Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👑𝐘𝐀𝐑𝐈𝐌𝐀 𝐀𝐙𝐀𝐃🤴



💖🌹𝐇𝐨𝐭 𝐥𝐨𝐯𝐞💖🌹



𝐚𝐧𝐝 𝐫𝐨𝐦𝐚𝐭𝐢𝐜 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐲👄


Story and Writes by

Zainab Abdullahi~pinky Darling


(𝐆𝐢𝐦𝐛𝐢𝐲𝐚𝐫 𝐣𝐚𝐣𝐢𝐫𝐭𝐚𝐭𝐭𝐮👸)


Yarima Azad paid book ne duk wacce ta shirya biya ga account number 7060577995
Zainab Abdullahi opay
Kitura min shaidar biya Sannan in sakaki a paid group
__________________________________________________________________________https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________________________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
________________________________________
Bismillahi Rahamanin Raheem 💫

(Da suna Allah mai rahama mai jinƙai )

Allah yadda kabani ikon fara rubuta littafin nan lafiya ya Allah kabani ikon gamasa lafiya
Allah ya sa jama'a su amfana da abinda keciki abinda a kuskure Allah ka ya femin

Na rubuta wannan labari ne domin ilmantar wa da faɗakarwa banyi wanan liltafi don cin zarafin kowa ba idan akwai ɓangaren da ya yi dai-dai da rauwar ka/ki tu arashi ne. Wannan littafin mallakina ne ban yarda wani ko wata ya juya min abu ba batare da izinina ba

Duk wadda ta juya min book na barta da Allah.

𝐅𝐫𝐞𝐞 𝐩𝐚𝐠𝐞

PAGE 1

"Ke Azra Yarima Azad na ne manki a sashensa." wadda aka kira da Azra ta waro idu waje ta na kallon Sarkin fadar Yarima Azad, "lafiya me na yi masa ya ke ne mana.?" Ta faɗa kamar zata fashe da kuka "Idan kika je ai zakiji abinda kika aikata." hankaliata tashi tabi bayan Sarkin fada zuciyarta na dukan uku-uku sai da sukayi tafiya mai tsayi kana suka iso ɓangaren Yarima duk inda suka wuce kallon ta a'ke yarinyar da ba ruwanta ko magana wahala ta ke mata me ya haɗa ta da Yarima Azad da kowa ya san bashida mutunci, ɗan iska ne number ɗaya gurin lalata da yaran bayi musamman idan ya ga yarinya na da kamun kai, haka dai suka yi ta maganganu ƙasa ƙasa

suna isa ɓangaren Yarima Azad Sarkin fada ya ce mata ta jira sa anan ciki ya shiga Sarauniya Mulaifa kishin giɗe saman wata kujerar alfarma ta sarkunan da suka amsa sunan su ta yi shiga ta alfarma ya "ce ran Sarauniya ya daɗi ga ya rinyar nan na zo da ita." Kamar bazata yi magana sai da ta nisa kana ta ce" kashigo da ita ciki kasan ɓangaren da zaka kaita." Angama ranki shi daɗe Sauraniyar matan duniya." Wani shu'umin murmushi ta yi kana ta ɗauko wata ƙaramar jaka ta miƙa masa, Sarkin fada kamar ya yi mata sujada wurin karɓar jakar ya na ta zuba mata kirari sai da ta ɗaga masa hannu kana ya tashi ya fita ya koma wurin Azra "ke wuce mutafi." biyarsa kawai ta ke wani sihir taccen ɗaki ya kai Azra ya ce ta zauna nan a tsorace ta "ce amma ai nan ba ɓangaren Yarima bane." "Eh na sani ba Yarima ya sa a'kawo ki ba Sarauniya ce hasali ma Yarima ba ya ƙasar Misira ya na ƙasar India saboda haka kijira zuwan Sarauniya shawarar da zan baki duk Abinda ta sakaki kiyi kawai idan ba haka bazaki fitu da rai ba." Ya na gama faɗar haka ya juya ya tafiyarsa ya barta tsayi cikin ruɗani,
Sarkin fada na fita ya ci karo da Sarauniya da Boka Shaldas hanya ya basu suka wuce sanan shima ya wuce cike da mamakin me ya haɗa ta da Boka shi dai iya saninsa duk ƴan matan da ya ke kawo mata yaronta Sadauki Arjun ki lalata da su kana ayi ma yaran barazana 'akan duk wadda bata ce Yarima Azad ya yi lalata da ita ba zasu kashe ta idan kuma ta na da Iyaye harsu za'a haɗa, duk wannan abin dake faruwa Yarima Azad bai san wainar da a'ke tuyawa ba haka Sarki Mahir shi ya sa duk rabin jama'ar da ke Masarautar suke ɗaukar Yarima Azad tantirin ɗan iska, Azra na nan tsaye kamar wadda aka dasa sai ga Sarauniya ta shigo ita da Boka Shaldas da shigar su sai da Boka ya ja baya nan ta ke sandar hannunsa ta kama da wuta cikin firgice ya fara nuna Azra da hannu ya na son yima Sarauniya magana ai kuwa ji ya yi an shaƙe sa an saka masa wata ƙatuwar sarƙa mai wuta wata guguwa ce ta taso daga rufin ɗakin ta yi sama da Boka Shaldas ɓat ya ɓace kamar bai taɓa wanzuwa ba a'wurin ita kuma Azra babu abinda ta gani illa kawai bata ga Boka ba Sarauniya kuwa suman tsaye ta yi, wani zufa ne ke yanko mata ta ko ina da sauri ta fito ɗakin wani bafade ya kira mata Sarkin fada Sarkin fada na zuwa ta ce masa ya je ya kai Azra gidan kurkukun da ke cikin Masarauta.


PAGE 2

______Suna fitowa suka ci karo da Yarima Azad riƙe da a'kwati zai shiga ɓangarensa ga duk kan alama yanzu ya dawo da sauri Sarkin faɗa ya durƙusa ƙasa ya na kwasar gaisuwa
Amma ko kallon inda ya ke Yarima Azad bai yi ba balle ya sa ran zai amsa gaisuwar cikin azama ya saka hannu zai karɓi akwatin amma Azad ya ɗaga masa hannu ya shi gewarsa ciki ya bar Sarkin fada duƙushe, kaɗan ke nan daga halin Yarima Azad don ko mai martaba haka ya ke fama da Azad sai ya yi ta yi masa magana amma uffan bazai ce ba sai ya ga dama idan ma ya yi magana to baza ta wuce Eh ko a'a ba ko ok iyakar maganarsa kenan ba zaka taɓa jin ya yi maganar da wuce haka ba, shi ya sa a'lumar da ke Masarautar Misira suka ɗauke Yarima Azad mai girman kai________ta ɓangaren Yarima kuwa ba ya son ya wan magana shi gaba ɗaya magana bata damesa ba idan har ya na ƙasar tu ko fada idan ba mai Martaba ya kirasa ba shi da Sadauki tu bazai je ba haka zai sa laptop ga ba ya yi ta aikinsa saboda shi business ya sama gaba shi ya sa bai cika zama ba ya na Company a ƙasashe da ban da ban sun fi talatin shi kansa bai san iya duƙiyar da ya tara ba don har Company narkar da gorl ga rai duk wanan kasuwanci da ya ke yi banda Mahaifinsa babu wanda ya sani ko Sarauniya Mulaifa ba ta sani
saboda idan har ta sani sai ta lalata komai
muguwa ce ajin karshe ya sa baƙar azaba hanunta kafin ya san ciyon kansa har riƙesa tayi Maciji ya sare sa sai da ya suma satin sa ɗaya bai san inda kansa ya ke ba ko mai Martaba bai sa ni ba, ba yan kwana2 sai ga Yarima Azad ya tashi Sarauniya ta matuƙar mamaki ganin Azad ya ta shi bayan Boka Shaldas ya tabbatar ma ta bazai ta shi ba ƙarshe ma mutuwa za shiyi Abinda ba ta saniba
lokacin da ta sa Sarkin fada ya ɗauko mata Yarima wani Aljani ya ɗauke sa ya ɓoye sannan ya rikiɗe zuwa saffar Yarima Azad Sarkin fada ya kaisa matsayin Yarima Azad
ta riƙesa Maciji ya sare sa da gan-gan ya yi kwanciyar sa har na tsawon sati ɗaya saboda kar ta gano ba Yarima bane bayan ya cika sati ya mai da Yarima Azad shi kuma ya yi tafiyarsa wannan Aljani shi ke taimakon Yarima Azad duk lokacin da Sarauniya ta yi niyar halaka shi ba tare da ta sani ba hankalinta ta she ta je gurin Boka Shaldas ya duba mata me ke faruwa amma Boka Shaldas ya yi iya yinsa bai gane komai ba haka ta haƙora ta fara neman wata hanyar halakar da Azad, amma Allah bai bata da ma ba ta yi ta saka masa magani ga abinci amma sai wanan Aljani ya sauya abincin haka dai ya yi ta tai makon Yarima Azad har ya girma, kuma shi ya ke baiyana ma Azad duk abinda Sarauniya ke ai katawa Sarauniya Mulaifa ta sha alwashin yadda ta halaka Gimbiya Nasrin sai ta halaka ɗanta Yarima Azad saboda ɗanta Sadauki Arjun ta ke so ya mulke ƙasar Misra.
Wannan shine dalilin da ya sa ta ke kullama Yarima Azad makirci ya na lalata ya ran bayi
Sarkin fada kuwa daret gidan kurkuku ya kai Azra ya rufe mutane sai tsegumi su ke ya a'kayi Yarima ya sa akai Azra gidan kurkuku
abinka da Masarauta nan da nan labari ya bazu Yarima Azad ya sa a'nkai buya Azra gidan kurkuku.......




𝗣𝗔𝗚𝗘 3

_________Yarima Azad kuwa ya na shiga ɓangarensa ɓanɗaki ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin shigar kayan ya ƙi riga da wando na sulken ƙarfen gorld yau ko fakin ɗin gashin kansa bai yi ba tajesa kawai ya yi mai makon gashin ya hargitse sai ma a'do ya yi masa wani ya yi ta gefen face ɗinsa saura kuma ya yi baya wata red ɗin riga ya a'aza saman rigar yaƙi mai tambarin zaki sai wata sharɓeɓeyar takobi shiri ya yi sosai da ka gansa ka ga jarumin maza Wow! masha Allah saboda kayan yaƙin ba ƙaramin kyau soka yima Azad ba saboda Azad kyakkyawa ne ajin karshe dogo ne amma ba sosai sa ba ya na da murɗaɗɗen jiki irin na manyan gwarazan maza da suka amsa sunan su wurin jarumta fari ne tas fatarsa har yallow yallow ta keyi ya na da dogon hanci kamar a'ntsaga kara sai ɗan ƙaramin bakinsa mai ɗauke da pink lips da suka ƙarama fuskar sa kyau ya na da dara daran idanu irin sexy eyes kwayar cikin idonsa blue ta ko ina Yarima Azad ya haɗu ba ya da maƙosa;

Yarima Azad irin Handsome guy ɗin nan ne da kowace mace ke burin samu.

Ya na kammala shiryawa ɓangaren Maimartaba ya nufa saboda shine ya kirasa kiran gaugawa saboda ya samu labarin Sarkin ƙasar Habasha ya turo ɗansa Yarima Rishaf da da karonsa sunaki dubu biyu a'kan su yaƙe masarautar Sarki Mahir su kashe sa ya mai da ɗansa Yarima Rishaf Sarkin Misira




wannan shine dalilin da wowarsa daga Indai,
saboda Yarima Arjun bai iya komai ba da ya shafe harkokin yaƙi ko ta kobi bai iya sarrafa wa ba sha shanci kawai ya iya gaba ɗaya Mahaifiyarsa Sarauniya Mulaifa ta lalata shi wai a haka ta ke so ya mulke ƙasar Misra,


bayi ne ke zubewa ƙasa suna kaima Yarima gaisuwa amma ko inda suke bai kalla ba saboda zuciyarsa har ta farfasa ta ke muradinsa kawai ya ga kansa a'filin daga ya na shiga ya iske Mahaifinsu cikin shirin fita yaƙi shima Sadauki Arjun ba'abarsa a'baya ba ya yi shigar yaƙi sai ka rantse wani babban jarumi ne;


Azad kuwa bai zame ko ina ba sai wurin Mahaifinsa suka rungume juna sanan ya duƙa ya gaida Mahaifinsa
abinda Arjun ba ya yi shi tunda ya na ɗan sarki ai basai ya duƙa ya gaida Mahaifinsa ba,
Sarauniya Mulaifa ce ta ce "kai Azad ba ka iya gaida mutane ba ne.?" Azad kuwa kamar ba dashi ta ke ba
don ya sa ma ta bakin ciki ya kalli Arjun ya ce "kai ragwun namiji wannan shigar fa ina zaka je.?" mai makon Arjun ya ji haushi sai ma murmushi ya yi ma ɗan uwansa saboda ba bu abinda ya keso fiye da ɗan uwansa Azad amma Mahaifiyarsa ke cusa masa tsanar Azad ba ta bari ya ji inda Azad yake tun suna yara ya san halin Mahaifiyarsa sarai shi yasa baya nuna ma Azad ƙauna saima ya nuna ma ta ya fita tsanar Azad, idan ya fito shi kaɗai ya na zuwa ɓangaren Azad amma sam baya samun fuska wurin Azad don sai ya shiga ya yi ta magana amma Azad ya yi banza da shi ƙarshe ma shigewarsa ya ke bedroom ya barsa nan:


Sarauniya Mulaifa ce ta katse masa tunanin saboda wani wawan mari ta ɗauke Azad da shi ko gizau Azad bai yi ba cikin azama Arjun ya taso da niyar da Katar da Mahaifiyasa aiko Azad ya saka hannu ya wanke sa da wasu mahaukatan maruka sai da bakinsa da hancin sa suka fashe kukan kura tayi tayo kan Azad sai da ya bari ta kusa zuwa kansa ya kawce ƙafarta ta zame ta faɗi tim kaji ƙarar faɗuwar ta duk abinda a'ke Maimartaba na zaune ya na kallonsu ya kasa magana,
sai da yaga Azad ya cire ta kobi kana cikin wata murya ya ce "kai Azad! me kake shirin aikatawa haka.?" Shiru Azad ya yi saboda yadda yake ji kamar ya cire ma Sarauniya Mulaifa kai "Azad ba da kai nike magana ba.?" nan ma shiru ya yi sai tsuma jiknsa keyi zuciyarsa na tafarfasa sanin halinsa da Sarki Mahir ya yi da muguwar zuciya tun ya na yaro idan har wani ya kuskura ya taɓa lafiyar jikinsa tu ranar sai na lahira ya fika jin daɗi har ya girma haka ya ke bai canza ba ko yaƙi suka fita haka za ka ga ya na da gargaza manyan mazaje sai dai kaga kanunsu ƙasa,


dole Sarki ya taso ya ji hannusa ya kai sa cinkin turakarsa kana ya dawo ya kira jekadiya ta zo ita da bayin Sarauniya suka yi ciki da ita kana ya koma gun Arjun da ke zaune dafe da hanci tsabar azaba ko magana ya kasa yi hannunsa Sarki Mahir ya ja bai zame da shi ko ina ba sai ɗakin magani san nan ya dawo ya fara lallashin Yarima Azad;

saida ya tabbatar Azad ya sauko da fushin da ya ke ka na suka fita a'ka shirya dakarun da za'afita da su yaƙi cikin tsari shu gaban dakaru da Sarkin yaƙi suka shirya komai ka na a'ka busa ƙahon fita yaƙi,

Arjun ne ya fito da sauri ya hau dokinsa ya bi bayansu basu zame ko ina ba sai wajen gari inda nan ne Yarima Rishaf yake da dakarun sa ko wanensu cikin baƙar shiga ta yaƙin ko a mutu ko a'yi rai




Paid book

Free page

PAGE 4





Wani azababben yaƙi ne ya kacame tsakanin ɓangaren biyu banda ƙarar makamai da ihun maza babu abinda kake ji sai da suka shafe awa huɗu kana ɓangaren su Yarima Azad sukayi nasara, har ya ɗaga takobi zai cire kan Yarima Rishaf sai kuma ya fasa ƙatuwar sarƙa ya ɗauko ya ɗaure Rishaf da ita sauran bayin da ba su mutu ba suka tafi da su matsiyin bayi,
da isar su cikin Masarauta gidan kurkuku Azad ya jefa Rishaf ba tare da ya cire mai sarƙar da ya ɗauresa ba lokacin da Azad ya shigo da Rishaf Azra na tsaye bakin tagar ɗakin da ta ke kallon Azad ta ke cike da mamakin irin ƙarfin da Allah ya bashi Uwa Uba kuma ga kyau kamar shi ya yi kansa tun da suka fita yaƙi baiwa Hibba da suke ɗaki guda ta ke ba Azra labarin irin ƙarfi da jarumtar Azad, kamar ance Azad ya juya sukayi ido huɗu da Azra wani haske ne kamar hayaƙi ya fito cikin idon Azra ya shige jikin Azad hasken na shigarsa sai da ya ji wani shokin ajikinsa da sauri ya kawar da kansa ya tafiyarsa Azra kuwa jikinta ne ya ɗauki makarkata da sauri Hibba ta zo ta kamata ta kwantar da ita, saboda duk abinda ya faru itace sila saboda ita ta tura wannan haske cikin idon Azra jikin Azra ya yi mugun zafi murza zoben hannunta ta yi wani farin haske ya fito ya rinƙa shiga jikin Azra sai da jikin ta ya yi sanyi ta fara dawowa dai dai sanan Hibba ta koma murza zoben hasken ya ɓace ,

wani murmushin jin daɗi tayi cikin ranta ta ke cewa burinta ya kusa cika shekararta ishirin da biyar Sarauniya Mulaifa ta sa a'nrufeta don ta cinma mugun nufinta akan Yarima Azad to ga mai ceton sa nan ta baiyana don tun shigowar Azra cikin Masarauta ta san dole Boka Shaldas ya faɗa ma Sarauniya suyi saurin kawar da ita kar ta basu matsala,

sai dai abinda basu saniba Aljani Mirza shine ya ɗauke Boka Shaldas lakacin da ya ga Azra ba komai ne ya firgita shi ba illa Aljani Mirza da ya gani tare da Azra;

sai kuma kuskuren da Sarauniya ta koma yi shine kai Azra gidan kurkuku aka haɗeta da Gimbiya Hibba ɗiyar Sarki Salman,


Gimbiya Hibba ƙanwar Mahaifiyar Yarima Azad ce bayan Sarauniya Mulaifa ta kashe
Gimbiya Nasrin itace Mahaifiyar Azad

lokacin Gimbiya Hibba na bedroom ɗin Nasrin jin ƙarar ƴar uwarta ya sa ta fito ta iske Mulaifa ta kashe Gimbiya Nasrin ta ɗauko Azad za ta fito da shi wata uwar ƙara Hibba ta yi tayo ƙan Mulaifa kafin ta ƙaraso Mulaifa ta jefeta da tsafi ta yan ke jiki ta faɗi sumammiya, kana ta sa aka kai Hibba gidan kurkuku;

Azra ce ta riƙo hannun Hibba ta na cewa "ki taimaka min da ruwa." Ruwa Hibba ta kawo ma ta sannan ta koma gefe ta na son Azra ta yi bacci akwai binciken da ta keson yi sosai akan yadda za ta sa Yarima Azad ya rinƙa shigowa gidan kurkukun idan ba haka ba babu yadda za'ayi su kawar da da Mulaifa

gashi iya binciken da ta yi tun kawo Azra ta ga Azad da Azra sai sunyi aure sannan ko zai samu mulkar ƙasar Misra......


paid book

Free page


𝐏𝐀𝐆𝐄5


______Azra na shan ruwan wani bacci ya gaba da ita murmushin Hibba ta yi kana ta jawo wani ɗan ƙaramin akwati ta buɗe wasu abubuwa ta fara karantawa ta ke wani tsoho fito cikin akwatin ya na cewa "yake Gimbiya Hibba a halin yanzu ba bu abinda zan iya yi miki sai dai ki nemo Aljani Mirza da ya ɗauke Boka Shaldas akwai wata sarƙa dake jikin Boka Shaldas ya ɗauko miki idan ya kawo miki ki saka wannan abin ajikin sarƙar hannu ta sa ta karɓe abin idan ke saka ki murza ta da kanta zata ɓace ta je gurin Yarima Azad, idan ta isa hayaƙi zata koma ta shiga jikinsa da kansa zai rinƙa shigowa gidan kurkuku batare da Sarauniya Mulaifa da sani ba amma idan keyi aiki da sarƙar yadda ya kamata." Ya na gama faɗar haka ya shige cikin akwatin ya ɓace;

tunani Hibba ta shiga yi ta ina zata fara neman Aljani Mirza don sun rabu akan ita zata idar da aikin
ganin wankin hula zai kaita dare dole ta tashi ta fara neman hanyoyin da zata bi wani tunani ne ya zo mata da sauri ta ɗauko wani baƙin mayafi ta buɗe ta fara karanta wasu abubuwa nan da nan ta ɓace ba ta bayyana ko ina ba sai bakin ƙofar wani gidan dutse,
wata guguwa ce ta ɗauke ta sai cikin gidan Aljani Mirza ne zaune sai Boka Shaldas da ke ɗaure sai azaba yake sha ga wasu ƙananan Aljanu ta buɗe baki za ta yi magana Aljani Mirza ya ɗaga mata hannu tare da miƙa mata sarƙar ya na cewa "kiyi gaggawar komawa don komai zai iya faruwa ga wannan duk lokacin da ki ke son ganina da ke taɓa sa zan baiyana agareki." ya na gama faɗar haka guguwa ta ɗauke Hibba ba ta aje ta ko ina ba sai tsakiyar ɗakinsu ita da Azra, har lokacin bacci Azra ke yi

da isowarta ta yi duk abinda wannan tsohon Aljani ya umurce ta sarƙar bata tsaya ko ina ba sai ɗakin Azad ya na kwance ya na bacci ta isar sarƙar ta koma hayaƙi ta shige jikinsa,

Sarauniya Mulaifa duk abin duniya ya dame ta halwar tsafinta ta shiga tana bincike inda Boka Shaldas ya ke amma abu ya gagara ƙarshe ma sai ɗakin ya kama da wuta,

hankalinta ya tashi sosai wata baƙar riga ta saka ta tsafi ta busa wani ƙahu ta ɓace sa wani ƙasurgumin daji mai masifar duhu da hakukuwa idan kai ba jarumin gaske bane to iya duhun dajin ma ya isa ya firgita ka, haka ta ci gaba da tafiya babu alamar tsoro atare da ita bata za tsaya ko ina ba sai wani gida da aka zagaye da duwatsu sai wuta dake ci saman gidan kai da gani kasan wutar tsafi ce,


tun bakin ƙofar shiga gidan ta fara cire kayan jikinta tsirara ta shiga haihuwar uwarta Boka Darbuzu na zaune saman wani gadon tsafi tun shigowar ta dajin ya san da zuwanta ya san yau zai ja kaya saboda ya daɗe bai kusance ta ba, tana shigowa ta yi cikin jikin Boka Darbuzu rungume meta ya yi suka shiga aikata masha'a ta darzu hannun Boka Darbuzu sai da komai ya lafa kana ya ce "nasan duk abinda ya kawo ki yanzu kije zuwa gobe ki dawo zan baki duk abinda ki ke so." Shiru ta yi saboda ta san halin Boka sarai zai iya yi mata komai yanzu don kawai ya koma kusantar ta ne shi ya sa ba ta zuwa wurinsa sosai sai dai Boka Shaldas shi kuma cikin bayinta ta ke ba sa ya Sha shagali amma ba komai indai buƙatar ta zata biya

komai zata iya yi



Free page ya kusa ƙarewa
Duk wacce ke son cigaba da karantawa

sai ta biya300 Account name zainab Abdullahi taj bank 0002129023

Page 6



_______Ta na wanann zancen zuci ne har ta koma cikin Masarauta,

Azad kuwa falkawa ya yi da ga bacci banɗaki ya shi ga ya watsa, ruwa kana ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

2 Comments On YARIMA AZAD
avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Much appreciated

avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Very good

Please Login or Register in order to submit comment