Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/4, 19:10] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


🅿️.....3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣


____________✍🏻 Cikin jin haushi Nana ta ce " amma dai Hameeda bakida hankali, nufi kike agaban Daddy zance inason Jawad ?" murmushi ta yi ta ce " haka nake nufi Nana saboda hakan ne kaɗai mafitarki, idan kika faɗa masa haka zaiji haushi kuma jin haushin zaisa ya dinga kulawa da ke ko dan saboda kada ya ga kin kula wani " cikin gamsuwa Azrah ta ce " kuma hakane Nana kawai ki gwada idan an dace fine, in kuma bai yuhuba shikenan sai asami wata hanyar " ahaka suka ƙarƙare sannan Hameeda ta ce " kawai kedai Nana gobe kishirya kiyi kwalliya tare zamu zo da Jawaad " ohk Nana ta ce sannan sukai sallama kowa ya yi gida .....




Bayan ta yi wanka ta na zaune a parlour ta na cin salad saboda sha'awarsa da tayi akayi sallama aka shigo, ɗaga kanta ta yi ganin Jalhan yasa ta yi murmushi. Murmushin itama ta mayar mata sannan ta ce " Nana yau kece a parlour? ɗazu naji uncle na cewa wai Daddynki sun tafi abuja " cikin sanyin murya ta ce "Eh nima haka naji dana dawo amma ai anjima zasu dawo "



Ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannunta ta riƙe ta ce "Nana kizo muje part ɗina mu zauna kinji " girgiza kai ta yi ta ce


"Bazan biki ba saboda idan Daddy ya ji labari faɗa zaimun" kallonta ta yi sosai ta ke tausaya mata ta ce


"Shikenan Nana babu komai, amma dan Allah Nana ki dinga cin abinci kodan abinda ke cikin ki kinji " ɗaga mata kai ta yi ta ce "toh zan dinga ci, nagode sosai " murmushi ta yi ta ce " babu komai Nana, amma dan Allah Nana ki ƙara haƙuri, nasan halin da kike ciki amma babu damar fitarda ke saboda haka ki dinga addu'a kuma ki dinga yiwa Daddynki kinji, kar kiji haushinsa domin Daddynki nasonki har gobe kawai dai shima baisan haka na faruwa bane kinji Nana " fashewa ta yi da kuka ta ce


" Daddyna baya sona kwata-kwata, wallahi Jalhan ji nake kamar na kashe kaina na huta daddy baya sona, baya tausayina, babu ruwanshi da halin da nake koda kuwa gani ya yi zan mutu wallahi bazai taimakeni ba " rungumeta ta yi ta ce


"Nooo Nana Daddynki nasonki, ki dinga yimasa addu'a shi ne zaki dawo da soyayyarki kinji " ɗaga mata kai ta yi, haka tayi ta bata baki har ta kwantar da hankalinta sannan ta tafi..........




Sai kusan ƙarfe tara suka shigo gidan, alokacin ta na kitchen tana girka indomie. Zama sukayi a parlour'n suna hira har ta gama dafawa ta fito don hucewa sama ta gansu a zaune, har ta yi gaba sai Hafsa ta hangi plate ɗin hannunta hakan ya sa ta ce


"Dear dan Allah kirawo Nana taban indomie ɗin hannunta wallahi ta ban sha'awa " ohk kawai ya ce mata kai kace Mama ce ta bashi umarni ya ce


"Nana zo nan"


Komowa baya ta yi ta tsuguna agabansa ta ce "daddy gani " kallonta ya yi from head to toe sannan ya ce " kibawa auntynki indomie zata ci idan yaso ke saiki sake dafa wata kinga ita ta yi tafiya ta gaji " tunda ya fara magana take kallonsa har ya idar sannan ta ce "daddy nima yunwu nakeji kuma bazan iya sake dafa wata ba wannan ma da ƙyar na dafa banasan ƙanshin dahuwarta ita ta tashi ta dafa " kallonta ya yi afusace ya ce " eehhhyy wato ni nake faɗar magana kina mayarmin Nana?, ni nayi magana bazaki ce toh ba " batai auneba sai jin mari ta yi har biyu, tsabar gigicewa tama kasa kukan sai ajiyar zuciya take, ya daka mata wata tsawa ya ce " tashi kiban gurin, shashasha kawai " da gudu ta shige bedroom ɗinta ta na kuka kamar ranta zai fita, bayan ta shiga ɗaki Hafsa ta kalleshi ta ce " haba dear ai da kabita ahankali yarinyace " tashi ya yi ya shige ɗaki bai ko bata amsaba, bayan taga ya shiga ta yi wani killer smile ta ce " aikin banza ai wallahi saina sa ka kasheta da hannunka " tayi wata dariyar mugunta sannan ta ja plate ɗin abincin ta faraci , bayan ta ci loma biyu ta ce " shegiya kuma ta iya girki".......




Misalin ƙarfe ukun dare ta farka banda yunwa babu abinda take ji ahaka har akayi kiran sallar asuba.....





Tun kusan ƙarfe shidda ta fito ta yi apartment ɗin Amma, ta na shiga ta huce kitchen ta yi ta dubawa ko zata samu abinda zata ci amma babu hakan yasa ta haɗa tea ta fito tabuɗe frigde ai kuwa ta yi sa'a akwai cake ta ɗauko, zama ta yi ta hau ci kamar almajira saida ta cinye tas ko kaɗan bata rageba sannan ta shiga ɗakinta ta kwanta, nandanan bacci ya ɗauketa......




Zaune suke suna breakfast wayarshi ta fara ƙara ɗagawa ya yi ya ce "Big bro! Allah ya taimakeka " can kuma ya ce " ohk nazo na ɗaukeka " sannan ya kashe wayar, kallonsa Hafsa ta yi ta ce " dear kai dawa?" murmushi ya yi ya ce " wallahi wai ya Aleey ne zaizo nigeria shine ya kira ya faɗa "

"Ohk ya Aleey'n kawu " ɗaga mata kai ya yi ta ce " Allah sarki ya daɗe bai zoba dan inaga har yafika daɗewa " tashi ya yi ya ce "gaskiya kam dan rabonshi da nan tun kan rasuwar Baba don baizo da mutuwar Baba ba, bari na shirya kafin yazo " daga haka ya shige bedroom......






Wajen ƙarfe tara suna zaune suna breakfast kasancewar Abba bai fitaba Nana ta fito daga cikin ɗaki, kallonta suke dan basusan ta shigoba har ta ƙaraso ta zauna sannan Amma ta ce "Nana yaushe kikazo?" turo baki ta yi ta ce " ɗazu kuna bacci, inajin yunwa kuma Daddy basu tashiba shine na tawo nan naci abinci na kwanta " lallaima toh ya miki kyau cewar Amma.


Murmushi Abba ya yi ya ce "toh yanzu kin ƙoshi ko zaki ƙara " tasowa ta yi ta zauna gefenshi ta ce " Abba zan ƙara " zuba mata Amma ta yi ta ce "karɓi " karɓa ta yi ta miƙawa Abba ta ce "Abba ka bani abaki kaji " ohk ya ce sannan ya fara bata abincin ta murmushi, girgiza kai Amma ta yi ta ce " Allah ya shirye ki Nana"........




Fitorwasa kenan, sanye ya ke da wata shadda gezner maroon colour ya yi kyau kamar ango Hafsa ta kalleshi ta ce " dear tafiyarce ?" ɗaga mata kai ya yi ta ce " baka turominba kuma yanzu nima zan fita " kallonta ya yi ya ce " oh sorry na manta nawama kika ce?" two million ta faɗa, murmushi ya yi ya ce " don't worry idan nashiga mota zan turo miki " dariya ta yi ta ce "thank you, Allah ya tsare " murmushi ya yi ya ce "Ameen" sannan ya yi waje......




Yana fito ita kuma zata shigo hakan yasa suka haɗu kallo ɗaya ta yi masa ta juya zata gudu ya kamota batareda ya ce mata komai ba ya kama hannunta sukai gaba, buɗe musu kofa guard ya yi suka shiga sannan sauran guards ɗin suka shiga ta su motocin sai convey ne ke tashi ahaka har sukai waje.....



Sai bayan daya tura mata kuɗin sannan ya kalleta ya ce" ke daga ina kike?, kuma ina makarantar?" turo baki ta yi gaba ta ce "gurin Amma naje naci abinci sannan kuma ni banida lafiya shiyasa banje makaranta ba " ta faɗa tana kallon waje. Jawota ya yi jikinsa ya ce


"Ohk wa kika faɗawa bakida lafiya?, kuma daman da safe ake zuwa gurin Amma ko bamuda abinci ne ?" fashewa ta yi da kuka ta ce "ni ka kyaleni babu ruwanka dani, karka sake kulani har abada " murmushi ya yi ya ce " ohk kwaci kan ki toh ko anfaɗa miki ni kulaki nake " yana gama faɗin hakan ya matseta ajikinsa, sosai take kokowar kwace kanta amma ta kasa hakan yasa tafara dukanshi tana cizonshi amma kamar bashi take yiwaba ahaka har ta haƙura ta yi shuru, kusan five minutes ya leƙata yaga ta yi bacci, murmushi ya yi ya gyara mata kwanciyarta kafin su ƙarasa.......





Zaune suke gaban malamin mai ƙirar aljanu ya na magana ya ce " kamar yanda na faɗa miki asirin ya kusa karyewa nan bada jimawa ba" cikin tashin hankali ta ce "malam to mene abinyi?, so nake kawai arabasu " wata mahaukaciyar dariya ya yi sannan ya ce "hanya ɗaya ce ta rage amma idan kin yarda zakibar sallah daga nan zuwa wani satin" kallonsa ta yi ta ce "indai zan samu biyan bukata to nayarda malam" dariya ya yi irinta bokaye sannan ya fara faɗa mata maganin ni kuwa nace Allah ya shirye ki ya kuma ganar da ke Hafsa.......






Shiga motar ya yi yaga Nana kwance tana bacci, murmushi ya yi ya ce " Nana rigima kamar dole rakiyar ana bacci amota" dariya ya yi ya ce "ba bacci take muka tawoba ahanya ta yi, naganka kai kaɗai?" " eh ni kaɗai nazo suna makaranta shiyasa basu zoba saidai idan zan dawo sai mu tawo tare " kallonsa ya yi ya ce "gaskiya bakaso ka tawo da suba " murmushi ya yi ya ce "ohk naji ya Niger?" "tana nan kalau ka bari mu ƙarasa sai kaga yanda ta koma........






Wajejen la'asar Hameeda da Jawaad sukazo, bayan sun zauna Hameeda ta ce "naga baki shiryaba ?" murmushi ta yi ta ce "Hameeda na fasa bazan iya ba kiyi haƙuri" kallonta ta yi ta ce "ai shikenan sai kiyita zama bakida ƴanci agidan mijinki " murmushi ta yi ta ce " ban ɗauki Daddy matsayin mijiba kamar yanda shima baya ɗaukata matsayin matarsa kallon ƴa yakemun nima kuma kallon uba nake masa, nayi alƙawarin komai zai mun zan jure kodan na yi masa hallacin da ya yi wa rayuwata, Hameeda ban ƙara jin zan iya jurewa ba sai ɗazu da Amma ta bani labarai kala-kala, wallahi inason Daddyna fiye da komai arayuwata kuma zan iya sadaukar da farin cikina saboda nashi" miƙewa Hameeda ta yi ta ce" Allah ya taimaka kuma ya baki ikon ɗaukar jarrabawarki Nana, sai anjima na tafi " tashi itama ta yi ta rakata sannan ta dawo............






Kusan sati biyu kenan yanzu abin Daddyn nata har yaci tura dan duk mutanen gidan sunfara ganewa gashi babu wanda yake jin magana bare a tsawartar masa tunda kawu baya ƙasar baisan meke faruwa ba, kuwa na gidan tausayinta yake Amma kullum cikin kuka take saboda idan kaga Nana bazaka sake son ganinta ba. Yau kamar kullum ta tashi babu abinda zata ci , yana bacci bai sani ba ta fito saboda ya hana kowa ganinta, kai tsaye apartment ɗin Amma ta shiga tana zuwa ta tadda Amma na kitchen ta na girki, cikin sanyin murya ta ce

"Ammata"

Juyowa Amma ta yi ta kalleta, bata taɓa zaton Nana ta yi lalacewar hakaba kawai sai ta fashe da kuka, ƙarasawa Nana ta yi ta rungumeta ta ce "Amma kiyi shuru kinji, babu abinda zai sameni ki daina kuka " cikin kuka Amma ta ce


"Nana bazan iya jure ganin ki a wannan hali ba zo muje" ta kama hannun Nana suka shiga ɗakinta, hijab kawai ta sako ta fito ganin haka yasa Nana ta ce "Amma ina zamu?" kallonta ta yi tana share hawayen fuskarta ta ce "gidanmu Nana, zanje na ɓoyeki inda baza su gankiba Nana " cikin kuka Nana ta ce "karmuyi haka Amma, nayi alƙawarin zan jure,yanzu idan muka fita Abba zai miki faɗa Amma tunda shiba baya ganin laifin Daddy , gwanda nayi haƙuri wata rana sai labari Amma, kuma.....daka mata tsawa Amma ta yi ta jawota suka fito harabar gidan abun mamaki mutanen gidan kowa ya fito. Komawa bayan Amma ta yi ta na ɓuya sanda Abba da Abdussamad sukayo wajensu, suna zuwa Abba yasa hannu ya wanke Amma da mari har biyu sannan ya ce " munafuka, wato zaki gudu da ita saboda antsaneta agidan nan ko?,toh wallahi bari kiji duk randa kika sake irin wannan abun wallahi abakin auranki" kallonta Abdussamad ya yi ya ce " ai Abba duk da baka aureta ba da haka bata faru ba tayi hakane saboda ita ba jinin gidan nan bace shiyasa, Amma kin ban mamaki " Fashewa Amma ta yi da kuka tana sake riƙe Nana gudun kar su daketa ga ciki ajikinta. Ahankali kowa ya watse ya barsu anan suna ta kuka abin tausayi........








Sai wajen ƙarfe taran dare sannan Abba ya shigo gidan alokacin akwai hadari sosai agarin kasancewar lokacin tsakiyar damuna ne, zaune ya sami Nana kana ganinta kasan batada lafiya sosai, kallonta ya yi cikin daka tsawa ya ce " ke!! ubanki kikeyi anan?, tashi ki tafi gida " tashi ta yi jikinta na rawa ta yi waje, saidai tana fita ta tarar anfara ruwa kuma ya tawo da ƙarfinsa hakan yasa ta tawo ta kalli Abba ta ce " Abba ruwa akeyi bazan iya tafiya ba ruwa ake" kallonta ya yi ya ce "koo" ɗaga mishi kai ta yi aikuwa ya biyota da gudu , ta yi waje. Ahaka cikin ruwan ta tafi gidan wanda aƙalla tazarar mintuna goma ne tsakaninsu, tana shiga ta tararda Daddynta zaune suna kallo, kallonta ya yi ya ce "fita daga gidan nan" haɗe hannayenta ta yi alamar roƙo ta ce "Daddy dan Allah kayi haƙuri wallahi ruwa akeyi " ta ƙarashe maganar ta na hawaye, wata gigitacciyar tsawa daya daka mata yasa ta yi waje da gudu, ya rufe ƙofa sannan ya koma ya zauna....



Tana fita ta rasa wace hanya za tabi ga ruwa anayi kamar da bakin kwarya, ga yunwa tana ci gashi Asma ta na neman tashi, ga kuma cikin jikinta tun tana tsaye harta yanke jiki ta faɗi kasa sumammiya......







Tsakar dare ya dinga mafarke mafarke haka ya kwana baiyi bacci ba, sai kusan ƙarfe shidda na safe ya farka a firgice ya ce "Nana" amma yaji shuru ya sakko ya fito daga ɗakin Hafsa ya tafi kiran Nana, yana shiga ɗakinta ya kuma ce wa "NAANAH" nanma ya ji shuru ya duba banɗaki amma bai ganta ba hakan yasa ya fito parlour yace "Hafsa ina NAANAH " kallonsa ta yi ta ce "Nana kuma banda Nanan daka kora jiya ai saidai kaje apartment ɗin Abba ka kirata " kallonta ya yi ya ce "da gaske na kori NAANAH a gaske ba amarkiba ?" shuru ta yi masa ta na kallonsa dan tasan asirinta ya gama karyewa, waje ya yi kamar mahaukaci ya nufi apartment ɗin Abba.......





Yana shiga ya tarar da ana irin wannan drama Abba sai neman Nana yake ya ce shima amafarki ya aikita, kallon kallo sukai Abdussamad ya ce " Abba yanzu ina zamuga Nana?,amma bari naje apartment ɗin mama" daga haka ya yi waje ......



Yana zuwa Mama ta ce batazo ba, Ma'a kuwa fashewa ta yi da kuka ta ce "ni dama nasan duk abinda kuka aikata bayin kanku bane Allah ya bayyana yarinyar nan " , wasa-wasa kusan har magrib ba'aga Nana ba kuma ba'a sami labarinta ba, su Jalhan banda kuka babu abinda suke, sukuwa Abdussamad,Abba da kuma Amma tuni suka yanke jiki suka faɗi.

Next Day




End of BOOK ONE



NAANAH BOOK TWO isn't free its 200#only via 9086030007
Hauwa lawan
Opay




*Shin da gaske NAANAH ta ɓata?*
*Shin idan NAANAH ta ɓata ina ne inda tashiga?*Shin za'aga NAANAH ko kuwa ta ɓata kenan?*
*Shin za'a gane Hafsa ce ta kulla dukkan abinda ya faru?kuma mene ne ƙarshen Hafsa?*
*Shin ya Abdussamad da Abba zasu ɗauki al'amarin ɓatan NAANAH?*
*Shin mene ne makomar NAANAH da abinda ke cikinta? Zata haifeshi ne ko kuwa A'a?*

*Duka zaku sami amsoshinku ne acikin BOOK TWO ɗin NAANAH wanda kuma isnt free it's 200#only evidence via 09086030007 sai mun haɗu a paid book*




Comments,share nd like.



Story and written by:
*Nanameera*



Meera Love's yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[1/8, 17:11] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




🅿️....4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣




_________✍🏻Gabaɗaya hankalin Family ɗin ya gama tashi, wajejen ƙarfe goma na dare Aliyu suka shigo da Hameed, zama sukai Mama ta kallesu ta ce " ya ake ciki?" Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya ce " wallahi Mama babu wani labari mai daɗi har yanzu, babu inda bamu shiga ba amma kwata-kwata babu wata alamar Nana" cikin tashin hankali Mama ta ce " innalil-lahi wa ina ilaihi raji'un yanzu shi ina Abdussamad ɗin suke?"

Kallonta Hameed ya yi ya ce " maganar gaskiya basa cikin yanayi mai kyau dan har gwara Abba akan Abdussamad har yanzu ko farfaɗowa bai yi ba, shi kuma Abba baya umh baya um'umh " hawaye nasauka a fuskarta ta ce " wannan wace irin ƙaddarace ?, Allah ka bayyana yarinyar nan " Ameen suka ce sannan Aliyu ya ce "Mama ki kwantar da hankalinki in sha Allah za'a ganta su kuma zasu sami lafiya kawai ki tayasu da Addu'a " toh ta ce sannan sukai waje .....






Zaune take kan gadon asibitin ta yi shuru akayi sallama aka shigo ɗaga kai ta yi ganin Ma'a yasa ta ce "sannu da zuwa Ma'a " zama ta yi sannan ta ce "yawwa ya mai jikin?" dasauƙi ta amsa kallonta Ma'a ta yi ta ce " Zainab" cikin girmamawa Amma ta ce "na'am " Dan Allah kiyi haƙuri da duk abinda ya faru kinsan ba'a hayyacinsu sukeba shiyasa suka aikata hakan amadinsu ina mai baki haƙuri dan Allah ki yafe musu " hawayen fuskarta ta goge ta ce " Ma'a wallahi ko kaɗan ban ƙullacesu ba hasalima kullum cikin yi musu Addu'a nake Allah ya rabasu da abinda ya damesu, nasan daga Abdussamad har Abba babu wanda zai aikatawa Nana haka da gangan nidai burina bai huce Allah ya bayyanata ba kodan asamu kansu " cikeda tausayawa Ma'a ta ce " in sha Allah za'a ganta nan bada daɗewa ba " Allah yasa. Kallon Abba ta yi ta ce "Allah ubangiji ya baka lafiya, bari naje na duba Abdussamad" kallonta ta yi ta ce " ai ba'a bari aganshi kwata kwata ɗazu da kawu yashigo ya ke faɗamin" tooh Allah shima ya yaye masa Allah ya rabamu da wannan masifar data tunkaromu " Ameen cewar Amma.........



Wasa-wasa kusan one week kenan babu NAANAH babu labarinta gabaɗaya gidan ya zama kamar gidan mutuwa, shigowarsu kenan saboda kiranda Doctor ya yi musu, Kawu ne ya ce " Doctor meya faru ?" zare glass ɗin idanunshi ya yi sannan ya ce


" Kawu maganar farko dai congratulation dan Abba ya sami sauƙi sosai " murmushi Kawu ya yi ya ce "Alhamdulillah masha Allah shikuma Abdussamad ɗin fa ?" numfasawa ya yi ya ce " maganar gaskiya yana cikin mawuyacin hali dan har yanzu baisan wane akansa ba, maganar da ake yanzu saidai afitar dashi ƙasar waje in sha Allah " cikeda damuwa Kawu ya ce " yanzu yaushe za'a tafi dashi ɗin?" kallonsu ya yi ya ce " In sha Allah zuwa gobe zamu tafi dan kar tun abu yana ƙarami yazo ya zama babba " ohk kawu ya ce sannan suka fito.....



Bayan sun fito Kawu ya ce " Aliyu idan munje Abba ka huce wajen Hajiya Khadija ka sanar da'ita " kallansa ya yi ya ce "_ toh kawu i will do so " daga nan suka shiga ɗakin da aka kwantar da Abba .......





Zaune ya ke Amma tana bashi abinci wanda dakyar ta lallaɓashi ya karɓa, bayan sun zauna Aliyu da sapwan suka gaisheshi ya amsa Kawu ya ce " ya jikin naka?" kallonsa ya yi ya ce " dasauƙi " Allah ya ƙara sauki" ganin yanda ya rame yasa ya ce " ka dinga cin abinci yanda ya kamata idan baso kake wani ciwon na daban ya kamaka ba, insha Allah duk inda Nana take za'a samota nan bada daɗewa ba saboda haka karkasa abin aranka please " hawaye nasauka afuskarshi ya ce " yaya da'ace nabar Nana ta kwana da yanzu nasan bata ɓataba, yanzu kuwa babban tashin hankalin ba'asan inda takeba ba'asan inda za'a samota ba, sannan ga ciki ajikinta me zancewa Allah idan ya tambayeni? I fail as a father " ya ƙarashe maganar yana hawaye. Zama Kawu ya yi kusada shi ya ce " bakada laifi har awajen Allah saboda bakasan ka aikata hakaba , kaidai kawai kayi ta addu'a Allah ya bayyanata amma kadaina ji aranka kanada kamasho acikin ɓatanta " share hawayen fuskarshi ya yi ya ce " In sha Allah zanyi " murmushi ya yi ya ce " Allah ya ƙara sauƙi" Ameen ya amsa sannan ya yi wa Amma sallama sukai waje.........






Zaune suke agidan zeeta Hafsa ta rafka uban tagumi Zeeta ta ce " dan Allah kibar wannan tunanin haka " kallonta Hafsa ta yi ta ce " haba zeeta to idan banyi tunani ba mai zanyi ?mijina fa yana kwance a asibiti baya ko motsi bai masan wane akansa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment