Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fita suna rike da hannu juna. Rai ɓace Aysha ta ce"banda rainin hankali tasan yau akwai paper amma tayi zamanta haka ranar Friday ma tayi ko ubanme take nufi da kanta bansani ba" murmushi Fa'eeza ta yi ta ce"ke kuma kin fiye saurin fusata maybe akwai wani abun kinsan haka kawai Fateemah ba zata ƙi zuwa exam ba" Zainab ce ta ce"wlh kuwa amma mu kirata awaya mana naga kwana biyu bata hau online kwata-kwata" tsaki Aysha ta yi ta ce"ai babu waya a hannunta bare a kirata kuma gashi bamusan gidan da take ba balle muje muga ko lafiya" da damuwa Fa'eeza ta ce"gaskiya kam Allah dai yasa lafiya" Ameen Zainab ta ce sannan suka miƙe dan sannan zasu shiga biology.





Dakyar ta idar da sallar asuba ɗin sannan ta zauna gefen gadon banda raɗaɗi babu abinda jikinta ke mata ko'ina babu daɗi ga bakinta wanda take jin yana yi mata wani irin ɗaci rabonta da abinci har ta manta dan bata iya cin komai ruwa ma dakyar take samu tasha kuma shima sai ƙishirwar ta ƙure kuma bata iya sha da yawa saidai kaɗan hakan yasa duk fatar jikinta ta fara yamushewa kana ganinta kasan babu wadataccen jini da ruwa ajikinta cikin sati ɗaya da tayi a haka koda sau ɗaya Imad bai leƙo da niyyar dubata ba saidai kullum taji alamun tashin motarsa idan zai fita idan har wanda yasan Fattomah watanni uku da suka shige zai ganta yanzu toh tabbas sai ya yi dagaske kafin ya iya gane itace duk tayi baƙi ga wata uwar rama da tayi idanuwanta duk sun faɗa ciki Fattomah wacce ta kasance mai yawan hira da wasa da dariya yau sai tayi kwanaki ba tace uffan ba idan har zata buɗi bakinta to saidai wajen karatun sallah amma ko kaɗan bata hira to dawa ma zata yi hiran???????? Ita ba uwa ba ita ba uba ba Allah sarki kaɗan daga cikin ƙalubalen maraici kenan. Cikin kwantar da murya da son faɗa masa gaskiya ya ce


"Wallahi dagaske nake maka babu amfanin wannan abinda kake aikatawa, yarinya ce ƙarama batasan komai ba ko wace irin tarbiyya kake so zaka iya ɗorata kuma tabi amma wlh duk ranar da Fattum ta fara gane kanta bazaka taɓa iya lankwasa taba, duka baya taɓa sakawa yaro ya daina abu saima tunzurashi da yake wasu lokutan bare kuma Fattomah da batada saka magana ko kaɗan yarinya ce wacce bata damu da rayuwar kowa ba beside kuma batada laifi dan ba itace ta kawo kanta gidanka ba bata cancanci irin wannan rayuwar ba kamata ya yi ka tausayawa maraicinta ka kula da rayuwarta naɗan wannan lokacin ka daina dukanta domin hakan tamkar zaluntarta ka ke, ka dinga ƙoƙarin sassauta fushinka akanta kuma wani lokacin ba laifi tayi ba kawai saboda kanajin cewa ka tsaneta cikin ranka yasa kake mata haka, dan Allah Imad ka faɗa min mene ne lafin Fattomah daya sanya ka tsaneta dan Allah ka faɗa min?" Shiru Imad ya yi dan tabbas bashida amsar bashi kuma baisan dalilin hakan ba kawai yaji baya ƙaunarta ko kaɗan cikin ransa aduk sanda ya ganta ji yake tamkar ya shaƙe mata wuya ta mutu ko ya daina ganin fuskarta bai taɓa jin tsanar mutum cikin zuciyarsa irin Fattomah ba ko mene dalili ohooooo?????, Jawaad ya cigaba da faɗin"dan Allah ka buɗe yarinyar nan kuma karka sake rufe ta saboda alfarmar Annabi koda bazaka kula da'ita ba to karka cutar da'ita kabarta haka nan please Bro" ajiyar zuciya Imadudden ya sauke sannan ya gyaɗa masa kai a hankali ya ce"in sha Allah kodan saboda kai nasan bakason kaga matarka cikin damuwa right?" kallonsa Jawaad ya yi amma bai ce komai ba, da sallama ta shigo parlon tana sanye cikin wata atamfa Holland coffee color ta sanya farin mayafi ɗan ƙarami hannunta riƙe da mukullin mota, gaisawa suka yi da Jawaad sannan ta kalli Imad ta ce"daman zan fitan ne" okay ya ce mata sannan ta juya ta fita abinta. Kwance ya tarar da'ita ta duƙunƙune cikin duvet, ahankali ya ƙarasa gaban gadon ya tsaya yana kallon fuskarta wacce tagama sauya kammani gefen duvet ɗin ya daka hakan yasa ta buɗe idanunta saboda batada nauyin bacci da sauri tayi baya cikin tashin hankali ta fara faɗin


"Da..Da...dan Allah Uncle kayi haƙuri da. n Allah"


Kallonta kawai ya tsaya yana yi dan baima san abinda zai ce mata ba kuma daman ba shigowa ya yi dan ya yi mata maganar ba tsayawa tayi da kukan ganin ya juya ya yi fitarsa jingina tayi da jikin gadon tana sauke numfashi ahankali, saida ta nutsu sosai sannan ta miƙe tana tafiya a hankali ta shige toilet.



Da mamaki ta ƙaraso tana kallonsa murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa amma kana ganinta kasan mamakine fal fuskarta, gaisawa suka yi ya ce"sannu kinganni gidanku ko?" gyada masa kai Aysha ta yi ta ce"Eh mana kamar na taɓa ganinka" murmushi kawai Kamal ya yi ya ce"Eh mana kece ƙawar Fattomah ko?" gyaɗa masa kai tayi nan ma ya ce"daman ina son na tambayeki ne" Aysha ta ce"Allah yasa na sani" gyara tsaiwarsa ya yi sannan ya ce

"Daman Fattomah ce bana ganinta kwana biyu kuma na kira wayarta several times switch up to shine nazo school ɗinku jiya na tambayi wasu yan class ɗin ku suka cemin kece best friend ɗinta shine nazo na tambayeki ko lafiya?" numfasawa Aysha ta yi sai kuma ta ce"wlh nima abinda ke damuna kenan ina cikin tashin hankali yau kusan sati biyu kenan banga Fattum ba kuma bansan inda zan sameta ba bata zuwa makaranta kuma babu waya ahannunta duk na damu" da mamaki ya ce"kema bakisan inda take ba toh, kina ƙawarta bakisan gidan su ba?" hawayen da yake zubowa afuskarta ta goge sannan ta ce asanyaye


"Ai bata gidansu saboda babanta ya rasu Mamanta kuma bata garin nan tana gidan relative ɗinta kuma ban sani ba" dafe kansa ya yi cikin ɗunbin damuwa ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wlh ina matukar son ganin yarinyar nan yanzu babu inda zan ganta hasbunallah" kallonsa kawai Aysha tayi dan ita tama fishi son ganin Fattum tunda suke basu taɓa rabuwa irin haka ba koda kuwa hutu aka yi Aysha zataje gurinta su zauna suyita hira amma sai gashi cikin lokaci ƙanƙani ta nemata ta rasa, shuru ya yi na wasu mintuna sai kuma ya ce"shikenan zan tafi in sha zan sake shigowa naji ko akwai wani abu da kika samu" okay Aysha ta ce masa sannan ya zaro rafar yan ɗari biyu a aljihunsa yana kallonta ya miƙa mata ya ce"take this" girgiza kanta ta yi ta ce"A'a nagode sosai" murmushi ya yi sannan ya ajiye mata kuɗin gefenta ya bar wajen tana nan tsaye har taga tashin motarsa sannan ta ɗauki kuɗin ta shige gida.



Tsaki Saleem ya yi ya ce"kai ma ai kayi ganganci har zaka bari baka karɓi address nata ba to yanzu gashi babu wayar kuma bakasan inda take ba" hannunsa ya sanya ya wargatsa gashin kansa sannan ya ce"idan har inada rabon aurenta nasan tabbas watarana zamu sake haɗuwa naji haka cikin rai na" gyaɗa kansa ya yi ya ce"Ehh Lallai to Allah ya tabbatar da Alkhairi" jingina ya yi da jikin kujerar ya ce"oh god!!" kallonsa kawai Saleem ya yi sannan ya girgiza kai.



Kallonta kawai Jawaad yake har ta karasa sakkowa daga benen tafiya take kamar wacce kwai ya fashewa ajiki har ta ƙaraso wajensu, tsugunawa tayi tana cize laɓe saboda wata irin azaba data ziyarci kwakwalwarta, Imad ne ya ce"tashi anan wajen" toh ta ce sannan ta kama kujera tana niyyar tashi dakyar ta miƙe ta haɗa wani uban gumi ta zauna kan kujerar tana maida numfashi, Jawaad ne ya ce"bakida lafiya ne Fattum?" girgiza masa kai ta yi ya ce"A'a ki faɗa min gaskiya mene yake damunki" a hankali ta kallesa hawaye na taruwa a idanunta ta ce"yaya ƙafata ciwo take kullum haka" Jawaad ya ce"Ayyah sannu kinji bari zan kawo miki magani sai ki dinga shafawa okay?" gyaɗa masa kai ta yi Imad ya ce"have you eaten?" girgiza kanta ta yi ya ce"tashi kije ki ɗebi abinci" kwaɓe fuskarta ta yi bata ce komai ba, ganin yanda tayi yasa ya ce"ko maid ta kawo miki?" girgiza masa kai ta yi ta ce"A'a na ƙoshi ni" haɗe rai ya yi sannan ya kira wata maid cikeda ladabi ta ce"gani sir" "ki kawo abinci amma bamai nauyi ba something liquid haka" okay ta ce sannan ta juya tabar wajen.




Juyi kawai take kan gadon amma ta kasa bacci banda ciwo babu abinda cikinta ke mata gashi daman wajen ya yi wani irin ja da kuma kumbura tun ranar da Imad ya daketa koda wasa bata taɓa nuna wani abu agabansa wanda zai sa ya fahimci haka ba dakyar take iya taka ƙafarta duk jijiyoyin wajen sun riƙe haka take kasancewa duk dare cikin rashin samun bacci wadattace,



Fitowar ta kenan daga wanka tana tsaye tana ƙoƙarin shafa mai ajikinta batasan sanda ya shigo ɗakin ba har ta gama shafa man sannan ta zame towel ɗin da niyyar ɗaukan rigarta



"Keeeeee!!"


Afirgice ta juyo tana kallonsa dan batasan sanda ta karasa yarda towel ɗinba hankali tashe yake kallon cikin nata yama kasa furta komai ita kuwa fashewa tayi da kuka tana ƙoƙarin rufe jikinta batasan ko kaɗan tunanin Imad bai zo wajen ba, tsugunawa ya yi gabanta yana kai hannunsa kan cikin nata, sosai abun ya bashi mamaki haɗi da tashin hankali dan bai taɓa ganin irin abun azahiri ba saidai akaratu bakinsa na rawa ya furta


"Keeee..keee...Mee..mene wannan?"


Cikin kukan ta ce"dan Allah Uncle kayi haƙuri dan Allah karka dakeni wlh mutuwa zanyi dan Allah Uncle" miƙewa ya yi kawai bai ce komai ba ya miƙa mata rigarta sannan ya juya ya yi waje, rigar ta sanya har sannan tana ci-gaba da kukanta dan gani take kamar sake dukanta zai yi, shi kuwa rasa abinda zai yi, ya yi duk hankalinsa ya tashi ko yaushe ta samu wannan ciwon???.





Suna shiga cikin asibitin aka shige da'ita emergency Imad kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye dan tashin hankalinsa ɗaya abinda zai cewa Daddy idan ya tambaye shi ya kuma san halin Daddyn nasa, Jawaad ne ya ƙara so yana kallonsa amma ya kasa ce masa komai dan ransa a matuƙar ɓace yake kusan 5mins suna tsaye kafin ya ƙaraso yana kallonsa ya ce"friend wane bashida lafiya?" asanyaye Imad ya ce"wlh yarinya ce kuma gaskiya abun ba karami bane please kaje ka gani" okay ya ce sannan ya kalli Jawaad da sauri ya sake kallonsa ganin kamar yaso ya tuna inda ya sanshi kallonsa shima Jawaad ya yi amma bai ce komai ba shima Kamal shigewa ya yi saboda ya duba mara lafiyar.




Kusan mutuwar tsaye Kamal ya yi ganin Fattomah kwance an sanya mata oxygen bai taɓa tsammatar haka ba dukda ya yi mamakin ganin Jawaad amma bai ɗauka ita ce batada lafiyar ba tunaninshi ɗaya yanzu mene ne alaƙarta da abokinsa Imadudden har zai kawota asibiti shidai yasan shi kaɗai iyayensa suka haifa bare yace ƙanwarsa ce wannan tunanin shine abinda ya sanya duk ya zama moody har aka shiga da yarinyar domin dubata.




Da sauri Jawaad ya fizge takardar hannun Kamal ɗin cikin son gazgata abinda Kamal ɗin yake faɗa ji ya yi numfashinsa na neman barin jikinsa lokacin daya gama karanta takardar bai taɓa tunanin haka ba koda kuwa cikin mafarki ne zama ya koma ya yi jin jiri na neman ɗibansa ba shi kaɗai ba shima kansa Kamal ya kasa magana ji yake inama ace mafarkine wannan abinda yake faruwa ɗin ba gaskiya ba, inama ya farka daga wannan mafarkin wanda yake neman tarwatsa masa farin cikinsa zuciyarsa da kwakwalwarsa duk a dagule suke kuma cikeda tambayoyi masu tarin yawa. Kamar wani zaki haka ya mike yana riƙeda takardar ya fice daga cikin office ɗin, shigowarsa kenan bayan yaje gida dan ɗauko mata kaya ganin Jawaad tsaye ya haɗe hannayensa a ƙirji yasa ya ƙara sa ya dafa shi cikin sanyin murya ya ce"Jawaad ya jikin nata?"




"Ka kyauta Imad!! Ka kyauta wannan shine cika alƙawari haka shine daidai wllh ban taɓa zaton haka daga gareka ka koda kuwa a mafarki ne ban ɗauka zaka kasance mai son zuciya kuma mara imani har haka ba nasan kawai Kanada saurin fushi da fusata amma ban yi zaton kai azzalumi neba Imadudden kaci amana kayi yaudara kuma kayi zalunci wanda kai ma kasan Ubangiji bazai taɓa barinka ba kai ɗin azzalumi ne!!!"


Kallonsa kawai Imad yake yi tunda ya fara maganar dan baisan abinda yake nufi ba kuma baisan akan me yake magana duk sai ya ruɗe gashi Jawaad sai surfa masifa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba



"Ka sanar dani wai mene ne abinda ke faruwa Jawaad?" murmushin takaici Jawaad ya yi sannan ya miƙa masa takardar hannunsa, ahankali ya warwareta ya fara karantawa anutse, wani irin gumi ne ki tsassafo masa tundaga tsakiyar kansa da sauri ya kalli Jawaad yaga shi yake kallo da alamar tuhuma, zama Imad ya yi kan wata kujera daya gani wajen dan ji yake kamar ya yi hauka ya rasa mene ne yake shirin faruwa farin ciki ya kamata ya yi ko kuwa baƙi ciki???, damuwa ce fal ransa da kuma tashin hankali dan baisan da wane idanu zai tari Daddy ba shine babban tashin hankalinsa, kallonsa Jawaad ya yi sai kuma ya ce


"Imad why??why??why??, Dan Allah wace irin tsana ka yiwa wannan yarinyar?, mene laifinta daka yanke shawarar rabata da farin ciki?, me ta aikata maka wanda kake tunanin ta cancanci wannan hukuncin?, akan wane dalili ne Imad?" Dafe kansa ya yi dan bashida amsar da zai bawa Jawaad a halin yanzu dan kome zai faɗa masa bazai ɗauka ba. Miƙewa Imad ya yi bai ce komai ba ya yi waje yana haɗa hanya saboda ciwon da kansa ke masa, da kallo Jawaad da bisa yasan tunda ya yi haka bazai faɗa masa sannan bane shiyasa shima ya rabu dashi.





Kallonsa Kamal ya yi jiki babu kwari ya ce"yarinyar matarka ce daman?" girgiza masa kai ya yi ya ce"A'a matar ɗan uwa nace" "wanne kenan?" "Imadudden" da sauri Kamal ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kansa yana tunani yaushe Imad ya yi aure bashida labari?, kuma ina yaga Fattomah ya aureta?? "Zan yi maka bayani dalla dalla da zarar na samu lokaci" kallonsa Kamal ya yi dan duk a zatonsa azuciyarsa ya faɗi maganar bai ɗauka afili bane. Kamal ya ce"abinda ke jikinta ya ɗan daɗe gaskiya kuma bata samun kulawa yanda ya kamata that's why har ba'a gane ba cikin jikinta zai kai kusan 7weeks saboda haka tana da buƙatar kulawa sosai, sannan maganar abunda yake cikinta ciwone taji kuma gaskiya ya yi worth sosai dole saidai ayi mata aiki dan gyara wajen" ajiyar zuciya Jawaad ya sauke sannan ya ce"okay shikenan a shirya yi mata aikin" Kamal ya ce"to ai ba zai yiwu ayi mata aikin ba saidai idan har an cire cikin dake jikinta shine kawai zai bada wannan damar" shuru Jawaad ya yi sai kuma ya ce"dole saidai a cire cikin?" gyaɗa masa kai Kamal ya yi, miƙewa ya yi ya ce"taɓ bari naje wajen Imad sai muyi maganar" Okay Kamal ya ce sannan ya juya ya fita.





Shuru Imad ya yi sai kuma ya ce"why ana bata magani ai hakanma zai yiwu ba dole sai an cire cikin jikinta ba, beside kaima kasan bazan taɓa yarda acire abinda ke cikinta ba saboda idan babu shi nifa bazan sake samun wani cikin ba har abada bazan iya wannan kasadar ba gaskiya" Jawaad ya ce"Imad magana fa ake ta lafiyarta idan batada lafiya ka faɗa min ta ina zata iya haifa maka ɗan?, sannan idan Allah yaso sai kaga nan gaba ka sake samun wani cikin daban yanda kayi da niyyar taimakon rayuwarta to wannan karanma haka zaka yi domin shine kaɗai mafitarka" girgiza kai ya yi ya ce"Jawaad bafa zan yarda ba shima kuma Kamal ɗin yasan da hakan wlh bazan taɓa yarda ba zan dai siya mata magani daga Naira ɗaya har abinda ya turewa buzu naɗi koda zan rasa duk abinda na mallaka bazan gaji da siya mata magani ba duk tsadarsa kuwa amma gaskiya i won't tolerate cire ciki bazan taɓa iyawa ba" miƙewa Jawaad ya yi ya ce" zan koma asibitin idan ka gama yanke shawara sai ka biyo ni dan zaka yi sign jikin file kafin a shiga aiki" miƙewa shima ya yi ya ce"Jawaad koda zamu shekara ɗari kalma ɗaya zan sake faɗa bazan yarda ba i won't tolerate Kuma nima yanzu zan je asibitin" gaba Jawaad ya yi yana binsa a baya.




Cikin kwantar da murya Kamal ya ce"dan Allah Friend kayi haƙuri ka bari ayi mata aikin nan kaga wlh tana sake kaiwa matakin ƙarshe dan Allah ka duba maganar" ransa ne ya fara ɓaci ya ce"kunga please ku daina faɗa min irin waɗannan maganganun please wlh bazan iyaba okay ku rabu dani bance kowa sai yaji tausayina ba amma ni ina tausayin kaina Wlh bazan iya ba" cikin faɗa Jawaad ya ce"dole kace haka tunda kana tunanin ka gama da rayuwar yarinya kayi mata ciki ka yaudari mutane da dama da cewa baka sonta ka fake da cewa kayi ne saboda ta samu lafiya amma yanzu ka kasa yin abinda zaka taimaketa wlh Imad ka yi matukar bani mamaki kuma bari na faɗa maka idan har baka yarda an zubar da cikin nan ta daɗin rai ba toh wlh saina ɓallo maka ruwa sai na yi abinda ko kanaso ko bakaso dole ka bari a zubar saboda haka zaɓi ya rage naka"



Wani banzan kallo Imad ya yi masa sannan ya ce


"Idan ka fasa baka ƙaunar Allah da Annabi Jawaad wlh babu wanda ya isa ya sanya ni nayi abinda banyi niyya ba kuma Wlh kowane zaka faɗa wa bazan bari a zubar da abinda ke cikin yarinyar nan ba saboda haka karka fasa kaje duk inda zaka"


Waje Jawaad ya yi bai ce komai ba zuciyarsa a matuƙar ɓace, kallonsa Kamal ya yi kafin ya yi magana ya ɗaga masa hannu ya ce"dan Allah Kamal" shuru ya yi bai faɗi abinda y yi niyya ba yace masa "ina take?" nuna masa ɗakin ya yi sannan yabar wajen.







Zaune yake gefenta yana bata tea a hankali take karɓa ko rabi bata sha ba ta girgiza masa kai babu yanda bai yi da'ita ba taƙi karɓa hakan yasa ya ajiye, komawa tayi ta kwanta tana sauke numfashi kusan 5mins sai kuma ta ce"Uncle" da sauri ya ce"na'am" "ka siyamin mango please" shafa kanta ya yi ya ce"mango ki ke so?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"toh bari na siyo miki amma kar kiyi bacci" gyaɗa masa kai tayi sannan ya tashi ya gyara mata duvet ɗin ya fice daga ward ɗin, waro idanunta tayi dukda yanda sukayi ciki bakinta na rawa ta ce" Da..Da ..Daddy!" riƙe hannunta ya yi yana jin kamar ya fashe da kuka ya ce"Faɗeematoh" fashewa tayi da kuka tanajin numfashi, girgiza mata kai Daddy ya yi ya ce"daina kuka irin haka kinji Faɗemah I'm sorry ni ne duk na jawo miki kinji I'm so sorry Fateemah I'm....." Kasa ƙara sawa ya yi saboda wani kuka daya ci ƙarfinsa rabonda ya yi kuka a rayuwarsa har ya manta sai yau dalilin abinda Imad ya yiwa Fattomah, shafa kanta ya yi ya ce"don't worry dear karki damu zanyi abinda ya kamata zan kwato miki haƙƙinki" Kallon Jawaad ya yi ya ce"ɗauketa Jawaad" okay Jawaad ya ce sannan ya ɗauketa kamar yanda Daddy ya bashi umarni suka fita daga asibitin.




Kai tsaye Airport suka shige inda jirginsu ke jiransu cikin mintuna kaɗan jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja.



Kalle-Kalle ya shiga yi a ward ɗin amma bai ga alamar ta ba, har toilet ya duba amma babu Fattum fitowa ya yi yana ganin wata nurse ya ce"hyyy please Kinga inda Fattomah tayi?" da yake sun santa ta ce"Eh sir General Ibrahim ya tafi da'ita tun ɗazu" ji ya yi gabansa ya yi wani irin mugun faɗuwa ya ce"yaushe?" ta ce"sun ɗan jima dan gaskiya yanzu sun kai Abuja" bai tsaya sake sauraronta ba ya yi waje cikin tashin hankali. Cikin yan mintuna ya gama haɗa komai zuwa rabin awa jirginsa ya sauka cikin garin ABUJA.




Sosai yake kallon compound ɗin gidan ganin motoci dayawa yasa ya tabbatar da cewa ba Daddy ne kaɗai ya dawo ba, ko sallama bai yiba ya shiga parlon. Zaune ya tarar dasu da alama wani tattaunawa suke akan maganar, tsayawa ya yi daga gefen kujera yana kallon Mommy ko gaisheta bai iya yiba ya ce"Mommy ina FATTOMAH?" kallonsa kawai tayi amma batace komai ba ya kalli Daddy wanda yake kallonsa tunda ya shigo, Jawaad ne wanda ke zaune gefen Daddy ya kalla ya ce"tana ina Jawaad?" shiru shima ya yi masa ya yi tsaki sannan ya kalli Daddy ya ce"Daddy she's under medication Bai kamata ka ɗaukota daga asibiti ba kamata ya yi......" Wasu maruka da Daddy ya yi masa ya sanya ya riƙe kuncinsa kafin ya yi magana Daddy yara magana cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin rai

"Kai har kanada bakin magana?, har kanajin zaka iya zuwa ka tsaya a gabana Saboda bakada kunya kenan?, na baka yarinya amana kawai ka zauna da'ita na wata uku shine abinda ka kasa, har ka iya saka hannun ka dinga dukanta, ka zageta kaci mutuncinta duka bai isheka har ka iya yi mata ciki bayan lalurar daka sanya mata kuma shine yanzu ka iya takowa kazo nan wajen ko?"


Shiru Imad ya yi bai ce komai ba Daddy ya cigaba faɗin"wallahi idan har sunana Ibraheem Baira babu kai babu Fateema har abada babu wata alaƙa da zata haɗaku sannan cikin dake jikinta sai an zubar dashi a yau ba sai gobe ba kai kayi kaɗan ka raina min hankali ba'a haifi ɗa ba, zan nuna maka true colour na yanzu" afusace Imad ya kalli Daddy da duk sauran mutanen dake parlon sai kuma ya ce

"Daddy I'm sorry abinda ya faru zan kuma karɓi laifina duk inda za'a je amma wlh bazan taɓa yarda a zubar da abinda ke cikin yarinyar ba saboda daga shi bazan taɓa samun wani ba kamar yanda ka sani a baya yanzu ma haka take saboda haka na shirya karbar kowane irin hukunci amma banda na cire cikin dake jikinta I'm sorry"


Murmushi Daddy ya yi sannan ya ce"Okay mu zuba mu gani tsakanin ni dakai zan ga mai gaskiya" Mai martaba ne ya mike yana kallonsu ya buɗe baki zai magana, ɗaga masa hannu Daddy ya yi ya ce"babu ruwanka Muhammad banason kowa ya shiga maganar nan kowa ya yi shiru" shuru mai martaba ya yi dan tunda yaga Daddy ya yi haka to ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci kuma abune ma wuyaci ya sakko. Kallon Imad ya yi ya ce"banason ganin cikin gidan nan ina the next 10mins kabar gidan nan" Imad ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi amma ka fara kirawon Fattomah saboda tare zamu.........." Wasu tagwayen maruka Daddy ya ƙara sauke masa a fuskarsa zuwa lokacin fuskar tayi jajawur saboda kasan cewar sa fari cikin zallar ɓacin rai Daddy ya ce


"Wlh na rantse da Allah baka isa ka ɗauki yarinyar nan ba har ƙarshen rayuwarka kuwa sannan kuma abinda ke cikinta tamkar an zubar dashi ne ka rubuta takardar saki ka turon kamar yanda na tsara"


Cikin zallar ɓacin rai Imad ya shige cikin bedroom ɗin Mommy, da kallo suka bisa har ya fito hannunsa riƙe da Fattomah wacce take kallonsa sai rarraba idanu take, yana zuwa ya kalli Daddy ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi da'ita saboda she's under medication kamar yanda na faɗa ba zai yiwu abarta haka ba" gaba ya zo zai yi Daddy ya sha gabansa yana yi masa wani irin mugun kallo mai cikeda ma'anoni daban-daban ya ce".



*End of book 1*


*Shin mene ne abinda Daddy zai ce?*
*Shin wane hukunci zai yanke akan Imad?*
*Shin dagaske za'a zubar da cikin dake jikin FATTOMAH ko A'a?*
*Shin FATTOMAH zata auri yaya Jawaad ko A'a?*
*Shin da gaske Kamal zai aureta ko A'a?*
*Shin IMADUDDEN zai cigaba da zama da FATTOMAH ko kuwa za'a raba auren kamar yanda Daddy ya yi Alkawari?*
*Shin Ammi zata dawo Kano ko

Please Login or Register in order to submit comment