Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi sannan ta ce"yarinyar dake gidan nan Fattomah da'ita zamu yi amfani wajen aiwatar da abinda muka yi niyya batareda kowa ya zarge muba idan har zaki iya yin abu yanda na tsara wlh zamu samu nasara kawai ki cire tsoro malama" numfasawa Salma ta yi ta ce"zanyi tunani akai Ameesha dan bazanyi abinda zai dawo kai na ba wlh nasan halin Imadudden bashida mutunci idan yaso kome zai iya aikatawa saboda haka bazanyi Abinda zan jawo a ɗaureni ba gwara na rabu dashi cikin mutuntawa" miƙewa ta yi daidai lokacin suka shigo cikin parlon bakinsu ɗauke da sallama, da kallo suka bisu har suka zauna sannan suka gaisa Jawaad ya ce"Ameesha ke ce anan?" murmushi ta yi ta ce"wallahi fa Doctor na ɗan shigo sada zumunci ne ya Ayrah?" "tana nan klao Alhamdulillah" "Masha Allah". Satar kallon Imad ta yi taga ko inuwarta bai kalla ba hakan yasa ta ce"yallaɓai ina yini"


"Lafiya"


Abinda kawai Imad ya ce kenan ya ɗauke kansa yana cigaba da danna wayarsa, shuru Ameesha ta yi dan daman tasan haka zata iya faruwa dan tun ba yau ba Imadudden baya wani ƙaunarta dan murmushin yaƙe ta yi ta ce"toh Salma sai anjima" miƙewa ta yi ta ce"muje na raka ki" okay ta ce sannan sukai waje. Kallon Fattomah ya yi wacce take kwance kan kujera 3seater ya ce"tashi ki tafi " ahankali ta miƙe daga kwancen ta fara hawa stairs ɗin kamar ta waɗo har Allah ya taimaka takai ɗakin nata, saida ta shige sannan Jawaad ya ce"wai what wrong with her?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wai menstrual pain ke damunta shine fa harda kwanciyar asibiti" Jawaad ya ce"ayyah to Allah ya ƙara sauƙi ya rabata dashi kuma" Ameen Imad ya ce sannan ya cigaba da abinda yake.




"Kin gani ko Ameesha ke daga ganin irin kallon da Imad ke miki kinsan akwai wani abun a ƙasa nidai ki rufamin asiri ki rufawa iyayena idan zamuyi magana dake mu haɗu gidan Ayrah ko muyi chat idan ya zama worth akwai buƙatar na ganki ko park ne sai muje please" taɓe baki Ameesha ta yi ta ce"ke kam Allah ya yaye miki ai shikenan mayi wayar" okay ta ce sannan ta shiga mota ta fita ita kuma ta koma ciki, zaunar ta tarar dasu da alama wani abun suke tattaunawa hakan yasa tana yin sallama ta tafi zata hau sama


"Salma!"


Da sauri ta juyo jin ya kira sunanta, gani tayi ba ita ce wacce ya ke kallo ba amma tabbas da'ita yake hakan yasa ta dawo wajen ta zauna kan kujera


"Gani"


Ɗago dara-daran idanuwansa ya yi ya saukesu akanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idanun haka kawai taji gabanta na faɗuwa tabbas akwai abinda ya sanya ya yi mata wannan kiran, kusan 2mins sannan ya ce"karna sake ganin wannan yarinyar cikin gidan nan okay?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce"in sha Allah" kallon Jawaad ya yi ya ce"as i said before" ganin sun cigaba da maganarsu yasa ta miƙe ta haye sama tana dafe ƙirji.





Cikin kwanaki uku data ɗauka tana period tayi matukar shan wahala duk ta rame kamar ba itaba dukda yanda Imad ya yi ƙoƙari wajen ganin ta samu duk wani abu da take da buƙata har ta kammala sannan ta cigaba da zuwa makaranta zuwa yanzu kuma sun kusa fara yin Neco, murmushi ta yi tana kallon Fa'eeza ta ce"ke kam ki dinga jin tsoron Allah wallahi duk irin amsar da kika kwafa" dariya Fa'eeza ta yi ta ce"wallahi ƙarya kike Banason sharri ayaushe ai wallahi sai na faɗawa Daddyna dama ya sani bai biyamin anan makarantar ba" dariya suka hau yi mata Aysha ta ce"abanza dai tunda har kin fara zanawa" Shuru Fattomah ta yi ganin motarsa tsaye bakin gate ɗinsu sai na guards ɗinsa kusan guda biyar, kallonsu Aysha ta yi ta ce"sai anjima anzo ɗaukana" bye bye suka yi mata sannan ta tafi.





Zaune ta sameshi cikin motar yana danna system da alama wani abu mai muhimmanci yake gabatar dan duk attention ɗinsa yana can, shiru Fattomah ta yi bayan ta shiga tana jin wani sanyi na ratsata ga ƙamshin turarensa wanda ya haɗe da sanyi A.C ya bata wani irin sanyi mai ban sha'awa, lumshe idanunta ta yi tanajin duk wata gajiyarta na sauka kallonta kawai Imad ya yi ganin yanda ta fara bacci jikin motar ajiye system ɗin hannunsa ya yi ya ɗauko wata leda ƙarama a hannunsa buɗewa ya yi ya ɗauki wata injection saida ya gama haɗawa sannan ya matsa kusa da'ita ahankali cikin dabara ya yi mata allurar motsawa ta yi amma Saboda yanda baccin yake kanta ya sanya ta cigaba da abinta.




Fitowa ya yi daga toilet ɗin yana tsane jikinsa, wayarsa ce ta fara ringing ya ɗauka cikeda ladabi ya ce"ina yini Daddy?" Daddy ya ce"lafiya Imad kuna lafiya?" ya ce"Alhamdulillah Daddy ina Mommy?" "Tana nan, ka bawa Fateemah zan yi magana da'ita" kallon Fattomah ya yi wacce take ta faman bacci ya ce"Daddy bacci take wallahi saidai zuwa anjima ko gobe" okay Daddy ya yi Sannan ya yi hangup na kiran. Ajiye wayar ya yi sannan ya cigaba da gyara jikinsa saida ya gama shiryawa sannan ya ɗauko wani tablet sosai ya dinga tunani kusan 5mins sai kuma ya zaro wayarsa dialing number Doctor ya yi ring biyu ya ɗauka bayan sun gaisa ya ce


"Nifa ina ganin bazan iya ba she's to small" girgiza kai doctor ya yi ya ce "daurewa zaka yi saboda haka ne kawai taimakon da zaka yi mata kuma kaga yarinya ce beside kuma kai ɗin mijinta ne banajin akwai abinda ba daidai ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka kayi komai anutse muddin kayi mata injection ɗin to bazata ji wani zafi ba kuma bazata fahimta ba tunda daman batasan komai ba amma idan ba haka ba wallahi zata dinga shan wahala ne daga nan har sanda zatayi auren tunda Allah yasa tana dashi kawai ayi amfani da dama please sir" numfasawa Imad ya yi ya ce"shikenan naji I'll try my best in Sha Allah" okay ya ce sannan sukai sallama. Miƙewa ya yi yana sake kallonta ganin yanda take baccinta hankali kwance light ɗin ɗakin ya kashe sannan ya hau kan gadon.






Tsaki Kamal ya yi ya ce"kai ka fiye gaggawa to yarinyar yanzu tana kan rubuta exams ne so nake da zarar ta kammala sai naje muyi magana da iyayenta" dariya Saleem ya yi ya ce" na ɗauka ai yaudararka ta yi kamar sauran ƴanmanta naka" harararsa Kamal ya yi ya ce"banza kawai in Sha Allah sai na auri Fattomah sooner or later" murmushi Salem ya yi ya ce"Allah ya sa Friend nima haka nake fata".





Murmushi Khaltum ta yi ta ce"yawwa yaya dan Allah idan zaka je nima ka tafi dani inason ganin Fattum please" murmushi ya yi ya ce"ke nima fa duk a tsorace nake gashi banason nabar garinnan bamu haɗu ba wlh inama su bani ita muje taga Ammi" Khaltum ta ce"wallahi ba zasu baka ba kaga ko Ammi babu yanda ba tayi ba suka hanata ƴarta bare kuma kai" Fu'ad ya ce"idanma suka bari na ganta ai sun yimin zanji daɗi" murmushi ta yi ta ce"Allah yasa toh" .





Ahankali ta buɗe idanunta tana kallon inda take baccin ita dai tasan a mota tayi bacci amma yanzu ta ganta cikin bedroom wanda bata taɓa gani cikin gidan ba, tsorone ya kama Fattomah ta miƙe daga kwancen da take tana sake kallon ɗakin wani enlargement ɗin hotonsa data gani ya sanya taji relief to amma a ina ne nan?, yaushe tazo nan?, buɗe ƙofar akayi ya sanya ta kalli wajen kamar idanunta zasu fito shigowa ya yi hannunsa riƙeda drip yana ya ce"lafiya?" girgiza masa kai ta yi ya ce"tashi kije kiyi wanka" gyaɗa masa kai ta yi kawai sannan ta miƙe ganin yanda take tafiya ya yi har ta shige toilet ɗin sannan ya sauke ajiyar zuciya.



Babu kowa a bedroom ɗin sanda ta fito sai kaya da taga ya ajiye mata gefen gado shiryawa ta yi cikin abayar black colour wacce tayi mata kyau Masha Allah tana ɗaura veil ɗinta ya shigo yana kallonta ya ce"idan kin gama ki fita parlon ki ci abinci" toh kawai ta iya ce masa sannan ya juya ya fita, da kallo kawai Salma ke binta irin kallon tsanar nan ita kaɗai tasan abinda take ji cikin zuciyarta kamar ta kamata ta shaƙeta ta mutu musamman yanzu da ya fara mayar da hankalinsa akanta hakan yana matuƙar ƙona mata rai.




Fotwarsu kenan daga paper civic education wacce ta kasance ita ce paper ta karshe a Waec sosai suke farinciki da murna banda Fattomah wacce tayi shuru sai kallo da idanu, Aysha ce ta zo inda take zaune tana kallonta ta ce"wai ke ma aka yi miki ne?, kina gani anata hira amma kin zo nan kin wani zauna ke kaɗai" kallonta Fattomah tayi ta ce" ke ni ki kyaleni banajin daɗi wlh" harararta ta yi ta ce"to da waye yake jindaɗi kin fiye rainin hankali kefa" murmushi kawai Fattomah ta yi ta ce"wallahi da gaske nake banajin daɗi tun jiya duk jikina amace nake jinsa" Aysha ta ce"toh Allah ya baki lafiya yasa ki dinga jindaɗi" tsaki Fattum ta yi ta ce"kefa ƴar iska ce" dariya ta yi ta ce"ay addu'a nayi miki, sai ki tashi ki tafi gida" miƙewa ta yi ta ce"ko baki faɗa ba yanzu zan tafi Allah yasa driver yazo dan kawai so nake na jini akwance wallahi" taɓe baki Aysha ta yi ta ce"sannu ƴar hutu sai kije ki ta kwanciya har gobe ai daman ba wani aikin arxiƙi ki ke yi ba" murmushi ta yi sannan ta ce"byeeee" bye itama ta ce mata sannan tabar wajen. Tana shiga ta kwanta nan kan kujera a parlon nan da nan wani irin bacci mai nauyi ya ɗauketa, fitowa ta yi daga kitchen ta ganta kwance kan kujerar sai baccinta take hankali kwance tsayawa tayi akanta sai kiamtta juya ta koma kitchen freezer ta buɗe da ɗauki ruwa mai sanyi tana zuwa ta balle bottle ɗin ta sheƙa mata afuska a razane Fattomah ta miƙe kamar zata shiɗe take kallon Salma harararta ta yi ta ce"dan ubanki an faɗa miki nan parlon saboda bacci aka yisa?" shiru Fattomah ta yi ta cigaba da faɗin"duk randa na sake ganin kin zo kin kwanta anan wallahi sai ranki ya yi mugun ɓaci shashasha kawai" fashewa tayi da kuka ta miƙe daga kan kujerar ta haye sama tana cigaba da kukanta, tana shiga apartment ɗinta ta kwanta gefen gadonta tana cigaba da kukan har wani baccin ya ɗauketa. Kallonta ya yi ya ce"maybe next Friday ne tafiyar so get ready" zama Salma ta yi ta ce"ok Allah ya kaimu daman ni ashire nake" okay ya ce sannan ya cigaba da cin abincinsa, zama ta yi daga gefen kujerar tana kallonsa ta ce"Uncle" kallonta Imad ya yi ya ce"lafiya kuma?" shiru ta yi ya ce"keee I'm play with you?" girgiza masa kai ta yi ya ce"idan baki da abin faɗi tashi kibar nan" hawayene ya kawo idanunta cikin rawar murya ta ce"ko..koba aunty Salma bace ta watsa mini ruwa kuma banason ruwa ni" fashewa ta yi da sabon kuka kamar sannan aka yi abun, kallon Salma ya yi yaga ta ɗauke kai, kallonta ya yi ya ce" idan har ba zaki daina sheɗanci ba to za'a dinga yi miki abubuwa daban-daban karki nutsu ki zama kamar kowace mace ki cigaba da rashin hankali kinji" kallonsa kawai Fattomah ta yi hawaye na biyo idanunta bata taɓa zaton abinda zai ce mata kenan ba, miƙewa tayi jiki asanyaye zata koma sama



"Dawo Malama"


Dawowa ta yi ta tsuguna tana ɗauke idanunta, ya ce"ubanki ki ke kallo atanan?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce"Uncle Abbana fa ya mutu ka daina zaginsa please" baki buɗe Imad yake kallonta sai kuma ya ce"ni kike faɗawa haka?" girgiza masa kai ta yi ya ce"tashi anan wajen ko nayi ball dake shashasha kawai mahaukaciya" da gudu ta tashi daga wajen tana zuwa ta faɗa kan gadon tana sakin wani raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Fattomah take kuka har tana ƙoƙarin shiɗewa kullum sake tsaanr zaman gidan take, kullum ji take inama ita ce wacce ta mutu tabar Daddy araye da ta huta ganin irin wannan tsanar tunda take ba'a taɓa tsanarta arayuwa irin yanda Imadudden ya tsaneta ba kowa ƙaunarta yake batasan mene ne tsangwama ba saida ranar data fara haɗuwa da Imad gashi har yau bai daina nuna mata irin wannan tsanar ba, tunanin wani abun tayi aranta yasa ta miƙe daga kwancen ta goge idanunta sannan ta tashi wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko trolley ta fara jera kayanta ciki kamar wacce zata bar gari.





Wajejen ƙarfe 12pm ne ta fito daga ɗakin nata without making any sound take tafiya kamar wata mara gaskiya, ahankali ta fita daga cikin parlon tana ɗan waige-waige gudun kada wani ya hangota, tafiya ta fara yi har takai bakin gate tana ƙoƙarin buɗewa gateman ɗin dake wajen ya ce


"Keee ina ne inda zaki cikin daren nan?"


Hannayenta guda biyu ta ce"dan Allah dan Annabi ka rufamin asiri ka barni na fita kaji dan Allah karka faɗawa Uncle ka barni na fita daga nan gidan dan Allah wallahi zan iya mutuwa idan na cigaba da zama agidan nan" murmushi matashin saurayin ya yi ya ce"kiyi haƙuri bazan iya bari ki fita ba kuma bazan faɗawa mai gida ba ki koma ki kwanta idan safiya tayi sai ki faɗa masa gaskiya kina son kibar gidan nan ina ganin kamar zai fi Fattum" hawaye na zubowa cikin idanunta ta ce"dan Allah ka taimakeni" girgiza mata kai ya yi ya ce"taimakon da zan iya yi miki kenan ki koma ki kwanta dare ya yi" gyaɗa masa kai ta yi sannan taja trolley ɗinta ta koma gidan.




Inuwar mutum ta gani tsaye yana shan tea da sauri tayi baya zata koma, riƙe hannunta ya yi ya sanya ta fashe da kuka hannunsa ya sanya ya rufe mata baki sannan ya ɗauketa bai direta ko inaba sai parlonsa hasken data gani ya sanya ta sake ruɗewa fara zagaye parlon ta yi ta ce"dan Allah dan Annabi Uncle kayi haƙuri wlh bazan sake ba" ko kallonta Imad bai yiba ya shiga bedroom ɗinsa not too long ya fito hannunsa ɗauke da bulala wata irin razana ta yi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita ya ce"dan Annabi kayi haƙuri wayyoooo Allahna Uncle......"kasa ƙara sawa ta yi saboda wata irin bulala daya shiga sauke mata tun Fattomah na bashi haƙuri har saida tayi shuru dan ta shiɗe ya fi sau nawa, saida yaga ya yi mata laga-laga sannan ya rabu da'ita, kama hannunta ya yi ya jata har cikin bedroom ɗin sannan ya kulle ƙofar da key ya fito ya koma master bedroom ɗinsa dan daman anan yake kwana.





Dakyar take buɗe idanunta wanda sukayi mata nauyi sosai hasken data gani ya sanya ta runtse idanunta dan rabonda taga haske yau kwana 4 kenan, kallonta ya yi ya ce"tashi ki fita ko ranki ya ɓaci" kasa koda motsi Fattomah ta yi, kukanma na zuci take domin hawaye ya daɗe da ƙafewa daga idanunta, kama gefen gadon ta yi ta miƙe wani jiri taji yana ɗibanta komawa ta yi ta zauna kan gadon ta fashe da kuka ta ma rasa abinda zatayi ga ciwon da jikinta ke mata, ga yunwa, ga ciwon da cikinta ke mata goge hawayen idanunta ta yi sannan ta sake attempting na miƙewa akaro na biyu baya tayi zata faɗi taji an riƙe ta, kwantar da'ita Jawaad ya yi akan gadon sannan ya kalli Imad wanda ya shigo sannan rai a ɓace ya ce


"Wannan abunda kake zalunci ne Imad, wane Irin rashin imani ne wannan har ka kulleta a ɗaki for almost 4days babu abinci baka damu wane hali zata shiga ba wannan ba adalci bane Imad kuma wlh sai Allah ya tambayeka, idan kana ganin bazaka iya zama da'ita ba ta kusa ƙarasa makarantarta ka bani ita na tafi da'ita gida idan ta ƙarasa sai na mayar da'ita wajen Daddy"


Murmushi Imad ya yi ya ce"abinda nakeson naji ka faɗa kenan, wato na baka ita ka tafi da'ita gidanka to bazan bayar ba, kuma wlh ko yanzu zata sake gwada aikata sheɗanci wlh saina hukuntata daidai da laifin data aikata idan kuma tana ja dan Allah yau ma ta sake haɗa kayanta zata bar gidan nan taga" kallonsa kawai Jawaad ya yi dan shi arayuwarsa bai iya tashin hankali ba idan kaga yayi faɗa toh tabbas abinda akai ya kai abu, tsaki Imad ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Ƙara sawa gabanta ya yi yana kallonta ganin duk yanda ta rame ga jikinta duk tabon duka tayi duhu ba kamar da ba, runtse idanunsa ya yi sannan ya ce"sannu kinji bari na kai ki asibiti" juyawa ya yi zai fita ta riƙe masa hannu kallonta ya yi yana sanya hannayensa cikin nata ya ce"mene ne?" Murya can ƙasa ta ce"yaya karka tafi ka barni ka tafi dani" yanda take maganar zaka gane har cikin ranta haka take nufi, shafa kanta ya yi ya ce"kiyi haƙuri babu inda zani Fattomah asibiti zan kai ki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya sake ya fita.




Wani banzan kallo Imad ya watsa masa sannan ya ce"babu wani asibiti da za'a kai ta ko mene za'a yi mata ai mata a gida wlh babu inda zata je, kai bari kaji ma babu inda zata sake fita indai tana cikin gidan nan" murmushin takaici Jawaad ya yi ya ce"shikenan duk abinda kake dai ka dinga tuna akwai ranar sakamako akwai ranar da zakayi regreting abinda ka dinga aikata mata alokacin kuma ba zai amfane kaba, dan kana ganinta yarinya ko kuma marainiya wacce batada wani gata to ka sani Allah yana nan a madakata kuma wlh bazai barka ba Imad ya kamata ka daina wannan abunda kake I'm not force you kawai shawara nake baka a matsayina na ɗan uwanka" cikeda rainin hankali Imad ya ce"aikuwa nagode" gaba ya yi bai sake bi takansa ba.



Sosai ta sami sauƙi saboda yanda yaya Jawaad ya kula da rayuwarta har yaga ya ta samu sauƙi sosai sannan dukda Imad ya hana akaita asibiti haka ya dinga jigilar zuwa gidan safe da yamma, zaune take kan kujera tana kallon dramar da ake a arewa 24 sosai ta bawa kallon muhimmanci dan batasan sanda ya shigo ba tsaki ya yi sannan ya kashe tv hakan yasa ta ɗago idanunta tana kallonsa, harararta ya yi sannan ya zauna kan kujera yana kallonta ya ce



"Duk randa na sake ganin kina wannan kallon na asara sai ranki ya ɓaci wlh" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba ya ce"zan tafi Spain yanzu and bansan tsawon lokacin dazan ɗauka ba maybe one week maybe kuma yafi haka ina sanar dake ne saboda idan har na dawo na samu kina aikata wani abu daban wlh Fateemah sai ranki ya ɓaci ki kama kanki ki zauna idan safiya tayi ki tafi makaranta idan kin dawo babu ke babu yawo" raurau tayi da idanu tana kallonsa ta ce"Uncle ka kaini gidan yaya Jawaad tsoro inaji" harararta yayi ya ce"ki mutu" miƙewa ya yi ya fice daga parlon without looking at her, hawayene suka shiga sakko mata kan kuncinta tana sharesu wasu na sake zubowa.




Convey ɗin da taji ya sanya ta mike taje jikin window tana kallonsu har suka shiga mota shima Salma sannan guards suka shiga suka rakashi, sauke idanunta tayi tana rufe bakinta saboda wani kuka daya tawo mata tayi saurin komawa parlon ta faɗa kan kujera ta rushe da kuka.




*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*



*Like nd share*
[5/18, 9:52 PM] Nanameera: *💞 FATTOMAH 💞*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.



*Ameenatou I Ibrahim*
Nanameera



PAGE 36-39.


Da sauri ta gama shiryawa dan ta kusa makara ko kallon abincin da maid ta ajiye mata batayi ba tayi waje, bayan ta zauna a motar tana ɗan Kalle-kallenta drivern ya ce"Hajiya ƙarfe nawa zaku tashi dan sir ya ce azo a ɗauke ki da wuri" kallonsa ta yi ta mudubi sai kuma ta ce"sai 4pm sannan"okay ya ce sannan suka ci-gaba da tafiya ba tareda ta sake furta wata kalma ba. Fa'eeza ta ce"wai yanzu babu kowa a gidan sai ke kaɗai?" gyaɗa mata kai Fattum ta yi ta ce"kuma kika zauna tab ni ce ke wallahi bazan zauna ba ko tsoro baki ji" murmushi kawai Fattomah ta yi batace komai ba Aysha ta ce"kawai ki zo mu tafi gidanmu idan aka tashi sai ki dinga kwana acan" da sauri Fattum ta kalleta ta ce"ke bakida kai ne?, so kike Uncle ya kusa kasheni idan ya dawo?" tsaki ta yi ta ce"to ai bai saniba kuma baya nan yanzu ke kinfiye tsoro wllh" dariya kawai ta yi ta ce"ni babu inda zani kinji" harararta ta yi"to kar kije mara mutunci".




Kallon noodles ɗin tayi wacce taji kayan haɗi kana gani kasan ba ƙaramin daɗi zata yiba, Aysha ta ce"kee Fattum nasan halinki wlh karki yi cin mugunta kinga mu ukune" harararta ta yi ta ce"saboda kin maidani kwaɗayayyiya?" ta ce"nasan halinki da indomie shiyasa" "to ni bama ci zanyi ba" kallonta Aysha tayi ta ce"dan Allah kiyi haƙuri da wasa fa nake" ta ce"nima wlh nasani kawai bana cine rabonda naci indomie har na manta ni mango ma zan siya" haɗe rai Aysha ta yi ta ce"shikenan Nagode babu matsala amma wallahi nima bazan sake cin abin hannunki ba har muyi graduation" dafata Fattomah tayi ta ce"I'm sorry dear wlh na ƙoshi shiyasa kema kinsan bama haka dake" doke hannunta ta yi ta ce"dallah rabu dani" dariya ta yi ta ce"bari naje na siyo Mango kafin sannan kun kammala cinyewa" ko kallonta Aysha ba tayi ba bare ta bata amsa ta cewa Fa'eeza"please muci na rabu da wannan yar iskar" dariya Fa'eeza ta yi sannan suka fara cin abincin.




Ganin yanda take haɗe rai yasa Fa'eeza ta ce"wai Fateema lafiya?" ya mutse fuska Fattum ta yi ta ce"wlh Mangon babu daɗi kamar gwanda" tuntsirewa sukayi da dariya Aysha ta ce"A'a kin manta kamar abarba" harararta ta yi ta ce"na saka ki a maganata?" Aysha ta ce"ban sani ba" miƙewa tayi ta ce"nidai na tafi gida sai kuma Friday please ku shigo da wuri" Aysha ta ce"wai bazaki gidan namu ba?" girgiza mata kai Fattum tayi sannan tayi gaba dan ba wani son yawan magana take ba. Tsaye taga drivern da alama bai koma gida ba saida suka fara tafiya sannan ta ce masa"wai anan ka zauna tunda safe?" murmushi ya yi ya ce"Eh haka sir ya ce idan mun kai ki azauna a jiraki har ki gama sannan"taɓe baki Fattum ta yi aranta tana cewa"wato ashe har ma'aikatan nasa ma muguntar yake musu?????".





Sosai tasha baccinta sai wajen ƙarfe 8pm sannan ta shirya cikin wasu riga da wando ash colour wandon iya gwuiwa yazo mata kasancewar ita kaɗai ce gidan yasa bata damu ba, murmushi tayi ganin yanda abincin ke turiri saboda tsabar dawuwar da ya yi zama tayi ƙasan carpet ta tankwashe ƙafafunta ta ajiye plate ɗin jallof rice ɗin gabanta wani ɗan bowl ta ɗauko wanda Aysha ta kawo mata yajin daddawa ta buɗe ta zuba akai har saida abincin ya fara yin wannan kalar sannan ta rufe ta fara ci, haka ta dinga cin abincin kamar mayya saboda yaji sai shuuuuuu take da baki amma hakan bai sa ta haƙura ba, saida ta jinye tasss sannan ta ɗauki wani ruwa mai mugun sanyi ta sha gyatsa tayi sannan ta ce"Alhamdulillah" tashi tayi ta kwashe plate ɗin ta kwanta kan kujera nan da nan wani sabon baccin ya ɗauketa




Da gudu ta ƙarasa toilet ɗin tana zuwa ta zube nan ƙasa ta shiga gwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta saida duk abincin ya fita sannan ta jingina da bango hannunta bisa cikinta tana sauke numfashi, dakyar ta samu ta mike ta ɗauraye bakinta da wajen Sannan ta fito tana bin bango sake kwanciya tayi amma kwata-kwata ta kasa baccin banda ciwo babu abinda cikinta ke mata gashi babu wani magani cikin gidan bare ta ɗauka tasha kuma batada waya bare

Please Login or Register in order to submit comment