Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta girgiza tana tunanin irin tambayar da zeyi mata."Do you have feelings on me ? don't lie"

     Sam batayi tunanin wannan tambayar zeyi mata ba duk da bata rasa amsar fad'a masa ba sede kuma tana mamakin dalilinsa na tambayar.Ya tsireta da ido kawai jiran amsarta yake.

     "No" Ta amsa ba tare da ta bari sun had'a ido ba.

      "No" Ya maimaita abinda ta fad'a.

       "Ok,let's assume I love you? Will you love me back?"

       "No"

        "Why?"

        "Because I don't love you"

         "Your heart is for only one person?"

         "I want to sleep" Ta  fad'a tana janyo blanket d'in.

       "Are yo sleeping like this?"Ganin ba sleeping dress bane a jikinta.

     " Uhm"Ta rufe kanta.

     Tashi yayi yazo fita ya kashe wutar d'akin sannan yaja 'kofar,tana jin fitarsa ta bud'e kanta,  tambayoyin da yayi mata ta shiga yi ,seda ta jima kafin bacci ya d'auketa.

       12:13am ya farka daga bacci ,da tunanin Laila a ransa ya farka.Drawer side lamp ya kunna ya tashi zaune agogon d'akin ya kalla yaga 12am,mi'kewa yayi tsaye ya bud'e 'kofarsa ya fita zuwa d'akinta,yana murd'a handle d'in yaga a bud'e 'kofar ma take.Tana ta baccinta yau ma tafin hannunta na kan fuskarta kamar rannan hakan yasa shi yin murmushi yanzu ya fahimci d'abi'arta ce haka.A hankali ya d'akko stool d'in mirrorn d'akin ya ajje opposite da ita ya zauna se 'kare mata kallo yake,tuna ko pic d'inta bashida yasa ya koma d'akinsa ya d'akko wayarsa ya komo ,hannun data kare fuskarta dashi ya matsar yadda fuskarta zata fito,pictures kala-kala yayi ta d'auka har kusan 12:40am tukun ya koma d'akinsa.

            ★★★
 
      Kwanaki suna sake yin nisa ,Laila lecture d'insu yayi nisa  kullum Amjad ne yake kaita school baya ta'ba bari ta tafi da kanta,hatta dawowa gida wasu lokutan shi yake d'akkota hatta saba ma yanzu ta dena gudun.Haka ta 'bangaren abinci ma inde tayi girki zeci inba wai yaga besan   irin abincin ba.A kullum Laila sake shiga ransa take duk wani abu da tayi birgeshi take haka idan yana office yata kallon photos nata kenan ,tunanin ta ba 'karamin d'auke masa hankula yake ba daga al'amuransa na yau da kullum ana meeting seya tsinci kanshi yana tunaninta wanin sa'in harse P.A d'insa ya masa magana.

     Yau ma bayan ya tashi daga aiki ya biya mall 'yan siyayya,wani henna ya gani wanda ya tuna masa da 'kunshin da Laila tayi kwanakin baya,jiyai yanaso yaga ta sake yi dan haka ya siya mata.

        Yana zuwa school d'insu tana fitowa,suna tafiya yana mata tambayoyi da suka shafi school d'inta rabi maganar da yaran hausa yake dan yanzu ya fara iya hausa sosai sede wajen pronouncing ne ake samun kura-kurai  , kad'an -kad'an take bashi amsa dan ita har yanzu ta'ki sakin jiki dashi.Seda suka isa gida tazo fita ya kira sunanta."Laila"

      Tana juyowa taga ya mi'ko mata package na  henna d'in.Seda ta 'karewa lallen kallo sannan ta dawo da kallonta kansa daga bisani kuma ta kar'ba ba ko godiya tayi ficewarta.

       Tana shiga d'aki ta bud'e drawer ta ajje ciki ta rufe ta wuce bathroom tana fitowa bayan ta shirya tayi sallahr asr.

     Knock!Knock! Taji bugun 'kofarta.Dama hijab d'in ta na jikinta ta tashi ta bud'e,yana tsaye bakin 'kofar fuskarsa d'auke da murmushi.

      "I just wanna inform you that I will take a trip tomorrow morning"

    Kai kawai ta kad'a a ranta dad'i kamar ta ziba ruwa a 'kasa tasha.
       
        "Alhamdulillah " Ta fad'a a ranta.

     Dama gobe Saturday bikin Bahijja 'kawarta,tasan idan yana nan ba yadda za'ai ta kwana a gida yanzu kuwa setai amfani da wannan damar.

     Yayi tunanin zega ta damu amma yaga sa'banin hakan ,du seyaji jikinsa yayi sanyi,gwiwa ba 'kwari ya koma d'akinsa.

      Laila da farinciki ta kwana a ranta da sassafe ta soma had'a kayanta,dan tsabar farinciki kota kan breakfast bata biba,se wajen 9:30am ta sakko 'kasa  a kan dinning ta  hangi wata takarda dake ninke.Har zata shige ta ta dawo, tana bud'ewa  taga short note.

      I'm sorry for leaving without saying goodbye, I don't wanna wake you up.

Amjad

    Duk da ba wani damuwa tayi ba amma seda taji wani iri dan tayi tunanin yana d'aki,ninke ta tayi ta ajje kan table d'in sannan ta shiga kitchen had'a breakfast.

         Cikin azar'ba'bi tayi sauri tayi breakfast tana kammalawa ta koma d'aki ta shirya,kit d'in data sa kayanta ta d'auka ta fito daga gidan ,a hanya ta kira Maryam ta fad'a mata tana tahowa.Laila tana isa gida ta tafi gidan 'kunshi aka tsantsara mata ta dawo gida.

      "Gan d'oki" Mami ta fad'a.

       "Nice fa babbar 'kawa Mami"

        "Da haka nan aka ce kiyi 'kunshi da tuni kina nan kina zun'buro baki amma dayake kin sa kanki har rawar jiki kike"

     "Kwana nawa zeyi?"

      "Sati d'aya" Tayi 'karya.

       "Abin nema ya samu"

       Kallon Mami kawai tayi a ranta ta san 'karya take.Wajajen 4:30pm ta tsantsara kwalliyarta ta rangad'a d'auri ta yafa gyale d'an 'karami ta fito.
  
      "Inde a haka zakije kuwa sede bazaki fita ba,haka kike fita mijin naki ya barki?"

      "Mami biki ne fa?"

       "Koh meye zaki wani d'ora mayafi a wuya ke bakisan babbancinki da 'yan mata ba?"

     Bata fita ba seda ta koma ta sauya mayafin ,ita kad'ai ko 'yan rakiya ma bata d'auka ba.

      7:30pm ta komo gida Mami kam tayi ta mata fad'a tana kallo Amjad yana kiranta a waya amma ta'ki d'auka,daga baya taga text nashi.

      Hi,how was the day? Hope you're doing good.

      "Ina ruwanka?" Ta fad'a a fili tayi cilli da wayar.

      "Komai ace aure..aure "

       Tunda ta cillar da wayar bata sake dubata ba tayi baccinta,Amjad kuwa baida tunanin daya wuce nata ya matsu yaji muryarta yana ta jiran reply amma shiru.Ko washegari ma beyi zuciya ba da safe seda ya kirawo ganin bata d'aga ba yayi mata message.

       Morning hope you're doing good?

      Laila ba ita taga message d'in ba se to 10am shima 'kin reply tayi ta maida wayar ta ajje.Dan saboda Mami ta barta taje yinin bikin seta d'auki Fauzan suka je tare da ita aka kai amarya sannan ta komo gida.

       Messages da missed call ba adadi ta tarar a wayarta banyan ta komo  gida.

     "D'azu kuwa Amjad ya kirani " Taji Mami ta fad'a.

     "D'azu" Ta maimata tana zare ido a ranta tana fad'in Allah yasa Mami bata gani 'karya nayi ba.

     "Mami se kuka gaisa?" Ta tambaya tana neman 'karin bayani.

      "Ehyi naji yanzu ma ai Hausa ta shiga bakinsa ba kamar da ba"

     "Uhm" Ta fad'a zuciyarta na raya nata Mami batasan komai akai ba.

     "Ashe ma gobe ze dawo" Taji Mami ta fad'a.

      Ita a tunaninta ze iya yin sati d'aya ,nan take murnarta ta koma ciki.

      "Uhm" Ta fad'a a ciki.

        "Toh gobe seki koma da safe aiko"

         Nan ma ta amsa da "Uhm".

      Haka ta kwanta tana jin haushi plan d'inta ya rushe kwana biyun datai d'in ma bata gode ba.Washegari da safe tayi ta la'kai-la'kai ta gaji da baccin safen ma amma ta'ki tashi seda taga dama kafin tayi wankan ma tayi ta la'kai-la'kai haka breakfast ma, ba ita ta tafi ba se wajen 1pm,tan d'an sahu taji shigowar text.

      I'm on my way back home

     " Naji"Ta fad'a.

      Tana shiga gida tayi zamanta a d'aki ko kitchen bata kalla ba balle tayi tunanin wani abu shi girki.Tana yin sallah ta kwanta bacci, bama baccin take ji ba ta dole kawai tayi forcing kanta tayi baccin.

    3:30pm 'karar doorbell ya tasheta daga bacci,seda ta d'auka mayafi ta yafa dan ta ayyana shine ya dawo.Fuakarsa d'auke da murmushi  yake kallonta amma ita kuwa...

      Bata tsaya ya shigo  ba ta komo ciki."Laila, you don't like me here?"Ya fad'a bayan ya shigo.

       Shiru tayi bata amsa ba kuma bata cigaba da tafiyar ba haka bata juyo ba.

       "Are you mad at me?"

       "No I'm not" Ta amsa sannan ta hau sama.

      Shide ya rasa gane kanta the more yana showing mata kindness the more tana gudun sa besan dalili ba.Hakannan ya wuce d'akinsa ya watsa ruwa ,daga shi se singlet ya sakko 'kasa neman abinda zeci dan yunwa yake ji.

      Babu wani alamar girki daya gani,'karshe se 'bigewa yayi da shan cornflakes,ya fito daga kitchen d'in ya had'u da Laila.Yanzu ba mayafin daga ita se doguwar riga na material red colour,'kunshin hannunta ya yi rad'au a fatarta,idanunsa basu sauka a ko ina ba se hannunta.Ba 'karamin dad'i yaji ba ganin tayi 'kunshi,a hankali ya taka zuwa inda take.

    "Beautiful, I like it" Ya fad'a lokacin ya dawo da kallonsa kan Laila.

   Hannayen nata ta 'boye a bayanta tana sunkui da kai.Batayi aune ba taji ya ri'ko hannayenta biyu kamar yarinya,duka biyun ya d'ago dasu kusa da face d'inshi ta rasa ma abinda zatai illa tsayawa kallan ikon Allah.

     "Your hands always look good" Kamar 'kiftawar ido taga yayi kissing hannayen ta tsaya uwa gunki,seda hankalinta ya dawo jikinta tayi saurin 'kwatar hannun ta koma d'aki da sauri ta barshi a tsaye ya rasa ma mey zeyi sam ya kasa controlling kansa shikansa besan yadda akai haka ta faru ba.

     Tana shiga d'aki tasa key ta rufe,hannayen nata tayi ta kallo tana tinawa.

      Da'kyar ta iya tashi yin sallahr asr dan tsabar hankalinta ya kasa kwanciya se recalling take.Yunwa take ji amma ta kasa sakkowa kitchen, har bayan maghrib se shawara take daga 'karshe de ha'kura tayi ta kwanta a haka yunwa na addabarta.

       Washegari 8:12am ya gama shirin office saboda makarar da yayi ko tunanin breakfast ma beba ,koda ya sakko 'kasa yaga be ganta ba.Haka ya hau bene yayi knocking d'akinta,tana zaune dama ba zuwa zatai ba yau.

      "Laila" Ya kirata.

   Da farko 'kin amsawa tayi se a karo na biyu ta amsa .

     "Are you not going to school today?"

      "Yes" Ta amsa daga ciki ta'ki tasowa ma daga kan gadon balle ta bud'e 'kofa.

      Jin haka yasa ya kama hanya  ya sauka,yau duk seya ji ba dad'i fitar kasancewar ba ita.Yana driving kusan rabin hankalinsa baya gurin,ya hau gadar sama yana driving be lura ba da wuri sega mey d'an sahu ya biyo one way garin kaucewa mey napep d'in   motarsa ta daki gefen gadar ta fad'a 'kasa,upside down ta sauka ,tayi mugun chanja kamanni,mey d'an sahu ya daki gini, lokaci guda jama'a aka hau salati a take waje ya d'inke da mutane.

     *Shocked?? Don't forget to comment.*

*Dijensy❤*

     

     

     

     

   

    

    
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

  *Thank you for your warm support sister,Amjad fans kuma ina godiya ,ana tare*


2⃣5⃣-2⃣6⃣


       Mey d'an sahun da aka yi 'ko'karin ciro shi daga d'an sahun aka ga ko numfashi bayayi ,kwance aka ajje shi gefe,daga 'kasan gada kuwa mutane uku ne suka shiga kici kicin bud'e 'kofar motar amma abu ya gagara ,seda ambulance suka 'karaso suka ciro Amjad da 'kyar sakamakon belt dake ma'kale a jikinsa, jini ya wanke fuskarsa haka aka sanya shi a mota a sheme.

               ★★★

     2hrs later,tana d'aki tana duba handout wayarta tayi ringing,ganin Canada jikin screen ta'ki picking.Sau biyu ana kira bata d'aga ba se ana uku."Hello".Cikeda  'kosawa.

      Jin murya daban bana Amjad ba yasa ta gyara zama.Tana jin abinda aka fad'a ta d'ayan 'bangaren ta saki wayar kan gado.

       Ta rasa abinda zatai,wayar ta d'auka ta sake kallan call d'in."Amjad "Ta furta a tsorace.Tafi 10min kafin daga baya ta d'au waya ta kira Mami.

      " Innalilahi wa innailaihirraji'un"Mami ta fad'a.

      "Kina asibitin?" Mami ta tambaya cikin rud'ani.

        "A'a"Ta amsa feeling guilty.

        " Mey kika zauna yi da baza ki tafi ba?"

        "Zan tafi yanzu" Ta fad'a.

         "Toh nima ina tahowa".

Mami kafin ta tafi seda taje gidan Kawu Yunus ta fad'a masa halin da ake ciki,tare suka tafi asibitin kusan tare suka isa da Laila, Kawu Yunus ne ya kira Dad ya sanar masa.A gabansu aka shiga dashi theatre room hankalinsu yayi mugun tashi dan yanayin da suka tsince shi.8:15pm aka fito dashi daga nan aka kaishi d'akin kwanciya,suna kan bench ko d'akin basu samu shiga se bayan doctor ya fita daga d'akin,Mami da Kawu suka shiga abin tausayi hannunsa yasha plaster sakamakon karaya se kanshi an zagaye masa da bandage, ga 'karin jini da ake masa.

" Allah ya baka lafiya"

"Ameen" Mami ta amsa cikin nuna jimami.

Kawu Yunus se can dare ya tafi ya bar Mami da Laila data kasa shigowa tana waje kan bench itama daga baya Mami fitowa tayi ta zauna kan bench d'in.

Mom kuwa basu san mey ake ciki ba se ji sukai Dad yasa su shirin tahowa Nigeria da suka tambayesa dalili ya'ki fad'a musu.Koda ta kira Amjad d'in ma ta fad'a masa suna zuwa taji wayar a kashe.

Washegari 9pm suna Nigeria, Mom tunda taga an shigo asibiti jikinta yayi sanyi."Tell me what's going on?"

"It's Amjad..."

"Mey ya sameshi ? What happened to my son?"

"He had an accident"

Dukansu ba wanda be firgita ba,cikin rashin ha'kuri driver na parking ta fita a motar Dad yana kiranta amma ta'ki tsayawa,da 'kyar ya samu ta tsaya ganin ba sanin d'akin tai ba.Seda suka kira Mami ta fad'a musu numbern room d'in.Cikin rud'ani suka 'karasa ,Laila tana zaune kan bench tagansu tsidik cikin hanzari suka shiga ita de ta bisu da kallo dan har lokacin ta'ki shiga d'akin.

Har yanzu yana kwance same position ko motsi beyi ba,Mami da Zakia tuni suka fara tsiyayar hawaye.

"Amjad" Ta 'karasa gefen gadon.

Hannunta ta d'ora kan gashin kansa tana shafawa.

"My child"

Suna tsaye a kansa Mami ta shigo d'akin,bayan sun gaisa suka jajantawa juna Mami se bawa Mom ha'kuri take amma ta'ki dena sharar hawaye.

"Ina Laila" Mom tayi 'ko'karin tambaya.

"Ta'ki shigowa tana waje" Mami ta amsa.

Mom da kanta ta fita wajenta ta tararda ita ta jingina da alama tayi nisa cikin tunani."Laila"Ta kira sunanta.

Da sauri ta dawo daga tunanin data tsillima."Mom,Ina yini"Ta gaisheta tana sunkui dakai.

Hannu tasa ta d'ora a kafad'arta."Kiyi ha'kuri kinji,pray for him ze zamu sau'ki"

Kai kawai ta kad'a ba tare da ta d'ago ba,bata ankara ba taji Mom ta jawota jikinta kamar 'yar baby tana shafa bayanta se bata ha'kuri take.Itade Laila tayi lif ita kad'ai tasan abinda take ji a ranta.

Sun dad'e a asibitin kamar baza su tafi ba Dad ya tashesu suka tafi,aka bar Mom se Laila Mami ma gida ta koma. Mom bata da buri irin taga ya farka,tafi 1hr tana zaune gefen gadon tana kallonsa.Laila data shigo d'akin ma daga can baya ta ta tsaya kamar bodyguard ta'ki zama.

Seda dare ya nisa ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin,a hankali gyangyad'i ya fara d'aukanta daga bisani tayi bacci.Mom data kalleta du setaji tausayinta ya kamata.


★★★

Kullum se su Dad sunzo asibitin ,yawanci su suke kawo musu abinci sometimes Mami ,har anyi kwana shida amma Amjad be farka ba abin har ya soma damin Mom ko tashi ta shiga bathroom ba son yi take ba dan gani take kamar idan ta dawo bazata ganshi ba.Laila dan ma Allah yasa yawancin coaurses d'in duk anyi covering ba zuwa school take ba.

Yau ne ma da Aliya ta kirata take fad'a mata za'ai test shine taje school d'in tana yi ta komo asibitin.Ganin Dad ,Shaheed Zakia da Kawu duk suna d'akin yasa ta fito ta samu bench tayi zamanta,sun jima kafin su fito tayi bacci kan bench d'in lokacin 10pm yayi.

★★★

Gidansu Amjad taf yake da mutane,tana shigowa taga su Mami suna zaune kan carpet da sauran mutanen da ba sanin fuskokinsu tayi ba,Mom ta hanga daga kan step d'in bene gefenta Zakia se kuka take tana wata magana da baji take ba.Gwiwa a sanyaye ta 'karasa inda suke bata yi musu magana ba ta haye saman ,'kofa ta gani daga gefen side d'inta a bud'e tana shiga taga gawa a kan makara cikin likafani ba kowa d'akin a tsorace ta 'karasa tana zuwa taga fuskar a bud'e ganin Amjad ta saka ihu.

"Amjad!"Ta mi'ke firgit se zufa take ,asibitin yayi shiru se yanzu ta gane mafarki take,zuciyarta se dukan uku-uku take da sauri ta tashi ta bud'e 'kofar d'akin ta shiga.

Mom ta gani tana bacci a zaune kan kujera,1:28pm agogon d'akin ya nuna.A hankali ta 'karasa gadon tana kallonsa ko 'kifta ido ta'kiyi,gefen gadon ta zauna tana 'kare masa kallo mafarkin datai yana dawo mata ,zuciyarta ce ta raya mata what if da gaske mutuwa yayi.Tsoro ne ya hauta lokaci guda, hannunsa ta d'ago ta d'ora a tafin hannunta 'kwallar dake ma'kale a idanuwanta ta zubo kuka sosai ta shiga yi mara sauti.Mom dede lokacin ta bud'e idanuwanta ta d'ora su kan Laila dake zaune gefen gadon ri'ke da hannunsa, ganin haka setayi murmurshi ta maida idanuwanta ta rife a zuciyarta tana mey jin dad'i ta wani 'bangaren tana jin tausayin halin da Laila ta shiga.Tafi 20min a haka har lolacin bata sake masa hannunsa ba sede yanzu ta dena kukan,kamar gangan taji motsin yatsansa d'aya a hannunta.Tana kalla taga ba gangan bane ,a sanyaye ta mayar da hannunsa ta ajje ta mi'ke daga kan gadon zuciyarta kuwa wani irin farinciki mara misaltuwa ne ya ziyarce ta.Gefe ta samu wani kujerar ta zauna cikin 'kan'kanin lokaci bacci ya saceta.

Yau ma da safe akai mata waya ake fad'a mata za'ai test dan haka ta shirya ta tafi school,har se to 12pm akai musu test d'in bayan nan kuma aka shiga lecture,hakannan ta samu ta zauna se 4pm tukun ta komo asibitin.Tana shiga ta tsaya daga 'kofa ganin mutum ido biyu tayi yana magana da Mom amma bata san mey yake cewa ba.Ba wanda ya lura da shigowarta se Zakia ta kira sunanta,se lokacin kallo ya komo kanta Amjad yana daga kwance ya kallota a wahale idanunsa sun 'kan'kance fuskarsa ta nuna alamar ramewa.

"Laila,I'm glad you're back" Mom ta fad'a tana kallonta sannan ta komar da kallonta kan Amjad irin alamar ya farka d'innan take nuna mata.Kallo d'aya ta sake yi masa ta kawar da kanta,duk wani move datake yana kallonta gashi ko magana yaga ta'ki yi ,su Mom kuwa basu ma lura da hakan ba.Mami da sukai waya da Mom take sanar mata ya farfad'o tare da kawu suka zo suka duba shi daga nan ta sake tahowa da Laila wasu kayan nata.Se 9:30pm suka bar asibitin aka bar Mom da Laila,gabaki d'aya ta kasa sake wa fiye da da.

"Amjad you need to eat" Mom ta fad'a dan tun d'azu da rana dayaci chicken spaghetti be kuma cin wani abu ba.

"No I'm ok"

Fruit salad d'in ta samu ya sha kad'an,ita de Laila kallonsu kawai take duk abinda suke,jinta take a takure dama ta koma gida da yafi mata take fad'a a zuciyarta.Bayan yasha magani ya kwanta bacci daga baya Mom itama tayi,Laila 'karshe se tunanin yadda zata 'kare wannan zaman take.

Washegari 5:40am Mom ta tashi bayan tayi sallah Amjad ya farka ta taimaka masa yayi taimama yayi sallah,Laila dama bayin sallah zatai ba amma dukda haka takan tashi sede kuma yau baccinta tayi har se wajen 7:30am ta farka.Tana bud'e ido taga Mom tana gefen d'anta tasa abinci a gaba tana bashi yana ci da 'kyar,duk kunya taji ta isheta tashar'bi bacci surukarta na kallo abin kunya tayi tunani a ranta.Kamar ko yaushe cikin rissinawa ta gaisheda Mom ganin ido yasa shima ta gaishehi harda tambayarsa ya jiki, shikuwa ya'ki amsawa yayi kamar beji ba.

Bayan awanni kad'an sega su Zakia sunzo asibitin,dama haka take so tana ganinsu tayi fitowarta ta fita can waje ta samu bench ta zauna tana kallon shuke-shuke.

"Mom are you staying here until..." Shaheed be 'kare magana ba Mom tace."No..no I'm not going to stay here beside I' m going back home today"

"What? Are you leaving me like this?"

"Amjad ,Laila is here and I think is ok like that"

"Yes!" Zakia da ba da ita ake ba ta tsomo baki.

Kallonta kawai yayi ya kawar da kai ba tare da yace komai ba dan yanzu ba lokacin wannan bane.

"Your wife is here,I'm sure she will take good care of you I knew it"

"But.."

"Do you want me to tell you something you don't know?"Ta tambaya bayan data ga yaran hankalinsu baya gun.

"What?"Ya tambaya.

" The time when you was unconscious I saw Laila holding your hands crying, tears flowing down her cheeks,you know why? Because she cares about you she don't wanna lose you "

Kallanta ha tsaya yi saroro yana tunanin anya kuwa Laila ce zatai haka.

"Didn't you believed me?"

"I do 100% remember I trust you Mom" Ya fad'a yana murmushi har cikin ransa ,farinciki ya mamayeshi.

"Laila cried for me ,does this means she loved me?" Abinda ya shiga tambayar zuciyarsa kenan yana mamaki.Ya 'kosa yaganta a halin yanzu amma ya neme ta a d'akin ya rasa ko ina tayi?

Laila seda ta gaji da zaman wajen ta komo ciki,abinda take gudun shi ta sake tararwa watoh kallon da yake mata,ko abinci ta'ki sakewa taci Zakia tana mata hira kad'an-kad'an tana amsawa,suna zaune har Dad yazo bayan 'yan awanni suka tashi tafiya jin Mom tace tafiya zatai itama Laila hankalinta ya d'aga.Kamar ta tsuguna ta ro'keta ta zauna haka taji,tana kallo ta tattara inata-inata suka tafi tare

Please Login or Register in order to submit comment