Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba , yanzu idan ya mutu alhakinshi akaina wallahi" Tsaki nusy ta yi ta ce "toh so what idan ya mutu? ke ai gaba ta kaiki saboda ko banza sai anbaki tumunin takaba wanda kuma zai isheki har ƙarshen rayuwarki " afusace Hafsa ta ce " aikin banza ke meyasa har kullum bakida fahimta yanzu kowa ya gane nice nayi musu asiri saboda haka kowa ciki yake dani kinga idan har ya mutu nasan wallahi sai sun ɗaureni " murmushi zeeta ta yi ta ce " abu ɗaya zakiyi yanzu" mene shi Hafsa ta tambaya, murmushi ta yi ta ce " nasan wani malami aikinshi kamar yankan huƙa kizo muje idan yaso duk arufe bakinsu babu wanda zai iya ja dake " kallon kin zama mahaukaciya Hafsa ta yi mata ta ce " amma Zeeta bakida hankali masifar da kuka sanyani bai isaba sai kin haɗan da wata ? wallahi nida zuwa wajen boka har abada " tana gama faɗin haka ta yi waje huuuu....



Tana fita suka sheƙe da dariya harda tafawa sannan nusy ta ce " kai zeeta halinki sai ke " murmushin mugunta ta yi ta ce " ai wallahi saina san yanda nayi rayuwarta ta wulaƙanta sai tasan dani ta ke magana " dariya nusy ta yi ta ce " Hafsa kenan kin mutu........






Next Day...



Zaune ya ke yana shiryawa ya kalleta ganin yanda ta yi tagumi ya ce " Jalhan lafiya?" numfasawa ta yi ta ce " wallahi uncle tunanin Nana nake Allah sarki ko yanzu tana ina?ko taci abinci?wallahi inajin tausayinta bare idan na tuna sanda naje gurinta idan kaganta sai kayi kuka " kallonta ya yi ganin yanda take kuka ya ce " Jalhan ki daina kuka kiyi mata addu'a sannan kiyiwa Dude addu'a wannan abun ba komai bane face ƙaddara kuma kinsan ta riga fata " cikin kuka ta ce " wallahi uncle ba kowane ya aikata hakaba sai Hafsa " haɗe rai ya yi ya ce " karna sake jin irin wannan maganar abakinki " ɗaga mishi kai ta yi sannan ya miƙe ya ce "saimun dawo, akula " murmushi ta yi ta ce "Allah ya tsare ya bada abinda akaje nema" Ameen ya ce sannan ya yi waje......







Yana fitowa ya samesu duk family ɗin sun fito kowa yana alhinin abinda zai je ya dawo, kusan two minutes aka fito dashi amotar asibitin, masu dakiya na dakiya wasu kuwa sai kuka suke , Hafsa ma tana jikin mommynta sai kuka take kamar ranta zai fita, ƙarasowa Aleey ya yi gaban Mama ya ce " toh Mama ni daga nan zan huce America saina dinga zuwa ina ganinsa " kallonshi Mama ta yi ta ce " toh Allah ya kiyaye hanya , Allah kuma ya bada abinda akaje nema " Ameen ya ce sannan ya kalli Ma'a wacce ta keta gursheƙen kuka kamar wacce aka cewa Abdussamad ya mutu ya ce "Ma'a ki daina kuka dan Allah addu'a zaki tayashi dashi "ɗaga masa kai tayi dan ta kasa magana sannan ya yi gaba.......



Kawu ne da Daddy sai Aliyu zasu tafi su kaiwa kowa sallama sannan suka shiga mota dan zuwa airport' daga nan kuma suka huce india.....




Comments,like.


Story nd written by:

*Nanameera*






Meera Loves' yhu🥰🥰😍😍[1/9, 11:41] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




🅿️......4️⃣3️⃣&4️⃣4️⃣





________________✍🏻A babban birnin Mumbai na ƙasar india suka sauka kasancewar ansan da zuwansu yasa nan da nan aka shige dashi babban asibitin zuciya na ƙasar mai suna *Apollo heart hospital* ya yinda su kuma suka shige gidansu na india kasancewar sunada apartment a ƙasar....






Kusan kwana biyu amma babu wanda ya sami damar ganinsa acikinsu, Aleey daya kasance likita ya shirya ya je wajen likitocin dasuke kula dashi bayan ya zauna a office ɗin likitan ya zare glass ɗin idonsa ya fara magana cikin harshen turanci " maganar gaskiya patient ɗinku yana cikin wani hali dubada yanda zuciyarsa ta buga hakan ya haifar masa da ciwon zuciya me ƙarfi amma muna iya bakin ƙoƙarinmu ganin ya sami lafiya " numfasawa Aleey ya yi ya ce " yanzu zan iya ganinshi please ?" why not ? Likitan ya faɗa , daga haka suka miƙe dan rakashi wajensa........






Suna shiga ward ɗin wanda ya kasance private ward ne banda ƙarar computer babu abinda kakeji. Suna shiga ɗakin kuwa kusan mutuwar tsaye ya yi duk irin dauriya irin tashi saida ya zubar da hawaye sannan ya ƙarasa gaban gadon, banda kanajin ƙarar bugun zuciyarsa da saika ce mataccene dan babu alamun rai atareda shi banda wannan bugun zuciyar, kusan two minutes yana tsaye akansa sai kuma ya ce " Allah ubangiji ya baka lafiya bro"sannan ya yi waje.......






Tunda ya fito suke kallonshi har ya ƙaraso sannan Daddy ya ce " me ake ciki?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "kudai ku tayashi da addu'a" kallonsa kawu ya yi ya ce " awane hali yake, me Doctors ɗin suka cema ?" " kamar yanda na ce kawai kuyi addu'a Allah ya yaye masa zaifi, ni yanzu zan tafi turkey In sha Allah zuwa next week zan dawo but duk yanda ake ciki ku sanar dani " ok Aliyu ya ce sannan ya tafi dan kaishi airport.........




*Three months later*



Zaune yake yana karatun al-qur'ani akayi sallama aka shigo kallon mai shigowar ya yi batareda ya amsa sallamar ba ko ya amsa a ransa???. Zama Aliyu ya yi ya ce " Dude ga abinci kazo kaci please " kallonsa ya yi amma baice komaiba, cikin kwantar da murya ya ce "please kaci abinci In sha Allah this week zamu koma Nigeria kaji " cikin ƙasa da murya wanda badon su biyu ne a ɗakinba bazai jiba ya ce " ka cewa Mama tazo gobe " da mamaki ya ce " meyasa ?" haka nace maka, ya faɗa batareda ya kalleshi ba, murmushi Aliyu ya yi ya ce "shikenan zan faɗa mata amma please kazo ka ci abinci kaji " tashi ya yi ya shige toilet ba tareda ya bashi amsaba. Girgiza kai ya yi sannan ya tashi ya fita........






Kamar yanda ya bukata hakace ta kasance wajejen ƙarfe biyar na yamma ta sauka agarin kasancewar yamma ta yi yasa Aliyu ya ce tabari idan akayi sallar magrib taci abinci tai wanka sai taje....






Yana kwance ya yi shuru kamar mai bacci amma ba baccin yake ba suka shigo, sallamar Mama dayaji yasa ya yi saurin miƙewa, tana murmushi ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tana kallonsa. Tasowa ya yi ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya, itama tsam ta rungumeshi saboda Allah ya sani tana matuƙar son ɗanta, cikin damuwa ya ce " Mama ba'aga Nana ba ko?" jiki a sanyaye ta ce " eh Abdussamad har yanzu ba'a sami labarinta ba sai dai mu ƙara haƙuri " .


" Mama yanzu mezancewa Baba idan ya tambaye ni ina amanarsa?, banida amsa Mama, me zancewa Allah abisa haƙƙin kulawa da ita da yake kaina ?, i'm looser Mama wallahi nayi asara" ya ƙarashe maganar yana sakin kuka. Rungumeshi Mama tayi tana shafa kansa ta ce " Abdussamad ka daina kuka Allah ba zaima hukunci akan abinda bakada laifi ba, kowa ya san ba laifin ka bane ƙaddara ce kuma babu yanda aka iya dole akarɓa dan haka ka daina damun kanka please, karkasa wani ciwon da ban ya kamaka kaji" ta faɗa tana share masa hawayen fuskarshi ya ce "Mama yanzu ko anga Nana nasan bazata taɓa yafemin ba Mama, na zalunci rayuwarta abanza babban tashin hankalin ma cikin dake jikinta ko tana ina yanzu ban sani ba " In sha Allah tana hannu nagari baza'a cutar da'ita ba kaji" ɗaga mata kai ya yi Aliyu ya ce " Mama ga abincinsa nan wallahi kullum baya ci idan nai masa magana saiya harareni ko yaimin banza" kallonsa Mama ta yi ta ce " meyasa?" kwabe fuska ya yi ya ce " Mama bazan iya cin abinci ba bayan bansani ba ko Nana taci abinci" murmushi ta yi ta ce " taci ma kaima kazo kaci naka kafin mu koma Nigeria kayi ƙiba ka rame sosai " "Mama ni bazan koma nigeria ba, bazan iya zama acikin ƙasarba yanzu " da mamaki Mama ta ce " Meyasa zaka yanke wannan hukunci?" kallonta ya yi ya ce " kiyi haƙuri Mama amma wallahi bazan iya komawa ba kawai kimin addu'a" to matarka fa ? "Sai acemata ta tawo ko kuma tazauna wanda taga yafi ".....






*Three years later*

*Turkey*

Wasu kyawayan yara na gani suna wasa a harabar wani ƙatoton gida, kana ganinsu kasan ƴaƴan madara ne kyawawane ajin farko kwata-kwata baza su huce shekara biyu da rabi ba kana ganinsu kasan ƴan biyu ne namiji da mace, wata balarabiyar mata ce ta fito ta kallasu ta ce " Akeel!!Akeelah kuzo kuje ku shirya yau Daddynku zai fita daku " da gudu suka ƙaraso wajenta Akeelah ta ce " Abla ina zamu ?" murmushi wacce aka kira da Abla ta yi ta ce " shopping zakuje " dariya sukayi suna tsalle sai kuma namijin ya ce " Amma Abla da Mommy zamu tafi ?" ɗaukansa ta yi ta ce " A'a banda Mommy zaku sai dai idan kunje ku tawo mata da tsaraba " ok sukace sannan suka shiga gidan.....





Kai tsaye wani ɗaki suka shiga wanda yakasance ƙarami amma kuma mai kyau bayan ta shirya su ta ce "ohhhya kuje ku nunawa Mommy kwalliyar kafin su Zaitoon su gama shiryawa " murmushi sukai sannan sukai waje da gudu, wani babban ɗaki suka shiga wanda yake ɗauke da parlour dakuma bedroom sai kitchen, suna shiga suka fara kiran "Mommy!!Mommy!!Mommy!!" tana murmushi ta fito daga kitchen ta ce "na'am ƴaran Mommy what's wrong ?" daga sama har ƙasa na kalleta kusan two minutes kafin nagane ba kowa bace fa ce NAANAH.





Comments,like.



Story and written by:
*Nanameera*





Meera Loves' yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[1/10, 17:25] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*





🅿️........4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣






____________✍Kwata-kwata idan baka ƙura idoba bazakace NAANAH bace ta zama babbar mace ta ƙara kyau abinta...




Ɗaukansu ta yi gabadayansu ta zauna kan kujera ta ɗorasu a cinyarta, Akeelah ce ta ce cikin gwaranci " Mommy zamu tafi shopping da Daddy shine Abla ta ce muzo mu faɗa miki " murmushi ta yi ta ce " ok to saikun dawo amma kutawonda kayan daɗi " dariya Akeel ya yi ya ce " Mommy zan siyo miki chocolate da teddies dayawa" rungumeshi ta yi ta ce "thank you, much love " Akeelah ce ta fashe da kuka ganin hakan yasa ta rungumeta itama tana dariya ta ce " Akeelah kishinki ya yi yawa " kwabe fuska ta yi ta sauka daga jikinta ta ce "Mommy bye bye" murmushi ta yi ta ce "ok bye Allah ya tsare " sannan sukai waje ita kuma ta koma kitchen dan ƙarasa abinda take.......







Zaune suke a parlour su kusan bakwai cikin kwanciyar hankali suna cin abinci Akeelah ce ta ce " Daddy kace zaka kaimu Nigeria ranar birthday ɗinmu kuma ya kusa " murmushi wanda aka kira da Daddy ya yi ya ɗago ba kowaneba face Aleey ya ce " In sha Allah Akeelah zamuje Nigeria bada daɗewaba kunaso kuje kuga Daddynku ?" murmushi sukai duka su biyun suna ɗaga mishi kai, dariya ya yi ya ce "yara nason suga Daddynsu kuma kunsan idan ya ganku sai yaji kamar ansashi a al-janna " Abla ta ce " wallahi kuwa dan nasan no more heartache " dariya sukai dukkansu, Nana kuwa miƙewa ta yi tsam tabar gurin dan idan da abinda ta tsani ayi maganarsa bai huce Abdussamad ba , tana shigewa Abla ta yi dariya ta ce "Allah ya sauƙaƙa zafin zuciyarki Nana .......





America........

Zaune suke a gaban Doctor aka kawo musu result ɗin, Abdussamad ne ya karɓa ya buɗe ya fara karantawa, bayan ya gama ya kalli Doctor ya ce " yanzu mene abinyi ?" murmushi Doctor ya yi ya ce cikin harshen turanci " ai babu wata matsala kawai dai za'a kula da ita ne saboda abinda ke cikinta " ok ya ce sannan suka fito......






Bayan sunkoma gida ta na zaune tana cin apple ya kalleta ya ce " In sha Allah gobe zamu tafi Nigeria " murmushi ta yi ta ce " Allah ya kaimu "......




Da daddare suna kwance suna bacci amma azahiri ita ba bacci takeba ganin ya yi nisa a baccin yasa ta tashi ta fito parlour ta ɗauki wayarta ta yi ƙira bayan anɗauka ta ce " Taj yanzu ya za'ayi " bayan wasu daƙiƙu ta ce " Taj wallahi bazan iya ba haba so kake naje abanza narasa aurena?, ka riga kasani cikin jikina na kane to kawai atafi ahaka dan Allah " Hafsa !! taji ankira sunanta, afirgice ta ce " na'am dear" kallonta yake ya ce " meya fito dake adarennan ?" murmushi ta yi ta ce " ruwa nafito nasha" ok ya ce sannan ya yi gaba kallonsa ta yi ta ce " A'a ina zaka kuma?" masjid ya faɗa sannan ya yi waje, ɗaga kafaɗa ta yi alamun bata damuba sannan ta koma ɗaki.....





Zaune yake amasallacin bayan ya idar da sallar banda tunani babu abinda yake kwata-kwata al-amarin Hafsa ya isheshi sai yanzu hankalinsa ya kawo cewa abinda ke cikinta ba nashi bane dan rabonda wani abu ya shiga tsakaninsu har ya manta kamar yanda ya yanke hukuncin da sunje Nigeria to bazai sake dawowa da ita ba, yana wannan tunanin ne Nana ta faɗo mishi arai girgiza kai ya yi ya ce "Allah sarki Nana Allah ya bayyana min ke In sha Allah bazan mutu ba sai na sake ganin ki "yana waɗannan sake-_saƙen har akayi kiran sallar asuba, ya tashi yay sallah yana sake roƙon Allah ya bayyana Nana....






Turkey........



Tafiya sukeyi ita da Ƙawarta bayan sun fito daga lecture ƙawarta ta mai suna Zoya ta ce " yanzu Nana yaushe zaki koma wajen mijinki nasan duk inda yake hankalinsa ba akwance yake ba " murmushin takaici Nana ta yi ta ce " haka kike gani amma ni nasan hankalinsa akwance yake dan daya damu dani da kome zan masa bazai taɓa korata ba " kallonta Zoya ta yi ta ce " haba Nana zuwa yanzu yaci ace kin yafe masa kodan arziƙin ƴaƴansa bai kamata ki ƙullaceshi haka ba kizama mai yafiya" afusace ta ce " har abada bazan taɓa yafewa wanda yaso tarwatsamin rayuwata ba , akan me yasa zaki dinga bani haƙuri akan abinda kinsan ni aka cuta ba daban uncle Aleey ba da yanzu wata maganar ake ba wannan ba saboda haka idan har kinason nadinga ganin mutuncinki to karki sake yimin makamanciyar irin wannan maganar" tana gama faɗin haka ta shige mota ta tafi, kallo Zoya ta bita dashi harta ɓacewa ganinta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce " Allah ya rabaki da taurin zuciya NAANAH.....






Tunda ta koma gida babu wanda tayiwa magana saboda har sannan haushin maganar da Zoya ta faɗa mata take, bayan sallar isha Aleey yasa aka kira masa ita bayan ta zauna ya kalleta ya ce " Nana " cikin girmamawa ta ce " na'am " ya ce " inason daga yau zuwa gobe ki haɗa duk wasu kayanku saboda zamu tafi Nigeria lokaci ya yi da zaki koma wajen mijinki kuma uban ƴaƴanki " afirgice ta ce " dan Allah uncle karufamin asiri kabarni anan please " da mamaki ya ce "Nana har yanzu baki haƙura da wannan maganar ba?, wallahi da nasan zakiyi haka da ban ɗaukeki ba meyasa kikeda taurin kai? To bari kiji ko kina so ko bakya so In sha Allah gobe ni zan maida ke Nigeria na nemi gafarar waƴanda na ɓatawa, tashi kiban guri " tana kuka ta tashi ta shige part ɗinta kallo ƴaƴanta suka bita dashi sai kuma Akeelah ta ce " Daddy me akaiwa mommy?" murmushi ya yi ya ce " babu komai sweetheart kinason zuwa gurin Dadynki ko ?" ɗaga masa kai ta yi ta ce " sosaima inason naga Daddy na " hancinta ya ja ya ce "toh zuwa jibi In sha Allah zaki ganshi tafi ki kwanta " Da murna sosai ta ce " really ?" dariya ya yi ya ce " ki bari ki iya magana sannan kice really kinji " da gudu ta tafi ɗakinsu batareda ta bashi amsaba, shima Akeel tashi ya yi ya bita kasancewar shi ba mai magana bane irin biyunin tasa......






Nigeria.........



Misalin ƙarfe ɗaya na rana suka iso kasancewar ranar sallah ce yasa duk family ɗin kowa yazo na kusa dana nesa, bayan sunyi parking ya kalli Nana ya ce " ki zauna ki jirani anan da yaran " ɗaga mishi kai ta yi sannan shi ya sauka da Abla sai yaransa guda biyu zaitoon da raihan....






Da sallama suka shiga aikuwa kowa ya yi kansu ana murna saboda rabonda su zo kamar haka tun kafin Abla ta haihu, bayan sun zauna kowa sai kallon yaran ake ana masha Allah Aleey ya kalli Abdussamad ya ce " bro ya jikin ?" harararsa ya yi ya ce " ban sani ba sai yau ka tuna dani " dariya ya yi ya ce " Allah ya huci zuciyarka " kallon Abba ya yi ya ce " yanzu Abba kamar wannan mutumin ne ya kwanta akan ciyarka " murmushi Abba ya yi ya ce " toh ya zanyi " dariya Abdussamad ya yi ya ce " toh sai a sauraramin " dariya dukansu su kayi kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki...





Hafsa ce ta shigo da gudu tazo ta tsuguna gaban Abdussamad ta ce " dan Allah Abdussamad kayi haƙuri wallahi sharrin shaiɗan ne " kallonta ya yi ya ce " sheɗan kuma Hafsa ai idan akwai sheɗan to kece babbar shaiɗaniya kin rani da abinda nafiso arayuwata, kin zalunci rayuwar ƙaramar yarinya kin rabata iyaye da tilon ƴarsu ai ko ban sakeki ba wallahi haƙƙi bazai barki ba, sannan kin zubar da mutuncinki tun awaje kuma bayan kinyi aure ma baki fasaba har takai da da aurenki amma kina aikata zina harda ciki, wallahi Hafsa bazan taɓa iya rayuwa dake ba saboda ni ba mazinaci bane, inai miki fatan Allah ya yafe miki zunubanki " fashewa ta yi da kuka ta ce " na cuci kaina nashiga ukuna " babu wanda ya kulata acikinsu saboda agaban kowa ƙawayenta suka faɗi duk abinda ta yi kuma babu wanda sukai mata sharri, gashi kuma ta ƙare da cikin shege, haka ta gaji da kuka ta tashi ta fita bayan ta fita suka ce Allah ya kyauta ....






Aleey ne ya ce " bro inason kabani aron hankalinka nan saboda wannan zuwan nayishi ne saboda kai " kallonsa ya yi ya ce " toh me kuma ya faru?" numfasawa ya yi ya ce " da farko dai inason nabawa kowa na nan haƙuri saboda abunda na aikata ina roƙon ku yafe min " da mamaki kowa ya ke kallonsa ya ciga da faɗin " ban aikata abinda na aikata ba saboda inason zalintarka A'a na aikata ne saboda na taimaki rayuwarku gaba ɗaya " kallonsa Abdussamad ya yi ya ce " please bro faɗamin meya faru, me ka aikata?" cikin nutsuwa ya ce "








Comments, like.






Story and written by:

*Nanameera*







Meera Loves'yhu🥰🥰🥰🥰[1/11, 22:20] Nanameera: *🌹🌹NAANAH*🌹

*BOOK TWO*



Story and written by:
*Nanameera*


..*Tauraruwar royal Star*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*







🅿️..........4️⃣7️⃣&4️⃣8️⃣




____________✍️Ya ce " ni ne na ɗauki Nana " kowa na parlour'n kallonsa yake da mamaki Abdussamad kuwa miƙewa ya yi ya nunashi da yatsa ya ce " kai kaɗauki Nana, bangane wannan maganar ba wace Nanan?" kallonsa Aleey ya yi ya ce " yi haƙuri ka zauna sai namaka bayani " girgiza kai ya yi ya ce afusace " kamarya na zauna banganeba, ya zan tambaye ka kuma kace wani na zauna " murmushi Aleey ya yi ya ce " ni kuma indai baka zauna ba to wallahi bazan faɗaba " Abba ne ya ce " Son zo kazauna please " saboda Abba ne ya yi maganar yasa ya koma ya zauna, Kawu ya ce Aleeyu muna jinka " sauke numfashi ya yi ya ce


" Daddy kamar yanda na faɗa nine na ɗauke Nana shekara uku da suka huce, kuma ban ɗauketa da wata manufa ba sai alkhairi " da mamaki kawu ya ce " Aleeyu meyasa zakai haka? Meyasa" murmushi ya yi ya ce " Daddy ba komai bane yasa nayi haka sai dan inason na taimaki rayuwarta, sanin kanku ne a wannan lokacin da anbarsa da ita to babu shakka wani mummunan abun zai iya faru gareta saboda tanada ƙarancin shekaru bazata iya kare kanta ba shikuma ga halin da yake shiyasa kawai na yanke shawarar na ɗauketa idan ƙura ta lafa saina dawo da'ita" Mama ce ta ce " tabbas abinda kayi shine daidai amma ya akai ka ɗauke Nana?" murmushi ya yi ya ce " Mama kenan, da da farko banyi niyya ɗaukanta ba dukda sanda nazo ƙasar nan aduk lokacin dana ganta sai naji ina matuƙar tausayinta, aranar da wannan abun ya faru ni kuma bana gida bandawo ba sai kusan ƙarfe biyu na dare, toh asanda nayi parking na fito kasancewar ana ruwa ya sa na ɗauko laima na buɗe, ina cikin tafiya sai naji kamar na taka abu dana duba sai naga ashe Nana ce kwance a ƙasa a sume saboda haka nayi saurin ɗaukanta na sakata amota" ruwa ya sha sannan ya cigaba da faɗin " kasancewar ana ruwa sosai yasa duka ma'aikatan basu lura ba har na fita da'ita, a lokacin da safiya ta yi naji anata cigiyarta kuma nasan za'a iya zuwa asibitin yasa nayiwa wani abokina magana ƙaninshi ya rakata turkey na ce akaiwa Abla ita, sanda jikinka ya yi tsamari naso na kawota itama alokacin sai ta faɗa lalura shine dalilin dayasa ban maidota ba, amma yanzu dan Allah bro ka yafemin, Abba kuyi haƙuri " murmushi Abba ya yi ya ce " babu komai kaidai sannunka " kallon Abdussamad ya yi ya ce " bro kaifa? ka yafemin please " murmushi Aliyu ya yi ya ce " Dude please ka yafe masa bagashi ya dawo maka da ita ba " kallon Aleey ya yi ya ce " shikenan ya huce Allah ya yafe mana baki ɗaya " Ameen kowa ya ce Sannan Ma'a ta ce " amma mene ne yasa baka dawo da'ita ba tsawon wannan shekarun sai yanzu?" murmushi ya yi ya ce " Ma' tunda Nana ta haihu nake roƙonta tazo mu tafi, amma taƙi saboda maganar gaskiya Nana ta ƙullaci Abdussamad da Abba fiye da misali kwata-kwata batai musu uziriba ko kaɗan ko maganar su akeyi toh yanzu zatabar gurin, ganin haka yasa na sakata makaranta dan har ta kusa gamawa yanzunma bada son ranta muka tawoba" cikin tashin hankali suke kallonsa Abdussamad ya ce " yanzu ina take ?" ta shi ya yi ya ce " bari na ƙirawota sannan ya yi waje, gaba kiɗaya ya ruɗe Abba ya kalleshi ya ce " ka kwantar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment