Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito ya shirya cikin ƙananan kaya masu masifar kyau da ɗaukar hankali, feshe jikinsa ya yi da turare kan ya fita, zuciyarsa na ƙara ƙwaɗaita ma sa son ganin kyakkyawar fukar Azra,
bai zame ko ina ba sai gidan kurkuku duk inda ya gifta sai ka ga bayi na zubewa ƙasa su na kwasar gaisuwa, sai dai ya ɗaga mu su hannu idan ya ga dama amma bazai yi mu su magana ba, dai-dai ɗakin da ya ganta ya je ya tsaya, sarkin gida ne ya zo ya buɗe masa ɗakin ya san halinsa bazai yi magana ba, cikin wani cool voice ya ce "fito min da duk wacce ke cikin ɗakin."
Ya ƙarashe maganar kamar wadda aka cilasta, jikin Sarkin gida har karkarwa ya ke wurin buɗe ɗakin, Hibba na zaune ita da Azra su na fira ganin an buɗe ɗakin abin ya ba ta mamaki saboda iya rayuwar da ta yi ko abinci ta taga ake bata, har zuwa lokacin da aka kawo Azra, Sarkin gida ne ya katse mata tunani " Mai girma Yarima mai jiran gado na son ganinku a waje." Azra ta da fe ƙirji ta na zaro idu Hibba kuwa wani shu'umin murmushi ta yi kana ta ja hannun Azra suka fito, tsaye su ka gansa ya zuba hannuwansa cikin aljuhu iskar da ke kaɗawa wurin ta sa gashin kansa kaɗawa har ya na rufe ma sa idanu,

har ƙasa su ka durƙusa su na kwasar gaisuwa, a hankali ya jiyo ya kalli su ɗaya bayan ɗaya kana ya juya ya fara tafiya, Sarkin gida ne ya ce " kai banzaye kun samu gata ku ta shi ku bishi idan ba haka ba kashenku ya bushe." Zabura su ka yi da sauri su ka bi bayansa,

Lokacin ba kowa duk an fita da su cikin Masarauta wurin aiki sai dare ake mai da su,

Sarkin gida ku ma ba ƙarimin daɗi ya ji ba ganin Yarima Azad ya fitar da ƙanwar Mahaifiyarsa gidan kurkuku, ba ta re da ya san ko ita wacece ba awurinsa, ya san komai daɗewa watarana gaskiya za ta yi halinta,
makircin da Sarauniya Mulaifa ke aikatawa cikin Masarauta ya kusa ƙarewa, saboda zaluncinta ba iya bayi ba har ga matan Sarki duk wadda ya aura to sai ta ga bayanta, ga shi ba ita ce matarsa ta farko ba Gimbiya Nasrin itace matarsa ta farko ɗiyar Sarkin Hindu, amma sai da ta ga bayanta lokacin da ta haife Yarima Azad,


ɓangaren su Yarima kuwa Hibba ce ta murza zoben hannunta nan da nan su ka ko ma kiyashi su na biyi da Yarima har cikin ɓangarensa ita kuma Azra ba tasan abinda ke faruwa ba ita dai tafiya ta ga su na yi har su ka iso, dalilin da ya sa Hibba ta yi haka kuwa shine ta san dole Sarauniya Mulaifa ta waiwayo ta kansu, ku ma cikin bayi dole sai an samu ma su zuwa su kai mata labari, amma da tayi haka ba bu wanda ya gansu,

wani ɓangare da ga cikin sa shensa ya nu na mu su alamr nan ne masaukinsu, bedroom ɗinsa ya shige su ma ciki ɗakinsu su ka shi ga cikin jin daɗi, Azra ce ta ka sa haƙora ta ce " ya ke Hibba wai da ma haka Yarima ya ke da tausayi da kirki amma sai inji bayi na zaginsa wai ɗan iska ne mazinaci, wai ya na lalata mu su yara.?" Hibba ta ce " ya ke Azra ke yi sa ni cewa Yarima ba haka ya ke ba hasli ma Sarauniya ce ke sa ana kamo mata yaran bayi da sunan Azad ta sa Boka Shaldas ya yi amfani da su kana ayi mu su barazana, duk wanda ya tambaye su su ce Yarima ne ya yi lalata da su idan ba haka za'a kashe su da Iyayensu, kuma ta na nayin wannan abin ne don kar Yarima ya samu karagar mulkin ƙasar Misira, amma kuma ta yi mantuwa da ƙa idar masarautar nan ba za ka mulke ta ba har sai ka samu matar da ka ke so za'a ɗaura muku aure da ta yi shekara ɗaya ba ta haihu ba to ba za ka iya mulkar ƙasar Misra ba,
na biyu kuma duk matar da ka aure duk jekadiya ba ta kawo kyalen jinin budurcinta ba to ba za ka zama sarkin Misira ba."
Ajir zuciya Azra ta sauke jikinta ya yi sanyi sosai zuciyarta ta kamu da tausayin Yarima Azad sosai, gyara zama ta yi saman bed ta na kallon Hibba kana ta ce "amma Hibba ina Mahaifiyarsa ku ma ina ɗangin Mahaifiyarsa.?" "Azra ke nan wannan dogon labari ne amma watarana zan baki tarihin kowaye Yarima Azad."

Shiru ta yi saboda ta ƙagu ta san waye Azad ku ma miye dalilin da ya sa Gimbiya ke ma sa haka ku ma ya aka yi Hibba ta san waye Azad,

"Amma Hibba da ke taimaka min ke faɗa min waye Azad ke ma wacece ke wata ƙila zan iya taimakama ma sa." Murmushi Hibba ta yi da ma haka ta ke son ji

kana ta fara magana kamar haka "Ni........




Free page ya ƙare duk mai Son cigaba sai yabiya 300


______Ni ƙanwar Mahaifiyarsa ce sunana Hibba bin Arif ni ƴace ga Sarki Arif sarkin ƙasar Hindu mu uku ne wurin Iyayenmu Arishi ne na farko amma ba mahaifiyarmu ɗaya ba sai Yayata Nisrin sanan ni, muntaso cikin gata da kuma da soyayya amma sam Yaya Arishi baya ƙaunarmu ya tsanemu banda kyara da tsangwama ba bu abinda muke samu wurinsa, ana haka ne har muku girma ni da Yayata Nisrin kyakkyawa ce ajen farko saboda duk kyaun da ki ka gani tattare da ni to ko rabin na Yayata banyi ba haka ƴan ƙasashen duniya ke kiran Yayata Sarauniyar kyau, saboda sun tabbatar ba bu macen da tayi kyanta, bayan ta cika shekara ashirin da haihuwa Sarkin ƙasar Misra ya zo neman aurenta lokaci guda ta amince kowa ya yi mamakin yardar da ta yi da shi saboda sarakuna da ɗiyan sarakuna masu ji da mulki da tarin dukiya sunyi ta zuwa neman aurenta amma bata kula su ba, sai Sarki Mahir shima ba lafiya kyakkyawa ne na gaban kwatance,
haka akayi shagalin aurensu kana muka tafi ƙasar Misira wurin kai Yayata, watanmu ɗaya ana wani sabon shagali kana mu ka dawo gida, shikara huɗu da aurensu sai ga Sarauniya Mulaifa ɗiyar Sarkin ƙasar Sin ta bayyana matsayin matar Sarki Mahir ta biyu,

hankalin Yayata ya yi matuƙar tashi saboda gaba ɗaya ta juyar da hankalin Sarki baya kula da Yayata Mulaifa matsafiya ce ta gaske,

gashi Yayata sam ba ta harakar tsafi sam bata iya ba ni ce kawai na iya, tun shigowar Mulaifa ta fahimci Yayata na da ciki ta ɗauki alwashin salwantar da cikin har Yayata, baza ta bari da rai ba, ga shi lokacin mahaifiyar mu ta mutu dole na dawo wurin Yayata, ina kula da ita nan na fara walwale duk wani mugun abinda Mulaifa ta shuka, hankalin Sarki ya dawo kan Yayata ita da abinda ke cikinta,

ganin haƙarta bata cinma ruwa ba ya sa ta nu na ta aje makaman yaƙinta, sosai ta shiga ba Yayata kulawa amma ni sam ban yarda da ita ba saboda ina ganin tsana ƙiri-ƙiri cikin idanunta, ana haka har cikin Yayata ya isa Haihuwa ta santalo ɗanta kaykkyawa ita da shi kamar an tsaga kara, nan da nan Masarauta ta rikice da marnar samun haihuwar Yarima, to anan ne Mulaifa ta ida mugun nufinta akan Yayata ta shigo ta same ta kwance ta na bacci ni kuma ina bedroom ta re da Yarima Azad ta sa hannu ta shaƙeta har sai da ta mutu tun ta na ihu har ta ɗena saboda ba bu wanda zai jiyota, kamar a mafalki na ji Yayata na kiran sunana fituwar da na yi, na ci karo da Mulaifa ta sa hannu ta fisge Azad ta kira Sarkin fada ya kaini gidan kurkuku sannan ta sa akayi sanarwar Gimbiya Nasrin ta mutu sanadiyar ciyon na ƙuda da bai saketa ba, ba bu yadda ba tayi ba ta halakar da Azad amma abu ya ga gara saboda na tattara rabin ƙarfin tsafina na mallaka mai sannan ga Aljani da ke ta re da shi saboda shi ya taimaka ma Nasrin lokacin da za ta haife Azda tun da ya ga Azad ya zo duniya ya ɗauke soyayyar duniya ya ɗora ma sa kuma ya yi alkawarin kulawa da shi har tsawon rauwarsa, ba bu kalar azabar da Mulaifa ba ta gwada ma Azad ba amma bai mutu ba har ya girma lokacin ita kuma ta samu cikin Arjun sai dai Sadauki Arjun ba ɗan Sarki ba ne ko ita ba ta sa ni amma Boka Shaldas ya sa ni ƙin faɗa mata ya yi saboda shi ma akwai burinsa da ya ke son cikawa akanta, da ko ita ba ta sa ni ba Arjun ɗan Boka Darbuzu ne ko shi boka bai san ɗansa ne ba, Sarki Mahir ko biɗata bai yi ba saboda Mulaifa ta rufe ma sa baki iya tsawon shekarun da na yi gidan kurkuku bai taɓa zuwa ciki ba, kuma Yayanmu Arishi ya san duk abinda ke faruwa amma ya yi amfani da ƙarfin tsafinsa ya hana Mahaifinmu ne man mu balle ya san halin da muke ciki, sanan ba iya wannan ba akwai wani ɗan Sarkin Aljanu mai suna Raihan da ya so auren Nasrin amma aka ba shi haƙori saboda ba jinsumu ba ne sai dai bai rabuda Yayata ba har bayan aurenta idan ta na bacci ya na zuwa ya sadu da ita yanzu haka Azad ya na cikin tsaka mai wuya saboda rabim haliltarsa ta aljanu ce rabi kuma ta mutane ya na ta re da Yarima Azad saboda ƙaunar da ya ke ma Yayata ta koma kansa akwai lokacin da zai baiyana nayi iya binciken da zanyi amma na kasa gane yaushe zai baiyana ko me zai kawo shi, na dai ga wata babbar ƙura da masifa da tashin hankalin da zai faru har ma da mutuwar.... ƙofar ɗakin aka toro dole ta yi shiru batare da ƙarasa maganar ba, ba kowa bane Azad ne ɗauke da kayan sawa na alfarma ya aje kan gado ya fita, ajiyar zuciya Hibba ta sauke ta re da da fa kafaɗar Azra da ta bi Azad da kallo, "Azra wannan shine cikakken tarihinmu sai kuma mujira abinda zai faru nan kusa, saura ke Ina son insan ko ke wacece.?"

"Labari ne mai tsayi watarana zan faɗa miki." "To badamuwa." Azra ta ce "Gaskiya
Gimibiya Hibba tun da na ji labarin Azad wata irin soyayyarsa da ƙaunarsa sun mamaye min jini da zuciya."
Murmushi Hibba ta yi dama haka ta ke son ji yanzu ta san Azad ne ya rage

"To Azra ina fatan shima ya soki kamar yadda ki ke sonsa."


Muje zuwa yanzu ma aka fara labarin
Ɗaya ma farin ƙidaya

Ku kasance tare da ni domin jin yadda za ta kaya shin Yarima Azad za aure Azra
Sarauniya Mulaifa zatayi nasara akansu ko ya ya







👑 YARIMA AZAD🤴


Love and romantic story


Story and Writes
bey Zainab Abdullahi
pinky Darling 👄 ~matar jay~

((Gimbiyar jajirtattu 👸💮))
Free page ya ƙare fa daga yau duk mai son ciga da karantawa ya biya ɗari uku kacal

Account number 0002129023 zainab Abdullahi

https://whatsapp.com/channel/0029VacH5RqG8l5MFep9AI3q
________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
____________________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
Allah ya ƙara yi muna jagora ya ƙara haɗa kanmu😍


Mage ke dame ni to ga shi nan na yi
na huta asha karatu lafiya😜😂



PAGE 8

__***** Haka su ka cigaba da hira amma sam hankalinta baya jikinta ya ma wurin Azad,

wata ƙara su ka ji da mai razanarwa, da gudu su ka fito ji wani gurnani su ka yi ta ɓangaren Yarima da saura Hibba ta ja hannun Azra su ka shiga ciki Azad ne kwance duk rabin haliltarsa ta sauya zuwa ta aljanu, ga wasu fuka fukai manya sun fito, ga yatsunsa sun ƙara tsayi idanunsa sun kuma kamr wuta, ya na son ta shi amma fuka fukai sunyi ma sa nauyi da ka gansa kasan ya na cikin wahala gwada ta shi ya yi amma abu ya ga gara, Hibba ta yi duk abinda ta iya amma ga banza, Azra ce wasu hawaye ma su kama da walƙiya su ka fara fitowa cikin idunta, ta ɗaga hanunta sama ta juya sai ga wata uwar tsawa gifta ta re da jefo mata wata buta ta azurfa, da wusa fararen ruwa, ta kawa ta yi har inda Azad ya ke ta buɗe butar ta fara tsiyaya ma sa ruwan cikin baki, nan da nan jikinsa ya ɗauki rawa, cikin minti goma, jikinsa ya dawo nurmal, wani bacci mai nauyi ya ɗauke sa, wata tsawa aka koma yi butar ta yi sama ta ɓace,. Azra ta yanke jiki ta faɗi
Hibba ta ɗauke ta su ka koma ɗakinsu,

cike da mamakin irin bai war Azra, dai binciken da ta yi ya nu na mata Azra ce inuwar Azad itace kariyarsa, amma ba ta san ko wacece ba, har Aljani Mirza ya kasa gane wacece Azra,

ɓangaren Azad kuwa ya na falkawa ya ji jikinsa wasai ba kamar da ba duk lokacin da abin ya taso ma sa, idan ya samu sauƙi, sai jikinsa ya yi ta ciyon, tunuwa ya yi da yadda ya ga Azra da Hibba yadda idanunta su ka sauya komai ya dawo kansa kamar yanzu abin ke faruwa, wanka ya yi amma ya kasa samun sukuni har sai ya je ya duba lafiyar Azra ta shi ya yi ya nufe ɗakinsu, kwance ya iske ta ta na bacci ita kuma Hibba na gefe ta na karanta wani littafi da Aljani murufuf dawaz, ya kawo mata, gaba ɗaya sai ya ga Hibba ta yi ma sa kwarjini sosai amma ya basar ya nufe inda Azra, Hibba na kallonsa ta gefen idu hannu ya sa ya shafe gefen face ɗinta, hakan ya yi dai-dai da falkawarta ta na buɗe idu sai cikin na Azad sai kawai ya samu kansa da yi mata murmushinsa mai tsada wanda bayan mai martaba ba bu wanda ya isa ya gani, ita ma mayar ma sa ta yi wanda sai da fararen haƙoranta su ka baiyana,

hannunta ya kamo ya cire wani zoben zinari da ke hannunsa ya saka mata kana ya juya ya fita, ba ta re da ya ce komai ba, daɗi ne ya kama Azra da Hibba, Azra ta zo wurin Hibba ta ce "Gimbiya mai daraja ko ince Uwa ga Yarima shin ke ga kyautar da Yarima ya bani."

"Eh na gani Surukata, ke san Yarona akwai miskilanci sosai har ya dame ni ya shanye,
amma na san nan gaba kaɗan zai nuna miki SO amma bai zama lallai ya furta da bakinsa ba." Ajiyar zuciya Azra ta sauke kana ta ce "ina fatan haka ya maye min wani gurbi da na rasa."

sun jima su na hira har lokacin bacci ya yi kana su ka kwanta, amma sam Azad ya kasa samun sukuni har sai ya ji ɗumin jikin Azra,

ɓangaren Sarauniya Mulaifa kuwa ta koma wurin Boka Darbuzu, sai da ya koma aikata ma sha'a da ita kana ya ba ta wata laya ya ce ta samu dabbar da ba ta taɓa haihuwa ba ta tura mata layar ta kashinta sai ta kwana uku sanan ta fitar, ta yanke dabbar cikin dare ta saka layar cikin jinin dabbar kana ta jefa sama idan ta yi haka ta nemi baƙin kare ya kwanta da ita, idan har ta yi haka to tabbas Boka Shaldas zai dawo duk inda ya ke cikin daren, kana ta dowa gida, haka ko akayi ta yi duk abinda Boka ya sa ta har da baƙin karen ta samu, cikin daren Boka Shaldas ya baiyana,

ya ce "dama za ki iya dawowa da Ni amma ki ka barni sai azaba Ni ke sha hannun Aljanu.?"

"To ni ma ai na sha wahala kana na dawo da kai yanzu miye abin yi.?" "Yanzu dai zan koma halwar tsafina don akwai abinda na samo,
zuwa gobe zan dawo sannan ki sa afito da Yarinyar nan da ga gidan kurkuku saboda komai na iya faruwa, akwai wani babban abu ta re da yarinya ko na miki bayani ba ganewa za ki yi ba, amma zuwa gobe zan fallsa miki komai, idan na gama bincike, sannan ki haɗa ni da wata Buya don amatse Ni ke."


"To." Kawai ta ce ma sa ta kira wata Buya ta haɗa su su ka bar cikin Masarauta,

ta shige bedroom ɗinta da zumar gobe za ta sa afito mata da Azra:.......

Ko biyoni don jin yadda zata kasance
Idan Mulaifa bata ga Azra da Hibba ba

Shin za ta gano inda suke ita da boka Shaldas shin wacece Azra Yarima Azad zai baiyana ma Azra soyayyarsa zai aureta
Shin miye abinda ya sa Yarima rabin jikinsa
ya ke zama na aljanu

Kibiya kisha karatu, 300 kacal


YARIMA👑 AZAD 🤴

Hot love ❤️🌹
& romantic story 💋
Story & writes by
pinky Darling🌷

((Gimbiyar jajirtatu 👸💮))


I Love you lodi-lodi my dear friends Ina alfahari da ku

paid book 300 kacal wacce ta shirya biya ta yimin magana



Free PAGE

PAGE 9

******~~~~~~~~Washegari Mulaifa ta aika Sarkin gida ya taho mata da Azra, aiko aka neme ta aka rasa, hankalin Mulaifa idan ya yi dubu to ya tashi, Sarkin gidan kurkuku ta aika akira nan ta banbame sa da masifa, sai ya faɗa mata inda ya kai Azra da Hibba, amma ya kafe akan bai taɓa baɗe su ba hasali ma bai san ba su cikin gidan ba,


ta gamsu da maganarsa saboda ta san halinsa bazai mata ƙarya ba, sosai sa dakaru su bazama neman su Hibba ta tabbatar Hibba ce ta gudu da Azra, a haukace ta shiga neman Boka Shaldas, sai ga shi ya bayyana, shi ma a hargitse, ya na cewa "Mulaifa kinyi sake, abinda ake gudu ya faru saboda yanzu na yi iya yi na amma madubin tsafina ya fashe saboda ina son na gano inda su ke, amma tabbas su na cikin garin nan ko Masarautar nan."

"To yanzu miye abin yi saboda itace komai na mu idan har bata kusa to burinmu bazai taɓa cika ba.?" "Ni yanzu ta shin hankalina Yarima Azad ya samu wani ƙarfin iko, da iya wuya duk ba mu samu damar kwace wannan ƙarfin iko ba.... "Kai! ta ya aka yi wanda ba matsafi ba ya samu wani ƙarfin iko to waye ya bashi ƙarfin iko,sannan ina gudun ya fara gano shirin da muke akansa, don kasan yaron sam bashi da mutunci, ya yi mugun rainani, yanzu.?" "Ni ma ban gano komai ba amma kafin ya kai ga haka mu fara samo yarinyar kafin mudawo kansa, kuma bazai gano komai ba saboda sai ankoya ma sa yadda ake amfani da ƙarfin tsafin da ya samu."


"To yanzu ta ina zamu fara kasan duk wani ƙarfin tsafi da ni ke taƙama da shi naka ya fi nawa, saboda haka kai kaji ka gano yadda zamu karɓe wannan ƙarfin iko, ni kuma zan banciko su Hibba."


"To shikenan." Kana ya buga sandarsa ya ɓace,

ita kuma ta shirya bata zame ko ina ba sai wurin Boka Darbuzu, wanda duk abinda ke wakana tsakaninta da Boka Shaldas ya na gani, hasali ma shine ya fashe madubin tsafin Boka Shaldas, don ya na bukatar sheƙi ayarsa da Mulaifa, da zuwanta ta tuɓe kayanta ta koma haihuwar uwarta, yau da kanta ta rungume Boka Darbuzu, saboda ta na son buƙatarta ta biya, nan su ka shiga aikata masha'a yau ta gurzu hannun Boka Darbuzu,
kana ta buɗe baki zatayi magana ya da katar da ita ya ce "duk na san abinda ke faruwa tun kafin kizo, yanzu zan baki wani magani ki tabbatar ki zuba ma Yarima shi ga abinci indai har ya ci to wannan ƙarfin iko zai salwanta, koma na yi iya binciken da zanyi amma na kasa gano wanda ya ba shi ƙarfin iko na manyan Sarakunan Aljanu, wanda idan har ba gawurta kayi ba to ba za ka iya mallakarsa ba, sai abu na biyu Azra da Hibba na cikin Masarauta koma su na ɓangaren Yarima, idan har kina son burinki ya cika to ki bar Yarima ya auri wannan yarinya, idan har bai aureta ba to burinki bazai cika ba, karki yadda ki cutar da ita, muddin ki ka yi wani mugun abu akanta to burinki ba zai taɓa cika ba, har'abada."

Sosai ta gamsu da maganar Boka Darbuzu saboda ta san bazai yi mata ƙarya ba,
sai dai abinda bata sa ni ba shi ma ya na da na shi buri amma sai da ita burinsa zai cika,
magani ya bata kana su ka yi sallama ta tafi zuciyarta fes burinta zai cika,

ta na dawowa ta yi sa'a jekadiya za ta kaima Yarima abinci ta bata maganin ta zuba kana ta tafi, sosai Yarima ya ke jin ya damu da Azra ya na son ganinta kusa da shi ,

itama Azra haka yau kwananta biyu ba ta ga Azad ba ta yanke shawarar zuwa ɗakinsa,

koma Hibba ta bata goyon baya, wanka ta yi ta shirya kana ta nufe ɓangaren Yarima, ta na shiga Jekadiya na shigowa ta aje kayan abinci ta fita da sauri don kaima Sarauniya labari ko ta samu kuɗi,

cikin fargaba ta zauna kan sofa da ke gefen bed, ta na zama Azad na fitowa wanka:......


Ko biyo ni don jin yadda zata kasance
Taku har kullum Pinky Darling 👄
~Matar Jay~








👑YARIMA AZAD🤴

Hot love ❤️🌹
&
Romantic 💋💄

Story and writes by
Zainab Abdullah
Pinky Darling 🌷

((Gimbiyar jajirtatu 👸))

Free page ya ƙare duk wacce ta shirya biya tayi min magana 09033580667
______________________________________
https://chat.whatsapp.com/F7S7KjlbquBL30fuhZidFb
_________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
__________________________________________


*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
Allah ya ƙara haɗa kanmu


Bismillahi Rahamanin Raheem 💫

Paid book


Free page

Page 10


_____ Kallon juna su ka tsaya yi ya na mamakin me ya kawota ɗakinsa, ita kuma tsoro ne ya mamaye ta ta na jiran ta ji ya yi mata tsiwa, amma sai ta ji shiru, shi kuma banza ya yi da ita, ya cigaba da shiryawa, kamar bai san da mutum ɗakin ba, ita kuma Azra kallonsa kawai ta ke yadda ya ke komai cikin, natsuwa kaya ya ɗauko zai sa ka, amma ya ga bata da niyar fita, shi ko bazai yi mata magana ba, gabanta zai sa ka kaya, yau zaiga ƙarshen rashin kunya, janye tawol ɗin jikinsa ya yi ai da sauri Azra ta runtse ido ta fara lalabar hanyar fita amma idanunta rufe,
ba zato ba tsammani, ta ji ta yi karo da mutum, ta na lalabar hanya 😂 shi kam Azad suman tsaye ya yi saboda bananarsa ta riƙe ya kasa ko da mutsin kirki, ita kuma jin kamar ta riƙe wani abu kamar sanda da sauri ta buɗe idanu, a'razane, ta sa ki abin ta ja baya hadda sai da ta faɗi gefen bed goshinta ya tavel ɗin da ke wurin, da sauri ya ɗauka tawol ɗinsa ya zo ya ɗaga ta ya na duba face ɗinta ya gani ko taji ciyo, amma kumbura wurin ya yi kaɗan hannu ya aza wurin ya na luddawa wata siririyar ƙara ta sa ki ta re da shigewa jikinsa, wani shokin su ka ji ajinkinsu,

saboda wanna shine karon farko da jikinsu ya taɓa haɗuwa wani baƙon ya na yi ya ziyarci Azad, sai da ya tattara na tsuwarsa kana ya ida kudde mata wurin, ya ta shi, bai ce mata komai ba, sa ka kayansa ya feshe jikinsa da turaruka ma su mayen ƙamashi, saman sofar da ta ta shi ya zauna ta re da jawo laptop ɗinsa ya fara dubawa, ko kallonta bai koma yi ba,


takaici ne ya sa Azra ta shi ta bar ɗakin, ta na ta masifa da Azad cikin ranta wato shi bazai iya yi mata magana ba, ai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On YARIMA AZAD
avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Much appreciated

avatar
khadija-muhammad-ibrah

2 months ago

Reply

Very good

Please Login or Register in order to submit comment