Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko don ta shigo ɗakinsa ya kamata ya yi mata magana, wai shi Sarkin miskilanci,
harta isa ɗakinsu Hibba na zaune ta na karatun littafin tsafi, ko da ta ga yanayin Azra batayi mamaki saboda ta san halinsa ida kwana Azra zatayi ɗakin bazai mata magana ba, indai ba ita ta yi ma sa magana ita ma sai ya ga dama zai amsa,


batayi ainu ba ta ji Azra ta faɗa jikinta ta na kuka, ba ta kula ta ba, saida ta yi shiru don kanta kana, ta ce "kiyi haƙori ƴata na san Azad ya yi miki halinsa, amma ai ke za ki canza shi da kanki zai fara magana, amma sai ke rinƙa danne fushinki, yanzu ki kwanta kamar baki da lafiya duk dare ya yi ina ganin sa ya shigo duba lafiyar mu, sannan ya fita to yau bazanyi bacci ba, zan zauna ina kuka ina jijjiga ki kamar bakida lafiya sosai, tabbas indai ya na sonki to zai ɗauke ki zuwa ɗakinsa ya ba ki magani ya kula da ke sosai, har sai ya ga ke samu sauƙi."


"To yanzu ta ya hakan zata faru kesan ya na da mugun wayo zai gane lafiyata lau fa.?"

"Ai abu ne mai sauƙi ki shanye wannan yanzu jikinki zai ɗau zafi, zazzaɓi mai zafi zai sauko miki."

Wasu ruwa ne cikin kofi ta bata ta shinye kana ta kwanta nan da nan jikinta ya ɗau zafi zazzaɓi ya rufe ta,


Boka Shaldas ne shigo ɗakin Mulaifa a haukace, kwance ya sa me ta, kan bed ta na hutawa, jin motsin mutum ya sa ta ɗagowa ta san ba kowa bane Boka Shaldas ne,

"Lafiya ka zo min wannan lokaci.?"
"Ina lafiya kesan abinda ke faruwa kuwa.?"
"Ina sane ya akayi ne, kana da matsala da hakan ne.?" "Amma Mulaifa ke ban mamaki banda sha shanci ya za'ayi kesan Azad ya na ta re da Yarinyar nan amma ki ka kyalesu, sanan kesan duk Azad ya baiyana ta matsayin matar da zai aura ta mafalkinki ba zai taɓa cika ba.?"


"Waye ya faɗa ma hakan to Boka Darbuzu ya tabbatar min duk ban amince Azad ya aure yarinyar ba to burina bazai taɓa cika ba, to kai miye matsalarka da hakan.?"


Mamaki ne ya cika Boka Shaldas amma sai ya basar ya ce "Banda matsla amma duk abinda ya biyo baya karki yi kuka da ni."

Wata dariya ta yi kana ta ce " na ji hakan ma bazata faru ba yanzu kasamo hanyar da za ka amshe ƙarfin ikon da Azad ya samu ko ya ya.?"

"Ina dai bincike koma da na samu zan kawo miki ƙarfin ikon kesan nasararki ta wace."
Ya faɗi hakan ne saboda ko ta halin ƙaƙa sai ya kifar da Mulaifa sai ta dawo wurinsa ta na roƙonsa, zaiyi amfani da wannan damar ya cinma burinsa akanta, saboda ya lura sam Mulaifa wawoyace, ya san tarko ne Boka Darbuzu ya ɗana mata amma zai bincaka ya ga ko menene saboda shi ma yanzu ya samu ƙarfin tsafi da lunka na Boka Darbuzu amma bazai nuna mata ba, zai yi maganinta,

"To Boka Shaldas sai anjima ina son in huta ne." Badamuwa na tafi ki huta lafiya."
Kana ɓace da ga ɗakin,
ɓangaren su Hibba kuwa na ta ganin lokacin zuwan Azad ya yi ta fashe da kuka ta na jijjiga Azra,
haka ya shigo ya same su abin ya bashi mamaki ɗazu fa ya ga yarinyar nan marar kunya me ya sa meta ne, ya ke tambayar kansa,

ta ko wa ya yi har inda ta ke kwance ya sa hannu cak ya ɗauke ta ya juya ya fita Hibba kuwa daɗi kamar ta taka rawa saboda shirinsu ya tafi dai -dai,

bedroom ɗinsa ya kaita ya aje kan bed kana ya shiga toilet ya haɗa ruwan wanka ya dawo ya na tunanin yadda zai cire mata kaya, ganin wanken hula na neman kaisa dare dole ya rufe idanunsa ya fara cire mata kaya Azra duk da ta na cikin zafin zazzaɓi amma tsoro ya cika ta saboda jin mutu na rabata da kayan jikinta, Azad ido rufe ya kai hannu zai cire mata riga karaf hanunsa yakai saman:......

To anan na kowo ƙarshen free page Hajiya ki biya Kisha karatu labarin yanzu aka fara soman taɓe ni

writes bye pinky Darling 🌷
~Matar Jay~




👑YARIMA AZAD 🤴

Hot love 🌹❤️& romantic story 💋💄

Story & writes by Zainab Abdullah
Pinky Darling 🌷)
((Gimbiyar jajirtatu 👸))

Paid book



https://whatsapp.com/channel/0029VacH5RqG8l5MFep9AI3q
____________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

_______________________________________

*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝




Bismillahi Rahamanin Raheem 💫

Page 11


****** Buɗe ido ta yi da sauri jin saukar lallausan hannunsa akan na shanunta, ganin idonsa ta yi rufe sai ƙoƙarin cire mata riga ya ke, dariya ce ta kwace mata, hakan ya yi dai-dai da buɗe idonsa da ya yi, su na haɗa ido ya kawar da kansa ya ta shi cikin ba da umarni, ya ce "Ke! marar kunya ta shi kije zuwa wanka." Ya juya ya fita batare da ya ji abinda zata ce ba,


ita mamaki ma ya bata da bata yi dariya kenan da shi zai mata wankan, jiki ba ƙarfi haka ta lallaɓa ta shiga toilet ta yi wanka da ruwan da ya haɗa mata, sai tashin ƙamshi su ke, lallai Azad akwai tsafta da son ƙamari,


ta jima a toilet ɗin kafin ta fito, gaban mirror ta je ta shafa mayunkansa masu masifar ƙamshi da tsada, kana ta koma kan bed da niyar mai da rigarta amma bata gani ba, wata rigar bacci ta gani baƙa iya guiwa da ɗan ƙaramin pant, rigar ta burgeta,


sa ka rigar ta yi kana feshe jikinta da turarensa masu ƙamshi, kana zauna kan sifa saboda kanta da ke wani irin sarawa, jikinta ya ɗauke makarkata, sai rawar sanyi ta ke,


ta na cikin wannan hali ne ya dawo ya yi shirin bacci ga dukan alama wanka ya yi sai baza ƙamshi ya ke, shi ya ma manta da ita ya zata ta koma ɗakinsu, ya na kallonta da niyar masifa amma sai ya yi shiru ganin yadda jikinta ke tsuma, kafin ya ƙarasa wurinta ta faɗo kan sofa idanunta sun rufe ta dena motsi, da gudu ya ƙaraso wurinta ya na kiran

"Azra! ke Azra! ke buɗe idonki mana, meke damunki Please tell me." Haka ya ke ta magana shi kaɗai saboda lokacin ko lumfashi bata yi,

jikinsa ne ya shiga wata irin girgiza ya rufe idanunsa sai ga wani blue haske na fita jikinsa zuwa jikinta, jiji yoyin jikinsa duk sun firfito radau kamar wanda ya ɗauke wani ƙaton ƙarfe ko dutse,

a hankali ta fara buɗe idanunta ta na kallonsa dishi-dishi, rufe idanunta ta koma yi kana ta buɗe, har lokacin ya durƙushe idanunsa rufe, wannan haske bai dena fita jikinsa ba, Hibba ta faɗa mata Azad bai iya tsafi ba amma ta ina ya samu wannan ƙarfin ikon na manyan Sarakunn Aljanu masu ji da kansu,

wani bacci ne ya ɗauke ta lokaci guda, a hankali jikin Azda ya fara dawowa dai-dai ya jima wurin kafin ya tashi kansa na wani mugun ciyo, hannu ya sa ya dauki Azra zai maida ta ɗakinsu, kamar da ga sama ya ji muryar wani mutum mai cike da izza da ƙasaita, ya na cewa "Yarimana karka maida ta dakin kabar ta ɗakinka, shine samun maslaha a wurinka, karka yadda kayi nesa da ita, wannan umurni ne ba shawara ba."

Tsit ya ji muryar ta tsaya amma bai san inda ta fito ba, bai yi gardama ba ya juya ya kaita kan bed ya kwanatar kana shima ya kwanata ne sa da ita, ya na tunanin "wai me ke shirin faruwa da rayuwarsa ne, to days ya na yawan mafalkai masu rikitarwa, koma da Azra da wani kyakkyawan Basarake, su na zaune cikin wata ƙasaitacciyar fada mai cike da kayan more rayuwa,


duk abinda ke cikin fadar na zallar zinari ne har ginar masarautar, ga wasu manyan mutane kamar dutse da ke gadin cikin Masarautar da wajen ta,

shi da Azra na zaune saman wata haɗaɗɗeyar kujera ta zinari, sunyi shiga ta alfarma, wannan kaykkyawan mutumin ya na riƙe da hannun wata kaykkyawar mace, da ke masifar kama da shi,

ya na ma sa wasu maganganu da bazai iya fassarawa ba,"

ya na wannan. tunani ne bacci ya ɗauke sa,
ɓangaren Hibba kuwa ita ce ta sa ka Azra wannan ciyon ta re da ɗauke mata lumfashi, saboda ita binciken da ta yi ta gano Azad ya sa mu ƙarfin iko, kuma idan har bata yi gaugawar sa ka shi ya yi amfani da wannan ƙarfin iko ba to Boka Darbuzu ko Boka Shaldas zasu iya samun nasarar kwace shi batare da sun sha wahala ba,

amma dole ta yi gaugawar koya ma Azad amfani da shi saboda baya buƙatar tsafi ƙarfin ikon da ya samu ya fi kowane tsafi girma da kuma haɗari,

amma ta yaya zata iya haka dole ta na buƙatar kusanci da shi saboda Azra kaɗai bazata iya ba,

Azad kuwa wani mugun mafalki ya yi da ya rikita shi ya hita hayyacinsa, ya kama Azra ya riƙe sai cusa kansa ya ke ciki rigarta, jikinsa na tsuma, dai-dai lokacin Azra ta falka ta ji yadda jikinsa ke tsuma ya yi zafi ga dukan alama mugun mafalki ya ke, saboda ta ga kamar tsorace ya ke,

ba ta ankara ba ta ya kamo bobs ɗinta da ƙarfe ya riƙe, kawai sai ya fashe da kuka,
ta na so ta tashi amma ya riƙe ta ga azabar ciwon da bobs ɗinta ke yi da ya riƙe, hannu ta sa saman kansa ta rufe ido nan da nan ya fara sauke ajiyar zuciya, ya jima haka nan wani zufa ya wanke ma sa fuska, a hankali ya buɗe ido ya gansa cikin jikin Azra ga hannunsa cike da bobs ɗinta,

janye hannunsa ya yi da sauri saboda kunya ta kama sa amma sai ya basar ta re da tashi kan bed ya shige toilet ya yi wanka ya jima haka kafin ya fito ya sauya kaya, kana ya kwanta ya juya mata baya,

ya na tunanin mafalkin da ya yi da maganar da muryar ɗazu ta faɗa ma sa, da ma haka zata faru shi ya sa akace kar ya yi nesa da Azra, wai me ya sa don lokacin da ya shiga wannan hali ita ke helpen ɗinsa, ton kafin su haɗu ya sha ganinta a mafalki,

me hakan ke nufi, wannan murya ya koma ji ya na cewa " baka da amsar wannan tambaya, amma kaje wurin Gimbiya Hibba da ka ɗauko gidan kurkuku zata am sa ma wasu tambayoyi."

Da ga haka ya ji shiru waigawa ya yi ya ga ko Azra ta je amma sa yai ga bacci ta ke sosai, ta sa ka ɗan ya tsanta guda cikin baki, kamar mai shan nono, sosai ya zuba mata ido ya na kallo ta burge shi sosai, kamar ya jawota jikinsa ya rungume su yi bacci,

ita kuwa Azra cikin magagin bacci ta wuntsila sai cikin jikinsa, wata ajiyar zuciya ya sauke ya sa hannu ya zagaye jikinta da shi dayan kuma ya na shafa dogon gashin kanta mai laushi,

Writes by 𝓟𝓲𝓷𝓴𝔂 Darling 👄
~Matar Jay~





👑YARIMA AZAD🤴

Hot love💝🌹
&
romantic story 💋💄

Story & writes by
Zainab Abdullah
pinky Darling 🌷
((Gimbiyar jajirtatu 👸))

Paid book 500

masu roƙon aƙara musu free page gashi nan amma da ga wannan ba ƙari.
________________________________


https://chat.whatsapp.com/F7S7KjlbquBL30fuhZidFb
___________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝



Bismillahi Rahamanin Raheem 💫

Free page 12


____Wani bacci mai nauyi ne ya yi awon gaba da shi, washegari ƙarfe goma ya shirya don ko da ya tashi bai ga Azra ba, ya haɗa copey ya sha kana, ya nufe ɗakinsu, Hibba ta amsa mai tambayoyi,

ko da ya shiga Hibba na zaune ta na gyara ma Azra gaahinta, wuri ya samu ya zaune ba ta re da ya amsa gaisuwar da Hibba ke ma sa ba, ya ɗan jima kafin ya buɗe baki ya ce "wurin ki na zo ki ce ma wannan marar kunya ta fita."

Ton kafin Hibba ta yi magana, Azra ta fita ko kallonsa batayi ba, zatayi maganinsa idan ya shi go hannu,
Hibba ce ta ce "Me ke tafe da kai.?" " Da ma jiya ne na yi wani mafalki." ta ce "ina jinka."
Nan ya kwashe komai ya faɗa mata har matar da ya ke gani mai kama da shi sosai,
ba ƙaramar kaɗuwa Hibba ta yi ba da jin abinda Azad ya faɗa indai hasashenta gaskiya ne to Nasrin ta na raye bata mutu ba,

ta na wurin Raihan, kenan to ya akayi hakan ta kasance, Azad ne ya katse mata tunani ya na cewa "Please ke wacece.?" Wata ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta ce "idan lokacin ya yi zaka san ko ni wacece,

sai koma amsar tambayoyinka, abu na farko idan har kana son Azra ko ba ka sonta dole ka aure ta, saboda itace inuwarka, idan har baka aureta ba to tabbas Sarauniya Mulaifa zatayi nasara akanka ita da Boka Darbuzu,
don bazan sa Boka Shaldas ba, saboda burinsa akanta ya ke ba akanka ba,

sai abu na biyu tabbas wannan matar da ka ke gani Mahaifiyarka ce sai dai abinda ya ɗaure min kai ta ya haka ya kasance, idan har muna son yin nasara tu dole ka bamu haɗin kai, abu na uku ƙarfin ikon da ka samu dole ka koyi sarrafa shi ta kowanne fanni, idan ba ayi saurin fara aiki da shi ba komai na iya faruwa, ba iya Boka Darbuzu ba hatta mayan Aljanu da ƙanana su na neman sa,


ajiyar zuciya ya yi kana ya ce "yanzu ya za'ayi aure na da marar kunyar nan.?" "Wannan aikinka ne kai za ka gabatar ma Sarki ita matsiyin matar da zaka aura."

"Ok ita Kuma fa ni zanyi magana.?" "Sosai ko idan kayi mata magana ka faɗa min zan ida shawoma kanta." Bai ce komai ba ya fita bakin ƙofa ya ganta, wata harara ya galla mata kana ya fita wai wannan marar kunya za'a shawo ma sa kanta,

tsaki ya ja kana ya shige bedroom ɗinsa, ya yi shirin tafiya fada don bazai yi mata magana ba, kuma dole ta amince da aurensa, da ga baya ya samu wacce ya ke so ya sake ta, da wannan tunani ya gama shiri ya nufe faɗa,


ya ko yi sa'a ba kowa faɗa sai da ya gaida Mahaifinsa sanan ya rungume shi sai da su ka ɗan taɓa hira kafin ya ce "Abeey na samu mata fa." "Haba! wai da gaske My Son ƴar sarkin ina ce haka mai sa'a.?"

"Ba ƴar kowa bace Abeey." "To ina ta ke ita da Iyayenta.?" "Abeey marainiya ce bata da kowa sai ƙanwar Mamanta."

"Badamuwa Azad farincikinka shine ni keso,don haka sai ko taho ta re da Yarinyar agabatar da ita cikin Masarauta asaka ranar aure." "Godiya ni ke Abeey."

Bayan ya koma ya sanar da Hibba duk yadda su kayi ta ce to ya yi magana da Azra ya ce mata shi bazai yi mata magana ba, kawai ita ta faɗa mata gobe ta shirya zai aiko mata da kaya zasu je fada,


ita Hibba ta na mamakin irin miskilanci da izza irin na Azad kamar ɗan Sarkin Aljanu,
ko da ya ke ruwa ba ya tsami banza, Azra ce ta fito da ga toilet duk ta ji abinda suke magana, amma ta sa ma ranta bazata je ba idan har bai mata magana da bakinsa ba duk da ta na maasifar sonsa,


Hibba ta yi mata bayanin komai kuma ta amince don burinta kenan ta aure Azad,
wasa-wasa har dare ya yi ta na jiran Azad ya zo ya yi mata magana, amma shiru har Hibba ta yi bacci ta barta, ka sa haƙori ta yi ta shirya ta ta je ɗakinsa zaune ta tarar da shi kan sopa ya na danna wayarsa,

ya ji shigowarta amma ko ɗagowa bai yi ba,
wuri ta samu ta zauna kana ta kalle sa ta ce
"Kai Yarima nifa bazan aure ka ba, saboda haka sai kaje zuwa neman miskila irinka, don ni bazan iya aurenka ba kafiye izza da ji da kai kamar kaine Sarki, kaje kace ni zaka aura to kaje kace ni bana sonka!."

Tun da ta fara magana danna wayarsa ya ke amma jin kalmar bata sonsa ta dakesa sosai,
hannu ya sa ya fisgota sai da fuskarta ta buge da hanunsa, kana ya ce "Ke ƙaramar marar kunya angaya miki nima sonki nike to ko da wasa bazan taɓa sonki ba, kuma dole ki aure ni idan na zama sarkin Misra sakinki zanyi in aure wata wadda tafiki, ke har mace ce, to ko mata sunƙare babu abinda zanyi da ke sha-sha kawai, kuma aure ba fashi."


Ya na gama faɗar haka ya hanka ɗata ƙasa ta faɗi ta fashe da kuka mai ban tausai ga mari ga tsinka jaka,

"Ke!." Sai da ta tsorata, kana ya ce "rufe min bakinki maza wuce ki kwanta, ke cika min kunne da ihu." Jikinta na rawa ta nufi hanyar waje "Ke dawo anan za ki kwana." Sum-Sum ta je kan bed ta kwanta,

sai da ya kammala abinda zaiyi kana ya yi wanka ya yi shirn kwanciya, "Ke ta shi kiyi wanka don bazan kwanta da ƙazama ba." Azra ta ƙulu sosai amma da tuna da maganar Hibba sai ta yi kamar bata damu ba ta je tayi wanka ta shirya cikin kayan baccin da ta gani kan sopa,

kwantawa ta yi nesa da shi ta juya ma sa baya, shi dariya ma ta bashi, amma don ya tunzura ta sai cewa ya yi "Ke marar kunya juyo nan waye ya ba ki izinin kwanciya haka.?"

Shiru ta yi ta na turu ɗan ƙaramin bakinta, hannu ya sa ya ɓallar mata lips kana ya riƙe mata kunne ya ce" idan ina magana ki ka koma turo min wannan shigen bakin naki mai kama da na aku sai na.." Ya yi shiru ya sakar mata kunne ya kwanta,


itama kwanciya ta yi ta na mamakin hali irin na Azad, ita ma bacci ya ɗauke ta, yauma kamar jiya Azad ya fara mugayen mafalkai, jikinsa sai karkarwa ya ke, ya na wasu suratai,
Azra ce ta falka ta ga halinda ya ke ciki, sosai ya bata tausayi, rungumusa ta yi jikinta ta na shafar gashin kansa ta na wasu abubuwa har ya fara samun sauƙi, jikinsa ya dena rawa,

Ƙara shigewa jikinta ya yi ya na sauƙe ajiyar zuciya,


Writes by pinky Darling 🌷
~Matar Jay~



👑YARIMA AZAD🤴

# Hot Love 💝🌹&
#romantic 💋💄

Story & Writes by
Zainab Abdullah
pinky Darling 🌷
((Gimbiyar jajirtatu 👸))
Paid Book ₦500
_________________________________________
https://whatsapp.com/channel/0029VacH5RqG8l5MFep9AI3q
_________________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
__________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝


Bismillahi Rahamanin Raheem 💫


Page 14



_____Ƙarfe shida Azra ta ta shi ta koma ɗakinsu ta kwanta Azad kuwa sai goma ya ta shi ya yi wanka ya shirya cikin wasu sut blue ya masifar kyau gashin kansa ya sha gyara sai ssheƙi ya ke, abinci ya ci kafin ya ɗauke wasu kaya na alfarma ya shiga ɗakinsu Hibba, ya ajema mata kan bed ya na amsa gaisuwar da Hibba ke ma sa,

Azra ya kalla kana ya ce "Ke ina jiran ki waje kishirya minti goma kacal na ba ki." Ya juya ya fita, banza ta yi da maganar shi ta kwanta, Hibba ce ta "Ke Azra ta shi kishirya ko ba ki ji abinda ya ce bane.?" "Na ji kawai bazan je ba." "To bari in samo mai wata wadda zata iya su tafi ta re amma duk abinda ya biyo baya, karki kuskura ki faɗa min."

Toro baki ta yi ta shiga shiryawa da ma ta yi wanka, ita banda ta na sonsa da bazata ba, dogowar riga ce baƙa har ja ta ke ga ƙasa mai dogon hannu anyi mata ado da wane zane mai masifar kyau, saman rigar ya matse ta ƙasa kuma ya baje, sosai rigar ta ƙara fito da asalin kyaun Azra, sai wata hula itama baƙa ta sa ka ta gashen kanta ya baje bayanta,

janbaki ta shafa read ta murza kwalli, kana ta saka ta kalama masu tsini sosai, Azra ta fito sak Gimbiya, Hibba ce ta shiga ya ba irin kyaun da ta yi, kana ta feshe ta da mayunkan turaruka, kana ta rakata har parlo inda Azad Ke jiranta, ya shagala da kallonta sosai ta yi ma sa kyau, sai da ta ce "Idan bamu tashi tafiya ba zan koma ciki."

Basarwa ya yi kamar ba shi ba, ya tsare gida kana ya kama hanunta, su ka fita da fadawa da ke mu su rakiya, har fada sai bushe-bushi ake masu Camera aka fara haskesu da hotona, har su ka isa fada ta cika sosai, su kaɗai ake jira, manyan fadawa ne da su ka fara kaima Yarima gaisuwa shida Azra, kana ƙanana su ka kawo tasu gaisuwa, su na zabga mai kirari,

wurin Abeeynsa ya nufa ya durƙusa ya gaida shi kana suka rungume juna, kiran Azra ya yi itama har ƙasa ta gaida Sarki cikin girmamawa, kana Azad ya riƙa hanunta su ka zauna wurin na alfarma da aka ta nadar musu, sanan Waziri ya ta shi ya yi jawabi kana ya gabatar da Azra matsayin Suruka ga Masarauta Misira,


nan manyan Sarakuna da masu kuɗi da Sarki Mahir ya gaiyata su ka fara kawo ma Azad da Azra kyaututtuka masu ban mamaki, ciki hadda Sarkin Aljanu watun Raihan, saidai babu wanda ya gansa idan ba Azad da Azra ba wani zoben zinari ne mai ɗauke da harfin sunayensu Azad ya saka ma Azra, sai sheƙi ya ke ya haɗu sosai, kana ya saka ma Azad agogon azurfa, mai masifar kyau, shima mai ɗauke da harfin sunayensu,




kana ya tafiyarsa, Azra ta bishi kallo kamar ta san shi wani wuri amma ina ne, bayan an kammala liyafar da aka shirya musu kana kowa ya watse, Azad ya ja Azra su ka koma ɓangarensa, sai wata bai da kwaso musu kyaututtukan su, ta aje parlo, Azad wanka ya yi kana ya kwanta, da tunani fal aransa saboda Sarki ya ce "nan da sati mai zuwa za'ayi hidimar biki,


Azra ce da Hibba ta na nuna mata zoben zinari da wannan mutumin ya bata, ta na saffian ta mata kamaninsa, nan Hibba ta gane cewa Raihan ne ya zo wurin, tabbas akwai abinda ke shirin faruwa, amma zata zurfafa bincike ta gano kome mene, shirye shiryen biki ya kama Sarauniya Mulaifa hankalinta kwance, saboda Boka Darbuzu ya ce karta aikata komai sai an kammala bikin,


zasu fara aiwatar da ƙudirinsu, Boka Shaldas kuwa ya na nan ya na shirya ma Mulaifa gadar zare saboda ya gano Arjun ba ɗan Sarki Mahir bane ɗan Boka Darbuzu ne koma gaba ɗayansu babu wanda ya san da haka ba, saboda haka da Arjun zaiyi amfani wurin cinma burinsa,


sai da ya ga wata guguwa mai tsananin ƙarfe da manyan Aljanu sun shigo cikin Masarauta,ciki hadda Sarkin Aljanu Raihan kuma ya ga alamun zasuyi nasara amma sai ansha baƙin artabu, saboda su jinsin Musulmai ne, ga kuma Gimbiya Nasrin tsohowar matar Sarki Mahir Mahaifiyar Yarima Azad,


kenan ta na raye bata mutu ba, bayan gabansa Mulaifa ta shiƙeta, ya yi iya binciken da zai don sanin dalilin zuwan Sarki Raihan amma abu ya citura, da ya matsa ɗakinsa ya kama da wuta hankalisa ya ta shi sosai, amma bazai taɓa faɗama Mulaifa ba, saboda ta watsa ma sa ƙasa ga ido kawai zai cigaba da nuna mata ya na ta re da ita,


yau saura kwana uku bikin Azad da Azra manya manyan Sarakuna da ƴan kasuwa harsun fara isowa, Azra kuwa gyaran jiki ta ke samu wurin Hibba ba na wasa ba, ta ƙara wani kyau mai ɗaukar hankali, jikinta sai shiƙi ya ke, Azad ne ya shigo ɗakinsu ya miƙa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On YARIMA AZAD
avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Much appreciated

avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Very good

Please Login or Register in order to submit comment