Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa"

        "Mami goma ma fa batai ba" Ta fad'a tana murza ido.

      "Kin ajje waya tun d'azu ana ta kira"

       Tana jin haka ta ayyana Amjad ne,bataso ba ta mi'ke ta shiga bathroom tayi wanka bayan ta shirya tayi breakfast.Data duba wayarta kuwa 6missed call ta gani na kiran Amjad,ganin ta gaji da ganin numbernshi ba suna ta shiga yi saving, sunan da zata saka mashi tayi ta tunanowa.Ta san idan tasa Amjad gatsau da matsala dan su Mami zasu iya gani.

       'Hus...' Ta fara seta goge."Hauka ma kenan".

     'Na dole...'

       "A'a"Ta goge.

         Finally de tayi saving da " Canada ".

       12:34pm suna kitchen da Mami suka  ji knock,Fauzan yana d'aki ,Laila ganin ta fi kusa da 'kofar yasa ta tafi bud'ewa.

      Tsegege ta tsaya tana kallonsa shima kallon nata yake cikin ido hakan yasa tayi sauri ta kawar da idonta.

   *Don't forget to comment,vote and share.love ur💋*

*Dijensy❤*
    

     
       

    

       

    
    

     
      

   
  
 

      

   

   
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*


*Wannan page d'in naku ne masoyan Amjad*

1⃣7⃣-1⃣8⃣


Tana tsaye ita bata ce ya shigo ba kuma bata rife 'kofar ba.

"Can I come in?" Ya tambaya.

    "No" Ta girgiza kai.

    "OK,then I will wait for you outside"

    "Me..? "

     "Yes ,you're following me home"

      "I will not"

       "Stop wasting your time,just hurry up and park your things"

       "Laila!" Tajiyo Mami ta kirata.

       Sauri tayi ta bar gun ta tafi."Naji shiru,waye?

      "Uh..Amjad ne"

       "D'aukan ki yazo yi kenan?"

       "Mami nifa.."

        "Ke mey?,kinga ki shiga ki shirya kayanki"

       A kasalance ta shige d'aki,cikin sanyin jiki ta soma shirya kayanta  kamar mara laka a jiki.Hijab d'inta ta d'akko ta zirma ta ri'ke niqab d'in a hannu ta fito d'ayan hannun ta ri'ko akwatin.

     "Kin fito?"

       "Uhmm" Ta amsa.

        Su Maryam suna daga d'agi suka fito,ganin Fauzan yasa ta fad'in."Mami dan Allah Fauzan ya bini".

      "A'a ba yanzu ba,se anyi hutun makaranta"

      Ita tama manta yau Sunday,tana jin haushi ta fita su Maryam suka rakota har bakin mota,Amjad yana ciki yana jiranta.Da kanshi ya fita ya taimaka mata tasa kayan a baya,kafin ya koma motar ta rigashi shiga.Niqab dake ri'ke a hannunta ta d'aura a fuska ko idanuwanta ba'a gani,jin alamar ya shigo motar ta kawar da kanta window.Har suka hau titi ba wanda yayi magana ,sede lokaci-lokaci yana kallonta.Suna isa gida tayi tafiyarta ko kayan bata bi ta kansu ba,key dake jakarta ta ciro ta bud'e 'kofar.

      Sama ta haye direct d'akinta ta shiga ta rufo 'kofarta.

      "An dawo Prison"Ta fad'a a fili.

      Knock!knock! Tajiyo bugu,handbag d'in ta ajje sannan taje bud'ewa.Amjad ta gani ri'ke da akwatinta,jira take taga ya mi'ko mata amma shiru.

       "Remove this from your face" Yayi nuni da hannunsa.

       "I wanted it this way"

        "And I don't like it"

         "But you don't wanna see ugly face"

        Se yanzu ya tuna ,dariya abin ya bashi dan shi ya mance ya fad'a.Seda ya d'an murmusa tukun yace"So now you believed you're ugly?"

     Komawa tayi cikin d'akin ta barshi a tsaye gun, gefen gado ta samu ta zauna tare da ciro wayarta cikin jakarta.    Akwatin ya ri'ko ya shigo da ita d'akin daga gefen gado ya ajjeta."Answer my question "

      "Did you believed?"

       An d'au mintina a haka ita bata amsa ba shi be fita ba yana tsaye a kanta.Laila data gaji da zaman hakan tashi tayi ta wuce bathroom kafin ya farga ta rufo 'kofar.

      "Laila!" Ya kira sunanta.

       "I'm not going anywhere until you answer my question?"

         "Shiru tayi kamar ba jinsa take ba,niqab d'in kuwa ta yaye shi tana tsaye jikin 'kofar tana jira ya fita.

      " Laila,can't you hear me? talk to me"

      Ya gama surutansa ko 'kala batace ba,can jin shiru yasa ta kasa kunne taji ko ya fita,alwala ta d'auro ta cire hijab d'in ta had'a da niqab d'in ta ri'ke a hannunta.

      "Am..Amjad" Ta kira a hankali kamar mey rad'a.

     Amjad dake zaune kan gadon dariya ya soma yi yana rife bakinsa.

     "Amjad" Ta sake kira.

     Jin shiru zuciyarta ta raya mata ya fita dan haka ta murd'a handle d'in a hankali,cikin sand'a ta fara takowa.Data duba ko ina taga ba kowa ta saki hamdala,kamar ance juya ta ganshi tsaye a bayan 'kofa .

     Da sauri ta kwasa da sauri zata koma bathroom d'in carpet dake wajen ya zamar da ita "Aghh!" Ta 'kwala ihu tana jira ta jita a 'kasa.

     A hankali ta bud'e ido,taganshi  ri'ke da ita 'kiris ya rage bata kai 'kasa ba ,kallo suke ido cikin ido ,d'ankwalinta da be gama zama a kanta ba ya zame 'kasa,kitson gaba ya yarfo a goshinta har yana rufe mata ido d'aya.Hannunsa ya d'ora kan gashin a hankali yana matsar dashi daga fuskarta.

        "Let me go"Ta fara kici-kici.

        Mi'kewa yayi completely tare da d'ago da ita,hannunta tasa ta ture nasa daga 'kugunta ta matsa gefe.

      Ring! Ring! Wayarsa tayi 'kara,daya duba yaga daga office ne.Bece komai ba ya fita daga d'akin,yana fita ta rufo 'kofarta tare da murd'a key d'in.

          ★★★

     Laila tunda ta rufo 'kofarta bata sake budewa ba ,har 4pm tayi gashi yunwa take ji biscuit dake jakarta ma ta cinye shi.

      Hijab ta zumbula har 'kasa tana ta 'boye hannayenta ciki,sekace mara gaskiya tana sakkowa daga benen she waige-waige take.Kitchen ta shiga ta bud'e fridge tana dube-dube,fruit salad ta had'a tasha abinta ,data fito daga kitchen ta bud'e 'kofar waje ta fito.Gani tayi ba motarsa " Ashe ma ya fita"Ta fad'a.

     Komowa tayi sitting room ta kunna TV,Bollywood ta kai  tayi zamanta kan sofa.Tunawa tayi da aya mey gishirinta data taho da ita daga gida dan haka ta koma d'aki ta d'akko sannan ta dawo ta cigaba da kallonta tana yi tana cin abarta.

     Maghrib nayi ta tafi d'aki seda tayi sallah ta sakko kitchen, jollof d'in taliya tayi dede bakinta tana gama ci ta dawo sitting room ta iske an fara film d'in data ke so.Zamanta tayi harda dad'o volume.

    9:45pm,ya shigo gida ganin TV a kunne kuma bega alamar mutum a parloun ba ya 'karasa ze kashe.Se lokacin ya lura da ita tana kwance se bacci take hankali kwance ta d'ora tafin hannunta a fuskarta ,yawanci haka take baccinta inde zatai bacci seta d'ora tafin hannunta ta kare fuskarta shiyasa ya zame mata jiki ko bata san tayi bacci ba se tayi haka.

      Ba abinda yake kalla se 'kunshin hannunta daya sake maroon barin ma ga'bo'bin yastsunta data rufe fuska.Ba sosai ya fiya ganin 'kunshi ba ,dan ko su Mom da Zakia ba yi suke ba inba a TV ba.

      Idansa ne ya sauka kan 'kafafunta da zanen 'kunshi ya bayyana sosai,'karasawa yayi inda take ya zauna kan gwiwoyinsa ,zanen 'kunshin ne yaja hankalinsa har da ri'ko hannunta yana  kalla.

      Kamar a mafarki taji ana motsa mata hannu, kad'an-kad'an tana bud'e idonta har ta bud'e tar tayi ido hud'u dashi ,a razane ta mi'ke daga kwanciyar ,shi dake zaune seda ya mi'ke tsaye.

     "Is ok"Ya fad'a a sanyaye.

      " Is ok a ina ana shafan hannu"ta fad'a a ranta.

      Tashi tayi daga zaunen ta matsa can gefe,10:05pm taga agogon parlorn ya nuna TVn ma ta kula har an gama film d'in datake kallan ma.

       D'an 'karamin bowl d'in data zuba ti'kar ayar data ci ta d'auka kan center table d'in ta wuce kitchen se wuri wuri take.A kitchen d'in ta dad'e ba abinda take tana tsaye se murza yatsunta take tana kallon hannun.Du da batai 'kunshin ba da ba haka ba.

      "Laila" Taji ya kira sunanta.

    A rud'e ta d'ago ta kalleshi yana daga bakin 'kofa."Are you alright?"

     "Yes" Ta amsa a hankali.

     "Aren't you watching movie?"

      "No I'm not...I will not.." Ta shiga stammering.

      "What are you waiting for?"

       "I'm going to bed"

        "Ok,let's go"

         "Uhn..aa'ai ba ..uh.." Du ta diririce.

      Kamar yayi dariya ganin yadda ta rikice dama yana sane ya fad'i haka,takawa ciki ya soma yi.Laila ganin yana doso inda take ta fara baya ,gefen locker tayi tabi tana zagayewa the more yana tahowa the more tana kewaye drawer d'in kitchen d'in.Ganin ya tsaya tayi sauri tabi gefe ta fice daga kitchen d'in, binta kawai yai da kallo yana dariya.

      Tana shiga d'akinta ta shige bathroom dan gani take kamar d'akin ma she is not safe.Se yanzu taji gumin daya tsatstsafo  mata a jiki alhali ba zafi.

    "Mey  ya sami kansa a Canadan?" Ta tambayi kanta.

    "Wayyo!"

     
     Washegari

       7:30am ya gama shirinsa cikin blue T-shirt mey long sleeves,se black jeans.Abubuwan da suka faru jiya ne sukai ta fad'o masa,shikad'ai ya hau murmushi agogon hannunsa yake sawa amma ya tsaya seda wayarsa yayi ringing ya dawo daga duniyar tunani.

      Laila data farka tun 7:14am amma ta kasa fitowa se le'ken window take tana jira taga ya fita,aiko cikin le'ken ta hangoshi ta sakankance tana kallonsa yazo bud'e mota kamar ance kalli ya d'ago kansa.Laila tsabar rikicewa ta kasa barin window d'in kunya ce ta rifeta seda tayi da tasanin le'kawa,shikuwa be fasa kallonta ba seda ta bar wajen.Murmushi yayi yana zira specs a idonsa ya shiga motar.

       Tana jin ya fita ta sakko 'kasa ta shiga kitchen domin had'a breakfast.Bayan ta gama breakfast ne ta koma d'aki tayi wanka ta shirya,jitai shirun ya isheta ta d'auka waya ta shiga chat.

Amjad:"Mrs Amjad" Yai mata sending ganinta online.

  Laila:"I'm not"

Amjad:"What were you doing at the window ?"

Laila: Nothing

Amjad:You missed your husband.

  Laila:No you're not my husband "

   Amjad: Stop pretending.

    Amjad: Who was your ex bf ? "

      Laila:Someone

     Amjad: Name?

     Laila:You don't have to know "

      Amjad:"Ok,What are you doing now?

     Ganin tambayoyinshi sun'ki 'karewa yasa ta sauka ,aiko ba jimawa sega kira ya shigo.'Canada'Ta gani jikin screen.Ajje wayar tayi ta'ki picking har ya gaji da kira,daga baya ma tashi tayi ta sauka parlor ta kunna kallo.

          ★★★

   4:30pm yau ya tashi daga aiki, Laila tana parlour jin shigowarshi yasa tayi saurin mi'kewa ta koma d'akinta.Tana shigowa yaga ba kowa a parlour sede ga TV a kunne ,hakan yasa ya gane da tana zaune kallon wata'kila ko taji dawowarsa ne.

     Tana jin sanda ya shiga d'akinsa ,dan haka ta zauna kan gado aikin zama.

      1hr later,Knock! Knock! Taji bugu,tana daga shingid'e tayi saurin mi'kewa zaune zuciyarta na dukan uku-uku.

    "Laila" Ya kira sunanta.

   'Kin amsawa tayi se wararo idanuwa take wata zuciyar tana ce mata ta bud'e 'kofar bathroom immediately ta bud'e masa 'kofar seta shige bathroom,haka tayi ta sa'ke-sa'kenta.

     "Laila open this door"

     Hijab d'inta ta d'auka ta zurma ta ma'kale shi a jikinta, a hankali ta bud'e 'kofar ta ra'be daga baya-baya.Tsayawa yayi daga bakin 'kofar bema shigo ba,wani card dake hannunsa ya mi'ke mata,a tsorace tasa hannu ta 'kar'ba ba tare da ta d'ago sun had'a ido ba.

    Anniversary  Invitation ne wanda taga yau ne ranar zuwan 8:00pm aka rubuta a jiki,bata gane nasu waye ba ita de ta karanta.Tana d'ago da kai taga har yana komawa d'aki dan haka ta shigo ta rufo 'kofarta.

      "Ni naje nayi mey acan? wa na sani a wajen? Tare zamu?" Ta jero wa kanta tambayoyi.    

   Har bayan maghrib bata soma shiryawa ba seda taga ya turo mata text."Are you ready?"

    "No" Tayi reply.

     "What are you waiting for?"

     Bata sake wani reply d'in ba ta tashi ,wardrobe ta bud'e ta soma duba kayan da zata saka,ganin zata 'bata lokaci ta ciro wani ba'kin abaya me golden duwatsu,nan da nan ta saka.Powder ,lipstick da kwalli kawai ta sa ta fesa turare mey taushin 'kamshi,red mayafi tayi rolling dashi.

     Wayarta kawai ta d'auka ta zira takalmi mey matsakaicin tudu golden ta samu waje ta zauna.7:41 knock! Knock!

    Tsaye ta ganshi yayi shigarsa cikin dark blue suit ciki white shirt da ba'kin jeans ,gashin kanshi yasha gyara se shining yake,turarensa mey 'kamshin gaske se dukan hancinta ake.

    "Ready?"

    "Uhm" Ta amsa ciki-ciki.

     "Let's go" Yayi nuni da hannu.

      'Kofar d'akin ta rufo tabi bayansa dan ta'ki bari su jera ,a haka har suka sauka 'kasa.A mota shiru ba mey magana,laila ita tama kau da kai can tana kallon waje.Suna isa gurin mutane an hallara ,ita de kallo take binsu dashi dan ba wanda ta sani,se gaisawa yake da mutane wanda yawanci duk abokanan business ne.Wani table suka zauna kafin daga bisani ya tashi amsa kira,bayan 'kan'kanin lokaci sega iyayen taro sun shigo wajen tare da baby d'insu wanda bata wuce 3yrs ba sunsha 'kwalliya gwanin sha'awa,ana ta gaggaisawa dasu tana gani Amjad yaje suka gaisa bata ankara ba taga sun nufo inda take.

     "Wayyo ni Laila" Ta fad'a a fili.

       Matar cikin fara'a ta soma mata magana Laila ma 'karfin hali tayi suka gaisa tayi musu fatan alkairi,sede taga Nigerians ne kuma hausawa "how come's Amjad ya sansu?" Abinda ta tambayi kanta kenan dan a iya saninta  dashi baida wani abokai.

   "Laila ko?" Macen ta fad'a.

  "Eh" Ta amsa.

   "Ni kuma Aisha,yau Allah yasa min had'u de"

    "Gaskiya kam" Cewar Laila.

     Sauran ba'ki da suka zo gaisawa da Aishan yasa suka katse hirar da suke,Amjad d'in ma se hangoshi tayi daga nesa yana gaisawa da mutane.

      Farouq d'an abokin Dad ne yawanci inde suka zo Nigeria suna zuwa gidansu,shekararsu hud'u kenan da yin aure ,duk a Nigeria shikad'ai ne wanda Amjad zece suna abota ,bayan shi baida wasu abokai.

      Laila Tana zaune Aisha tazo "Nan hayaniya,taso mije ciki" Ta taso laila dan ta lura kamar laila bata son hayaniya.

      Cikin gidan nasu ta shiga da laila ta kaita wani parlour."Bari gani zuwa".Ta fad'a tare da barin parlourn.

    Kitchen ta shiga d'aya daga cikin masu aikinta tasa ta kawowa Laila abinci,kiran waya da akai mata yasa ta fita zuwa wajen ba'kin .Ita kuwa mey aikin ganin aiki ya mata yawa yasa tasa wata 'yar uwarta da tazo daga 'kauye ta zibawa Laila.

     Kai tsaye ta bud'e wani plate dake kan drawer ganin friedrice tasha chicken akai ga kayan had'i burjik ,dama ma'kuiyaciyace  yasa kawai tasa spoon ta d'ora plate d'in a tray tare da d'ora robar ruwa da orange juice ta kaiwa Laila.

     Laila dama tun yamma take jin yunwa,ba 'bata lokaci ta bud'e plate ta soma ci,sede taji abincin taste d'in ba dad'i cabbage d'in yayi wani iri gashi ba zafi ita a tunaninta ko hucewa yayi.Haka ta lalla'ba taci, naman ma ba sosai ta iya ci ba,rabi taci ta rife plate d'in.Leman ne ma tasha da yawa ta kora da ruwa.

       Wayarta ta kunna Tana d'an duddubawa a haka lokaci naja har taci fin 30min.Sede kuma tun bayan cin abincin ta fara jin suka a cikinta kad'an-kad'an yana murd'awa.
     

      *Let's stop here,yau na fita hakannan na daure nayi  typing coz bana so na barku kuna jira.Don't forget to comment,vote and share.Love u all💋*

*Dijensy❤*
    

       

  

    

    
      

    

   

   

    

    

           

       

   
   
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

1⃣9⃣-2⃣0⃣


        Wani irin murd'awa cikinta ya hau yi,nan take gumi ya soma keto mata ta rasa abinda ke mata dad'i wayar ma ajje ta tayi gefe.Tashi tayi a rud'e ta nufi inda taga mey aikin ta shiga,a kitchen ta tarar da ita tana wanke-wanke.Laila tambayarta tayi toilet tana ta zufa.D'aki ta rakata wanda yake d'auke da toilet a ciki,da sauri-sauri laila ta fad'a  ciki.

     Minutes later ta dawo parlour gwiwoyinta sun fara sanyi gashi cikin har yanzu be dena hautsinawa ba,wayarta ta duba taga 3missed na Amjad. Bata ko zauna ba ta fita,a chan  farfajiyar gidan ta hangeshi yana zaune a table shi kad'ai jama'ar wajen ma sun fara raguwa.A hankali ta taka zuwa inda yake,sede ta 'karaso ya kula da ita.

    "Where have you been?"

     "Gani na fito ai"Ta fad'a.

      Mi'kewa yayi tsaye ya fara tafiya tana biye a bayansa Farouq da Aisha suka 'karaso inda suke.

     " Tafiya?"Ta tambayi Laila.

    Laila cikin ya'ke ta amsa da "Eh"

    "Toh bari na kar'bi numbernki".

     Numbernta ta fad'a mata a take tayi flashing itama Laila tayi saving, har waje suka rakosu ita de Laila kawai basarwa take cikinta ba abinda yake se hautsunawa ta 'kagu su koma gida.

      Tunda ta shiga mota bata ce 'kala ba,gani take kamar ba tu'ki yake ba har wani le'kawa take tana ganin speed d'in."Mtchww" Tayi tsaki ba tare da ta sani ba.

    "Are you alright?" Ya tambaya.

     Kai ta kad'a alamar "eh" se kad'a 'kafa take tana tapping cinyarta."Innalilahi wainna ilaihirraji'un"Ta fad'a  a ranta ganin traffic light ya tsayar dasu.

    Da 'kyar ta samu ta iya jurewa har suka koma gida,cikin sauri ta fad'a toilet ko 'kofar d'akin yau bata rufe ba.Daga dawowarsu zuwa yanzu Laila ta shiga toilet yafi sau uku,gwiwoyinta gabad'aya sunyi sanyi da'kyar take takawa.Gashi batasan inda zata sami magani ba,lokaci guda tayi zuru-zuru jinta take kamar kara dan tsabar rashin 'kwarin jiki.

       11:29pm Ring!Ring! wayar ta tayi 'kara lokacin tana toilet har 3 missed call batai picking ba.

   
     Amjad yana d'akinsa dede lokacin yake shirin kwanciya wayarsa tayi 'kara,koda ya duba yaga Farouq.

      
     Knock! Knock! Ya 'kwan'kwasa 'kofar d'akinta shiru,handle d'in ya murd'a ya shiga beganta ba.

     "Laila" Ya kira sunanta.

    Tana shirin fitowa taji ya kira sunanta ,zaro ido  tayi ido tana mamakin jinsa a d'akinta a irin wannan lokacin.

     "Laila ,come on open the door"

       Tsit kake ji ko motsi ta'ki yi gashi tsaiwar ta isheta,kan bathtub ta samu ta zauna ta dafe  cikinta.

     "Laila,can't you hear me? open the door now stop pretending I know everything"

     "Mey? Waya fad'a masa? Yasan..." Ta dafe kai shikenan tonon silili.

    "Laila don't let  me  open it myself, you know I have a spare key right?"

     "Innalillah" Jiki ba 'kwari ta mi'ke tsaya a daddafe ta 'karasa jikin 'kofar gashi jikinta kayan bacci ne riga da wando  kusan ¾,inda Allah ya taimaka ma rigar ta hauro kusan cinya,d'an'kwalin kanta ta ware yadda ze sakko 'kasa , a sanyaye ta bud'e 'kofar kanta a 'kasa.

       "Laila" Ya kira sunanta.

      A hankali ta d'ago da kanta kallo d'aya tayi masa ta maida kanta 'kasa,se jan mayafin take tana kare 'kirjinta.

    "Uh...you need to see a doctor"

       "I'm fine" Ta fad'a murya 'kasa-'kasa.

       "You're not,you better stop pretending I know you're not ok they explained everything to me, you ate a spoiled food"

     Shiru tayi bata musa masa ba,ta kasa d'ago da kai dan tsabar kunya a ranta tana da tasanin cin abincin.

     "We need to go now".

      Tana jin kunya ta wuce zuwa wardrobe ta ciro hijab d'inta ta zira, wata doguwar riga ta d'auka tana so tasa gashi yana tsaya a d'akin se so take ya fita amma yayi burus sema folding arms da yayi yana kallonta.'Karfin hali tayi ta ri'ko doguwar rigar a hannu ta wuce bathroom yana kallonta.

     Tana fitowa ya tafi d'akinsa ya d'auka key ya fito,a sitting room ya taradda ita zaune kan sofa dan ko tsaiwa ta kasa.

     Ganin ya sakko ta mi'ke a kasalance ,suna fita kafin ta shiga mota kawai amai ya tunkaro ta kafin ta koma ciki ta she'kashi a cikin flowers.Kafin aje asibiti ta sake galabaita ,suna zuwa aka sa mata drip,tana kwance  se kallon carnula d'in dake hannunta take,hijab d'in ta cire se mayafin kanta ta yafa.Amjad yana daga zaune kan kujera daga gefenta.Gashi ta manta wayarta ba dama ta kira Mami,ga abinci daya siyo mata ta kasa ci  maganin ma da'kyar tasha.

     "You need to eat"

       "Na 'koshi" Ta fad'a a ciki.
       
         Be sake ce mata komai ba ya cigaba da tapping wayarsa.

            ★★★

      5:06am ,ta bud'e idonta hannunta ta d'aga ganin carnula ta mayar,a kan kujera ta kalleshi ya jingina se baccinsa yake.Data kalli ledar ruwan taga ya kusa 'karewa,tunanin yadda za'ai ta tashesa ta fad'a masa ta shiga yi.Pillow ta d'auka ta d'an buga 'karshen gadon amma kamar bayi take ba,haka tayi -tayi harta gaji,daga baya kawai ta cilla masa pillow d'in aiko ya sauka kan fuskarsa.Yana bud'e ido ta sunkui da kai kamar ba ita tayi ba.

    Pillow d'in ya kalla kan cinyarsa ya dawo da kallonsa kanta,ganin ba pillow kan gadon yasa ya gano abinda tayi."What do you want?" Ya tambaya.

    Drip d'in ta kalla tayi masa nuni dashi yanda tayi da bakinta ne yaso bashi dariya har ma da birgeshi,cikeda shagwa'ba ta ta'be bakinta.

       Da kanshi ya cire mata ,bayan ya kira nurse kuma ta cire carnula d'in.Cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga toilet ta d'auro alwala,shima masjid ya fita sallah.Bayan ya dawo daga masjid ya siya mata abinci,dama yunwa take ji tana ci tasha magani.Wajajen 8:30am akai discharging d'insu suka koma gida,se bayan sun dawo ta tuna da office d'insa,tana so ta tambayesa zeje amma ta kasa."Toh zaman mey kake ai na warke"Ta fad'a a ranta.

    "How are you feeling now?" Ya tambayeta.

     "I'm fine" Ta amsa kamar bata so.

     Daga yadda ta amsa ya gano bata son maganar."Any story? tell me about it how does it started? "

      Tasan dama za'a rina,bade yaga taji sau'ki ba.Sake murtuke fuska tayi ta kauda kai.

      "Come on,it started with stomach ache followed by...." Be 'kare ba yayi shiru yana murmushi.

     Ring!Ring! Wayarta tayi 'kara 'Aisha'Ta gani a screen.

    "Hello"

     "Hello Laila,ya jikinki?"

     "Da sau'ki"

      "Ayya ,kiyi ha'kuri shirmen mey aiki ne bata duba ba ta baki lalataccen abinci"

       "Karki damu ba komai na samu sau'ki"

        "Aha,Allah ya 'kara sau'ki se munzo"

       "Nagode" Daga haka sukai sallama.

     Suna gama wayar tayi dialing number Mami   har lokacin Amjad be fita ba,ita kuwa tayi hakane dan karya dameta.Bayan ta gaisa da Mami  ta shiga labarta mata abinda ya faru harda 'kara langa'be murya."Mami ruwa leda 2 fa aka 'kara min"

    "Toh Allah ya sawwa'ke"

    "Mami su Maryam suzo"

     "Har sai kin ro'ka? sarkin

Please Login or Register in order to submit comment