Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne, idan kika kashe Jibril da wane ido zaki kalli Noor? Anya Nawwara akwai imani a zuciyarki kuwa?”

Zubewa na yi kasan guiwoyina ina kukan da ban san ta ina yake fito min, kukan da ya hanani cewa komai har su Inna suka shigo sai Abbah ya juya ya fita bayan ya gaisa da su. Inna kamar jira take ya fita sai ta hau ni da masifa ranta a bace

“Karkar kuka kike Nawwara, da kukan jini zaki yi, ba sakike kike so ba? Bari Allah ya bashi lafiya zan sa ya sakeki kije ki auri Bilal din mahaifiyarsa ta yi ta gasa miki garwashi a hannu ba ma gida ba, mutumiyar banza marar hankali wannan hakin naki ba haline na mutanen kirki ba, kuma duk mai irin rayuwarki ba zai taba jindadin zama duniya ba, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne ko ke kin fi uban kowa ne, Jahila kawai ilminki ba shi da amfani Nawwara kin yi hasara jindadin zama da mutane indai haka zaki cigaba da rayuwa”

Babu bakar maganar da Inna bata fada min ba, ita da Mama Turai mutuwa ce kawai ban yi a gurin saboda kuka, amman har numfashina kokarin fita ya rikayi. Hakan be sa Inna ta tausaya min ba sai ma haushina da take ina kokarin rike mata zane ta buge min hannu ta fice a fusace, babu wanda ya tsaya ya saurari ni. Kuka na yi a gurin har sai da na gode Allah sannan na tashi na koma saman kujerar na zauna ba dan hawaye sun daina min zuba ba. Wata yar uwar Jibril ce ta shigo da kayan abinci ta aje sai ta dafani

“Adda Nawwara ki yi hakuri Yaya zai tashi Insha-Allah”

Uffan ban ce mata ba har ta fice, sai na maida kaina na kwantar jikin gadon na lumshe ido kaina na mugun ciwo kamar zai tsage.


JIBRIL POV.

Misalin goma da rabi na safe ya bude idonsa, ya dade yana gani dishi² sannan ya soma gani dai dai har ya gane asibiti aka kawo shi. A hankali ya maida dubansa gurin Nawwara da kanta ke kwance saman gadon idanuwanta a lumshe da alama bachi take amman sai shesshekar kuka take. Hannu ya kai ya shafa saman kanta, ya lumshe ido. Sai kuma ya kai dayan hannunsa ya cire oxygen din da ke bakinsa ya unkura cike da karfi hali ya tashi zaune, yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu.
Hakan ne ya farkarda Nawwara daga bachin da take suna hada ido sai taga abun kamar mafarki saurin mikewa tsaye ta yi sai ta rumgume shi tsabar jindadin ya farka be mutu ba, sai ta fashe da kuka.

“Ka yi hakuri Jibril ba zan sake ba, ban zata abun ya kai har haka ba”

Rumgumeta ya yi tsantsan a kirjinta ya lumshe ido, rabon da yaji irin wannan sukunin da sakewa har ya manta, a take ya ji sanyi a zuciyarsa har wani kuzari yana rabarsa. Saurin sakinsa ta yi tana share hawayenta.

“Bari na kira likita”

Sai ya rike mata hannu ya bude ido a hankali yana kallonta da bakinsa da ya yi fari ya bushe.

“Doctor be da abunda zai min Nawwara, ki ce likita na komai za a min a duniyar nan ba zan warkeba matukar babu kulawarki da sonki a kusa da ni, babu ciwon da zai rabeni matukar kina kusa da ni, na san ba nine wanda kika so but please stay with me ko da na dan lokaci ne, i feel like rayuwata ba zata tsawaita da har zan hanaki jindadin rayuwarki ta nan gaba i need you”

Dawowa ta yi ta zauna bakin gadon da yake zaune, hannunta na cikin na shi fuskarta kuma na zubar da hawayen, dayan hannunta tasa ta jimke hannunsa a tsakiyar hannayenta.

“Har yanzu akwai son Jibril a zuciyarki, ki rantse min da Allah baki son Jibril, ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki Jibril take so ko da na aureki gangar jikin kawai na aura. Haka Bilal ya fada ranar ganina na karshe da shi saboda ya ga son ka a idanuwana, karya na ke na ce bana son ka Jibril kawai na kasa manta abunda ka yi min ne, amman yanzu komai ya wuce i promise you ba zan sake yin wani abun da zai tashi hankalinka ba”

Hawayene suka zubo masa hawayen da shi ma kansa be san na minene ba. Hannunsa ya dauka ya dora saman nata.

“Fada min wani abu Nawwara, ina jin kamar ba ke bace, wata kila saboda na kusa mutane ne kike so na yanzu”

“Daman can ina son ka nothing changed no one can take your place, da ace yau na rasa ba da na wayi gari cikin wata duniya mai rudani da rikitarwa, ban tabbatar da ina son ka ba sai da na ganka kwance a saman gadon nan, Jibril i love more than I did before”

Ido ya tsura mata yana ta kallonta, gaskiyar zancenta yake karanta a idanuwanta, kawai ya kasa yarda cewar Nawwara din ce, abunda ya dade yana jiran jin daga bakinta yau ya jishi. Hannunshi ta daga ta kai gefen kunci ta lumshe ido.

“Am sorry”

Ta furta cikin kuka. Sai ya matsa kusa da ita ya sumbaci goshinta ya sumbanci saman hancinta ya sumbanci lips dinta, sannan ya rumgumeta shima ya lumshe ido kamar yadda na ta idon suke a lumshe....
[11/22, 9:43 AM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤*

Wattpad @KhadeejaCandy


6⃣0⃣

Jihadin da na yi ba duk mace ba ce zata iya yinsa, zama da mutumen da ya nuna maka ba kaunarka, yanzu kuma ya dawo yana son ka kamar ya mutu.
Annabi ya yi gaskiya da ya ce mu yi so kadan kuma mu yi ki kadan domin wata rana masoyinka ya kan iya zama makiyinka ko kuma makiyinka ya zama masoyinka, har ga Allah ya yarda Jibril yana so na kuma i believe without me there is no Jibril. But for what Jibril did to me is unforgivable pain, hada hotona da hoton wani namiji shine abunda na ke gani a duk lokacin da na kalli fuskar mijina.
Ina cikin hada masa tea na ji hannayensa zagaye da kunkuruna ya dora fuskarsa saman wuyana yana goga min hancinsa a gefen fuskata.

“Karki wahalar da kanki gurin hada tea nan ba zan iya shan sa a yanxu ba”

Ya fada saitin kunnena kadan-kadan kamar mai rada.

“Saboda me?”

“Saboda ban wanke bakina ba kuma ban rama sallah da ake bina ba, kara ki bari kawai har muje gida”

“Fine zan je gida da kaina sai na dauko maka brush din da toothpaste”

Kokarin juyowa na ke amman sai ya ki bani dama saboda ya ji dadin yadda muke tsaye a haka.

“Kar wani ya tarar da mu a haka fa”

Ya sakeni sai na juyo na kalli fuskarsa yana murmushi sai ya dora hannayensa saman kafadata ya hade goshinsa da nawa.

“To miye a ciki haramun muka aikata?”

Har na bude baki na yi magana sai a turo kofar dakin aka shigo hakan yasa dukanmu muka tsargu ganin Abbah ne, bama kamar ni da nafi jin kunya, domin shi nuna yayi kamar be yi komai ba ya zauna saman gado yana gaisheshi.
  Nima gaisuwar na mika masa ga mamakina sai ya amsa min sai dai fuskarsa babu yabo ba fallasa. Kofa na nufa da zimmar fice sai ya kirani hakan yasa na juyo ma dawo still kaina na kasa.

“Ki yi hakuri da abunda na fada miki, raina ne kawai ya bace amman dukan wani furuki da na yi agareki bana da nufin aikata ko daya kawai dai na ce ne dan an tsorota ki”

“Ba komai Abbah”

Na fada sai Jibril ya kalleni ya kalleshi

“Wani abun ne ya faru?”

“Lokacin da kake unconscious na fada mata masu Maganganun da basu da ce ba, saboda na yi tunanin ko da hannunta a abunda ya faru da kai ne”

“Aa ita ma bata san abunda ya same ni, domin na turata kitchen ta dauko plate kawai sai na ji jiri ya dibeni ban sake sani inda nake ba”

Abbah ya juyo ya kalleni.

“Amman Nawwara shine baki fada ba, kika kyale ina ta miki fada?”

“Ba lallai ne ka saurareni a lokacin ba, amman yanzu komai ya wuce, bari na je na dauko maka brush din”

Na karasa ina kallom Jibril sai ya kada min kai.

“Amman kisa direba ya kai ki karki hau Napep”

Da kai na amsa masa sannan na fice zuciyata cike da jindadi da kuma rashin jindadin da ban san na minene ba. Harabar asibitin na nufa inda aka faka motoci a nan na samu direansa da ban san sunansa ,bayan mun gaisa ya tambayani mai jiki sai na ce masa ya kai ni gida. Gida bayan na shiga shi kuma yana mazaunin direba kamar kullum.
  Ko da a muka isa gida wato sama road ina hawayen da bansan na minene ba. Bayan ya faka motar na bude na fito ina share hawayena na nan na samu damar kallon wani bangare na gida, irin tsarin nan na manyan masu kudi gurin faka motoci an kawata ko kna da furanni masu kyau da daukar hankali.  Babbar kofar shiga falon kuma tana da stairs biyar an kawata gefen karfen stairs din da furani kamar gidanjen turawa ko kuma na ce na indiya.
  Ina shiga na samu falo kamar yadda na barshi, sai dai komai na falo fari kamar fentin gidan, ya kawata falon da hotuna na da na Noor sai kuma na Abbah da na Mahaifiyarsa, amman babu nasa ko daya. Lokacin da na shiga bedroom sai na manta da abunda ya kawo ni gidan kawai na hau gyara dakin saboda ya bace da jinin da Jibril ya amayar jiya da dare.

“Allah ka bani ikon jure komai”

Ya roka yayinda na ke dauke kazar jiya da har ta soma yauki, bayan na gyara ko ina na shiga bandaki na hada ruwa na yi wanka, sannan na fito na shafa mai na dauki atamfa maroon color na saka, gaban madubi ya zo na tsaya ina kallon kaina kitson da aka min ya kwanta a kaina sosai gashina ya yi baki kuma ya sauko har gadon bayana. Kamar a mafarki na hango mutum ta cikin madubi ya doso inda yake fuskarsa dauke da murmushi, saurin juyowa na yi na kalleshi.

“Ya aka yi ka zo”

“Baki ji mota ba?”

Ya fada yana muna min window.

“Sam ban ji ba”

“Hankalinki yana iya?”

“Yana can asibiti gurin mijina”

Goshinsa ya hade da nawa ya kama hannuna na dama ya shinsshina ya lumshe ido.

“Ya akayi aka barka ka fito? Na san dai babu likitan da zai sallami mai jiyanci irin a yau din na asibitin bayan kuma jiya da dare aka kai ka”

Be amsa min ba sai na ji kafarsa saman tawa yana goga min ita a hankali.

“Su Momi suna waje suna jiranki”

Ya furta sai ya sakeni ya yi baya baya yana murmushi har ya isa bandaki, sannan ya bude ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan na dauki mayafi na ya rufe kaina na nufi falo.

JIBRIL POV.

Zaune yake ruwan shower na dukan kansa, sai dai hakan be hana hawaye zubo masa ba, kuka yake kukan da be san na minene ba farincikin dawowar Nawwara a duniyarsa ko kuma bakincikin kwanakin da yake ji a jikinsa su suka rage masa, wanda hakam ba zai ba shi damar rayuwa irin wacce yake so a tare da ita mai tsowo ba?

Bayan na gama wanka yaje gaban madubi ya wanke bakinsa sai ya bude cabinet ya dauko maganinsa ya sha, sannan ya juya ya fito daga bathroom din. A gaggauce ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan na fashe jikinsa da turare ya fito falo. Hajiya ya samu wato Step Mother dinsa tare da sisters dinsa a zaune suna ta fira da Nawwara sama sama.
  A ranar wuni suka yi baki daga masu zuwa ganin amarya wandanda  ba su san an kwantar da Jibril asibiti ba, sai masu zuwa diba shi idan sun je asibiti ace musu ya dawo gida. Abbah dai tun asibiti suka yi sallama da shi Hajiya ce kawai ta jira taga jikinnasa kamin ita ta kama hanyar abuja gobe.

NAWWARA POV.

Sai kusan isha'i sannan kowa ya watse, muka shiga gyara gidan ni da Jidda da Sakina, sai da muka gyara ko ina muka masa tas sannan muka kunna turaren wuta gidan ya dauki kamshi.

“Gaskiya Nawwara kin da ce, ga mijinki yana son ki duk abunda kike so shi zai miki, yan uwansa ma ba baya ba suma na ga suna son ki”

Ta fada tana karewa falon kallo. Ni kuma na yi murmushi na ce

“Ni ko kin ga duk wannan dukiyar bata gabana, na rasa dalilin da zai sani na ji dadin zama a gidan nan”

“Aiko kara ki fara ji tun yanzu, domin wanda kike takama da shi ya yi aure rana daya da ke”

“What? me kike nufi”

“An daurawa Bilal aure da wata yar'uwarsa, Mamansa ta ce ba za a daga ranar ba tun da kowa ya san an saka rana kara kawai ya auri yar'uwarsa wata yarinya ce da ake riko a gidan”

Na ji babu dadi, dan nasan ba dan yana son ta ne ya aureta ba sai dan kawai mahaifiyarsa ta cilas masa.

“Hakika ta yi dacen miji mai kawaici da sanin ya kamata, miji mai gudun kukan matarsa mai son duk wani abu da zai faranta rai”

“Kuma ba ki ganta ba, ta ninka ki kyau sau ashiri”

“Ina ruwana”

Na fada ina harararta, ita kuma ta sa min dariya, sai da Jibril ya dawo sannan suka fice suka barmi cikin rashin dadin rai. Ina ta kokarin kawai da abunda yake zuciyata gudun kar Jibril ya zarge ni ko kuma damuwata ta saka masa damuwa, iya inda far'ata take na yi kokarin nemota na yabama fuskata. Bayan na fito wanka na hada masa nasa ruwan na fito daure da tawul da kuma Hijab a jikina. Tun da na fito daga bathroom din ya sakarmin ido yana ta kallona har na zauna bakin gado kamar yau ya fara ganina. Hakan yasa na soma tsarguwa.

“Ga ruwan wanka can na hada maka”

Murmushi ya yi sai ya bar jikin kofar dakin da yake tsaye ya nufoni ya zauna daf da ni ya kawo fuskarsa kusa da tawa har muna iya juyo mumfashin juna. Jin bakinsa daf da nawa yasa na runtse idona na dauki numfashi ina sauraren yadda yake watsa da yatsansa a gefen fuskata.

“I love you”

Ya furta muryarsa can ciki kamar marar kuzari, ji nayi yana huramin iska kamshin sweet candy a hankali daga saman goshina zuwa bakina. Lokaci daya na daina jin iska hakan yasa na bude ido sai na gashi tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Hannayensa yasa ya tasheni tsaye ya rumgumeni tsantsan a kirjinsa.

“Ina son ki sosai Nawwara”

Ya furta yana kokarin ciremin Hijab din da ke jikina, ni ko gabana sai faduwa yake, hannuna ya rika ya dora saitin zuciyarsa, wani irin bugawa na ji zuciyarsa na yi da karfi har sai dai na tsorata, Dagowa na yi na kalleshi sai ya sauke idonshin cikin nawa yana min wani kallo mai wuyar fassara, hannunsa ya kai ya kama fuskata ya soma sumbantar bakina. Kasa kasa na ke saboda na kwaci kaina shi kuma sai biyoni yake hakan yasa muka fada saman gadon a tare. Dariya ya soma yi kamar yadda nima na ke dariyar, kunya tasa na yi saurin juyowa na kife fuskata cikin Bedsheet, sai ya dora kansa a bayana yasa yatsansa yana wasa da wuya. Sai da ya sumbanci kunnena sannan ya tashi daga bayana da dora kansa.

“Babe-Naj gaskiya wankan nan tare ya kamata mu yi shi”

Ya fada yana kokarin jan tawul din da nake daure da shi, hakan yasa na yi saurin sauka saman gado ina zare ido.

“Na fa yi nawa wanka kuma ka gani”

“Gaskiya ban gani ba”

Ya dosoni gadan-gadan hakan yasa na haye gado na koma can karshe ina ta kokarin rike tawul din dake son subucewa daga jikina.

“Ki sauko nan kawai Hajiyata”

“Aa gaskiya haka kawai na yi abuna kuma ka ce sai na sake wani”

Na fada ina turo baki, sai ya yi dariya.

“Fine”

Kokarin hawan gadon yake ni kuma na sa masa ihu.

“Tsaya tsaya zan sauko, amman Wallahi na yi wankan kwarai”

Tsayawa ya yi na sauko da kaina fuskata kamar na fasa kuka ina daga masa na ce.

“Dan Allah karka cilasta min wanka tare da kai Wallahi na yi wanka na kwarai”

Kyaleni ya yi har ya juya sai kuma ya juyo da sauri ya janye tawul din dake jikina, rudewa na yi na rumgume shi ina kokarin fashewa da kuka. Shi kuma sai ya fashe da dariya ya duka ya dauko tawul din ya daura min.

“Yi hakuri”

Kuka na ke da gaske har da hawaye domin na ji haushi kuma na ji kunya sosai musamman rumgumar da na masa. Sai ya nufi bathroom yana ta kyalkyatar dariyar mugunta kamar ba shi ba, ni ma har na soma dariyar kaina.
Sai da ya shiga bandakin ni kuma na je na kulleshi daga waje.

“Sai ka fadi wanda ya aikeka ka yi min haka nan ko kuma ka kwana a bandakin nan”

“Yi hakuri idan na fito sai ki rama”

“Ni ba zan rama ta yadda ka yi min ba, sai dai ta wannan hanyar”

“Ashe ke matsoraciya ce ma, karki yarda na fito sai na miki abunda ya fi wannan yarinya”

“Waye yarinya?”

“Ke mana, kin san da auren kauye aka min da yanzu na haifeki”

“Sannu Baba”

Na fada ina dariya, da gangan na ki bude shi har na shirya cikin kayan bachi na nufi falo inda ya aje ledodin da ya shigo da su dazu. Zaunawa na yi a dinning din na ci abincina sai da na koshi sannan na bude freezer na dauko ruwa na sha.

“Al-hamdulillah”

Na furta ina mamakin yadda na soma sakewa a gidan kamar ba ni ba, ina kokarin maida ruwan na ji hannayensa kan kwankwasona, ba shiri na saki goran ruwan ya juyo da sauri ina ihu.

“Ya aka yi ka fito”

“Aljanine ni, waya ce ki ci amin abinci”

Shi ma kayan bachi ne a jikinsa irin kalar nawa sai dai na shi na maza ne nawa na mata. Hannayensa yasa ya daukeni kamar wata yar baby, ni kuma na dora hannayena saman wuyansa.

“Mrs baki da kunya, jiya fa aka kawo ki gidan nan amman har sakin tawul kike gabana”

Na yi saurin boye fuskarta a kirjinsa ina dariya.

*RAI BIYU...♥🖤*

Wattpad @KhadeejaCandy


6⃣1⃣

JIBRIL POV.

Yana zaune saman kujerarsa yana juyawa wayarsa ta yi ringing, yana duba mai kiran yayi dariya, da gangan ya ki dauka domin a yanzu ba zai iya da rigimarta ba, idan ya dauka ba zai tsira ba idan kuma ya dauka still dai masifar ce zata masa. Haka ta jera masa kira har uku sannan ya dauka.

“Kina ta damuna da kira kuma kin san ina tare da budurwata”

“Au haka ma zaka ce min?”

“To kin fi son na yi miki karya?”

“Kana ina?”

“Ina gurin budurwata, ba ke kika ce karna dawo ba?”

Ya katse wayar, shi kuma ya mike tsaye yana dariya ya fice daga office din, cike da so da kaunar matarsa ya fito daga lifter kallo daya zaka masa ka fahimce yana cikin farinciki, rayuwa yake da matarsa irin rayuwar da be tsammani zai samu daga gurin Nawwara ba, irin son da take nuna masa be tsammaci samunsa a gunta ba, rayuwa suke irin rayuwar da ko a littafi aabu ce mai wahalar samu.
A yanzu ya zama mutum kawar kowa ciwon da yake jin kamar ba zai barshi ba, gashi yanzu ya samu sauki tun bayan jinyar da yayi a india, he can now read Quran daga fatiha har bakaqa and Nawwarar tana tare da shi da Noor what else zai roka bayan godiya ga Ubangijinsa?

A masallacin da ke unguwarsu Sama road ya yi sallah la'asar sannan ya shigo cikin gida, a hankali ya yi parking dan baya son ta ji tsayawar motarsa. Yasan by this time Noor yana makarantar islamiya dan haka Gimbiyarsa ce kawai a gidan, yana fitowa daga motar ya leka window kitchen hangota da yayi tsaye gaban fanfan yasa shi jindadi sai ya dawo kofar shiga falon ya tura kofar a hankali ya shiga, amman hakan be sa ya tsira ba, sai saukar ruwa ya ji a jikinsa.

“Haba Madam miyasa baki min adalci babu ne?”

“Adalcin kenan kai waya ce ka jikani”

“Amman dai dazu da kayan bachi a jikinki na jikaki, ni kuma shadda ce kuma gurin zan ce zan je fa”

“Fade kawai kake amman babu wata mace da zata kulaka”

“Inji wa? Kin ga yadda ake rushing din na kuwa kai ni fa handsome guy ne irin na bugawa a jarida ma”

Ta ji haushi har da zuba masa ragowar ruwan gorar a jiki.

“A haka din duk ka wani tsufa ai ni kadai zan iya da kai”

“Ko yanxu ina driving wata har kashe min ido daya take”

“Karuwa ce”

“Wane irin karuwa kuma? Kin ganta kuwa kyakkyawa ga dogon hanci ga karamin baki gata fara kuma ga katon ciki haihuwa yau ko gobe sai shegen matsifa ta fitini kowa ta hana kowa sakewa”

Ta jefa masa gorar ruwan tana ƙaƙarin kuka ita ala dole ta yi fushi da gaske, yayi saurin kai hannu ya rika ya juyo da da ita sai ya risina ya kara kunnensa dai dai cinin cikinta.

“Yi hakuri Babe na fada min ya Baby yake?”

“Ban sani ba”

Ta fada tana kokarin ture kansa daga cikinta.

“Ni dai Allah yasa karki haifo min fitininayar yarinya, Wallahi Nawwara kin cika masifa”

“Au haka ma zaka ce”

Ya yi saurin rufe bakinsa ya mike tsaye.

“Mantawa na yi”

Ya jata ya zauna saman kujera sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa.

“Fada min miye na wannan fushi? ”

Ta kara turo baki.

“Baka siyo min komai ba”

“Daga gurin budurwata na ke kin san kuma...”

Be gama ba ta ja masa kunne har sai da yayi yar kara.

“Wace budurwa kuma ba zaka daina jana ba?”

“Wallahi ba wasa na ke miki ba, akwai wace ta dauki min hankali sosai, bana son jin muryar kowa sai nata bana son ganin kowa sai ita sunan kawai idan na ji raina fari yake”

“Nawwara ce”

Ya fada da fuskar zolaya sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume suna dariya. Hannunsa ya kai ya shafa cikin ya lumshe ido.

“Ban tsammaci zan kara samu wani dan ba bayan Noor but look at us right now”

Murya kasa kasa yake mata maganar kamar mai rada, har kasan ruhinsa yake jin son Nawwara da duk wani abu da ya dangance ta, more especially ma cikinsa da take dauke da  shi a yanzu bayan ya cire rai daga haihuwa tun bayan a abunda ya faru da shi amman gashi yau Nawwararsa tana dauke da cikinsa.
A yanzu ba shi da wani buri da tunani sai na Nawwara, ko da wasa baya son abunda zai bata mata rai, idana yana zaune tare da ita a gida har baya son fita ita kuma ya yi nisa da ita suna makkale a waya, tunaninta ta dinga addabarsa kenan kamar yadda ita tuaninsa yake hanata sukuni, lokatu da dama idan zai anbaci sunan wata sai ya kira Nawwara shi da kansa wani lokacin yana mamakin kansa, a lokacin da ya fahimce cewar tana da ciki sai ya kasa sukuni kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda murna da jindadi.

Yau ma kamar kullum Jibril be sake fita ba tun da ya dawo, tare suka karasa girkinsu na dare,  around six direba ya dauka Noor daga islamiya, da gudu ya shigo yana sallama tare da fadin.

“Daddyna ya dawo”

Yana shigowa Jibril ya safkeshi ya yi sama da shi.

“Oyoyo dan daddynsa”

Dauke da shi ya shiga bedroom dinsa wato dakin Noor dakin da aka kawata da kayan wasan yara da duk wani abu na jindadi.

“Ka cire uniform ka zo muje masallaci an kusa sallah”

Ya fada yana direshi saman gado.

“Okay Daddy”

A nan jibril ya juya ya shiga bedroom din Nawwara, a gaban madubi ya sameta tana gyara kayan da ke gurin, a jikin kofa ya ya jingina yana kallonta har sai da ta kammala sannan yaje ya rumgume ta baya ya dora kansa saman wuyanta.

“Ke baki gajiya da aiki ne? Ba na ce ki bari sai gobe mu gyara ba”

“Haka kake ce min tun shekaran jiya ai, Noor ya dawo”

“Eh ya dawo yana dakinsa uniform din islamiya zai cire”

“Ya cire ya zo

Please Login or Register in order to submit comment