Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hankali nothing will happend " ɗaga masa kai kawai ya iya .........






Sallama ya yi ya shigo hannusa riƙe da Twins ya yinda ita kuma ta maƙale abayansa, gaba ya yi hakan yasa kowa ya ganta sanye take da wata turkey abaya wacce tai matuƙar karɓarta kowa kallonta ya ke saboda yadda Nana ta koma babbar mace kuma asalin kyakyawa, shi kuwa Abdussamad ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta ya maidata kamar wata tv, hange hange ta keyi har idanunta ya sauka akan Amma ai kuwa da gudu ta tafi ta rungumeta tana kuka tana dariya, itama Amma dariyar take dan ta fidda rai da sake ganin ƴarta bayan wasu mintuna ta tashi daga jikin Amma ta tafi gurin Mama ta rungumeta sosai take cikin farin cikin ganin family ɗin nata, bayan ta gaisa da kowa taje ta tsuguna gaban kawu ta gaisheshi shafa kanta ya yi ya ce " Allah ya yi miki Albarka " murmushi ta yi tace " Ameen" sannan ta koma wajen Abba ta ce " ina wuni " murmushi ya yi ya ce " lafiya lau Nana ya gida ?" ba tareda ta kalleshi ba ta ce " lafiya " sannan ta kalli Aliyu ta ce " uncle ina Jalhan ?" murmushi ya yi ya ce " suna backyard suna girki da Ayrah " Ok ta ce sannan ta yi hanyar backyard ɗin ba tareda ta kalli Abdussamad ba bare yasa ran zata kulashi ...






Bayan ta wuce ya bita da kallo ya kifa hannunsa a fuskarshi kowa na gurin tausayinsa yake saboda ko amafarki babu wanda zai kawo Nana zata guje Daddynta ba komai zai mata, Abba ne ya dafashi ya ce " kayi haƙuri Son zata sakko In sha Allahu " fashewa ya yi da kuka ya ce " Abba wallahi banga laifin Nana ba ko me taimin nasan na cancanci haka koma fiye da haka, nima ban kula da rayuwarta ba alokacin da take tsananin buƙata ta alokacin na banzatar da ita, saboda haka kome zataimin bazanji haushi ba " kafin Abba ya yi magana sukaji ance " Daddy" jin muryar yara yasa ya ɗago kai idanunsa ya sauka akan Akeelah da Akeel suna kallonshi, kallansu yake sosai dan neman ƙarin bayani, Akeelah ce ta hau kan cinyarsa ta zauna ta na share masa hawayen fuskarsa da ƴan ƙananun hannu ta ta ce " kayi haƙuri Daddy ka daina kuka ba gamu ba, ko Akeel ta faɗa ta na kallon biyunin nata, hawa kansa ya yi shima ya ce " Eh Daddy stop crying kaji " sosai yaran suke kama dashi dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ƴaƴansa ne, kallon Aleey ya yi ya ce " who are they ?" murmushi Aleey ya yi ya ce ",yaranka ne " kallonsa ya yi ya ce " wai ni waɗannan ƴaƴana ne ?" dariya sukemai ya ɗaga masa kai baisan lokacin daya fashe da kuka ba ya rungume su yana ƙara sakin kuka, ganin haka yasa yaran fashewa da kuka suka ce atare " Daddy stop crying please " rungumesu ya yi dukda yana cikin damuwa amma tabbas yaji daɗin ganinsu dan ko amafarki bai taɓa tunanin zai samesu ba, murmushi kawu ya yi ya ce " to tunda ansami ƴaƴa sai adaina kukan banza ko" dariya kowa na parlour yake ya ce " In sha Allah Kawu ni yanzu matsala ta ɗaya Nana please Kawu ku tayani bata haƙuri" dariya Aliyu ya yi ya ce " tab wai yau ƴar rainon tasa ya ke tsoro Allah ya kyauta " miƙewa ya yi ya ɗauki yaran ya ce " zamu fita sai mun dawo" dariya suke mai Aliyu ya ce " Allah na godemaka daya zamana nima ina ɗa da munsha hulaƙanci gurin Dude " waje ya yi yana cewa " banza banida lokacin ka ........











Zaune suke a parlour'n Ayrah sai hira suke abinsu, kallon Nana Jalhan ta yi ta ce " oh wai Nana ce da ƴaƴa ni wallahi abun mamaki yake bani har andaina rigimar Daddy toys, Daddy ice-cream" murmushi ta yi ta ce " abun yake baki mamaki ko yake ban ni wallahi wani lokacin idan na kalli su Akeelah kunya nakeji ace kamata ta haifi ƴan shekara kusan uku " dariya Ayrah ta yi ta ce " kuma gashi kwanan nan zamu sake ganin Twins idan kin gado Mama za'a sha ƴaƴa " haɗe rai ta yi ta ce " Ayrah banson hulaƙanci tom" dariya ta yi ta ce "wallahi da gaske nake Nana kwanan nan zaki cika mana gida da ƴaƴa " tashi ta yi ta ce " ke kin fiye abun haushi ni na tafi gurin Amma saida safe" murmushi Jalhan ta yi ta ce " tsayani mu tafi tare kar mijina ya dinga nemana " dariya sukai atare suka ce " Awwwn kaga mai miji Allah ya ƙara danƙon soyayya " dariya ta yi ta ce " Ameen, ƴan iska soyayya ai sai ku Nana nasan kamar a india " waje ta yi ta ce " ina jiranki " ok ta ce sannan suka yi sallama suka tafi...........







Misalin ƙarfe takwas na dare suka shigo gidan tunda safe da suka fita sosai suka gaji hakan yasa direct suka nufi ɓangarensa, bayan sun shiga Akeel ya ce " Daddy yanzu wa zai mana wanka ?" murmushi ya yi ya ce " ni mana sweertheart " gemunshi yaja ya ce " Daddy daman ka iya wanka " ɗaukansa ya yi ya ce " muje na nuna maka".........







Suna zaune suna kallon movies ɗin da ake haskawa a mbc max Akeelah ta fito riƙe da wani hoto ta zaune gefensa ta ce " Daddy wannan wace?" murmushi ya yi ya ce " ƴar aljanna kenan rigimammiyar Daddy " haɗe rai ta yi ta ce " Daddy baka sonmu kafi sonta ?" rungumeta ya yi yana dariya ya ce " A'a wallahi duk inasonku ni bansan wanda nafi soba, ku jinana ce ita kuma rayuwata ce " dariya sukai suka haɗa baki suka ce " love you Dad" me too ya faɗa shima.....







Kwata-kwata bataga su Akeelah ba kuma batasan wa zata tambaya ba, kallonta Mama ta yi ta ce " takwara lafiya dai ?" murmushi ta yi ta ce "lafiya lao Mama kawai daman banga su Akeelah bane " murmushi Mama ta yi ta ce " ai ɗazu kin tafi gurin su Jalhan Abdussamad ya fita dasu nima nayi mamaki da har yanzu bai dawo dasu ba amma ko kije apartment ɗinsa ki duba " da sauri ta ce " nooo ba sai naje ba ni bacci ma nakeji " ta tashi ta ce " mama saida safe " Allah ya tashe mu lafiya cewar Mama sannan ta shige ɗakinta. Nima nace Allah ya tashe mu da rai da lafiya.........









Comments,and like....







Story and written by:
*Nanameera*










Meera Loves' yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[1/12, 21:39] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*







🅿️.......4️⃣9️⃣&5️⃣0️⃣





____________✍️Wajejen ƙarfe goma suka shigo sanye yake da wani farin voyel ɗinkin jamfa da babbar riga shima Akeel irinsa ya saka sukai anko yayinda Akeelah tasa wata ƴar kanti fara sunyi kyau kamar ka ɗaukesu sukai sallama suka shiga, Mama ce ta amsa ta ce " oyoyo sannu da zuwa shine jiya baku dawoba Mamanku na tambayarku " zama ya yi sukuma suka ƙarasa gurin Mama suka ce atare " good morning granny " murmushi ta yi ta ce " morning ya kuka kwana yara ansha kyau " dariya sukai Akeelah ta ce " Mama Daddy ne ya yi mana wanka " Allah? Mama ta tambaya daidai nan Nana ta fito daga kitchen hannunta riƙe da plate, da gudu suka rungumeta suka ce " Mommy good morning" shafa kan su ta yi ta ce " morning sweethearts kun ɓuya abinku " murmushi sukai ta jasu suka zauna ta ce " ok kuzo muyi breakfast " Mommy munyi gurin Daddy suka faɗa ok ta ce sannan ta hau cin abinci nta ba tareda ta kalleshi ba bare yasa ran gaisuwa. Ganin haka yasa Mama ta ce " Nana bakiga Daddynki bane?" ɗagowa ta yi ta ce " au naganshi good morning " morning yace ganin sunyi shuru yasa Mama ta tashi ta shiga ɗaki dan basu waje.......










Yana ganin haka kuwa ya taso ya dawo kusada ita ya zauna yana kallonta ya ce " Nana meyasa kike ignoring ganina ko kimin magana?, nasan i made a mistake amma dan Allah Nana kiyi haƙuri kimin uziri please kinji karki ƙullaceni Nana wallahi bazan jure ba kinji please i'm sorry Babyn Daddy " wani kallon kazama mahaukaci tai masa ba tareda tace komai ba ta tashi ta ɗau plate ɗin abincinta tayi gaba, kallo ya bita dashi sannan ya kalli su Akeelah ya ce " kuzo muje gurin Abba " ok suka ce sannan sukai waje......







Tana shiga ɗakin ta zauna bakin gado lokaci ɗaya ta fashe da kuka don ayanzu babu wanda take jin haushi fiyeda Daddynta zata iya yiwa kowa uziri amma banda shi saboda gani take kamar da gangan ya yi, kwanciya ta yi tana tuna irin abubuwan da suka faru awancen lokacin tanajin har abada bazata iya yafewa Daddy ba.......








Da sallama suka shiga parlour yayinda su Abba suke zaune bayan sun gama breakfast, ganinsu yasa Abba ya ce " yau Twins nan akayo?" dariya Akeel ya yi ya ce " papa Nigeria akwai daɗi sosai " murmushi Abba ya yi ya ce " daman ai Nigeria akwai daɗi kaga daman bazaka koma wata turkey ba sai kayi zamanka abinka " dariya Akeelah ta yi ta ce " papa wallahi bakaga jiya ba da Daddy ya kaimu wani waje mai kyau " Allah kuce ƴan gatan Daddynsu yawo kuka sha amma harda Mommy aka tafi ko?" girgiza kai sukai Akeel ya ce " Mommy haushi takeji yanzu ma Daddy yay mata magana ta yi masa shuru " Allah? Suka ɗaga masa kai ya ce " ok kuje cikin bedroom zakuga chocolates ku ɗauka kusha " tashi sukai suka ce " thank you papa sannan suka shiga.....








Kallon Abdussamad ya yi ya ce "Son meya faru naga ranka aɓace ko har yanzu Nana ce ?" murmushi ya yi ya ce " Abba ai daman nasan rigimar Nana zansha wahala kafin ta yarda saboda ta ɗau zafi da yawa " Allah ya kyauta Abba ya ce sannan Amma ta ce " karka damu zan mata magana " A'a Amma kibarta kawai tana gaskiya nasan zata sakko please ki kyaleta har ta haƙura da kanta " ok ta ce sannan ya kalli Abba ya ce " Abba zani Abuja su Akeelah su zauna agurinka " murmushi Abba ya yi ya ce " ok Allah ya kiyaye hanya " Ameen ya ce sannan ya yi waje.....









Hafsa ce zaune gaban Mommynta Hajiya Fadeela sai kuka ta ke Mommyn ta ce " Hafsa me nake faɗa miki?, amma kwata-kwata ki ka ƙi ki saurare ni babu yanda banyi dake ba amma wai Hafsa har wajen boka kika je abun yaban mamaki ace kamarki da iliminki Hafsa kije gurin boka saboda zigar ƙawaye gashi sun ɗoraki a keken ɓera sun gudu ita kuma wacce ki kai dominta yanzu gashi nan ta dawo kuma zata zauna da mijinta lafiya harda arziƙin ƴaƴa kefa wai Hafsa cikin shege ajikinki cikin shege Hafsa wallahi kin cuci kan ki " tana kai wa nan ta fashe da kuka, share hawayen fuskarta ta yi ta ce " dan Allah Mommy kiyi haƙuri wallahi nayi nadama nagane duk abinda haƙuri bai baka ba to rashinsa bazai baka ba dan Allah mommy ki yafemin kinji " kallonta Hajiya Fadeela ta yi ta ce " toh Hafsa idan ban yafe miki ba yazanyi dake Allah ya yafe mana baki ɗaya " goge fuskarta ta yi ta ce " nagode mommy, amma dan Allah ki tayani bawa Daddy haƙuri kinji Mommy " ok bari ya dawo amma Allah yasa ya yarda Hafsa dan ni har tsoro yake bani" In sha Allah zai yarda " Allah yasa.......







Zaune yake shi da Aliyu ganin yanda ya rame yasa Aliyu ya ce " wai Dude mene ne matsalar ?, ni wallahi kana bani mamaki ace ƴar daka raina kakejin tsoro wannan ai abun kunya ne gaskiya " kallonsa ya yi ya ce " Dude dole na lallaɓa Nana tunda nine banida gaskiya kaga bazai yiwu banida gaskiya ba kuma nace zan tada hankali" tsaki ya yi ya miƙe ya ce " haba bansan rainin hankali wallahi bazai yiwu ba dole muɗau mataki har nawa Nanan take wallahi yau sai nayi mata magana " riƙeshi ya yi ya ce " please mubi komai asannu mana dan Allah" fincikewa ya yi ya ce " kaga dallah malami rabu dani wannan ma ai rainin hankali ne kai kuma kawani tsaya kamar yaronta aikin banza zakaga abinda zanyi " yana gama faɗin haka ya yi gaba........










Zaune take kusada Mama tana kallo a tv ya shigo yana kallonta ya ce " Nana zo mana " tashi tayi ta ce " ok " sannan ta ɗau gyale ta yi waje.......







Zaune suke a wani waje mai ɗauke da kujeru dan shan iska, su kusan bakwai ne awajen Aliyu ya kalli Nana ya ce " ba komai bane yasa na kiraki ba sai dan inason na tambayeki mene ne abinda Abdussamad ya yi miki wanda har bazaki iya yafe masa ba ?" kallonsu ta yi duka sannan ta ce " abubuwa da yawa" kamar mefa ya tambaya, ajiyar zuciya ta sauke ta ce " kamar zalunci, ya zalunci rayuwata abanza ya ɗaukeni kamar baiwarsa shida matarsa wanda ni alokacin banɗauki haka matsayin tsanaba inajin zan masa komai kodan hallacin da yayimin arayuwa amma kash! Shi sai ya maida haka makamin cutar da rayuwata wallahi har abada bazan taɓa yafe masa ba shida matarsa kuma kada ya sake tunanin zan koma gidansa matsayin matarsa dan babu abinda zanyi da tsoho irinsa ƙabari kusa nima zanje na auri daidai da shekarunsa sai yaje yaƙarata da karuwar matarsa " tana gama faɗin haka tayi gaba abinta...





Juyowa Aliyu ya yi da niyyar ya yi masa magana yaga ya riƙe zuciyarsa da gudu sukai kansa ya riƙe hannun Aliyu ya ce " Dude zuciyata zata fito please ko na mutu ka cewa Nana ta yafemin kuma..... Wani guda gudan jinine suka fito daga bakinsa sai kuma jikinsa ya saki riƙeshi Aliyu ya yi ya ce " Dude!! Dude!! Please Dude karka mutu saboda Nana baka cancanci ka mutu akanta ba please Dude kodansu Twins ka tashi" shuru kake ji hakan yasa suka fashe da kuka Hameed ya yi waje da gudu yana kiran guards ɗinshi..








Comments, and like.







Story and written by:
*Nanameera*







Meera Loves' yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[1/13, 22:55] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*











🅿️.......5️⃣1️⃣&5️⃣2️⃣






___________✍️Kai tsaye asibiti suka wuce dashi ita kuwa da yake bataga sanda ya waɗi ba yasa tayi tafiyarta abinta.....









Bayan sallar magrib Abba ya shigo parlour'n Mama hankalinsa tashe ya ce ",Mama kinji wai Abdussamad yana asibiti wai ciwon zuciyarsa ya tashi" zunbur Mama tayi ta ce " subhanalahi yaushe naga ɗazu ma yashigo " wallahi ban sani ba nima yanzu zamu tafi da Kawu shine ya ce nashigo na faɗa miki " toh dan Allah duk yanda ake ciki ku kirani " ok insha Allah sannan ya yi waje......







Dadaddare wajen ƙarfe goma ta shigo parlour'n amma ga mamakinta sai ta gansu har sannan sunyi shuru zama ta yi kusada su ta ce " Twins lafiya ba kuje kunyi bacci ba?" fashewa Akeelah ta yi da kuka ganin haka yasa ta ce " Akeel meya faru?" kallonta ya yi ya ce " Mommy we are looking for Daddy tun ɗazu amma shuru kuma ya ce zai saya mana chocolates amma har yanzu bai zoba, Mommy dan Allah ki nemo mana shi please saboda...... Wata tsawa ta daka masa hakan yasa ya fashe da kuka ta ce cikeda bala'i " saina kwaɗa maka mari idan ni sa'ar ka ce nice zan kira maka Daddy,wallahi koda wasa naji kunsake maganarsa sai naci ubanku ku tashi ku ban waje!" da gudu suka shiga ɗakin suka kwanta babu jimawa bacci ya ɗaukesu......




Next Day.






Sosai ranar ya tashi da jikin dan ko motsi ba yayi gaba ɗaya sun rasa yanda zasuyi dashi Abba ne ya kalli Aliyu ya ce " haidar wai mene ne yasa meshi har ciwon ya tashi ?" shuru yayi da farko dan bayason ya haɗa Nana da mahaifinta ganin yaƙi cewa komai yasa yace atsawace " ba dakai nake magana ba " numfasawa ya yi sannan ya bawa Abba labarin duk abinda ya faru, idan ran Abba yayi dubu to ya ɓaci dan idanunshi har wani jaa sukai na ɓacin rai, lokaci ɗaya ya juya ya fita daga ɗakin kai tsaye kuma apartment ɗin Mama ya nufa.......







Yana shiga ya tarar da ita tana bawa su Akeel abinci tana ganinsa tayi murmushi ta miƙe tace " Abba sannu da zuwa ya.....Wani wawan mari ya ɗauketa dashi bata wartsakeba ya ƙara mata wani daidai nan Mama ta fito ya kalleta cikin faɗa ya ce " mahaukaciya kawai ban taɓa tunanin bakida hankali har haka ba Nana ban ɗauka rashin tunaninki ya kai haka ba Ashe kin huce sanina, na ɗauka koda Abdussamad yankan naman jikinki yake yanada Alfarmar dazaki ɗauki hakan ba komai ba amma Ashe ba haka bane, banda rashin tunani ace mutumin da ya riƙe ki tamkar ƴar daya haifa har shine abin wulaƙantawa?, mutumin daya sadaukar da farin cikinsa saboda naki har shine abin wofantarwa?, mutumin da yayi miki abinda ko uwarki da ubanki basuyi miki ba idan aka cire haihuwa shine abin tsana?, uban ƴaƴanki kuma kema ubanki amma shine zaki jefa a mawuyacin hali Nana wannan wacce irin rayuwa ce ace wanda yayi miki rana shine zaki yiwa dare?, kin ban mamaki Nana kinban mamaki NAANAH!! ganin yana shirin faɗuwa yasa tayi saurin riƙeshi ya zauna tace " Abba dan Allah kayi haƙuri wallahi banyi haka saboda ran Daddy ya ɓaci ba, banyi haka da niyyar cutarda rayuwarshi ba dan Allah kayi haƙuri Abba" ruwan da Mama ta miƙo masa ya karɓa yasha sannan ya ce " Nana naɗauka yanzu kinyi girman da zaki gane mai sonki da mai ƙinki, naɗauka ba saina zaunar dake nayi miki irin wannan bayanin ba kinsani Nana wallahi kaf duniya idan kika cire nida mahaifiyarki babu wanda yake sonki so na gaskiya samada Abdussamad nasan kinsan haka, ai ko badan shiba kin kulasa albarkacin ƴaƴansa, da kin san irin wahalar da yasha maybe da bakiyi masa hakaba, amma ace a dalilinki ciwon zuciyarsa ya tashi kuma ciwon ma wanda dalilinki ya samu ciwon tur da wannan abu Nana" fashewa tayi da kuka ta ce " nashiga uku wallahi Abba bansan yanada ciwon zuciya, bansan Abba nada ciwon zuciya ba da wallahi bazan aikata ba please Abba ka taimakeni kada na rasa Daddy wallahi zan iya mutuwa dan Allah Abba " tashi ya yi ya ce " bani zaki bawa haƙuri ba shi zaki samu ki bawa haƙuri amma ki sani koda wasa kika sake ɓata masa rai wallahi ban yafe mikiba NAANAH " tashi tayi ta ce " naji Abba wallahi na yarda nagode sosai " tana gama faɗin haka ta yi waje.........










Tana shiga ta tarar dashi yanda Abba ya fita ya barshi, ƙarasawa tayi kusada shi ta fashe da kuka ta ce " Daddy !! Daddy!!" shuru amma babu amsa hakan yasa hankalinta yayi mugun tashi, ganin yanda take kuka yasa Aliyu ya ce " kiyi haƙuri Nana In sha Allah zai samu sauƙi kinji ki tayashi da addu'a " kallonsa tayi ta haɗe hannayaenta tace " uncle dan Allah kayi haƙuri abinda nayi maku jiya ka yafe min " murmushi ya yi ya ce " Nana babu komai ya huce Allah ya yafe mana baki ɗaya " goge hawayen fuskanta ta yi ta ce " nagode sosai" sannan ta koma gefen gadon ta zauna tana kallonsa tana hawaye, ganin haka yasa Aliyu ya juya ya fita daga ɗakin....,








Wajejen ƙarfe sha ɗaya na safe ya farka tana zaune tayi tagumi ganin haka yasa ta tashi zaune sosai ta kai hannunta jikinshi cikin farin ciki ta ce " Daddyna " runtse idanunsa yayi ganin yasa ta ce cikin rauni " dan Allah Daddy kayi haƙuri wallahi banyi da gaske ba nayi hakane saboda na tabbatar har yanzu kana sona dan Allah kayi haƙuri ka yafemin " hawayen fuskarta ya share mata cikin sanyin murya ya ce " stop crying Nana bakiyimin komai ba har yanzu kinanan a matsayinki na favourite ɗina kinji stop crying banso " rungumesa tayi tana kukan takaicin abinda ta aikata ta ce " Daddy wallahi bazan sakeba forgive me Dad " ganin taƙiyin shuru yasa ya haɗe bakinsa da nata hakan yasa dole ta yi shuru tana jin yanda yake tsotsar bakinta kusan five minutes sannan ya cire bakinsa yana maida numfashi. Tashi tayi ta ce " Daddy zo muje kayi wanka sai kaci abinci" babu musu ya tashi ta taimaka masa yashiga banɗakin sannan ita kuma ta tafi ɗauko masa kaya da abinci.........









Zaune yake tana bashi abincin abaki yana ci shima ya bata ahaka har suka kammala sannan ta fita da kayan shi kuma ya shiga banɗaki, tana shigowa ta tararda Aliyu yana cewa " wato daman ciwon ƙarya ne wato kaga Nana ka warke ko?, to wallahi yau zaku tattara kubar asibitin nan " harararsa ya yi ya ce " kaga ni dai banida lafiya please ka rabu dani " dariya ya yi ya ce " aikam ga rashin lafiya nan nagani " zama tayi gaefen gadon ya kalleta ya ce " ke Nana ki dinga jin tsoron Allah " kwabe fuska tayi ta ce " kai uncle menayi kuma?" tashi ya yi ya ce " bansani ba, yanzu gurin Doctor zani azo ayi maza-maza a sallameku " daga nan ya yi waje, ganin yanda tayi shuru yasa ya kira sunanta yayi mata alama da tazo tasowa tayi ta zaune kusadashi sosai ya kalleta yayi murmushi ya ce " meya faru naji kinyi shuru ina Twins na?" kwabe Fuska Tayi ta ce " Daddy yanzu kafison Twins ko?" dariya ya yi ya ce " ni na isa inason Twins inason Maman Twins, ikon Allah wai yau Nana ce da ƴaƴa " rufe fuskanta tayi tana dariya ta ce ",Allah Daddy banaso ka daina please " dariya ya yi ya ce " shikenan princess na daina sorry kinji " Dariya doctor'n ya yi ya ce " gaskiya Aliyu ya faɗa daman ciwon rashin Nana ne yanzu kuwa sai sallama sai aje asha Amarci Allah ya bada zaman lafiya" dariya ya yi ya ce " narantse ranka zai ɓaci daga kai har Aliyun" dariya shima yake ya aje masa takardun magungunansa ya yi waje, kallon Nana ya yi ya ce " Baby tashi mutafi tunda kinga na warke " dariya tayi ta ce " kaii Daddy wai da gaske tafiya zakayi?" tashi yayi ya ce " idan zaki zo ki riƙeni toh idan kuma bazakiyiba toh zan tafi idan na waɗi ke za'a zaga" tasowa ta yi ta ce " ni awa ai dole nazo na riƙeka dan idan ka waɗi ina na kama " dariya sukayi dukkansu sannan sukai waje, niko nace Allah ya ƙara danƙon soyyaya.......









Comments, and likes.








Story and written by:
*Nanameera*









Meera Loves' yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[1/14, 23:32] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment