Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

this?"Taga ya ajje kud'i kan table d'in 'yan 1000 ne sede bata san nawa bane.

    "Take it" Ya fad'a.

     Shawara ta shiga yi ta d'auka ko karta d'auka? Ganin lokaci yana ja ta daure ta saka hannu ta d'auka.

     "Shame" Yana fad'ar haka ya fita.

       "Eh d'in ai ba sata nayi ba". Ta fad'a a ranta.

       Seda ta bari ya fita tukun ta fita,tana shiga school ta had'u da Aliya wanda dede lokacin mijinta ya sauketa a mota.Se 4:30pm ta dawo gida tana sigowa taga motarsa,hakan ya nuna ya dawo gida.Se bayan ta ajje handbag d'inta ta sakko kitchen daga bakin 'kofa ta tsaya saboda abinda ta gani.

    
      *Let's stop here,inshaAllah I will update as soon as possible. Your comment are needed.*

0803558412

*Dijensy❤*

    

      
    
      

     

    

   
    
    

   
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

🅿 1⃣1⃣

   Wani 'katon cake ta gani daya sha ado sosai pink and white rubutu akai masa akai "Happy birthday sweetheart" da candle jere a kai.
Sede ita bata ga abinda aka rubuta ba tunda bata 'karasa ba.Gefensa kuwa laptop d'insa ce yana video call,tana jiyo murya mace amma bazata iya ganin fuskarta ba,bata bari ya d'ago ya kalleta ba tayi saurin komawa d'aki.

     "Happy birthday baby" Tare suka bushe candle d'in as if tana kusa da cake d'in.

     "Thank you Baby" Ta fad'a tana washe ha'kora dan ta kasa rufe baki saboda farinciki.Balloons manya daya sa'kala  jikin fridge ya ciro su."Do you like this baby?"

    "Yes I love it "

    Teddy bear dayai hiding a  bayan laptop d'insa ya ciro 'kato pink colour a tsakkiyar cikin an rubuta happy birthday beautiful "

    Nan ma wani sabon farincikin ne ya rufeta."Baby you're so sweet"

    "You deserved more than this baby"

      Hira suka shiga yi abinsu ,Laila kuwa jitai dama bata sauka 'kasan ba dan ma Allah yasa bai ganta ba.Dama ba wani yunwa take ji ba,gasasshen masarar data suyo a hanya ta d'akko a jaka ta soma gagayar kayanta, tana yi tana danna wayarta.

  Se wajajen 8:15pm ta sakko kitchen, balloons d'in duk nemansu tayi ta rasa seda ta bud'e fridge taga cake ,yaci iya wanda zeci ya bari .Rubutun da akai ta kalla ta ta'be baki ta d'auki abinda zata d'auka a fridge d'in ta rufe.

              ★★★
     
     Washegari da safe ta makara se sauri take ko living room bata gyara ba kitchen kawai tayi goge-gogenta bayan tayi breakfast ta koma d'aki ta shirya.Tana daf da fita taji ya kira sunan da yafi son gaya mata.

      "Madam chef"

       A hankali ta waiwayo fuskarta a rufe tana kallonsa ko shirin office beyi ba 3qtr ne da shirt a jikinsa.Ganin ya 'karaso ta sauke kanta 'kasa.

    "Remember you're now a  married woman don't tell me that you don't know your duties, I mean what you suppose to do here"

       "Mey kuma zanyi bayan wanda nake"Ta fad'a a ranta.

       " What?"
      
      "Prepare me a meal"Ya amsata.

      "It's getting late,it's almost 8 "

       "I don't care "

        "But.."

        "Just go on with your works and stop wasting much time"

       Har ya koma ya dawo "I forgot to tell you,I need omelette and  sandwiches"Daga haka ya koma d'akinsa.

     
       Tunani ta shiga yi ko tayi tafiyarta,amma kuma tana gudun abinda ze biyo baya.Haka tana ji tana gani ta cire hijab da niqab d'in ta fara ,tana yi tana mita."Da abincin kake cewa ai maka,ko dan kaga ka bani kud'i"

       "Kuma Allah ya kaimu gobe, baza ka san lokacin da zan tafi ba".

       Ba ita ta gama ba se 8:53am tana gama ajje masa a dinning ta saka hijab d'in ta ta fice.Yana daga d'aki ya hango fitarta,murmushin gefen fuska kawai yayi ya cigaba da harkokinsa.

       Lokacin data isa makarantar har an shiga lecture,seda tayi missing wannan lecture d'in.Se na 'karfe 12pm ta samu 2:30pm ta dawo gida.

      Motar sa da ta gani hakan ya tabbatar mata yana gida,lokacin da ta shiga a living room ta ajje jakarta ta nufi kitchen ganin plate na d'azu inda ta barsu yasa ta ci birki,'karasawa tayi table d'in ta bud'e ba abinda aka ci na ciki d'ayan ma haka ,ta rasa ma mey zatayi saboda tsabar takaici.

  " It's Nasty! It  smells bad"Tajiyo muryarsa.

   Kallo ta bishi dashi almost harara ta shiga kitchen, abinda take so tayi a kitchen d'in ma ta kasa saboda tsabar ba'kin ciki dan haka ta fasa girka komai ta komo living room ta d'auke handbag d'inta zuwa d'aki.

     "Allah ya isa" Ta fad'a a fili tana cilli da jakar.

      Ga yunwa tana ji amma haushi baze bari ta iya cin komai ba.Se bayan asr ta sakko ganin bata ga plates d'in ba yasa ta shiga tunani "Ko yaci?"

     Wainar fulawa ta had'a ta soya kayanta taci a kitchen d'in, wajen daya d'an 'baci a kitchen d'in ta share lokacin data bud'e dustbin tasha mamaki ganin sandwich a yashe a wula'kance.

     "Wannan ai almabazzaranci ne"

     Haushi de ranar tasha shi,bayan maghrib tayi plunging charge a wayarta ta sakko 'kasa,kan d'aya daga cikin sofa a living room ta zauna tare da d'aukan remote control ta kunna  TV.

    Chanja channel d'in tayi zuwa Bollywood aiko ta riska ana film d'in da take so "Veer zaara".Sosai ta bada attention a kai tana jin dad'in kalla dan har taji fishin da take ya tafi.

      1hr later sega Amjad yana sakkowa ,tana jin motsintsa amma tai kamar bata san dashi ba.Kitchen ya fara shiga ko mey ze d'auka oho ,koda ya fito har ya nufi upstair ya dawo.

     " She's enjoying it"Ya fad'a a ransa.

      "Excuse me!"

       Banza tayi dashi ta cigaba da kallonta,ganin ta'ki kulasa ya 'karaso yayi blocking d'inta yadda bazata iya ganin komai ba.

     "Are you deaf?"

      Maimakon yaga tayi magana se gani yayi ta mi'ke tsaye tayi tafiyarta d'aki.Har cikin ransa ba haka yaso ba se yanzu yake daya sanin barinta na tafiya.Laila kuwa a d'aki harda kukanta dan tsabar takaici ya katse mata kallonta tasan dama abinda yake so kenan kuma burinsa ya cika,a ranta kuwa ta 'kudura ba'kanta masa itama.

                 ★★★

     Washegari da asubar fari ta tashi da wuri tayi shirinta hatta breakfast datai a flask tasa ta zira a jaka.7:16am nayi ta fita daga gidan.

    Knock! Knock! Laila! Ya 'kwala mata kira amma shiru ,yana murd'a 'kofar yaga bata ciki.Da 'karfi yayi banging 'kofar ya koma d'aki ,a niyyarsa yau ma ya sake sata dafa masa abinci duk da ba cin zeyi ba.

     "Nigeria"Sunan da yayi saving number d'inta kenan. Daga yayi dialing seya kashe da 'kyar ya bari kiran ya shiga.Ya kirata sau biyu batai picking ba,wurgi yayi da wayar gefe sau biyu kenan yana kiranta bata ta'ba d'aga wa, lokacin bikinsu da yau.

     Laila kuwa tana shiga school tasa wayar a silent,tana zuwa ta samu gu taci abincinta ,a ranta tana mey jin dad'i dan tasan duk tsiya seya ji haushi.

      Koda aka tashi ba gida ta komo ba gidan Mami ta wuce dama ta dad'e tana planning yin hakan tunda tayi aure bata ta'ba zuwa ba.

      " Ga yaya!ga yaya!"Fauzan ya tafi da gudu yayi hugging d'inta.

      "Tohh,zuwa ba zato ba tsammani"Mami ta fad'a tana fitowa daga kitchen.

     " Daga makaranta nake"Ta  fad'a tare cire niqab d'in.

      Kowa murnar ganinta yake ,tuni ta mance da rayuwar gidanta.Kitso tasa Maryam tayi mata bayan sunci abinci,4pm taje gidan Kawu Yunus nan d'inma seda ta shafe kusan awa d'ayan ta komo gida.

     Amjad 4:23 pm ya dawo gida be sameta ba,Mom ta dad'e tana masa maganar zuwa gidan Mami se yanzu  yaga dama shine ya dawo su tafi  tare amma be sameta ba,shiru-shiru har 5:15pm bega dawowarta ba dan haka yayi fitowarsa shi kad'ai.

    
       "Laila yanzu dubi hannunki sungul kamar taliya ba ko jan 'kunshi" Mami ta fad'a.

     "Mami makaranta ba lokaci"

     "Toh 'yar boko..." Bata 'karasa ba sega Fauzan ya shigo da uniform d'in islamiyya a jikinshi."Mami unnhh..yaya Amjat yazo"

     Laila dake shingid'e a wani razane ta mi'ke zaune."Kace mey?"

     "Baki ji ba,mijinki ne yazo dama shi zezo d'aukan ki?"

     "Uhmm..shi..shine" Ta amsa cikin in'ina.

     "Toh ki tashi ki shirya".

    "Mami zaku gaisa ai" Laila ta fad'a.

    "Fauzan kace ya shigo" Cewar Laila.

     Da'kyar ya fuskanci abinda Fauzan yace,lokacin da  Fauzan ya shigo Amjad yana biye dashi.Yana zaune kan kujera lokacin da Mami ta shigo ya d'an du'ka kad'an shima tuna yadda Laila tayi sanda taje gidansu ne yasa yayi haka.

      Laila kuwa a d'aki se fiffita take da hannunta tunanin yadda zata fita take."Shikam taya yasan ina nan?"

    "Laila ki fito toh har ya fita yana jiranki" Tajiyo muryar Mami.

     "Gani" Ta amsa 'kasa-'kasa.

       Jiki ba 'kwari ta shirya tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta.Har waje Nusaiba suka rakota jiki a sanyaye ta bud'e gidan gaba ta shiga.A nitse yake tu'kinsa har suka isa  bakin titi,daga gefe taga yayi parking.

     "Get out" Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba.

     "Naje ina ?" Ta fad'a a fili.

      "Dismiss from my eye's!" Ya tsawata.

      Shawara ta shiga yi ta fita ko ta zauna?

*Dijensy❤*


      

      

      

    

      
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

🅿 1⃣2⃣

      Zaman jakarta ta gyara tayi kamar bata jin yaran."I said get out"

     Tayi yun'kurin yin magana ya daka mata tsawa"Now!"

      Cikin sauri ta bud'e 'kofar ta rufe da 'karfi tayi gaba abinta.Shima cikin zafin rai ya figi motarsa ya bar wajen.Haka tayi ta jiran d'an sahu seda 'kyar ta samu,tana isa gida direct ta wuce d'aki.

     Knock! Knock taji bugu dede lokacin ta fito daga bathroom, towel ne iya gwiwa a jikinta.Cikin hanzari ta d'auki hijab ta zira,la'bewa tayi a bayan 'kofar ta bud'e kad'an ba ko ina za'a iya gani bama a d'akin.

     "What are you hiding?"

      'Sangalalen 'kafarta data ke karewa ya kalla ,se lokacin ya gano dalilinta na 'buyan.

     "What do you think you're doing? I knew this is not the first time.."

     Be 'karasa maganar ba ya saki atishawa ba zato ba tsammani har yana sunkuyawa,hakan ba 'karamin dariya ya bawa Laila ba amma ta basar."Cha'kwai'kwaiwa yanzu ai kayi shiru"Ta fad'a a ranta.

     "Don't you ever.." Wata atishawar ce ta sake zuwan masa a jere har uku,Laila harda kawar da fuska.Harara ya bita dashi ya bar wajen, yana shiga d'akinsa yayi banging 'kofar.

     Bayan sallahr maghrib lokaci guda zazza'bi ya rifeshi harda ciwon kai ga dukkan alamu yana ji mura ce ta kamashi.Tuni ya fara fita daga hayyacinsa,yana kwance shame-shame hanci se tsiyaya yake yayi jazir, kwalin tissue ya ajje gefe daga ya share seya cillar duk inda yaga dama.

      Da'kyar ya samu ya mi'ke daga kwance ya d'auko wayarsa ya kira Mom ya wani kwantar da murya yana mata complain.Ji tayi dama tana kusa dan tasan yanayin dayake shiga idan baida lafiya rakin tsiya komai se an mashi kamar za'a goya shi.

      "Please try and take your medicine"

       "Get well soon my dear"

        "Mom,my head chest every where is paining"

         "Sorry,wish you quick recovery my love"

      Haka ta dad'e suna waya dashi wai duk dan ya samu relief, da 'kyar ya samu yayi sallahr isha'i.Laila kuwa bata san halin da ake ciki ba tana d'aki abinta.

     Hancinsa a toshe ko bacci ya kasa yi gashi a lalle baze kashe AC ba shi karya ji zafi,banda yunwa dake addabarsa a yanzu ba abinda yake bu'kata irin black tea amma mey had'a masa ne ya rasa.

       Washegari da safe kamar koyaushe ta gama shirinta breakfast ne kawai ya rage.

     Laila! Laila! Tana daga kitchen tajiyo shi yana kiranta.Tea take had'awa seda ta gama tukun ta hau sama,'kofarsa tayi knocking shiru ba amsa a hankali ta tura kamar bazata shiga ba.

     Yana bathroom tajiyo kakarin amai ,data kalli flow d'in d'akin kuwa tissue ce fal ba adadi duk ya cillar. Ba iya 'kasa ba hatta kan gadon a birkice yake.

      Ganin ya fito a daddafe ta kawar da kai gefe,tana ji ya 'karaso tare da zama kan gado.

     " Why are you so evil?, do you want me to die here?"

      "Nina d'ora maka?"Ta kalleshi.

     
         "Allah ya 'kara alhaki na ne".

         "Make me tea"

     
           Juyawa tayi ba tare da tayi magana ba, bata  dad'e ba ta had'a masa ta kawo.Tazo ba'kin 'kofa fita ya tsayar da ita.

       "Are you living me like this?"

        "Mey zanyi ma?" Ta fad'a.

         "Speak in English"

          "I'm hungry"Taji ya fad'a.

        "Bring me water"

         Tana turo baki ta tafi kitchen, dankalin data soya ta zibo masa tare da soya masa egg ta kawo,se bottle of water da cup ta jero a plate.Tana direwa tasa 'kafa zata fita."Laila"Ya kira sunanta daga kwance.

     "Where are you going?"

      "School" Ta amsa.

       Kai kawai ya girgiza bece komai ba ya d'ora d'aya hannunsa a kai se squeezing yake.

     Tana sauri haka ta fice koh  a jikinta ciwonsa be d'aga mata hankali ba.Yauma bayan sun fito daga lecture na farko ita da Aliya suna zaune kan bench suna duba wani aiki.

     Ring!Ring!Taji kira ya shigo wayarta,unknown number ta gani seda ya kusan katsewa tayi picking.

     "Hello"

     "Laila come back home" Taji an fad'a daga d'aya 'bangaren.

      "Who am I talking to?"

      "It's me Amjad"
     
      "Why do I have to come back"

      "I'm dying Laila, I totally can't breath"

       "Then take your medicine"

        "I can't"

        "Naji gani" Ta fad'a tare da katsewa.

        "Mtchww!" Bata san tayi tsaki bama.

         "Tohh,keda wa?" Aliya ta tambaya.

         "Uhnm,tafiya zanyi" Ta fad'a rai a d'an 'bace.

       "Tafiya kuma? Sauran lectures fah?"

       "Ya zanyi? Wata'kila na dawo".

       " Ok,Allah yasa lafiya"

        "Hmm" Abinda ta fad'a kenan ta tashi

         Ita de Aliya kallo ta bita dashi dan har yanzu ta rasa gane kanta.

      10:45am ta koma gida,seda ta shiga d'akinta ta ajje jakar tukun tai knocking d'akinsa."Come in"Ya fad'a.

     Lokacin data shiga ma yana zaune ita sam bata ga alamar wani tsananin ciwo ba,basarwa yayi kamar ba shine wanda ya kirata ba."Why are you here? "

     "You called me"

       "I'm fine,you can go coz I don't need you now"

       "Tabd'ijan,wannan yana haukane?" Ta fad'a cinkin ranta.

      "'Kazami kawai" Tayi 'kun'kuni ta fita daga d'akin.

      Abincin data kawo masa ma be bud'e ba se yanzu,loman farko yayi ya ajje fork d'in bayaso yaci abincinta sam amma dad'in dayaji yayi yasa ya cigaba da ci.Kad'an ya rage badan ba dad'i ba sedan ya 'koshi,da'kyar ya samu yasha magani tukun ya kwanta.

      12:30pm haka ta tashi ta koma makaranta,lecture d'aya suka 'kara yi ta komo gida duk a gajiye dan ma seda taci abinci ta taho.Tana watsa ruwa ta kwanta bacci,se kusan maghrib ta tashi.Tunda ta sakko 'kasa d'aukan ruwa bata sake fitowa ba se wata washegarin.

      Yana 'kudundune cikin blanket yau ma da zazza'bin ya tashi da 'kyar a daddafe yayi sallah.Tana shiryawa wayarta tayi 'kara koda ta duba taga number da Amjad ya kirata jiya ne.

       "Hello" Ta amsa.

        "Make me ginger tea"

         "Uhum" Ta fad'a ciki bata bari ya sake wata maganar ba ta kashe.

        Seda ta gama abinda zatai tukun ta sauka zuwa kitchen,fara had'a nata breakfast d'in tayi kafin daga bisani ta had'a masa tea d'in."Come in"Ya fad'a bayan tayi knocking.

     Kan  drawer na gefen gado ta d'ire masa,bako sannu tayi fitowarta.Komawa tayi dinning tayi breakfast d'inta tukun ta dawo d'aki ta d'auki handbag d'inta tayi tafiyarta.

     Shikad'ai yayi ta fama da ciwonsa,yanzu daya ji wuya ya kashe Ac d'aki kuwa yana nan yadda yake kaca-kaca.

                 ★★★★

   Yau ta samu lecturen farko ba kamar jiya ba,seda sukai lecture biyu 12:15pm suka tafi cafeteria.Suna fitowa ne wani saurayi dake ciki ya soma biyo bayansu,yana daga side d'in Laila.

     "Assalamu Alaykum"

     Kamar bazata amsa ba ,ta amsa da "waalaikassalm" amma bata kallon inda yake.

    "Baiwar Allah ko zan iya jin sunan?" Ya tambaya yana murmushi.

    Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta, Aliya se bugin hannunta take "Ke baki ji ? Ki sallameshi ya dena bunmu"

     "Please ko zan iya samun number ki?" Ya sake wata tambaya.

       "Bawan Allah kai baka san matar aure bane" Laila ta fad'a rai a 'bace.

       "Ayi min afuwa amma dake matar aure ce nima zan gane hakan,dan Allah ki taimaka ko numbern ki ne ki bani".

     " Mtchww!"Taja tsuka tayi gaba tabar Aliya anan.

     Kai ta girgiza ta bita a bayan dan ita a tunaninta ta fad'i haka ne saboda ya rabu da ita.Ita kanta Laila mamaki ta shiga yi na 'bacin ranta bata zaci haka ba.

    "Haba Laila, shine kike yin 'karya da aure akan bakyaso ki kula wani?"

      "'Karya? akan mey zanyi 'karya shi baida tunani ze tare ni..." Laila bata 'kare maganar ba se ji tayi kuka ya ku'buce mata ,Aliya dake tsaye ta ri'ko kafad'arta ta zaunar kan bench.

     "Abin yakai ga haka?"

      "Aliya baza ki gane ba" Ta fad'a tana 'ko'karin share hawayenta da tissue.

     Shiru sukai na d'an lokaci kafin Aliya ta sake wata maganar."Laila na tambayeki?"

     Kai ta kad'a alamar "Eh".

     "Da gaske ne abinda kike fad'a ,kina da aure?"

      "Ina da aure Aliya.."

      "Kina nufin kice jiya wayar da kikai da mijinki kikai?"

      "Uhmm"

      "Amma  shine kike magana haka? Laila sekace a 'kauye"

      "Please mu bar maganar nan"

      "Keko dan Allah tun yaushe kikai aure?"

      "4month,ki tashi mu tafi ko an shiga lecture" Tayi 'ko'karin kawar da zancen.

     "Idan kince yanzu mu bar maganar ai gobe ma rana ce,idan kikai wasa ma har gidan naki zanzo"

    "Jibeki ni tashi kin fiya manyancen tsiya"

     "Naji,ke kuma babba dake amm..."

      "Amma mey?"

      "Abar kaza cikin gashinta" Tayi dariya tare da mi'kewa.

      "Oho miki" Suka  jera suna tafiya.

     Lecture da aka shiga yasa basi samu lokacin sake magana ba,ana fitowa kowa ya tafi gida.

    Tana shiga gida taga kiran su Aunty bilki ,nan take fad'a  mata suna hanyar zuwa gidanta ita da sauran sisters d'in Mami.

      *Short and boring chappy I know,don't forget to comment,share and vote. Love ur❤*

*Dijensy❤*


    

    
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

1⃣3⃣ - 1⃣4⃣


Lokaci guda cikinta ya d'uru ruwa,ba shiri ta fito daga d'akinta ta sakko laundry room anan ta  d'akko broom stick tare da mop.Tunanin yanda zatai masa bayani ta shiga yi kafin tayi knocking tafi 4min,jin shiru yasa ta murd'a handle d'in 'kofar ta shiga.Gani tayi baya ciki kuma ba alamar yana bathroom ,hakan ba 'karamin dad'i yayi mata ba.Cikin sauri ta fara  gyaran d'akin tana yi tana masif-masife."K'azami kawai ,dubi  kan katifa mtchww!"ba dan Allah ba haka ta gyara d'akin tass bathroom d'in ma haka ta gyaresa.Tana goge kan mirror ne taga wani d'an 'karamin doki da aka sassa'ka da katako,d'auka tayi  tana ta kallansa ta juya can ta juya nan garin haka ya su'buce ya fad'i,aiko tana dubawa taga kansa ya gutsire,salallami ta hau yi tana tarkatoshi.

    D'akinta ta koma ta d'akko wani super glue ta shiga mannawa a wuyan, daya jonu seya 'bintire har ta 'karar da glue d'in gashi duk ta 'bata dokin yayi fari-fari a brown colour d'in

        Amjad kuwa jin zaman d'akin ya isheshi yasa ya fice waje garden yayi zamansa,seda ya shafe 'yan mintina ya komo.

    "What is she doing?" Ya fad'a a ransa ganinta bakin mirror ta juya baya.

      "What are you doing in my room?"

       Nan da nan ta soma mutsu-mustsu ,da sauri ta 'boye dokin a bayanta,gashi yau ba gyale a jikinta doguwar rigar atamfa ce da d'ankwali.

    "You're hiding something" Ya 'karaso inda take a fusace ya mi'ka mata hannu ta fito da abunda take 'boyewa.
  
     "Let me see"

      "Ni babu abinda na d'auka" Ta turo baki.

      Ganin zata 'bata masa lokaci ya mi'ka hannu bayanta ze kar'be abinda take 'boyewa,da sauri ta juya  bayanta gam ta ri'ke dokin kamar nata.Kici-kici suka shigayi yana murd'e mata hannu tana ihu amma ta'ki saki,jin nauyinsa gabaki d'aya a bayanta yasa tayi saurin saki da 'karfi ya wafce body d'in dokin. Ba shiri taja jiki ta matsa gefe du se taji wani irin dama bata ri'ke ba.

     Ganin tsurar doki ba kai yasa Amjad ya waigo ya dubeta."You broke it "

     Shiru tayi bata ce komai ba kan dokin na hannunta na hagu ta dam'ke.

    "Give me the other part" Ya mi'ka mata hannu.

     Tana so ta bashi kuma tana tsoro kar yayi mata wani abun dan ta kula ta irin expression d'in fuskarsa d'auke da guntun murmushi mey manufofin.

     A sanyaye ta bud'e ta mi'ka  masa daga nesa -nesa,ganin hannunta be kai ba ta d'an matsa aiko abinda take tunanin shiya faru.Hannunta ya janyo har kan dokin ya fad'i 'kas ita kuma ta fad'o jikinsa.

       "Can't you apologize?"

          "Ka cika ni,kai kayi min godiya?"

           Ta kasa ku'bucewa sam se raba idanuwa take."Shut up!"

       "Toh ka cikani"

        "Keep your mouth shut"

         Ya sake matso da fuskarsa har numfashinsu na had'uwa.Tsoro ne ya fara kamata dan haka tayi shiru mutsunma ta dena idanunta a rufe.

        Door bell rang qlin! Jin haka yasa ya cika mata hannu har tana shirin fad'uwa da'kyar ta iya balancing kanta,a kunyace tayi sauri ta fita daga d'akin.

      "Aunty" Ta furta lokacin data bud'e 'kofar.

        "Sannunku da zuwa" Ta fad'a tana bud'e musu 'kofar widely.

        Waje suka samu suka zauna su hud'un ,bayan data gaishesu ta kawo musu drinks."D'ayan d'an kunnen fad'uwa yayi?"Wata daga Cikin

Please Login or Register in order to submit comment