Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sirri har sai yaso don kansa sannan zai bayyana ni ga abokansa a lokacin da ya tabbata idan suka ganni sai sun san ya iya zaben mace aliyu ya shirya kansa ckn kaftani a shadda ya isa gidan sagir da misalin karfe takwas na dare. Bisa teburun cin abinci ya iske su suna cin sbinci, safiyya ta sha ubansun kwalliya na wani(lace) tayi kyan amarci har ta gaji sai yaji innama ace yadda rahamansa ke da bala in kyua gaka take babba ga waye wa,gsky da sai tafi safiyya hadewa tunda zai dinga sai mata kaya masu tsadar gske, sai dai kash kafin yaga rahama cikakkiya haka za a kwashi shekaru biyar koma fiya da haka. sagir ya mike ya tarbo shi ckn fara'a suka zauna dinin table din ya dubi safiyya yace " amarya kin sha kamshi yaya amarci? ckm mirmushi tace " amarci gamu nan a cikinsa tsundun" suka yi dry ta mike ta shirya masa abinci a gabansa ya dube ta yace " kayya safiyya gsky da kyar zan iya cin abinci nan bana jin dadin jikina" sagir yace " wai meke damunka ne ckn satin nan duk wani (so weak) nake ganinka? yayi dan gajern murmushi yace " kai dai barni kawai sagir probs na iske barkatai a katagum abn ba dama" ganin bai fito fili ya sanar da sagir matsalar dake katagum ba sai shima ya bar zancen illa kawai yace " to Allah ya kyauta kuma ya jisshe mu alheri amma don Allah kayi kokari ka ci abinci ko yaya yake ni kaina bana jin dadin ganin ka haka duk da ban san problems din ba ( but yhu must try to eat)" ganin sun takura shi sai ya soma cin abincin amma sam baya jin dadin abincin ko rabi bai ci ba yaji bai iya ci gaba da ci dole ya hakura ya dinga kwararawa cknsa tacaccen ya yan itatuwa. hirar ma sama sama suke yi, safiyya ta dubi aliyu tace " shin aliyu ko ka sami min wata yar kawa ne? ni naga tunanin naka(so deep) ne yayi dan yake yana dubanta yace ' ta iya yiwuwa haka ta iya yiwuwa kuma ba haka ba abin ne wani iri( i don't knw hw to explain but tym will tell) tace " au haka ne abin yar boyo? yace kingane ko safiyya wata yarinyace nake nema ckn wasa ashe iyayenta sun yi (serious) da batun shine suka ce in fito ayi mana aure to ni kuma a shekaru na sai ina ganin ban isa aure ba ko safiyya ta tintsire da dariy har da kyakyatawa ta dubi sagir tace " dear kaji wani shirme gun wannan tsohon tuzurun in yarinyar bata ce kayi mata tsufa ba ai ka auna arziki ko ni yanzu ai tsoho na aura don dai ina son abi na haka ne amma yaushe? suka yi dariya sagir yace ' yanzu nan safiyya nine tsoho? to ki sha kuruminki kwanan nan zan karo maki kanwa wadda tafiki yarinta under 16 zan auro sai ki tabbatar cewa yanzu irinmu 'yan mata ke nema ido rufe" ta shagwabe fuska tace " don ALLAH na tuba dear kar muyi haka da kai daga wasa sai tsole ido" sukayi dry duk wata damuwa da aliyu ke tattare da ita ta kau sai jefi-jefi da yakan tuno nan da sati war haka ya zama ango.
[03/11 7:17 pm] * +234 802 874 8204, : =��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��
" " " Alqawarin da Ciwo 8" " "
=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��

Yana zaune a ofis din sa ranar alhamis ana gobe zai tafi katagum ke nan yayi bala in zurfi ckn tunani gashi dai gobe zai tafi amma har yau ckn abokansa babu wnd ya san cewa zai yi aure shi bawai auren ne bai so ba ila kankantar rahaman da yake gani. Nan take sai ya tuno da babban amininsa a bauchi wato kabir yayi hanzarin janyo wayrsa ta (landline ya latsa ko minti guda ba'ayiba ya samo layin kabir suka fara da gaisuwa sannan aliyu yace "KB yaya madam? kai ma ya kake da bauchi?" yace " everything is fyn ai nayo zaton ba zaka neme ni ba in yaso ranar daurina auren sai mu hadu a katagum sai in ga abokin da ya finin" aliyu yace " oh kb am sori wlh ayyuka ne sun yi min yawa a ofis ashe ka sami labarin daurin auren? ya ce nima jiya alhajinmu yake sanar mani su baba na katagum sun aiko masa da gron daura aure shine nima na sani, aliyu (what is happening) ne akan auran nan? ya ja dogon numfashi yace, "kai dai bari kawai kabir wlh kai kanka shaida ne ina son rahama (too much but) ni ban shirya mana aure yanzu ba (last week) na zo ma su baab da maganar zan sama mata (boarding scul) ana bauchi to anan ne nana ya ke sanar da ni shirinsa na aurenmu gsky kuma na amince da hujjar da ya kafa min na dalilin auren amma don Allah kabir ina son kar ka sanar da kowa maganar auren na don kuwa zai zamo (in secret) ckn sirri ka gane ai?" yace gsky(i don't understand wat u mean) shin ko kacanza ra'ayin aurenka da rahamar ne? gsky yarinyar is very nice ga tsabar kyau ni ina ganin nan da 2 yrs idan kayi kiwonta sosai zata yimaiko har ka gaji moriyar ta" suka sheke da dariya abin ka ga shakiyyan abokai aliyu yace" wlh (i never change my mind but the prob is) ka san ni da nuna matsayi akan komai nawa (could u imagine frnds) anan lagos dariya zasu min idan suka san zan auri yar shekara sha uku? (dat is y) na ke son kayi (taking care ) daga kai sai sakina ne ckn frnds dina suka san auren nan. kabr ya sauke wani gwauron munfashi yace" kana ganin haka zai yiwu? shin ina ka taba ganin aure ya boyu ko ayi zaman aure ckin sirri? ina ce lagos zaka kai rahama? kana ganin zai kyautu ka boye ta gidanka ba tare da kowa ya sani ba? ya ce " kwarai zai yiwu kai dai ka taimaka min da abinda nak so daga baya zan sanar da kai (plans) dina" yace" shi kenan sai mun hadu a katagun" aliyu yace "yaushe zaka zo? Ina ganin nima gobe da yamma zamu isa can sbd daura auren na safe ne" yace " amma gida zaka bar sakina ko? yace " kai zai wuya in bar ta a gida ita kanta tana son zuwa katagum din kaga daganan sai su raka amarya lagos ko? aliyu yace"what! dn Allah ka rufa min asiri akan zancen kai amaryan nan kai ana abu cikin sirri zaka janyo tonon silili. gsky ko su baba na shaida masu bana bukatar 'yan rakiya wa rahama daga ni sai ita zamu tafi duk mai son zuwa gidanmu ya iya zuwa daga baya" kabir yace '" gsky ni aliyu na rasa inda kasa gaba, anya kuwa kana son yarinyar nan ko dai auren dole su baab zasu hada ba su sani ba? ni kam ina tausayawa rahama irin zaman da zatayi a gidanka muddin baka son ta illa biyayyar iyaye yasa ka aureta. don ALLAH aliyu in baka son yarinyar nan ka gaya min wlh na san yadda zanyi in fahimtar da su baba su hakura da auren yanzu" yayai murnushi har sautin ya isa kunnen kabir yace "wlh, wlh kaji rantsuwa kanen? ina son rahama tsananin so kuwa ta yadda bana jin zan iya rayuwar aure ba tare da ita ba kuma ina tsammanin ko ckn tsumman goyo aka ban auren rahama zan iya amsa inyi rainonta har ta girma a hannuna bale yanzu na tabbata rainon da zanyi mata bai wuce(2 to 3 yrs) ba kafin mu soma zaman aure na sossai sbd haka kr kayi kokwanto akan auren muko na dole ne don biyayyar iyaye ina son ka saka shi a cikin ire iren auren soyayyar daka sani kamar irin naka da sakina kil ma ya zarta naku" suka yi dry, kabir yace shin wani abu da bangane ba shine maganar rainon da naji kana cewa zakayi wa rahamar(i don't understand)?" ya murmusa yace " kar kayi kokwanton abinda nace . Zanyi rainon raaham har sai naga ta zama mace sosai sannan zan fara dora mata lalurar aure kaga tayi girma ta sami ishasshen ililmi akan abin ka gane yanzu? ya numfasa yace " kwarai na gane manufarka, amma abin da kamar wuya yadda kake gwauro a bakaa auren wadda kake so sannan kace zaka zura mata ido kai ban yarda ba kunma ba zan taba yarda ba" aliyu ya keec da dariya yace " ni kam zan iya kuma wlh wannan alkawaru ne nayi in sha Allahu sai na cika shi(5 yrs) zan diba ma rahamar kaga lokacin zan nemi hakkina (she is 18) ai yayi ko? anan kama kabir yayi dry iya son ransa yace" kwarai yayi daidai amma wlh wannan alkawarun da ka dauka wa kanka nasa masa suna ALKAWARIN DA CIWO! kuma sai ka fadi haka da bakinka. to wai tsyaa idan ita rahama ta nemi hakkinta fa ya zaka yi?" yace " nasan zai yi wuya ta nema sbd na lura bata san komai ba game da sha'anin aure kuma tun yanzu tana min kuka wai ita tsoron haihuwa take yi tunda kawarta ta zo hihuwa ta zama yar yoyon fitsari kaga ke nan na sami madogarar da zan dinga kafa mata hujja ina tsorata ta da abun in kuma har ta matsa shi kenn" yace " wlh aliyu wannan alkawarin da ka dauka zai yi wuya kuma n tabbata kafin rahama ta bata kai ne na farko na san kuma kai ne zaka sha wuyar alkawarin" suka yi dry gaba daya sun kusan fin awa guda suna hira a waya daga karshe sukayi sallama.

('('('('('('('('('('('('('('('('

Haka aliyu yaci gaba da shirye shiryen zuwa katagum daura auren sa ba tare da ya sanar wa da kowa ckn abokansa ba balle gurin aikinsu. shi ko dan irin hutun nan da angwaye suke dauka na cin amarci bai nema ba sabod yasan shi ba wani amarcin da zaici tunda kwna biyu kacal zai yi a katagum sai ya dauko amaryarsa zuwa gidnasa lagos.sagir ya kusa ya dago abin da ke faruwa da yage setin akwatuna a dakin baccin aliyu amma da yake wayom aliyu ya zarta misali sai ya juye shi bai bai ya shirya masa karyae na wani cousin dinsa ne y siyo masa zai yi aure. taiba kuwa har kuka tayi sbd ganin aliyu ya rame a ckn satin nen. Ana sauran kwana daya daurin aure na da yaya Aliyu ya iso garin katagum,ranar jumaa kenan da misalin karfe bakwai na marece lkcn sallar magrib,ko cikin gida bai shiga ba ya nufi masallaci don yin salla.Tare suka jero da babana daga masallaci zuwa gida suna tafe suma tattaunawa gane da daurin aurenmu gobe.Dakin da yaya Aliyu kan sauka na soro nan suka shiga shi da baba,ya nuna masa akwatunan da ya yomin na aure guda hudu shakare da kaya masu tsadar gaske yawanci duk dinkakkune tun a lagos ya bada aka dinka sannan ya fiddo rafar kudi yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya mikawa baba yace,gashi baba wannan sadakin rahama ne,baba yana rike da kudi a hannunsa yace,"haba Aliyu yaushe ne kana dan mu har sai ka bada sadakin rahama.To ka bar abinka kayi wata hidimar ni ba zan amsa ba",Aliyu yace,"Aa baba baayi haka ba sadaki ai shine aure kuma ya zama dole a ba rahama sadakinta muddin ina son aurenta tunda ba sadaka kuka ban aurentaba ba kuma ko sadaka ne dole diya take ba baiwaba ta cancanci sadaki''.Baba yayi ajiyar zuciya yace, kwarai na san da haka ko auren sadaka da ake bayar wa ai dole a biya sadaki balle ma ku kuna son junanku. A matsayi na na kanin mahaifinka ni zan biya sadakin.Yayi saurin cewa aa baba wlh na yafe maka tunda ina da hali na ni dai fatana ku dinga mana addua kuna sa mana albarka tare da fatan ayi a saa.Yace shikenan Allah yayi maka albarka ya albarkaci auren ya ce amin baba. Aliyu ya nemo yan matasan gidanmu suka jida Akwatunan suka shige dasu cikin gida dakin goggo shi kuma na biye da su da dan kit a hannunsa.A lkcn ina takure bisa gadon goggo ina rusa kuka sbd yan uwa da suka tasani gaba wai sai sun samin lalle.Aliyu yana shigowa suka tasa shi gaba da tsiya wata abokiyar wasanmu tace,lah!lah!me zan gani?yanzu nan angonne da kanka dauke da akwatin kayan lefen?lallai zamani ya canza maimakon kayi kiranmu mu zo mu kawo shine ka kawo da kanka?ina ganin ma amaryar bari mu kai makaba kai ne zaka kai abarka chan legos din,Yayi murmushi duk da yake Aliyu sam ba mai son surutu bane valle irin wadannan wasannin abokan wasa inkaga yawan maganar aliyu to a gaba na yake ko kuma ana magana akan abinda yashafeni.Ya dubi msi maganar yace,Au baba bai gaya muku babu yan kai amarya ba?Daga ni sai ita zamu tafi in yaso daga baya zanzo da kaina in kaiku kuga wuri sukace gsky mu wannan tsarin bai mana ba,ya zaka maishe mana ya tamkar ba yar dangi ba gashi ita kenan mace a gidan kamar rai daga rahma fa an gama auren ya mace a gidan nan don Allah yaya aliyu kayi hkr ka barmu mu raka ta muna son ganin birnin ikko,Yayi dan murmushi cikin ire iren murmushinsa masu burgeni in dai bai amince da maganarkaba haka yake irin wannan murmushin yace shikenan zamu tattauna dasu baba za'a san abinyi. Ni kam ina leken sa ta cikin mayafi na ashe ya hankaltu da ni sai naga yayi saurin aje akewatin hannunsa ya nufo inda nake ya zauna a gefen gadon yasa hannunsa yana kokarin yaye rufar da nayiwa fuska ta yace"Amarya ba dai har an fara kukan amarcin ba ne tun yanzu?Yana cire mayafin yaga fuskata sharkaf da hawaye nan da nan sai naga ya hade rai ya juya ya kalli wadanda ke shirin sa mani kalle yace"Yanzu don Allah har kun farasa yarinyarnan kuka tun yanzu?gsky zamu bata da wanda yasata kuka shin me kukayi mata hafsa?Tace wlh babu illa dai sa mata lalle da muka zo yi shine abin kuka mu kuma wlh sai mun sa mata tunda muma haka aka yi mana"Yace a kan al'ada kawai sai ku sa min ita kuka? Ina dai sa lallen nan bawai ya zama dole bane to yau akan rahams an dai na,suka sheke da daria shi kuma ya juya ya ci gaba da lallashina na da cewa yi shiru kinji baby na babu mai bata miki jiki da lallen aure in dai ina gidannan sai dai in sun yarda in sa maki da kaina.
[03/11 7:17 pm] * +234 802 874 8204, : =��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��
" " " Alqawarin da Ciwo 9" " " =��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��

Suka yi dariya tare da cewa,ai zaka iya tunda ma lefen da kanka ka kawo.Ke kam rahama kinyi sa'ar miji mai tattali da lallashinki Allah yasa ya dore haka"suka fice suna dariya shi kuma ya cigaba da lallashi har da hirarraki har sai da yaga dariyata sannan ya nufi sassan mahaifinsa.Yana fita danginmu tare da su gwoggo suka antayo cikin dakin don ganin kayan lefe na. Kaya kam sun amsa sunansu kowa sai tofa albrkacin bakinsa yake tareda sam barka masu mamaki nayi sbd irin yawan kayan tare da haduwarsu. ni kaina duk da a lillibe nake sai da na dinga liken kayan ta ksan mayafina. lallai yaya aliyu ya jibgo mini kaya na gani na fada. Ina jin masu kirgwa suka ce zannuwa kala talatinne cif. duk sakankance gurin ganin kaya ashe masu niyyar sa mana lalle basu fasa ba sai ji nayi sun yaye lullubi na sun goga min lalle tare da fesa min nono daga bisani suka feshe ni da turare. In banda aikin kuka babu abin da nake yi. Karfe takwas na dare su kabir da sakina suka iso kasancewar suna da dangi da kuma gida a katagum shi yasa suka sauka a gidnsu. washegari da misalin karfe tara na safe aka daura aure na da yaya aliyu. wlh ni tamkar a mafarki nake ganin abin ban tantance da gaskiyar haka ba sai da naji abokan wasa na rangadamin guda suna cewa yau na tabbata matar aliu gobe sai lagos sannan ne na saka kuka sbd jin zan tafi wata uwa duniya lagos in bar iyayena . ni kam dari bisa dari ina son yaya aliyu illa lagos din ne bana son inji ana cewa zan tafi. ni a son samu nama a ce bayan auren a nan gidanmu zan zauna shi kuma ya dinga zuwa kamar da amma ina babu yadda za'ayi haka ya faru. ban sami ganin yaya aliyu ba sai bayan sallah isha'i aka sani nayi wanka aka bani wata tsaleliyar atamfa ckn kayan aure na na saka sai sheki da kyalli na keyi ni kaina na san na kara kyau a ranar fiye da nawa na baya. aliyu ma da ya shigo dkn gwaggo ya ganni rudewa naga yayi har yana rayawa a ransa anya zai iya cika alkawarin daya kudirta a ransa na kyale ni?

('('('('('('('('('('('('('('('('
Gsky da yana ganin nayi kankantar aure amma yau sai ya ga na kara yi masa girma tamkar yar shekara sha biyar ko sha shida da ma ganu da manyan gabobin girma irin na mahaifiyata. ya tsaya kusan minti biyu yana kare min kallo sama da kasa ni kam kaina a sadde yake a kasa gaba daya yau kunyarsa na ke ji. daga ni har shi kamshin turare muke mai dadin gske. haka nan ya daure yace " rahama' na amsa ckn sanyin murya " na'am" gabansa sai da ya ba da ras! da yaji murya ta domin yau itace rana ta farko da murya ta ta sa shi jin sanyin jiki ya sake cewa " raahama yau kuma baki iya kallo na sai dukar da kai ko nayi laifi ne baki ganni ba tun bayan daura aurenmu? na yi saurin dago kai nace masa" ni wlh ba haka bane" yace " to menene? nace " ba komai" yace " ko kunya ce " na gyada kai nace "uhm" yayi dariyarsa ta kasaita yace" yanzu nan kunya ta kuma kike ji rahama? ashe abn da sake wai an baiwa mai kaza kai. to bari kiji yanzu ni aliyu na zama mijinki tsakanin mu babu zancen jin kunya duk wata damuwarki ni zaki gayawa tunda yanzu dani zaki zauna. kinga gobe idan na tafi dake gida na can lagos to komai ya kare najin kunya daga ni sai ke zamu zauna babu su gwaggo ko su baba a kusa kila ma sai kin haihu zaki zo gida su ganki, haba wa kaman jiransa nake sai kawai na saka masa kuka shi kansa da ya san maganar da yayi zata sani yin kuka na tabbata da bai fade ta ba. kuka na shiga yi ba kadan ba duk ya bi ya birkice ya shiga ckn rudani ya ce " subhanallahi! meye abin kuka don nace ba zaki ga su gwaggo ba ko don nace zaki haihu? to yi hkr ni sam na manta kina tsoron haihuwa ba zan yarda ki haihu ba kinji? bil hakki da gskiya ni fa tsoron haihuwa nake har bana kaunar in ji ance wani ya haihu. da yaga na dan tsagaita da kukan sai yace" ba kya son ki bini lagos ki ci gaba da karatun ki? nace " ina son karatun amma ni bana son tafiya lagos dinne idan munje wanene zai taya ni zama? yace " ni zan taya ki ko ba kya so? nace " ina so to idan ka tafi gurin aiki fa ya zanyi? ya ce " ai inajin a lokacin ke kuma kin fara zuwa makaranta, kinga lokacin da zaki dawo nima na taso aiki ba shike nan ba idan na dauko ki a makaranta sai mu wuce gida abin mu" nace " dawa zan dinga kwana?" yayi murmushi yace " dani mana ko ba kya so?" na dan yi murmushi nace " ina so" washegari lahadi da aka wayi gari na ga ana ta min shirye-shiryen tafiya ga dangin mahaifiyata sun ce aladole ko mtum biyu ne sai sun raka ni gidan miji na, shi kuma yaya aliyu ya tubure sam baya son ' yan rakiya. dole haka kowa ya hakura ni dai bani da wani aiki ranar sai kuka sbd jin wai ni kadai zan tafi sai aliyu wanda ko duk kawaye na da ake masu aure dangi da kawaye ke raka su gidan mazajensu har ma a kwana amma ni yaya aiyu ya hana. su gwaggo da iyayenmu maza sune suka tasa mu gaba ni da yaya aliyu suna man nasiha" baban aliyu shi aliyun yafi tsananta fada da nasihar akansa yace"don Allah abba (sunan da su kan kira aliyu da shi kenan sbd sunan kakanmu ke gare shi) ya ci gaab " ka kula da amanar yarinyar nan kar ka kuskura ka ci amanarta ko musguna mata don Allah ka kula da addininta duk da yake na san rahama akwai son addini to amma kayi kokari ka kula sosai. mu dai nauyinta ya tashi a kanmu ya koma gare ka to kar kayi sakaci ka bi ta sannu a hankli sbd ka san yarinyace akwai tsabar kuruciya a tare da ita, Allah ya taya ka riko ya baka zama lfy kuma ya albakarkci auren" gaab daya dakin aka ce amin. baba na shima yayi mana nasiha shima kaninsu yayi mana sannan suka fice daga dkn sai mu sai gwaggo. itama ta dora da tata nasihar daga karshe tace ' to mai gida na ga dau yar kanwarka nan ka bi ta sannu kan hankali na tabbata zaku yi zama lfy tunda ku na son juna. amma don ALlah ka rage irin sangarta rahama da kake yi sbd yanzu zaman aure zaku yi ya ban banta da irin zaman da kukeyi da. ke kuma ban hana ki shagwaba ba amma ban da rainu da rashin kunya, kar ini kar in gani in ba haka ba ni in zo in amshe mijin inyi zama na a lagos ke kuma ki dawo nan dakin" muka yi dan murmushi sai a nan ne na san nayi murmsuhi amma da kuka kawai nake yi. haka aka sako ni gaban motar yaya aliyu ina ta aikin kuka yan uwa suka zagaye motar suna mana Allah kiyaye hanya. kabir ma yace suna na zuwa shida sakina. muka yi sallama da yan uwa motar mu ta daga ni daya tilo kamar yar mayy sai aliyu. motar jeep yar karama mai(tint glass) wato irin mai duhun nan haka ya dinga sharara gudu yana yi yana lallashi na sbd kukan da nakeyi.
[03/11 7:17 pm] * +234 802 874 8204, : =��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��
" " " Alqawarin da Ciwo 10" " "
=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��=��

Mun bar garin bauchi sosai sannan na saurara da kuka sbd na fara jin bacci, ido na a lumshe yaya aliyu ya dubeni yace" rahama ya akayi ne" na dago dara daran idanuna da suka zama tamkar an gulof sbd kuka na kalle shi nace " na am" yace kina jin baccine ? nace ' eh' ya ce "ok bari inyi parking sai kikoma baya ki kwanta ko? yayi parking a gafen hanya ya riko min hannu na fito na koma gidan baya na kwanta ya cire malim malim din da ke jikinsa ta lallausan shadda ya lilliba mini sannan ya koma mazauninsa ya ce gaba da tuku. ya zuge dukkan gilashan motar ya kunna mana A.C sannan ya saka mana kaset na turanci wakar celen dion ta (A NEW DAY HAS COME) tun ina jin wakar har sarkin barayi ya sace ni kwance ckn babbar rigar yaya aliyu ina shaker kamshin ni'imtaccen turarensa (HEAVEN).resemble amma gsky she is beautiful ko zaka ban aurenta idan tayi girma don na san yanzu karatu take ko?Yace ja bari sai ta girma in tana sonka sai in baka ita(second wife)suka yi dariya na kalli Aliyu alamar tambaya a ido na ya kashemin

1 Comments On ALKAWARIN DA CIWO
avatar
raulat

3 months ago

Reply

Babu complete?

Please Login or Register in order to submit comment