Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan sai na masa duka ai”

“Mi kuma yayi miki?”

“Da ya gama cin abincin rana haka ya bar min plate a falo ya wuce islamiya kuma na sha fada masa ya daina min haka amman ya ki”

“Saboda wannan zaki dakeshi”

Ta yi shiru, sai kawai ya yi dariya ya kara rumgumeta, domin a yanzu ya saba da halin abu kadan zata ce sai ta hukunta shi ko Noor ko da kuwa abun be kai ya kawo ba, tun da ta dauki cikin nan ba wani zaman lafiya, kullum da kalar fitinar da take masa shi da Noor.

A bakin kofar bedroom din Noor ya tsaya ya leko kansa dan yasan laifin da ya yi ya ce

“Daddy muje an fara kira”

Suna hada ido da Nawwara ya yi saurin komawa yaja kofar.

“Ni gaskiya sai na dakeshi ko kuma kai na hukunta ka”

“Hukunci ai ba zai wuce na cewar ba zamu ci miki abinci ba, ni kuma sai na dauki da na muje restaurant mu ci abinci mai dadi”

“Ba dai irin nawa na”

“Har ya fi naki dadi ga waiters din da iya tarbon baki”

Ya fada yana kanne mata ido daya. Ita kuma ta dauki filo ta jefa masa ya gwace yana mata dariyar keta.

Washe gari ma haka ta tashe da masifar ta kamar kullum, sassauci daya ta samu bayan Noor ya wuce school ya dora kanta saman cinyarsa ya bude suratul kaffi yana karanta, ita kuma tana saurare har bachi ya dauketa, bayan ya gama ya dauke kanta ya maida saman matashin kai ya shiga kitchen ya shirya musu abun karyawa, bata farka ba sai kusan goma na safe. Da taimakonsa tayi wanka ta saka abaya black, sannan suka dawo falo suna karyawa. Shi yake feeding dinta ita tana feeding dinsa kamar yadda suka saba har a gaba ko da kuwa Noor yana nan.
Basu gama karyarwa ba aka danna door bell amalar akwai wani a bakin kofar, har ta kai je zata tashi sai ya zaunar da ita.

“Bari na duba”

Yana bude kofar ya karbi sakon da ke hannun mutumen sai ya maida kofar ya rufe, ya dawo yana fadin.

“Rufe idonki”

“Mi zaka bani?”

“Just close your eyes please”

Mikewa tayi tsaye ta soma zagayensa ita ala dole sai ta ga abunda ya shigo da shi shi kuma ya rika juya hannayesa ta kasa ganin a dole ta hakura ta rufe idanuwanta.

“To na rufe”

“Ban yarda da wannan rufewan ba, juya bayanki”

Ba musu ta juya baya, zuciyarta cike da zumudin son ganin abunda yake boye mata. Da sauri ya juya ya koma gurin kofar ya bude musu suka shigo da kayan da suke dauke da su suka dora saman center table sannan suka fice da sauri, har lokacin Nawwara bata juyo ba duk ta tana jin kamar motin abu a bayanta.

“Juyo ki bude idonki”

Juyowa tayi sai dai bata bude idon ba, har sai da ya sake fadin ta bude idonta. A hankali ta soma bude idon sai idanuwanta suka sauka kansa. Still har yanzu hannayensa suna bayansa da alama akwai abunda yake cigaba da boyewa.

“Minene tau?”

Ya nuna mata tsakiyar falon inda center table yake, what a surprise katon cake ne a saman teburi an rubuta masa HAPPY BIRTHDAY MY PRINCESS, da mayan haruffa da sauri ta doshi gurin tana kallon cake din cike da excitement. Katuwar farar paper da ke gefen cake din da aka kawata da flowers da masu harufa an rubuta FOR MY LOVELY WIFE, ta kai hannu ta dauka ta bude jikinta ya rawa ta soma karantawa.

_Happy birthday to someone close to me, today my queen was born, the queen of queens, how can I forget your birthday Queen? The woman whos make feel better person, she's stay by my side i learned many things about life and love, she's the only woman i love and i know lucky is the man who is the first love of a woman, but luckier is the woman who is the last love of a man, you got it all Baby, I loves you yesterday. I love you still. I always have .. I always will. Happy birthday to you my heart_

Dagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta cike da kwalla.

“My soul i love you so much”

Hannunta ya kama ya saka mata zoben da ke hannunsa mai alphabet din NJ.

“Happy birthday Princess”

“Thank you, ni na manta da yau ne birthday na ma”

Ta kwantar da kanta jikinsa tana hawaye.

“Ni kan ba zan manta ba, taya zan manta birthday din babbar mace kamar wannan? Matar da ita farincikina mace da ta zame min RAI BIYU, kuma muka zama RAI BIYU ni da ita”

Ta yi farincikin da abunda ya yi mata har bata iya misalta jindadinta, haka yake mata a ko da yaushe yana surprising dinta da abunda zai sata farincikin ko ya kara mata son sa a zuciyarta. A ranar farinciki ya hana Nawwara bachi kamar yadda yake hanata a duk lokaci da wani abun farinciki ya same ta, baya da bukatar godiyarta domin yana tunanin duk wata hanya da zata gode masa ta yi masa yawa, shine ya kamata ace yana gode mata ko dan canjin rayuwar da ya samu.



*** *** ***

BAYAN WASU SHEKARU.....

Rayuwa ta canja mana, lallai dukan abunda Allah ya rubuta zai samu bawa babu makawa sai ya sameshi, lokuta da dama muna son abu sai ya zamo ba alheri ba ne a garemu wani lokacin kuma mukan ki abu kuma ya zama shine alheri a garemu, shiyasa ka bawa Allah zabi shine abunda ya fi domin shi zai zaba maka dukan abunda zai zama alheri a gareka ko kuwa kai kana ganin kamar ba alherin ba ne.

Kaddara data rubuta cewar ni matar Jibril ce a karo na biyu ita ce ta sake rubuta min farincikina da jindadi a gidansa, abunda ko da a mafarki aka cemin zan yi rayuwar jindadi da farinciki a gidan Jibril ba zan yarda ba amman yau gashi ina ganin kamar ma nafi kowa ce mace dace da mijin aure, you deserved happiness shine a abunda yake yawan fada min kuma yake ta kokari wajen ganin ya faranta min a rayuwata. Lallai Jibril bango ne shafi kuma jigo a rayuwata majinginata mai share hawayena a duk lokacin da kuka ya tunkaroni.

Bayan yankewa Siraj da abokan ta-addacinsa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso bamu da sauran fargaba ni da Jibril, ba ma kamar yanzu da hankalina ya kwanta sosai ganin cewar Zinatu ta yi aure, macen da take barazana ga rayuwata da kuma ta miji, irin rayuwar da nake a gidan mijina rayuwace da ko wace mace mai aure zata so kasancewa a cikinta, domin kuwa Jibril yana sani na manta da damuwata a duk wani fargaba da yake tare da ni, a da na yi tunanin rasa Yar'uwata Habiba da na yi da kuma Mahaifina farinciki ba zai sake ziyarta ta, ashe shirme na ke ta yi Allah ya tsara min wani jindadi da farinciki a gidan Jibril. Wani lokacin na yi dariya idan na tuna irin kiyayyar da na nuna masa ko kuma na ce irin soyayyar da na yi da Bilal wacce na ke ganin kamar idan babu shi babu farinciki a rayuwata, lallai yan karon magana sun yi gaskiya da suka ce karshen kiyayya soyayya domin kuwa ni da Jibril a yanzu kamar mu hade junanmu muke wa ma zai ganmu a yanzu ya zaci mun taba wata rayuwar ta bakinciki da kiyayyar juna.

Lokuta da dama na kanyi ma Allah godiya akan zabin da yayi min na auren Jibril sama da Bilal domin kuwa a yanzu na gane irin tazarar dake tsakaminsu da kuma irin rayuwar farinciki da jindadi da Bilal yake ciki, domin shi ma na samu labarin irin rayuwar jindadin da yake da matarsa tun bayan da kama aiki a kamfanin hakar man fetur na dangote dake Lagos, wata kila da ni ya aura da mahaifiyarsa ba ta barmu munyi zaman aure kamar yadda ta barshi yana zaune da matarsa a yanxu ba.

Na kanyi kokarin taimakawa a duk gurin da na ana bukatar taimako domin kuwa a yanxu na fahinci yadda rashi yake da kuma shiga halin rayuwa, duk a yanxu muna cikin ni'imar Allah Al-hamdulillah. Inna ma a yanxu ba zaka ganta ka ce ita ba ce, domin sun tare da sabon gidan da Jibril ya siya musu, duk wani wulakanci da halin ko inkula da familyn suke nuna mana a yanzu ya wuce mu ne kan gaba a komai, ashe daman rashin yake sa ake wulakanta mu kamar marar galihu.
Bayan Haihuwar Nana Asma'u wato yata ta biyu da take bin Noor na sake haibuwar Bashir wanda na kira da Babana, sai kuma na sake haihuwar Fatima da Aisha, a duk lokacin da muka samu hutu mu kan kwashesu muje hutu Abuja.
Idan kuma muna sokoto ranakun Assabar da Lahadi sai na sa direba ya kaisu gurin Inna a can suke hutun sati, har bana son su dawo saboda hayaniyarsu. A ranar da muka samu hutun karshen shekara nasa ya kaimu Katsina gurin Hajiya Aisha wato matar margayi Alhaji Dahiru, ta yi mamakin ganinmu kamar yadda na yi mamakin halin da na sameta a cikin, da bakinta take fada min, zaman abuja ya gagareta saboda gadon da Alhaji ya bar masu ta soma business da shi tana zuwa har Dubai da china amman abun be karbu ba sai ya kare a yanzu ma babban danta ne yake dauke da ita sai taimakon da sauran yayanta nata suke kawo mata, na yi mamakin ganin har yanzu Salima bata sake wani auren ba wato autarta wacce ta kasance kawata a lokacin da nake gidan, na ji mutuwar aurenta tun lokacin da Hajiya Aisha ta so a hada Jibril da ita a lokacin da aurenta ya mutu. Kwanan mu biyu a garin muka koma garin Abuja gurin da yara suka fi jindadin zama.




MUSTAPHA POV.

A ko yaushe yana yi ma Allah godiya da ya bashi Jidda a matsayin mata, domin kula da soyayyar da take nuna masa, a yanzu yana ganin ko Nawwara ya aura ba zai sameta ba, shi kansa a yanzu ya zage dantse yana nuna mata kula sosai domin ko da wasa baya son bacin rai Jidda kamar yadda ita ma
bata son bacin ransa. Gudun wannan yasa ya nemi transfer aka maida shi Kaduna domin a ganinsa idan ya yi nisa da mutumen da yake ganin kamar barazana ne a rayuwarsa zai fi samun kwamciyar hankali, musamman ma Nawwara da ya kasa cirewa a zuciyarsa.

A Kano ta haifa masa Amina da Amal wato twins duka mata, a lokacin har baya iya misalta irin farincikinsa, a dole tasa suka tattara suka dawo garin sokoto da zama har yaran suka yi kwari duk da kasancewar can yake aiki sai dai yaje ya dawo.
Bayan yara sun yi wayo ya dauki matarsa suka koma Kaduna tare da mai ronon yara saboda rage mata aiki, ita kanta Jidda a yanzu take jin ta yi dacen abokin rayuwa, domin kuwa be rage ta da komai ba, irin soyayyar da yake nuna mata har sai ka zata ita ya fara so ba Nawwara ba. A haihuwarta ta biyu Nawwara ta so ta je amman Jibril ya hanata saboda yana ganin Mustapha a matsayin masoyinta, be duba aminta dake tsakaninsu da Jidda kirkiri ya hanata zuwa a tunaninsa idan taje can Mustapha zai ganta kuma a gidansa zata sauka, shi be ga dalilin da zai sa ya barta taje ba.
Babu irin fushi da fadan da Jidda batayi da Nawwara ba akan hakan domin ita a nata tunanin Nawwara ce ta ki zuwan ba wai Jibril din ne ya hanata ba, domin a yanzu tana ganin kamar Nawwara da Mustapha an zama yan'uwa ba dai masoya ba, domin tun aurensu da Mustapha be taba mata maganar Nawwara ba ko da wasa, idan ma ta dauko masa maganar abunda ya shafeta sai ya nuna mata baya so hakan yasa bata taba zancen Nawwara ko wani abunda ya shafeta a gaban Mustapha.

A lokacin da Nawwara ta haifi Aisha Mustapha be hana Jidda zuwa ba duk da yana bakin aiki a lokacin sai ya sa direban abokinsa ya kawota har sokoto domin ahi kansa a lokacin ta matsa masa da zancen gida, tayi marmarin gida. Bayan suna da sati daya ta dawo domin ya bukaci hakan, ita kuma bata son tsabawa matsa, kawayenta har zolayarta suke wai ta cika son mijinta da yawa, ita kuma ya nana musu cewar shi ma yana ji da ita ne, kuma ya san darajarta kamar yadda ta san tashi darajar.
A zamantakewar rayuwarsu abun burgewa ga ko wadanne ma'aurata abu ne mai wahala ka ji kansu ne, tana kokarin kare mutuncin mijinta Jidda bata daga cikin matan nan da zasu zauna suna fadin sirrin mijinsu ko kuma familysu wanda ya zama ruwan dare a yanzu, hakuri shine abunda ya gina gidanta kuma ya ingantashi, da kuma bawa juna shawarwari, tana saurin bawa mijinta hakuri idan ta bata masa rai ko da kuwa ita ce mai gaskiyar, idan ta ga abunda be mata ba ta kan fito ta yi nuna masa ko kuma ta masa magana sai ya gyara saboda gaba, shi ma haka yake mata idan ta bata masa rai ko da masa wani abun ba daidai ba ya kan fito ya fada mata. Basa kunlatar junansu da komai wannan ne yasa a kullum suke cikin farinciki da kaunar juna marar misaltuwa.



NAWWARA POV.

Rayuwa ta koya min abubuwa guda uku zuwa hudu, na farko shine hakuri wanda shine jigon komai da komai na rayuwa da kuma zaman duniya, na koyi juriya da kuma jajjircewa akan komai na rayuwa, akan yasa na kara tabbatar ayar nan da Allah yake fadin lallai ne bayan ko wane tsanana akwai sauki a tare da shi, sam ba zaka ganni a yanzu ka ce mi ce a wacan duniyar mai hayaki da gobara ba, har sai idan na bude maka shafin rayuwata.
Rauwa ta da koya min zama da mutane da iya rike sirrin, ba kowa mutum ba ne na kwarai kamar yadda Siraj ya ha'incin Jibril akwai kawayena na kwarai irin su Jidda da Salima, kawaye da a yanzu sun ce na ce muau aminar muna kiran junanmu da yan'uwan juna. Yar'uwata haka na rubuta a Number Jidda kamar yadda ita ta rubuta My Blood Sisi a numberta.

Wani lokacin idan na zauna ina tunanin yadda rayuwa ta zo mana ni da Jibril sai abun ya rika bani dariya da kuma mamaki, lallai abunda duk Allah ya so ga bawa babu wanda ya isa ya hana shi ko da kuwa duniya zata taru akansa ne, abunda kuma Allah ya rubuta zai sameshi sai ya sameshi no matter what. Hakika soyayya bata tsufa sai dai masoya su tsufa, ban taba yarda da wannan ba shiyasa kullum cikin kwaliyata na ke da yin duk wani abun da zai daukewa Jibril hankali, ban yarda akwai wata mace da zata iya daukewa hankalin mijina ba, sai dai ni na dauke masa hankali daga wasu matan, idan yana gida ina makkale da shi, domin yarana sun bude ido sun ganni tare da Abbasu so na abun mamaki bane idan na kwanta a jikinsa kamar yadda dukansu wani lokacin suke zuwa mu kwanta tare
mu tausheshi muna dariya.
Idan kuma baya gida to waya tana kunnena ina jin labarin duk wani abu da ya gani a waje, kamar yadda nima nake labarta masa dukan abunda na aikata a gidan matukar ba aiki yake ba. Sakwannin barka da safiya kan sun zame min kamar jiki dole ne kullum sai na tura masa a waya, ko kuma na rubuta masa a paper ma aje masa.
Goodnight massage kuma kullum sai na tura masa kamar yadda shi ma yake turo min, wa zai ga rayuwarmu a yanzu ya ce mune a wacan lokacin? Lallai na yarda Kaddara ta riga fata!


Kamar yadda aka rubuta a iv yau ce ta kama 23 ga watan November, yau ake daura auren Sakina da angonta wato Mahmoud, hakan yasa na tashi da wuri na yi duka aikina amman hakan be hanani yin latti zuwa gida ba domin Jibril ya yi rantsuwa ba zan bar gidan ba sai na gyara masa ko ina kuma sai na tafi da yara kamar yadda yake min a duk lokacin daya fuskanci bana son zuwa da yara gida. Ko da tara tayi na gama komai na yi ma yara wanka ni ma na yi. Aai dai ba mu shirya ba domin bana son au bata atamfar ankonsu tun yanzu kara su kara wasu tufafin da aka dinka musu na cin biki kamin mu isa can.

Muma tsaye harabar gidan gurin mota muna jiran fitowarsa ya aje mu gida domin direbansa baya nan yana can ana hidima da shi ni kuma ya ki yarje min na toka motata wai a ganinsa ban gwari yadda ya kamata ba, hakan yasa indai da yaransa zan je yawo baya bari na yi driving sai idan ni kadaice ko kuma ni da shi. Farar shadda ce a jikinsa ta karbeshi sosai kai ka ce ma shine angon, fuskarsa sai annuri take, yana ta kamshin turare. Kallo daya na yi masa na ji kaunarsa ta kara shiga zuciyata, hakan yasa na kasa dauke idona akansa har ya shiga motar ya yi mata keys.

“Wannan irin kallo haka barakkala Masha-Allah karki cinye ni”

Sai duk muka sa dariya har yara da suke bayan mota. Ni dai ban ce masa komai ba har muka isa gida yana aje mu ya wuce gurin daure aure da aka ce goma na safe za ayi. Mun yi biki lafiya mun kare aka kai Sakina Birnin Kebbi gurin da Mijinta yake aiki, kasancewar mai mata ne ta aura sai dai asalinsa shi ma dan sokoto.

Ranar data zagoyo Assabar babu kowa gidan sai ni da Jibril, a ranar muka sha soyayyar kamar wasu sabbin ma'aurata, washe gari shi ya girka mana abun karyawa domin ni ban tashi ba sai da rana ta fito. Haka muke a duk lokacin da yara basa nan sai abunda muka manta ne kawai bama yi amman ko wace irin kulawa da soyayyar na yi kokarin nunawa mijina kamar yadda shi ma yake muna min, muna jindadin zama da junanmu sama da yadda duk wani mai tsammani yake tsammani, ba mu da wata fargaba ko tunani a zama da muke da juna,muna karan junanmu da sunan da yayi mana dadi, idan kuma yana fushi da ni nasan irin sunan da yake min ka kaka da kakkani, ko ya kira da wani suna a cikin kayan girki, nima kuma na akan masa wannan lakanin kamar yadda yake min.
Al-hamdulillah a ko yaushe na kan yi ma Allah godiya da ya bani miji kamar Jibril domin ni da shi RAI BIYU ne bayan RAI BIYU da na rasa wato Habiba da kuma mahaifina. A yauzu a kullum ni nawa godiya ne a garin Allah.



___________________________

Al-hamdulillah nima na gode Allah daya nani ikon gama RAI BIYU Lafiya, duk da kasan ba kuso ya kare a haka ba ko kuma na ce a yanzu ba, ku gafarci idan akwai idan na bata musu rai tun farkom fara rubutun nan zuwa yau, ma gode da irin goyan bayan da kuka bani da kuma juriyar karanta lattafin da ba ayi editing ba.

Mu tara a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA yarinyar kauye kuma labarin kauye kuma labarin sarauta mai sarkakiya da ban dariya da kuma tausayi, sai dai shi ba Free ba ne kamar wannan, HAFSATU MANGA na kudi ne, kuma ina fatar zaku bani hadin kai kamar yadda kuka ba ni a wannan, da ma sauran da zasu zo a gaba.

Godiya ta musamman gareku Whatsapp people baki ba zai iya gode musu akan irin soyayyar da kuka nuna min a littafin nan, sunanyenku ba zai lisafu ba amman ina son ku san cewa Khadeeja Candy tana son ku so na hakika. Gaisuwa da yabo gareku Wattpad readers I really appreciate your votes your comments your support, thank you so much, I love you All fisabilillah.

Littafin nan Sadaukarwa ne gareki Asma'u My Asmee Allah ya bar kauna da zumunci mai dorewa har Aljanna.


Ga Mai son siyen Littafin Hasfatu manga wanda zaizo nan da one month Insha-Allah ba wato 2020 zai iya nemana ta wannan line 08036126660, ta layin zaku iya turo min gyara ko kuma shawara akan littafin RAI BIYU da ma wasu littafan da suka gabata ko kuma masu zuwa nan gaba, I thank you so much my fans without you guys there's no Khadeeja Candy 😍

LTTAFAINA MASU ZUWA

HAFSATU MANGA (Labarin kauye)
KILAKI (Karuwa)
HASKEN ANNURI (the light and darkness)
And many more....


Best regards 😍
Khadeeja Candy
One heart
One love.

#Don't forget to follow me and also add Hafsatu manga to your library, thank you all stay bless 😪🙌

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment