsa.

"Oho miki, gashi in ji Abba" Ya faɗa yana dangwarar mata ƙatuwar ledar goro, alewa, da kuma dibono wacce Abba (Sa'adu) Ya bashi ya kawo mata saboda ta ce matsawar ba a sayi goro da alewa da dabino an raba a wurin ɗaurin aure ba sai ran kowa ya ɓaci.

Juyawar da Abubakar zai yi aikuwa Inna taku ɗaya biyu ta yi fisgoshi, ji kake ƙiii ta maido dashi baya ta hanyar riƙo wuyan rigar jikinsa, sai da ta kawo shi gabanta sannan ta damƙe wuyan rigar da hannu ɗaya, ɗaya hannun ta dunƙule ta dage ƙarfinta na tuwo ta duma masa dundu a baya sai da ta masa dundu kifi uku sannan ta ce


"Ko ubanka Sa'adu ya yi kaɗan ya yiwa goron ɗaurin aurena da Jauro wannan dangwararwar yo Allah na tuba ba gwara ka ce Inna kwanta a ƙasa ba idan na kwanta ka fisgi ƙafata riiii har sai ka dangana ni da ƙofar gida, ai sai ya fi mini sauƙi a kan yadda na ji da ka yiwa goro da alewar ɗaurin aurenmu da Jauro riƙon sakainar kashi tare da dangwarar da su kamar an maka dole" Ta faɗa tana sakin rigarsa da ta riƙe wanda wurin gabaɗaya ya cukurkuɗe kamar an fito da rigar daga bakin kura.

Wani takaici ne ya rufe Abubakar ganin abin da kakarsa mahaifiyar ubansa ta masa a cikin mutane, dama ransa a matuƙar ɓace yake na auren da ta yi, dan abin kunya tsofe-tsofe da ita duk ta yi yaba amma wai za ta yi auren ƘARA'I. Wani irin kumburo baki ya yi yana wani huhhura hanci ya juya yana wani fisfisga ya fice daga falon.


"Au ko da na ji, she dai an ɗaura wallahi har gabana ya faɗi" Cewar Shattu tana buɗa ledojin.

"Rabu dashi ɗan kan uwa, an ɗauremu ni da Jauro, mugun hali ne irin na uwarsa, baƙinciki suke da auren sun fi so na zo mutuwa ana cewa matar marigayi ce haka kawai ai gwara a ce ka mutu da mijinka duk da ba a san gawar fari ba" Ta faɗa suna ɗaukar ledojin shiga rabawa mutanen da suke falon, dan dama duk daga ƙauyensu suke Shattu ta gayyato mata su, haka suka shiga rabawa mutane bakin Inna dan dama duk tsofaffi ne bakin Inna har kunne yau dai burinta ya cika, ɗaki ta shiga ta ɗakko wata shadda ƴar ubansu ta saka ta cakara ɗaurin ɗankwali har ta yi gwaggwaro ta koma ta ware ta ɗauki wani kofi a cikin ɗakin ɗan ƙarami da shi ta ɗora a tsakiyar kan nata tare da ɗaura ɗankwalin a kan kofin mudubi ta kalla aikuwa ɗaurin ya mata yadda take so.

"Ai gwara dai yau ɗaya in yi ƘARA'I in yi ɗaurin ɗankwali irin na yaran ƙauyenmu da suke wanda ake cewa a cuci maza"Cewar Inna tana dubawa ta ga ya yi kamar yadda yaran ke yi. Ƙaramar lokar mudubin ɗakin ta janyo ta ɗakko fanfas na yara guda biyu, jimƙe ɗaya ta yi ta ɗaga bireziyarta ta saka fanfas ɗaya a ƙasan nonon nata sai ta maida nonon ya zamana shi ne a akan fanfas ɗin ɗayan ma haka ta masa tun da ta zubawa jikinta da fuskarta ido a mudubi take ta faman doka murmushi, walwala ta kasa barin fuskarta.

"Taɓ lallai na yi maida tsohuwa yarinya ni Delu ai za mu kwashi ƙara'i ta faɗa tana washe bakinta har haƙorin makkarta ya bayyana.

Hanyar fitowa daga ɗakin ta yi domin ta san yanzu Jauro yana dab da zuwa, tana fitowa hakan ya yi dai dai da wata uwar guɗa da Shattu ƙawarta ta carara ba komai ya kawo guɗar ba kuwa sai shigowar Jauro falon shi da abokinsa Mati. Tunda ya shigo yake wuwulga ido ya ga ta inda zai ga Delunsa.

"Shattu ina amaryar take?" Ya faɗa yana washe bakinsa.

"Baka gane ni ba" Cewar Inna Delu tana wani farrr da ido ita ala dole amarya.


"De, De,Delu" Ya faɗa idanunsa a waje baki sake yana nuna ta da yatsansa. Kowa ma na falon maida kallonsa ya yi kan Inna Delu ganin ɗaurin ɗankwali mai acuci gashi fanfas ɗin da ta saka ya ɗago da nonon nata sai suka hayo ƙirji hakan ya sanya ta zama kamar yarinyar mace dan sosai fandas ɗin ya yi ɗoɗar a cikin shaddar.
"Wallahi Delu kin fiye mini Kande sau miliyan" Cewar Jauro yana kallonta baki sake.

"Ai baka haɗa bama Jauro" Cewar Mati yana ƙarewa Inna Delu kallo a ransa yana rayawa ina ma a ce shi ne ya yi wannan dacen tsuntsu daga sama gashasshshe, dan ya matuƙar so a ce shi ne musamman ma da ya ji wai a binnin a wannan ƙerarran gidan Jauron zai zauna da Delun dan ɗaurewa ƙarya tsantsa ma har da ɓangaren da zai saka matarsa Kande dan Kanden ta tada badaƙala cewar ba zai tafi binni ya barta a ƙauye ba ita kuma Inna da yake so take yi tana ganin mijinta kullum sai ta saka aka gyarawa Kande wani ɗaki ciki ɗaya daga can gefe yake.Ita kuma Kanden saboda son zaman binni take gani ba za ta yi saki na dafe ba gwara dai ta zo ko a akurkin kaji ne ta zauna.

"Kai jama'a wallahi na tsinci dami a kala" Ya faɗa yana shafo farin gashin gemunsa.

"Ai yau sai ka biya mu kwalliyar nan Jauro ango" Cewar Shattu tana washe bakinta wanda ta tauna goro.

Baki ya washe ya ce


"Ai in kin ji biya ma ɗaya kenan, kar ki samu damuwa aminiyar amarya sha kuruminki, kwantar da hankalinki kamar kin kashe ɗan mutum, ko kamar tsumma a randa" Ya faɗa har lokacin idanunsa a kan amaryarsa. Nan aka shiga gaisawa da mutanen ƙauye da suka zo domin ɗaurin aure, da la'asar suka koma garinsu dan Inna ta ce sai nan da sati guda za su zo shagalin biki dan yanzu aure kawai aka ɗaura dan hankalinta da na Jauro ya kwanta.

Da daddare bayan sallar isha'i Inna ta aika aka kirawo mata Abba Sa'adu da Baba Umar a kan tana son magana da su, cikin bin umarninta suka taho a tare da sallama suka shiga lokacin ta ɗaga waya za ta kara a kunne, sai da ta amsa sallamar tasu ta musu izinin shiga sannan ta kara wayar a kunne

"Alo Jaurona ango" Ta faɗa tana wani murmushi tare da kashe murya kamar wata ƙaramar budurwa.

Daga ɗaya ɓangaren Jauro ya ce

"Amarya, amarya, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Cewar Jauro yana waya dariya da sautin dariya ya karaɗe kunnuwan Abba da Baba, da yake bolum ɗin wayar a ƙure yake ana iya jiyo maganar tasa.

"Angona kenan bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ina ƙaunarka Jaurona"

"Ai kin zama mallakina yanzu Deluwa maƙwallaton zuciyata"

Gabaɗaya Abba da Baba kai kawai suka sunkuyar saboda tsabar kunyar da ta ziyarce su a ce uwarsu mahaifiyarsu ta yi sabon aure yau kuma tana wayar soyayya har da kalamai kamar wata farin shiga, ƙaramar yarinya ko nauyinsu bata ji.


"Ka zo ɓangarena za a yi magana kan shagalin bikinmu" Ta faɗa tana ƙara kashe muryarta har da wani lanƙwasa muryar kamar wani lauje.

"Yanzu kuwa" Ya faɗa yana kashe wayar ya taso zai taho.

Ajiye wayar ta yi har lokacin murmushi bai bar yamutsatstsiyar fuskarta wacce tun tuni tsufa ya yiwa kamun kazar kuku. Dakyar ta iya dakayar da murmushin, ta kalli ɗiyan nata ta ce bari Baban naku ya ƙaraso dan na fi so a yi maganar shagulgulan bikin namu a gabansa ko yana da wani tsare-tsaren shi ma"

Baki sake ƴaƴan nata suke kallonta fuskarsu fal mamaki.

"Umaru, Sa'adu wai ko bakwa son albarkar iyaye ne, ya ina maganar abin da zai saka ni farinciki kuna wani kauce

Please Login or Register in order to submit comment