Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi.

Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani sheri saboda ya san na san sirrinsa, kuma a matsayin na wacce ke aiki karkashin Jibril ba zan iya fada masa wannan ba, bana da wata hanyar sai ta ki, ke kadai ce zaki iya hankaltar da shi domin ceton rayuwarki da ta danki da kuma ta Jibril har ma da tawa gaba daya, ki kuma tsirarta da Bilal daga sherin da yake kokarin laka masa, kin san idan wani abu ya samu Noor dole Jibril ya zargi Bilal kuma ba zai taba kyaleshi ba”

Hannu nasa na rufe bakina sai kuma na sauke ajiyar zuciya, kaina ya yi nauyi sosai kalamanta sun min hawa har na rasa wanne zan fara tunani balle na samu abunda zan ce mata, ji na yi ta dafani.

“Nasan yana da nauyi Nawwara, ki yi tunani akai, ban san abunda ya raba ki da Jibril ba, amman yana da kyau ki shiga rayuwarsa ko dan gaba ko kuma na ce ko dan danki, abu na karshe da zan fada miki shine Jibril yana son ki sosai da sosai, domin lokacin da Siraj ya sanar masa cewar kin mutu ya yi kamar na haukace, ba sai na gargadeki akan karki fadawa kowa wannan sirrin ba saboda ina ganin a mace mai tunani da hangen nesa na barki lafiya”

Da ido kawai na bita har ta fice, sannan na dawo duniyar mamaki da aljabi anya zan iya wannan aikin kuwa? Mi ma zai kai ni taimakon mutumen da ya nemi salwantar da tawa rayuwar? Abu na farko da ya zo min a rai shine Inna dole ne na fada mata komai ko dan neman shawararta, cikin hanzari na tashi na fita waje gurin Inna.
[11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤*

Wattpad @KhadeejaCandy


5⃣1⃣

Inna ta tsorata sosai da abunda na fada mata hankalinta duk sai ya tashi.

“Taya zaki iya shiga cikin wannan lamarin Nawwara?ke fa mace ce ba namiji ba, kuma irin wadannan mutanen hatsarine rabarsu”

“Nima abunda na ke ta tunani kenan! Ona ganin aiki zan sa Jibril ya koma sai mu koma tare kin ga duk wani taimako zan iya bashi ta nan kuma ina lurar da shi akan wasu abubuwan”

“Gaskiya Nawwara ina jin tsoro, karki je ki janyo mana wani abun na daban kuma”

“Babu komai Inna ba zan fito kiri da muzu na fada masa abunda yake faruwa ba, ta dabara zan yi”

“Kina tunanin hakan ba zai haifar da wata matsala ba?”

“Inshallah ba zai haifar ba”

Ta kawar da kai ba dan ta yarda din ba, ni kuma ina ganin bana da wata mafita sai wannan.



JIBRIL POV.

Lokacin da Noor ya ji cewar Momynsa ba zata zo ba sai duk yanayinsa ya canja ya koma cikin jin bakinciki da damuwa, duk yadda Jibril ya so kar ya bata rai sai da Noor ya bata kuka ma sai da ya yi. A gado daya suka kwanta under one bedsheet, misalin biyu da rabi na dare Jibril ya farka ya shiga bedroom ya dauro alwala ya fito ya shinfida carpet ya soma sallah nafila da a yanzu ta soma zame masa jiki.
Kuka ya yi sosai yana neman yafiyar Allah akan abubuwan da ya gabatar marasa kyau sannan ya roko Allah bukatunsa tare da neman shiriyar Allah. Be san yadda zai karanta qur'ane ba but yasan yadda zai yi iistigifari da hailala da kuma tasbishi da kuma salatin Annabi. Yana zaune saman carpet din har aka yi asalati sannan ya tashi ya fita zuwa masallaci.


Misalin takwas da rabi Noor ya farka a lokacin Jibril na kitchen yana hada musu breakfast, ko da Jibril ya fito ya samu Noor tsaye bakin kofar bedroom yana ta kallon falon.

“Good morning Noor”

Sai kawai ya saka dariya kamar ba shine ya kwanta da fushi jiya ba, kuma ya rufe ido wai yaji kunya an gaishe shi. Jibril ya aje kayan da ke hannunshi saman dinning sannan ya nufo Noor ya duka daidai shi ya kama hannayensa ya rike.

“Ka tashi lafiya?”

“Lafiya kalau, Dady na manta ban tashi ba sai yanzu”

“Yeah ai kara ka yi bachi mai kyau ka samu ka huta ko?”

“Momy da wuri take tada ni na yi sallah”

“Yanzu ma ai lokaci be kure ba muje bedroom ka yi sallah”

Tare suka shiga bedroom din Jibril ya taimaka masa ya wanke bashinsa sannan yaa yi masa wanka ya yi alwalah sannan ya daura masa tawul suka fito yana dauke da shi. Ko da ya fito wayarsa na ringing da sauri ya dauka ya kara a kunne.

“Assalamu Alaikum Malam, okay gani nan fito”

Sai ya zaunar da Noor saman gado.

“Jira ni a nan ina zuwa”

Number Rabi ya nemo ya tura mata sakon daga bisani ya yi mata transfer na kudi i zuwa account dinta dan ta siyoma Noor tufafi, ko da ya fito Malamin na tsaye waje kusa achabansa yana jiran fitowarsa, cikin girmamawa Jibril ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya dora masa da.

“Na san yau ya kamata ace mun fara but yau ina tare da yarona kuma yanzu idan mun gama karyawa zan kaishi gida, so ina baka hakuri zuwa gobe sai mu fara, kuma in fa hali ina son bayan mun yi da safe mu yi da yamma”

“Ba matsala, zamu iya farawa gobe din Allah ya kaimu amman kamar wane lokaci?”

“Irin takwas na safe haka, da dare kuma tara na dare nasan bayan wannan lokacin ina gida, sai salarinka nawa ake biyanka per month?”

“Aa ranka ya dade bana son sisinka, zan koya maka komai saboda da Allah”

“Kai amman ina godiya sosai Allah ya saka da alheri”

“Amin amin sai dai littafan da za a siyo”

“tau kamar nawa za a kashe?”

“Zamu siyo ahalari sai kuma husnul muslim da kuma dan goma mai hade da bakaken harufan arabi ta yadda zai maka sauki ganewa”

“Kana da account ne?”

“Eh akwai”

“Okay ina zuwa”

Wayarsa ya bude ya yi masa transfer 10k na siyen littafan, har Malamin na cewa kudin ya yi yawa sai ya ce ya dauki sauran abunda ya rage. Cikin dadin rai ya dawo parlour saboda yana jin ya fara taka wani mataki na gyara rayuwarsa, abunda yake ta kokarin yi shine ya zama uba na gari gurin Noor wanda zai yi alfahari da shi ko bayan ransa.
Da kansa ya yi feeding Noor sannan ya shiga wanka ko da ya fito Rabi tana parlour zaune ta kawo masa kayan Noor da ya bukaci taje ta siyo, ita yasa ta shirya Noor, shi kuma ya shiga ciki ya shirya kansa sannan suka fito tare harabar gidan ita ta wuce shi kuma ya kama hanyar gidansu Nawwara tare da Noor dake gaban Mota.

Jibril ne ya fara fitowa cikin motar sannan ya zagaya ya budewa Noor ya dauko ya dorashi kofar gidan.

“Shiga ciki ka ce da Mamanka ina waje”

Da gudu Noor ya shiga cikin gidan, bayan few seconds ya dawo ya ce

“Wai ta ce ka shigo”

Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya dora kafarsa a kofar gidan ya shiga bakinsa kumshe da sallama.

“Wa'alaikaissalam”

Inna da amsa masa, sai ya zube a gurin yana kwasar gaisuwa kai baka ce ma shi ba ne, kansa a kasa yana mai jin kunyar Inna sosai kamar yau ya fara haduwa da ita.

“Tashi Jibril shigo ciki, ashe an sallami Noor”

“Eh an sallame shi jiya shine naje da shi gida”

“Allah ya kara lafiya”

“Amin ya rabb”

Daga haka ya mike tsaye.

“Bari na wuce daman wani gurin zanje na ce bari na fara kawoshi”

“To an gode”

Tashi ya yi ya juyo ba dan kuma yana da gurin zuwan ba, yace hakan ne kawai saboda ya kare kansa, yana son ya tambaya ina Nawwara kuma yana jin kunyar haka ga alheri yana son ya yi ma Inna kuma be san yadda zata kalleshi ba. Bayan na fito ya nufi motarsa sai yaji Muryar Nawwara ta kirashi.

“Jibril”

Ya juyo da sauri ya dawo zuwa inda take.

“Nawwara kina lafiya”

“Lafiya kalau”

“Am sorry about yesterday”

Ya fada yana kallon yanayinta sai kawai ya ga murmushi a fuskarta abunda ya bashi tsoro da kuma mamaki a lokaci daya, dan ya yi zaton wata bakar maganar zata fada sai kawai ya ji ta ce

“Never mind, ni har na manta da wannan ma, amman Jibril ka ce min zaka canja ko?”

Ya kara matsowa kusa da ita.

“Na canja Nawwara ba wai zan canja ba, Wallahi na canja”

“Idan har ka canja zaka zama uba na gari Jibril, kuma da na gari gurin Mahaifinka”

“Abunda na ke kokarin yi kenan ganin na zama uba na gari wa Noor”

“Miyasa zaka mikawa Siraj ragamar kamfanin mahaifinka?”

“Saboda na yarda da shi kuma mahaifina ya yarda da shi, kuma ba zan iya jan raganar kamfanin ba a yanzu”

“Saboda mai?”

“Saboda ke Nawwara tunanina da damuwata duka akanki suke”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce

“Ya kamata ka yarda da kaddara Jibril, ka yarda abunda ya sameka da wanda zai sameka nan gaba duka daga Allah ne, ka daina saka tunani a cikin ranka saboda ni matar wani ce, idan har ka yarda da kaddara ina son ka cireni a cikin rayuwarka, Jibril ina son ka nuna min irin son gaskiyar da kake min ta hanyar maida hankalinka akan rayuwarka da kuma ta danka, ina son ka min alkawari Jibril cewar ba zaka sake shan cocaine ba, kuma zaka maida ragamar kamfanin mahaifinka a hannunka, ina son ka zama jarumi Jibril”

Kallonta yake yi ido cikin ido yake karantar gaskiyar kalaman dake zuciyarta, duka abunda ta rokeshi yayi zai iya yi matukar hakan zai faranta ranta.

“Na miki alkawari Nawwara zan yi duka abunda kika fada”

“And lastly ina son ka cireni cikin ranka Jibril, ka yi focusing akan rayuwarka ta nan gaba da kuma ta danka, ka sa a ranka ko babu Nawwara zaka iya rayuwa, domin can baya babu ni a duniyarka, a yanzu ma idan babu ni zaka iya, na tabbatar min da canjin da kake cewa ka yi Jibril ka zama namijin gaske”

Ya gyada mata kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.

“I promise you Nawwara zan yi dukan abunda kike bukata”

“Zan maka addu'ah, kuma ina son na koma aikina tare da kai”

“Zamu koma yaushe kike so?”

“Allah ya kaimu, but Nawwara ina fatar ba za ki hanani kusanci da dana ba, kuma ba za ki hanani kyautatawa family ki ba”

“Na fi kowa son ka yi kusanci da Noor Jibril saboda na san ko nayi aure ba zaka bar ni naje da shi, so tun yanzu ina son Noor ya saba da kai sosai da sosai, matukar wannan canjin da na gani a yanzu a tare da kai ya tabbata zan fi kowa farinciki Jibril I'm ever ready to help you ko dan saboda Noor”

Matsowa ya yi kusa da ita kamar zai taba ta sai dai yasan babu wannan damar domin bata son ya tabata kuma shi ma kansa yana son sabawa kansa da wannan.

“Thank you so much Nawwara, Wallahi Ina son ki sosai ina son ki yarda da wannan”

“Na yarda Jibril”

“Ina jin kamar mafarki na ke Nawwara, you actually changed”

Ta yi murmushi tare da sanda kanta kasa abunda ya kara burge Jibril ya ji wani sonta na kara shigarsa, sai dai kalamanta na cewar ya fitar da ita daga ranshi be masa dadi ba, but shi kansa yasan yana bukarta cireta a ranshi ko dan ya samu sukuni a rayuwarsa.


MUSTAPHA POV.

Yau kwanansa biyu da dawowa daga asibiti, tun lokacin da Hajiyarsa ta yi ma Nawwara wannan furucin ransa ya sosu matuka yake jin rashin dacewa da kyautawa abunda Momynsa ta yi.
Dan haka ya yanke shawarar yau sai ya kaiwa Nawwara ziyara saboda ya bata hakuri kan abunda ya faru, dan haka yana fita sallah magariba be dawo ba ya wuce gidansu Nawwara, ya taki sa'a yana aikawa kiranta sai gata ta fito cikin Hijabi sai kamshin turare take, sallama ta fara masa sannan gaisuwa ta biyo baya, daga nan kuma sai dukaninsu suka yi shiru ita tana jiran abunda zai fada mata shi kuma yana tunanin ta ina zai fara, da ta fara gajiya da shirun ne yasa ta ce

“Ya jikinka? Sorry ban je na dubaka a asibiti ba”

Yayi mamakin jin furuncinta domin sam be tsammaci ma zata fito ba balle har ta kula shi haka har da tambayar jikinsa.

“Naji sauki sosai Nawwara, ina son na baki hakuri akan abunda Momy ta yi miki last time...”

Ta daga masa hannu.

“Mahaifiyarka tana da gaskiya Mustapha, na kaina uwa ce kuma uwa kadai tasan abunda wata uwar take ji game da danta, ni kaina ba zan yarda dana ya rasa rayuwarsa akan wacce bata san zafinsa ba, wacce na san ba zata taba aurensa ba.

Mustapha ya kamata ka yi tunani, ni da kai ba daya ba ne, ballanta wani abun ya shiga tsakanin ni da kai, yar uwata ka yi ma fyade taya kuma ni zan aureka? Zuciyarka ta daina yaudararka abunda ba zai taba tabbatuwa a gareka ba, ka daina hangen abunda ba naka ba, Ina tunanin mutuwar Habiba ta canja mana rayuwa dukanmu, ta zamo silar shiriyarka, shin miyasa ba zaka tsayardar tunaninka guri daya ba ka yi abunda zai fiddaka?

Duk yadda zaka so ni aikin banza ne, saboda komai ya riga ya lalace, a zan boye maka Mustapha soyayyarka ba zata taba samun gurbi a zuciyata ba ko da kadan ne, ka daina wahalar da rayuwarka akaina, ka yarda kaddara ce a haka sai kaga Allah ya kawo maka mafi alherinta”

“Thank you Nawwara na gode da kika fada min gaskiya, har gobe ina alfari kuma zan kasance a cikin alfari da son ki har abada, domin son ki ya canja min rayuwa, ya sa na zama kalar da ban taba tsammanin zama ba”

Ya fada idanuwansa na cika da kwalla.

“Ina maka fata ta gari Mustapha, domin ni Bilal zan aura kai ma ina maka fatar samun matar da zata so ka sosai kuma iyayenka su so ta tadda zaka ji dadin zama da ita”

“Thank you but ina son ki taya ni da addu'a domin abun ba sauki”

Ya fada yana murmushin karfin hali tare da share hawayen da suka zubo masa.

“Zan taya ka, ina maka fatar alheri”

Ya dade a tsaye yana kallonta yadda zai yi rayuwa babu ita yake hange, ya san gaskiya ta fada masa shi kanshi yana jin kamar ba zata aureshi ba, sai dai a ganinsa idan har bata aureshi ba ba zai taba gamsuwa cewar ta yafe masa ba, but kalaman da tayi masa a yanzu yasa shi canja tunaninsa kuma ya samu gansuwa a ransa cewar Nawwara ta yafe masa har zuciyarta, ya riga yasan matukar yana son ya shirya da iyayensa dole ya rabu da ita, duk da yana jin a yanzu ta zama wani bangare na jikinsa.
Kamar marar lafiya haka ya dawo gida nan da nan sai zazzabi ya rufe sai dai be bari mahaifiyarsa ta sani ba.
[11/8, 9:40 PM] CANDY_♥️🖤: *RAI BIYU...♥🖤*

Wattpad @KhadeejaCandy


5⃣2⃣

SIX MONTHS LATER...

Rayuwar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba ita na ke a yanzu, ni kaina ina canjin da na yi a jikina da kuma ruhina, na zama RAI BIYU a gurin mutum biyu Noor da Jibril, na yi fadi tashin rayuwa kamin na kawo yanzu, na yaki zuciyata kuma na yi nasara akan kudirina.

Komai ya canja a yanzu wa zai yarda da ni idan na ce ina rayuwa da Jibril a matsayin kanwa kuma abokiya, ni kaina na kan yi dariyar kaina kamin mamaki ya biyo baya, na zauna a matakin da ban taba tsammanin zan zauna ba, na shiga na fita na gyara rayuwar da na fi tsana a duniya abunda ko a mafarki ban taba tsammanin afkuwarsa ba, a yanzu Jibril ba shi wani madubi ko kuma tsarin rayuwa sai nawa, dukan wani abu daya shafi kamfaninsa da rayuwarsa ko kuma ta Noor da ni yake shawara kamin ya aiwatar da shi, hakan yasa kara tsanar da Siraj ya ke min har bayan son ganin sai dole, gashi case din da muke a kotu ashe yayarsa ce da ke aure nan domin a asalinsu su yan kaduna ne, shi kansa be taba sani ba sai da muka yi zaman kotu na hudu aka je da shi muka hadu, akwai nasara sosai a shariyar ta mu kasancewar Dpo ya tsaya kai da fata wajen ganin an yi mana adalci kuma an bi maka hakkin mahaifinmu, gaskiya na yaba da irin kokarin da dpo yake mana hakan ya kara tabbatar min mana cewar ba duka yan sanda marasa na na gari ba, domin a cikin bata garin ana samun na gari a cikin na garin kuma ake samun bata gari, Inna ma ta yaba da kokarin shi duk da ita tafi maida hankalin akan cewar wai so na ke, ni kan ina ganin kamar dai yana yi dan Allah kawai domin ni ai yasan an samin rana, duk da wani lokacin haka kawai xai kirani a waya ya ce fira yake son muyi ko ya ce yana son jin muryata, sai dai duk wannan firar da muke a waya Bilal be sani ba da sai ya kusa hadiye zuciya saboda mugun kishina da yake ko da yake na lura kamar ya fi kishina akan abunda ya shafi bangaren Jibril, kamar yadda shi ma Jibril yake nuna min kinshinsa na banza a duk lokacin da na ambaci Bilal a gabansa ko kuma na yi waya da shi, ni kuma na kanyi hakan ne saboda ya daina wahalar da kansa yana kusa kansa gareni domin na dade da zama matar wani.

Na yi nasarar shiga na kanannade duk wata hanya da zata sa Siraj ya samu wani abun a karkashin Jibril, idan zuwa wani aikin ne ko taro ni kaina na ke cilasta Jibril zuwa, kuma na sa ya karbe komai nasa da yake hannun Siraj duk da be so haka ba, har ta kai ta kawo idan ban ga dama ba Siraj ba zai iya ganin Jibril ba indai a office ne,  da fari Jibril da shi kansa Siraj din sun zarge ni da shiga tsakaninsu na neman rabasu, sai dai nasarorin da Jibril ya yi a cikin watan nan shida ba tare da Siraj ba yasa na fahimci shi kadai ma zai iya ba sai tare da wani, ko da wasa ban taba fadawa Jibril cewar Siraj yana masa Zagon kasa ba, sai dai na kan yi kokarin nuna masa haka ta hanyar wasu abubuwan da Siraj yake yi, tare da Rabi muke komai ita take sanar da ni duk wani kudiri na Siraj ni kuma sai na yi kokarin Jibril aikatawa, Jibril bw taba yarda da ni sosai ba kamar lokacin da na daukeshi muka je bypass da kansa ya ga kamfanin da Siraj yake ginawa wanda be taba fada masa ba, hakan yasa shi ma na ya fara ja baya da shi har suka soma samun sabani saboda rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu Jibril yana ganin be kamata ace Siraj ya boye masa abu mai muhimmanci kamar haka ba, shi kuma Siraj yana ganin Jibril ya dauki amana ya bani har ina shiga tsakaninsu.

Jibril ya sake shiga rayuwata a karo na biyu, na sake jiki da shi irin sakewar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba, ya canjawa Noor da Jamila makaranta daga makarantar gwanati zuwa Imam international school, da school bus ake kawo su kuma a dauke su da safe, shakuwar data shiga tsakanin Noor da Jibril a yanzu har mamaki take bani lallai na yarda da aka ce yara sun fi sabawa da iyayensu maza. Sakina kuma ya maida Khalifa International School wace ke can kusa da Polytechnic bypass, dukan wani abu da za'a ci a gidan daga aljihun Jibril yake zuwa, idan na yi magana yace dansa yake yi ma, ni kuma na kan bashi damar hakan ne saboda nima na samu damar shiga cikin tasa rayuwar, ni ce na yi ruwa na yi tsaki a rayuwar mutumen da na fi tsana a duniya, bana da matsala a yanzu sai ta mutum biyu Bilal da kuma Siraj, na rasa yadda zan yi na fito kai tsaye na nunawa Jibril irin kudirin da Siraj yake da shi akansa, ina son nayi masa yadda zai fahimta ne kuma ya kamashi dumudumu amman na rasa yadda zan fahimtar da shi.

Sai Bilal da ya kasa fahimta ya kasai daina zargina duk kuwa da kasancesar an saka ranar aurenmu a yanzu, zuciyarsa ba raya masa kamar ina son Jibril ne, ga kuma ta bangaren Familynsa har yanzu mahaifiyarsa fushi take dashi ta kasa sakewa da ni saboda bata son auren, gashi tana ganin kamar saboda ni aka kore shi aiki daman mahaifinsa ne ya tsaya kai da fata akan maganar har aka saka ranar auren.
  Ko ranar da aka kawo tufafin sakawata sai sa yan'uwansa mata suka yi ta Maganganun kamar na habaici, ni dai ko kadan hakan be dame ni domin iya abunda na sani Bilal yana so na ni ma kuma ina son shi so kiyayyar yan'uwansa ba zata dame ni ba, domin ina jin a jikina zan iya canja musu rayuwa su soni ta hanyar kyautata musu da kuma yi musu biyayya.
  Ban tsammaci Bilal zai zuba min lefe kamar haka ba, domin kala talatin da biyu ya yi min kamar wata budurwa babu abunda be saka ba a cikin lefen, da na masa magana sai ya ce wai daman ya dade da siye ya aje ba a yanzu ya siya ba, baya aikin komai a yanzu sai tsaron wani shagon computers suna biyanshi kullum, amman ya yi applying a cbn

Please Login or Register in order to submit comment