Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take aiki sai kwancen Kaya kala biyar.
Duk da cewa girman mu Daya da karamar kanwar tawa sai tabani kala biyu a cikin Kayan,muka gyara dakin baba muka koma.
Dama abinci nace muku andade da ciremu a cikin 'yan gida.

Rayuwa muke mai cike da nishadi,Ina manta Ina da damuwa sai na je gidan aikina,mahaifiyar mu Bata damu dajin matsalolinmu ba,a haka nafara al'ada Wanda da temakon Yaya kaltume nasan komai,ita takasance mana tamkar uwa,ita ke mana nasiha danuna mana tsoron Allah, barimma ni Dana fara wannan Jan motar,tafi jamun kunne saboda gidan danike aiki suma 'yayan Allah shirya ne,mazan duk suna neman mata.

A kwana a tashi muka dauki shekara da fara aiki Babu karatun Arabic ta bangarena balle na boko,itako dijeee gabadaya tana xuwa makarantun,ta cika tazama big girl Bata da matsala wajen uwar daki da mijinta,sun dauketa tamkar 'ya! Da yake Basu taba haihuwa ba.

A hankali tafara koyamun karatu daga bokon har islamiyar.
Hmmmmm da mahaifiyar mu a raye gwanda Babu ita,domin mun koma kamar abokan gabarta,gashi bamusan dangin mahaifiyar mu,ita kanta tsintar ta akayi,mahaifiyar babam mu.

Wata rana haka na tashi da ciwon ciki Wanda yahanani zuwa wajen aiki,Kuma idan banje ba Koro na za'ayi Bayan Ina samu Ina rufawa kaina asiri nida kanwata.

Dijee na roka Wanda takoma amfani da khadeeja Aliyu,Akan tajemun gidan aiki a makofin ni

A take anan Fauzi da fashe da kuka Wanda yasa Shakeerah da khadee Suma kukan,ta cigaba da cewa"da nasan abinda zai faru da khadee kenan wallahi da ban turata gidan aiki ba.
Domin kuwa Daya daga cikin yaran Hon Ahmad yayimata fyade na wulakanci da tozarci,Wanda tunda ya haike mata sai da Allah yayi mata rasuwa.


Dalilin haka Inna ta tasake tsanata sannan Tace nabar gidan ta.
Kada kumanta a kasar nan mai hali shine Mai gaskiya,don haka kirir-kiri akaki hukunta yaron Hon Ahmad,sannan sukace karyane take tsintar ta sukayi,Bayan masu aikin gidan da masu gadi sun sheda haka.

Inna kuwa korar cin Kare tayimun Wanda zaka rantse ba ita ta tsuguna ta haifeni ba,Yaya kaltume na kuka Ina kuka mukarabu,sai dai takara jadadda mun duk inda zanje a fadin duniyar Nan nakula da kaina da rayuwata sannan kada na manta da mahaifata,nayimata alkawarin haka mukarabu.

Rasa inda xan nufa nayi,daga karshe nayanke hukuncin nufar inda khadeeja ke aiki,matar Cike da mutumci ta tarbeni tana tambayar Ina khadeeja?

Anan nake sanarda ita da mijinta abinda yafaru.
Tayi kuka sosai,saboda sunji mutuwar khadeeja.

Daganan rayuwata ta koma hannun Daddy Alhj Kamal da mama hjy rahama,tunda ga wannan ranar ban sake komawa takan gidammu ba,daga karshema garin fantami muka koma da maza.
Sai dai na dauki alkawarin daukar fansan abinda akayiwa dijee Ina Mata addu'ah ita da baba.

To wannan shine labarina.


Gaba daya ajiyan zuciya suka sauke,itako khadee Banda kuka Babu abinda takeyi.
Shakeerah cikin bacin rai da kunar zuciya tace"tabbas dole mu dauki fansa a rayuwar mu,Amma meyasa Kika CE kinada matsalar matar uba?
Fauzi tace"gud question daimond lady dama nasan a halinki sai kimmun tambayar Nan,to abinda yasa da naso boye Miki asalina ne,Amma Dana fahimci mu din hadin Alla NE sai na bayyana Miki komai.

Shakeerah tace"Kai duniya Ina Zaki damu?wannan kalubale da muke fuskanta a rayuwarmu,diamond ladies so nake mu dauki fansa Wanda tunda ake ko a tarihi ba'a taba jinsa sai dai dole ya Zama na da temakon wani namiji.

Shiru sukayi gabadaya ko wacce tana thinking...... Shakeerah tace"yauwa khadee kince brother naki barrister ne,ya kamata ace mun fara hada kai dashi tunda babban lawyer ne ko ya kuka ganin babe's?

Cikin Sauri sukace gsky ne hakane.
Shiru sukayi gaba dayan su ko wacce da abinda ke damunta.
Shakeerah tace"ya kamata mu kwanta saboda school gobe da wuri zamu Shiga idan mundawo munci abinci sai na Baku nawa labarin.

Amsawa sukayi da to kowacce ta shige bedroom dinta don bacci.

Asuba tagari diamond ladies.


Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )




Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciyar⬇️

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_


*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_


*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*



Bismillahir-rahmanir-raheem.


*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai....*


Page:1️⃣3️⃣--1️⃣4️⃣🖊️




_________Kijina ne yaketa aikin lugude da faduwa tashin hankali ya bayyana a fuskata nace"A'ah Abba karabu dasu Sunaso ayi kure ne Kuma ni banaso na fallasa abin kunyar da yayi namai haka.
Abba yace"koma menene sai anje islamiyar.

La'asar nayi Abba yatasa keyata har office din headmaster sannan aka Kira mal shafi'u,Nan kuwa ta zayyane duk abinda yafaru.
Cikin bacin Rai Abba yace katanan ku zaneta,ko Kuma ni nazaneta da kaina,kukan munafurci na saka Ina fadin wallahi shegemaster ba haka akayi ba(Wai headmaster ne shegemaster) gabadaya saura rena akayi nayi nawa bayanin,nafara da cewa"tunda nashigo islamiyar yake mun maganar 'yan iska Yana cewa yasan mu talakawa ne nazo yayi iskanci Dani zai bani kudi,kullum-kullum haka yake fada da yaga naki yarda ne shine ya tsaneni yayi ta zanana,abin duka da bana duka ba yadau jibgata,shine ranan yatareni a lungun oske Wai zaiyyi iska*ci Dani nikuma na masa haka.
Gabadaya Office din salati Akasa,shikuwa mal shafi'u Banda zufa Babu abinda yake alamun rashin gaskiya, shegemaster yace Ashe Mal shafi'u baka bar wannan banzar halin naka ba?to ni bazan iya ba wallahi wannan Karan Dole kabar islamiyar nan kada ka lalata yara azo ana kuka dani.
Malamai kowa yace gaskiya kam kada wani Abu yafaru ayi kuka da makarantarmu,hakuri Mal shafi'u ke badawa,Ina nan kuwa akabashi red card,Ni kaina sai da yabani tausayi,but a zahiri hakinsa kenan sai dai ni baimun ba,kawai nema ma kaina mafita nayi.

Nan naciga da zuwa islamiya, Aunty Saudah ma tadawo,yanzu tadena zuwa talla ni ke zuwa Ni kadai,wata Rana nayi sha'awar shiga kasuwan tudun Wada don Kai tallah,wata matace na hango tsohuwa da ita tana tafe tana dingisa kafa daka ganta bata cikin wahala sai dai daga gani rigimammiya ce,wani ne ya taho da Sauri ya bangaje ta,Aiko tsohuwar nan ta baje a kasa,babu Wanda yamasa magana nan kuwa yafara magana Yana karkata mouth alamu dai Dan daba ne ku tsofaffin nan 'yan iska ne taya Zaki shigo kasuwar mu wallahi kinci darajar ke tsohuwa ce da nayi Miki bakin aiki,cikin tsiwa na taho na dagata ina cewa sannu kaka,amsawa tayi tanamun godiya.
Zagina yafara Yana cewa Ni ajawon inace don uwata?banza na masa ganin hakan yasa yajiyo gabana ya dauke ni da mari dafe kunci na nayi Cike da azaba don naji zafi sosai kada kumanta a lokacin 12years gareni bansan sanda nayi kukan kura na dauki bucket din pure water Dina ba na buga masa, dai-dai lokacin wani Dan sanda yazo wucewa Aiko ya kariso Yana tambayar neje faruwa?Nan kuwa tsohuwan nan ta zayyane mai komai tana kuka,albarka yasamun sosai sannan yace nakai tsohuwar gida,tab nida bansanta ba daga haduwa taya zansan gidanta,a gaskiya tacema Dan adai-dai tan da ya daukemu take,tayimai kwantancen layin Aiko nan aka kaimu.

Wani dankareren gida mukaje Wanda tunda nake bantaba ganin gida mai kyau da haduwa irin gidan ba don haka nema cikin zumudi nabita gidan,gani nayi ma'aikata kowa na ya duke a kasa Yana kwasan gaisuwa tsoro ne yakamani bansan sanda na diddilo idanuwa waje ba Fadi nake " _innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir-rahmanir-raheem_ yau nakawo kaina mahallaka garin temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat.
Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida sarautar mata gani gareki fulani.
Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba.
Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali?
Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda yafaru,Jakadiya tace haka ne.
Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba.
Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa.
Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin bread.
Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka budemun.
Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala.

Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje.
Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu kudi ne.
Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don wajen babu wajen fakewa Rana.
Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi fesss.
Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara gaisawa da Ammi cike da fargaba.
Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba?
Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa tana son ganin Abba.
Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread.

Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana.

Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba.
Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don ganin iyayen ta.
A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai nabaka jari mai karfi.
Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna.
Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli.
Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace a kwangila.
A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta da yunwa,sosai sukaji dadin alalen.

Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu.

Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan 1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu golden saikace glass Sunyi kyau sosai.

Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da motoci.
Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota.
Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne.
Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local government,gwanda ma baba sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu.

Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma?
Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani.
Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki.
Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni saina samo Mai bazawara.
Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani.
_I need ur comment and sharhi_



Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )




Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciyar⬇️

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_


*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_


*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*



Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai...*


Page:1️⃣1️⃣--1️⃣2️⃣🖊️




_________Tunda suka shigo cikin school din kallonsu ake daga student din har lecturer's din,bawai kwalliyar su kadai ke burge mutane ba,hadda salon tafiyar su day kyansu da iya magana ke burge mutane,uwa uba Kuma ga kwanya suna jinsu kamar gifted.

Shigar larabawa sukayi gaba daya,Wanda yasake haskasu.
Shiga hall sukayi domin gabatar da Exam nan sukayi suka gama batare da sun kula kowa ba.

Bayan sun fito suka wuce gida Cike da gajiya,da yake yau khadee ce da girki,cake kawai sukasha da lemu ta Shiga kitchen don dora girki.

Sai da aka yi sallar magrib sannan khadee ta sauke shinkafa da miyar souce Wanda yaji attarugu,basuci abincin ba sai da suka gabatar da Isha tukuna sannan sukaci abinci sunayi suna shewa da hira.
Sun kammala cin abinci ,Fauzi ta dubi Shakeerah tace"babee muna jinki.
Murmushi Shakeerah tayi tace"dama nasan kina Nan kina kwakwa da kokarin son Jin labari.
Dariya suka sa gabadaya,khadee tace wallahi nima haka shi naketa kwa-kwan son ji.

Shiru tayi ta dauki tsawon minti 3 zuwa can tafara magana kamar haka.
"Da fari dai ni Sunana Maryam Muhammad Adali, Ni haifaffiyar Zaria ce anan na girma anan nataso,gaskiya tun tasowar mu muka taso masu rufin asiri azahiri bamu dashi domin kuwa mu ba 'yayan masu kudi bane,ba musan wani Abu karatun boko ba sai dai na Allo wannan fa akwai shi Wanda mahaifin mu yatsaya Kai da fata yabamu nida Aunty ta.
Mu biyu ne Abba ya haifemu Dani da yayata mafi soyuwa a gareni ta nuna mun so fiye da komai,kun ganni hatta talla nayi tallan biredi saboda tsaban rashi,tun Ina karama ake daurawa Aunty Saudah tallah,macace mai hakuri tare da kawaici irin Ammi,kada kuyi tunanin Wai a son ran iyayen mu muke talla a'ah Babu CE takawo haka,tun farko Abba shagon Saida agoguna yake Rana Daya Bari suka tsiyatar dashi.

Aunty Saudah haka zata dauki tallah batare da ta karya ba,Kai hatta ni mutan gidan,da yawa idan takai ba siya ake ba sai dai a lallatsa a tafi a bar mata,wani ma a kwance aci,ace baza'a siya ba.

'Yan uwan baban mu suna da Hali dai dai gwar-gwado sai dai temako ne baza suyi ba.
Aunty Saudah kuwa duk abinda ke faruwa bashi yake hanata gobe fita da bread ba,ana cikin haka na girma Wanda na taso da shegen rashin ji da fitsari,ba anuna mun yatsa a maida lafiya ba'amun na kyale,tun Ina gida,dalilin haka yasa Ammi ba kasa fai take Bari na fita ba.

Koda nakai 9years tsiyata kuwa ta karu,domin kuwa rigima nasa akan abarni Nima nadinga fita talla kamar yanda Aunty Saudah ke fita,munada kyau daga mu har iyayen mu,Amma tsabar wahala tasa mun kode,kafafuwa na kuwa duk Sunyi faso tsabar gantali yamun yawa da yawo Babu takalmi.
Kullum nasihar Ammi da Abba shine mu natso,nikuwa Shiga takeyi tanan tafita ta can.

Tallah nafara bin Aunty Saudah ita a lokacin tana da 14years, Nikuma Ina Daukar pure water.
Wata rana muka dauki tallah da ita gashi garin da Rana sosai,wani gareji mukazo wucewa kunsan dai garejin masu gyaran motoci to nan.

Alamu sukayi mana da baki kamar fito, Aunty Saudah ce ta juyo da Sauri ta nufi wajen su,domin ita burin ta a kullum da tafito a siye tanajin nauyin komawa gida ba ayi ciniki ba.

Zugwi-zugwi nabi bayanta kamar tsohuwar munafuka,wasu maza ne suka kariso tare da Daukar bread din,Daya ya bude ya dauki na hamsin ya ciye tassss tare da Daukar pure water na yasha,gyatsa yayi irin na 'yan iskan Nan,shikuwa dayan da ya dauki bread din rabi yawafce sannan ya aje ragowan.

Daure face Wanda yacinye ledan bread Daya yayi,sannan ya dubi Aunty Saudah yace"wareee anan wajen,Cike da tsoro Aunty Saudah ta sungumi farantin bread dinta domin gudu.
Dubana yayi yace"kema dauki wannan ajawon ruwan naki ki wuce,yayi maganar Yana wurgi da bucket din ruwana.
Nan kuwa ruwa ya fadi wasu Kuma suka farfashe,cikin bacin Rai na dago na dubeshi sannan na dube bucket dina.
Daya a cikinsu yace"ba magana ake Miki ba don uwarkiiiiii?
Itakuwa Aunty Saudah fara jana tayi Cike da tsoro tana cewa"Shakeerah zo mune gida mu barsu da Allah .
Fusge hannuna nayi na nufi inda bucket Dina yake,da yake irin na karfen nan ne Mai murfi,dauka nayi ba nufo su,sukuma a lokacin sun juya sai dariya suke tikawa ba suyi aune ba sukaji saukar bucket akan daya a cikinsu,ihu yasaka,a firgice dayan shima yajuyo Aiko na sakin mai bucket din a gushi,duk cikansu ihu sukasa domin wajen ya fashe bucket din datsan su yayi.
Cikin Sauri ragowar mutanen dake garejin suka kariso ana tambayar meke faruwa?a ciki kuwa harda ogan wajen.
Cikin bacin rai nafara magana"Saboda zalunci irin naku da mugunta akan me zakuci bread kuce mutafi sannan kuyimun fatali da bucket din ruwa,oho dayake tasaba zuwa ita kadai dama kume masu Mata haka Koh?to idan ita ta dauka Ni bazan dauka ba eheeee,na karishe maganar Ina murguda baki.
Ogan su ya tambayi ba'asi Nan kuwa na zauna na zayyane komai harda karawa da gishiri,Cike da bacin rai yake dubansu yace"lallai abinda yarinyar nan tayi tamun dai-dai gaba kwasake......cikin Sauri nace"wallahi gobe ma kuka sake sai nayimuku mafiyin wannan,kudena ganina 'yar karama akan ahalina babu abinda bazanyi ba,kowa Cike da mamaki take dubana sukuwa samarin tsoro na ne yashigesu.
Tambaya na shugaban garejin yayi ruwan nawane?nace jakar leda uku CE.
Nan kuwa yaciro dari biyar ya bani,sannan yace bread na nawa sukaci?bashi amsa nayi da cewa da bread din hamsin da rabi sannan ai ba yau sukafara mata haka.
Karshe dai Sai da mukabar gareji da Naira dubu Daya da dari uku,sannan nace"Babu Wanda ya Isa yahanamu kawo talla garejin.
Daukar bucket Dina nayi muka tafi,a ranar dai nayi dambe Yafi a kirga,Kuma duk akan bread da ruwa,masu yima Aunty Saudah rainin wayo sai da na Rama Mata.

Abin mamaki mun siye bread din nan tass Babu ko lankare, murna sosai Aunty Saudah tayi.
Haka kuwa muka nufi hanyar gida muna Cike da farin ciki,a hanya muka hadu da wani wan baban mu akan mashin dinsa Sabo fil,harara yabimu dashi Yana cewa shegu 'yayan Allah shirya masu kama da almajirai,Baku da aiki sai gantalin talla.
Juyowa nayi nace"Kaine dai babban almajiri Mai yawon maula,Kuma ai da sauki mu gumummu muke ci,wasu kuwa gumin haramun suke ci.
Ashe ramawar Nan danayi ya Sosa masa rai Aiko Nan yafara tsiya,kome yafada na bashi martani a karshe dai tsaki naja mai tare da tofar da miyau muka wuce.
Ni ban Sani ba Ashe hakan ya bata masa Rai sosai.
Aunty Saudah kuwa tsiya tadinga mun a hanya akan nadena rashin kunya,dukar da kai nayi kamar gaske nace toh Aunty Saudah nadena.
Tayi farin ciki sosai da amsar da nabata,wato nadena.
Gida muka Shiga Cike da farin ciki na fada jikin Ammi da Abba nace"Ammi Abba yau munyi ciniki Sosai,domin gabadaya aka cinye,murna sukayi sosai kamar su goyamu,tuwon dawar da Ammi tayi da miyar kukan da ko isashshen magi baiji ba muka fara ci Cike dajin yunwa.
Ammi kuwa tasamu tayi tana kallon mu tana Murmushi Cike da kaunar mu a ranta,shikuwa Abba daki yashiga.
Langa-langar kofan mu aka bugo da karfi Wanda yasamu zabura gabadaya,baba Ayuba ne yashigo Yana masifa,ganina yasashi yowa inda nake direct.
Nikuwa ganin haka yasa na Miki nayi hanyar bayin mu,ai kuwa baba tsalha ya biyo baya na shima a gunen , da yake wajen da santsi sai na zille nayi gefe guda.
Yana kuwa karisowa wajen santsin jiake timmmm baba tsalha yafadi,Kara yasaka tare da fadin"wayyo Allah na kunguru na.
Nikuwa mezanyi Banda dariya,dariya nake sosai harda rike Cike,Cike da bacin Rai yadago Yana dubana.
Abba ne yakariso cikin Sauri Yana fadin "Subhanallah yaya Ayuba meyasa Meka?cikin Sauri Abba ya kamashi ya dagashi,Nuno ni da yatsa yayi yace"wancan tsinanniyar yarinyar taka Mai Kama da aljanu nan yashiga bawa Abba labarin komai.
Cike da bacin Rai Abba yadago Yana duba na yace"Mama haka kayi?
Girgiza Kai nayi cikin Sauri

Please Login or Register in order to submit comment