Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Haɗaka palace*
*kungiyar masu posting ce ba marubuta ba*




*Bismillahi rahmani raheem*





🅿️. ONE..




*KANO STATE*




Gama shirya warta kenan ta buɗe ƙofa ta shigo, kallonta ta yi ta ce " haba samha wannan wane irin wulaƙanci ne ace tun ɗazu common wanka da saka kaya amma kinfi awa guda kuma kinsan driver na jiranmu awaje wannan bai kamata ba " wacce aka kira da Samha ta juyo sai a sannan na ƙare mata kallo fara ce tas kuma asalin kyakyawa dan tafi kamada half-case ɗin nan cikin ƙasa da murya na rashin son hayaniya ta ce " meyasa kika fiye ƙorafi Saima?, kina gani fa banda wankan babu abinda nayi amma kinzo kina mana shouting aka " tsayawa Saima ta yi tana kallon zallar rainin hankalin biyunin tata, tsabar baƙinciki yasa tayi waje ba tareda ta ce mata komai ba. Ganin ta fita yasa ta ɗauko veil ɗin abayar jikinta ta yafa, tayi kyau sosai musamman yanda black abayar ta karɓi white skin ɗinta ta ɗauka hand bag sannan ta ɗauki wayarta ƙirar iphone 13pro max tayi waje, tsaye ta samesu ta tsuguna ƙasa ta ce " good morning Dad, good morning Mom " murmushi Wanda aka kira da Daddyn ya yi sannan ya ce " Samha meyasa kuke makara makaranta kuma ke ce kike jawowa " cikeda ladabi ta ce " wallahi Daddy ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na shirya da wuri kawai saboda ita Saima ta nada gaggawa yasa ake ganin bana saurin " miƙewa ya yi ya ce " adinga ƙoƙari ana tafi da wuri kinji, tashi ku tafi " sai a sannan ta miƙe ta ce " Mom sai mun dawo" murmushi Mom ɗin ta yi ta ce " Allah ya tsare my Twins please ku kiyaye mutuncinku kunji " toh suka ce duka sanann sukai waje don tafiya makarantar.........






*Su wanene Saima da Samha?*


Alhaji Ahmad wanda ya kasance shine mahaifinsu sai kuma mahaifiyarsu wato Doctor Maryam ta kasance professer kuma likita dan tana da asibiti mai zaman kansa, mijinta Alhaji Ahmad ya kasance ɗan ƙasar Etopia ne wanda kasuwanci ne ya dawo dashi ƙasar Nigeria kuma cikakken ɗan boko ne a gefe guda, sunɗauki shekaru a ƙalla goma da aure kafin Allah yasa su sami ƴaƴansu wato Fatima wacce suke kira da Samha sai kuma Zainab wacce suke cewa Saima kasancewar su kaɗai iyayensu suka mallaka kuma ga tarin dukiya yasa duk abinda suke so arayuwa suke samu sai dai idan ya saɓawa Addinin musulunci, bazasu wuce shekaru sha bakwai ba suna level one a jami'ar bayero inda Samha take karantar pharmacy ita kuma Saima computer science. Kasan cewar sun ban-banta a fanni karatu yasa dasun shiga makaranta suke rabuwa sai kuma antashi kamarsu ɗaya dan irin identical Twins ɗin nanne abu ɗaya ne ya rabasu ita Samha fara ce ita kuma Saima chocolate colour ce wannan shine abinda ya rabasu dan hatta sutura iri ɗaya suke sawa, akwai shaƙuwa sosai Tsakaninsu wani lokacin idan suna abu Mommy takance"
wannan abun naku wata rana baza kuyi ba saboda aure dole sai ya rabaku " dariya suke suce atare " ai Mommy babu wanda zai shiga *TSAKANINMU* sai mutuwa dan ko aure zamuyi to Twins irinmu zamu aura " sai tayi murmushi ta ce " Allah yasa".......


*Wannan kenan*


Suna shiga makarantar bayan driver ya yi parking suka fito atare daidai lokacin motar ƙawar Saima Aleeya ta shigo bayan tafito ta zo ta rungume ƙawar tata cikeda jindaɗin ganin juna kallo kawai Samha ta bisu dashi sannan tayi gaba cikin rashin jindaɗi Aleeya ta ce " wai Saima meyasa Samha batason kula kowa?, bakiga yanda ake munafurcinta ba" kama hannunta Saima tayi suna tafiya sannan ta ce" wallahi bansani ba ni kai wani lokacin *TSAKANINMU* da juna sai kallo ko agida haka take batada yawan magana " ajiyar zuciya Aleeya ta sauke sannan ta ce "ai kuwa kudinga bata shawara ta daina, gashi ko maza bata kulawa kamar ba maceba wasu cewa suke wai ƴar wulaƙanci ce " ɗaga kafaɗa Saima tayi alamar bai dametaba ta ce " tai tayi ni babu ruwana" dariya Aleeya ta yi ta ce " aikuwa kice da ruwa " shiru sukayi saboda ƙofar class ɗinsu da suka zo.....






Sosai take sauri saboda tasan halin lecturer'n su ai kuwa ilai ta zuwa ta tarar ya shiga, da sallama tashiga ajin a ɗan tsoroce cikin kakkausar murya ya ce " keee! Get out " juyowa ta yi ta kalleshi ta ce " sir please sorry" cikin faɗa ya ce " sorry For your self, get out!!! " da sauri ta yi waje saboda ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba. Haka ta dinga zama har aka fito break sannan wata ƙawarta wacce suke mutunci tazo gurinta ta zauna budurwa mai suna Aysha ta ce " Samha meyasa kike makara wai?, duk randa lecturer'n nan zai shigo bakya zuwa da huri kuma kinsan hakan zai jawo miki matsala " kallonta Samha ta yi kamar bazatai magana ba sai kuma ta ce " isn't my fault kawai ya tsaneni ne yasa yake yimin haka amma ai bakowa yake cewa ya fita ba kina gani bayan ya koreni wata tashiga kuma ya barta " cikin damuwa Aysha ta ce " nasani amma kidinga ƙoƙari duk ran lecture sa kina zuwa da wuri " murmushi ta yi har saida beauty point ɗinta suka loma sannan ta ce " thank for caring In sha Allah zan dunga zuwa before yazo " murmushi itama ta yi ta ce " yawwa ko kefa, tashi muje muci abinci " ok ta ce sannan suka tafi.......






Inda tayi parking motarta suka zo da mamaki Samha ta ce " A'a ba abinci zamuje siyaba ?" murmushi Aysha ta yi ta buɗe motarta ta ɗauko wani kwondo sannan ta ce " banason abincin makaranta shiyasa yau na dafo mana agida kizo muje mu zauna muci " murmushi ta yi ta ce " ok amma sannunki har kikai girki kika tawo kuma kika zo da wuri tab" dariya Aysha tayi ta ce " toh aka ce miki kowa irinki ne rago me zama bacci " kwaɓe fuska tayi ta ce " zan mara ne" dariya ta yi sannan sukai gaba dan samun inda zasu ci abincin........






Ɓangaren Saima kuwa zaune suke sunata hira da ƴan click ɗinta saboda ita friendful ce ba kamar Samha ba wani namiji mai suna Khaleepa ya ce " wai Saima ina yayarki Samha kwana biyu batazo wajenki ba?" harara ta galla mai sannan ta ce " wace yayar tawa?, wallahi sai na maka rashin mutunci ka sake cewa Samha yata banda iskanci yaushe ta zama yar tawa?" sheƙewa sukai da dariya gaba ɗayansu sannan Khaleepa ya ce " ai kowa yasan yarki ce saboda saida ta fito daga ciki sannan kika fito kinga kuwa yayarki ce ni wallahi Saima ina sonta kuma zan aureta please kimin campaing " kallonsa ta yi irin kayi haukan nan sannan ta ce " game fili ga mai doki kaje da kanka wajenta ɗan rainin hankali " murmushi ya yi ya ce " wallahi Saima da gaske nake inason Samha dan Allah " tashi tayi tsam ta ce " lallaima!! To bari kaji idan ba Twins ba babu wanda zamu aura saboda bazamu auri waƴanda zasu rabamu ba " zai ƙara magana ta ɗaga mai hannu ta ce " please karka ɓatamin rai zan maka rashin mutunci wallahi " ganin yanda ta fusata yasa ya ce " Allah ya baki haƙuri sarkin zuciya " bata tsaya saurarenshi ba ta ɗau jakarta ta bar wajen rai ɓace......







Sai kusan magrib sannan suka dawo gida, suna shiga ko wacce tayi ɗakinta kasancewar parlour suka haɗa amma bedroom ɗin kowa daban. Bayan sunyi sallah suka zauna karatun al-qur'ani sakamakon sabon da sukai na duk bayan sallar asuba da magrib sai sun karanta al-qur'ani.....






Banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi a dinning area ɗin Daddy ne ya kallasu ya ce " when zakuyi exams? " Next month suka faɗa, a nutse ya ce " ok idan kun gama zamuje Etopia saboda granny ɗinku ta matsamin " murmushi sukai sannan suka cigaba da cin abincinsu kusan two minutes sai kuma Saima ta ce " Dad" uhmm"ya amsa cikin shagwaba ta ce " Dad please abarmu mu dinga zuwa makaranta da kanmu ba sai driver ya kaimu ba wallahi kowa da kanshi yake zuwa " murmushi ya yi saikuma ya girgiza kai ya ce " zan baku mota amma not now " cikin ladabi ta ce "ok Dad " murmushi ya yi ya ce "good girl " kallonta Samha ta yi sai kuma ta fashe da dariya tana mata gwalo, wata uwar harara ta galla mata sai kuma ta ce " Dad ka ganta ko" kallon Samha ya yi ya ce " gidanku kina mata gwalo " kwaɓe fuska ta yi ta ce " Daddy ƙarya take fa " harararta Mommy ta yi ta ce " ina kallo kikai mata gwalo shine zakice ba kiyi ba " turo baki tayi sannan ta miƙe tayi ɗaki, kallo suka bita dashi Mommy ta ce " Allah ya yaye miki abinda ke damunki Samha " Ameen suka amsa gabaɗaya...




*NEXT DAY*



Yau kam da sassafe ta tashi bayan ta gama shiryawa ta shiga ɗakin Saima dan tashinta, zaune ta sameta tana waya sai bayan ta idar sannan Samha ta ce " ke dawa kike waya?" murmushi ta yi ta ce " my boyfriend kuma wanda zan aura kuma kema inason ki auri ɗan uwansa kamar mu suke please Samha " tashi ta yi ta ce "ina jiranki awaje " kallo ta bita dashi sannan ta ce " twinny kenan In sha Allah sai na sauya miki wannan dabi'ar taki kuma zaki auri mubarak " daga nan ta tashi ta ɗauki wayarta tayi waje........







Comments,like, and share.





Written by:
*Nanameera*







Meera love's yhu💖💖💖💖
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*





*Bismillahi-rahmani-raheem*





🅿️....TWO.




Jakarta ta ɗauka ta fito bata sameta a parlour'n ba babu kowa sai wata maid ta kalleta ta ce " Talatu ina mommy? da Daddy" cikin girmamawa ta ce " hajiya tunda safe kusan ƙarfe shidda suka fita ita kuma ƴar uwarki yanzu tafita " ok ta ce sannan tayi waje.....





Bayan sunshiga mota sunyi nisa Saima ta ce " wai dan Allah Samha mece ce matsalarki?, wallahi Mubarak bashida matsala baki ganshi ba handsome guy kuma milloniere babansu fa shine ministan man fetur please Samha kiyi accepting soyyyar shi kuma wallahi yana sonki kinga su ba Twins bane kamarmu amma kamar Twins suke gidansu ɗaya suka gina zasu zauna please Samha " wani kallo Samha tayi mata sannan ta ce " Saima na hanaki ki auri wanda kike so?, who stop you?, kije ki aureshi Allah ya bada zaman lafiya ki rabu dani please " da mamaki ta ce " haba Samha dan Allah ki daina faɗin haka karki manta alƙawarin da mukai a *TSAKANINMU* dan Allah Samha ki amince kinji kodan farin cikina " girgiza kai ta yi ta ce " Saima ke ya kamata ki tuna alƙawarin da mukai na zamu kasance atare kuma zamu zama masu ɗaukan shawarar ɗayanmu, idan haka ne to ke zan faɗawa kiyi haƙuri Saima ki rabu da Yazeed saboda ni " shuru Saima ta yi nawasu daƙiƙu sannan ta ce " faɗamin meya sa bazaki amince ba ?" murmushi takaici Samha ta yi ta ce "Saima please and please karki sake yimin wannan maganar kawai nace banaso fine just leave karka fara ɓatamin rai " kallon-kallo suka shiga yiwa juna kowanne da abinda yake saƙawa acikin ransa har suka ƙarasa makarantar....






Yaukam tana shiga ta zauna kusada Aysha murmushi Aysha ta yi ta ce " morning " murmushin ta mayar mata sannan ta ce " morning sweetheart how are you ?" " fine yau kinzo da wuri " dariya ta yi ta ce " wallahi kam yau nasha wahala tun asuba nake shiri " yawwa ai gwara haka da makarar, kinga yau komai masifarsa ai dole ya kyaleki " murmushi ta yi ta ce " Allah yakyauta ni bansan mena yi masa ba yabi ya tsaneni " shiyasani Aysha ta faɗa ....





Tunda ta shiga ajin bata kula kowaba kamar yanda tasaba duk sunyi mamaki saida aka fito break sannan Aleeya ta jata wani waje suka zauna ta ce "Saima yau me akai miki naganki so silent ?" ranta aɓace ta ce " badole raina ya ɓaci ba Samha kwata-kwata bata ganewa " to me tayi miki ? Cikin jin haushi ta ce " wai mubarak ɗan uwan Yazeed ya ce yana sonta amma taƙi yarda ni bansan yanda zanyiba saboda Samha taurin kai gareta ko zaka kasheta idan bataga damaba ba zataiba " cikin damuwa Aleeya ta ce " to yanzu mene abunyi ?" ajiyar Zuciya ta sauke ta ce " kawai saidai na haƙura da Yazeed saboda bazan iya aure na barta ba mun riga munyi alƙawari a *TSAKANINMU*" da mamaki Aleeya ta ce "what!!, amma dai Saima bakida hankali akan bata yarda ba kema zaki haƙura a wannan lokacin da mazan aure ke wahala " cikin sanyin murya ta ce " yanzu ya kike so nayi idan na haƙura sanda duk ta shirya muyi aure sai muyi " tsaki Aleeya ta yi ta ce " lallaima tab, to wallahi tun wuri ki farka daga wannan mafarki dan babu inda zai kaiki sai danasani " "to yanzu ke mene ne shawararki ?" murmushi ta yi ta ce " ki samu kije ki faɗawa Daddynku ke kinsami mijin aure idan yaji haka itama zai mata magana kinga dole zata tsaida wani sai ki kawo maganar Mubarak kinga dole ta yarda ta aureshi " dariya tayi suka tafa sannan ta ce " thank you shiyasa nake sonki amma bari zanyi sai mungama exams sai nayi masa magana sanda zamu Ethopia, yanzu tashi muje dan Yazeed ya ce min zasu zo " ok ta ce sannan sukai gaba......






Wani restaurant da babu nisa da makaranta suka je, zaune suke su biyu kamar Twins sunada kyau daidai misali sunsha ƙananun kaya bazaka cemusu baƙaƙeba dan daɗan haskensu kuma da murjewar jiki ta ƴaƴa ajebo. Zama sukai kusada su Yazeed ya ce " welcome beb " murmushi ta yi ta ce " thank you " kallonta mubarak ya yi ya ce " Saima ya alƙawarina ?" numfasawa ta yi ta ce " i'm sorry Mubarak wallahi bata yarda ba kwata-kwata batada interest akan soyayya infact " kallonta ya yi ya ce " shikenan dan Allah kibani dama nazo gidanku nasan dole zata fito sai muzo da Mubarak " murmushi ta yi ta ce " karka damu ina maka fighting amma zuwa gidanmu ku bari sai mungama exams tukunna " cikeda jindaɗi ya ce " ok thank you Saima " dariya ta yi ta ce " never mind ai munzama ɗaya " dariya sukai duka sannan suka cigaba da cin abincin.....






Bayan sungama jarrabawarsu ta second semister wata asabar suna zaune Saima ta ce " yanzu Samha bazaki sauya ra'ayinki ba?, please ko saboda ni wallahi inason Yazeed sosai kuma bazan iya aure na barki ba, kin san ina faɗawa Daddy cewa zaiyi su fito ayi magana " murmushi Samha ta yi ta ce " please Saima kiyi aurenki ni zan fadawa Daddy amma ki rabu dani dan Allah dan Annabi wallahi bazan aureshi ba ko me zakiyi " kuka Saima ta fashe dashi sannan ta ce " shikenan Samha babu komai kije kiyi rayuwarki yanda kika shiryawa kanki In sha Allah bazan sake yimiki magana ba kuma zan auri Yazeed " miƙewa ta yi cikin faɗa ta ce " ina ruwana yanzuma kije a ɗaura muku aure ko kuma ya ɗaukeki babu auren nace bazan aureshi ba kuma babu abinda kika isa kimin akan haka " tana gama faɗin hakan tayi waje ta bar ɗakin....





Ranta a ɓace ta shiga ɗakinta ta zauna gefen gado tana tunani, lokaci ɗaya ta fashe da kuka ko me ta tuna ?.....






Da daddare suna zaune suna cin abinci kamar kullum duk sunyi so silent Mommy ta ce " wai meyake damunku tunda safe ina kula da motsinku ?" murmushi Samha ta yi ta ce " wallahi babu komai, Daddy yaushe zamu tafi Ethopia ɗin ?" kallonta ya yi ya ce " in sha Allah ranar friday saboda haka ku shirya " ok ta ce, Mommy ta ce " Samha ni zaki yiwa ƙarya?, tabbas akwai abinda yake faruwa a tsakaninku ku faɗan gaskiya " dariya Samha ta yi ta ce " haba Mommy kinsan idan wani abun ne ai zamu faɗa wallahi babu komai da.......katseta Saima ta yi ta ce " ba wani nan wallahi ƙarya take Mommy kuma saina faɗi abinda yake faruwa " kallonsu iyayen sukai da mamaki saboda tunda suke In kacire wasa basu taɓa faɗaba, Daddy yace " Saima faɗamin what's wrong " cikin sanyin murya ta ce " Daddy dama Samha ce wai saboda nace mata wani ya ce yana sonta kuma aurenta zaiyi shikenan ta daina kulani " da mamaki Mommy ta ce " kamarya ya ce yanasonta meyasa ya faɗa miki bai sameta ya faɗamata ba ?" ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce " ni ya sani shiyasa ya bani saƙo na faɗa mata amma kwata-kwata Samha taƙi saurarata " cikin faɗa Samha ta ce "lier!! wallahi ƙarya take ba saboda yana sona kike haka ba saboda kinaso ki auri ɗan uwansa yasa kike haka kar ace kin karya alƙawarin da mukai *TSAKANINMU* ko anfaɗa miki ban sani bane, kuma ni indai sunana Fatima Ahmad Azaad(Samha) bazan aureshi " cikin hasala itama ta ce " to saime karki aureshi kan ki ki kaiwa ba niba nagaji da lallaɓaki karki yarda ɗin wallahi idan har sunana Zainab Ahmad Azaad(Saima) saina aureshi sai dai ace na karya alƙawarin dake *TSAKANINMU* kuma..... Wata kyakyawar tsawa Daddy ya daka musu hakan yasa sukai shuru kowanne yana huci, cikin faɗa ya ce " mene haka ?, bakuda hankali ne ko me?, akan wannan abun shine zaku yarda ku karya amincin dake tsakaninku?, a wane hadisin akace sai kun auri yan biyu kamarku?, wa yay muku dole?, duk wacce ta sami miji tayi aurenta, dan anhaifeku tare bashine yake nufin zakuyi aure tareba banson tashin hankali " Mommy ce ta ce " mene na ɗaga wa juna hankali, idan Saima kinsami miji ya fito itama sanda duk tasamu nata mijin sai ayi nata auren " kallansu Daddy ya yi ya ce " Saima kina son wanda kika faɗa ɗin ?" ɗago kai ta yi ta na kuka ta ce " Daddy wallahi indai Samha bataso na haƙura Allah yasa hakane mafi alkhairi " cikin faɗa ya ce " i asked you kina sonsa ko A'a bawai Samha ta yarda ko bata yarda ba " "Eh Daddy ina sonsa amma nafi son Samha dashi " tashi ya yi ya ce " kice masa ya turo iyayensa suzo ai magana " da mugun mamaki suka kalleshi duka dan basu ɗauka zai yarda ba cikin rawar murya Samha ta ce "Daddy dan Allah karka aura mata Yazeed kaji Daddy please " murmushi ya yi ya ce " Samha kiyiwa ƴar uwarki addu'ar zaman lafiya amma idan har nayi bincike na tabbatar da tarbiyarsu to zan aura masa Saima " dawowa gabansa ta yi ta riƙe ƙafarshi ta ce "









Comments, like and share.







Written by:
*Nanameera*








Meera Love's yhu 💖💖💖💖
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*





*Haɗaka palace*
Kungiyar masu posting ce ba marubutaba.





🅿️....THREE...




Cikin kuka ta ce " Daddy kasan bazan cutarda Saima ba, kuma bazan so ace ta yi danasani a rayuwarta ba please Daddy abar maganar Yazeed dan Allah " ta ƙarasa faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciya, a fusace Mommy tazo gabanta ta ɗagota zatai magana ta wanketa da mari ji kake tass. Abinda bata taɓai mata a rayuwarta ba kenan sai yau, cikin faɗa ta ce " ke wace irin yarinya ce mai baƙin hali saboda ƴar'uwarki ta sami mijin aure shine kike mata baƙin ciki?, to wallahi koda wasa na sake jin kinyi makamanciyar wannan maganar saina ɓata miki rai fiyeda tunaninki, wawiya kawai " tsabar shock ta kasa magana yau ita ake jifa da irin wannan mugayen kalaman?, goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ce " shikenan Daddy, Mommy, Saima kuyi haƙuri In sha Allah haka bazata sake faruwa ba, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba mai amfani ku gafarceni idan na ɓata muku rai " numfasawa Daddy ya yi deep down baiji daɗin abinda ya faru ba ya ce " shikenan ya huce karna sake jin antada maganar please idan ba hakaba ranku duka zai ɓaci

Please Login or Register in order to submit comment