Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kannan Mami ta tambayeta.

    Se lokacin ta shafa kunnenta taji ba d'an kunne d'aya,zuciyarta ce ta bata a d'akin Amjad ta yar.

     Amjad bayan fitarta ya lura da d'an kunnen ma'kale a jikin shirt d'inshi,kallo d'aya yayi mishi ya bud'e drawer ya cillar a ciki coz yana expecting zata zo kar'ba.

     Hira suka shiga yi irin ta 'yan uwa har wajen maghrib tukun suka tafi.Suna tafiya ta koma d'aki ta d'akko mayafi ta yafa ,d'akkunen kuwa ta cire ta sauya wani dan bata jin zata iya komawa ta d'akko kayanta.

              ★★★

     Tun abinda ya faru Laila bata sake yarda ta shiga d'akinsa ba ,Amjad ya samu sau'ki har ya koma aikinsa.Aliya a makaranta daga tayi mata maganar aurenta seta share zancen gashi lecture tayi nisa  yanzu har sun fara test,tana dad'ewa ma bata sakko 'kasa ba rabon data had'u dashi tun da safe yanzu har 10:23pm gashi an shigo watan azumi gajiya take sata kwanciya da wuri.

      Amjad ma yanzu da wuri yake barin wajen aiki kuma yaci abincin ta ya'ki ko tayi dayawa sede ta bawa mey gadi da yazo kwanannan,wani lokacin fita yake restaurant ko ya siyo ya taho dashi kullum a wahale.

     Aliya haka tayi ta 'ko'karin turo mata video girke-girke iri-iri idan taga dama tayi wani kuma ta share musamman idan taga mey wuya ne.

     Yau ba school,tunda ta tashi take jin alamar ciwon mara kad'an-kad'an aikuwa wajen 11:30am azuminta ya karye,dan haka ta shiga kitchen dan had'a abinda zata ci indomie kawai ta dafa bayan taci tasha magani ta komo d'aki tayi kwanciyarta.

      Amjad shaf ya mance be tafi da key ba,2:30pm ya dawo a gajiye.Qlin!Qlin ya danna door bell shiru, har ya soma gajiya da tsaiwa.Laila kuwa baccinta take ta shara bata san yana yi ba.Gwada kiranta yayi a waya amma switchoff tana charge.

     Ransa ba 'karamin 'baci yayi ba gashi ko mey gadi baida key d'insu na ciki,cikin mota ya koma ya kunna Ac.Se wajen  3:45pm ya koma ya sake ringing,dede lokacin ta sakko 'kasa ita a tunaninta ma ko ba'ki tayi.Yana tsaye fuskarsa ba annuri kamar ya sha'keta haka yaji, gefe ta matsa ya shigo tukun ta rufe 'kofar.

      "I spent more than 1hr waiting for you to open this fucking door"

       "Ni na hanaka fita da key"

        "You..." Ya nuna ta da yatsa.

        Matsawa tayi daga pointing d'inta da yayi ta waiga gefe."You're disrespecting me"

      "Nasan   matsalarka ,yunwa" Ta fad'a a ranta.

      Ring! Ring! Wayarsa tayi 'kara, Dad ya gani  jikin screen.Be sake wata maganar ba ya bar gun.Gwalo ta bishi dashi ba tare da yasan tana yi ba.

   Da lokacin shan ruwa doya da 'kwai kawai tayi ta d'ibawa mey gadi saura data ci ta ajje,Amjad yau ko fita ya siyo abincin beba koda aka sha ruwa iya fruits yasha da. dabino.Seda ya dawo daga masjid ya lura da flask d'in da ta ajje doya da 'kwan,d'aya ya d'auka yasa a baki yana feeling taste d'in.

     "Not bad" Ya fad'a kafin ya sake d'aukan wata ya lun'kume a wasa awasa har ya kusan cinyewa.

    
Washegari da safe bayan ta gama shirinta tayi toasting bread da d'an yawa saboda zata je school dashi.Tana cikin yin breakfast Amjad ya shigo,jitai kunya ta kama ta lomar dake bakinta ta had'iye da 'kyar ,saboda gudun karya ganta yasa bata ci a dinning ba amma duk da haka seda ya ganta.

     "Are you suppose to eat? You don't even feel guilty of what you're doing"Ya 'karaso yana janye plate d'in gefe ,kuma ya gane amma jan magana yasa shi yin haka.

    " Meya shafe ka?"

     "Repeat what you said, I can understand little of it"

     Jin ya fad'i haka tayi shiru bata kuma wata maganar ba.

   "Yarinya I'm soon living you here alone"

    D'agowa tayi ta kalleshi jin ya anbaci yarinya"Toh a ina ya fara koyan wannan?"

      "Surprised koh?"Murmushi kawai yayi ya fita daga kitchen d'in, abincinta ta cigaba da ci tana tunanin yadda ya fara iya Hausa.

     Tunda aka fara azumi sau d'aya ta sake zuwa gida yanzu har za'a 'kar'kare.Tana d'aki bayan ansha ruwa yazo yace mata ta shirya su fita,seda suka tsaya a mall tasan inda zasu.Siyayyar kayan sallah suka yi,daga nan suka komo gida ,su Maryam da suka zo ta basu suka kai mata d'inki,ranar sallah ji take kamar ba sallah ba ita kad'ai sede idan kunna chat tayi,jitai tayi missing tuwon Mami na sallah ,kira tayi a ways race su kawo mata ko abincinta 'kinci tayi tana jira anjima su Nusaiba su kawo mata tuwo.

    Basu suka zo ba se 4pm,ganin 'kunshinsu datai taji ya birgeta jitai dama itama taje anyi mata ,Aliya seda tayi ta fad'a mata amma ta'ki.

    Biyu ga sallah ta shirya zata gida,Amjad ne ya d'auketa badan yaga dama ba saboda Mom tace yaje.Suna tafiya a hanya ta ciro mirror d'in powdernta tana kallan fuskarta." You better stop it ,you're not even beautiful "Taji ya fad'a.

    Har cikin ranta taji haushi" Banyi dan kace nayi kyau ba"Tayi maganar a fili.

     "I can understand all you're saying better watch your tongue"

     Baki ta zun'buro ta mayar da mirror d'in, sam bata lura dashi ba yana ta satar kallonta,kayan jikinta ya amsheta sosai.Lace tasa maroon da torches golden se sar'karta ma golden data kwanta a wuyanta,fuskarta ma tayi makeup dede ,lipstick maroon tasa da eye liner kwalli ya fito tar a idonta.Mayafinta ma golden ne tayi d'aurin....(guess).

   Zaman kurame sukayi har suka isa gidan Mami,ta bud'e  'kofar zata fita ya tsayar da ita."Don't expect me to take you back home ".

     " Better "Ta fita.

     Se bayan ta shiga ya shiga gidan ,yana gaisawa da Mami ya fita daya had'u da Fauzan  a 'kofar gida ya bashi 10k 'yan 500 sabbi.

    " Ashe de da sauran mutunci"Laila ta fad'a sanda Fauzan ya shigo yana nunawa su Mami.

     "D'azu nayi waya da Maman shi take fad'a min Amjad d'in zeje can Canada d'in" Mami ta fad'a.

    "Uhm..eh" Ta fad'a a ranta kuwa tunani ta shiga yi,da gaske yake ashe.

     "Mami yaya gida zata dawo ko?Nusaiba ta tambaya.

     "Eh toh.."

     "Ehmana nan zan komo" Laila tayi saurin fad'a.

      Dad'i taji sosai dama exam zasu fara ba dad'ewa ,a ranta tana fad'in"Na huta yaje can ya 'karata da ba'kin halinsa".

       Laila bayan ta 'kare wuninta a gida wajen 5 :30pm ta tashi tafiya dan tasan ba zuwa ze d'aukanta ba.Lokacin da ta koma gida ta tarar yana gida,d'akinta tayi wucewarta.

     Haka ta 'kare sallah ba inda ta sake zuwa,bayan 1week suka koma school,yanzu shirye-shiryen exam suke ba dad'ewa suke ba 12pm wani sa'in ta komo gida,ita jira take taji yayi mata maganar tafiyarsa amma shiru beyi ba.

       8:05am ta sakko 'kasa,'karamar trolley dake girke a living room ta tsaya kallo bata gama sa'ke-sa'ke ba sega Amjad yana sakkowa daga steps. Yau ana ganinsa za'a san yana cikin farinciki,specs dake idansa ya zare.

     "Home alone" Taji ya fad'a.

      "Ni nace maka anan zan zauna?"

      "You can speak the way you like to but you can't change it ,I'm leaving now".Yaja trolley ze fita Laila tace." I'm not staying here alone "

      "That is none of my business, the decision is yours" Yayi mata waving bye cikin rainin hankali.

     Tana gani driver ya amshi trolleyn yasa a bayan mota ,Amjad ya shige baya abinsa driver ya jasu suka fice. Bata 'kara ko minti d'aya ba tayi sauri-sauri ta haye sama.Nan take ta soma had'a nata kayan duk wani school things ta d'auka tazo duba phone d'inta kan drawer ta lura da kud'ad'e kan drawer d'in 50k ta gani.Handbag d'inta kuwa ta d'auka ta zira a ciki tasa wayarta key d'in gidan ta d'auka ta sakko bayan data kulle d'akinta,sauran doors na 'kasa ma ta rife tukun exit door taja akwatinta ,mey gadi ne ya samar mata Napep ta tafi.

    Tun a hanya ta kira Mami take fad'a mata tana hanya.Tana shiga gida ta ajje akwatinta a d'aki ,se murna take."Se yaushe ze dawo?"Mami ta tambaya.

     "Uhnmm.uh..3weeks" Ta kintata ta fad'a.

      "Allah ya kaimu"

      "Ameen" Ta amsa.

       "Mami wainar gero nake son ci" Laila ta fad'a.

        "Toh ta rashin ta idon zaki min" Cewar Mami.

      Ita kwata-kwata Laila bata zaci za'a d'auki hakan da wani manufa ba da bata fad'a ba,kawai de ta dad'e bata ci bane shiyasa taji sha'awa.

    "Kai mami nifa.."

     "A'a kina sani kawai de  tareraya irin ta yaran zamani"

     Tashi tayi ta koma d'aki ta d'auko handout d'inta ta soma duba kayanta tunda su Maryam basa nan gidan shiru,wainar ma fasa siyowa tayi.

              ★★★

   Amjad kuwa koda ya isa be damu da kiranta ba ,shi sam hankalinsa ba anan yake ba baida buri irin ya had'u da Rosie.

     Mom ,Zakia da Shaheed  ne suka taro shi a airport,Dad yayi tafiya,Mom ce first d'in ganinsa cikin sauri ta 'karasa tayi hugging d'insa tightly."My baby ,missed you so much"

     "Missed you too"

      Jitai kamar karta cika shi,su Zakia ma sukai hug lastly Shaheed, brother's hug

      Tunda suka taho a mota zuwa gida Mom hirar Nigeria take masa tana tambayarsa amma yana amsa mata kad'an -kad'an wani abun ma 'karya yake mata idan yaga ta isheshi.

     "Laila told me she's staying there with her Mom" Yaji Mom ta fad'a.

     "Uhmm" Ya kawar da maganar amma a ransa yayi 'kwafa dan shi bece mata ta tafi ba.
    
       Dinner na musamman aka shirya masa, se ji dashi Mom take zakia har tana tsokanarsa momy's bae amma wannan karan be taya ta ba.Sam ranar be samu chance ba balle yaje wajen Rosie, se washegari da safe 10am bayan sunyi breakfast yace zeje wajen Sam abokinsa duk da kuwa Mom jikinta ya bata wajen Rosie zeje.Be tashi zuwa ba seda ya siya mata flowers da bracelet mey tsadan gaske,har wani rawar jiki yake.

       "Angel I'm on my way to your house"Ya tura mata text.

     Few minutes later ya isa gidan,3missed call yayi mata bata d'aga ba,yasan wani lokacin tana yin haka idan tana so tayi surprising d'inshi sometimes seya shiga gidan.'Karasawa yayi hannunsa ri'ke da flowers d'in se bracelet d'in a aljihunsa ,knock! knock! Yai knocking ba'a bud'e ba.Handle d'in ya murd'a ya Shiga.
 
      " Hello"

      "Hello"Ya 'karasa living room." Hel...."

      'Karashen lo d'inne ya ma'kale a ma'kogoro dan tsananin tashin hankali ,jiyai kunnensa ya dena jin sound tsaiwar ma da'kyar yake.Irin yanayin da ya tsinceta yasa ya kasa  magana,a zuciyarsa yana 'kokonto anya Rosie d'insa ce.Tana zaune a cinyar wani guy da besan waye ba suna kissing passionately ,tana sanye da wani fitinannun sleeping dress wanda dashi da babu duk d'aya.Guy d'inne ya fara lura da Amjad dake tsaye kamar gunki,ganin guy d'in ya dakata yasa ta d'ago tana kallon direction da yake kalla."Amjad "Ta fad'a a hankali cikeda mamaki....


*Duba da yanayin lokaci azumi na tahowa ,shiyasa na maidashi page 2 in 1,and na 'kara tsahon page d'in,hope hakan yayi muku.Don't forget to vote.*

        
 
*Dijensy❤*

   

   

    

   

  

 
  
    

    

    

   

    

   

     

   

     

     
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*



*Sorry for the late update*


1⃣5⃣ - 1⃣6⃣


       A inde yake tsaye ya yasar da flowers d'in ba tare da ya san yayi hakan ba ,kamar 'kiftawar ido ya fita daga gidan. Da fitarsa da shiga mota be wuci 'yan sakanni ba,tu'ki yake amma besan inda zashi ba,seda ya tabbata yayi nisa da area d'in ya samu yayi parking can bayan gari."No!"Ya daki steering d'in motar ya zira yatsansa cikin sumarshi se mutstsukawa yake kamar ze cire gashin kansa."It can't be,No! Rose why? why?"be ankara ba yaji idanuwansa na tsiyayar hawaye,feeling his heart broken into pieces.
Tunanin rayuwarsu da suka shafe tare ya shiga yi,ko a mafarki idan aka ce Rosie zata ci amanarsa baze yarda ba amman yau ya gani da idansa.

      Yafi 20 min yana abu d'aya wayarsa da tayi ringing yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.

     "Mom" Ya gani a jikin screen.

     Ta kira har sau uku amma ya'ki d'agawa,lokaci guda yaji ciwon kai ya kamashi.Da 'kyar ya samu ya iya komawa gida, image d'inta ya'ki gushewa daga idansa.

      Mom ganinsa ya shigo gida tayi sauri ta 'karasa inda yake."Son, where have you been? are you ok?"

     Kai kawai ya kad'a yana 'ko'karin cire jacket d'inshi.

     "Amjad, you're looking sick" Ta fad'a tana dafa kafad'arsa fuskarta d'auke da damuwa.

    "Mom ,I just need to rest"Yayi 'ko'karin fad'a.

     "Ok ,go to your room I will prepare your a meal immediately you woke up"

     Yana shiga d'akinsa ya rufo 'kofar,yana ciro wayarsa daga aljihu sega kiran Rosie.

    "Baby boo" Ya bayyana a screen.

    Gabaki d'aya wayar yayi switching off ya cilla gefe,ya fad'a kan gadon ya rufe idansa trying to force him self to sleep.

    An hours later,2:30pm ya farka har lokacin kanshi be dena ciwon ba,tashi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa yayo alwala ya tada sallah.

    Knock! Knock! Mom tayi knocking ,ganin be bud'e ba ta murd'a handle ta shiga,sallah ta tarar yana yi haka yasa ta koma.Chicken Spaghetti  ta dafa mashi tayi arranging,tana gamawa ta koma sama ta kirashi.

    Ga abincin yasa a gaba amma ya kasa ci ,Mom data san Chicken spaghetti ne favorite d'insa tayi mamaki ganin ko fork d'in be d'aga ba.

     "Amjad, don't you wanna eat?"

     "I lost my appetite"Yana fad'ar haka ya mi'ke ya bar wajen.

     " Am.."Bata 'kare ba taga har ya 'bace mata daga gani.

             ★★★

      Laila

       7:12pm suna d'aki ita dasu Maryam se hirarsu suke ta mance da wani Amjad,idan Mami ta tambayeta suna waya da Amjad setace eh,wani lokacin har alarm take sawa idan yayi ringing setai pretending kamar kiran waya ne.

      Amjad kuwa cikin dare 11:00pm sam ya kasa bacci kawai juye-juye yake akan gado daga ya rufe ido Rosie yake gani da wannan guy d'in,tashi yayi ya d'auko wani box a 'kar'kashin gado.Hotuna ne ciki na Rosie harda wanda sukai tare dashi tun suna teens daga gefe kuwa teddy ne 'karami mey heart a cikinsa wanda Rosie ce ta bashi wani lokaci da yayi birthday. D'aukansu yayi ya tarkata duka ya fita can  backyard ya cinna musu wuta yana kallo har suka 'kone ya watsa tokar a dustbin.Hatta phone d'insa babu wani abu na Rosie daya bari pictures nata na musamman daya tanada musu folder seda yayi deleting,seda ya tabbata ba abinda ya ragu nata a wayarsa ya iya samun yin bacci.Amjad sam be iya so ba haka be iya tsana ba,ya tsani yaudara mutum ne mey zafin kishi ko Zakia idan ya ganta da wani classmate bama boyfriend ba  seya ji haushi.

      "I hate you like hell"

       "I hate you forever,I never wanna see  your face again"

     Idansa a rufe yake fad'ar haka ,firgit! Ya farka ,se lokacin ya lura 5:54am yayi,nan ya tashi yayi sallah.Yana idarwa ya sauka 'kasa "Morning"

     "Morning" Mom ta amsa.
 
      Da 'kyar ya samu ya iya yin breakfast d'in, data tambayeshi meyake damunsa ya'ki fad'a.

           ★★★

    Amjad ko kwana uku beyi ba ya koma Nigeria dan ji yake kamar a kan 'kaya yake a Canada,sede ba wanda yasan Nigeria ya koma 'karya yayi musu yace Ethiopia yaje daga can ze wuce Nigeria.

     Yana komawa Nigeria ya cigaba da zuwa aikinsa dan so yake ya mance da komai har 'karawa kansa lokaci yake kafin ya tashi se wajen 5:30pm,daya koma gida ma baya hutawa wani aikin ze tsiri yi yaita dube-dube a system, a 'yan kwanakin da akai har ya rame da an ganshi za'a san yana da damuwa.

      Laila kuwa cikin kwanciyar hankali take exam d'inta,ji take kamar ta komo gida kenan dan ko maganar komawa bata yi.Seda suka kwashe 2weeks da 'yan kwanaki suna exam,yanzu anyi hutu na 'yan weeks kad'an.Yanzu ta komo hawa online sosai ba kamar sanda suna exam ba idan ba abu daya shafi karatu ba bata bud'e data.

     Yau bayan sun gama cin abincin dare,su Maryam suna parlor suna kallo ita kuwa tana d'aki se chat d'inta take hankali kwance.

        9:45pm,yana d'aki be jima da dawowa ba daga restaurant kullum seya je yaci abinci acan,yana watsa ruwa ya d'auka waya ya hau whatapp chat ,abinda ya dad'e beyi ba.Contact ya shiga yana ta duba numbers ,yazo N letter idansa ya sauka kan Nigeria,daya duba kuwa yaga tana online. Profile d'inta ya shiga viewing inda yaga profile picture d'inta dake d'auke da photo d'inta tayi  rolling da red mayafi kuma fuskarta tasha make-up sede ba duka ta d'ago fuskar ba ta d'an sunkuya inba wanda yasanta ba baze gane itace ba.

      "Hi" Yayi sending da 'kyar dan ya dad'e kafin ya iya  turawa.

      Tana cikin chat taga "hi" data dubi number d'in taga na Amjad ne ,tafi 10min kafin tayi reply da .

      "Hello" Tayi reply.

       "Why are you chatting at this time, aren't you suppose to be reading ?"

    "Exam is over ,hutawa zanyi"

      "What did you mean by those last words?"

       "You don't need to know"

        "Ok,can you please change that profile pic with something better? coz you're looking ugly"

      "I choosed it myself and I like how I'm looking"

     Murmurshi abinda ta fad'a yasa shi."But I don't like it"

     "I don't care"

      "Ok,where are you now?"

       "Home"

        "You're Lying, Mom told me everything"

        "Your house is not my home, I'm referring to Mami's house"

       "Good for you,you're soon coming back"

        "No"

        "You must"

     Laila: "When are you coming back?"

    Amjad:" Do you care?"

        Laila:  "No"

       Amjad: "Then why did you ask?"

       Laila: "Just wannan know"

        Amjad: "I knew you missed me"

          "Wallahi a'a"

        Amjad:"Lier"

        Laila:"I'm not"

    Amjad:"You are!"

               Daga haka bata sake tura wani abu ba tayi banza dashi ta cigaba da sauran chat d'inta. Amjad kuwa da  tun tini dama da ita yake chat in banda it a ba kowa,ganin shiru ya sake yi mata  magana.

   Amjad:"Laila"

   Laila:"Mene?"

   Amjad:What is your problem?
    
     Amjad: What is the meaning of "mene" ?

     Laila :"It means "what"   

     Amjad: What of "why" Ya sake tambaya dukda kuwa ya san ma'anar kawai jan magana be.

     Laila: "Meyasa"

     Amjad:I gerrit,what of  "Ni nace" You often say the words.

       Laila:I'm not a teacher, I'm going to bed"

       Amjad:😏 who care to learn your language? disgusting!

         Laila:Eh d'in chat d'in ma baza a sake yi dakai ba"

         Amjad:Rubbish!

    Sauka tayi daga chat d'in ta zira charger a wayarta tayi shirin kwanciya,tana kwance chat d'in da sukai yana ta dawo mata wani abun ya bata dariya wani ya bata haushi.Se to 11:30pm tayi bacci.

     Ta 'bangaren Amjad kuwa ganin ta sauka ya koma Instagram,"Lai-mus" sunan da take amfani dashi a insta.526 followers,jiyai ya damu da yaga followers d'in kad'an-kad'an yana scrolling  jama'a iri-iri maza sunfi ma yawa ,post d'inta ya koma dubawa yaga har 27 sede photo d'inta a ciki 3 ne sauran duk qoutes pic ne,+200 yaga like da + 62 comment kan wani pic nata da niqab nema a fuskarta idanuwanta ne kawai suka fito wanda sunsha kwalli rad'au.
  
      Nan take yaji wani Abu ya tokare mashi a ma'kogoro,musamman wani comment dayaga wani guy yayi."Baby I love your sparkling eyes🔥🔥"

      Instagram d'in ma fita yayi ya ha'kura da chat d'in,se jin haushi yake ,chat d'in da sukai ya shiga ya soma dubawa a haka har bacci ya d'aukeshi.

    Washegari

     Laila bayan tayi breakfast su Maryam dake gida kasancewar yau Saturday basu je makaranata ba suna parlor suna kallo tare.

      "Laila" Mami ta kirata daga d'aki.

      "Na'am" Ta amsa tare da mi'kewa.

        "Mami gani" Ta fad'a bayan ta shiga d'akin.

      "Ke ashe Amjad d'in ya dawo baki fad'a min ba" Cewar Mami.

       "Uhmm?" Ta waro ido tana kallon Mami.

        "Ehyi,yanzunnan muka gama waya da mamansa take fad'a min jiya ya dawo"

         "Uuhm"

         "Toh yau zaki koma kenan?"

          "A'a Mami ba yau ba" Ta diririce harda kad'a hannu tana maganar.

         "Se yaushe kuma?"

          "Uhnmm wani satin"

          "Kin manta wata shekarar,ke mijin naki ya dawo ma ba ko d'an 'kunshi single kamar namiji"

      "Ni bana so"

       "Aiko anjima ki shirya Maryam ta raka ki ,hannu kamar muciya"

       Ring!Ring tajiyo 'karar wayarta daga d'aki,haka yasa ta dakata da maganar da suke da Mami ta tafi d'aukan wayar.

      Numbern Amjad ta gani jikin screen aiko ta'ki picking bayan kiran ya 'kare ta saka wayar a silent.Seda ya kira sau uku ganin batai picking ba dole ya ha'kura.

       Wajen 3:30pm Mami tasa Laila zuwa gidan 'kunshi,haka bata so akai mata ja.Ba 'karamin kyau yayi mata ba yayi maroon a  farar 'kafarta ,a hanya zira hannayenta tayi a hijab tana karewa dan jitake wani iri.

        "Toh baga shi ba ,amma da sekace namiji" Mami ta fad'a sanda suka shiga gidan.

      Ita de bata ce komai ba ta wuce d'aki,ita kanta se kallon hannun  take  yana birgeta.Idan ta tuna da batun komawa gidan Amjad kuwa setaji 'bacin rai.

       "Ko bazan 'kara sati ba sena yi kwana hud'u kafin na koma" Ta fad'a a ranta.

          Amjad ganin bata d'aga kiran nashi ba seya hau WhatsApp ko ze ganta online amma shiru ba alama, tashi yayi ya fita daga gidan ,dan yanzu idan yana zaune shi kad'ai tunanin Rosie ne yake addabarsa.

       Har ya dawo gida ya sake dubawa ko ta hau online amma shiru se ha'kura yayi ya kwanta.

      Itama ta 'bangarenta tana so ta hau chat amma kuma tana gudun kar yau ma yayi mata magana ,shiyasa ta ha'kura da chat d'in ta ajje wayar.

              ★★★

      Yau tun 4:30am ya farka bacci amma ya kasa komawa sakamakon mafarkai marasa dad'i da yayi tayi wanda duk akan Rosie ne.Asuba nayi ya tashi ya fita masjid,koda ya dawo be koma bacci ba ,wayar tashi ya sake duba last seen d'inta ko zega ta hau jiyan amma still bata hau ba.

       Laila kuwa yau se 9:53am ta tashi daga bacci tun bayan sallahr subh,hakan ma seda Mami ta tashe ta da kanta.

        "Yini zaki a haka? sekace

Please Login or Register in order to submit comment