Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinji" gyada masa kai tayi sannan ya ci-gaba da tafiyar. Wani pharmacy ya tsaya ya siya mata magunguna Sannan suka fito tafiyar 5mins ta kawosu wajen wani suya spot Banda ƙamshi mai daɗi babu abinda yake tashi a wajen fita ya yi ya karɓo kaza leda biyu sai chilli yoghurt daya siya sannan ya dawo, da idanu kawai Fattomah ta bishi har ya sake barin wajen.





Zaune suka tadda Mommy tana danna system da alama wani abun mai muhimmanci take gabatarwa, sallama sukayi ta ɗago idanunta tana kallonsu zare glass ɗin idonta, kwanciya Fattum tayi akan cinyarta tana lumshe idanunta sosai take jin Mommy tamkar Amminta kodan saboda yanda itama ta ɗauke ta matsayin ƴa ne????, Zama ya yi suka gaisa da Mommy sannan ya kalli Fattum wacce take shirin fara bacci ya ce"keee zo nan" a hankali ta miƙe tana tafiya kamar bata so ta ƙara so wajensa hannunta ya kama ya zaunar da'ita gefensa sannan ya buɗe ledar da ya shigo da'ita, kallonsa ta tsaya tana yi har ya kutsuro kazar yana kallonta ya ce"haaaa" babu musu ta buɗe bakinta ya dinga bata kazar har Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya bata maganin ya miƙe ya ce" yanzu kije ki kwanta saida safe" tashi tayi ta shige apartment ɗinta shi kuma ya yiwa Mommy sallama, Mommy ta ce"wai lafiya naga ka dawo da'ita da daren nan?" murmushi ya yi ya ce"rigima ta sanya sai na dawo da'ita kuma zazzaɓi take" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya fita, nima da naga dare ya yi kuma ga Meeyrah ta sanyani gaba da kallo yasa na tattara alƙamin na ajiye naje na kwanta.


*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*
[5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*


*PAGE 15-16*


Kusan 5days kenan basu haɗu da Imad ba dan daman Jawaad ne mai nemansa sosai kuma shima ransa ya ɓaci, kasancewar yau Friday yasa da wuri suka tashi daga makaranta, tsaye suke itada Aysha tana mata hira wacce ita kaɗai take abarta dan Fattomah ba saurarenta take ba, tsaki Aysha ta yi tana kallonta ta ce"wai ke wannan wane irin wulaƙanci ne ina yi miki magana kin yimin shuru" langwaɓar da kai ta yi ta ce"bana cikin yanayi na magana ne Aysha please ki rabu dani" murmushi Aysha ta yi ta ce"shikenan thank you" gaba ta yi Fattum ta bita da idanu dan ko ajikinta. Har wajen 12:30pm babu wanda ya zo tafiya da ita hakan yasa ranta ya ɓaci duba jakarta ta yi taga tanada kuɗi hakan yasa ta tsayar da keke napep ta sanar dashi inda zai kaita sannan ta shiga, shiga parlon ta yi bayan tayi sallama babu kowa cikinsa sai tv dake faman aiki ita kaɗai hakan yasa tayi shigewarta apartment ɗinta dan a matuƙar gajiye take, wanka kawai tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar riga ta lace ɗinkin bubu sosai ya yi mata kyau musamman yanda maroon colour ɗin ta haska fatarta, veil ta ɗauko fari ta sanya sai takalmi half cover shima fari yi tayi kamar amarya dalilin mayafin data ɗora akanta, wasu yari da sarƙa ne na gold wanda Mommy ta bata ta ɗauko ta sanya sannan ta saka agogo wanda yaya Jawaad ya siya mata lokacin da suka je super market, Masha Allah sosai Fattomah tayi kyau abinta bazaka taɓa cewa she's under 16yrs ba domin ko ƴar 20yrs ba zata gaya mata cika ido ba sannan kuma nutsuwarta dan idan ba magana tayi maka ba bazaka taɓa ganin yarintar tata ba da zarar tayi magana tofah zaka gane yarinya ce.




Fitowa parlon tayi tana faman zuba ƙamshi murmushi Jawaad ya yi yana kallonta ya ce"enyeeee kinyi kyau sosai princess" rufe fuskarta tayi da hannunta cikin shagwaɓa ta ce"Allah yaya bansooo" yanda tayi maganar ya kwaikwaya ya ce" Allah kanwa inasoo" tuntsirewa da dariya ta yi shima yana taya ta ya ce"nima ai na iya shagwaɓar" turo bakinta wanda yasha lip gloss ta yi ta ce"Allah babu kyau" murmushi ya yi ya ce"shikenan muje lokaci na tafiya" gaba ya yi tana biye dashi abaya har suka fice daga cikin parlon.




Kalle-Kalle kawai Fattomah keyi tunda suka shigo cikin gidan sarkin wanda bata taɓa zuwa ba kafin sannan, sosai gidan yake bata sha'awa dan tana shige shi idan zata tafi Makaranta, ko ina suka shige bayine ki tsugunawa suna gaishesu ita ce kawai take mayar musu da murmushi shi kuwa Jawaad ko kallon inda suke ba ya yi, a babbar fadar gidan suka zaune inda nan ne suka tadda mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Baira, murmushi ya yi yana kallon Fattomah ya ce"sannu kinji" yanda ya yi maganar tamkar Daddy ne ya yi yanayinsu ɗaya kana ganinsu kasan sarauta da arziƙi ya gama ratsa su, sunkuyar da kanta ta yi hakan yasa Jawaad ya ce"Dad wai kunyar ka take ji fa" murmushi mai martaba ya yi ya ce"wai haka Faɗeemah?" Saurin girgiza kanta ta yi tana kallon Jawaad, murmushi Jawaad ya yi ya ce"hakane mana"turo baki tayi amma batace komai ba saboda mai martaba da yake wajen, sosai ya dinga janta da hira tun tana sunkuyar da kai har ta saki jikinta itama tana bashi amsa. Sai wajejen ƙarfe 6pm sannan suka baro gidan sarkin kai tsaye kuma gidansa suka shige, suna shigowa gidan bayan ya yi parking ta kalleshi ta ce"wai yaya naga ka kawoni nan?" Yana kashe motar ya ce"E, meya faru?" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"Ni fa gida zan koma" Jawaad bai ce mata komai ba ya sauka daga motar ya shige gidan da kallo ta bisa tanajin zuciyarta na tafarfasa wato yama mayar da ita ƴar iska, kwafa tayi sannan tabi bayansa tana turo baki, zaune ta tarar dashi yana magana da Ayrah wacce take zaune gefensa kamar ta shige jikinsa, sunkuyar da kanta ta yi ta shige bedroom ɗin ba tare da ta yarda ta kallesu ba.



Murmushi ta yi tana kallon Daddy ya ce"Eh mana yaushe zaku gama ni kuma nayi alƙawarin kai ki kamar yanda nace" dariya Fattomah ta yi ta ce"sauran 3months kaga yanzu Waec zamu fara" Daddy ya ce"okay toh Allah ya bada sa'a dear" murmushi ta yi ta ce"Thank you Daddy", murmushi Daddy ya yi lokacin da Imad yake zama gefensa bayan ya yi sallama cikin parlon da sauri Fattomah ta miƙe tana shirin barin wajen Daddy ya ce"ina kuma zakije Fattum?" cikin rawar murya ta ce"Daddy zan ɗan duba abune a ɗaki"okay Daddy ya ce sannan ta fice daga parlon da sauri har tana ƙoƙarin tuntube. Taɓe baki Imad ya yi bayan yaga shigewarta, kallonsa Daddy ya yi ya ce"Imad daman inason magana dakai" kallonsa ya yi ya ce"ina jin ka Daddy" Daddy ya ce"in sha Allah next week zamu tafi Abuja kasan daman zama nake temporary anan, kuma akwai abubuwa dayawa" kallonsa Imad ya yi ya ce"Okay Daddy Allah ya kaimu" tashi ya yi ya ce"Ameen zuwa gobe zan sanar dakai abinda ake ciki" tashi shima Imad ɗin ya yi yana zube hannayensa cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya ce"Allah ya kaimu bari naje wajen Mommy"okay Daddy ya ce sannan shima ya yi waje.






Shiru Fattomah ta yi tana zaune tsakiyar royal bed ɗinta banda tunani babu abinda take, hawayene suka fara sintiri akan fuskanta tunanin Abbanta take Allah sarki rayuwa tasan da yanzu duk inda yake daya nemata yafi a ƙirga sannan ga rashin Ammi wanda shima yake matuƙar taɓa mata zuciya dukda babu abinda ta rasa cikin gidan Daddy amma ko yaya da tana ganin gilmawar iyayenta zata ji daɗi gashi batasan wanda ma zata tambaya akan maganar ganin Ammi ba tabbas Amminta tayi mata nisa sosai tuna hakan yasa ta sake fashewa da kuka wannan karan har saida muryata ta fito, kwanciya tayi kan gadon tana rufe fuskarta jikin filo ta ci-gaba da kukanta.





Tashi ta yi kanta nayi mata ciwo hakan yasa tana yin wanka ta fito a hankali kamar me tsoron wani abu haka ta buɗe ƙofar apartment ɗin nasa, wani irin ƙanshi ne ya daki hancinta lumshe idanunta ta yi sannan ta buɗe su cikin kyakkyawan parlon wanda ya gaji da haɗuwa, kallon parlon ta shiga yi kamar bata taɓa ganinsa ba koda yake a rayuwarta zata iya girƙa shigar ta ɗakin, domin Imad baya bata damar shiga ɗakin saidai su haɗu a nata ɗakin




"Lafiya??"


A ɗan firgice ta juyo suka haɗa idanu dashi, saurin sauke idanunta ƙasa ta yi ya ce a gajarce"mene?" haɗa nutsuwarta ta yi sannan ta ce"daman kai na ne yake min ciwo shine nace bari na sanar dakai please ka bani magani" ba tare da ya kalleta ba ya yi gaba yana faɗin" ki shirya ki fito" okay ta ce sannan tabi bayansa. Kallonsa Jawaad ya yi ya ce"amma Imad sai yanzu zaka kawota asibiti kenan?" haɗe ransa ya yi ya ce"bangane ba yaushe ka keson na kawota?" girgiza kai Jawaad ya yi ya ce"wannan fa ba daidai bane kaga jikin nata har ya fara worth da ka sanar dani ai sai nazo na dubata a gidan" wani shegen kallo Imad ya yi masa ya ce"toh babana Jawaad Allah ya baka haƙuri" murmushi Jawaad ya yi ya ce"ai gaskiya ka faɗa" harararsa ya yi bai ce komai ba Jawaad ya ce"nasa ansaka mata drip kuma sai ya ƙare za'a cire saboda haka kana iya tsayawa ka jirata" miƙewa Imadudden ya yi ya ce"no idan angama driver zai zo ya tafi da'ita ni inada wajen zuwa" da kallo Jawaad ya bisa dan ya kasa magana, ganin kamar ya tafi tunani yasa Imad ya daki table ɗin gabansa, da sauri ya ɗaga idanuwansa ya kallesa ya ce"sorry na tafi wani tunanin ne shikenan muje na rakaka" waje ya yi yana biye dashi har suka isa parking lot na asibitin, saida yaga ya bar asibitin sannan ya sauke numfashi yana jinjina hali irin na Imad tabbas halinsa ya banbanta dana mutane ko kaɗan mace bata gabansa idan ba haka ba ya ci ace Imad ya haifi ɗa ko ƴa saboda aƙalla ya kai shekara 5 da aure amma idan da za'a zauna to za'a iya ƙirga tarayyarsa da Salma, tun tana jin haushinsa har itama ta saba da rayuwa a haka wanda hakan babbar illa ce ga rayuwar ma'aurata.






Shuru Ayrah ta yi tana nazarin maganganun da Ameesha ta faɗa mata tabbas sai yanzu abun yake kawowa kanta, ganin kamar tunani take yasa Ameesha ta ce"ke a tunaninki yana kawota gidan nan ne saboda tana matsayin ƴar uwarsa?, meyasa shi wanda babansa ne ya ɗaukota bai ɗauketa ya kaita gidansa ba, ke kuma saboda baki san ciwon kanki ba shine kike wani sakar mata fuska har take da zarafin shiga cikin bedroom ɗinki wanda ya kasance sirrinki keda mijinki Wlh kin bani mamaki Ayrah bansan yaushe kika zama haka ba domin nasan ba halinki bane" ajiyar zuciya Ayrah ta sauke tana kallon ƙawartata ta ce"ni Kawai na ɗauke ta matsayin ƙanwata ne ganin yarinyar marainiya ce kuma tanada hali mai kyau Fattomah batada matsala gashi naga yanda suke ji da'ita cikin family ɗinsu kinga nima idan inason zaman lafiya dolena na so abinda mijina ke so" da wani expression Ameesha ta kalleta har ta gama maganganunta sannan ta yi tsaki ta ce"amma wlh kin bani mamaki wato saboda kin makance cikin soyayyar mijinki ya sanya har zaki ɗauki wannan kasadar toh ki zauna wlh zaki ce na faɗa miki kina nan zaki je ana rangaɗa guɗa ankawo sabuwar amarya daga nan zai fara daina kulaki tunda ya samu ƴar yarinya under 18yrs Kuma ƴar uwarsa kinga ta ko'ina bakida amfani danginsa zasu koma san ƴar uwarsu ke kuma kinzama shara bola mara amfani" shuru Ayrah ta yi tana kallonta duk hankalinta yabi ya tashi idan da abinda tafi ƙauna a rayuwarta to mijinta ne kwata-kwata batasan abinda zai rabata dashi ko me ƙanƙantarsa, tana matuƙar kishin mijinta idan kuwa hakane to zata ɗauki matakin gaggawa ga Fattomah dan bata shirya rabuwa da mijinta ba kuma bata shirya zama da kishiya ba, katse mata tunani Ameesha ta yi ta hanyar faɗin


"Ni zan tafi amma ki sake tunani akan maganar nan zaki ce na faɗi gaskiya sannan koda na kwana ɗaya ki saka idanunki akansu zaki fahimci abinda nake faɗa miki"


Miƙewa Ayrah ta yi duk jikinta ya yi sanyi ta ce"shikenan I'll do so in Sha Allah nagode Ameesha" murmushi ta yi ta ce"karki manta babu wannan a tsakaninmu yi wa kai ne" ajiyar zuciya Ayrah ta yi sannan tai murmushi ta ce"sai anjima muje na rakaki"okay ta ce sannan suka fita a parlon, suna cikin magana bayan sun fito Fattomah ta fito daga cikin motar tana sanye cikin wata abaya black colour ta yi rolling kanta da veil ɗin abayar babu komai a hannunta sai wayarta ƙirar iphone 13pro Max wacce yaya Jawaad ya siya mata, kallonta suka tsaya yi domin yanda tayi wani siritaccen kyau kamar ba itaba kullum sake canza kama take abinta, da murmushi a fuskarta ta ƙaraso wajensu tana zuwa ta kallesu cikeda farin ciki da sakin fuska ta ce" laaaaa Aunty Ameesha kece a gidan?" wani kallon banza Ameesha ta watsa mata sannan ta ce"Eh" shuru Fattomah ta yi lokaci ɗaya murmushin fuskanta ya yi padding dukda batasan abinda ya sanya tayi mata hakan ba amma taji babu daɗi, kallon Ayrah ta yi taga ta ɗauke kai bata kawo wani abu ba ta shige cikin gidan with thousands of though on her mind, saida ta shige Ameesha ta bita da harara sannan ta kalli Ayrah ta ce"kinga munafuka ko?" kwafa Ayrah ta yi ta ce"karki damu ki barni da'ita dani take zancen" murmushi Ameesha ta yi sannan ta ce"bari naje mayi waya"okay Ayrah ta ce sannan ta shige motarta ita kuma ta koma gidan.




*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*


*Like nd share*
[5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


PAGE 17-18.


Zaune ta tarar da Fattomah idanunta akan wayarta da alama wani abu mai muhimmancin take yi a wayar, kallo ɗaya Ayrah ta yi mata ta ɗauke kai banda maganganun Ameesha babu abinda ke yawo cikin kwakwalwarta kallon Fattomah ta yi jin yanda ta yi shuru ta ce"Aunty Ayrah naji kin yi shuru ko wani abun ya faru ne?" batareda ta kalleta ba ta ce"babu komai" bata sake cewa komai ba ta miƙe ta haye sama, da idanu Fattum ta bita tana mamakin abinda ya sameta wanda ya sa ta canza lokaci ɗaya ita dai tasan ita ta kirata tazo zasu dafa wani kalar abinci amma gashi tazo ta rar da Ameesha wacce ada suke wasa da dariya ta haɗe mata rai yanzu kuma Aunty Ayrah tabbas akwai abinda ba daidai ba ko mene ne?????, Rashin sanin wanda zai bata wannan amsar ya sanya ta maida hankalinta kan wayar hannunta tana cigaba da chat ɗin da take da class mate ɗinta, tana shiga ɗakin ta zauna gefen gadon haka kawai taji har shi Jawaad ɗin haushinsa take ji dukda bata tabbatar da abinda Ameesha ta faɗa mata ba amma taji tana son Fattomah ta nisanta da'ita domin tabbas aka cigaba da tafiya a haka watarana sai Jawaad yaji yana son aurenta musamman idan tafi haka girma tunda kullum ƙara girma take hallitarta na sake fitowa tana sake zama cikakkiyar mace, da wannan tunanin har bacci ɓarawo ya ɗauketa bata saniba.






Tsayawa tayi bakin titin tana jiran napep wanda zai kaita gida dan gaba ɗaya bata jindaɗi duk ta zama moody saɓanin yanda ta fito daga gida cikeda farin ciki, har ya yi gaba ya hangota ta cikin mirror ɗinsa hakan yasa ya komo baya kaɗan dan ssmun zarafin yi mata magana, ganin mota ta tsaya gabanta ya sanya ta ɗanyi baya kaɗan gudun kada ya takura mata wajen samun abun hawa, kashe motar ya yi sannan ya fito yana sanye cikin wata dakkakiyar shadda milk colour sai sheƙi take ya ɗora hularsa zanna bukhar akansa, hannun maƙale da agogo ya sanya gilashi a kyakkyawar fuskarsa haɗaɗɗen saurayine irin ajin farkon nan kana ganinsa kasan kuɗi ya zauna daram a wajensa, kallonta ya yi yaga kwata-kwata bata kalli inda yake ba hakan yasa y rufe motar tashi sannan ya tako cikin tafiyarsa ta isasshen namiji ya ƙaraso gabanta



"Assalamu alaikum"


Juyowa tayi tana kallon wanda yake mata sallama dan ita dai tasan ita kaɗai ta fito batareda wani ba kuma babu kowa a wajen da take, idanu biyu sukayi da Kamal wanda yake sakar mata wani kyakkyawan murmushi, shuru Fattomah ta yi ba tace komai hakan yasa ya ce"haba baiwar Allah ko bazaki kulani ya kamata ace kin amsa sallama a matsayinki na musulma ko?" shiru ta yi sai kuma ta ce "wa alaika salaam" murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"yawwa nagode sosai" bata sake ce masa komai ba kusan 2mins hakan ya sa ya ce"dan Allah idan bazaki damu ba kibani number wayarki idan yaso sai nazo gidanku later" da sauri ta kalleshi taga ya kashe mata ido ɗaya saurin ɗauke kanta ta yi sai kuma ta ce a hankali"nikam karka dameni please" dariya Kamal ya yi ya ce"toh Madam ai girmanki ne yanda kika ce haka za'a yi" taɓe baki Fattum ta yi dan har cikin ranta ya fara damunta da magana gashi babu alamar napep a hanyar daman kuma titin ba'a fiye samunsu ba duk sai motocin gida, numfasawa ta yi sai kuma ta ce"nifa ka tafi please kada ma wani ya ganmu tare" Kamal ya ce"idan baki so aganmu a hanya kibani address naki sai nazo nima banason tsayar dake akan hanya ko kuma ki shiga motana na kai ki inda zaki sai mu ƙarasa maganar" wani kallon kayi hauka Fattomah ta watsa masa sannan ta ce" Allah ya kiyaye na shiga motar namiji har abada" girgiza kai Kamal ya yi sai a sannan ya fahimci cewa yarinya ce kuma daman auran irin su shine muradin zuciyarsa tabbas sai ya mallaketa matsayin matarsa. Ganin lokaci na tafiya yasa ya ce"ki bani number kin ji dan Allah" ajiyar zuciya ta sauke kusan 2mins sai kuma ta fara karanto masa numbern wayartata,




"Fattomah!"

Aɗan firgice ta juya inda sukayi 4eyes da yaya Jawaad sai taji gabanta ya faɗi dukda bawai tsoronsa take jiba kuma tasan babu abinda zai mata amma sai taji kamar bata kyauta ba, kallonsa Kamal ya yi sai kuma ya kalleta ya ce"Kinsan shi ne?" gyaɗa masa kai tayi tana sauke kanta ƙasa cikin sassarfa ya ƙaraso wajen without looking at her ya ja hannayenta kasa cewa komi Fattomah ta yi har ya sanyata amotar sannan ya shiga cikin ƴan sakwanni suka ɓace daga wajen, da kallo Kamal ya bisu har sukayi disappearing a wajen kallon wayarsa ya yi yaga ta gama sanya masa numbern hakan yasa bai damu ba ya koma tasa motar shima yabar wajen.






Har suka je gida Jawaad bai ce mata komai ba amma kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake, yana gama parking ya fice daga cikin motar bai ko kalleta ba samun kanta tayi da kasa fitowa daga cikin motar dan ko ba'a faɗa mata ba tasan yaya Jawaad fushi ya yi da'ita ga abinda ya faru ɗazu ita da Ayrah shiyasa ma tabar gidan bata jirasa ba, kusan 10mins tana cikin motar kafin a hankali ta fito daga ciki ta shiga cikin gidan kamar wacce kwai ya fashewa ajiki.





Bataga kowa cikin parlon ba hakan yasa Kawai ta shige bedroom ɗinta dan daman batason haɗuwa dashi, har akayi sallar magrib Fattomah bata fito ba, kwata-kwata ta kasa fitowa parlon gudun kada ta haɗu da yaya Jawaad ga wata uwar yunwa da take ji dan rabonta da abinci tunda tayi breakfast ganin babu sarki sai Allah ya sanya ta sakko daga kan gadon ta ɗaura veil ɗinta sannan ta fito parlon tana ƴan kalle-kalle, gabanta taji ya faɗi ganinsa da tayi zaune kan kujera 2seater yana operating laptop ɗinsa kasa ƙarasowa gabansa tayi unlike da da take zama tana kallon abinda ya ke yi suna hira, ji tayi wasu hawaye sun zubo mata ta sanya hannuta ta share sannan ta shige cikin kitchen ɗin da sauri ta fito ganin Ayrah tsaye da alama abinci take dafawa, rasa inda zataje tayi hakan yasa a hankali kamar me koyan tafiya ta ƙarasa gaban Jawaad.





Tsugunawa ta yi daidai wajen ƙafafunsa cikin rawar murya ta ce" yaya Jawaad" shuru ya yi mata babu reply badan bai ji abinda ta ce ba, sau uku tana kiran sunansa amma ya ƙi amsawa wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, cikin sanyin murya da kuma rauni take cewa


"Dan Allah dan Annabi yaya Jawaad kayi haƙuri wlh ba laifina bane ko kulashi banyi ba dan Allah yaya" rufe system ɗin gabansa ya yi sannan ya zuba mata narkakkun idanunsa akanta, sunkuyar da nata tayi dan bata iya jure kallonsa, kusan 3mins suna haka sannan ya ce"wane shi?" girgiza masa kai tayi ta ce"wlh ban sanshi ba" "amma kike kulashi har kike ganin kin isa tsayawa da samari akan titi daman irin tarbiyyar da aka miki kenan?" girgiza masa kai kawai take dan ta gagara magana batasan da wani harafi zata yi masa bayani ya fahimceta ba sai faɗa yake mata akan abinda bata da laifi, cikeda masifa wacce batasan Jawaad ya iyata ba yake cigaba da faɗin


"Wlh Fattomah duk ranar dana sake ganin kamamancin wannan abun ya faru nayi miki alƙawarin ɓata miki rai irin wanda ba'a taɓa yi miki ba, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci daga ke har shi shegen wanda kike kulawar, har yaushe kika yi girman kula saurayi nawa kike?, You Are just 15yrs amma kina tunanin namiji kodan kin ganki da girman jiki?, toh ki sani ko nan da 2yrs baki isa barinki tsayawa da wani ƙato ba bare yanzu shashasha kawai get out of my side"



Da sauri ta tashi har tana ƙoƙarin bigewa ta shige bedroom ɗinta tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananci kuka, kallonsa Ayrah ta yi bayan ta ajiye food flask ɗin hannunta ta ce"doctor lafiya?" tsaki ya yi ya ce"babu komai" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"haba dan Allah ai tunda naga kana wannan faɗan dole akwai abinda ta aikata dan Allah ka sanar dani" numfasawa ya yi sannan ya bata labarin abinda ya faru briefly. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke ta ce"toh akan wannan kake ta faman faɗa doctor macace fa dole daman ai maza su biyota musamman Fattum" wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"Eh tunda ita mace akuyace da ake barinta sakaka ke kina kamar shekarunta aka fara barinki tsayawa da samari?" Murmushi ta yi ta ce"Allah ya baka haƙuri yallaɓai ni da wasa nake, saida na kammala secondary school na shiga University sannan Daddy ya fara barinmu" harararta ya yi ya ce"okay shine ita kike son abarta tun yanzu ko?" girgiza kai tayi ta ce"tuba nake dear" murmushi ya yi sannan ta fara serving nasa.






Tashi tayi duk idanuwanta a kumbure dalilin kukan data kusan kwana tanayi, a hankali ta sakko daga saman without making any sound ta fice daga parlon, ko kallon masu gadin gidan bata yi taje ta buɗe ƙofa tayi fitarta, cikin Sa'a ta samu wani napep ya shiga ɗaukan ƴan makaranta ta faɗa masa inda zata ya ce to tahau suka tafi.




Murmushi ta yi ta ce"kayi kyau sosai doctor" jan kumatunta ya yi ya ce"kema haka dear" dariya ta yi ta ce"mu tafi?" girgiza kansa ya yi ya ce" kirawo Fattum" haɗe rai ta yi sai kuma ta juya ta shige bedroom ɗin da take, kalle-kallenta ta gama ta fito tana kallonsa ta ce"dear bafa ta cikin ɗakin" da mamaki Jawaad ya ce"kamar ya?" ɗaga masa kafaɗa tayi alamar bata sani ba, da kansa ya shiga ɗakin dan tabbatar da gaske Fattomah bata ciki ɗin, tsaki ya yi sannan ya fita wajen masu gadi zuwa sannan hankalinsa ya fara tashi yana zuwa ya kalli gateman ɗin ya ce"kai ina kaga Fattum?" cikeda ladabi yake cewa" yallaɓai naga sanda ta fita ina yi mata magana taƙi kallona wajen 3hrs kenan" da mamaki Jawaad yake furta kalmar ta fita ɗin toh ina ta tafi da safiyar nan da sauri ya shiga motarsa Ayrah ma ta shiga sannan suka bar gidan.





*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*


*Like nd share*[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.



PAGE 19-20.



A hankali yake ƙarewa farfajiyar gidan kallo wacce ta kasance iya ganinka sosai ya

Please Login or Register in order to submit comment