Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ta yi ma Habiba, Sakina da Jamila sannan suka maido min da wayar.

“Kin rasa RAI BIYU masu muhimmanci Nawwara mutuwa mai ɗaci , kin rasa Abban Noor yanzu kuma Babanki Allah ya baki ikon ɗaukar wannan lamarin”

“Amin Salima na gode”

“Inshallah idan na dawo Nigeria zan zo har nan na yi miki gaisuwa”

“To Allah ya yarda”

Daga haka muka yi sallama, na amsa mata da to ne kawai ba dan na gamsu zata zo ɗin ba, duk tsawon zaman da muka yi da ita bata taɓa tako ƙafarta sokoto ba ai ba zata taɓa zuwa ba.
Da gudu Noor ya zo gurin yana ƙoƙarin karɓar wayar.

“Momy waya baki waya? Momy kira min Gwaggota Murja kin ji”

Haka yake idonsa idon ganin waya, baya da magana sai ta a kira masa Murja wato Ƙanwar mijina wacce ya shaƙu da ita sosai.

“An ya ma sun ji maganar rasuwar baban ku kuwa?”

Maganar Inna tasa na ɗago kai na kalleta.

“Ina zasu ji tun da ba a nan suke ba kuma babu waya a lokacin”

“Ya kamata dai kan ki faɗa mata”

“Bari na mata please Call me dan ba ni da kati gaskiya”

A take na aikama mata please Call, ko minti biyu ba a ƙara ba sai gata ta kirani, mun gaisa sosai sannan na bata Inna, ita ta labarta mata cewar Baban mu ya rasu, ta shiga ɗimuwa da kiɗima sosai, har da kukanta kamar Babanta ne ya rasu.
Bayan ta yi min gaisuwa ta faɗa min zata shaedawa sauran ƴan'uwan margayi Sadiq zasu zo har sokoto su yi min gaisuwa, duk ƙoƙarin dakatar da ita da na yi akan zuwan sai ta nuna min sam ba zai yiyu sai ta zo, ai daga sokoto zuwa Kebbi ba wani nisa ba ne. Sun daɗe suna waya da Noor sannan bashi yaranta suka yi magana sai ta kashe.

Takwas da rabi wayar Bilal ta shigo, ina ɗauka ya shaida min yana waje. Sai da na faɗawa Inna sannan na tashi na saka Hijab ɗina na fita. Jikingine da ƙofar gida na same shi, ina masa sallama ya amsa fuskarsa da murmushi har wani ƙyali take.

“Nawancy”

“Bilal”

Sai yasa dariya.

“Ina jin daɗin ki kira sunana yana mugun daɗi a bakinki”

Na yi murmushi ina rausayar da kai. Bayan mun gaisa ya bijiro min da fira cikin har da zancen marin da na yi Mustapha, sai na nuna masa ya yi min ba dai-dai ba ne shiyasa. Sai tara da rabi muka yi sallama.

WASHE GARI....

Yau kan ba laifi dukanmu mun tashi cikin walwala, Sakina da Jamila tuni suka wuce makaranta, Habiba ma shirin makarantar ta ke, ni kuma ina gyaran gida, Inna kuma na ɗaki tana bachin safe.

“Nawwara canjin kuɗin Koko yana nan ƙarƙashin fillo, Inna ta ce a siye ruwa”

Cewar Habiba tana tsaye riƙe da littafan makarantarta.

“Yau Fanfan ba zai zo ba ne hala?”

“Yau kwana biyu be zo ba, ruwan da muke amfani da su sun ƙare, ƙara a siya da wuri idan ma ya zo kin ga kaɗan kawai za mu ɗebo”

“Allah ya bada sa'ah”

“Amin na tafi”

Fitarta da kamar minti biyar, wata matashiyar yarinya ta shigo sanye da dogowar rigar atamfa da wani minafukin gyale a kafaɗa, sallama ta fara yi na amsa mata.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikissalam”

“Sannu ina kwana?”

“Lafiya ƙalau”

“Dan Allah nan ne gidan Musa Kafinta?”

“Nan ne, lafiya?”

“Lafiya ƙalau, Sunana Shafa Ibrahim ni ƴar jarida ce ina aiki da jaridar Arewa a yau, tare da abokin aikina na ke ina son mu tattauna da iyalansa ne akan abunda ya faru”

Ta ƙarasa tana miƙa min katin shedarta.





CANDY ✍️
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy

RIJF Mama A'i, ke da kika tafi ba ki yi sauri ba, mu da mika rage ba mu yi nawa ba. Allah kasa mutuwa ta zama hutu gareki Allah ya miki rahama ya gafarta miki kurakuranki. I will never forget you. Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe.

1⃣2⃣

Na kai hannu na karɓi cati na duba, sunanta ne da kuma hotonta a jikin catin hakan ya tabbatar min da cewar lallai ƴar jaridar ƙwarai ce. Na mayar mata da katinta.

“Ba mu san komai a kai ba, waya faɗa miki nan gurin kuma?”

“Jama'a ne suka kwatanta min, kuma na tabbatar min da cewar ƴan sanda suka duki margayin har ya mutu”

Na nuna mata ƙofar fita raina a ɓace.

“Fita ki bar mana gida, mutanen da suka labarta miki abunda ya faru ki je can su ƙarasa miki, mu bamu san komai ba”

“Haba Baiwar Allah...”

“Ki fita Wallahi ko na sa taɓarya na fasa miki kai yanzu”

Da gudu ta juya ta fice daga gidan. Ni kuma na cigaba da aikina zuciya na zafi har na gama gyara komai, ciki na shiga na samu Inna har lokacin tana bachi Hijabina na saka na ɗauki kuɗin da suke ƙarƙashin filo na fita neman mai ruwa.

Karo na ci da Dpo dake tsaye jikin motarsa yana kallon ƙofar gidanmu, ban gama tabbatar da shi ɗin ne ko a'a ba saboda yau a cikin kayan gida yake.

“Assalamu Alaikum Malama”

A maimakon na amsa masa sai kawai na watsa masa wata muguwar harara.

“Ni ba gurinki na zo ba, matar gidan na ke son magana da ita”

“Bachi ta ke”

“Ki taimaka ki tashe ta kuma ki nema minlH izinin shiga cikin gidan”

“Saboda?”

Ya gyara tsayuwarsa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Na ga dai ke ba ƴar jarida ba ce, be kamata ki tsare ni kina min irin waɗannan tambayoyin ba, beside ni ba gurinki na zo ba gurin Inna na zo”

“Gida mallakinmu, mahaifiya bachi take baƙincikin kashe mahaifinmu da ka yi take ragewa saboda hawan jini”

Ban tsaya jiran abunda zai ce ba, na cigaba ta tafiyata. Sai ya zagayo ta gaban motarsa ya sha gabana, cikin ɗaga murya ya fara magana.

“Miyasa kuke rayawa zuciyarku cewa ni na kashe mahaifinki? Mi mahaifinki ya yi min da zan kasheshi? Idan na kashe shi wace riba zan ci?”

Nima cikin zafin rai na zaburo masa.

“Saboda zalincin ƴan sanda, yayarka ta laƙaba masa sata bayan kuma be sata ba, kuka yi ta dukansa har sai da kuka kasheshi akan kawai sai ya amsa laifinsa, wannan ba halinku ba ne? Saboda yayarka tana taƙamar kai dpo ne yasa kuka wulaƙanta mana mahaifi cika tozarta shi sannan kuka ɗauki gawa kuka kawo mana, yanzu kuma kana raina mana hankali har kana wasa da hankalinmu”

Ya matso kusa da ni ya nuna ni da yatsa yana magana cikin jin zafin kalaman da na yi masa, har haƙoransa na ƙasa na haɗuwa da na sama yana cizonsu tare da zaro min ido.

“Karki sake saka bakinki a akan aikina, karki sake yin furucin akan abunda kika jahilta, i hate nonsense, na zo nan ne dan na faɗa muku karku kuskura bada bayanin mutuwar mahaifinku ga ƴan jarida”

Na yi baya-baya ina hawaye, tare da murmushin da ya fi kuka ciwo.

“Kamin ta zo nan ashe sai da ta bi ta gurinka, ka yi nasara ban faɗa mata komai ba, amman yanzu kan ni zan tara ƴan jarida da kaina na labarta musu irin zaluncin da kuka mana, wato so kuka a rufa muku asiri kar kowa ya ji ko? Ta yadda muma zaku samu damar ɓatar da mu, Wallahi Allah ba zai barku ba azzalumai macuta-”

Ya ƙara matsowa kusa da ni har sai da na matsa baya.

“Ki tara ƴan jarida, ki faɗa muku ƴan sanda sun kama mahaifinki sun masa duka har ya mutu, za su tambaye ki dalilin hakan, kuma ki faɗa muku komai karki ɓoye, ni da ke za a ga waye zai ji kunya, idan ba ki yi haka ba to baki haifu ba!”


Yana kaiwa nan ya haɗa hannunsa na dama da na hagu ta taɓa saitin fuskata, har sai da na rufe ido. Sannan ya buɗe motarsa ƙirar 406 ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama, ko da na ɓuɗe idona ƙurar motar kawai na gani hawaye ya sauko daga idona, lallai wannan shi ne a dakika a hana kuka, kuma a mareka a ƙwace maka jaka!

Kasa zuwa kiran mai ruwan na yi saboda kuka da ya ci ƙarfina, na koma cikin gida da sauri. Bana son na tashi Inna balle har ta ga hawayena hakan yasa na shige ɗakinmu na kwanta saman tabarma, na ci kuka na sai da na ƙoshi sannan bachi ya yi gaba da ni.
Motsin shigowar su Habiba ne ya tasheni daga dogon banchin da ya ɗaukeni, babu komai a mafarkina sai wacan tashin hankalin da ya faru, Baba ne kawai na ke ta gani sai kuma irin zamantewar da muka yi a gidan kamin rasuwarsa.
Ko da na fito na samu Inna ta farka har suna fira da Habiba ma da ke cire safa.

“Nawwara kin tashi?”

Inna ta tambaya tana kallona, sai na zauna bakin ƙofar ina amsa mata.

“Eh ashe rana ta yi”

“Tun ɗazu su Noor suka dawo na ce kar ya tasheki kin gaji da yawa, ƙara ki samu bachi ki ɗan huta”

Kallo ɗaya Habiba ta yi min ta ɗauke kai, kamar ba ta ganni ba, hakan ya karatar da ni da akwai wani abu a ƙasa, sai dai ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauki bula na shiga banɗaki, bayan na fito na yi alwala na shiga ɗakinmu dan Sallah.
A ciki na sameta tana ɗaura zane, naje kusa da ita na tsaya.

“Habiba kamar akwai abunda ya ke damunki?”

Ta ɗaga kai ta kalleni a maimakon ta yi magana sai ta kawar da kai ta soma magana.

“Nawwara ɗazu da zanje makaranta na haɗu da Mustapha, na tsayarda shi na bashi haƙuri akan abunda kika masa, sai yake tambayata ke yayata na ce eh, shine ya ce wai tun da yake a rayuwarshi wata mace bata taɓa ɗaga hannu taareshi ba ko da uwarsa ce sai ke, akan me zaki mareshi, bayan da ke yake magana ba, kawai ya buga motarsa ya yi tafiyarsa. Nawwara miyasa kika mareshi? Zaki ƙara ja mana matsala”

“Shiyasa kike jin haushi na? Babu abunda zai faru Habiba, kuma bari kiji na faɗa miki ko da Mustapha zai yanka ni ya dafa namana ya soma ya ci, ba zan bashi haƙuri ba, ke ma kuma kinyi kuskure da kika tunkare shi kika ba shi haƙuri wannan ba halinki ba ne Habiba”

“To ya kike son na yi? Bamu da wani gata sai na Allah mutane kamar jiranmu suke su yi mana abu, yanzu idan wani abu ya sake samun family mu ban san ya zan yi ba, Allah kasa ni ce zan fara bin Baba na gaji da wannan rayuwar”

Ta fashe da kuka. Ni kuma na riƙeta muka zauna tare ina rarrashinta.

“Babu abunda zai sake faruwa inshallahu, na miki alƙawari, share hawayenki kar Inna ta ji”

Ta ɗaga min kai tana share hawayen.

Haka muka zauna cikin jiran tsamanin abunda zai same ni daga Mustapha domin na san ba zai bar ni ba, Habiba ma kullum cikin tunanin wannan abun take, bata ƙaunar ko waje na leƙa saboda gani take kamar zan iya haɗuwa da shi ya yi min wani abu. Wasa-wasa muka kwashe sati uku babu abunda ya faru sai dai tunanin abun zai faru ya hanani sukuni ni da Habiba, a cikin satin ne su Murja da Hajiya Umaima da Hasana suka zo min gaisuwa tun ɗaga Kebbi. Wato Yayar tsohon mijina da kuma ƙannensa, mahaifiyarsa kuma ta yi min aike ni da Noor. Ba su kwana ba ranar da suka zo ranar suka koma bayan mun yi ma Noor tsaraɓar kayan maƙulashe da kuma tufafi, Inna kuma suka kawo mata atamfa da buhun kishinka ƙarami.

Ranar da suka kwana biyu da tafiya ina zaune tsakar gida misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe wayata ta yi ƙara alamar saƙo, ban kulata ba dan na daina ɗaukin aikin a yanzu tunani ba zan samu ba, tun da kullum ina sa ran ganin saƙon kamfanin amman sai na samu saƙon mtn. Sai da na gaji da kwancin da nake na tashi zaune ya miƙa hannu na ɗauki wayar da ke kusa da ni ina dubawa. Ina ganin sunan Kamfanin One-On-One jikina ya fara rawa, cikin zumuɗi na buɗe saƙon Congratulations na ga an rubuta a sama.ban iya tsayawa karanta sauran ba na buga tsalle ina ihun daɗi.



WHO IS READY FOR THE NEXT CHAPTER?
I can't wait to see Nawwara in One-On-One limitless company. 😍
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


1⃣3⃣

Ihun da na yi ne yasa Inna fitowa daga ɗaki da sauri tana kallona.

“Na samu aikin Inna sun ɗauke ni”

Murmushin haukan da na ke ta yi, tana girgiza kai for first time bayan rasuwar mahaifinmu yau na ga murmushin Inna. Zuwa na yi da gudu na rumgumeta ina ta murna kamar babu abunda ke damuna. Haka na wuni cikin farinciki da jindaɗi kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka. Ban san farincikina kaɗan ne har sai da Habiba ta dawo na sanar mata da labarin sai ta yi kamar zata haɗe kanta dan murna kai kace ma ita ta samu aikin ba ni ba, a ranar Habiba bata iya cin abincin rana ba dan tsananin murna, da maraici ta siye alawa da kuɗin Inna ta yi sadaka. Haka ta ke nunawa kulawarta da damuwa a duk lokacin da wani abun ya sameni, ta kan zauna ta labarta min abunda Inna bata sani ba, zata iya ɓoyewa Inna abu amman ni bata ɓoye min ba, mutune har mamakin yadda muke son junanmu suke, ganin ita take bina amman bama taɓa samun saɓani, ko ma mun samu tun anjima kaɗan zanje na rarrasheta ko kuma ita ta zo ta bani haƙuri ko da kuwa ni ce bana da gaskiya, irin tsabanin da ake samu tsakanin mabiyi da mabiyi ni ban cika samunsa da Habiba ba, muna son junanmu sosai, ko ciwo ɗayan mu yake sai ɗayan ya ji kamar ya cirewa ɗan'uwansa ya sakawa kansa.
Lokacin da Baba na da rai idan ya tashi zolayarmu har cewa yake yadda muke son junanmu bama sonsa haka, wani gurin ma idan mukaje ba dan kamanni ba da mutane za su ce Habiba ƙawata ce ba ƙanwata ba.
Ba zan iya misalta irin son da take yi ma Noor ba, tun da na haifeshi ita ce da ɗawainiyarsa har ya kawo yanzu, babu kuma wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa a unguwarmu ko ma a cikin gidanmu ni kaina ban isa na hukunta Noor ba indai a kan idon Habiba ne. Ni kaina shaƙuwar ta kan ba ni mamaki, wata ƙila dan akwai tazarar shekara bakwai a tsakaninmu.

Duk farinciki da ɗaukin aikin da nake idan na tuna Baba ba ya raye sai na ji babu daɗi, na so ace na samu aikin yana da rai na san zai yi farinciki sosai, sai dai kuma ƙaddara ta riga fata abunda Allah ya rubuta dole shi zai samu bawa. A daren ranar da na samu aiki sai ga Bilal ya kirana ni a waya na yi zaton zai ce na fito ne sai ya ce na aiko masa Noor yana bakin ƙofar gida, ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.

“Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba”

Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina.

“Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi”

Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi.

“Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba”

Habiba ta watsa min harara.

“Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa”

Na yi dariya ina girgiza kai.

“To ya kike son na yi?”

“Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba”

Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma.

Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne.

“Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida”

Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne.

“Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba”

Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi.

“Assalamu alaikum”

Sai ya amsa min da murmushi.

“Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki”

“Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai”

“Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba”

“Uniform kuma?”

“Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi”

“Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba”

“Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be dace ba”

‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’

Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce.

“Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama”

“Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi”

Cike da mamaki na ce

“Ba musulmi ba ne hala?”

“Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne”

Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba

“Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani”

“Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin”

“Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?”

“No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne”

Na jinjina kai ina faɗin.

“Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba”

Sai kawai yasa min dariya.

“Kina tsoro ne Nawancy?”

“A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba”

Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida.
Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi.

“Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?”

“Eh mana dan kin samu ma mun rage miki”

Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce

“Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?”

Sakin baki Habiba ta yi.

“Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?”

Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima.


*** *** ***

Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep.
Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba.
Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina.
Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan.

Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu

Please Login or Register in order to submit comment